Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Free Page 2*

Har tsakiyar dare bacci ya ƙi zuwa min sai juyi na ke akan "yar katifarmu Jamila ta na ta baccin ta, tufka na ke ina warwara abu biyu ke ɗaga min hankali,menene dalilin rabuwa da matansa? Kuma komai nasa dole sai Hajiya ta sani? Zuwa yanzu nasan cewa Hajiya dai ba matarsa ba ce, ko dai mahaifiyarsa ko kuma uwar ɗakinsa. Da safe ina raba mana abin kari awara ce da koko duk muna tsakar gida harda Abbanmu. Umma ta dube ni,"Ke kuma lafiya duk jikin ki a sanyaye?" Nace, lafiya lau, kawai yau kasala nake ji. Ta dubi, Abbanmu tace, "Abban Baby kace ka yaba da saurayin nata jiya?" Ya ce gaskiya Salamatu na yaba sosai, in har sun dai-daita zanyi farin ciki domin alamu sun nuna shi mai hankali ne.Umma ta ce "To ɗan unguwar nan ne?" Yace, A a yace min shi ɗan Gama ne can aka haifeshi amma yanzu suna nan haka ko gurin Janbulo ne, ya ce da ɗan gidan sa a gurin da ya gina suna zaune da mahaifiyar sa. Kuma yace a kwari yake tsaron shagon wani mai gidansa, amma yace asali su 'yan Gaya ne. Umma ta ce "To, Allah ya daidaita su.
Ni dai bance komai ba,mutumin ya maƙale a zuciyata duk yadda na auno matsaloli sai zuciyata ta kawo wani uzri ta wanke shi. Haka nan har naje makaranta na dawo ina tunanin Aliyu Shamaki.
Da dare muna 'yar hira da Umma, ta tambaye ni da cewa "Ni ko Baby mutumin nan ya yi miki kina ganin cewa zaki iya aurenshi?" Na ce to Amma Ni dai ina ta waswasi. "Game da me?" Ta katse ni da tambaya. Na ce aurensa uku duk sun rabu da matan, 'yayansa uku duka mata kuma duka sunan mahaifiyarsa ya saka, sai ina jin tsoro ko mahaifiyarsa ce bata barin matan. Umma tace "Karki fara lamarinki da zargi, tabbas dole ki damu game da rabuwa da matansa, shawarar da zan baki shine ki sa hankalin ki sosai ki gano raunisa da fushin sa, ta haka zaki iya samun zaman lafiya da shi. Baby a irin tarbiyyar da nake baku ina sa rai ko mutum yana fidda wuta ta baki dan bala'i za ki iya zama dashi, haka duk wata kissa ko kisisina, ko shirka bai kamata kiji ɗarba." Na yi 'yar dariya haka ne Umma.
wayar Umma ta yi ringin Jamila tace Yaya Baby lambar jiya ce da kika ajiye. Gabana ya faɗi harda juyawar ciki,take naji banɗaki kawai na ke son shiga. Na amshi wayar na shige ɗakin Umma ina jinshi yana sallama, sai da na zauna sannan na amsa sallamar da wata murya da bansan ina da itaba. Na gaida shi,ya amsa na tambayi Hajiya da yara,yace duk suna lafiya. Yace, "Shine ko ki kira ni kiji ya naje gida jiya." Na ce to kayi haƙuri amma gaskiya na so in kira ka sai kuma na yi tunanin kar kana kan Kekenka kuma in tsaida kai, har kuma bacci ya ɗauke ni. Ya numfasa "To na amshi uzrin ki, amma ya kike gani zuwa yanzu a zuciyarki ta kuwa fara sona?" Na kwanta tare da ƙara manna wayar a kunnena. Ba zan iya tabbatar da haha ba Yaya,sai dai ka faɗamin yaya son ya ke ko zan gane.
