Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi zafi dan yaga ogan nasu ya hau sama, "Zaid kana son ta" Hameed ya fad'a yana kallan Zaid da yake tsaye.

"Mtsww bakwa ganewa ne wai? Nace muku na tsane ta bana son ta bana son me son ta kar wanda ya kuma cemin ina son ta" ya fad'a cikin b'acin rai yana kallan dukkan su, dariya Hameed yayi ya mik'e tsaye shima yace, "Shikenan munji baka son ta amma kana son ganin ta, yanzu dai ya maganar mu?". "In anjima ka dawo nan ka same ni muyi maganar." "Ba'a gida ba?". Tab'e baki yayi yace, "Bazan koma gida yanzu ba har sai Daddy ya nemi ni, Wizzy muje ka kaini gidan su."

Zaro ido Wizzy yayi yace, "Gidan su wa?".

Maimakon ya bashi amsa sai yaja tsaki tare da ficewa daga gidan, da sauri Mugu da Wizzy suka bi bayan sa Hameed yana ta dariya.

A b'angaren Ibteesam kuwa suna zaune a harabar gidan su ita da Khalid suna hira, Ibteesam ta kalli Khalid tace, "kasancewar kai lawyer ne ina so ka tsaya min wajan bi min hakki na a wajan azzalumin da ya sace ni." Gyara zama Khalid yayi yace, "Baki da damuwa Ibteesam nake yiwa wani ma balle ke? Fad'a min akan abinda za'a yi k'arar sa." Ajiyar zuciya tayi kana tace, "Na farko kaga bashi da wani dalili mai k'arfi da ya sace ni, na biyu kuma duka babu irin wanda bansha ba gabad'aya jiki na shatin dukan sane......" ta k'arasa fad'a muryar ta na canjawa zuwa muryar kuka.

Hankalin Khalid ya tashi sosai ya rud'e ganin tana kuka ya saka yace, "Ki daina kuka dan Allah duk abinda kike so za'a amma ki daure ki goge hawayen nan ina jin zafin su a zuciya ta". Hannu ta saka ta goge idon ta ta kalle shi tace, "Yanzu yaushe za'a shigar da k'arar?". "Kinga yau saturday sai dai mu bari zuwa monday, amma bayan wannan bai miki komai ba?" Ya tambaya yana kafe ta da idon sa.

Zata yi magana kawai aka bud'e gate d'in aka shigo without excuse, d'ago kai sukayi dukkan su suka kalli wanda suke shigowa, mik'ewa tayi a gigice tana zaro ido waje tana nuna su da yatsa, caraf taji an rik'e yatsan nata dan bata san ya k'araso bama an lak'wasa shi da k'arfi, ihu take sosai amma hakan bai hana ya saki hannun nata ba, "Ke wace da zaki nuna ni da tsaya? Nace wacece ke?" Ya fad'a yana zaro mata idanu.

Cika mata hannu yayi ya zuba hannayen sa a aljihu yana k'arewa gidan nasu kallo tare da tab'e baki, "Wizzy" ya furta a hankali yana sake kallan gidan, "Mai gida" ya amsa yana matsowa kusa dashi, "ashe ma yarinyar y'ar matsiyata ce amma take min rashin kunya." "Mai gida ka gani da idon ka" ya fad'a yana kallan sa.

"Su waye ku? Daga ina kuke zaku shigowa mutane gida haka kawai babu neman izini?" Khalid ya fad'a yana kallan su da b'acin rai, kallan Khalid Zaid yayi ya mayar da kallan sa ga Wizzy tare da furta, "Shine?". Wizzy yace, "Shine mai gida." K'arewa Khalid kallo Zaid yake tun daga sama har k'asa kamar yadda shima yake k'are masa kallo, Khalid shima fari ne amma ba irin farin nan sosai ba yana da tsayi sosai, yana da kyau shima dai-dai nasa, "kai kasan wace waccan?" Ya tambayi Khalid yana nuna masa Ibteesam.

