Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auka ya kara a kunne tare da fad'in, "Ya akayi?". "Mai gida batu ne akan Ibteesam." "Waye haka?". "Yarinyar nan da take Kaduna'". "Oh wani abun ne?". "Mai gida Gaye yana can kasan kuma halin sa ganin baka nan tsaf zai iya farwa yarinyar nan dan ba imani gare shi ba." Tab'e baki yayi ya d'an ja tsaki yace, "so what? Ba sai ya nuna mata halin y'an iska ba." "Amma mai gida kai da kanka kace zakayi mata hukunci ai bai kamata ace wani daban bane zai aikata." "Okay Wizzy zan san abinda za'ayi yanzu na gaji da yawa" yana gama fad'ar hakan kawai ya kashe wayar ya ajjiye akan gadon yana kulle idon sa.

Haka ya k'araci wunin sa a sama gabad'aya ya manta da wani batun Ibteesam sabgar sa kawai yake yi.

Washe gari ta kama ranar talata da wuri ya sakko haka kawai yaji yana san sakkowa da wuri, kitchen ya shiga dan sha'awar cin noodles yake yi, baya jiran azo ayi masa girki indai yaso ci da kansa zai dafa, d'ora ruwa a tukunya yayi ya fara dafa indomie cikin k'warewa, magana yake jiyowa sama-sama daga cikin store hakan ya saka ya tsaya da aikin cak ya k'arasa bakin k'ofar store din ya tsaya yana jiyo abinda ake fad'a.

"Na Fad'a muku yaron nan baya cin abinci na sam wallahi na rasa yadda zan masa amma zan saka mahaifin sa ya bashi lemon dan naga yana san zob'o sau da dama ina gani yana siyowa, in na bawa uban nace ya bashi zai bashi wata k'ila yasha" shiru tayi alamun tana sauraron me ake ce mata kafin ta cigaba da fad'in, "Mu gama da yaron tukkuna ta uban mai sauk'i ce kawar dashi daga duniya bazai yi mana wahala ba kamar yadda aka kawar da matar sa shima haka za'a kawar dashi" dariya tayi sosai kafin tace, "ahh to dole ai sai mun dage mu gama dasu suma su bi bayan Maryam d'in" ta fad'a tana murd'a handle d'in k'ofar ta fito tana cigaba da dariya.

Abinda ta gani ya kusa saka ta sakin fitsari a wando jikin ta ya soma rawa tana zare ido irin na marasa gaskiya, ta bud'e baki zatayi magana kawai taji saukar mari a kumatun ta, sai da ta tafi hutun wucin gadi sabida yadda marin ya ratsa ta kafin ta dawo hayyacin ta ta d'ago dak'yar ta kalle shi ya kuma marin ta a d'aya b'angaren.

Ihu tayi mai k'arfi tana tsalle a wajan kamar yarinya k'arama ta fashe da kukan azaba, noodles d'in da take kan wuta ya d'auki tunkuyar a fusace ya watso mata akayi sa'a tayi saurin sunkuyawa noodles d'in ta zube a k'asa tunkuyar ta daki k'ofar store d'in ta fad'i k'asa a dai-dai lokacin da Daddy ya shigo kitchen d'in, kafin Zaid yayi wata magana Daddy ya d'auke shi da maruka guda biyu zafafa kafin ya dawo dai-dai yace, "Amina a matsayi na na mijin ki ina baki umarnin ki tashi ki mari Zaid". Jikin ta har b'ari yake sabida ciwon kan da ya saukar mata lokaci d'aya, "ba magana nake miki ba?". Daddy ya fad'a a fusace yana kallan ta, aikam bata raga ba tana mik'ewa ta d'auke Zaid da mari ta koma bayan Daddy ta tsaya dan taga alama tsaf zai iya naushin ta.

"Zaid tsuguna ka bata hak'uri.". D'ago jar fuskar sa yayi ya kalle shi da jajayen idon sa bakin sa na rawa alamun yana so yayi magana, "Ba maganar ka nake so ba Zaid in dai ni na haife ka ka d'urkusa ka bata hak'uri".

