Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne amma bayan shi dan Allah ka b'oye farin cikin ka a zuciyar ka kar ka bari ya bayyana" ta fad'a tana had'e hannayen ta waje daya idon ta na kawo ruwa. Sauke hannun ta yayi yace, "Kar ki damu Amina nayi miki wannan alqawarin duk da ban san dalilin ki na fad'ar hakan ba amma zan miki." Murmushi tayi tare da ajiyar zuciya tace, "Nagode sosai Allah ya inganta mana". "Amin Minali, ina zuwa" ya fad'a yana ficewa da sauri kamar zai fad'i.

Ajiyar zuciya tayi ta bishi da kallo tana aiyana abubuwa da yawa a ranta, fargabar ta d'aya bai wuce ace su Yaya babba sun san da maganar cikin jikin ta ba shiyasa ta saka Daddy yayi alqawarin bazai fad'a ba dan matsawar ya fad'a tabbas sai sun salwantar da cikin dan baza su tab'a bari ya rayu ba, murmushi tayi tana aiyana irin abubuwan da zata tara da cikin jikin ta.

Lokacin da Daddy ya sakko lokacin y'an uwan sa suka shigo gidan, turus yayi ya kalle su yace, "Sannun ku da zuwa" ya fad'a cikin fara'a da annushuwa tare da k'arasowa cikin falon.

Da yauwa suka amsa suka zauna suka gaisa, Yaya babba yace, "Abubakar kamar yadda na sanar da kai jiya hakan ce ta kasance, ga goro da alawa nan an d'aura auren Zaid da Eman d'azu a masallaci anjima kad'an zata tawo nan gidan mijin ta bama buk'atar wani shagalin biki." Tunda ya fara magana kawai Daddy ya zuba masa ido yana kallan sa cikin mamakin k'arfin hali irin na baban Yayan nasa, kasa furta komai yayi sai sauraran maganar su kawai da yake yi dan shi ban san abinda zai ce ba kuma, "to daman wanne shagali za'a yi abu na gida, anjima amarya zata tare sai kayi masa waya duk inda yake ya dawo amarya bata tare ango baya nan ba" Yaya Bala ya fad'a yana kallan Daddy da ya k'ame a wajan kamar an dasa shi.
"Kayi shiru baka ce komai ba?" Yaya babba ya katse masa tunanin da yake yi, murmushin k'arfin hali yayi yace, "To me zance tunda kun riga kun yanke hukunci? Allah ya sanya albarka" suka amsa da amin suka shiga wata hirar daban.

Shi dai Daddy kawai yana jin su ne amma baya gane abinda suke cewa dan yasan akwai gagarumar rigima dan babu ta yadda za'ayi Zaid ya amince da auren Eman har ya zauna da ita matsayin mata abu ne mai wahalar yuwa, duk sai fargaba ta kama Daddy domin duk abinda Zaid zai aikata cewa zasuyi da sanin sa yayi, a haka suka k'araci surutun su suka kama gaban su suka bar Daddy da tunani.

*Kaduna.*

A tsaye take sanye da towel iya guiwa da alama daga wanka ta fito, sauri-sauri take ta shirya dan ba son tsayuwa take ba sabida ciwon da yake kanta, hannun ta ta saka tana nad'e gashin kanta taji an bud'e k'ofar a shigo d'akin, idon sune ya had'u dana juna ta zaro ido tare da saurin juyawa baya idon ta a kulle, ta baya yake k'are mata kallo tun daga fararen k'afar ta har zuwa inda towel d'in ya tsaya, wani irin abu had'd'iye ya ja k'afar sa a hankali ya fita daga d'akin tare da kullo mata k'ofar.

Tsaki tayi ta k'arasa da sauri ta sakawa k'ofar key, "Aikin banza aikin wofi kawai a shigowa mutane ba tare da neman izini ba balle sallama, na tsane shi wallahi bana san ganin sa ko mafarki" ta fad'a tana cigaba da shiryawa.

