Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"In kika kuma yi mana k'ara ko ihu a gidan nan sai na kashe ki har lahira, an fad'a miki nan gidan dambe ne ko kuma club da zaki zo kina cika mana kunne da ihu,? Ki shiga hankalin ki wallahi ki kula da duk abinda zakiyi kamar yadda zan kashe kiyashi haka zan kashe ki, shashasha mara hankali" ya fad'a yana jan k'ofar da k'arfi.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku na lalace ni Maryam, na jawo kaina bala'in da ban san k'arshen sa ba, ya Allah ina rok'on ka ka kub'utar dani daga hannun wad'an nan mutanen, ya Allah kada ka basu ikon cin galaba a kaina" ta k'arasa fad'a cikin kuka mai sauti, Sai da tayi kukan ta san ranta kafin ta koma sauke ajiyar zuciya ga yunwar da take d'awainiya da ita amma ta kasa cin abincin sabida rashin kwanciyar hankali da take ciki,tana zaune tana sak'a da warwara har bacci ya d'auke ta.

Tun k'arfe hud'u na asuba ta farka sabida yunwar da take ji dole ta tashi ta wanke bakin ta ta dawo ta fara cin abincin da aka kawo mata a daren, kamar za'a kwace mata abincin haka take ci sai da ta kusa cinyewa sannan ta sha ruwa ta koma gefe ta zauna cikin ta na wani irin k'ullewa, tana zaune har akayi kiran assalatu ta mik'e ta d'auro alwala ta dawo ta tayar da raka'ataul fijir, bata jima da idarwa ba aka tayar da sallah a masallacin da take jiyowa ta bi jam'i.

Tunda ta idar da sallar take ta d'ora kukan ta daga inda ta tsaya, babu wanda yake hangowa a idon ta sai Umman ta, ko waye yake mata aiki yanzu oho, sai ta sake fashewa da kuka, gari ya fara haske tana zaune a inda take kamar wacce aka tsikara da allura ta mik'e ta yaye labulen da yake d'akin akayi sa'a kuwa tagar da take d'akin ana hangon harabar gidan, kallan harabar gidan take babu kowa sai motocin da suke ajjiye a wajan sai sautin tsuntsaye da suke tashi a hankali, da azama ta juya ta nufi k'ofa da sauri ta bud'e ta fito falon, nan ma babu kowa sai duhu amma kana ganin gaban ka sai dai ba sosai ba, a hankali take tafiya har tazo steps d'in ta fara sauka a hankali har ta sauka falon da yake k'asan, kalle-kalle take tana tunanin wacce k'ofar zata bud'e ta sada ta da harabar gidan? Wacce take kallan ta kawai ta tunkara ta murd'a lock d'in ya bada sautin k'uttt ta murd'a handle d'in ta bud'e k'ofar, wani farin ciki ne ya ratsa ta ganin k'ofar ta bud'e ai da sauri ta sauka daga steps d'in dake k'ofar falon ta fita harabar gidan tare nufar gate din gadan-gadan dan burin ta a lokacin bai wuce ta bar gidan ba.

Har ta k'arasa gate din babu motsin kowa a gidan sai ita kad'ai hakan ya sake bata k'arfin guiwa ta isa inda gate d'in yake, a hankali take kai hannun ta ga lock d'in jikin gate d'in kamar mai jin tsoron wani abu a jikin gate d'in,tana d'ora hannun ta da niyar bud'ewa taji anyi sama da ita an cillar da ita can gefe kamar an cillar da kayan wanki kanta ya bugu da bayan mota, "washhh" ta furta dan ta bugu sosai ga wani irin zirr zirrr da take ji tun daga kanta har yatsun k'afar ta, hannun ta ta kalla da yayi sanyi yana wani iri kamar ba a jikin ta yake ba.

Zaid yana tsaye a jikin window hannun sa rik'e da cup yana kurb'ar coffee yana kallan ta, ganin yadda shocking d'in jikin k'ofar ya wancakalar da ita gefe ya saka shi wani d'an murmushi hakan ya saka ya saki fuska duk da baiyi murmushin ba amma fuskar sa ta saki, ajjiye cup d'in yayi kana ya fito daga d'akin ya sakko k'asan.