"Ban sani ba sai ka sanar dani" ya fad'a cikin gatse yana hararar sa, "Love shine fa wanda nake baka labari, shine d'an shaye-shayen da nake fad'a maka yanzu" Ibteesam ta fad'a daga can gefe tana hararar sa. "Ohh i see shiyasa kana ganin sa kaga mara tarbiyya, wannan abinda yafi abinda yayi miki ma ai tsaf zai aikata kalle shi fa." Bai kula Khalid ba sai takawa da yake a hankali ya zura hannayen sa cikin aljihun wandon sa, yana zuwa kusa da bai tsaya jiran wani abu ba ya d'auke ta da mari mai zafi, "kar a sake" ya furta yana d'aga mata gira d'aya.

Sai da Ibteesam ta kifa sabida yadda marin ya shige ta tunda unexpected taji marin, ganin hakan ya saka Khalid cikin masifa yace, "Kai waye da zaka zo har cikin gidan su ka dake ta? Wato shaye-shayen naka har ya kaika ga zuwa har gidan su ka dake ta bayan dukan da tasha da ka d'auke ta?". A fusace ya juya ya kalli Mugu yace, "Ku rik'e min shi". Ai ba musu suka kama Khalid suka bank'ara hannayen sa kamar kaza, dawo da kallon sa yayi ga Ibteesam fuskar sa a had'e kamar kullum yace, "Kee kalle ni daga da kyau ki fad'awa wannan kod'ad'an saurayin naki ya fita a harkar ki tun kafin na saka a illata shi" ya fad'a yana nuna ta da yatsa.

"Wallahi baka isa ka raba mu ba domin kuwa shine wanda zan aura" ta fad'a tana jifan sa da mugun kallo, "Keee! Har ni zaki kalli ido na kice min shine wanda zaki aura,? Kina da hankali kuaa" Ya fad'a yana yin kanta kamar zai dake ta.

Tsayawa yayi ya dawo da baya ya kalli Khalid yace, "Kana ji tun muna shaida juna da kai ka fita harkar ta, in ina tare da abu nawa ne ni kad'ai ba'a rab'ar sa in kuma kana so ka bak'unci lahira shikenan" ya fad'a yana d'age kafad'ar sa.

"A kan me zakace na rabu da ita? Kai waye d'in ta?" Khalid ya tambaya yana kallan sa, juyowa Zaid yayi ya zuba masa ido kafin ya mayar da kallan sa ga Ibteesam da take tsaye tana hararar sa, "baka buk'atar kasan waye ni d'in na fad'a maka ne kawai in kaji" ya bashi amsa yana d'an dafe jijiyoyin kan sa da suka fara harbawa, "wallahi baka isa ka raba mu ba kayi kad'an, kome kake tak'ama dashi nima ina tak'ama dashi". Yana juyowa ya d'auke shi da mari mai zafin gaske ya nuna shi da yatsa yace, "bana magana ana magana ka gane ko? In naso yanzu a nan wajan zan saka a fito min da kayan cikin ka ina yi maka warning ne badan kafi k'arfi na ba ka gane?".
"Ke kuma in na sake ganin ki da wani ranki ne zai b'aci, zan b'ata miki rai irin wanda baki tab'a tunani ba" ya fad'a yana kallan inda Ibteesam take yana nuna ta da yatsa.

"A matsayin ka nawa? Wallahi baka isa ba kayi kad'an. "

"Matsayi na wanda ya isa dake in kuma kina ganin kamar hakan bazai kasance ba ki k'ara ki gani."

Juyawa yayi da niyar barin gidan sai ya juyo ya dawo inda take yace, "and in na sake ji in kira wannan da suna Love wallahi sai na fasa miki baki, in kina musu kuma kiyi naji".

"Wallahi baka isa ba sabida ba kaine ka haife ni ba, na tsane ka bana son ka ba kuma na qaunar ganin ka."

