Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fashe. Na ce to. Na saka layi na sa katin na shiga ɗaki na kira wata Number ɗaya daga cikin lambobin da ke jikin wani kati da ya sako a ciki kwalin. Wani ya ɗauka, nace Aliyu nake nema. Yace mai gida baya nan ya yi tafiya. Nace Shamaki fa na ke tambaya? Yace nima shi nake magana ya tafi China ɗazu. Na ja tsaki sannan na kashe waya, ina faɗin Ni Aliyu na ko filin jirgi baya zuwa bare wata China. Na sake ɗakko katin don in duba wata Number. Sai naga ya yi wa wata lamba alama da biro a ƙasa ya rubuta ki kira wannan layin. Cikin sauri na saka na kira. Ya ɗaga "Baby zan kira ki kinji?" Na ce to Yaya na gode, ina jira fa ka kira ni fa. Yace karki damu. Haka dai abubuwa suka ci gaba da tafiya, iyayena suka tada hankali gurin neman kuɗin da za a yi min kayan ɗaki aure saura sati uku da 'yan kwanaki. Umma ta sanar da Baba har Kurna taje,Baba tace Allah ya sa hakan ya zama alkhairi, abinda za ayi yanzu zata sa akama Awakinta guda biyar a saida su, a zo a karɓa a sai min kayan kicin kuma zata sanar da sauran dangi. Shi kuma Abba an sanar da dangi sun nuna murna amma da suka keɓe sai ƙanwar Babanmu Saratu wadda dama basa shiri da Umma tace "Shi Abbana su Babyn da ya kama ya sa rana sati huɗu kila ya tanaji kuɗin da zai yi mata kaya da na abinci da za a dafa. Dija tace Nima dai na yi mamaki muna neman gudunmawar sauka mu bashi, shi kuma ya na tataro aure abinda Allah ya ba ni shi zan bada. Saratu tace ita matarsa dan hauka gata da tsohon ciki shine ta yadda da wannan gangancin koda yake ƙila ma ita ce tace a saka dan a ce yar ta ta riga 'yay'anmu aure. Dija tace ko wane kwashe ne kuma zai ɗebi wannan yarinyar kamar taɓarya oho. Matar waliyin ta taɓa baki tare da faɗin jiya da na shiga murna ai na ga 'yar da wata ƙatuwar waya wai saurayin ya aiko, shiko Abban su Zuhra sai rawar kai shi ga waliyyi nace dubu goma dai ya baka abikin Ummi dan haka sai ka nemi shabiyu kar kaji ance waliyyi ka fara neman siyan gado. Suka sa dariya gara dai ki faɗa masa dan ga sunan riɗa riɗa duk wadda ta samu shima hidimar ce a gaban sa. Haka suka yi ta maida zantuka ta re da alwashin zura ido su ga abin da zai biyo baya.
Har kwanaki biyu ina jiran kiran Yaya, Ni kuma inna kira bata shiga. Hankalina duk ya tashi amma babu dama inyi maganar sai Jamila kawai inna faɗa mata sai ta ce bani da aji wai in jira ya kira ni. Ranar kwana na uku ina zaune a kan tabarma a tsakar gida ina rubuta sunayen waɗanda zan kaiwa katin sauka 'yan uwa da yan makarantar bokonmu. Jamila na ke kira ta raka ni. Umma tace to kuma yaushe za ki kai na 'yan Kurna? Nace sai mu kai ranar Lahadi ko asabar tunda bata da Boko sai muje. Umma tace hakan ya yi saura ku kuma zuwa wani gidan nace imsha Allah babu inda zamu ƙara zuwa. Wayata ta soma kiɗan na ɗauka da sauri. Sanyin zuciyata, haka na rubuta a lambarsa. Na tashi na shiga ɗakinmu. Na ɗauka da sauri. Cikin shagwaɓa na ce sanyin zuciyata shine ka ƙi kazo ko? Yace "My Baby ki yi hakuri tafiyar gaggawa ta taso min." Nace na kira wata lamba aka ce ka tafi China . Yace a a Kaduna na je ina can har yanzu aka wasu kayanmu. Nace to Allah ya tsare shiyasa nace ni Aliyuna ko filin jirgi bana zaton ya taɓa zuwa. Ya yi dariya "Na taɓa raka maigada ba so ɗaya ba ma. " Nace Allah ya sa kai ma wata rana in raka ka. Yace "Ameen Allah ya sa mu hau jirgin tare. Na ce ameen. Ya ce "To ya ake ciki menene labari?" Nace wanne zan baka?" Yace "Sabo wanda ya ke tashe." Na ce kati zan kai in raba na sauka in Jamila ta dawo. "To kuma na bikin yaushe za araba?" Ya katse ni. Kaga karka wani damu da katin Biki duk kashe kuɗi ne, karatun saukaramu asabar ne ɗaurin aure Lahadi sai a faɗawa kowa a haka. Yace "Taɓ aurenmu ace ba kati Baby ko bashi ne ni zanci don in buga mana katin biki." Don Allah karka ci bashi a zo ana sallama da kai. Na faɗa cikin shagwaɓa. Yace "Ai misali na yi.
