Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take ji, jinin da a kan tiles ya tabbatar masa da kanta ya fashe sai ya girgiza kai ya nuna ta da yatsa yace, "Last warning" abinda yace kenan kawai ya fice ya barta a wajan a kwance cikin ciwo.

Kuka take so tayi amma ta kasa sabida yadda take jin azaba na ratsa ko wanne sassa na jikin ta, tabbas tsanar Zaid tafi kowai tasiri a zuciyar ta a halin yanzu ji take da tana da iko kashe shi tabbas zata iya kashe shi sabida yadda ta tsane shi tsana kuma mai muni.

Direct k'asa ya sauka ya zauna a kan kujerar da take kallan su Wizzy yana wuci, ganin hakan sai suka ja bakin su sukayi shiru suna jiran ya wuce, "yana wanne Station?" Ya tambaya bayan ya rank'wafo ya had'e hannayen sa guda biyu a waje d'aya. Sun fahimci wa yake nufi hakan ya saka suka kalli juna kafin Mugu yayi k'arfin halin cewa, "rashin lafiyar ka ta d'auke mana hankali har ya fita bamu lura dashi ba, kayi hak'uri". Cize bakin sa yana furzar da iska daga bakin sa kana yace, "Yana ina yanzu?". "Bamu sani ba muma." Shiru ya biyo baya babu wanda yayi magana sai da aka kwashe mintina k'alilan kafin yace, "a nemo dr yaje ya yiwa waccan yarinyar dressing" yana gama fad'ar hakan kawai ya mik'e ya fita daga falon suka bishi da kallo.

"Wizzy anya kuwa wannan yarinyar ba itace wacce ta taki sa'a ta sace zuciyar mai gida ba? Ka duba yadda ya kasa yi mata komai da kuma yadda ya shiga tashin hankali a d'azu?" Mugu ya tambaya yana y'ar dariya yana kallan Wizzy. Shima dariya yayi yace, "Anya kuwa Mugu? Kana jifa cewa yayi ayi mata dressing wata kila fasa mata baki yayi kasan yarinyar akwai tsinanniyar rashin kunya shi kuma akwai zuciya". "Yanzu dai muje mu nemo tun kafin yazo muma ya raba mana namu fad'an." Tare suka mik'e suka fito daga falon.

*Kano.*

Tunda ya yanke wayar Abba ya kalli Umma baki bud'e yace, "D'an Ambassador Abubakar fa, ita kuwa Ibteesam mai ya had'a ta da yaron da kowa yayi masa shaidar rashin tarbiyya?". Umma ta sauke numfashi tace, "Duka wannan yanzu bashi ba tashi zakayi kaje gidan mahaifin sa ka sanar dashi halin da ake ciki muji mai zaice in ba haka ba kuma a sanar da hukuma." "To yanzu samun ganin Ambassador Abubakar ma abu ne mai sauk'i? Wata k'ila ma baya k'asar gabad'aya." "Gwara kaje dai a duba a gani ko za'a dace tun kafin ya b'ata mana rayuwar y'ar mu, shi kad'ai ne zai iya dakatar dashi". Mik'ewa Abba yayi tare da fad'in, "To bara ayi la'asar sai na tambaya a waje a bani address d'in sa naje ko zan samu ganin nasa" yana gama fad'ar hakan ya fita jikin sa a sanyaye dan tunda yaji wanda ya d'auke ta jikin sa yayi sanyi sosai.

Kamar yadda Abba ya fad'a hakan ce ta kasance biyar saura kwata tayi masa a k'ofar gidan su Zaid, tun daga k'ofar gidan yake k'arewa gidan kallo ganin irin girma da tsaruwar sa yana dad'a jinjina kud'in da mahaifin Zaid ya mallaka.