Jikin sa na rawa ya d'an rage tsaho kad'an yana wani irin numfashi kamar numfashi k'arshe yace, "Sorry" abinda ya iya furtawa kenan ya mik'e a fusace ya daki glass din jikin oven ya tarwatse a kitchen d'in ya yanke shi a hannu, k'ofar baya ta kitchen d'in kawai ya bud'e ya fita, Saman sa ya haura ya d'auki wayar sa da key d'in motar sa ya sakko ya shiga mota ya jata da k'arfi ji kake k'iiiiiiiiii ya fice daga gidan da gudun gaske.

_Akwai complete nasa akan naira 200 kacal👌09030398006._


Comments Share fisabinillah 🙏❤️🥰

*ƘASAITAR SO!*


©️ *Nana Haleema*

*8*

A fusace Daddy ya juya ya bar kitchen d'in cikin fushi da takaici, duk da irin tashin hankali da tsoro da Amina take ciki sai da tayi wani juyin farin ciki har taso zamewa da noodles da Zaid ya watso mata, "Harira!" Ta fad'a cikin d'aga murya tana kallan k'ofar kitchen d'in da zata kaika harabar gidan, da gudu wacce aka kira da Harira ta shigo tana fad'in, "Gani Hajiya." "Zo ki gyara wajan nan" tana fad'ar haka ta fita da sauri ta nufi d'akin Daddy da saurin ta.

A zaune ta ganshi a falon sa ya d'aga kai sama yana kallan ginin pop d'in dake falon, da sallama ta shigo ta tako a hankali zuwa inda yake ta zauna a kusa dashi ta rik'e hannun sa guda d'aya da duka hannayen ta tace, "an kammala breakfast". Shiru yayi bai amsa ba bai kuma kalle ta ba cikin sanyin murya tace, "Dan Allah kayi hak'uri ka cire komai a ranka addu'a zamu cigaba da yiwa Zaid sai kaga an wayi gari ya shiryu ya koma kamar bashi ba."

"Yaushe kenan Amina? Gobe? Jibi? Ko kuma gata,? Allah ya sani lamarin Zaid ya fara bani tsoro wallahi, marin kifa yayi mari fa, tunda har ya iya d'aga hannu ya mare ki nima wata rana zai iya duka na, ni na fara tantama anya wannan ciwon kan da yake damun Zaid bai yi affecting d'in brain din sa ba kuwa Amina?" Daddy ya fad'a yana fuskantar ta jikin sa a sanyaye haka ma muryar sa.

"Haba Daddyn Zaid da kanka kake fad'ar wannan kalma ta tab'in hankali ga Zaid? Wannan sam bai kamata a ji maganar nan daga bakin ka ba, kai in kace haka to su kuma mak'iyan ka suce mene?."

Ajiyar Zuciya Daddy yayi yace, "Amina Zaid shine kad'ai d'an dana mallaka a duniya bayan shi bani da wani, meyasa bazai kalle ki a matsayin uwa ba tund shi tashi bata duniya,? Ranar nan ya watsa miki miya a jiki in badan Allah ya tak'aita ba da ya k'ona miki jikin ki, yau ya mare ki ya kuma so ya k'ona ki d'in again akan me duka yake aikata wannan banzayen halayyar tasa,? Amina shi kad'ai ne mai zuciya ne a duniya? Ko shi kad'ai ne me saurin fushi,? Dukkanin mu muna dasu wata k'ila namu yafi nasa amma banbancin mu dashi muna sarrafa namu amma shi baya iya sarrafa fushin sa da b'acin ransa a kan kowa da komai, anya rayuwa zata yu a haka? Tunda har ya iya aikata miki haka a matsayin ki na matata uwa a gare shi nima zai iya yi min wata rana, ki duba abinda ya yiwa su Yaya babba kwanaki, a gani na ko bai kalle su da matsayin su na iyayen sa ba ai ya kamata ya kalle su matsayin wanda suka haifi kamar sa, Yana da buk'atar ganin Psychiatrist dan gaskiya ban aminta da lafiyar sa ba yanzu."