"Nima na tsane ki bana son ki bana qaunar mai sonki, but na tsani na ganki da wani, wallahi na sake ganin ki da wani ranar kin jawo masa dan sai na saka an canja masa kammani yadda ko iyayen sa basu gane shi ba, umarni nake baki bawai shawara ba, i hate u alot but kika sake na ganki da saurari wani ko kika tsaya da wani ina......" ya nuna ta da hannu alamun zaki gani.

_Tofa akwai rikici fa... ga Zaid ya fara nuna iko akan Ibteesam, Anya zata bi dokar da ya kafa mata,? meye dalilin Ibteesam na cewa Zaid yayi mata fyad'e bayan babu abinda yayi mata? Wanne shiri take dashi a kan hakan...? kar ku manta a gida Eman tana can tana jiran dawowar mijin ta Zaid, yaya kuke gani anya Zaid zai karb'i auren Eman,? Wanne irin rikici za'ayi dashi a kan hakan? Gefe d'aya kuma ga cikin jikin Amina, Anya Zaid zai barta da cikin nan duba da yadda ya tsane ta da kuma tsanar had'a zuri'a da ita?? Y'an uwan Daddy fa zasu bar cikin nan ya zauna lafiya kuwa,? Anya Ibteesam zata karb'i Zaid a matsayin mijin ta? Ya matsayin auren su zai kasance ita tace ta tsane shi shima yace ya tsane ta,? Umma fa? Anya zata bar auren Ibteesam da Zaid? Khalid fa ya zaiji duk ranar da ya samu labarin Ibteesam matar Zaid ce,? Su waye iyayen Ibteesam? A ina suke?..... kar ku sake a ayi babu ku da a baku labari ai gwara ku bayar.._💃💃🥰

_free pages sun k'are ki biya kud'i k'alilan ki karanta a nutse ba takura babu tunanin me zai faru gaba dan complete za'a a baki, #200 kacal 09030398006._

Last free page.✋🏽

Comments and share fisabinillah

*ƘASAITAR SO!*



*12*
*Bonus page*⛹🏼♀️😻

"Hayaniyar me nake jiyowa haka ne?" Ta fad'a lokacin da ta k'araso wajan sanye da dogon hijjabi tana kallan su, a guje Ibteesam tayi wajan ta ta fad'a jikin ta tana kuka tana cewa, "Umma kin ganshi ya sake biyo ni nan bayan azabar da yayi min lokacin da ya d'auke ni" ta fad'a tana nuna mata Zaid da hannu da ya tsaya cak yana kallan su.

Hannu ya zuba aljihu ya k'araso kusa da Umma fuskar sa a had'e kamar koda yaushe yace, "Ammm Her mother right?" Ya tambaya yana nuna Ibteesam da hannu. Umma bata amsa masa ba sai kallan sa da take cikin mamaki, "Umma or Mama whatever ki sanar da ita bana san na sake ganin ta da wani in kuma tak'i" ya juyar da kansa gefe d'aya yayi k'wafa ya sake juyowa ya kalle su yace, "In kuma tak'i zata jawowa kanta za kuma ta jawowa wanda na gansu da ita d'in, u know Umma bana son ta amma kuma bana so na ganta da wani ki ja mata kunne ba'a tab'a tsallake abinda na saka" ya fad'a yana d'age gira guda d'aya yana kallan Ibteesam.

Umma da ta daskare a wajan sabida mamaki da takaicin sa tana sake hango zallar rashin mutunci a tare dashi da ita yadda ake bata labarin sa gani tayi ya wuce hakatace, "To kai a wa d'in ta,? Bayan sace ta d'in da kayi baka hak'ura ba sai da ka biyo ta har cikin gidan su kana kafa wata wasu banzayen sharud'an ka,? Ka shiga hankali ka ka kuma fita daga sabgar ta ka kuma fita daga gidan" ta fad'a cikin tana kallan sa cikin takaicin sa.