Ya yi yar dariya. "Bani labarin bayan rabuwa kin tuna da ni? Sau nawa? Kina tuna hirar mu? Wacce a ciki?" Na numfasa, gaskiya na tuna ka sosai amma ban lissafa dadin ba. A hirar mu dai nafi tuna batun auren ka guda uku,sai in ji fargaba. Yace, "Alhamdulillah Baby kin fara so na, karki damu da maganar matan da na rabu da su, ko tunanin dalilin rayuwar mu, zai fi kyau ki maida hankalin ki akan irin rayuwar auren da za mu yi. Zanzo gobe,ki tanadi labari mai daɗi da za ki bani." Nace,to Insha Allahu Allah ya taimaka a gaida Hajiya. "Zan faɗa mata." "Yaran ki fa?" Cikin sauri na ce agaida min su don Allah, koda bansan sunayen su ba. Ya ce "Haka ne ban faɗa miki ba, dukansu sunansu Zeena." Kamar yaya na tambaye shi cikin rashin fahimta. Yace Ƙwarai kuwa duk sunan Hajiya suka ci, amma kowace da laƙaninta Babbar Meema, mai binmata Mubina sai ƙaramar su Anisa." Na sauke ajiyar zuciya, gaskiya abin ya birge ni kuma har naji ina son in gansu. "Karki damu ke da 'ya'yanki kuma ke ma zaki haifa mana wata Zeena ɗin ko?" Kunya ta sa na yi saurin faɗin sai da safe, na kashe wayar sannan na yi rigingine a gadon ina jin farin ciki gami da fargaba. Dole in yi magana da Umma.

Kamar kullum ya zauna a gefe yana jan carbi yana jiran Hajiya ta gama addu'o'inta kafin ya gaida ita kuma su yi 'yar hirar da suka saba. Bayan ta kammala suka shafa tare, ya matsa gabanta sosai ya rusuna ya gaishe ta. Ta amsa tare da kai hannu ta shafa masa kai tana faɗin "Allah ya albarkaci rayuwarka, da ta 'ya'yanka, ya yi albarka a cikin neman ka, ya albarkaci abinda zaka samu. Allah ya tsare ka daga dukkan sharri mutum ko Aljan da duk wani abinƙi." Shi kuwa yana ta maimaita ameen. Bayan sun kammala sai ta gyara zama sannan ta ce, "Jiya Maman sani ta zo game da maganar abincin sadaka na ranar juma 'a wasu abubuwa sun ƙare, na ce ta lissafi kamar yadda aka saba, kuma ina son wannan karon za'a saka sunan mutum ɗari a kayan salla yara marayu, sai mu ba Zeena Foundation dama su nemo yaran da suke dace da buƙatar tallafin nan a ba su. sannan ɓangare kayan ɗaki Amina ta. Kawo sunan mutum biyu kuma sun gama bincike tabbas yaran mabuƙata ne duk marayu ne na ce taje gandu su yi magana a Zeena funitures da manajan kamar dai kowane lokaci. Ya ƙara yin ƙasa da kai cikin girmamawa to Hajiya duk yadda ki kayi dai-dai ne. Ta dubi fuskar shi, "Baka sanar da ni ko ka tattauna da yarinyar nan ba." Eh na samu ganin mahaifinta kamar yadda ki ka bani shawara, kuma ya min 'yan tambayoyi kafin daga bisani ya shiga ya turota. "Kamar wace tambaya ya yi maka?" E ya tambayi unguwarmu sannan ya tambaye ni game da addini da sana'a da aƙida. Ya gamsu duk da ce masa da na yi ni yaron shago ne, yace buƙatar kawai ace da sana'ar komi ƙanƙatar ta Allah shine mai buɗawa in yi magana da ita in har mun sasanta ya bani ita. Hajiya ta ɗan yi jim,sannan ta ce, "Mecece hikimarka ta ɓoye matsayinka? Ya gyara zama, Hajiya ina son in samu soyayya ta tsakani da Allah bata abin hannu na ba, ina son in shimfiɗa sabuwar rayuwa ba irin ta baya ba." Ta yi ɗan murmushi cikin ƙasaita ta ce "Wannan yaro na ne, tabbas akwai hikima cikin abinda za ka yi. Na amince da haka, to ita yarinyar ta karɓe ka ya kuka yi?". Ya sunkuyar da kai,to har yanzu dai ban same ta sosai ba, na yi mata uzri yarinya ce sosai yanzu ne zata gama Sakandire su za suyi sauka a Islamiyyar su, haka nan kuma ni ne saurayin ta na farko. To ta kasa gane ko tana sona. Hajiya ta yi hiru cikin nazari, sannan ta ce Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi, za mu ci gaba da addu'a." Ya ce Ameen ina godiya sosai. Haka suka kasance cikin tattaunawa har zuwa lokacin da Juma ta shigo ta na jera flas na ƙosai da hankali da wainar ƙwai da na ruwan zafi ga kunun gyaɗa ga kuma kayan shayi. Shamaki da kansa ya Haɗawa Hajiya Shayi mai kauri kamar yadda ta buƙata, ya shirya mata komai sannan ya saka abinda kanshi ke so ya shiga ci suna ƙara tattaunawa.


🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu 600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


Mamakin kansa ya ke yadda ya ƙosa dare ya yi yawan murmushin da ya ke in ya yi shiru ya sa yaran kantin suka soma tsegumin cewa maigida ya faɗa soyayya, musun da suka yi ya sa ɗaya daga cikin yaran mai suna Ɗahiru ya ce bari ya gwada shi. inhar haka ne zai gane. Ya kunna waƙar Hamisu Breaker ta soyayya. Yaje ya zauna a bakin Office ɗin yana ci gaba da shi'anin gaban sa. Daga ciki kuwa Shamaki ya yi tsam da ransa yana sauraron yadda mawaƙin ke yin falsafa akan so, sai kawai ya ƙwala wa Ɗahiru kira, ya amsa ya shigo cikin girmamawa yace "Gani Alhaji." Wai ku bakwa rabo da jin wakane duk da ita wannan naji ta yi daɗi da ma 'ana, amma waye ya yi ta ne, tura min ita a waccan wayar in yi wani nazari a kanta. Ya ɗauki wayar ya fita yaje yana basu labari suna dariya. Ranar haka ya yini jin waƙar. Da yamma ya kira Malam Bala direbansa ya ce a wanke mota zai fita bayan Isha'i. ya kuma fara lissafin zai bi ta Zeena Store ya kwashi alawoyi yaje Zeena Factory ya haɗa mata kayan ƙwalam na Snacks. Kamanta gurin wa zaka kuma wane matsayin kake a idon ta? Zuciyarsa ta jeho masa tambaya. ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce sai dai in nemi ɗata ko yalo? Ɗan tsaki ya saki sannan ya yi maganar da ƙarfi Ayaba da Lemo zan siya. Hassan dake cikin Office ɗin yana rubuta wani rasit ya ce "Karɓo wa za ayi Alhaji?" Ya dubi Hassan me nace? Yace,"Naji kana maganar Ayaba da Lemo." Ya yi ɗan tsaki eh da za a karɓo ne amma bari sai na fita sai in siya kawai.

Nikam kafin Isha'i na shirya tsaf, ba sallah zan yi ba don haka na kame ina jiran zuwansa, gabana kuwa sai faɗuwa yake ina ayyana yadda zanji idan mun kasance muna hira,ina ta baiwa kaina shawarar ya kamata ace ina zaɓo kalamai inzan furta masa,sannan kuma kar inyi masa magana da irin muryar da nake yi wa kowa hakan zai sa in ƙara birge shi. Take na gamsu da hakan,kuma na yarda shi na musamman ne.
Shamaki ya wahala kafin ya samu kayan da za su nuna shi a talaka,suma dai yadine fari mara nauyi, yanada mugun tsada amma ba kowa zai iya gane hakan ba sai wanda ya san kaya. Ya zube wayoyinsa guda huɗu a kan gadonsa, sannan ya saka mai boturan wadda ya sawa sabon layi domin ita kaɗai a alajihu agogo da zobe na azurfa duk ya zube su. Ya nufi sashen Hajiya.
Ta ƙare masa kallo sanna ta amsa gaisuwarsa. Ya ce zanje gurin Rabi a ne kamar yadda na sanar da ke tun shekaran Jiya. Ta ce "Na fahimta,kaje Allah ya bada nasara,kuma ka ce ina gaisheta. Sannan ka tabbata ka sami zuciyarta a yau,domin na lura kana matuƙar sonta. Allah ya yi muku albarka gabaɗayan ku." Ya ce Ameen sannan ya miƙe ya fice da sauri. Ta bishi da kallo a fili ta furta akwai matsala ya kamu da yawa, ni da nafi son ya samo wadda ta fi son sa dole inyi wani abu.
