Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ci amanar su, zan faɗa musu gaskiya in mun koma. Yace ba wata matsala ko da baƙi faɗa ba,amma zaki iya faɗa in kina ganin haka zai fi sama miki kwanciyar hankali. Kuma za a turo gobe,sai ki sanar dani nan gidan zan kawo su ko kuwa wani gurin ne daban." Nace zan yi magana da Umma sai in faɗa maka duk yadda suka ce. Ya sauke mu ƙofar gidan Baaba ya bamu dubu ɗaya ya ce ku ba Baaba ɗin kafin inzo. Jamila ya miƙawa ta amsa tana godiya Nima na yi masa godiya muka shiga ya juya.
Hajiya ta jingina ta lumshe ido duk wanda ya kalleta zai yi zaton bacci ta ke yi,amma kogin nazarin yarinyar ta faɗa. Ko shakka babu ta lura yarinyar ta na da kafirin wayo, ta goge laifin dana so ɗorawa iyayenta ta maida shi a kanta,har da wani kukan kirsa wai ita ga mai imani, sannan ta bata mamaki yadda ta ƙi amsar komai dan haka ta fasa bata kyautar da ta yi niyya. Ba shakka ta cinye jarabawar da take son yi mata saidai tsaron ta wayon "yar ya girmi shekarunta.Kome ma Shamaki ya gani ita ba sharaɓa ba, ba ƙirjin kirki ba, kuma a fuska ba wata mai kyawun a zo a gani ba. Ta ke ta tuna da dabino da ya ci ta tashi zaune da sauri,a zuciyarta tana rayawa tasan ba matsala tunda yace dan ita aka yi shi.Amma dan ta kore kokwanto sai ta ɗauki waya dan taji ta bakin Malam.
Suka gaisa ta sanar da shi matsalar da aka samu. Ya ce "Subhanallah Hajiya ya ki ka bari ya ci." Tace ban ankara ba malam sai da ya kai na biyun kuma gashi a gabanta ba dama ince ya zubar,dole zata tuhume ni akan me yasa ita na bata. Malam yace sunansa da nata aka yi aikin gashi aikin mai ƙarfi ne, sirrin Ya wadudu ne aka haɗa da basmala ƙafa dubu talatin da wasu haɗe haɗe. Wani mutum da muka yi masa irin aikin nan matar bata son shi Allah da ta ci Dabinon duk inda zashi binsa ta ke, kuma da Allah ya yi masa rasuwa a maƙabarta ta tare. Gaban Hajiya ya faɗi, to kenan gara da bata ci duka ba, yaushe zan so ta zame masa jela ko ina ya saka ƙafa ta mayar. Damuwa ta yanzu shima kenan zai ƙara sonta? Malam yace mu dai jira muga hukuncin Allah,amma dai ki yi addu'a aike mahaifiya ce harshen ki yafi komai. Tace to shikenan, addu'a a kai muke Allah ya yi mana mafi alkhairi. Suka yi sallama ta miƙe domin yin alwallar azahar.
Jamila ce ke baiwa Baba labarin Yaya Aliyu, sai murna take. Ta bata dubun daya aiko mata,tana ta addu'a muka yini har la'asar list munyi mata wanki da kwalemar gidan taji daɗi tace dama ko yaushe ina ta fatan kuzo duk cikin jikoki na kune kaɗai masu yi min irin wannan ƙoƙarin Allah ya baku miji na gari. Mun tarar umma har ta gama tuwon dare nan na amshi aikin miya Jamila ta kama shara ranar dai munyi fashin Islamiya. Da dare muna cin tuwo Jamila ta ce ""Yaya Baby ina ta tunawa da kayan alatun nan yawuna har tsinkewa ya ke." Nace ko ni wallahi amma ke baki so ci bane, ni kinga ba dama inci. Tace "Itama Hajiyar bata so mu ci ba, ai da ta so muci sai ta bamu guri ko ta sa a kai mu falon farko. Na ce taɓ wannan kinga ta yi kama da wadda zata tashi?"Umma ta katse mu da faɗin wacece? Muka kalli juna. Na ce Umma dama zanzo in kawo kaina, na yi muku babban laifi,dan Allah ku yafe min. Na tsame hannu na a tuwon na zo gabanta na zauna na zayyana mata duk yadda abin ya faru. Ta min faɗa sosai kuma ta jamin kunne akan kar mu sake aikata makamancin irin wannan kuskuren. Tace bazata faɗawa Babanmu ba,har ma ta ce gashi munja mata tana yiwa mahaifinmu rufarufa. Na ɓoye mata wasu tambayoyin da Hajiya ta min wanda nasan zata ji babu daɗi.
