Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin su yana da rufin asiri babu wanda za'a kalla ace masa talaka dan a cikin su babu wanda shekara zata zuwa ta wuce ba tare da sunje zirayar saudia ba, Abubakar ya fara aiki a k'ark'ashin Foreign affairs dake garin Abuja a lokacin Allah ya had'a shi da Maryam a garin, Maryam ta kasance marainiya bata san mahaifin ta ba sai a hoto ta rayu da mahaifiyar ta na wasu shekaru kafin ta bar duniya itama, tun daga lokacin take shan wahala a wajan matan uba kasancewar ta k'arama a wajan mahaifiyar su daga baya ta dawo Kano wajan Kakar ta da ta haifi Babar ta, Soyayya me tsafta ta shiga tsakanin su har ta kaisu ga aure, tun farkon auren su ta fara fuskantar wulaqanci daga dangin sa amma bata nunawa kasancewar mijin ta na santa bata damu ba.

Arzuk'in Abubakar yana ta k'aruwa kasancewar sa mai biyayya iyayen sa sun bar duniya suna saka masa albarka hakan ya saka babu wanda ya kama k'afar sa a y'an uwan sa, k'iri-k'iri y'an uwan sa suke nuna masa bak'i da hassada a fili, cikin ikon Allah arzukin Daddy na gaba nasu na dad'a k'asa a haka har cikin Zaid ya bayyana.

Bayan haihuwar Zaid sai abun nasu ya dad'a gaba dan a lokacin arzuk'in kamar a sama Daddy yake tsintar sa, duk wata sai ya aikawa da ko wannen su abinci da kayan shayi da kud'in cefane, banda mota da gida da ya bawa kowa wannen su amma kullum cikin rainuwa suke.

A lokacin da Zaid ya kai shekara hud'u a duniya a lokacin aka bawa Daddy Ambassador a k'asar Cyprus suka tarkata suka koma can da zama, wannan samun matsayi da Daddy yayi ya sake tsone musu ido sai suka fara yi masa fatan mutuwa su samu gado, tun daga lokacin da aka haifi Zaid ko sau d'aya ta yi b'ari daga lokacin bata sake ba koda b'atan wata ba.
Shekaru biyar yayi a Ambassador na Cyprus kafin su dawo Nigeria a lokacin Zaid nada shekaru tara a duniya.

Tun dawowar su aka fara farautar rayuwar Zaid ana yiwa babar sa Wulaqanci kamar zasu kashe ta, duk abinda ake Zaid yana gani kuma duka yana sane da duk abinda ake yi a lokacin yayi yarinta da fahimta.

Abdullah wato Zaid yaci sunan mahaifin Mama ne hakan ya saka take masa lak'abi da Zaid yaro ne mai zafin zuciya tun yana k'aramin sa, yana da saurin fushi abu kad'an ne yake harzuk'a masa zuciya, bashi da ya yawan magana kuma ya taso a cikin turawa wannan dalilin ya saka rashin maganar tasa yaso yayi yawa, Zaid baya san hayaniya sabida Allah ya jarabce shi da wani ciwon kai da indai ya shiga hayaniya sosai to tabbas zai tashi in kuma ciwon ya tashi kamar zai bar duniya dan sai an saka abu an d'aure masa kan dan ji yake kamar zai tarwatse, likitoci da dama sun duba shi amma basu ga wani abu a kan na sa ba haka yasa aka hak'ura aka cigaba da rok'on Allah.
Zaid yana san iyayen sa sosai da sosai lokacin da ya fara hankali ya fara lura da irin zallar k'iyayyar da dangin mahaifin sa suke masa shida mahaifiyar sa, Zaid baya san shiga mutane yafi so ya killace kansa a wajan da babu hayaniya ko kuma ya koma d'aki yayi ta kid'a da kayan kid'an sa dan Allah ya bashi fasahar iya kid'a.
A lokacin Daddy ya sake samun Ambassador of Finland suka sake tafiya k'asar, a can Zaid ya cigaba da makaranta zuwa lokacin ya shiga University inda yake karatun b'angaren zane-zane dan tun yara k'arami in ya iya zane sosoi, ta b'angaren tahfiz ma a can yayi karatun sa sabida akwai brach d'in wata makaranta da k'asar Dubai suka kawo ta k'asar a ciki ya sauke alkur'ani ya littafai da dama, shekara hud'u ya kammala karantun sa a lokacin shekarun sa ashirin cif a duniya a lokacin kuma suka sake dawowa Nigeria.
Zaid Allah ya bashi baiwar Fahimtar yanayin mutum tun kafin yayi magana hakan ya saka da yaga mara gaskiya a ido yake gane shi, ko a Finland y'an sandan can sukan neme shi in suna san kama marasa gaskiya, bayan dawowar Daddy ya gina masa kafaran kanfani mai suna ZAID DESIGN COMPANY kyau da tsari aka zuba ma'aikata, ana aiki kuma mai kyau dan da an zana takalmi an fitar turawa sakin kud'i suke yi su siyi design d'in.