Ido kawai ya zubawa Umman tabbas badan tayi masa kwarjini ba babu abinda zai hana bai kifar da ita a wajan ba, naushin iska yayi ya furzar da iska a bakin sa ya juya k'wayar idon sa ya kalli Umma yace, "Umma lokaci d'aya naji ina ganin girman ki in badan haka ba baza ki tsaya a gaba na kina fad'a min wannan maganar ba dan da yanzu na b'arar dake, kimar ki ya saka nake cewa ki mata warning amma naga kamar abin bazai yu ba, is okay we shall see" ya fad'a yana d'auko black d'in glass a aljihun sa ya kafa a idon sa.

Juyawa yayi da niyar barin gidan ya jiyo muryar Ibteesam tana fad'in, "Banza d'an shaye-shaye kawai wallahi nafi k'arfin ka". Cak ya tsaya ya dawo da baya, hannun sa ya cusa aljihun wandon sa ya zaro karan sigari guda d'aya ya kunna mata wuta ya saka a bakin sa, Zuk'a d'aya yayi mai kyau ya cillar da ita a wajan, unexpected Ibteesam taji ya jawo ta da k'arfin gaske ya matso da fuskar sa daf da tata ya sakar mata hayakin da ya tara a bakin sa, tari ta fara tana k'ifta ido k'wayar idon ta yana juyawa kamar zata suma, sakin hannun ta yayi tayi baya ta dafa bango tana cigana da tari kamar zata shid'e, kallan Umma yayi yaga kawai ta zuba masa ido da alama ta rasa abinda zata ce masa ne ya juya ya kalli Khalid da yake hannun su Wizzy shi kuma Ibteesam yake kallan a rud'e, d'an murmushin gefen baki yayi ya kad'a kawai ya fice daga gidan su Wizzy suka saki Khalid tare da rufa masa baya bayan Wizzy ya cillo mata wayar ta.

Yana fita ya shiga mota suka fito suka shiga suma suka shiga tare da barin unguwar, tafiya suke a hankali babu wanda yake magana sai sautin muryar kizz Daniel da take tashi cikin wakar oshey, kyakykyawan murmushi Zaid yayi wanda yayi sanadin bayyanar haqoran sa masu kyau da haske a jere reras, sitiyarin motar ne yaso kubcewa daga hannun Mugu sabida shagala da kallon Zaid da yayi, gimtse fuska yayi ya kalli Mugu a fusace yace, "kashe mu zakayi?". "Yi hak'uri mai gida na shagala da kallon kane, tunda muke ban tab'a ganin kayi murmushi haka ba gaskiya murmushi yana yi maka kyau sosai" Mugu ya fad'a a dai-dai lokacin da suke hawa flyover.

Had'e rai yayi baice komai ba dan shi kansa bai san meyasa shi murmushin ba abinda ya sani kawai shine tuna fuskar Ibteesam da yayi shine ya saka shi murmushi a lokacin, wayar sace tayi k'ara ganin sunan Daddy ya saka ya d'auka tare da sallama, da to ya amsa ya kashe wayar yace, "Muje gida".

A gidan su Ibteesam kuwa tun bayan fitar su Umma take wajan kamar an dasa ta sabida tunanin da ya cunkushe mata kai, babu abinda yake bata takaici sai in na tuna Zaid mijin Ibteesam ne sai abin ya bata haushi taja tsaki.

"Khalid kayi hak'uri dan Allah kaji ni ban san me mutumin nan nan yake so dani ba" Ibteesam ta fad'a tana kallan Khalid da ya matso kusa da ita. "Babu komai kar ki damu amma yana da kyau a shigar da k'arar nan da wuri duba da irin abinda ya kuma zuwa yayi yanzu gaskiya" ya fad'a yana kallan Umma da tayi shiru.