Cikin dare ina tsaka da bacci sai naji kamar an tasheni, ina farkawar sai na tsunduma tunanin Yaya take na samu kaina da tashi na nufi ɗakin iyayena na tura ƙofar na kalli gurin da nake zaton wayar Umma na ganta kuwa a caji na ciro Abba da ke kwance a ƙasa kan tabarma yace "Waye nan." Take na firgita nace Abba ni ce ban ɗaki zanje haskawa zanyi da wayar Umma. Yace kwan dake banɗakin ya mutune? Nace babu haske dai. Yace "Ɗauka kije." Banɗakin na shiga na kashe hasken sannan cikin rawar jiki na soma neman layin Yaya. Sai a kira na shida sannan ya ɗaga. "Baby lafiya?" Ya tambaya cikin yanayin bacci da kiɗima,. Na ce lafiya lau Yaya, na kasa bacci ne tunaninka ya dame ni. Goben za'a turo ɗin? Cikin matsanancin mamaki yace kije ki kwanta zamu yi magana da safe,na samu kaina da faɗin Yaya ina sonka sosai kaji? Ya ce "Naji Baby na yarda." Nace to kana sona? Yace sosai Baby. "Kije ki kwanta." Nace to Yaya. Na fito na je na maida wayar sannan na kwanta. Ji nake in har banga Yaya ba zan iya rasa rai..A wannan ranar dai ban samu bacci ba. Shamaki ya zauna cike da mamaki yana son ya ƙaryata kanshi cewa Baby ce, kodai ta gane shine Aliyu Shamaki,inhar ta gane to ba shakka zai fasa aurenta duk da irin son da yake mata. Ya soma tunanin abinda ya faru tun daga zuwanshi gidan har tafiyar shi,shin ko yayi wani abu ne ba daidai ba har ta gane. Yakasa tuna hakan,to ko Hajiya ta faɗa mata. Koda ya dawo kai su abinda Hajiya ta ce mishi kawai ka sanar da Alhaji Umaru da kawunka gobe za a tura kamar yadda kake buƙata. Harya tambaye ta ko yarinyar ta cinye jarabawar ne? Tace "Kayi abinda na ce kawai." Ya numfasa bayan ya gama tuno da komai.To


🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a tura shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 7*


Nayi sallar asbahi duk na rasa me ke min daɗi na koma na kwanta sai bacci ya kwashe ni. Jamila ce ta tashe ni tana cewa, baza ki makaranta bane Yaya Baby. Umma tace kar a tashe ki ƙila bakya jin daɗi ne, saboda ta tabbatar in har ki ka koma bacci baya sallar asbahi to baki da lafiya. Na yi miƙa Yaya yazo ne? "Wanene kuma Yaya?" Ta tambaye ni cikin mamaki. Yaya Aliyu mana ko mafarki nake yi ne? Har ma yace a ɗaura aurenmu kawai. Jamila ta saki dariya "Don Allah Yaya Baby ki tashi nikam." Na tashi naje na gaida Umma ta ce Abba ya fita, na ce kuma kin faɗa masa yau ne 'yan gidan su Yaya zasu zo?" Ta ce "Na faɗa masa tun juya da kika faɗa min,.amma kin faɗa masa cewa gidan su Abban Zuhra za su kai kuɗin ko? Kuma Abbanku ya ce,ki tambaye shi ƙarfe nawa zasu zo?" Nace to bani wayar ki in faɗa masa. Jamila ta fito ɗauke da jaka tana faɗin Wallahi bazan jira ki ba,gara ke jarabawa ki ke yau ne ma ƙarshe. Sai lokacin na tuna da batun makaranta. Nace dan ma dai daga yau na gama. Sai da na shirya sannan na ɗauki wayar zan kira amma ba kati,gashi bashi ne cankas a wayar. Na Umma ko kati za'a siyo? Tace "Wa zai siyo kunyi latti ki tafi in kin dawo kya kira shi,abinda nasan bai wuce da daddre za su zo ba, tunda gari ɗaya ne." Na ɗauki biro bana zuwa da jaka tunda jarabawa ce muka wuce.