Shiru Amina tayi har sai da ya kai k'arshe maganar sa kafin tace, "Akwai halitta wacce Allah yaka yiwa bawan sa ba sai tab'in hankali ko matsalar k'wakwalwa ba, Zaid yana daga cikin wanda Allah ya halitta a haka, ka daina zancen tab'in hankali ko rashin lafiyar k'wakwalwa a gare shi sabida kai mahaifin sane bakin ka yana da kaifin gaske a kansa yanzu sai hasashen ka ya zama gaskiya a kansa kuma azo hankali ya tashi ana da an sani, babu abinda yake damun Zaid sai zallar zuciya da fushi da yake dasu kuma ta bakin ka indai baya sarrafa su tabbas wata rana zasu kai shi su baro shi, kuma duka wannan abun nasa dan bashi da wanda zai dinga d'ebe masa kewa ne kullum shi kad'ai yake rayuwa dole fushin sa ya dinga gaba, ka dinga taya shi da addu'a Allah ya sassauta masa zafin zuciyar tasa dan addu'a ita kad'ai ce mafita a gare shi "

"Ance mace na canja mutum anya akwai macen da zata iya canja Zaid kuwa?" Daddy ya fad'a cikin tunani da al'ajabi. Dariya Amina tayi tace, "Tsaf kuwa, indai yana sonta wallahi babu abinda bazai yi ba, ina tabbatar maka mamaki ma zaka fara yi anya kuwa shine." D'an murmushi Daddy yayi yace, "Ai kuwa zan fara addu'a daga yau Allah ya had'a shi da wacce lokaci d'aya zaiji yana son ta kodan ta koya masa hankali". Kawar da zancen tayi ba tare da tace amin ba tace, "Yanzu dai breakfast d'in ka yana jiran ka kar yayi sanyi." "To shikenan, yanzu zan sakko" ya fad'a yana mik'ewa ya shiga bedroom d'in sa.

Da kallo ta bishi tana zuba masa harara har ya wuce tayi wani irin munafukin murmushin samun nasara tana aiyana abubuwa da dama a zuciyar ta.

*Kaduna.*

Kamar kullum tana zaune a d'aki tayi tagumi tana tunani kala-kala, tsaki tayi dan har ga Allah zaman kad'aici nan ya ishe ta wacce take d'an taya ta hira baje gida bata nan shiyasa zaman gabad'aya ya ishe ta, ajiyar zuciya tayi fuskar Khalid yana yi mata yawo a idon ta zuciyar ta cike take da kewar sa da san ganin sa, bud'e k'ofar da akayi ya saka ta d'ago kai tana kallan wanda ya shigo, gaban tane yayi mummunar fad'uwa ganin wanda ya shigo yana jifan ta da wani irin kallo, gyara zama tayi kafin ta kalle shi tace, "Lafiya?". Kulle k'ofar yayi kafin ya shigo cikin d'akin yace, "Lafiyar ce ta kawo haka y'an mata, zuwa nayi na taimake ki na kub'utar dake daga hannun wannan mai gidan namu amma fa in kin amince" ya fad'a k'asa-k'asa yana jifan ta da wani irin murmushi irin na y'an bariki.

Jin za'a kub'utar da ita ya saka tayi murmushi tace, "Na amince indai zaka fitar dani daga gidan nan ni kuma zan yi ko meye." Murmushi yayi ya zauna akan bedside yace, "Yauwa y'ar gari, so nake ki bani had'in kai mu more wannan lokacin ni kuma na miki alqawari zaki bar gidan nan a yau" ya fad'a yana lashe baki yana sake zuba mata idanu. "Mtsww wato ku dukkanin ku halayyar duka d'aya ce da kai da Ogan naku ko? To wallahi nafi k'arfin ku wanda ya fiku ma nafi k'arfin sa balle kuma ku, dallah malam tashi ka bani waje ban amince da buk'atar ka ba zan cigaba da rok'on Allah ya bani ikon fita daga nan lafiya ba tare da taimakon kowa a cikin ku ba" ta k'arasa fad'a cikin fad'a da rashin kunya.