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo evidence ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 8*


Abubuwa sun kankama lokaci yana ta ƙaratowa Munafinci ba ga maƙota ba ba kuma ga dangi ba. Umman su Fati har gida ta zo wai Allah ya sanya alkhairi amma harda cewa Umma ashe ku da tanajin ku,auren Fati sai bayan Babbar salla mu masu ƙaramin ƙarfi. Umma tace Allahn da ya kawo mijin a lokacin da masu gori suke gori shine zai kawo abinda zamu kai mata. Ina jinsu Umman su Fati aka wuce ana borin kunya. Umma tace Allah kai zaka yi mana wannan lamari Allah ka taimake mu. Sauran kwana huɗu walimarmu kwana biyar kuma a ɗaura mana aure. Yaya ya aiko min da katan Lemo guda biyar wai na walima a daran ranar ne ya zo gurin Abba ya nemi alfarmar a ɗaga aurenmu zuwa wani satin. Walimarmu da sati ɗaya kenan. Abba yace ba damuwa, ya shiga ciki ya sanar da Umma sannan ya ce in fito. Mun gaisa yake faɗa min wai gyaran banɗakin gidan za'ayi shine dalili. Na ce to Allah ya kaimu, amma banso haka ba,yace kamar yau ne. Yanzu ki faɗa min me da me kike buƙata a gurina. Na dube shi, kamar na me? Yace "Kuɗin lalle da pati ko baza ki yi ba?" Nace zanyi amma kana da kuɗin ne? Yace Inkinji makaho yana cewa a yi wasan jifa ai ya taka dutse ne ko? Ki lissafa min duk abinda ki ke so na biki zan miki daidai ƙarfina." Nace to kana son mu kira DJ ko baka son kiɗa? Ya yi 'yar dariya. Kinga Baby zan kama miki ɗan wuri ku yi party da ƙawayanki amma banda maza." Na zaro ido karka matsa wa kanka, kila Abba ma ya ce baza a fita party ba. Kawai zan yi DJ na a can filin,na nuno mishi da hannu. Ya kalli gurin "Shikenan zan sa a zo a sa kujeru." Na ce to na gode Ubangiji Allah ya bada yadda za ayi. Yace Ameen ina jin daɗin addu'o'in ki. Zan tafi ki tura min sauran abubuwan ta text,sai in kawo miki ko?" Na ce to yawwa dama zan tambaye ka ko zan iya buɗe Whatsapp? Yace wannan ki bari sai an kawo ki zan buɗe miki da kai na." Na yi murmushin tare da faɗin na gode. Na ce yawa jira ni ina zuwa. Na shiga gida da sauri,na ɗakko katin saukarmu na ɗakko na kawo masa, nace ga shi don Allah ka zo, tunda ma an ɗaga bikin ai dai zaka zo ko? "Insha Allah zan zo, ki shiga gida zan aiko miki da katin auren shima sai na party ki rubuto min yadda ki ke son ya kasance." Zan yi magana ya ɗaga min hannu,kar ki ce komai shiga gida." Na ce to sai da safe.Har na juya yace, yawa na tuna "Baby!" Na waiwayo, ki faɗawa Abba za a kawo lefe zuwa jibi." Zan dawo ya kuma cewa shiga gida kawai." Dole na wuce ina waiwayen sa. Fatana Allah ya sa ba bashi zai ci ba.