Hajiya ta kalli Shamaki, "Ƙarfe nawa zasu je su kawun naka?" Ya saki fara'a sai da dare in kowa ya gama sabgar sa bayan sallar Isha'i. Tace "To nawa za a kai?" Yace dubu Hamsin kinsan bana son ta san komai da wur ne. Tace "Akwai gejin da dole su sani, tunda za su yi bincike." Yace haka ne,amma kafin lokacin na samu abinda na ke so. Bayan sallar Isha'i Shamaki ya kwashi su Ƙanin Hajiya da kuma ƙanin mahaifinsa sai limamin masallacin gidansu suka nufi kai kuɗi, saidai tun a hanya ya ce musu ba zai ce suyi ƙarya ba, amma yana son kar su nuna shi mai arziki ne ya faɗa masu komai a taƙaice da kuma dalilin sa. Suka ce insha Allahu za su yi yadda ya ke so. Ya ɗauki waya zai kira layin Ummarsu. Sai lokacin yaga miss call da yawa, ya yi mamakin ina ya jefar da wayar har da Baby ta yi masa wannan kiran haka. Ta ɗaga wayar ya ji muryarta can ƙasa, ta gaishe shi, ya amsa tare da tambayar lafiya ya ji muryarta haka. Tace banajin daɗi ne, yace ashsha sannu, kin sanar da Abba mun kusa zuwa kuma nan gidan zamu zo? Ga mamakin sa sai ya ji tace dan Allah kun taho?" Ya ce kinsan abinda za ayi wasa daban ya ke ko?" Tace dama kiran da nake maka kenan ɗazu dan in faɗa maka Abba ya ce gidan wansa za a je,amma babu nisa daga nan gidanmu bari in kira Abban a waya ya fita yanzu." Yace "To faɗa mishi gamu tafe a hanya. Naje da gudu gurin Umma,nace Umma Yaya sun taho da iyayensa. Tace I kon Allah! Wai kuwa Baby lafiyarki ƙalau yau wane irin hali kika canza ne?" Na ce yi haƙuri Umma. Na koma gefe na tsaya. Umma ta ce sai ki kira Abban naku ki sanar da shi. Jiki na ɓari na kira Abba na faɗa masa. Yace gashi nan dawowa gidan.
Shamaki ya sanar da su wakilan nasa cewa su faɗawa iyayen yarinyar nan yana son auren ne a lokacin walimar saukar karatunsu. Direba ya sauke su bakin lungun ya tambayi Shamaki ko ya jira su? Ya ce e ka jira mana sai ka kai kowa gida sai ka dawo ka ɗauke ni. Yace "To" Abbansu Baby ya fito ƙofar gida ya tari su Shamaki yace ku zo muje can ayi mai gabaɗaya. Suka juya har shamaki. Ƙatuwar tabarma aka shinfiɗa a barandar ƙofar gidan inda dama anan suke salla kuma ana ɗaukar karatu daga gurin limamin da ke jan su sallar maƙocin shi ne. Annan ne Dai suka gaisa cikin mutunta juna sai Shamaki ya miƙe ya ce to bari ya dawo. Tun da aka ce ga su nan na hau ɓare ɓaren gyaran jiki, ina ta kwalliya sam ban damu da yadda Ummanmu ta haɗe fuska ba. Jamila kanta sai da ta tambaye ni wai kuwa lafiya na ke irin wannan abin? Nace me nayi dan kawai na yi kwalliya laifin ne,kar ki manta da daga yau ya zama mijina,kuma kinsan dai matsayin yiwa miji kwalliya ko?