D'aure fuska yayi ya mik'e tsaye ya fara b'alle ma6allan rigar yana kallan ta yace, "Daman ai zab'i biyu gare ki in kin amince na huta dake sannan na fitar dake, in baki yadda ba kuma na huta dake kuma ki cigaba da zama a nan d'in, kin san Allah ina ganin abinci bazan k'i ci ba" ya k'arasa fad'a yana zame rigar jikin sa. Yunk'urawa tayi zata mik'e ya tankad'a ta ta fad'a kan gadon a kwance, ta yunk'ura zata mik'e zaune ya fad'a kanta ya sakar mata nauyin sa ta kwalla k'ara mai k'arfin gaske.

A dai-dai Wizzy yayi parking a harabar gidan, gaban Zaid ne ya fad'i jin k'arar da yayi har tsakiyar kansa kasancewar tagar d'akin a harabar gidan take kuma a bud'e hakan ya saka aka jiyo k'arar rad'au, bai san dalilin fad'uwar gaban tasa ba hakan ya saka ya kalli Wizzy da shima shi yake kallo, kafin Wizzy yace wani abu Zaid ya fita daga motar da saurin gaske ya shiga cikin gidan, bai tsaya kulle motar ba shima ya bita ya bi bayan sa a guje suka hau saman.

Dambe sosai ake tsakanin Gaye da Ibteesam tana kuka tana ihu da k'okarin kwatar kanta zuwa lokacin ya zame kayan jikin sa daga shi sai boxer, k'okarin dira take daga kan gadon ya jawo rigar ta ta baya ta yage ta sake fad'awa kan gadon, "ke har kin isa ki hana ni abinda zanyi? Baki isa ba wallahi dole na samu abinda nake so a tare dake ko bakya so" ya fad'a yana k'okarin zame boxer d'in jikin sa. Bud'e k'ofar da akayi ya saka shi tsayawa cak tare da juyawa yana kallan wanda suka shigo gaban sa yana fad'uwa tsoro da fargaba suka taru suka masa yawa, a guje ta dire daga kan gadon tayi bayan Zaid tare da k'ank'ame shi tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi.

Runtse ido yayi jin yadda ta kwanta a baya ta ziro da hannayen ta ta rik'e cikin sa tana kuka, wani irin abu yaji yana masa yawo tun daga kansa har yatsun k'afar sa, wani irin d'umi jikin sa ya d'auka lokaci d'aya tsigar jikin sa na tashi kasala ta saukar masa a lokaci d'aya, hannu ya saka ya fincike ta daga jikin sa ya tura ta gefe ya mayar da kallan sa ga Gaye da yake rawar jiki gumi yana tsatstsafo masa daga jikin sa, "Gayee meye haka,? Kai a ko ina sai ka nuna halin ka na y'an bunshuru?" Wizzy ya fad'a yana kallan sa cikin b'acin rai.

Kar kar kar haka jikin sa yake rawa sabida bala'in tsoro ganin mai gidan nasa ya zuba masa ido kawai baice komai ba, Mugu da suke zaune yare da Gaye a gidan ya kalli Gaye cike da takaici yace, "Haba Gaye wannan wacce irin dabi'a ce? A gidan mai gida kake k'okarin aikata haka? Daga fita ta na siyo kati shine ka samu wannan damar?". Juyawa Zaid yayi kawai ya fice daga d'akin da saurin sa, bai jima ba ya dawo hannun sa d'auke da sabuwar wuk'a fil sai k'yalli take, "Wizzy ku danne min shi" ya fad'a muryar sa na wani irin shaking sabida yadda yake ransa a b'ace.