Jamila sai murna su ke yi ita da Ummu za a.kawo lefe, ni kam ba ta wanna na ke ba,ɗaga bikin shine abinda yafi komai bani takaici. Saidai ba ni da damar in yi maganar da wani, tunda duk ba su fahimta ta. Ashoben Walimarmu shi aka maida ashoben biki wannan ɗagawar sai ya bada damar zuwa a siyo musamman 'yan uwa da 'yanmatan lungunmu waɗan da suka bayyana kansu a matsayin ƙawayena harda su Fati. Kullum sai sun shigo muna tattauna yadda za ayi party. Tare da taimakon Jamila na rubuta wa Yaya abubuwan da nake buƙata. Kuɗin lalle da wankin kai. kuɗin Party kuɗin kwalliya. Ina tura masa ya rubuto cewa,kin manta da na gyaran jiki. Na yi 'yar dariya shidai Yaya baya rabo da ɗorawa kansa ɗawainiya. Umma ta tashi hankalinta game da kayan ɗaki da safe ta aiki Jamila a kira mata aminiyar ta Umman Amina. Jamila bata jima da da wowa ba Umman su Amina ta shigo, ina jin su daga ɗaki Umma tana faɗa mata zancen kawo lefe, ta ce tunda sunyi lefe maganar kaya katako muma dole mu dage ko ba masu tsada bane. Ummansu Amina ta ce, "Haka ne, dama abinda yasa na ce abar batun kayan katako a sai ka tifa da kayan girki saboda ya ce ba matsala kuma ba shi halin lefe akwai wata mafita guda ɗaya in har Abban su Baby zai yarda, akwai masu bada taimako na kayan ɗaki wani foundation mai suna Zeena. Umma tace ina jin su a Radio suna yi wallahi. Umman su Amina ta ce Da sai a rubuta takarda a tafi da yarinyar a kai musu in so samu ne yau ɗinnan. Umma tace ai damuwar da ƙyar Abbansu ya yarda Umman su Amina ta ce " Akwai mafita, Baby ba tana nan ba, tazo yanzu in faɗa mata abinda zata rubuta ni sai in sata a gaba mukai takardar." Na ɗan zaro ido a inda nake a laɓe, Zeena sune waɗanda Yaya ke yiwa yaron shago fa. Ƙwalamin kira Umma ta yi, na amsa naje a kace in ɗako takarda da biro na ɗakko. Muka zauna Umman Amina tana faɗamin ina rubutawa. Neman taimako ne dan Allah an saka bikin har ana ta ɗaga wa saboda. ba'a samu kayan ɗaki ba, har ma maganar tana nema ta lalace. Wai in sa cewa ni marainiya ce. Sai na rubuta iyayena basu da hali gashi an saka auren kusa. Da na gama aka sa lambar wayata da ta Umma. Ummansu Amina ta ce shirya maza bari inje in barwa Amina sallahun girki, tana fita nace A
Umma Hajiya Zeena ita ce Uwar ɗakin Yaya fa, Mahaifiyar mai gidansa da muka je. Tace "Tofa!" Wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa, bari ta zo inji ya za ayi." Data dawo Umma ta faɗa mata halin da ake ciki, sai ta ce ai mu ofishin su na Foundation ɗin zamu je,baza su sani ba ma bare yaji labari. Muka hau Adaidaita sahu zuwa titin Ɗanbare muka je wata Zeena plaza mun shiga ofishin muka gaida wadda muka samu, sannan muka faɗa mata buƙatarmu tace yaushe ne bikin mukace kwana shabiyu, ta ce shine zaku kawo takarda yanzu? Umman Amina ta ce 'yarnan ku yi haƙuri da muna sa rai cewa zamu iya sayen kayan ne sai kuma muka ga ba wata mafita. Ta amshi takardar ta buɗe ta karanta,ta yatsina baki, ku ba ma marainiya ba ce kenan? Kuma gashi babu sa hannun ta bare na mahaifinta. Umman su Amina ta lankwashe murya kamar marainiya tace mana a taimaka mana. Matar ta ce gashi nan an rubuta iyaye na basu da ƙarfi." Umman Amina ta kalle ni, na sunkuyar da kai, tace Hajiya ita ce ta rubuta bata iya rubutun bane a taimaka. Ta yatsina fuska. "Sai ku haifi yara ku kasa amfana musu komai,Hajiyar bata shigo ba,in ta shigo zan bata amma bana sa ran zaku samu domin an cire list na wannan wata." Ta kalli Umman Amina "Kamar kun bada ajiya sai a ƙurarren lokaci irin wannan." Umman Amina sai haƙuri take bata tana roƙonta, ita kuma sai yaɓa mana magana ta ke yi. Baƙin ciki kamar in fice ko in hau matar da duka,ta kalle ni, wannan ce mayar kenan Umman Amina tace ita ce. Ta taɓa baki. "Kada kiji haushina yarinya laifin iyayenki ne, zan bawa Hajiya takardar ku in ta shigo suma suna da bikine bata zuwa sosai. Nan dai mukayi godiya muka fice.
