Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa hanyar sashensa "Je ka yi waya." Tsam ya miƙe cikin sanyin jiki ya ɗan kuma risnawa tare da faɗin mu tashi lafiya Hajiya Allah ya huci zuciyarku. "Allah ya maka albarka." Ta furta cikin kallon gefe. Ya tafi ta bishi da kallo ranta ya sosu ƙwarai in da ne Shamaki ba zai tafi ba da tace ya tafi, zai tsugunna ne yana bata haƙuri ƙilama sai ya zubar da hawaye har sai ta huce, sannan zai ci abincin ko da baya jin yunwa,haka kuma za suyi lissafin kamar yadda suka saba. Lallai dole ta ɗauki dukkan mataki kafin abin ya wuce gona da iri, ta koma ta jingina sannan ta ɗauki waya ɗaya a cikin wayoyinta. Ta danna kira, suka gaisa da malamin wanda shine yake taya su da addu'o'in neman tsari da samun kariya. Ta ce Malam akwai wata matsala da ta soma tunkarowa cikin ahalina yaron nan Shamaki ya faɗa soyayya da wata yarinya, yadda ya koma kamar wawa abin ya tsorata ni. Ina son amin bincike shin ba wani abu yarinyar ta yi masa ba! Kuma tsakaninsu ina son in sani akwai alkhairi ma kuwa!Malam yace "Insha Allahu Hajiya za kiji sakamako zuwa gobe, za ayi bincike sosai zamu iya samun sunan yarinyar?" Hajiya ta ɗanyi shiru sannan ta ce ina zuwa. Ta katse layin ta soma kiran wayar Shamaki, ya gama shirin kwanciya kenan yana ta sauri dan ya kira masoyiyarsa, cikin sauri ya ɗaga kiran Hajiya gaban shi yana faɗuwa. Tace "Ya sunan yarinyar da kake so?" Cikin sauri yace Baby Amira ko Rabi atu duka suna kiranta da shi. Ta kashe layin ba tare da tace komai ba. Sai da ya gama komai sannan Ya danna kiran layin wayar mahaifiyar ta sannan ya kwanta a kan tsakiyar gadonsa ƙafafun sa na ƙasa.
Na jigata sosai da tunanin abinda ya hana Yaya Aliyu kira na, sai naji kamar in kira shi sai kuma wata zuciyar ta hane ni,har na kasa cin abinci a yinin na kuma shiga kaiwa Allah kuka in har da akwai matsala ina roƙon Ubangiji ya kauda matsalar, yanzu kam na samu tabbacin cewa ina son Aliyu har lokacin da muka je makwanci banji sautin wayar Umma ba, na sadaƙar cewa ya canza ra'ayi. Ƙarar kiɗan Nokia ya tashe ni zaune, na kasa kunne inji ko Umma zata kira ni, har kiran ya yanke, na tashi da sauri na fita, daidai lokacin da wayar ta sake daukan kiɗan na yi sallama a ƙofar ɗakin ba a amsa ba, na shiga Umma bacci ta ke wayar na caji Abba kuma bai shigo ba, na ɗauki wayar da sauri na nufi ɗakin mu ta kuma katsewa kafin in ɗaga, na fara danna lambobin cin bashi amma sai kira ya ƙara katse hakan, da sauri na faɗa kan lamammiyar katifar sannan na manna wayar a kunne tare da sallama. Ya amsa tare da tambayar ko dai har na yi bacci? Na ce masa e bacci ya fara ɗauka na. Ya ce "Ki min afwa abubuwa sun sha kaina ban kira ba kamar yadda na yi alƙawari." Na sauke numfashi hakan kuwa ya yi matuƙar ɗaga hankali na, na yini a damuwa ko dai ba lafiya ne, in kuma na yi kamar in kira ka, sai zuciyata ta faɗa min cewa in kana cikin wani uzri fa, yanzu dai da tunanin haka na kwanta. "Alhamdulillah! Ina da tabbacin kina so na a yanzu, kuma naji daɗi dan Allah karki dinga ɓoye min duk yadda ki ka ji a kaina ko daɗi ko akasin haka ina son wannan kinji Baby?" Nace To zan ke faɗa maka Yaya. ya ce "Yanzu faɗa min ya kuka yi da su Umma?" Na ce sun amince ka kawo kuɗi amma kamar yadda na faɗa maka baza su amince da auren lokacin walimar saukarmu ba, domin yanayi,kuma kai ma bana son ka takura kanka, kuma malamai suna cewa gaggawa yawancin ta daga sheɗan ne, abi a sannu. Ya numfasa "Gaskiya kika faɗa Rabi'atu amma ina son ki gane wani abu, na taɓa aure nasan daɗin shi kuma ina buƙatar shi. Bazan jure dogon zama ba, tunda har zaki iya sadaukarwa game da lefe, me zai hana ni ba zan sadaukar game da kayan ɗaki ba. Ko ba domin ni za ayi ba?" Na ce domin kai za 'ayi mana,amma kasan mutane akwai su da munafinci sosai za ayi ta gulma cewa ko kayan ɗaki iyayena ba su sai min ba. Lefe kuwa zamu iya cewa ankai ajiya. Yayi murmushi mai sauti, "Gadon ma sai muce kafinta bai gama ba." Ya faɗa cikin yanayin nishaɗi. Na ce in har su Umma za su yarda da haka ni bani da matsala kaine abinji nan katifar da nake kwance da kaɗan ta fi tabarmar kauri. Ya saki dariyar da sai kuma naji kunya ta kamani. Yace "Ina da katifa babba kuma Hajiyata ta na da tukunyar girki dan haka ni matata kawai na ke buƙata." Wani daɗi ya tsirga min da ya ambace ni da matarsa. Allah ya nuna min na faɗa a zuci, "Ameen Babyna." Nace kai araina nayi addu'arfa. Yayi "yar dariya,araina na amsa fa ke ma kinji ne?" Nace e mana, yace "A lallai mu na musamman ne gaskiya kunnuwanmu suna iya sauraron abinda zukatanmu suke faɗa kenan gaskiya mu gode wa Allah. Yawwa Baby in tambaye ki wani abu?" Na lumshe ido na sake yin ƙasa da murya domin bacci yana ɗan bibiyata. Na ce tambayi ko me ka ke so. "Zaki iya zama da uwar miji?" Cikin sauri na wartsake, a son zuciyarta shi ne 'a 'a bisa ga yadda na ga Umma tana fama da kiyayyar dangi Abba, kuma ta bamu labarin abin ya fara ne tun daga tsanar da mahaifiyar Abba tayi mata kafin ta rasu. "Kinyi shiru Baby." Yafaɗa da sanyi jiki. Nace mamaki na ke yi da wannan tambayar kuma ina nazarin dalilin yinta. Yace "Kar ki damu da dalili, ki faɗa min me kike mamaki." Nace to ya zaka tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyar da ta haife ni? Na marairaice murya ina magana cikin yanayi shagwaɓa. Yaya in har yadda nake jin ka a zuciya shine so to tayaya Mahaifiyar ka baza ta zama tawa ba? Sannan in har wani zai tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyata me zai hana in so jin dalilinsa cikin mamakina? Ya yi shiru Yarinyar ta gama gigita shi ta sukurkuta shi,dan haka ya fara da faɗin "kiyi haƙuri Babyna nasan mata da yawa suna gudun zama da Uwar miji wannan shine farkon matsala ta da matata ta fari Maman Meema, amma ba wai dan wani abu na yi wannan maganar ba." Nayi ɗan murmushi domin ganin na soma gano wasu abubuwa game dashi, kuma rauninsa ba zai min wahalar ganewa ba. Ya katse ni da cewa "Kin lashe babbar jarabawar da na fara miki kuma zan turo ranar Lahadi ni kuma zanzo jibi in kawo miki dubunki uku ta walima." Ba gobe kace min ba a jiya? Na katse shi, Ni ba damuwata kuɗin ba domin sai da na sha faɗa akan Lemon da ka kawo jiya, Abba yana zargin ko dai roƙon ka na yi ka siya min, Ni kuwa ina jin daɗin hirar da kai ne kawai ina son in ganni gani ga ka." Ya katse ni da cewa "Alhamdulillah na ci nasara Baby wallahi kin kamu da sona Baby dan Allah ki furta ki ce Aliyu ina sonka dan Allah! Ki faɗa inji." Na sunne kaina cikin ɗan yamusashshen filo na Na ce wayyo Allah Yaya kamin afwa zan faɗa maka amma banda yanzu. Ciki shagwaɓa yace haba Babyna." Gyaran muryar Abbanmu naji banji sallamar shi ba, nasan zai zo ne ya duba mu kamar yadda ya saba,don haka sai nace Yaya Abba ya shigo sai goben ka yi haƙuri, na kashe wayar ya taɓa ƙofar na yi laf, ya haska sannan ya yi addu'a ya tofa gabas da yamma kudu da arewa na ɗakin, sannan ya ja ƙofar ya fita.


🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 4*


Ta amsa gaisuwarsa tamkar ba wani abu, suka ci gaba da lissafin da ya kamata ace sun yi a jiya. Ya saki jiki ya karya duk da ta gano cewa ya yi ne domin ta huce daga saɓa matan da take ganin ya yi, amma ta ji daɗin hakan. Ya so matuƙa ta tambaye shi wani abu game da Baby domin ya faɗa mata yana son a tura a cikin satin amma ta ƙi maganar sam,wanda hakan ya sa dole ya bari sai zuwa yamma, duk da tana son taji yadda suke ciki amma ta bari sai ta ji daga Malam. Su Meema suka shigo da gudu duk suka nufi Hajiya suka tsugunna suka gaisheta, ta shafa kansu tare da yi musu addu'o'in da ta saba,sannan suka nufi jikin Dadin su suka gaida shi,ya amsa tare da sa musu albarka Rahin ta fito da kwandunan su da jakunkuna Azima ta kama musu hannu suka wuce suna ɗagawa Dadinsu da kakarsu hannu. Shamaki ya sallami Hajiya ya koma ɗaki don ya shirya ya fita kasuwa. Komai ya ke yana tuna Baby so biyu yana ɗaukar wayar sai ya danna kiran layin Umman su sai kuma ya katse. Ana ukun ya jure tayi ta ringin aka ɗaga tare da sallama. Ya amsa Umma ce, ya gaida ta cikin ladabi, ta amsa cike da jin kunya.ta ce "Sun tafi makaranta kasan ita jarabawa ta ke yi ta fita." Ya ce e ta faɗa min Umma, Allah ya bada nasara, dama na kira ta ne mu gaisa a gaishe su. Umma ta ce "Ba komai a gaida magabatan da kyau don Allah" Yace za suji, ya kashe wayar ya shirya ya fita. Hajiya tun tana sallar walaha wayarta ke ƙara, sai da ta idar ta yi addu'a sannan ta miƙa hannu ta ɗakko wayar Malam ne,don haka sai ta danna kiran shi,ya ɗauka suka gaisa ta tambaye shi abinda ya fuskanta game da binciken, yace "To alal haƙiƙa Hajiya abinda na gani shine, abu na farko dai aure babu fashi, abu na biyu kuma taurarin yarinyar masu haske ne sosai tana tare da arziƙi irin su ko matsiyaci suka aura albarkacin su yana ganin faraga, mai arziƙi kuma tamkar wuta ce sai a zuba mata fetur a bin nufi akwai alkhairi tare da ita,abu na uku Allah ya ɓoye min ban fuskance shiba amma shima ina zaton alkhairi ne,sannan yana sonta sosai irin wanda in ya rasata zai cutu kuma irin wannan son ba zai taɓa ganin aibunta ba ko da ita bata son shi. Wannan sune abubuwan da na gani." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce Malam kuma an bincika ba wani asiri ta yi masa ba? Malam yace "Abinda na fara dubawa kenan ita yarinya komai nata a rufe ya ke abin nufi bata taɓa ziyarar wani malami ba domin wani aiki. Sam babu kuma wata niyya ta cutar da shi ko kaɗan." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya,shike nan Malam a tayamu da addu'a ita ma ta kamu da son shi fiye da wanda yake mata, yace "Wannan mai sauƙi ne in har za taci abin da zan kawo." Hajiya tace ina zan ganta har wani taci wani abu? Amma ka kawo ɗin sai muga ya za ayi. Yayi yar dariya "Hajiya ko gida zaku iya aikawa,kuma koda kowa yaci bazai yi aiki akan saba sai ita da akayi da sunanta sai dai matsalar in har wata mai irin sunanta ta ci to ita ma zata kamuwa da sonsa." Hajiya tace babu damuwa ka aiko ɗin zan san yadda za ayi amma shi abin