Shi kuwa tunda ya fita ya jingina da bango idon sa a kulle yana jin wani irin yanayi yana ratsa ko ina na jikin sa, shifa ya rasa abinda yake ji game da yarinyar nan ko wanne second ji yake kamar ana bud'e jikin sa ana saka masa ita kad'an-kad'an, numfashi ya fesar ta dafe kansa da hannayen sa zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri.

Sai da ya tabbatar ta gama shiryawa kana ya koma d'akin ya same ta a zaune a kan gado ta buga uban tagumi tana kallan waje d'aya, lumshe ido yayi yana tuno yadda ya ganta d'azu, saurin kawar da tunanin yayi yace, "Ki shirya a mayar dake gida" ya fad'a murya a sanyaye kamar wanda yasha ruwan sanyi.

Da hanzari ta kalle shi ganin babu wasa a fuskar sa ya saka ta mik'e tsaye tace, "Da gaske gida za'a kaini?" Ta tambaya muryar ta na rawa. D'auke kai yayi daga kallan ta kana yace, "Na tab'a yi miki k'arya ne?." Saurin girgiza kai tayi alamun a'a farin ciki na bayyana a fuskar ta, "wayyo Allah yau zan ga Umma na" ta fad'a tana rufe fuska da hannun ta tana tsallem murna.

Ganin farin ciki a kan fuskar ta sai ya saka shi ya saki fuska kad'an ya kafin ya tab'e baki ya juya ya fice daga d'akin, ware mayafin tayi ta yafa ta zura takalmin ta ta fito daga d'akin ta sakko k'asa ta zauna jira, bata jima ba ya sakko da jakar sa a hannun sa kunne sa mak'ale da waya yana magana a hankali.

Mugu da Wizzy suka fito suma suna jiran suji abinda Mai gidan nasu zai ce musu, sai da ya kammala wayar gabad'aya kafin yace, "Ku kaita gida na wuce Abuja" daga haka bai jira mai zasu ce ba kawai ya fita daga falon yana kallon agogon hannun sa.

Tunda suka fita daga falon suka nufi mota bakin ta yak'i rufuwa har suka shiga suka zauna, kunna motar Wizzy yayi wanda yake tsaron gate ya bud'e musu suka fita daga gidan.

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske tana ji kamar ta fita daga wuta ta shiga waje mai sanyi, ta lumshe ido maimakon taji tsanar Zaid na raguwa sai k'aruwa da tayi tana jin ta a ranta kamar a lokacin Allah ya dasa mata tsanar sa mai zafi.

_Tofa akwai rikici fa, Saura page d'aya mu gama free pages. Ki biya 200 a baki complete document hajiya. 09030398006_😂💃🏻💃🏻



Comments and share fisabinillah

*ƘASAITAR SO!*

©️ *Nana Haleema*


*11*


*Kano.*

A bakin layin su Ibteesam Wizzy yayi parking ya kalle ta ta mirror yace, "fita" ba musu ta bud'e ta fita da hanzari ta juyo ta kalle su tace, "duk bak'in halin ku ni Maryam nafi k'arfin ku wallahi, aikin banza duk abinda kuka yi min ka fad'awa Ogan naku ban yafe ba, ba kuma zan yafe na har a tashi duniya" tana gama fad'ar hakan ta harare su ta juya ta shiga cikin layin su.

Mugu ya kalli Wizzy sukayi dariya a tare Wizzy yace, "Ita dai yarinyar nan bakin ta baya shiru koda yake dan ta samu ya k'yale tane shiyasa take da bakin magana". "Wizzy Allah mai gida yana jin wani abu a kan yarinyar nan kawai taurin zuciyar sa ya hana shi ya fahimta". Kunna motar Wizzy kawai yayi suka bar unguwar dan dukkan su a gajiye suke.