K'arasawa yayi wajan mai gadin yayi masa sallama ya amsa kafin Abba yace, "Dan Allah Ambassador yana gari?". "Eh yana nan" ya bashi amsa a takaice, "ko zan iya ganin sa? wallahi abu ne na ujila." "Yanzu ya koma ciki gaskiya, kai da ganin sa sai magariba in ya fito masallaci in Allah yayi zaka ganshi d'in." Da jin haka Abba yayi masa sallama ya koma motar sa ya ja ya bar unguwar.

A bakin gate d'in gidan sa ya hango Khalid a tsaye da alama jiran dawowar sa yake yana kallan hanya, murmushi yayi yana jinjina son da Khalid yake yiwa Ibteesam, a kullum in bai zo ya tambaye shi ya ake ciki da maganar ba zai masa waya, yadda yake nuna kulawar sa akan lamarin Ibteesam yana burge shi sosai yana kuma jin dad'in hakan, Khalid da yake tsaye ya hango Abba ya kashe motar yana k'okarin fitowa daga mota ya k'araso da sauri ya bud'ewa Abba motar ya fito, D'urkusawa yayi har k'asa ya gaida Abba ya amsa cikin sakin fuska kafin su fara tafiya yana Abba Khalid yana bayan sa, tare suka shiga har cikin gidan Abba yayi masa masauki a falon sa suka zauna, "Abba har yanzu ba'a sami labarin ta ba?" Khalid ya tamabaya kan sa a k'asa yana jiran abinda Abban zaice, "An samu labarin ta Khalid." A firgice ya d'ago kai ya kalli Abban yace, "Tana ina Abba?". "Tana wajan wanda ya d'auke ta amma munyi waya da ita d'azu" Abba ya bashi amsa a sanyaye.

"Nawa suka nema kud'in fansa to?". D'an murmushi Abba yayi kafin yace, "Ba y'an garkuwa da mutane ne suka sace ta bafa." Da mamakin Khalid yace, "To waye?". "Zaid d'an gidan Ambassador Abubakar Ali". Zaro ido Khalid yayi gaban sa ya fad'i ya had'd'iye yawu yace, "Zaid Abba?." "Eh Zaid Khalid." Khalid ya gyara zama yace, "To Abba sai a sanar da y'an sanda ai su san matakin da zasu d'auka."

"Khalid kenan, kana tunanin akwai hukuma a Nigeria da zata iya wani abu akan Zaid? Zancen fad'awa hukuma bai tashi ba Khalid yanzu haka daga gidan su nake naje wajan mahaifin sa ban gan shi ba amma anjima kad'an zan koma." Girgiza kai Khalid yayi kafin yace, "ko nazo muje tare?". "A'a kayi zaman ka duk abinda mukayi zaka samu labari insha Allah" Da haka sukayi sallama Khalid ya fita daga jikin sa a sanyaye.

Gab da magariba Abba ya koma gidan su Zaid ya zauna a mota har akayi kiran sallah ya fito yayi alwala ya shiga masallacin da yake kusa da gidan, bayan an idar da Sallah Abba ya ga Daddy yana k'okarin fita daga masallacin ai da hanzari ya mik'e ya k'arasa inda yake tare da yi masa sallama, amsawa Daddy yayi ya baahi hannu suka gaisa kafin Abba yace, "In babu damuwa ina so mu zauna mu tattauna wata magana ne mai mahimmaci take tafe dani akan d'an wajan ka Zaid." Daddy jin ance Zaid ya saka ya kalli Abba ganin sa babban mutum mai kamala ya saka yace, "to bismillah mu shiga daga ciki" tare suka shiga gidan akayi masa masauki a falon bak'i Daddy ya kalli Abba yace, "Ina jinka me ke tafe dakai?".