"Bara Abban nasu ya dawo muji abinda za'a yi duk yadda akayi zan saka tayi maka waya tunda ga wayar ta sun dawo mata da ita" Umma ta fad'a a sanyaye tana kallan Khalid cikin rashin abin yi, tausayin sane ya kamata ta da ta tuna bashi da hurumin da zai aure Ibteesam a yanzu duba da auren da yake kanta,daga haka suka yi sallama ya tafi su kuma suka shiga gida.

"Yanzu Umma haka za'a k'yale wannan mutumin duk abinda yayi min yayiwa banza? Kina gani gashi yanzu har gida ya fara biyo ni yana duka na dan akwai babban sa yana da kud'i" Ibteesam ta k'arasa fad'a cikin kuka sosai. Kwantar da ita Umma tayi a kafad'ar ta tace, "Kiyi hak'uri ki daina kuka za'a hukunta shi insha Allah, ki jira in Abban ku ya dawo zamu san abinda zamuyi a kai". Mik'ewa kawai Ibteesam tayi ta shiga d'aki ta kwanta a kan gado tana kuka.

Zaid kuwa koda ya koma gida bai shiga b'angaren sa ta cikin gida ba direct kawai saman sa ya hau, tunda ya bud'e k'ofar d'akin ya shak'i khamshin da bai saba dashi a d'akin nasa ba, yatsine fuska yake yana k'ara jan numfashi dan ya tabbatar da khamshin da yake ji, tabbas khamshin turaren wuta ne ba khamshin air freshener ba, "Me ya kawo turaren wuta falon nan?" Ya tambayi kansa yana sake shak'ar khamshin falon, sake jan numfashi yayi a karo na biyu ya tabbatarwa kansa turaren wuta ne akayi kuma ya kama d'akin, dogon tsaki yaja dan shi wannan khamshin turaren takaici yake bashi.

Turus yayi ganin an canja tsarin falon gabad'aya komai an canja masa mazauni a falon, Ran sa ya b'aci ya kama k'ugu cike da takaici yake furta, "amma wannan clener d'in ya raina ni da yawa, har aikin da ban saka ayi ba yayi mi,? Lallai k'arshen aikin sa dani ya zo" ya fad'a yana sake k'arewa falon kallo da mamaki.

A fusace ya nufi cikin d'akin yana bud'e k'ofar yayi karo da abinda ya bashi mamaki tare da d'aure kai, a hankali yake takawa cikin d'akin yana sake kallon kan gadon ganin mutum a kwance cikin bargon sa yana bacci cikin kwanciyar hankali, tsaye yayi yana kallo gadon cikin mummunan b'acin rai da ya bayya k'arara a kan fuskar sa.

Da hanzari ya saka hannu ya yaye blanket d'in, abin ne ya kuma razana shi ganin mace a kwance a kan gadon sa har lokacin bata tashi ba, k'wafa yayi ya fita falo ya bud'e fridge ya d'auko ruwa mai sanyin gaske ya dawo d'akin ya bud'e gorar ruwa ya juye mata shi tass a kan ta, a firgice Eman ta tashi tana wani irin numfashi sabida yadda ruwan ya ratsa ta, bata gama dawowa dai-dai ba ya shak'e mata wuya da hannu d'aya hannu d'aya ya dinga marin ta babu k'akkautawa, magana take so tayi amma yadda ya shak'e mata wuya ta kasa ga marin da yake ta kaiwa fuskar ta radad'in sa har cikin k'ashin ta take ji.

Cillar da kanta yayi ta bugu da fuskar gado goshin ta ya fashe, hakki take tana neman numfashin ta ya dawo dai-dai amma abin ya ci tura ji take kamar zata mutu, a fusace ya nufi wardrobe d'in sa ya bud'e ya sake karo da abinda ya sake mata masa rai, kayan take a jere reras kamar d'akin ta, a fusace ya jawo belt yana nad'ewa a hannun sa ya nufo ta ya fara zabga mata babu kama hannun yaro, ihuu take tana neman guduwa yana binta yana dukan ta, a guje ta bud'e k'ofar d'akin ta fito ya rufa mata baya tana gudu yana binta da sassarfa har k'asa, bai kula da wanda suke zaune a falon ba nufar ta kawai yake kamar zaki yana wani irin wuci kamar zaki.