Ibteesam kuwa tana nan kwance jikin ta yayi wani irin sanyi bata da kuzarin da zata iya mik'ewa bata tare da tsanmani ba taji saukar maruka lokaci d'aya a fuskar ta, gigicewa tayi zata saki ihu ya saka k'afa ya take mata baki yana zaro mata idanuwan sa, ba k'aramin tsorata tayi ba ganin yayi mata tsayi sosai gashi babu abinda take gani sai hasken idanuwan sa da ya zaro su yana mata kallan gargad'i, d'auke k'afar yayi daga kan bakin ta ya tsuguna kusa da ita yana kallan fuskar ta da shatin marukan suka fito rad'au a farar fatar ta yace, "kina tunanin zaki iya barin gidan nan?, Huhhh kima ajjiye wannan tunanin tun kafindare yayi miki dan kin shigo kenan, in ma zaki fita yadda kika shigo ba tare da kin sani ba haka zaki fita." abinda ya kenan ya mik'e tsaye yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa.

kawar da kai tayi daga kallan sa ganin daga shi dai gajeran wando wanda ko guiwa bai zo ba sai farar vest wacce ta kama masa jiki sosai, hannun ta ya damk'a ya jawo ta da k'arfin tsiya ta mik'e tsaye tana layi kamar wacce tasha wani abun da zai saka ta maye, ganin yanayin da take ya saka kawai ya saki hannun nata ta koma da baya ta fad'i ba tare da ta shiryawa hakan ba, "Hasbunallahu wani'imal wakil" ta furta tana runtse ido dan k'ugun ta ya bugu sosai.

Banzan kallo ya watsa mata tare da jan dogon tsaki yace, "na baki 30 seconds ki tabbatar kin shigo cikin gidan nan" ya juya yana tafiyar izzah ba tare da ya sake kallan ta ya koma cikin gidan, dak'yar ta samu ta mik'e tsaye tana dafe bayan ta dan ta bugu iya buguwa daurewa kawai tayi tana tafiya, a haka ta koma falon ta baje a kan kujera tana kuka mara sauti.

Wizzy da ya fito daga d'akin da yake matsayin nasa ya ganta a kwance tana kuka shima ya tamke fuska yace, "Keee tashi ki koma inda kika fito kar na sake ganin ki a k'asan nan" ya fad'a cikin fad'a kamar zai zo ya dake ta, haka ta lallab'a ta mik'e ta koma saman ta zube a d'akin.

Bata san adadin lokacin da ta take a kwance akan tiles d'in ba sai bud'e k'ofar da akayi ne ya saka ta Mike dak'yar tana kallan mai shigowa, Zaid ne ya shigo ya shirya tsaf cikin k'ananun kaya yana taunar cingom yana wani irin shan khamshi kamar mace, ledar da ya shigo da ita jiya ya kalla tana nan da alama yadda ya ajjiye ta ba'a tab'a ba, d'aukar ledar yayi ya k'arasa inda take ya jefa mata a fuska cikin muryar sa da take a tausashe yace, "duk wani abu da mace zata nema akwai shi a ciki" ya fad'a yana niyar juyawa ya fita.

"Dan Allah dan Annabin rahama dan darajar iyayen ka malam ka sallame ni na tafi gida nayi maka alqawarin bazan sake yi wa wani rashin kunya bama balle kai" tsabar kuka muryar ta ta dashe sai kad'an ake ji a haka take rok'on sa, "Gida! Kina so ki koma gida ne?". Da sauri ta d'aga masa kai dan yadda taji yayi maganar a hankali ta d'auka ya hak'ura ne, "good, get ready to be my prostitute ni kuma nayi miki alqawarin komawa gida har da tsarabar baby ma" ya fad'a yana kallan fuskar ta da tayi ja tare da d'age girar sa sama yana sake had'e rai.

"Kayi hak'uri na fad'a maka wallahi ni ba y'ar iska bace ban tab'a iskanci ba ban san ya ake yi ba kayi hak'uri kar ka lalata min rayuwa". Sai da ya kalle ta ya tab'e baki tsanar ta na sake huda tsokar sa yace, "Don't worry duka zan koya miki ko kin manta ni d'an iskan ne?". Girgiza kai tayi tace, "A'a kaima ba shi bane kayi hak'uri." D'an runtse ido yayi bai cika son doguwar magana ba ya bud'e idon yace, "Kar kiga jiya na kyale ki ki d'auka ko zan k'yale ki d'in ne gabad'aya, u have to know inda maradin na mayar dake y'ar iska na rana d'aya ne baza ki kwana biyu a gidan nan ba tare da na aikata hakan ba, butt ni karuwa nake so ki koma y'ar iska kama ta kinga munyi 50-50 nida ke the same." Ta bud'e baki zatayi magana yayi saurin d'aga mata hannu ya bud'e k'ofar ya fice daga d'akin.