"Na shiga uku, dan Allah dan Annabi Mai gida kayi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne ya jani ga aikata hakan, ka yafe min dan Allah" ya fad'a yana d'urkushewa tare had'e hannayen sa waje d'aya alamun rok'o, Wizzy da suka fahimci abinda mai gidan zai aikata duk sai suka tsorata Wizzy yayi saurin amsar wuk'ar hannun sa yace, "Ayi hak'uri mai gida a sassauta masa yaci darajar Maman mu". Fincike wuk'ar yayi daga hannun Wizzy ya nufi inda Gaye yake yana tattare hannun rigar sa, "dan Allah kayi hak'uri mai gida na tuba bazan sake ba" ya fad'a yana ja da baya Zaid yana sake tunkarar sa.

Da k'arfin gaske ya naushe shi a baki haqorin sa d'aya yayi tsalle ya fad'i a gefe jini ya fara fita daga bakin sa.

"Mai gida kayi hak'uri dan Allah ka sassauta masa, yayi kuskure babba mun sani amma dan Allah kayi hak'uri" Mugu ya fad'a yana kallan Mai gidan nasu cikin tsoro da kuma tausayin Gaye, da wani ne ba Gaye ba tabbas da kansu zasu rik'ewa Mai gida shi yayi abinda yake niya amma Gaye ana tare ko babu komai tun kafin had'uwar su da Mai gida a waje d'aya suke.

Ihun da Ibteesam tayi tare da kulle idon ta shine ya dakatar dashi ga k'okarin farka gajeren wandon jikin Gaye, sakin wuk'ar hannun sa yayi ya dafe kai yana runtse ido, "ke...." bai k'arasa abinda yake so yace ba ya fad'i a wajan a sume.

A hankali a tashe Wizzy suka yi kansa suna jijjiga shi amma babu alamun numfashi a tare dashi, "Wizzy ina jin ciwon sane fa ya tashi" Mugu ya fad'a hankali a tashe yana kallan Zaid da yake kwance a k'asa, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, kinga d'an bamu d'ankwalin kanki" Wizzy ya fad'a yana kallan Ibteesam da take kallan su tana mamakin wanne irin ciwo ne wannan. "D'ankwali na kuma?". "Kinga babu lokaci dallah malama ki bamu" ya fad'a a tsawace yana zare mata ido, cirewa tayi ta mik'a masa ya karb'a da hanzari ya kama kan Zaid ya d'aure da k'arfin gaske, "Yanzu ina zamu samo likita a garin nan?" Mugu ya tamabaya yana kallan Wizzy.

"Is better mu kaishi asibiti kaga babu likitan da muka sani a nan Kaduna balle mu kira shi yazo." "Ba magana ba Wizzy mu fara bashi taimakon gaggawa" ya fad'a yana ficewa daga d'akin ya nufi dakin ya Zaid d'in dan nema masa magani.

Wizzy ya kalli Gaye da yake rakub'e a jikin bango yana kuka yayi tsaki yace, "Dallah malam tashi ka bamu waje tun kafin ya farfad'o ya ganka a nan ranka ya b'aci". Ai da gudu ya kwashi kayan sa ya fice yana waiwayen Zaid.

Ibteesam kuwa tunda aka ambaci Kaduna ta d'auke wuta ta fara tunanin dama wai ba'a Kano take ba,? Ita duk a tunanin ta a Kano take shiyasa take tunanin guduwa, Hankalin ta ya k'ara tashi kawai itama ta fashe da kukan tausayin kanta.

Mugu ne ya dawo d'akin da magani a hannun sa da kuma gorar ruwa mara sanyi, bud'e rufin robar sukayi aka tsiyayo ruwan suka yayyafa masa a fuska a hankali ya motsa idon sa, kallan juna sukayi tare da yin murmushi cikin murnar motsawar sa, "Sannu mai gida" suke fad'a ganin yana k'okarin bud'e idon sa, k'okarin mik'ewa zaune yake suka taimaka masa ya mik'e suka bashi magani ya karb'a yasa idon sa a kulle, taimaka masa sukayi ya mik'e suka rik'e shi suka kaishi d'aki ya kwanta, Wizzy ya kalli Mugu yace, "Allah ya taimaka ciwon bai yi nisa ba da dole mu sanar da Daddy, mtswww amma gaskiya Gaye anyi d'an akuya wallahi."