"Wato Ambassador tun ranar juma'a aka nemi y'ar ta Ibteesam aka rasa munyi neman amma bamu samu labarin ta ba, d'azu muna zaune sai aka kira mu a waya..." nan Abba ya bashi labarin duk yadda sukayi da Zaid ya d'ora da cewa, "shiyasa nazo wajan ka dan Allah ka taimaka ka dakatar dashi, d'azu nazo ban same ka ba sai yanzu nayi sa'ar ganin ka, da zamu je mu sanar da hukuma amma sai naga gwara a fara sanar da kai" Tunda ya fara magana Daddy ya daskare a wajan jin wai jinin sane ya sace y'ar mutane har yana ik'irarin sai ta zama karuwar sa, numfashi ya sauke kafin yace, "Nagode sosai, naji dad'i da baku fara zuwa kun sanar da hukuma ba kuma same ni kai tsaye, wallahi ban san Zaid ya d'auki yarinyar ku har tsahon wannan kwanakin ba kuyi hak'uri dan Allah, hasalima ban san yana d'aukar yaran mutane ba" Daddy yana fad'a a sanyaye kamar mai shirin yin kuka.

"Babu wanda ya zarge ka wallahi babu wanda bai san halayyar ka ba mun san abinda zakayi da wanda baza kayi ba" Abba ya fad'a a tausashe, waya Daddy ya d'auko daga aljihun sa ya kira layin Zaid tare da sakawa a speaker, daga can b'angaren Zaid yace, "Dad". Daddy ya amsa da fad'in, "Zaid wacce yarinya ka d'auke tun ranar juma'a?". "Oh zuwa sukayi suka fad'a maka kenan?". Daddy yace, "Ina tambayar ka kana tambaya ta Zaid?". "Dad ban san ta ba ban san a inda take ba, tayi min rashin kunya ne na saka aka kawo min ita shikenan fa".

"Why Zaid! Kidnapper ka koma ban sani ba Zaid?". Daga can b'angaren ya dafe kai yace, "Dad nifa ban nemi kud'i a wajan su ba infact na musu waya ne akan su fad'awa yarinyar su tayi min abinda nake so in suna so su ganta ka tambaye su kaji iya abinda mukayi dasu kenan." "Ka k'yale yarinyar nan Zaid ta dawo gida kaji ko." "Dad har yanzu ban yi hukuncin da nace zanyi ba zan sake ta amma not know, kaina na ciwo Dad" daga haka ya yanke wayar Daddy ya bita da kallo yana jin kunyar Abba da yake zaune a kusa dashi kansa a sunkuye.

"Alhaji Yusuf kayi hak'uri bani da masaniya akan wannan sabuwar dabi'ar ta Zaid, ni na rasa abinda ma zance maka wallahi duk kunya ta kama ni". Abba yayi murmushi yana jinjina rashin girmama mutane irin na Zaid buda da yadda yake yiwa mahaifin sa magana yace, "Babu komai Ambassador yanzu dai mafita zamu nema tunda kaji abinda yace." "Bai mata komai ba tunda har ya fad'a k'arya bata cikin dabi'ar sa, ya zama dole mu dakatar dashi kafin faruwar hakan" Daddy ya fad'a yana kallan Abba.

"To ta wacce hanya kenan?". Gyara zama Daddy yayi yace, "Zaka bashi auren ta?". Da hanzari Abba ya d'ago ya kalli Daddy yace, "Aure kuma?ni da nazo neman mafita ya maganar aure zata shiga tsakani?". "Aura masa ita shine mafitar, nasan zakayi tunanin baza ka bawa y'ar ka yaro mara tarbiyya ba banga kuma laifin ka ba, abinda na duba shine da mu bar shi ya lalata mata rayuwa gwara mu d'aura musu auren sirri ba tare da ko wannen su ya sani ba, ni na haifi Zaid na kuma san halin sa kamar yunwar ciki na tunda yace bai mata hukunci ba bazai dawo da ita ba sai in shine yaga dama to kaga da mu bari a aikata b'arna muka kallo gwara a d'aura musu auren amma in ka amince." Numfashi Abba ya sauke yayi shiru yana tunanin mafita, shi dai gaskiya baya tunanin zai iya bawa Zaid auren Ibteesam duba da halayyar sa mara kyau in yayi mata haka bai zab'a mata miji na gari ba matsayin sa na uba a wajan ta, "Ba lallai bane sai anyi abinda nace amma a yanzu ita kad'ai ce mafita dan wallahi ko an kub'utar da ita a yanzu nan gaba sai ya sake d'auke ta, bawai ina goyan bayan sa bane sanin halayyar sa nayi shiyasa nake fad'a maka haka, in aka d'aura auren da zarar ya dawo da ita in wani abun ya faru a tsakanin su tabbas ba mace bace kamar kowa a wajan Zaid ba, Allah ya sani bawai ina kare shi bane amma Zaid baya neman mata k'yale shi da shan sigarin sa itama bayan ita baya shan komai indai har ya kusance ta babu shakka tana da matsayi babba a wajan sa, in kuma ya barta ta dawo bai mata komai ba to matsayin ta a wajan sa ya wuce matsayin farko sabida Zaid wani irin mutum ne da magana da jan ido baya hana shi yayi abinda yayi niya, ka yadda dani ina ji a jiki na auren nan zai jawo alkhairi ga ko wanne d'aya a cikin su."