Kamar an cillo ta haka mutanen Falon suka ga shigowar Ibteesam a gigice tana kalle-kalle, "Anty Ibteey" Jidda ta fad'a cikin ihu tana yo kanta da gudu, rungume ta tayi cikin farin ciki da kewar y'ar uwar ta ta d'ago da ita daga jikin ta tace, "Jidda ina Umma?". Umma da Jafar yaje ya sanar da ita ta fito kamar ana hankad'o ta tana so ta gasgata abinda Jafar ya fad'a, "Umma na" Ibteesam ta fad'a tana k'arasawa da d'an sauri ta fad'a jikin ta tana kuka. Itama Umman rungume ta tayi tana shafa bayan ta tana jin farin ciki mara misaltuwa a lokacin, "Umma na nayi kewar ku" ta fad'a tana sake k'ank'ame Umma tana cigaba da kuka.

"Ashe da gaske Ibteesam d'in ce" Mama ta fad'a da fara'a a fuskar ta tana kallan su, sakin Umma tayi taje wajan Mama ta rungume ta itama tana cigaba da kuka, "ki daina kuka mana Ibteesam tunda Allah ya kub'utar dake ai an gode Allah" Mama ta fad'a tana shafa bayan ta cikin rarrashi.

Cikin farin ciki aka dinga gaisawa da Ibteesam kafin a k'yale ta ta tafi d'aki dan ta huta.

Bayan sallar i'sha kasancewar Umma keda girki bayan ta kammala komai da yake k'ark'ashin ikon ta na ranar ta nufi falon Abba kamar ko da yaushe, yana zaune a falo yana kallan labarai ta shigo da sallama ya amsa yana kallan ta da murmushi a fuskar sa.

Har ta zauna bayan sallama bata sake cewa komai ganin hakan ya saka ya mayar da hankalin sa gare ta gabad'aya yace, "Na d'auka yau zan ga farin ciki kwance a fuskar ki amma sai nake k'okarin ganin akasin hakan, meya gusar da farin cikin dawowar y'ar mu akan kyakykyawar fuskar nan taki?". Gyara zama itama tayi kafin tace, "Allah ya dawo mana da y'ar mu lafiya ya maganar datse igiyoyin auren da suke kanta?". Murmushi yayi mai sauti kafin yace, "Haba Halisa kwata-kwata awan Ibteesam nawa da dawowa da zaki tayar da wannan maganar?." "Eh ai ya kamata ayi ta da wuri ne tun kafin lokaci ya k'ure, aikin gaggawa ma akayi in badan hakan ba da yanzu babu wani aure a kanta." "Halisa kenan, kin manta ya tsarin namu yake ne?". "Ban manta ba abinda ya saka nayi maganar kenan ma dan ni banga wata alama da a tare da Ibteesam da zata nuna yaron ya kusance ta." "Haka tace miki?" Ya tambaya yana kallan ta, "Haba dai yanzu har sai ta fad'a min zan fahinta,? Ai idon Ibteesam na kalla zan gane yanayin ta."

Dariya ta bawa Abba sai yayi murmushi kad'an yace, "naji, amma ki tambaye ta gobe in Allah ya kaimu nima kuma a goben zan dira a gidan su." "Amin, gwara dai a san nayi tun yanzu" tana fad'ar hakan ta mik'e ta shiga bedroom d'in da cikin falon.

Washe gari Ibteesam ta wuri ta tashi tayi wanka ta shirya ta tsaya a gaban mudubi tana gyara zaman bandage d'in da yake kanta ganin ya fara kwacewa, wuyan ta ta kalla nan tayi tozali da shatin dukan da tasha da belt yana nan da alama ya zamar mata tabon da zata je dashi lahira, "Allah ya shiga tsakani na dakai, na tsane ka bazan tab'a yafe maka ba har abada."