Bayan Anty Amina tayi a guje tana kuka jikin ta na rawa ga gaban rigar ta duk a jik'e, bai tsaya ba ya isa inda take tsaye yana k'okarin jawo ta tana sake rik'e Anty Amina, ransa ya sake b'aci ji yake kamar ya had'a su duka biyun ya zane dan ma haushin ta yake ji, "Kai Zaid meye haka ne?" Daddy ya fad'a a fusace yana isowa wajan tare da kwace belt d'in hannun sa.
Nuna ta kawai yake da hannu bakin sa na rawa yana so yayi magana amma ya kasa sabida b'acin ran da yake d'awainiya dashi.

"Zaid baka da hankali ne wai? Mace kake duka da belt d'in hannun ka dan baka da hankali eheee?" Daddy ya fad'a a fusace yana kallan sa da b'acin rai, "yanzu dan an raina ni a gidan nan har y'ar aiki ce zata hau sama na ta kwanta a kan gado na? Daddy me kake so nayi mata in ba duka ba?" ya fad'a shima da b'acin rai yana hakki kamar wanda yasha gudu ya k'oshi.

"Eman ce fa y'ar uwar kake ce mata y'ar aiki?." "Ina ruwa na da ita to? Ni naje inda take,? Kar ta sake zuwa inda nake har ta kwanta in ba haka ba wallahi zan b'alla ta."

"Zaid! Yarinyar nan da kake gani matar kace ba" Anty Amina ta fad'a tana kallan sa, hannun sa ya kalla yaga inda ya yanke da glass d'in oven sai ransa ya kuma b'aci ya kalle ta up and down yace, "Ina ruwan ki zaki saka min baki,? Kamar kun san na tsani ba da mutum nake magana ba ya saka min baki ko?" Ya tambaya yana zare mata ido.

"Zaid Eman matar kace kamar yadda aka fad'a maka" Daddy ya fad'a yana kallan sa, juyowa yayi ya kalli Daddy yace, "Daddy wai wacece matata?" Ya tambaya da alamun mamaki akan fuskar sa. "Eman wacce take tsaye a gaban ka matar kace ta sunnah shiyasa ta sauka a d'akin ka". "Matata?" Ya maimaita yana kallan Daddy shima shi yake kallo.

"Eh matar ka". "Daddy ya mukayi da kai akan maganar nan? Na fad'a maka tun farko bana so amma...." kasa k'arasawa yayi sabida takaicin da ya tokare masa k'irji. "Mun yanke hukunci ne matsayin mu na manyan ka ba shawarar ka muke nema ba ai". "Daddy sun yanke hukunci dai, na tabbata kai baza kayi min abinda bana so ba wannan aikin sune ba aikin ka ba, to wallahi bazan zauna da ita ba bana son auren, bazan tab'a yin abinda suke so ba" ya fad'a cikin d'aga murya.

"Zaid!" Daddy ya fad'a da b'acin rai, "Daddy kar kace komai bazan zauna da ita ba sakin ta zanyi". "Zaid indai na isa da kai kar ka sake ta". "Daddy a akan me? In kace haka ka cutar da rayuwa ta da yawa, kalle ta fa wannan abar ce matata" ya fad'a yana nuna Eman da har lokacin hakki take.

"Na dai fad'a maka indai na isa da kai kar ka sake ta" yana fad'ar hakan ya koma kan kujera ya zauna, a fusace Zaid yayi sama kamar an saka masa battery sabida sauri.

Tunda ya hau saman yake fashe-fashe duk abinda idon sa ya kai sai ya fasa shi in ba na fashewa bane sai ya b'alla shi, sai hakki yake jikin sa na rawa sosai, wardrobe ya bud'e duk kayan Eman ya d'iba ya dinga watso su k'asa yana fasa na fasawa, gabad'aya ya hargitsa d'akin hatta gadon ya d'aga shi komai yayi masa filla-filla.