Cikin
"Matsananci mamaki Jamila ta ce "Yaya Baby wai ina kunyarki da kawaicinki suka tafi ne?" Wallahi karki fara kice za ki ke irin wannan rawar kan, wai baki lura ma da yadda Umma ta ke jin haushin canzawar ki tun jiya ba?" Na ce ni banga wani canzawa da na yi ba. Kafin Jamila ta ce wani abu Muryar wani yaro ta ratso cikin kunnuwanmu yace ana sallama da Baby, cikin rawar jiki na ɗauki mayafi na zira takalmi ina faɗin Jamila ki kawo mana tabarma. Umma tace "Baby ki zo nan." Na nufi gurin ta a ƙofar ɗaki kan tabarma na ce ga ni. Ta ce, "Kinsan daga Allah ba wani in har baki haɗa min hankalin ki guri ɗaya ba zamu samu matsala da ke, tun jiya sai wani shashanci kike yi girma hauka ne? Wato kin riƙa kin so aure shine ki ke wannan rawar kan, dama rashin samun saurayin ne ya sa ki ka nutsu kamar ta Allah ko?" Na sunkuyar da kai ina faɗin Umma dan Allah ki yi haƙuri ni ban fahimci me nake yi ba,yanzun ma Jamila ta gama min faɗa wai na canza. Na daina Umma. Bari inje yana jira. Ban jira me Umma zata sake faɗi ba na yi waje da sauri har ina tintiɓe. Umma da Jamila dai abin har tsoro ya ba su. Ina fita yana jingine inda ya saba tsayawa, na isa da sauri ina faɗin sannu Yaya da zuwa. Yaya ce "Sannu Baby " Na gaida shi ya amsa. Na ce Yanzu sun can ana maganar aurenmu? Ya ce e na rungume hannuwana tare da ɗan tausaya wa ina faɗin Alhamdulillah Naji daɗi Yaya zan iya bacci in aka ɗaura mana aure kuwa? Mamaki ya hana Shamaki magana,duk da cewa shima fa yana jin wata ƙaunarta a zuciyarsa wadda bazata misali ba. Ta katse mishi tunani da faɗin lokacin walimar tamu za a saka ko? Yace ban sani ba gaskiya haka dai nace su tambayar min." Nace Kaga Yaya, asa hakan wallahi na yafe lefen, kuma kayan ɗàkin ma zan faɗawa Umma ba takura ko? Yace "Sai ki iya faɗa mata haka baza ta ga cewa kinyi rashin kunya ba?" Nace to wai me na ke yi ba daidai ba? Tun jiya ake cewa wai na canza ina ta zumuɗi, kuma ni ina jin wani sonka ne bansan ya zan fassara maka abin ba. Ina samun nishaɗi da jin daɗi ne kawai in naji muryarka, da na kira baka ɗaga ba har kuka fa na shiga ban ɗaki na yi, sai ina ji a jikina kamar zaka fasa. Yace "Gaskiyar magana kin canza gaba ɗaya kamar ba ke ba. Nima dai ina mamaki." Nace to Allah ya sa dai su amince shine damuwata. Yace "Ya maganar walimar ku?" Na yi ɗan jim sannan nace tana nan, amma gaskiya dai zaka zo min ko,duk da masana cewa kana cikin shirin biki lokacin ai na san zaka so ka ga karatu na. Yace in sha Allah zan zo sannan karki saka a ranki cewa dole sai lokacin da muka ce, in basu yarda ba dole mu jira lokacin da suke ganin ya fi." Na ce Ni fa damuwata kada ka zo ka ce ka fasa, wallahi zan iya mutuwa har lahira. Yace Baby in kinga na fasa aurenki wallahi na mutu ne,matsawar ina numfashi bazan fasa ba. Daɗi ya rufe ni, nace Allah na gode maka. Munata tattauna batun soyayyarmu na ga Abba ya zo ya shiga gida. Ya ce bari inje in sallame su, ki koma gida zan dawo nace to. Na shiga gida don inji yadda suka yi. Anan na samu Abba yana ba Amma labari ya zauna genen tabarmar da yake kai har Jamila ta kawo masa abinci. Yana faɗin "Wato Salamatu Allah ya amshi addu'armu ya kawo wa Jamila mijin ƙwarai ba sai mun bincika komai ba sun wanke shi tas. Limamin Unguwarsu inkinji yadda ya ke yabon sa abin zai