Ajiyar zuciya Abba yayi kansa ya kulle ya rasa abinda zaice sai can ya nisa yace, "in kuma maganar auren ta fita yarinyar ta nuna bata so fa? Dan gaskiya tana da wanda take so yanzu ma dashi muka rabu nazo nan."
"Sai na saka ya sawwake mata" Daddy ya fad'a a sanyaye yana jingina da kujera. Nan ma shiru Abba yayi shi fa aurawa Zaid y'ar sane bazai iya ba dan sam bai kwanta masa a rai ba jin abinda yake yiwa mahaifin sa a waya ya sake tabbatar masa da bai san darajar na gaba dashi ba, "Auren sirri za'a yi daga ni sai kai sai kuma shaidun auren" Daddy ya katse masa tunani da fad'in haka.
Shiru ne ya ziryarci falon kowa yayi shiru a cikin su yana sak'a da warwara Abba ya katse shirun da fad'in, "Shikenan na amince, amma in ta dawo wani abu bai shiga tsakanin sa da ita ba zai sake ta in kuma wani abun ya shiga zai cigaba da zama da ita amma baza'a fad'a masa ba sai ya canja halayyar sa" Abba ya fad'a kai tsaye duk da yaji nauyin furta hakan a gaban mahaifin sa.

"Hakan yayi ma ai Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, yanzu in mun shiga sallar i'sha za'a d'aura auren". "To Allah ya nuna mana, shi sha'anin aure ba aabin wasa bane komai aa fad'e shi gaskiya kar a saka k'arya a ciki, tsakani da Allah bani na haifi Maryam ba hasali ma a gidan marayu muka d'auko ta tun tana da shekara biyu a duniya." Daddy yayi shiru jin abinda Abba yace kafin shima yace, "wannan bazai zama matsala ba tunda dai ku kuka bata tarbiyya ai zance ya k'are. "
Jin kiran sallah ya saka suka mik'e suka tafi masallaci, bayan an idar da sallah mutane sun watse ya rage daga liman sai mutane biyar sai kuma Abba da Daddy aka d'aura auren Ibteesam da Zaid akan sadaki naira dubu saba'in.

Bayan sun fito ne Abba ya saka sadakin nata aljihu suka yi muyasar number tsakanin su Abba ya hau motar sa ya tafi zuciyar sa cike da waswasin abinda ya aikata.

Nufar cikin gida Daddy yayi jikin sa a sanyaye dan gabad'aya wani iri yake jin sa, da Yaya babba suka had'u a k'ofar gida ya fito daga gidan da alama wajan sa yaje baya nan, "A'a Yaya Babba sannu da zuwa." "Ba sannun ka nake so ba Abubakar zuwa nayi na shaida maka gobe da azahar zan yiwa Zaid wakilci za'a bashi auren Eman, ba kuma umarni nake bawar wa ba shawara ba, ko yana so ko baya so wannan aure kamar an d'aura shine an gama".