Ya dubi Malam Bala yace, in ka isa gurin masu Lemo na ɓawo za ka karɓo. Da suka isa ya rasa na nawa ya kamata ya siya yace Malam Bala ga dubu biyar su yi kashi biyu. Da aka kawo ya ga da yawa yace Malam Bala ka dauki kashi ɗaya. Sai da suka gota lungun sannan ya sauka,yace ka je zan kira ka nan da awa biyu. Ya taka da ledoji biyu a hannunsa ya dawo ya shiga lungu.
Jafar ya shigo da ledoji suna rinjayarsa, yace Umma wai gashi inji wani mutum wai yace Yaya Baby taje. Cikina ya juya da sauri na ɗauki buta zan shiga banɗaki, Umma ta ce "Ke dakata lafiyarki da tun ɗazu kuna zaune sai da yazo zaki tarki shiga banɗaki?" Nace wallahi Jafar yana faɗa sai naji cikina ya juya, na shige da sauri. Ina jiyo Jamila tana tsaki tana mitar "Yanzu da wari zaki gunsa?" Na fito na sake shafa turare sannan na fita na samu har Jamila ta shinfiɗa masa tabarma ta aje masa ruwan fiyawata.
Cikin girmamawa na gaida shi, na kuma tambayi Hajiya da yara. Yace tana gaida ni kuma duk suna lafiya. Nace shine harda wata ɗawainiya haka? Ni fa karka matsawa kanka a irin wannan yanayin ba sai ka min wata ɗawainiya ba. Ya ce "Karki damu, ina da halin yin hakan ne, yanzu ki bani labarin soyayyata. Na ƙosa mu soma musayar ta ni da ke, domin har na soma zama wawa ina kasa jurewa tunaninki." Nace koda bansan so ba, na tantance kai na musamman ne, duk wani kai kawo nawa kana zuciyata kuma na kasa gano aibunka, zuciyata tana faɗa min cewa in maka uzri kuma in amince ka zama mijina. Na gamsu sosai da shawarar zuciyata kuma na amince ka zama mijina in ina gidanka sai ka koya min soyayyarka. Na kai ƙarshen maganar tare da rufe ido. Ya ce "Alhamdulillah wannan yanayin da ki ke ji shima alamun so ne Baby, yanzu sai mu yi maganar aure, zuwa wane lokacin ya kamata mu zama miji da mata?" Nace ai wanna da su Abba zaku yi magana. Ya numfasa "An saka ranar da zakuyi walimar sauka?" Nace har an fitar da katin manyan baƙi an raba tun wancan satin. Na mu sai wannan satin insha Allahu zan baka ina fatan zaka zo ka ga karatunmu? Ya ce "Ai ina tunanin a haɗa bikinmu da saukar ki... Kai! Na katse shi. Na yi ƙasa da murya. Saura sati biyar fa ayi walimarmu yaushe aka shirya? Ya numfasa "Wane irin shiri kike magana a kai?" Na sunkuyar da kai, yaushe ka kawo kuɗi har aka sa rana, kuma ga maganar lefe su Abbanmu ga maganar kayan ɗaki abin da za a ci abiki, kaga duk abin dubawa ne. Yace "Kinyi gaskiya, amma zan ɗauki wani kuɗin dashi na zan bada kuɗi cikin satin nan a kawo dubu hamsin, sannan nasan dai ko ba lefe zaki aure ni ko?" Har a zuciyata zan iya hakan Yaya, sai dai matsalar iyayena basu da halin yimin kayan ɗaki a cikin wata guda, yanzu ma suna ta abinda zasu fiddani kunyar walimar saukar nan da zamuyi. Yace to ke da me za kuyi a saukar? Nace walima ce kawai a gida, ya ce nawa zaki kashe... Na katse shi da A a bazan ɗora maka nauyi ba, kar ka rene ni da haka, kabari in saba da yanayinka na asali,ka koya min yadda zamu rayu a lokutan akwai ko na babu. Ya ɗaga hannunshi ɗaya tare da faɗin kinga dakata kiji. "Inada shine shiyasa, kuma ba roƙona ki ka yi ba, kawai ki faɗa min nawa zai ishe ki ko inje in ɗauki kuɗin da zan kawo miki na aure inyi gaban kai na da