Komawa tayi ta kwanta a wajan tana cigaba da goge hawaye, tun tana tunanin har bacci ya d'auke ta.

Bata farka ba sai k'arfe goma na safe jikin ta duk yayi tsami haka ta mik'e ta fad'a band'aki tayi wanka ta fito tana kallan kayan da ya bata, mamaki take ganin hatta undies akwai kuma size d'inta sai taji tsoron kodai sun gama kalle tane lokacin da suka kawo ta gidan, haka take shiryawa cikin sanyin jiki da tunani har ta gama shiryawa tsaff ta mayar da sauran cikin ledar.

Wani tunani ne ya d'arsu a ranta jin k'arar tv da ta jiyo a falon ta mik'e dak'yar hannun ta yana bayan ta sabida mugun ciwon da yake mata ta bud'e k'ofar ta fito, yana zaune akan d'aya daga cikin kujerun yana danna laptop da alama aiki yake mai mahimmaci dan kacakan hankalin sa yana kan screen d'in laptop d'in, a kan carpet ta zube guiwowin ta mik'e tare da had'e hannayen ta alamun rok'o tace, "Bawan Allah ban sanka ba sai a ranar da muka had'u ban tab'a ganin ka ba sai a ranar da abin ya faru, na rok'e ka dan darajar sunayen Allah kyawawa kayi hak'uri ka barni na tafi gida, ni nake yiwa Umma ta aiki k'anwata kuma tana da stickler nice nake komai a gidan dan Allah kayi hak'uri kayi min ko wanne irin hukunci ne indai zaka barni na tafi amma banda hukuncin da kake fad'a" ta k'arasa fad'a hawaye na sakkowa daga idon ta. Kamar bai san Allah ya halicci wata halitta a wajan ba ya cigaba da aikin sa yana yi yana joting a takarda bai ko kalle ta ba balle ya amsa mata, "Dan Allah in kana k'aunar iyayen ka" ta sake fad'a jin da tayi yayi shiru.

Nan ma bai kalle ta ba ya cigaba da aikin sa kamar ma bai san abinda take yi ba, ganin hakan ya saka ta zauna ta cusa kanta cikin guiwowin ta tana kuka mara sauti, cigaba da aikin sa yayi har ya kammala ya rufe laptop d'in ya d'auka tare da mik'ewa yana shirin barin wajan, da sauri ta d'ago ta watsa masa wani banzan kallo tace, "Anya kai musulmi ne kuwa? Dan banga danshin imani da tausayi a tare da kai ba duk yadda akayi baka san Allah ba, na had'a ka da Allah na had'a ka da Annabin rahama na had'a ka da iyayen ka amma kayi burus dani, to kayi duk abinda zakayi kuma baza ka tab'a cimma burin ka a kaina ba sabida Allah bazai baka ikon keta min haddi ba dan ni ba y'ar iska bace irin ka" mik'ewa tsaye tayi ta cigaba da fad'in, "Na fad'a d'an iska ke kai d'an shaye-shaye wanda bai san darajar Allah da Annabi ba, mtswww ka barni a nan kar ka sallame ni har a tashi qiyama in ma ka tashi yi min hukunci ka kashe ni kar ka barni rai aikin banza aik....." ai bata kai ga k'arasawa bakin ya rufe gam kwakwalwar ta ta d'auke diff ta daina gane fari da bak'i, ta rasa gane a ina take a lokacin sabida tsabar gigicewa da tsananin azaba.

Wani irin wuci yake hannun sa yana rik'e da wuyan ta ya shak'e ta idon ta ya firfito shima haka nasa, cillar da ita yayi gefe kanta ya bugu da gefen kujera ya bada sautin kummm, belt d'in jikin sa ya kwance ya nad'e ta a hannun sa ya nufe ta kamar zakin da aka kwanto daga cikin keji.

_Akwai complete nashi naira 200 kacal 09030398006._😍



Comments and share fisabinillah 🙏🥰❤️

*ƘASAITAR SO!*

©️ *Nana Haleema*


*7*


Kamar daga sama aka aiko shi haka yake dukan ta da belt tana ihu, jin kuka da ihun yayi yawa a guje Wizzy ya hauro saman ganin irin dukan da yake mata yayi saurin rik'e shi yana fad'in, "Mai gida kayi hak'uri Allah ya wuci zuciyar ka". Fincike jikin sa yayi daga rik'o da yayi masa ya kalle ta da jajayen idon sa ya nuna ta da yatsa alamun last warning ya cillar da belt d'in a wajan ya fad'a d'aki yana layi kamar wanda ya bugu da kayan maye.