Daddy ya bud'e baki zaiyi magana Yaya Babba ya barshi a wajan a tsaye baki bud'e yana kallan ikon Allah.

*Kaduna.*

Tunda likita yazo ya gyara mata inda ya fashe a kan yayi mata allura da magani take baccin wahala, lokacin da Zaid ya kashe wayar ya kalli su Wizzy da suke zaune a kusa dashi yace, "wai k'ara ta suka kai wajan Daddy" ya fad'a yana tab'e baki.

"Mai gida nima a gani na tunda ka yiwa yarinyar nan hukunci dai-dai da ita gwara a sallame ta kodan mahaifiyar ta da take cikin damuwa mai tsanani na rashin ta" Wizyy ya fad'a yana kallan Zaid da yake kad'a k'afa.

Bai d'ago daga danna wayar ba balle su suka ran zai amsa, Mugu ne ya sake cewa, "Gaskiya ne maganar Wizzy mai gida, a k'yale ta kawai ta tafi ko iya yau taji jiki ta banbance tsakanin aya da tsakuwa nima ina bayan maganar Wizzy in zai yu kawai a k'yale ta." Sai a lokacin ya d'ago ya kalle su ya yatsine fuska yace, "ina so na sallame ta nima daman ban d'auko ta dan na mata komai ba rashin jin ta ya sake saka ni b'acin rai, but haka kawai nake ji bana so ta tafi ina so ta zauna ko kullum zamu dinga fad'a" ya fad'a ba tare da ya d'ago ba yana cigaba da danna wayar sa. "Mai gida ko dai kana son tane?" Wizzy ya fad'a yana kallan sa da murmushi a fuskar sa.

A fusace ya d'ago kai ya watsawa Wizzy wani banzzn kallo da ya saka shi ya tsorata yana dana sanin abinda ya furta, "Na tsane ta bana sonta bana kuma kaunar ta, abinda na sani kawai ina jin dad'i in na ganta amma ba santa nake ba kaji?" Ya fad'a yana nuna Wizzy da hannu tare da zaro masa ido.

"I'm sorry Mai gida baza'a sake ba" Wizyy ya fad'i yana d'an sosa kai". Daga haka ya mik'e ya shiga d'aki yana cigaba da danna wayar sa.

_Tofa ga Ibteesam da auren Zaid a kanta, ga kuma na Eman ana niya duka gogan naku bai sani ba Chakwakiya d'in kenan_ 🤣🤣


_Akwai complete din sa ki biya 200 a baki domin free pages gab suke da shekewa._💃🏼😂 09030398006.


Comments and share fisabinillah.

*ƘASAITAR SO!*

©️ *Nana Haleema*

*10*



Tunda Abba ya bar gidan su Zaid yake tuk'i cikin tunani har ya k'arasa gida, jiki a sanyaye ya shiga babban falon gidan kamar koda yaushe yaran duka suna nan, "Sannu da zuwa Abba" dukkan su suka fad'a a tare, "Yauwa sannun ku, ina Umman ku?". "Tana d'aki" Jafar ya bada amsa yana nuna b'angaren ta da hannun sa, baice komai ba ya nufi b'angaren nata.

Da sallama ya shiga ta amsa tana d'agowa ta kalle shi, "Sannu da zuwa" ta furta a hankali tana karantar yanayin sa, "yauwa" ya fad'a tare da zama a kan kujerar da take zaune. "Ya goyi bayan d'an ko?" D'agowa yayi ya kalle ta yace, "Meyasa kika ce haka?". "Sabida yanayin ka ya gwwda haka". "A'a ko d'aya hasalima hak'uri ya dinga kamar ba babban mutum ba." Gyara zama Umma tayi kana tace, "To lafiya na ganka a sanyaye haka?". Bai magana ba sai saka hannu da yayi a aljihu ya d'auko kud'i ya d'ora mata a akan cinya ya d'ago ya kalle ta, kallan sa tayi tare da kallan kud'in tace, "cin hanci ya baka ko me?".