Shigowar Umma ya saka ta mayar da hankalin ta ga Umma tana murmushi tace, "Ina kwana Umma na". Itama murmushin tayi tace, "lafiya lau, ya jikin naki? dan naga alamun baki da lafiya." "Da sauk'i Umma daman ciwon baya da ciwon k'ugu ne yake damu na sai wannan ciwon na kaina". Gaban Umma ya fad'i jin ta ambaci ciwon k'ugu ya saka ta ja hannun ta suka zauna a bakin gado tace, "duka me ya jawo miki wannan ciwon?". "Mugun ta mana Umma, wallahi wanda ya sace ni mugu ne bashi da imani" ta fad'a tana fashewa da kuka ta kwanta a jikin Umma.

Zuwa lokacin tsoro ya cika zuciyar Umma tana shafa kanta tace, "me yake miki?". Cikin muryar kuka tace, "Duka Umma, babu damar nayi magana kad'an sai ya zane ni sannan kuma ya saka a bani magani, ki duba kaina Umma haka ya saka k'afa ya fyad'e ni na fad'i a kan tiles, ya buga ni da mota dan ina k'ok'arin na bar gidan, ya zane ni da belt dan nace ya dawo dani gida bayan ya shak'e min wuya yana niyar kashe ni in badan wani yazo ya cece ni ba da yanzu sai dai kuji labarin mutuwa ta,Allah Umma ni bazan k'yale shi ba sai na kai k'arar sa wajan y'an sanda sai alkhali ya bimin hakki na". Shiru Umma tayi tana sauraron kukan da Ibteesam take yi tana bubbuga bayan ta, "Bayan wannan bai miki komai ba Ibteesam? Ina nufin bai san ki y'a mace ba?".

Shiru tayi tana tuna gamon da suka sha yi a kan hakan in ba dan Allah ya kiyaye ta ba da yanzu ba zancen aike yi ba, jin shirun ta ya saka zuciyar Umma cikin tsananin fargaba da tashin hankali ta sake cewa, "ki bani amsa." "Kiyi hak'uri Umma nayi iya k'okari na wajan ganin hakan bai kasance ba" ta fad'a tana d'agowa daga jikin Umma kanta a sunkuye. "Sanar dani mana Ibteesam ya kusance ki?". D'aga mata kai Ibteesam tayi alamun eh, "Hasbunallahu wani'imal wakil" Umma ta furta tana dafe kai da hannun ta.

"Kiyi hak'uri Umma ba laifi na bane ya saka min k'arfi ne babu yadda na iya" ta k'arasa fad'a da kuka sosai tana fad'awa jikin Umman, goge hawayen dake idon ta Umma tayi tace, "Sau nawa ne?". Murya a shak'e Ibteesam tace, "Sau d'aya" bakin ta na rawa, runtse ido Umma tayi tana jin wani irin d'aci yana ratsa cikin zuciyar ta, "yaushe ne hakan ta kasance?" Umma ta tamabaya muryar ta na rawa sabida kukan da yake k'okarin kwace mata. "Shekaran jiya ne, ana e gobe zan tawo". Shiru Umma tayi tana jin wani d'an sanyi yana cikin zuciyar ta kafin tace, "Ya kike jin jikin naki,? Bakya jin zafi? In kina ji ki fad'a min na kaiki asibiti a duba ki". "Babu Umma sai kad'an" ta fad'a kanta a k'asa ta kasa d'agowa ta kalli Umma.

Ajiyar Zuciya Umma tayi ta d'ago ta daga jikin ta tana kallan fuskar ta, sunkuyar da kai Ibteesam tayi kafin Umman tace, "ki kwantar da hankalin ki kinji za'a bi miki hakkin ki insha Allah sai ya girbi abinda ya shuka, baban fata na bai wuce Allah yasa baki samu ciki ba dan lokacin zuwan period d'in ki ya kuwa Ibteey dan bana tunanin ya kai four day's nan gaba ko?". D'aga kai tayi alamun eh kawai dan ta kasa cewa komai, "Sai an bi miki hakkin ki insha Allahu, sai ya girbi abinda ya shuka haka sai ya zauna a prison matsayin sa na wanda yayi miki fyad'e, yanzu bari na saka Jidda ta kawo miki abinci" ta fad'a tana mik'ewa ba tare da ta kalli Ibteesam ba ta fice daga d'akin.