Kuka take sosai fatan jikin ta duk ta tashi gefen wuyan ta ya fashe sabida dukan da ta sha, Wizzy bai tab'a tausaya mata ba sai a lokacin ya tsuguna a gaban ta yace, "Kinga in zaki nutsu ki daina masa rashin kunya gwara ki nutsu in ba haka ba wallahi zai kashe ki kuma ya kashe banza, duk zafin kanki ya dama ki ya shanye, ki kula da abinda yace miki baya so in ba haka ba wallahi a nan za'ayi jana'izar ki a binne iyayen ki basu ga gawar ki ba, ya wuce inda kike tunani duk inda kike kaishi ya wuce wajan, ina baki shawara a matsayin na na wanda nasan halin sa in kuma kina ganin yi masa rashin kunya shi zai saka ya k'yale ki sai ki cigaba ki gani, malama ki tashi ki koma inda ya ajjiye ki kisha magani in kuma ya fito ya ganki tsaf zai k'ara jibgar ki" Wizzy yana gama fad'a mata hakan ya sauka daga saman gabad'aya dan wannan lokacin bana yiwa Mai gida magana bane ba.

Da rarrafe take jan jikin ta zuwa d'akin da take tana shiga ta kulle k'ofar ta baje a bakin k'ofar daga cikin tana cigaba da kukan ta, ko wanne b'angare na jikin ta ciwo yake mata tun daga fatar jikin nata har cikin k'ashin ta ciwo take ji, tunda take ba'a tab'a yi mata irin wannan dukan ba kamar za'a kashe ta shiyasa nake ji kamar an tsamo ta daga wuta, runtse ido tayi tana kallo fuskar Umman ta da Abba cikin yanayin damuwa da tashin hankali, zuwa wani lokaci zazza6i mai zafi ya sauka a jikin ta jikin ta ya fara rawa haqoran ta na garuwa da juna sabida sanyin da take ji, knocking d'in k'ofar aka fara yi a hankali, tana ji amma bata tunanin zata bud'e dan tasan bazai wuce mugun da ya zane taba ko yaron sa hakan ya saka ta sake kwanciya sanyin tiles na ratsa jikn ta, "baiwar Allah kizo ki bud'e an turo ni na taimaka miki ne" aka fad'a daga waje ana cigaba da buga k'ofar, jin muryar mace ya saka hankalin ta ya kwanta ta d'an mik'a hannu ta cire lock d'in k'ofar taja baya k'ofar ta bud'e aka shigo, babbar macece wacce a shekaru zatayi shekara talatin da wani abun ta shigo d'akin ta mayar da k'ofar ta rufe ta mayar da kallon ta ga Ibteesam cikin tausayawa ganin yadda jikin ta yayi ja tace, "Sannu y'ar nan, tashi ki samu ki gasa jikin ki zaki fi jin dad'i." Ba musu ta yunk'ura ta taimaka mata ta mik'e ta kaita band'aki ta had'a mata ruwa ta fito ta barta, bata jima sosai ba ta fito hannun ta dafe da kanta sabida ciwon da yake mata, doguwar riga kawai ta zura ta kwanta a kan gadon tana sauke numfashi.

Magani ta b'allo mata ta bata tasha kafin ta kwashe kayan abincin da aka kawo mata bata ci ba ta kulle mata d'akin ta sauka, da kallo Ibteesam ta bita tana mamakin hali irin na Zaid, ya gama jibgar ta ya turo kuma a bata magani.

Zaid kuwa cikin nutsuwa ya kalli Wizzy yace, "Su Gaye basu k'araso ba har yanzu?" Ya fad'a lokacin da yake fitowa daga d'aki, "eh mai gida amma sunce min suna kawo". "Sun zo ma kenan, muje kawai" ya fad'a yana fara sauka daga saman Wizzy yana bayan sa. A falo suka gamu da Atine mai dafa musu abinci tana ganin sakkowar su tayi murmushi ta kalli Zaid tace, "yallab'ai Allah ya kaiki lafiya". Iya fatar bakin sa ya amsa da amin kafin ya d'auko kud'i ya bata yayi ficewar sa.
Mota suka shiga Wizzy yaja motar suka fita daga gidan motar su Gaye ta shigo gidan.