"Ba cin hanci bane ba Halisa" ya fad'a a sanyaye yana kallan gefen sa, "to meye?". "Sadakin y'ar ki ne Maryam" Abba ya fad'a yana kallan fuskar ta da mamaki yake kwance a kai, "Sadakin Ibteesam kuma,? Na auren wa?" Umma take tambaya da mamaki tana kallan Abba. "Na auran d'an wajan Ambassador wanda ya sace ta, a tak'aice dai Zaid wanda ya sace Ibteesam shi aka aura mata bayan sallar i'sha." Cikin tashin hankali da mamaki had'i da tsoro ta mik'e tsaye tace, "what! Aure? Kuma da d'an Ambassador wanda ya sace ta,? To ta yaya hakan ya kasance?". "Shiiii Halisa ki daina d'aga murya mana, kwantar da hankalin ki zauna nayi miki bayani yadda zaki fahimta".

Komawa tayi ta zauna ta kalle shi alamun ina jin ka, nan Abba ya kwashe duk yadda sukayi da Daddy ya fad'a mata ya d'ora da cewa, "Halisa na amince da hakan ne sabida a gani na shine mafitar matsalar da muke ciki, d'aura auren kamar shine mafi alkhairi akan abinda yake so ya aikata ga Ibteesam shiyasa kawai na amince."

Tunda ya fara magana Umma ta zuba masa ido tana yi masa kallan mamaki, "Amma dan Allah meyasa baka nemi shawara ta ba kafin ka yanke wannan d'anyan hukuncin,? Bank'i maganar ka ba tabbas mafita ce aura masa ita da su sab'awa Allah gwara hakan amma da wanne ido duniya zamu kalli ita Ibteesam d'in,? Muce mata mun aura mata yaro mara tarbiyya mai sace yaran mutane da lalata musu rayuwa? Anya mun mata adalci matsayin mu na iyayen ta kuwa,? Ka sani na sani wannan yaron ba yaro na gari bane ba duk d'an da zai sace d'iya mace yana kuma ik'irarin sai ya mayar da ita karuwa shi ka d'auka ka bawa y'ar mu,? Nida kai bamu san adadin yara matan da yayiwa haka ba in tamu ta kub'uta ta hanyar aura masa ita da kayi yanzu sauran fa Alhaji,? Duniya zata ce dan ba mu muka tsuguna muka haife ta bane shiyasa muka bayar da ita ga wanda bai daice ba, ko tantama banayi abinda mutanen gari zasu fad'a a kan mu kenan kuma basu da laifi, Meyasa ka amince da wannan auren?" Zuwa lokacin hawaye sun fara zuba daga idon ta, jikin sane ya sake yin sanyi yana juya maganar Umma a kwakwalwar sa, shima ya san zancen ta haka yake duk abinda ta fad'a batayi k'arya sai dai hausawa sunce aikin gama ya gama.

"Halisa rashin mafita ne na ya saka na amince da hakan bawai nima dan ina so ba, yadda yake cewa sai ya lalata mata rayuwa in yayi hakan ta samu ciki fa Halisa,? Bawai banyi imanin da k'addara bane koda hakan ta kasance ba a'a sai dan gwara ace da auren sa a kanta a lokacin da ace babu, ki fahimce ni wallahi banyi da niyar cutar da rayuwar Ibteesam ba nayi ne ni sabida inganta rayuwar ta, yadda zan aurar da Asiya haka zan aurar da Ibteesam duka y'ay'a nane Halisa kuma kome mutanen duniya zasu ce a game damu ya dai fi ace duniya tana zagin mu akan sabida ba y'ar mu bace mun bari tayi ciki ko kuma mun bari an lalata mata rayuwar ta." Ajiyar zuciya Umma tayi ta goge hawayen idon ta tace, "Haka ne, amma ka duba yaron da ka bata, bashi da inganci ko kad'an bai kama da miji na gari da ko wanne uba yake zab'awa y'ar sa ba, meyasa uban sa bai tsawatar masa ya dawo mana daa y'ar mu ba sai aure shine za'a ce mafita?."