A shekarar Mama ta had'u da wani irin ciwo da aka rasa meye iya bincike anyi amma ba'a gano wanne irin ciwo bane shine yayi sanadin da ya kaita har lahira babu irin maganin da ba'a yi ba amma Allah baiyi zata rayu ba, a lokacin dangin Daddy kamar su zuba ruwa a k'asa sha sabida farin ciki dan sun tsani Maryam gani suke kamar ita take cinye komai na dukiyar sa, wannan farin ciki da suka nuna k'arara ya sake jefa zuciyar Zaid cikin tsanar su me muni, Mama Asma'u ita kad'ai ce me zuciya mai kyau a ciki su ita kad'ai ce take san Zaid tsakani da Allah tun lokacin mahaifiyar sa take kuma kaunar yayan ta badan dukiyar sa ba.

Bayan rasuwar Mama Daddy ya sake barin k'asar aka sake bashi wani matsayin suka tafi shida Zaid dan bazai iya barin sa shi kad'ai ga ganin irin halin kiyayyar da ake nuna masa aka bar Company a hannun abokin Zaid wanda suka yi karatu tare, rayuwar Zaid ta shiga kunci na rashin mahaifiyar sa a kusa dashi ya sake zama wani shiru-shiru zafin zuciyar sa har ya ninka na baya, fara'a kuwa kamar ba'a halicce ta a fuskar sa ba.

Shekara biyar suka samu a k'asar suka sake dawowa Nigeria a lokacin ne Uncle Sani ya bud'e wuta sai Daddy yayi aure ya kawo masa Amina yace ya aura, babu yadda ya iya tunda shine matsayin uba a wajan sa akayi bincike akan Amina komai dai-dai sannan akayi auren a lokacin Zaid ya koma Finland k'aro karatu, Komawar Zaid a lokacin suka had'u da wata baturi me suna Rahana ta soshi sosai shima ya so ta daga baya ta yaudare shi har ta kai shi ga sanin ta tun daga lokacin ya tsane ta tun daga kanta kuma bai sake gigin yin wata budurwa ba dan a ganin sa dukkanin su halin su d'aya.
Ranar da ya dawo ranar ya fara ganin rashin gaskiya a lamarin Amina inda ya same ta dumu-dumu tana zuba masa garin magani a abinci, da yayi bincike ya gano yarinyar su Uncle Sani ce tun daga lokacin ya tsane ta itama ko abincin ta bai taɓa ci ba haka ya saka aka yi masa wani d'an small cafe a saman sa yana dafa coffe da tea a duk lokacin da yaso kasancewar abinci bai wani dame shi ba.
Babu mai hawar masa sama sai me gyara masa d'aki shima kuma namiji ya aminta dashi shiyasa ya bar shi kuma ba'a gidan yake da zama ba, silar had'uwa Zaid dasu Wizzy akwai ranar da motar sa ta lalace a k'ofar nassarawa da daddare yana tafiya a k'asa aka kwace masa waya a akan idon su Wizzy akayi suka kamo wanda ya kwace ya kawo masa da kansa kuma ya bashi hak'uri, tun daga lokacin in yazo wucewa ya kan kalli inda suke ya gansu su uku a killace babu ruwan su da mutane shi kuma yana san rayuwar zama waje d'aya hakan ya saka suka zama abokan sa, yana yi musu alkhairi sosai dan babu wanda bai san gidan su a cikin su yana zuwa ya har wajan iyayen dukkanin su in hakan ta kama.