Na ce da Umman Amina wallahi dama a kyale su, dubi yadda sai wulaƙanci ta ke mana. Umman Amina tace ai haka suke irin waɗannan aiki fa aka ɗauke ta karɓar takardar neman taimako, amma sai kace itace ta ce zata bada sai irin wannan rashin mutunci ta ce yi.
Umma bata faɗa wa Abbanmu ba, musamman da taji rashin tabbacin abin. Umman Amina tace in shirya in raka Amina kasuwa zata sai anko da mayafi. Nace to sai dai muje da kyalle tunda mu namu a gurin Safara aka siya. Tace bana son kayan Safara dan zata bada bashi saita Linka kuɗin ga rashin haƙurin bashi. Nace Umma da da kuɗi da kin bada na Jamila da yadin da kika ce zaki sai wa su Jafar da Habu. Tace sai in bada a kuɗin gudunmawar da 'yan Kurna suka aiko jiya, Allah ya rufa asiri kar in Lodi bashin Safara bayan biki ta uzzira min naji da naki saura dubu biyu da naira hamsin. Nace to maje gobe,ranar da za 'a kawo lefena kenan. Gidan su Zuhra za akai, gidan wan Abbanmu. Na shirya nasa doguwar baƙar riga da mayafi Amina ta zo har zamu wuce Umma tace kije gidansu Zuhra jiya Ummansu ta aiko tana tambayar inda za a samu anko.
Muka biya, nan "yan matan gidan aka taso, amarsu mai magar zuma, yau zamu sha lefe. Na ce ku ta lefe kuke. Ina Umma zamu kasuwane sayen anko. Murja tace Zuhra ce zata siya. Umman su ta fito muka gaisheta,ta taɓe baki, "Kaga 'ya'yan aminai to Zuhra ta baku saƙo ko kuwa ta biku?" Nace ta zo muje mana tafiyar zata fi daɗi. Dama tsararmu ce Tare mukayi Candy sai dai makarantarmu ba ɗaya ba, domin su ta kuɗi suke zuwa kasancewar Abbansu ya fi namu ƙarfi.
Muka hau adaidaita muka nufi kwari nace kai gabana sai faɗuwa ya ke yi, bansan ina ne gefen su Yaya ba, fatan karya ganni,sai ƙara kaɗe ƙura nake. Muna ta yawo sai wani ya amshi kyallen yace wannan kayan Zeena plaza ne. Gabana ya faɗi. Na tsaya cak, nace bari in baku kuɗi kuje ku siyo harda ta Jamila. Zuhra tace "Me yasa?" Nace a ɗaya daga cikin irin waɗannan kantunan ya ke yaron kanti. Amina ta ce to ai ba lallai shi a wannan yake ba. Nace to muje. Muna shiga wanda ya kawo mu ya tambaya ko akwai sauran wanna kayan?" Wani ya amsa ya duba yace akwai, muka shiga ƙaton kantin wani yace mu zauna a kawo mana saboda nan ba a bada ɗai ɗai sai dozin bari ya karɓo a ɗaya shagon.