menene? Yace,Dabino ne ƙwaya bakwai da za a samu ta ci duka zai wahala in bata zo ta tare a gidan ba kafin bikin kamar tai masa sujada haka zaki ga tana yi. Hajiya ta ce na gode sosai Suka yi sallama. Hajiya ta lushe ido ta nutsa cikin tunani, tabbas zata barshi ya auri yarinyar amma dole ta so shi da yawa domin bata buƙatar ta janye masa hankali. Duk da hakan kuma zata sa shi ya kawo mata yarinyar ta ga wace irin wayewa ce da ita wadda har ta ɗaukar masa hankalin yaro haka. Dole sai ta gano wasu abubuwa game da yarinyar domin ta saita mata sahunta don bata son rawar kai. Kuma ta gane ba a mulki sarakuna biyu aka karaga ɗaya. Sam bataji sallamar Anty Zainab ba sai gaisawa da taji suna yi da Juma. Ta buɗe ido ta kai kallo inda taji muryar Zainab ɗin, ta ɗago ta gyara zama tana faɗin yaushe kika shigo Maman Umar? Anty Zainab dake zaune can gefe cikin girmamawa tace "Naga kuna ɗan gyangyaɗi ne shiyasa na yi shiru." Ta gaida Hajiya cikin girmamawa. Hajiya tana tambayar yara, tace duk suna makaranta. Anty Zainab ta kira Juma tace ki zo ki ɗau ledar can ki wanko wa Hajiya tuffa da Inibi har gwabar da fiyar sai ki haɗo mata. Juma ta ɗauki ledar ta fita. Hajiya ta kalli babbar 'yartata tace Maman Umar Allah ya yi albarka har Fiya ta shigo kenan ta ce "Ta shigo nima jiya naje Store in duba jadawalin abinda ake buƙata shine naga sunsa harda Fiya a ɓangaren 'ya'yan itatuwa." Shine nace bari inje in duba miki a wani gurin." Hajiya ta ce Allah ya jiƙan mahaifinku. Zainab ta ce "Ameen Hajiya Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana. Sannan ta gyara zama ta ci gaba da magana. "Hajiya wata yarinya na gani na yiwa autanki shi'awa yarinyar tana da hankali sosai kuma tana da ilmi duka biyu,kuma iyayen ta dattawa ne, Babanta Farfesa ne a BUK." Hajiya ta ce,to ki kira shi ki faɗa masa in ya amince sai yaje ya ganta. Kira shi yanzu kiji amsar da zai baki.
Zainab ta kira wayar Shamaki na farko ta katse na biyu ya ɗauka tare da faɗin "Anty Maman Umar ya gida ya yara?" tace lafiya lau autan Hajiyarmu ƙaraminmu babbanmu. Suka yi 'yar dariya ya saba da wannan kirarin nasu, musamman tunda shike sa hannu a duk wani kuɗi in zai fita daga ko wane sashen ZEENA. Tace Shamaki mata na samo maka mai hankali,ga kyau 'yar gidan ilimi. Yayi 'yar dariya "Kin makara Anty,dan cikin satin nan za a kai kuɗina an bada ni Anty." ya kai ƙarshen maganar cikin tsokana. Ta ce bafa wasa nake ba, shima yace"Allah da gaske na ke yi kuma dama na daina auren haɗi abarni in gani da kai na." Tace shikenan amma duk da haka ka zo gidana zan sa a kira ta sai ka ganta,dama ban musu magana ba, bari na yi inji ta bakinka. Yace Ba sai na ganta ba, domin bazata kai Amira a komai ba, na gode da kulawa zanzo mu yi maganar yadda za a haɗa min lefe irin na yar manyan mutane,dattijai." Tace shike nan sai na jika suka yi sallama. Ta dubi Hajiya ,ashe ya samu? Hajiya ta ce shiyasa na ce ki kira shi,saboda wata irin soyayya naga ya fara mai ban tsoro ku taya shi da addu'a, bana son ya kawo macen da soyayyar ta zata kawo mana hari a cikin gidan nan, ina nufin ta yi amfani da