*******

Da sallama Khalid ya shiga gidan su Ibteesam kansa a sunkuye gaban sa na fad'uwa, Abba da yayi masa izinin shigowa yace, "Shigo mana Khalid". Takalimin k'afar sa ya cire ya shiga cikin falon har lokacin bai d'ago kai ba.
A kan carpet ya zauna cikin nutsuwa yace, "Umma ina wuni" Umma da take zaune tana jan jarbi ta amsa da fad'in, "Lafiya Lau Khalid ya mutan gidan naku?". "Lafiya lau, duk sunce ayi miki jaje Allah ya bayyana ta." "Amin Khalid nagode. "

"Abban Jafar basu yo wayar ba har yanzu ko?" Umma ta tamabaya tana kallan Abba, sai da yayi ajiyar zuciya kana yace, "Basu yo waya ba koda yaushe cikin jiran wayar su nake muji abinda zasu buk'ata amma har yanzu shiru." Shiru tayi bata sake cewa komai ba sai addu'a da tayi a zuciyar ta. Jiki a sanyaye Khalid yayi musu sallama ya fita daga gidan ya shiga motar sa da ya bar abokin sa a ciki, kifa kansa yayi a kan sitiyarin motar ba tare da ya shirya ba hawaye suka zubo daga idon sa, "Abdul ban san haka nake san Ibteesam sai a yanzu da aka neme ta aka rasa nake jin zuciya ta tana wani irin zafi kamar ana dafa ta, A yadda nake jin zuciya ta a yanzu ji nake kamar ana saka wuk'a ana yankar ta sabida bala'in radad'in da nake ji a cikin ta, Abdul ina san Ibteesam ina santa in na rasa ta basan ya zanyi ba" ya k'arasa fad'a cikin kuka sosai kamar yaro k'arami.

Abdul da yake sauraran sa jikin sa yayi bala'in sanyi tausayin abokin nasa ya kama shi cikin muryar rarrashi yace, "Kayi hak'uri Khalid insha Allah za'a ganta cikin k'oshin lafiya addu'a zaka taya ta Allah ya kare ta a duk inda take ka daina kuka dan Allah. " tissue ya zara ya goge idon sa kafin ya kunna motar su bar unguwar dan tunda Ibteesam ta b'ace ya bar zaman gidan kakanin sa a Yakasai koma gidan su.

Bayan fitar Khalid Abba ya kalli Umma da take goge hawaye yace, "Yanzu Halisa baza ki sakawa zuciyar ki dangana ba? Wannan kukan da kike yi ba shine mafita bafa,ki duba yadda kika rame kika yi bak'i a cikin kwana biyu, addu'a ita kad'ai zaki yi mata ki taimake ta, Allah zai bayyana ta zata dawo gare mu da izinin Allah amma sai mun karb'i jarabawar da Allah ya k'addaro mana hannu biyu, in kina kuka Jidda da Jafar su kuma suyi mene? Dan Allah ki daina wannan kukan Allah yana tare da ita a duk inda take." Goge hawayen idon ta tayi kawai bata ce komai ba ta cigaba da jan jarbin ta.

Sallamar da akayi ne ya saka Abba ya mik'e ya koma d'akin sa dan gidan koda yaushe cikin bak'i y'an jaje ake.

**********

Bayan sallar la'asar Daddy yana zaune akan kujerar da yake babban falon gidan sa yana shan fruit Amina na zaune a kusa dashi tana canja cannel d'in tv, ajjiye remote d'in tayi tace, "Nikam kwana biyu ina Zaid yake?". "Yaje Abuja gidan Mummyn sa" ya bata amsa yana kallan tv ba tare da ya kalle ta ba.

Zatayi magana aka shigo falon nasu da sallama, amsawa sukayi suna kallan masu shigowa, mik'ewa Amina tayi taje ta d'auko mayafi dan ganin bak'in da suka shigo, takaici ya kama Daddy sam baya san irin wannan rayuwar duk da y'an uwan sane amma ai yaci ace sun nemi izinin sa kafin su shigo masa falo kai tsaye tunda yana da iyali, "Sannu da Yaya Babba" ya fad'a fuskar sa babu walwala yana kallan yayyen nasa guda biyu.

Cikin fara'a Yaya Babba yace, "Yauwa Abubakar ya gida?". Mamaki ya kama ganin suna gaisawa da fara'a a fuskar su, shanye mamakin sa yayi yace, "Lafiya lau Alhamdulillah". Zama sukayi dukkan su kafin Yaya Babban yace, "Ina Zaid d'in?". "Yaje Abuja wajan yayar mahaifiyar sa". "Allah sarki ai gwara ya dinga zumunci" Yaya Bala ya fad'a da murmushi.