"Halisa auren nan na rashin mafita ne shima mahaifin nasa ya sani, auren sirri ne Halisa dan Allah ki hak'a rami ki bunne maganar nan yadda na fad'e ta nida ke bana so kowa yaji maganar nan koda ita Ibteesam d'in ce mu jira zuwa dawowar ta mu gani." "Shikenan naji, muyi yaya da yaron nan Khalid da yake zarya koda yaushe akan maganar Ibteesam d'in? Ka sani tana son sa shima kuma yana sonta ya zamuyi dasu?". "Shiyasa nace miki auren sirri ne ko ita bana so ta sani da zarar ta dawo zan koma wajan mahaifin ta a warware auren ba tare da kowa ya san da hakan ba." "Shikenan Allah ya kyauta". Ya amsa da amin ya mik'e ya fita.

Washe gari.

Juya PT stick d'in take a hannun ta tana zaga d'akin, bud'e k'ofar da akayi aka shigo ya tsayar da ita daga zaga d'akin da take ta kalli wanda ya shigo, "Amina lafiya kike kuwa?" Daddy ya tamabaya yana yi mata kallan tuhuma. Batayi magana ba sai mik'a masa PT d'in da tayi tare da kawar da kai, karb'a yayi yana kallan fuskar ta tare da juya PT d'in yace, "meye wannan d'in?". "Pregnant test ne ya nuna min positive kuma" ta fad'a a d'an sanyaye tana kallan sa.
Baki Daddy ya bud'e ya kalli abinda ya bashi ya d'ago ya kalle ta yace, "Wai kina nufin kina da ciki kenan?" Ya tamabaya a rud'e yana washe baki.

D'aga masa kai alamun eh, raba ta da k'asa yayi ya fara juyi da ita a cikin d'akin yana dariyar farin ciki, sai da ya gaji da kansa kana ya dire ta ya kalli gabad yayi sujadda ya godewa Allah ya mik'e ya ja hannun ta suka zauna a kan gado yace, "Alhamdulillah, Amina Allah yayi miki albarka ki fad'a min abinda kike so ko meye yanzu na baki shi" ya fad'a da murmushin farin cikin shinfid'e a fuskar sa. Itama murmushi tayi tana jin farin ciki a wani b'angaren na zuciyar ta wani b'angaren kuma tana jin fargaba da tashin hankali yana k'okarin rinjayar farin cikin nata, "abinda nake so guda d'aya ne kuma gashi kayi, buri na na saka ka a cikin farin ciki gashi kuma nayi" ta k'arasa fad'a da murmushi a fuskar ta. "Sai kin fad'i abinda kike so Amina domin ki bani abinda na jima ina nema, shekara sama da talatin kenan rabon da na samu abinda nake so amma gashi ta sanadin ki yau Allah ya bani, ki fad'i ko meye kike so zan baki Amina".

"Ka zauna dani a ko wanne irin da zan riski kaina ko yanzu konan gaba, ka yafe min duk wani laifi da zan maka ko nayi maka wanda na sani da wanda ban sani ba, wannan shine kad'ai abinda nake so kuma nake buk'ata a waja ka" ta k'arasa fad'a kamar zatayi kuka.

"Amina wannan kamar anyi a gama ne nida ke mutu ka raba insha Allah, amma fa dole nayi miki kyautar da in kika tuna zaki ji dad'i kema kamar yadda nima nake cikin farin ciki a yau". "Sannan dan Allah alfarma d'aya" ta fad'a a sanyaye tana kallan sa. "Ina jinki fad'i ko meye kike so." "Bana so kowa yasan da wannan cikin dan Allah in aka cire Zaid shima dan yana da kyau a sanar dashi

Please Login or Register in order to submit comment