hakan ta cutar damu, Shamaki shine jigon gidan kin san dai abinda nake nufi."Anty Zainab ta ce haka ne,to anyi bincike a unguwar su? Hajiya ta ce na kammala da duk wani bincike bana buƙatar inji me mutanen unguwarsu za su faɗa, yanzu kawai ina son ya dawo in faɗa masa,ya kawo min ita ne in yi mata jarabawar ƙarshe in ta haye shike nan in yana buƙata sati ɗaya kacal za a iya ɗaura musu aure in haka ya yi wa iyayenta. Zainab ta san Hajiya ta ƙare magana don haka ta ce Allah ya sanya alkhairi. Ameen Hajiya ta amsa tare da saka yankar fiya da aka jere mata a cikin tire. Anty Zainab ta tashi bari in shiga kicin ko akwai abinda zan iya ci a abincin gidan. Hajiya dai ta maida kanta ga TV inda wani malami ke nasiha ga 'yan mata masu fitowa suna fitsara a manhajar TikTok. Anty Zainab ta fito ɗauke da plate ta zubo kuskus ta kalli TV tace ai gaskiya yara suna fitsara a wannan TikTok ɗin. Hajiya ta ce "Wai Ni menene shi TikTok ɗinnan?" Zainab ta ɗakko wayarta tana nunawa Hajiya. Taga yadda 'yanmata kyawawa suke tallar tsiraici,da kuma yadda ƙananan yara da iyayen suke ɗora su suna maganganu na aure da haihuwa yaran da ko magana ba su gama iyawa ba. Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya kyauta wannan zamani, to wannan me za a kira su,ta yaya ɗanka zaka bari ya auro maka irin wannan yarinyar ya kawo maka gidanka! Wannan dai na tabbata harga Allah dole ta juya namiji da iri wannan karuwancin,dan su mazan irin abinda suke so kenan."Anty Zainab ta ce Allah ya shirya mana zuri'a kuma akwai Malamai ma su wa'azi da masu tallata abubuwa. Hajiya ta ce Allah dai ya tsare mana zuri'a gaba ɗaya da duk ɗan musulmi baki ɗaya. Anty Zainab ta a amsa da ameen ta kama cin abincinta tabar Hajiya da tunanin dole ma ta ga yarinyar ko dai ita ma tana cikin masu irin wannan rawar.
Ƙarfe shidda mun taso daga makaranta ina tafe ina tunanin kayan da zan sa yau in Yaya Aliyu ya zo. Turus na yi a ƙofar gidanmu ganin shi tsaye da wani ɗan buhu a gefen sa,sai kuma na soma kallon jikina duk da kayan makaranta ne a jikina amma ba su da guga kuma ƙafata duk tayi ƙura. "Ya kika tsaya Baby ki ƙaraso mana. Ya yi kamar bai lura da abinda na yi ba. Nace Yaya bari in cire kayan makaranta. Yace "Karki damu ba ruwana da kayan jikinki, dama na zo ne don in ganki da yamma sosai, ido na ganin ido." Na ɗan haɗe fuska alamun fushi na ce amma sai ka faɗa min ko? Yace to kiyi haƙuri,kinfi kyau a hakanki na ɗaga ido ina kallon shi, yana 'yar dariya ashe harda haƙorin maka fari tas a bakinsa, inda akwai maza masu kyau to ba shakka za a saka Yaya Aliyu a ciki yana da tsawo da kuma 'yar ƙiba harma da wani ɗan tumbin irin na matasan masu kuɗi, tsarinsa ya min ƙwarai. Ya katse ni Kin gama nazarin nawa? Na?" Na ja hijabi na rufe fuska, sannan nace bari to in ɗakko tabarma. Yace a a nan zaki dawo kawai ki zauna ni kuma ina nan a tsaye, ba jimawa zanyi ba dan kar anjima banzo ba ki fara lissafa rashin cika alƙawarina. Zanje aiken maigidana, baya gari ni ke kula da buƙatun mahaifiyarsa." Nace gaskiya na amshi uzrinka babbane,lamarin amana sai masu gaskiya. Ya