Da kallo tabi Umman tata tana jin wani irin so da k'aunar Umman tata yana sake bin jikin ta, ta kasance mace mai kula da yaranta ko yaya taga canji a tare da d'ayan su sai ta tambaye shi abinda yake faruwa ko kuma ita ta bincika da kanta, lokacin da ta fara period ma ita ta koya mata yadda zata saka pad da hatta wankan da zatayi da jinin ya d'auke ita tayi mata da kanta, ita take zaunar dasu ita da Jidda duk wani abu da iyaye mata ya kamata ta sanar da yaran ta mata take fad'a musu tun suna jin kunya har suka d'an rage suna tambayar ta duk abinda ya shige musu duhu, hakan ya saka tasan ranakun period d'in ta ita da Jidda tasan lokacin da suke farawa tasan lokacin da suke gamawa, Ajiyar Zuciya Ibteesam tayi tana tuno kamanin Zaid a idon ta, tsaki tayi tace, "na tsane ka wallahi bana san ganin ka ko kad'an, sai kyawun fuska babu kyaun zuciya."

Umma na fita daga d'akin ta saka Jidda ta kaiwa Ibteesam abinci ta koma b'angaren Abba, ya fito daga wanka yana shiryawa ta shiga d'akin da hanzari ko sallama bata yi ba, da sauri ya juyo yana kallan ta yace, "Halisa lafiya?" Meya faru kika shigo haka kamar an cillo ki?". Maimakon tayi magana sai kawai ta fashe da kuka ta zauna a gefen gadon tare da d'ora hannuyen ta a kan fuskar ta, da hanzari ya k'arasa inda take ya zauna ya sauke hannayen ta daga fuskar ta ya rik'e yace, "ki sanar dani abinda ya faru". "Ibteesam" abinda ta iya furtawa kenan tana cigaba da kuka.

"Me ya faru da ita? Ki daina kuka kiyi min bayani magana". "Yayi mata fyad'e Abban Jafar, abinda muke gudu ya faru" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da wani sabon kukan. Shiru Abba yayi shima hankalin sa a tashe jikin sa yayi sanyi sosai, matsowa yayi kusa da ita sosai kafin ya jawo ta ya rab'a ta da kafad'ar sa yace, "ita ta fad'a miki?". D'aga masa kai tayi kawai tana cigaba da kuka, "to amma ta sanar dake yaushe abun ya kasance? Ina nufin ranar yaushe kenan?". "Tace shekaran jiya ne" ta bashi amsa tana d'agowa daga jikin sa.
Shiru Abba yayi yana kallan ta cikin sanyin jiki yace, "To yanzu ya kike so ayi Halisa?".

"Kasan dai Yayan Dada da suke ciki d'aya shine alkhalin alkhalai na Kano, wajan zamu kai k'ara ya bi mata hakkin ta, na farko ya sace ta ta kwana shida a wajan sa ba tare da laifin komai ba, na biyu ya mata duka kai baka ga shatin belt a jikin ta ba bayan fasa mata kai d'in da yayi, jaka ce ita ko an fad'a masa bata da gata ne? Ko dan baban s Ambassador ne shiyasa yake ganin zaiyi abinda yaga dama,? Sannan yayi mata fyad'e na wulaqanci dan yana ganin kamar yafi k'arfin hukuma ne, to bai isa ba dole yayi zaman prison ko dan a nuna masa kud'i basu ne komai a rayuwa ba" ta k'arasa fad'a cikin fad'a hawaye na zuba a idon ta.

Shikam Abba zuba mata ido kawai yayi har ta kai k'arshen fad'an nata kafin yace, "Duka na amince da dalilin ki na farko na k'arshe ne ban amince dashi ba, kin manta da cewa a yanzu haka Ibteesam matar sace? Ko kin tab'a jin inda mace ta kai k'arar mijin ta tace yayi mata fyad'e Halisa?". "Nida kai mune kad'ai muka san mijin tane bayan mu babu wanda ya sani dan haka ka ajjiye zancen miji a gefe, ko da yake daman ai sai alkhali ya fara raba auren nasu kafin na zayyana masa duka tuhumar da muke masa."