su.". Na ce Umma za su min faɗa, duka yau ne zuwan ka na biyu fa, kuma... "Kuma me?" Nace shike nan dubu uku ne. Ya ce "To zan baki sai kuma me?" Na ce shike nan. Yace "Ankon walima da hijabi Lemo da kalanda kinsan dai nima na taɓa saukar nan nasan ya ake yi. Na ce ai duk Abba da Umma sun sai min. Ya ce to shike nan zan kawo miki dubu uku jibi mu koma kan maganarmu in turo a kawo kuɗin ko?"Nace bari in faɗawa su Umma, yace don Allah da kin shiga ki sanar musu,kuma zan kira komai dare yau inji ko sun amince." Na ce to shike nan, amma nima zan nemi wata alfarma a gurinka. Ya tattaro hankalinsa gurina "Faɗi da sauri in har zan iya kin samu." Ina son in ci gaba da karatu ko da makarantar koyon aikin jinya ne. Ya yi shiru can yace "Bazan miki alƙawari ba,saboda wasu dalilai amma mu aje maganar zuwa gaba." Nace to shike nan. Ya kwai kwayi muryata "Na gode Babyna." Na sa hannu na rufe fuska ta. Yace to bari in tafi, nace yau naga baka zo da Kekenka ba? Ya ce tayar ce ta yi faci ɗazu ina hanyar dawo wa daga kasuwa, na ce to Allah ya tsare ya ce "Ameen muka yi sallama cikin shauƙi da ƙauna.
Na samu Abba yana ta faɗa wai ko dai nice nace wa Aliyu zan sha Lemo domin yaran zamani ba abin yarda bane. Na zauna na ce Abba wallahi ban roƙeshi ba yanzu ma dan baku san ya mu ka yi da shi ba ne, cewa ya yi in faɗa masa abinda zan kashe a walima lokacin sauka zai bani kuɗin nace a a ya bari shine ya ji haushi. Umma tace "Abban Baby na faɗa maka ko Jamila bazata yi roƙo ba, bare kuma Baby, duk da ba 'a shedar 'yan zamani akwai abinda zaka shedi ɗanka dashi, yace "To Allah ya muku albarka dukanku har da ke Ummar ta su,domin tarbiyyar ki ce, shi kuma Allah ya saka masa da alkhairi ya jiƙan magabata." Muka ce Ameen ya ce "To sai a yanka aba kowa, ku rage akai gidan Yaya ba ma ci mu kaɗai ba." Jamila ce me yankawa Ni kuma na yi zugum ina tunanin ta ina zan fara sanar da iyayena saƙon shi. Umma ta ce, lafiya ke kuma ai Abban na ku ya gane ba roƙarsa aka yi ba. Nace ba wannan ba ne, haka ya ce wai a satin nan za a kawo kuɗi, kuma wai in kun yarda za a yi biki tare da walimar saukarmu... Tarin Umma ya sa nayi shiru ta ƙware da ayabar da ta ke ci, na tashi da sauri na kawo mata ruwa ina yi mata sannu.Abba ya taso shima cikin sauri yana mata sannu. Bayan ta samu kanta tana maida numfashi tana magana, "Baza a yi gaggawa ba gaskiya sai anyi bincike, kuma bamu da halin biki a wata ɗaya." Abba ya ce ki daina magana kin ƙware ki yi shiru tukunna. Sai da ta samu natsuwa sannan Abba ya ce, "Inda haka zata samu zanfi kowa murna ace na aurar da Baby a ranar saukar ta. To amma hidimar da yawa ga haihuwarki ko yau ko gabe." Umma tace, ta haihuwa mai sauƙi ne, ba taron suna zanyi ba Allah dai ya sauke ni lafiya. Abba ya ce "Ameen, dama tun farko ya faɗa min aure ya zo, sannan ya taɓa aure kinga dole ya buƙaci aure da wuri, ina ga abinda za a yi mu amince su fara kawo kuɗin sai mu yi maganar da ta dace." Umma ta ce to shikenan ke sai ki faɗa masa in yazo. Na sunkuyar da kai na ce yace infaɗa masa a waya zai kira a ta Umma in yaje gida. Abba ya ce to. Sai ki sanar dashi. Da wayar Umma na shiga ɗakinmu ina ta jiran kiransa har bacci ya kwashe ni.