dube ni, "Har kin bani lambar gaskiya Baby to ina godiya Allah ya sa hakan na ke." Nace haka ne ma insha Allahu. Na isa inda ya nuna min na zauna daidai lokacin da su Jamila suka iso da su Jafar, suka gaida shi,sannan na basu jakata nace su shigarmin da ita ciki, ya nuna wa Jamila ɗan buhun da ya zo dashi ya ce "Zaki iya ɗauka?" Ta kalle ni, nace "Me ka kawo min Yaya zaka ja min faɗa. Ya ce "Ɗauki kinji, shinkafa ce kwano uku ba yawa ki yi girkin walima." Ta ɗauka tana masa godiya ta shiga, nace Allah ya saka da alkhairi Yaya. Ubangiji ya sa a mizani. Yace "Amin mata ta ina godiya." Fatin Maman Fati mai awara ta zo wucewa ta kalle ni ta kalli Yaya,sai ta ɗan taɓa baki ta wuce.Na kalli Yaya ko ya kula sai naga shi ni kawai yake kallo, na yi ɗan fari tare da faɗin ya dai Yaya? Ya yi murmushi bari inzo in tafi gida kar a kira magariba nace har zaka tafi, yanzu fa ka zo. "Ya yi ɗan murmushi sai kin min uzrin zuwa zance, yanzu kawai in zanzo zan kira ki, ya kamata in sai miki waya ko 'yar ƙarama ce." Nace kana ta ƙirƙiro kashe kuɗi don Allah ka barshi. Ya ce "To na bari, tashi ki shiga gida." Na miƙe ya ce "Ga dubu ukunki." Na mai da hannuwana baya na maƙe su, ka barshi ga shinkafa ka sai min. Ya ɗaure fuska sannan yace karɓa, da sauri na miƙa hannu biyu na risina na amsa ina ta godiya da addu'a. Yace shiga gida kawai, na wuce ina waiwayen shi.



🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 5*


Umma tana kaɗa miyar kuka ta bini da kallo, "Shine baki shigo gida ki sanar cewa kin dawo sannan ki canza kaya ki fita gunsa ba, sai kitsaya da kayan makaranta. Nace,to Umma ba zan sake ba amma cewa ya yi yana sauri. Naje na miƙa mata kuɗin da ya bani,ta amsa tare da faɗin "Wannan kuma na menene?" Nace wanda ya ce zai bani ne na walima. Umma tace "Ni Salmai wannan wane irin mutum ne ko sati guda fa ba kuyi da haduwa ba. Nace in na ce ya barshi sai ya haɗe rai. Jamila da ke alwalla tace, Umma kinsan wasu mutanan ma su yi ne, Yaya Baby ta yi dace. Umma ta ce "Allah ya zaɓa mafi alkhairi shinkafa 'yar gwamnati gata can amshi kuɗin nan ki kai ki adana a cikin wannan jakata. Allah ya sa kar Malam ya yi faɗa." Na ce to. Gaskiya na yi farin cikin ganin Yaya da rana, na ɗakko hodar Umma na kalli fuskata a madubi ko me yaya ya gani yake sona Ni ba dogo hanci ba, kuma ba manyan ido ba, amma ina da gashin gira sai ƙananan haƙora da kuma wushirya. Muryata ma ina jin ana fadinta, bazan ce komai ba game da surar jiki domin yanzu ne maƙerin ya ke ƙirar.
Shamaki ya yanke shawarar zuwa gurin Baby ne dan baya son Hajiya ta ci gaba da nuna damuwa tun a tashin farko. Ya fi son komai ayi cikin daɗin rai to kuwa dole ya danne zumuɗin shi game da Baby. Lokacin da ya shiga bayan ya kammala da mabuƙata suna cin abinci ta ji bai yi batun yarinyar ba sai ta ce, ɗazu Maman Umar ta ke faɗa min ta maka budurwa ko? Ya ce "Haka ta faɗa amma ta zo a makare, tunda mun gama magana da Baby har ta sanar da mahaifanta cewar zan turo, na ce a cikin satin nan in kun ga hakan ya dace." Hajiya ta yi

Please Login or Register in order to submit comment