"To shikenan, kar kiyi magana da kowa ko Dada ce ki dai sanar da ita ta dawo ni kuma yanzu zanje unguwa daga nan zanje masallacin Juma'a bayan an idar kuma akwai d'aurin auren da zan tsaya, ki bari na dawo sai muyi maganar kinji ko?". "Yauwa gwara kaje ka dawo a san abin yi gaskiya" ta fad'a tana goge fuskar ta da hannun ta, murmushi yayi ya mik'e ya cigaba da shiryawa ya fita ya barta yana murmushin da shi kad'ai yasan ma'anar sa.

*Abuja.*

Zaune yake a falo yana kallan tv, a zahiri kallan tv yake amma a bad'ini wani tunanin kawai yake yi daban wanda bai san dalilin sa ba, ajiyar zuciya yayi ya mik'e zaune sosai yana sake lumshe ido tare da bud'ewa, numfashi ya fesar tare da furta, "Meyasa nake ganin ta always?" Ya fad'a yana d'an dukan kansa yana jan dogon tsaki.

Ajiyar zuciya yayi yace, "A jini na ina jin na tsane ta why nake ganin ta a ido na koda yaushe?." A fusace kawai ya mik'e ya d'auki wayar sa da key d'in motar sa gabad'aya zaman Abuja ya ishe shi.

*Kano.*

Tun bayan fitar Umma Ibteesam take a zaune tana kallan waje d'aya, Shigowar Jidda ya katse mata tunani ta kalle ta tace, "Jiddalo na nayi kewar ki" ta fad'i da murmushi a fuskar ta.

"Yaya ta ga abinci" Ta fad'a da murmushi tana zama kusa da ita, "Bani labarin abinda ya faru bayan bana nan". "Lah kin san mene Yaya? Yawancin kullum sai Khalid yazo gidan nan a kan maganar ki". Zaro ido Jidda tayi cikin farin ciki tace, "dan Allah da gaske?". "Wallahi da gaske, baki ga yadda yake shiga damuwa kullum in yazo akace ba'a yo waya ba."

Murmushin farin ciki Ibteesam tayi tana jin k'aunar Khalid na sake ratsa ko jikin ta tace, "Allah sarki ashe yana sane dani." "Gaskiya yana sonki sosai Wallahi baki ga yadda ya rame ba". "Ina wayar ki?". "Tana d'akin Umma." "Kinga d'auko min na kira shi tawa ni ban san a inda take ba". Da to ta Mik'e ta fita ta shiga d'akin Umma ta d'auko wayar ta kawo mata.

Number wayar Khalid da ta haddace saka tare da kiran wayar, har ta katse ba'a d'auka ba ta sake kira ta sake katsewa ba'a d'auka ba sai ta ajjiye wayar a kusa da ita, ba'a fi mintina biyar ba taji k'arar wayar a kusa da ita tana dubawa taga Number sa ta d'auka tare da sallama, daga can b'angaren ya amsa tare da fad'in, "Wake magana?". Ibteesam ta lumshe ido jin yadda muryar sa ta daki kunnen ta har cikin zuciyar ta taji, "ka gano da kanka" ta fad'a murya can k'asa tana murmushi. "Ina aiki ne pls a fad'a min wake magana before na kashe wayar". "Ibteesam" ta fad'a a hankali.