Shamaki ya ƙosa ƙwarai ya sallami mutanan da yakan gansu in an idar da sallar Isha'i, suka tsare shi, yana sauraron buƙatunsu wanda zai yi a gurin kamar kuɗi marasa yawa ya basu wanda sai ya tura su je Zeena Foundation sai ya tura su. Ya ƙagara sosai dan tun jiya ya so jin yadda Baby suka yi da mahaifanta, amma da yaga dare ya yi sai ya barwa yau. Ya dubi Malam Sabitu wanda shi ne limamin masallacinsu da ke jikin gidansu ya ce, Malam zan shiga gidan gobe zan baka kati ka ba mutumin sai a kaishi Zeena Hospital za su min magana game da abinda za' a biya. Ya ce "To Allaji Allah ya ƙara arziƙi muna godiya." Shamaki cikin ƙosawa ya ce ba komai, Malam Aba sauran jama'a haƙuri ina da uzri a ciki. Liman ya ce "To insha Allahu Ubangiji ya rufa asiri."
Kamar ya wuce amma dole ya shiga gurin Hajiya, tana lazimi, Azima tana gefe tana jira ta kammala dan ta mirza mata manta na ƙafa. Ya zauna shima yana jira, zuciyarsa ta tafi matuƙa ga tunanin Baby, nan da wata ɗaya tana gidansa zai bata rayuwa mai kyau, zai maida ita sarauniyar shi.,.. Yaya Shamaki! Muryar Azima ya ji ta kira sunan shi da ƙarfi, a firgice ya waiga ya dube ta tare da faɗin Baby lafiya?" Sai kuma ya dawo cikin hayyacinsa ya dubi Hajiya wadda ta tsare shi da ido, yace sannunku Hajiya. Bata amsa ba sai ta kalli Azima tace je ki dawo. Ta maido duban ta gare shi, "Aliyu." Ta ambaci sunan sa, ya ɗan zaro ido kafin ya zabura ya amsa da cewa na am Hajiya. Cike da Tsoro ya ke Domin a duk ranar da ta ambaci sunansa to ya tabbatar ranar ya kai maƙura gurin ɓata mata rai. Ta numfasa "Faɗa min tunanin me ka ke yi?" Yace ba wani abu bane waya nace wa yarinyar nan zan mata tun jiya to ban samu na cika alƙawarin ba. Ta nuna shi da yatsa shi yasa ka shigo gida da wuri ba domin ka gama jin matsalolin mutanan da ke da buƙata a gurinka ba? Ni kuma ka zo ka tasani ka faɗa kogin tunani, to in na janye amincewa ta da wannan yarinyar ya zaka yi kenan?" Gaban shi ya yi mummunar faɗuwa cikin sauri yace, Nasan baza kiyi haka ba Hajiya! Ta kuma zaro ido cike da mamaki, abinda ta tsammani zataji shine Duk yadda ki ka yi daidai Hajiya. Ta lumshe ido cike da damuwa, can ta ce "Shikenan yau nasan baza muci abincin dare da kai ba,bare muyi wasu bayanai ko wani lissafi,ka tashi kaje ka yi wayar." Ya san gatse ta yi masa,dan haka sai ya ce, za muyi lissafi Hajiya, abincin ne yau cikina duk a cushe ya ke. Ta kuma yin shiru tabbas ko ita yau abincin nan ba zai ciyu a gareta ba, ta numfasa sannan ta kai hannu ta ɗauki wayar ta a gefe ta shiga neman Hassan. Ya ɗauka cikin girmamawa suka gaisa, ta ce dama zan tambaye ka yau da aka kawo abinci kasuwa Shamaki ya ci Hassan ya ce "A'a kayan marmari ya ci sosai yau." Ta ce to na gode. Ta sake maida kallon ta ga Shamaki, tashi kaje za muyi magana da safe, yanzu kam bana zaton kana iya fahimtar duk abin da zan ce maka." Ya ce haba dai Hajiya karki tashi hankalin ki, wallahi abin ba kamar yadda ki ka zata bane. Ta nuna

Please Login or Register in order to submit comment