Shamaki ya ɗaga robar ruwan paro ya sha ya aje yana sake juya katin hannun shi, ko shakka babu wannan katin daga makarantar su Baby aka kawo masa gayyata da kuma takardar neman taimako. Yanzu a yaya zaije, ya mata alƙawarin zaije mata yaga karatunta kuma zata so ta ganshi a gurin ƙila ma har ta nuna wa ƙawayen ta cewa ga wanda zan aura. Sannan a ɗaya gefen Hajiya bata son yana wasa da zuwa irin waɗannan wuraren da ake bawa Allah rance. Ya kuma ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe ido dan neman mafita. Ya buɗe idanu ya zuba a kan fuskar laptop ɗin dake gaban shi wadda ta ke hasko mishi ko ina na Kantin sama da ƙasa. Ya tsura ido akan wasu 'yan mata dake zaune kan wasu kaya. Ya ɗauki wayar kantin ya danna kira Ɗahiru ya ɗaga, yace suwaye zaune akan kayan nan wasu "yan mata su uku?" Yace Atamfar nan mai ganye suke so, Hassan yaje kawo musu. Shamaki ya ce in yazo kace ya zo ina kiranshi kafin ya sallame su.

Zungureriyar motar ta tsaya a ƙofar gidan Yayan Abban su Baby, Bala direba bai manta gidan ba,dan haka ya fito yace bari ya yi sallama. Wani saurayi zai shiga gidan Malam Bala yace, yaro, dan Allah in kashiga ka yi mana sallama da mai gidan. Tare suka fito domin yasan da zuwansu bayan azahar kamar yadda Abban su Baby yazo ya sanar da shi tun jiya, dan haka ma bai fita ba, kuma ya sanar da ƙaninsu da kuma maƙotanshi kamar yadda suka saba duk lokacin da wani a cikinsu zai karɓi kaya irin haka. Suka gaisa da Malam Bala, sannan ya dubi yaronsa da ya yi sallama da shi, yace Halifa a fito da tabarmi ga baƙin sun iso bari kira Malam liman ya danna kiran maƙocin nasa yana faɗa musu sun iso, dama da suka yi azahar ya tuna musu. Ya kira Abban su Baby ya ce,kazo sun iso, ka taho da ruwa da Lemon kar ka manta. Nan suka hallara sai aka buɗe kujerar baya aka soma fito da akwatuna na zamani haka ma but ɗin motar. Guda shidda ne masu kyau daga gani an zuba kaya masu tsada. Abban su Zuhra ya ce, ba sai an buɗe ba, Allah ya sa albarka ya bada zama lafiya. Suka ɗakko ruwa katan biyu Lemo katan biyu suka ce gashi. Har kawun Aliyu yace su barshi,sai Abban su Zuhra ya ce, ko dai ya yi kaɗan ne?" Suka ce a a haba ba haka bane, Liman da suka zo dashi ya ce a karɓa Allah ya sa albarka.
Suna tafiya aka shiga da kaya ciki dama su Umman su Zuhra suna ciki sun ƙosa su gani koda abin arziƙi ita da yaranta. Nan kuwa jiki yayi sanyi domin Atamfa tirmi talatin ce ga lesuna ga Shadda da dogayen riguna abin dai na girma. Suka haɗa kaya suka aje,tace Hajara kije ki cewa Umman su Baby azo a ɗauki kayannan. Abbansu Zuhra ya ce, ina za a kai su tun yanzu, a bari mana 'yan uwa su gama gani." Tace a a kar wani abu ya ɓace gani da 'yar mata a zarge su, gara akai can kowa yaje can ɗin ya gani.
Ta ƙwarzaba dole yace su Halifa su ɗauka su kai. Suma 'yan lungu suna ganin ana shiga da akwatuna, nan da nan labari ya karaɗe kaffatanin lungun an kawo lefen Baby. Umman su Baby ta aika Jafar ta ce ya kira mata Umman Amina. Itace ta saka ido akan kayan saboda maƙota sun tsaya sai sun gani ba iyayen ba ba yaran ba. Kowa ya sha mamakin kayan Umma kasa magana ta yi saboda tunanin ta kayan ɗaki, suma sun fita kunya,ko da yace baya so shi dai a shiryen sa yake.