Zaid yana yawan zuwa gidan Mama Asma'u su gaisa sosai dan yana santa dan ya fahimci ita ba dukiyar su take so ba su take so, Mummy Aisha itace kad'ai yayar Mamar sa wacce ya sani kuma take kulawa dashi, tana zaune a garin Abuja itama yana yawan zuwa su gaisa dan ita yake yiwa kallan mahaifiya a gare shi.

Zaid Namiji ne me zubin k'arfafa ko ina na jikin sa a murd'e yake kana ganin sa kaga wanda yake yawan d'aga k'arfe, bashi da fara'a ko kad'an fuskar sa da zubin sa kamar jarumin indian film d'in nan John abraham, farin ciki ko bak'in ciki baya saka shi dariya sai kai sa'a shine zaka ga yayi murmushin gefen baki shima kuma sai dai in Mama da Daddy aka yiwa addu'a amma kafin kaga haqoran sa a waje ana jimawa sosai, zaman sa dasu Wizzy ya saka ake masa kallan d'an iska d'an shaye-shaye in da abinda ya tsana a duniya bai wuce wannan kalmomin ba baya iya yafe su ko kad'an dan sanin Rahana da yayi bai saka ya cigaba da neman mata ba dalilin da ya saka ya tsani kalmar d'an iska, ko wayee ka kira shi da haka baya saurara maka nan take zuciyar sa take harzuk'a yayi maka hukunci ko ya saka yaran sa suyi maka, Zaid abokin sa d'aya takk a duniya shine Hameed wanda companyn sa yake a hannun sa bayan shi bashi da wani aboki a duniya.

Uncle bala, Uncle Sani da Uncle Saifullahi a yanzu basu da burin da ya wuce kashe Zaid shine babban burin su da sun gama dashi su dawo kan Daddy in ya mutu su kuma su mallaki komai nasa wannan dalilin ya saka suka shigo da Amina cikin rayuwar sa, aikin suke amma babu nasara kuma duk da haka Daddy bai fasa kyautata musu ba amma su burin su suga bayan sa duka kud'in su a wajan malamai suke k'arewa wajan karb'o magani.

Zaid duka ya karance su kuma shima yana dagewa wajan taya Daddyn sa da addu'a kuma shima ya kan karb'o maganin tsari wanda aka samo shi daga alkur'ani mai girma a wajan wani malami dake kusa da gidan su Wizzy, kasancewar Daddy ya kasance mai taimakom talakawa koda yaushe gidan sa a cike yake da mabuk'ata addu'ar da suke masa ita take dad'a bashi kariya daga sharrin su Uncle Sani, wannan ya dalilin ya k'arawa Zaid tsanar iyayen nasa ko kad'an baya kaunar ganin su shiyasa koda wasa baya ziyartar ko wanne a cikin su kuma baya sakewa da d'an kowa a cikin su indai ba yaran Mama Asma'u ba, yana raga musu ne ma sabida da Daddy yana nuna masa b'acin ran sa akan hakan, har lokacin kuma Daddy ya kasa gane manufar su a kan sa sabida shi tsakani da Allah yake zaune dasu shi kuma Zaid bai sanar dashi ba sabida gudun shigar sa wani hali dan sosai yana kaunar mahaifin sa.

Had'uwar Zaid da Ibteey ba k'aramin b'atawa Zaid ran yayi ba, ta zagi Maman sa sannan tace masa d'an iska ta kira shi da d'an shaye-shaye mai lalata yaran mutane, wannan kalamai nata suka dasa masa tsanar ta lokaci d'aya gashi sam shi bai iya tsanar abu ba dan in yace bayayi kawai yayi, ba'a tab'a jifan sa da irin kalman ba shiyasa ya d'auki alwashin koya mata hankali yadda ko nan gaba akace ta yiwa wani abinda tayi masa baza tayi ba dan a kanta yake tunanin fara lalata yaran mutane kamar yadda ta fad'a.