Dafe kai yayi da hannu biyu d'akin na juya masa ya fara gani biyu-biyu, gabad'aya d'akin ji yake ya fita daga ransa tsanar d'akin da komai na ciki ya saukar masa lokaci d'aya, numfashi yake saukewa a hankali yana lumshe ido b'acin ransa na sake k'aruwa.

Bud'e k'ofar d'akin da akayi bai saka ya d'ago ba sai sake k'asa da kansa sa sa yayi, "Zaid lafiya?" Hameed ya fad'a yana k'arasowa cikin d'akin da sauri, kallon d'akin yake ganin d'akin a hargitse, kallon Zaid yayi yace, "Zaid me ya same ka haka?". Bai kula shi ba bai kuma d'ago kai ba, fita yayi falon ya d'auko masa ruwa mai sanyi ya bud'e gorar ruwan ya mik'a masa, karb'a yayi ya d'aga kai bai sauke kansa ba sai da ya shanye ruwa tass ya cillar da robar yana ajiyar zuciya.

"Lokacin da muna makaranta in ranka ya b'aci Mama kwantar da kai take a kan cinyar ta tana sha maka kanka, Allah ya jik'an Mama yayi mata rahma, Allah yasa Mama tana aljanna amin" Hameed ya fad'a cikin sanyin murya yana kallan yanayin Zaid, lokaci d'aya yanayin sa ya canja ya fara sauke ajiyar zuciya nutsuwa tana shiga cikin jikin sa b'acin ran nasa yana gushewa, k'aunar mahaifiyar sa da kewar ta suna maye gurbin b'acin ran da yake ciki, "Hameed wai aure su Daddy suka yi min, kuma wai y'ar gidan Uncle Sani aka bani na tsane ta Hameed bana son ta" ya furta a hankali idon sa a lumshe.

Shi kam rasa me zaice masa yayi sai yayi masa shiru yana jin yadda yake ajiyar zuciya, shi kansa yana mamakin wannan fushi da zuciya irin na Zaid lamarin sa har tsoro yake bashi, "kunje wajan yarinyar da ka tsana d'in?" Hameed ya tambaya dan ya kawar masa da zancen da yake yi dan shi bazai aibata masa iyaye ba dan kawai yace baya son su komai lalacewar su danjin sane, "Hameed bana so na ganta da wani raina b'aci yake, but na tsane ta" har lokacin idon sa a lumshe.

Jin ya bar waccan maganar ya sanya yayi ajiyar zuciya duk da yasan bai bar maganar ba, "Zaid ka bar batun ka tsane ta kana son tane." Sai a lokacin ya bud'e jajayen idon sa ya kalli Hameed yace, "what?". "Yess Zaid wannan shine so kana son ta ne shiyasa kake kishin ta, kasan dai bana yi maka k'aryato ina so ka yadda ka kuma tabbatarwa kanka son ta kake" Dogon tsaki yaja ya mik'e daga zaunen da yake yace, " Sau nawa zan fad'a muku ne wai,? Ni bana son ta bana k'aunar ta abinda na sani game da ita shine kawai ina so na ganta final, mu koma hotel d'in can na tsani d'akin nan gabad'aya" yana gama fad'ar hakan ya fice Hameed ya bi bayan sa yana masa kallon mamaki.

_Masoyan K'ASAITAR SO ga bonus page na baku🥹💃🏼 sai na jiku domin duk wanda ya bari labarin nan ya wuce shi I swear yayi missing🤣 duk yadda kuke d'aukar sa wallahi ya gota nan, akwai chakwakia a cikin sa ba kad'an ba ga soyayya me tsayawa a rai da zuciya. Naira dari biyu kacal a

Please Login or Register in order to submit comment