Tana fad'ar hakan ya d'auki muryar ta, cikin rud'u ya mik'e tsaye yake furta, "Ibteesam da gaske kece? Yaushe kika dawo,? Kin san adadin damuwar da na shiga da bakya nan,?" Ya fad'a murya a sanyaye kamar zaiyi kuka. Jin yadda ya rud'e ya bata nishad'i ta gyara kwanciyar ta tace, "Jiya da daddare na dawo gida." "Alhamdulillah masha Allah, Ibteesam na shiga damuwa bana iya komai sai tunanin ki, ina son ki Ibteesam ina k'aunar ki wallahi, ban tabbatar da son da nake miki ba sai yanzu ji nake in na rasa ki zan iya rasa raina?."

Ji take kamar an mata albishir da kujerar makka sabida farin cikin da take ji yana bin ko wanne sassa na jikin ta, bata ce komai ba sai sautin murmushin ta da yaji a kunnen sa, "Kinga yanzu ina Katsina amma yanzu zan tawo gobe zan shigo na ganki insha Allah". "Toh Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya." "Amin my love, ki rik'e wayar a hannun ki zan kira ki". Daga haka suka kashe wayar sukayi sallama.

Washe gari.

Zaid yana zaune a cikin Tahir guest palace ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'a k'afa, matashin saurayj ne a zaune kusa dashi fari kyakykyawa wanda a shekaru bazai wuce sa'an Zaid d'in ba, "Zaid magana nake maka fa" Hameed ya fad'a yana kallan Zaid. "Hameed me zance maka ne? Bani da time d'in da zan zana shoe design bana cikin nutsuwa at now." Da mamaki yake kallan sa yace, "Me yake damun ka?". "I don't know why nake ganin ta a ido na, Hameed i hate her alot but yanzu koda yaushe indai na kulle ido na ita nake gani" ya fad'a yana lumshe idon sa.

Hameed zaiyi magana aka buga k'ofar d'akin, Zaid ya bada izinin shigowa Wizzy da Mugu suka shigo, "Sai yanzu?" Ya tambaya yana hararar su, "Sorry Mai gida traffic yayi yawa ne" suna fad'a tare da zama a kan kujera. Wizzy ya gyara zama yace, "Mai gida Gaye yana ta kuka yana cewa a baka hak'uri bazai sake aikata abinda yayi ba". Tab'e baki Zaid yayi yace, "Bana buk'atar sa yanzu ko ganin sa bana so." "Mai gida Hameed ka taya mu bashi hak'uri ya yafe masa" Mugu ya fad'a yana kallan Hameed da yake kallan su.

"Me yayi masa?" Hameed ya tambaya yana kallan su Wizzy, sosa kai Mugu yayi kafin yace, "Akwai wata yarinya da Mai gida ya saka aka d'auke ta to shine muka same shi yana k'okarin yiwa yarinyar fyad'e shine yayi fushi dashi over shi kuma ya shiga damuwa sosai dan bai d'auka yarinyar da mahimmaci a wajan a wajan sa har haka ba" Hameed ya kalli Zaid yace, "A'a daman ba kace min abinda zakayi mata kenan ba? To meye abin damuwa dan yayi maka aikin da kake so zakayi?" Hameed ya tambaya yana kallan sa, dan lokacin ds ya sanar dashi babu yadda bai masa akan ya k'yale ta ba yak'i ji.

"U know what? Ban san meyasa nake jin ta a jiki na ba, abinda na sani kawai na tsane ta amma ko yanzu ma ina so na ganta" ya k'arasa fad'a yana runtse idon sa, Hameed ya zaro ido tare da kallon su Wizzy suka danne dariyar su Hameed yace, "Do you love her?". A firgice ya bud'e idon sa ya kalli Hameed yace, "What? Amma kamar yanzu na fad'a muku cewa i hate her ko baku da kunne ne? Na tsane ta bana son ta ko kad'an, but ina so na ganta" ya k'arasa fad'a a fusace yana mik'ewa tsaye. "Wai tsaya wacce yake cewa ya tsana din itace dai wacce Gaye d'in yayi attempting d'in yiwa fyad'e?" Hameed ya tambaya yana kallan Wizzy, d'aga masa kai yayi alamun eh dan baya so yayi magana tasa

Please Login or Register in order to submit comment