"Bari kawai Wizzy ban d'auka zai aikata haka a gidan Mai gida ba wallahi, ai Mai gida kamar uba yake a wajan mu tunda babu abinda baya mana muda iyayen mu". "Muje k'asan kawai" Wizzy ya fad'a suka sakko daga saman.

Bayan wasu awanni Ibteesam tana zaune tana tunanin y'an uwan ta da masoyin ta kamar koda yaushe aka shigo d'akin, kallan sa tayi ganin sa rass dashi kamar bashi ne ya fad'i d'azu a sume ba, saurin d'auke kai tayi ganin yadda yayi mata kyau a ido sai take ji kamar tai ta kallon sa, gefen gadon ya nufa ya kalle ta fuskar nan a d'aure kamar kullum yace, "kin shirya?". Gaban ta ya fad'i amma sai ta daure tace, "Me?". "Zama karuwa mana" ya fad'a kansa tsaye yana kallan ta. "Meyasa d'azu baka bari shi yayi min hukuncin ba?". "Ni nake so nayi miki da kaina ba wani ba." "Amma meyasa ranka ya b'aci har kayi ciwo?". Kallan ta yake cikin mamakin tambayar ta kafin ya tab'e baki yace, "Bana san yawan tambaya" ya fad'a yana mik'ewa zaune tare da zuba hannayen sa a cikin aljihun wandon sa, "koma meye sunan ki ina so ki sani babu abinda zai fitar dake daga gidan nan matuk'ar ban d'auki mataki a kanki ba ba'a yi min na k'yale ina fatan kin gane?".

Yawu ta had'd'iye idon ta ya kawo ruwa tace, "Dan Allah ka sanar da iyaye na ina hannun ka ko babu komai hankali su zai kwanta dan nasan yanzu suna ta tunanin inda nake" ta fad'a hawayen na sakkowa daga idon ta.

Hannu ya saka a aljihu ya d'auko waya tare da mik'a mata yace, "Kira su". Da mamaki ta kalle shi ta kalli wayar hannun ta na rawa ta karb'a, da hanzari take danna number Abba ta, buga biyu Abba ya d'auka tare da yin sallama, "Abba na" ta fad'a cikin muryar kuka hawaye na cigaba da zuba a idon ta.

A can b'angaren Abba da yake zaune cikin iyalan sa da hanzari ya saka wayar a speaker kafin yace, "Ibteesam! Kece?". Girgiza kai take kamar yana gaban ta kafin tace, "Nice Abba ina Umma?". Umma da take zaune muryar ta na rawa tace, "Ibteesam gani, kina ina? Ina kika shiga tsahon wannan kwanakin?". Kuka ne yaci k'arfin Ibteesam ta kasa magana sai kuka jin muryar iyayen ta ya taso mata da kewar su da take kwana da ita ta tashi da ita, "kiyi magana Ibteesam kina ina?" Abba ya fad'a da hanzari. Karb'ar wayar Zaid yayi daga hannun ta ya kara a kunne yace, "Tana hannu na". Abba ya kalli Umma itama ta kalle shi kafin Abba yace, "Kai waye? Meyasa ka d'auke ta?".
"Sanin ni waye bashi me mahimmaci ba abinda nake so shine mai mahimmaci". Da sauri Umma tace, "Mai kake so? Ka fad'a insha Allah zamu baka."