baki shi'awa ga neman na kansa ga alheri duk sun yabe shi,ƙanin mahaifiyarsa da ƙanin mahaifinsa banda albarka babu abinda suke sa masa. Kuma sun nemi alfarma ko za a sa aure tare da walimar saukar su nace a a saboda yanayi shima kar ya takura kansa muma haka, amma sai suka dage kan cewa gaskiya yana buƙatar aure sosai kafin nan da azumi. Sanna duk abinda ake dashi bashi da wata matsala akai wa yarinyar. Na ƙara kaso kunne inji me Umma zata ce. Sai naji tace, Gaskiya a sa shekara ya yi haƙuri dan shekara kwana ce Abban Baby, bikin 'yar fari ba mu yi mata komai ba ai sai mun shiga bakin duniya. Ban san lokacin da nace Umma zai fasa inhar aka sa shekara,ni dai gara lokacin da yace ɗin dan in ya fasa mutuwa zany.... Saukar ta kalmi da naji a fuska ta shine ya tuna min cewa bai kamata in tsoma baki a zancan aurena da mahaifana su ke yi ba. Na lalle su dan in gane waya jefe ni,sai naga ashe Umma ce, sai huci take ta rasa abin faɗi dan takaici. Shi kuma Abba ya sunkuyar da.kai, sai suka bani mamaki, domin a magabata banga wani abu na tashin hankali ba, na faɗa musu abinda ni nake so ne, kuma dai su iyayena ne wazan fadawa halin da zan samu kaina in an fasa. Sallamar wani yaro ce ta ratsa shirun da gidan ya yi kamar mutuwa ta gifta, Abba ya amsa sai yaron yace "Ance Baby ta zo." Na tashi da sauri na shuri takalma sai da na kai bakin soro sai na waiwayo dan naji a jikina ni suka bi da kallo dama na zargi haka. Na fita ina tunanin ko dai na kuma wani laifin ne? A fili nace garama amin auren in tafi tunda har sun soma gajiya da ni. Na isa gunsa ina faɗin yau Jamila ta ƙi kawo mana tabarma. Yaya sun tafi ke nan? Ya ce "Sun tafi." Nace amma sun faɗa maka komai yadda aka yi? Yace "bakiji ba da Abba ya shigo?" Na ce Banji matsaya ba a maganar na saka musu baki Umma ta jefe ni sai kuma suka yi shiru. Yace "Subhanallah! Me zai sa ki saka bakinki cikin managarsu?". Na ne Yaya Shekara fa Umma ta ce, kuma kai nasan baza ka shekara bada matarka ba. Yace Banda haka Yaya nima ba zan iya ba. Yace "Baby bai kamata ba kina saka baki a maganar manya. Hajiyata tana da zafi in kinje kina mata irin wannan za ku samu matsala wanda hakan zai kawo matsaloli a cikin zaman aurenmu. Ni kuma bana son a ce ni da ke mun rabu, saboda akan Hajiya zan iya komai. To gaskiya in kina son mu daidai ta ni da ke, to sai kin sawa bakinki linzami in manya suna magana babu ruwan ki." Na sunkuyar da kai, insha Allahu na dai na. Nima jiya ne suka fara wannan kukan da ni,amma bana yi, ko yanzu a maganar ka kaɗai suke cewa na canza. Ni kuma banga canjin ba. Ya ce "Nima na gani dan haka ki dawo kan hanya. Nace to, amma kai ai zamu iya tattauna maganar aurenmu ko? Ya ce "Sosai ma kuwa." Nace to yanzu faɗa min yadda aka tsaya. Yace Abba sunce za su yi shawara, domin shima Wan Abba cewa ya yi tunda na ce abinda ake dashi a kawo ki ba matsala to na shi ganin gara a yi bikin kawai. Shine aka ce a shawarci Ummanki. Nace to Umma tana kiran shekara. Yace Allah dai ya zaɓa mana mafi alkhairi. na ce ameen. Yace "Ni ma dai ya kamata in tafi, da har zan wuce, sai kuma nake tunanin ban muyi sallama ba." Nace yanzu sai yaushe? Yace, "Bazan sa lokaci ba gaskiya tunda an bani ke. amma kowane lokaci za ki iya gani na. Zan bada waya a kawo miki saboda za mu