"Abubakar dama magana ce ta kawo mu akan shi Abdullah" Yaya Babba ya fad'a cikin nutsuwa yana kallan Daddy, gyara zama Daddy yayi yace, "To Allah ya lafiya." "Lafiya qalau sai alkhairi, wato gani nayi sabida sake inganta dank'on zumunci naga mai zai hana baza'a had'a yaran nan aure ba." Daddy da ya kasa fahimtar sa yace,"Wanne yara kenan?". "Zaid da mai sunan Mama Eman, in akayi haka zumunci zai sake k'ulluwa sosai kuma daman wannan burin mahaifiyar mu ne kafin ta bar duniya."

Shiru Daddy yayi yana nazari kafin yace, " abu ne mai kyau in akayi hakan kuma zamu fi kowa farin ciki, amma Yaya Babba zanyi magana dashi Zaid d'in in ya dawo muji meye ra'ayin sa akai ita ma Eman d'in sai a tuntub'e ta aji ko?'". "Eh hakan yana da kyau kam gwara a tambayi yaran aji ta bakin su" Yaya Bala ya fad'i cikin sakin fuska. Jimm sukayi babu wanda ya sake magana a cikin su kafin su Mik'e ko wanne yana fama da babbar riga suyi sallama su tafi.

Fitar su babu jimawa Zaid ya shigo waya a mak'ale a kunne sa yana amsawa, tsayawa yayi a falon ya gama amsa wayar kafin ya kashe ya kalli Daddy yace, "Daddy sannu". "Welcome Son" ya fad'a da murmshi a fuskar sa, Daga haka Zaid bai sake cewa komai ba ya haura saman sa dan a gajiye yake sosai.

Lokacin Sallar magariba ne ya sakko dashi ya fita masallaci bayan an idar ya dawo yana niyar hawa sama Daddy yace, "Zaid dawo ka zauna" ba musu ya dawo ya zauna a akan kujera yana kallan Daddy. "Zaid yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?". Zaro ido waje yayi yace, "Me kuma nayi?". "Ka saka y'an daba sun wahalar da iyayen ka mana, yanzu wannan halayya ce mai kyau Zaid?." "Daddy basa sona ba kuma sa k'auna ta tun mahaifiya ta na raye suke nuna mata tsana har ta bar duniya, tsanar ta dawo kaina a gaba na suke zagi na su zage ka kuma na k'yale su? Impossible Daddy in na k'yale su gani zanyi kamar na aika babba sab'o shiyasa na sanya a gyara musu zama" ya k'arasa fad'a yana tab'e baki tare karkad'a k'afa.

Shiru Daddy yayi cikin rashin sanin abinda zai cewa Zaid d'in sai kawai yace, "D'azu sunzo sun same ni akan suna so a had'a ka aure da Eman." "Waye kuma haka?" Ya tambaya yana d'aga gira sama. "Y'ar wajan Yaya babba ce." "Kuma ni suke so na aure ta? Ai wannan labari kawai suka baka Dad because ni ko mata sun k'are mai zanyi da y'ar su? Kuma haka suke so su bawa d'an shaye-shaye auren yarinyar su,? Ko sun mata ni d'an iska ne,? Koda yake koma dai meye tasha zaman ni nikam bana son ta balle auren ta".

"Zaid! Ya kamata ka iya bakin ka akan y'an uwana, me suka tare maka har haka ne wai? Ko wanne lokaci zancen ka basa son ka yaushe kasan basa san naka,? Ka shiga hankalin ka ka daina fad'a musu duk abinda kaga dama a gaba na zan b'ata rai a kan hakan wallahi." "Okay sorry, but ka sanar dasu bana son y'ar su bazan kuma aure ta ba, in suka yi gangancin aura min ita kuma...." ya k'arasa fad'a yana girgiza kai, yana fad'ar hakan ya mik'e kawai ya nufi saman sa da sauri.

Washe gari da wuri Zaid ya shirya ya tafi Company sabida meeting d'in da zasuyi shida company sarrafa talamin da yake Malaysia mai suna vinci, tunda ya fita bai dawo ba sai bayan azahar ya dawo gidan a gajiye jikin sa kamar an masa duka haka yake ji sabida gajiya.

Saman sa ya hau yayi wanka ya kwanta yana lumshe ido cikin gajiya, wayar sace tayi k'ara ya

Please Login or Register in order to submit comment