Bayan mutane sun watse Umman Amina tace, gaskiya wannan kaya babu batun haƙura da kayan ɗaki. Tashi za kiyi mu koma can gurin tallafi in ba haka ba za aji kunya. Umman su Baby ta ce sai gobe dai yanzu su Baby basa nan ga kayan mutane. Umman Amina tace "To goben dai ya zama da wuri fa insha Allah kamar ƙarfe goma.

Jamila ta yi ta murna da ta dawo makaranta ta ga lefe tace amma gaskiya Yaya Aliyu da tanadin sa, dubi kaya kamar kati!" Umma tace gaskiya ya bada mamaki ya yi mamaya.

Muna jiran mai kawo mana zani, jim kaɗan sai gashi muka karɓa muna dubawa,ya faɗa mana kuɗin. Cikin mamaki na kalli Zuhra kinsa Safara dubu da ɗari biyar ta ɗora akan duk turmin atanfa ɗaya. "Amina tace shiyasa Ummanmu bata yarda da siyan kaya a gida." Zuhra tace dubu da ɗari biyar ta isa ayi ɗinki. Yaron ya katse mu ga ruwa. Ya miƙo mana ruwan Paro mai sanyi. Nace harda ruwa ku ke bayarwa? Yace mai gida yace a baku don daga gani kun gaji. Zuhra ta kalli wanda ke kan teburin a zaton ta shine mai gidan ta ce mun gode.Sai nima na dube shi nace Allah ya saka da alkhairi. Na basu baya ina shan ruwan kamar yadda suma suka nutse a shan ruwa.


🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 9*


Na tuna da yadin su Jafar na cire robar ruwan daga bakina, na dubi wanda dai ya kawo mana atamfar nace, don Allah kuna saida yadikan maza masu sauƙi haka ko shadda irin ishirunka maraya ɗin nan? Yace "Bama sai dawa sai kun koma kan wannan layin nan."
Nace wai gashi mun gaji kyanshi daga nan mu fita. Na zaunen ya ce Ɗahiru zo mana. Yaje, jim ya dawo ya ce ƙanwata kawo a yanko miki yadin, nawa ne kuɗin kuma wace kalar kike so? Nace yadi huɗu ne kala kuma irin dai ta maza ƙanne na za a ɗinkawa. Ya amshi kuɗin ya fita. Abinda ya faru shine Shamaki ya tattara duk wani kallonshi ga motsinshi akan Baby data yi magana sai ya bugawa Hassan waya yana tambayar shi metake so, sai ya sanar dashi, sai yace ka sa Dahiru ya amshi kuɗin ko nawa tazo dashi ya je can shagon ya ɗakko mata shadda yadi biyar,amma karya sake ya ce mata komai, ya bata kawai ya amshi kuɗin. Hassan cikin mamaki ya ce,to Allaji. Muna zaune ya kawo shadda mai kyau, nace gaskiya wannan ta yi sauƙi, amma ka duba ko nawa na baka kuwa? Yace "Na gani ita kaɗai ta rage shiyasa aka bar miki a haka." Nace to mun gode. Muna fitowa bakin shagon sai ga wani mai adaidaita kamar mai jiranmu, nace ɗan agundi. Yace "Dai-dai ina?" Amina tace ko bakin ƙofa ma sai mu ƙarasa. Zuhra ta ce nawa zamu baka? Yace "Ku hau muje kawai. Muka kama hanya. Sai dai yana sauke mu ya wuce wai mubar kuɗin. Muka cika da mamaki sannan muka masa godiya tare da hasashen ko wata ya ke so a cikinmu, amma me yasa bai tambayi lambar waya ba. Haka dai muka wuce zuwa gida muna al'ajabin ɗan sahu. Tun da muka shiga lungun yara suke bamu labarin wai an

Please Login or Register in order to submit comment