"Abinda nake so yana tare da y'ar ku amma tak'i ta bani gashi ni kuma ba ta k'arfi nake so na karb'a ba" ya fad'a yana yatsine fuska kamar yana gaban su, "Me kake so?" Abba ya tambaya cikin mamakin abinda Zaid yace, "Karuwa nake so na mayar da ita, y'ar ku ta kira ni d'an iska shiyasa nake so na mayar da ita y'ar iskar itama, kuyi mata fad'a ta amince dani ta dad'in rai tun kafin na nuna mata iko na". Babu wanda gaban sa bai fad'i ba tsakanin Umma da Abba, kallan juna sukayi kafin Abba yace, "Kayi hak'uri bawan Allah ka fad'i ko nawa kake da buk'ata mun maka alqawari zamu baka amma dan Allah kada ka raba ta da mutuncin ta."

Dafe kai Zaid yayi dan har ga Allah ya gaji da magana amma jin abinda Abban yace ya saka shi ya kama k'ugu kamar yana gaban su yace, "ohh kuma abinda zaku ce kenan? Okay to ku shirya ganin y'ar ku nan da shekara d'aya maybe tazo muku da baby". "Dan Allah kayi hak'uri ko nawa ne zamu baka amma kar ka cutar da ita dan Allah" Umma ta fad'a tana kuka sosai. Shifa b'ata masa rai suke in sukayi zancen ko nawa yake so d'in nan hakan yasa yace, "ko family d'in ku kaff za'a siyar baku da abinda zaku iya bani gwara ku daina zancen kud'i cos basa gaba na" ya fad'a yana runtse idon sa yana bud'ewa.

"Ka taimaka dan Allah ko nawa kake so zamu bayar mudai ka k'yale mana yarinyar mu". "Oh god wai baka ganewa ne? Meye a kanka ne har haka,? Na fad'a muku baku da abinda zaku iya biya na koda zaku saida kowa na dangin kune, ko kana da matsala toshewar basira ne ina fad'a baka ganewa?" Ya fad'a a fusace dan da a gaban su yake babu abinda zai hana bai kaiwa Abba duka ba.

"Kayi hak'uri bawan Allah ka dai duba dan Allah" Umma ta fad'a itama muryar ta a sanyaye sosai hawaye na bin idon ta.

"In shi baya ganewa kema bakya ganewa ne? Mai kuke dashi da zaku bawa Zaid d'an gidan Ambassador Abubakar Ali huhh,? In zaku bawa y'ar ku shawara a akan abinda nake so ku bata kun bi kun cika min kunne da surutan ku na banza da wofi mtsw" yaja dogon tsaki tare da datse wayar.

Duk da Ibteesam shiga rud'ani da jin waye shi amma hakan bai hana taji haushin abinda yayiwa iyayen ta ba, dan ita fushin ta yafi k'arfi in aka tab'a mata iyaye yanzu ranta zai b'aci ta fad'a maka abinda baza kaji dad'i ba, bata san lokacin da ta diro daga kan gadon tace, "Wai kai ba'a koya maka tarbiyya a gidan ku bane ba? Ba'a koya maka yadda zakayi magana da manya bane hala,? Ko da yake ma ai laifi nane nima kowa ya ganka ai yaga mara tarbiyya wanda bai san darajar na gaba dashi ba, ina k'yale komai amma bana k'yalewa in aka tab'a min iyaye kuma......" irin juyowar da yayi ya hana ta k'arasa abinda take son fad'a, baya take ja jikin ta na rawa tsoro ya cika mata zuciya dan yadda yake kallan ta bai tab'a yi mata irin kallon ba, k'afar ta ta dama ya saka k'afar sa ya dake ta ya raba ta da k'asa sai kuwa ta wuntsila ta fad'i da baya kanta ya bugu da tiles jini ya fara zuba.

_Akwai complete nasa naira 200 kacal👌 09030398006._


Comments Share fisabinillah 🙏❤️🥰

*ƘASAITAR SO!*

©️ *Nana Haleema*

*9*


Cize baki take tana runtse ido jin yadda kan ta yake mata wani irin zafi kamar an saka wuk'a an yanka k'eyar ta haka

Please Login or Register in order to submit comment