ke yin magana akai akai. Nace "To ɗan Allah kar ka manta da Ni kaji. Ya yi yar dariya sannan ya yi ƙasa da murya, ashe zan mantà kai na. Ina mugun sonki Baby. Cikin farin ciki nace ina sonka Aliyuna. Sai kuma naji kunya na saka hannu na rufe fuskata. Muryar Abba naji yana cewa "Malam Aliyu bari in baka saƙo ka faɗawa magabatan na ka.". Aliyu ya ce to shiga gida sai kin ga saƙon na ce to ka gaida su Hajiya da su Anisa. Na laɓe a soro ko zanji me za su faɗa amma banaji. Dole na shige ciki Umma harta kwanta na leƙa ɗakinta ina yi mata sannu, ko dai ta yi banza da ni, ko kuma ta yi bacci. Na fita na je na saka tuwo na ɗebi ruwa a kofi na shiga ɗakinmu na zauna ina ci. Jamila ta shigo da shirin baccin ta, tace Yaya Baby ki sa su Jafar su yi fitsari in kin gama, yau duk ni na yi aikin ki a gidan nan." Na ce me kika yi nawa da zaki faɗi haka?" Ta ce "Ni na tace gasara kuma na kammala komai." Na yi 'yar dariya. Ni da zan tafi ma gidan mijina daga can zan ke zuwa ina miki akin? Jamila ta yi gialala ta na kallona,sannan ta ce, gaskiya Yaya Baby abinki ya soma wuce tunani, kuma ko a jikin ki. Na kalleta Ni Kuma ke kike bani mamaki, ko da yake na miki Uzri bari ki faɗa soyayyar za ki gane abinda ya same ni. Tace haka ɗazu ki ka yi ta rera wakokin soyayya a gidan nan ke da ko wani ya yi waƙa sai kin masa wa'azi." Na suɗe robar ina lashe hannu, na ce duk ba wannan ba, faɗa min abinda su Umma suka yanke da na fita. Abba ya tsorata da yadda ki ka yi,Ya ce Umma ta yi haƙuri ayi bikinnan a haka yadda ki ke yi ya nuna kin matsu da aure,abinda aka samu a kai miki. Daƙyar Umma ta yarda domin har abin sai da ya kai su kamar za suyi sa'insa, daga bisani Abba ya lallasheta. Amma tana ciki da ke,zaku gauraya da safe. Na ɗanyi jim har ga Allah ni banga abin laifi ba amma dole in ke yin shiru dan in samu zama lafiya. Na dubi Jamila wadda ta kwanta tana ƙokarin rufa. Na ce amma ya suka yi matsaya a ƙarshe. Ta ɗago kai zakiji a bakin Umma da safe, shawarar da zan baki kuma ita ce, ki bawa Umma haƙuri, sannan ki daina magana sam in ana zance.Na miƙe tare da faɗin zan kula sosai. Da safe Umma bata amsa gaisuwa ta ba,to nan ne fa hankalina ya tashi na soma kuka ina bata haƙuri, tace haƙurin me zaki ba ni, ni a su wa ɗanwake a Otal ba dai ɗa namiji bane Baby Allah ya bada sa'a." Na ce Umma wallahi ni fa bansan me zance miki ba ne, kiyi haƙuri na tuba don Allah.Abba ku yi haƙuri ni ban san cewa ba a magana ba. Ya ce tashi kije ki yi aikin ki ta haƙura. Na fita ina sharɓen kuka. Ina jiyo Abba yana baiwa Umma baki, tare da nuna mata cewa ƙuruciya ce,kuma mu godewa Allah Salamatu da ya bamu yara masu kamun kai da nutsuwa, duk tsukunnan yaban su ake Allah ya sa musu albarka karki fusata Allah shine mai rufin asiri abar auren a lokacin da aka sa shi. A ranar wani matashi ya yi sallama muna Islamiya anci sa'a Abba yana gida . Suka gaisa yace Aliyu ne ya aikoshi da saƙo ya baiwa Amira. Abba ya amsa waya ce sabuwa a kwali sai layin da kuma kati wanda ya ce ace in ta saka ta kira shi. Abba ya ce to insha Allahu za a bata, taje islamiyya. Na yi murna sosai lokacin da muka dawo. Umma ta ɗan saki jiki harma ta karɓi wayar ta sa albarka. Tace ki kula irin wannan ta shafawar ba wuya ta

Please Login or Register in order to submit comment