*Akwai complete nashi #200 kacal 09030398006.*👌

*ƘASAITAR SO!*

©️ *Nana Haleema*


*4*


"Ibteey kiyi sauri ku tafi kinga rana har ta bud'e bana so kiyi dare" Umma ta fad'a tana fitowa daga d'aki da leda a hannun ta, mik'ewa tsaye Ibteey tayi ta gyara mayafin ta tace, "To Umma ai na shirya". "Ina Jidda?". "Umma kin san jiya anyi ruwa gwara ta huta sabida yanayin jikin ta." D'an jim Umma tayi tana kallan Ibteey kafin tace, "Bana san fitar ki ke kad'ai". D'an murmushi Ibteey tayi tace, "Babu komai Umma ki tayi min addu'a, na tafi kar lokacin sallah yayi" ta fad'a tana niyar ficewa daga falon.

"Ibteesam!" Umma ta kira ta daga baya cikin sanyin murya, juyowa tayi tace, "Na'am Umma na". "In dare yayi ki kwana kya dawo gobe kar ki tawo da daddare kinji ko?". "To Umma insha Allah sai na dawo" ta fad'a tana ficewa Umma ta bita da addu'a.

A hankali take takawa ta fito daga gidan tana D'an kalle-kalle, sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ganin wanda take so ta gani sun had'a ido, shima murmushin yayi ya nufo ta yace, "Ibteey na sai ina?" Ya tambaya cikin sanyin murya yana mata murmushi. D'an d'agowa tayi ta kalle shi kafin ta sake sunkuyar da kai tace, "hotoro zanje gidan Dada". Murmushi yake jifan ta dashi yace, "Ina Jidda zaki tafi ke d'aya?". "Kasan anyi ruwa ga yanayin ciwon ta ya saka nace a k'yale ta."
Gyara tsayuwa Khalid yayi yace, "Bana san fitar ki ke kad'ai kin sani ko?". "Na sani yanzu zan dawo ba jimawa zanyi ba" ta fad'a a d'an k'agauce dan ta gaji da maganar.

"To sai kin dawo" ya fad'a har lokacin idon sa a kanta, murmushi tayi kawai ta fara tafiya da d'an sauri dan so take ta isa titi da wuri ta samu mota, kallan ta yake har ta b'acewa ganin sa kafin ya d'auke kai ya kalli wanda ya tsaya a gefen sa yana kallan sa, "Mtswww munafuki meye?". Ya kwashe da dariya yace, "Wannan kallo da kake binta dashi Khalid ai sai ta fad'i." "Hmmm yarinyar ce akwai kyau wallahi" Khalid ya bashi amsa yana lumshe ido tare da bud'ewa.

"Hmmm ai tunda har tana sanka ai zance ya k'are Khalid in nine kai wallahi da yanzu nayi batun aure dan barin irin su Ibteey a k'asa wani minister na zuwa zaiyi wuff da ita." Khalid ya kalli abokin sa kafin yayi murmushi yace, "Kai kana tunanin akwai wanda Ibteey zata so bayan ni? Kai kasan san da take min kuwa?." "Na sani mana kai kuma ba irin wannan san kake mata ba."

D'an yatsine fuska yayi ya saka hannu d'aya yana sosa kansa kafin yace,"Ina santa mana amma gaskiya auren mace mai qiba baya tsari na". "Haba Khalid kasan da hakan kuma kake b'ata mata lokaci?". "Kai yarinyar tana so na ne over in yanzu nace mata ba auren ta zanyi ba tsaf zatayi ciwo, zo muje gida" yana gama fad'ar hakan yayi gaba shima yabi bayan sa.

Ibteesam kuwa tafiya take a hankali cikin nutsuwa har ta fita bakin titi duk da tazarar su babu yawa, a kan titin ta tsaya tana kallan wanda zaiyi hanyar da zata bi tana kuma kallan agogon hannun ta, wani mai napep d'in ta hango babu kowa ta saka masa hannu ya tsaya tace, "Hotoro bos stop". "Hajiya kud'in ki dari biyu". "Zan bada dari uku amma drop". "To hajiya" yana gama fad'ar hakan ta shiga yaja napep d'in.
Tun daga kan gada ana traffic ne har danger state road, "Hajiya ko zamu bi ta baya ne nan traffic yayi yawa wallahi sai mu kusa la'asar a nan wajan". "Eh muje d'in naga wajan a cakud'e." Juya kan Napep d'in yayi yabi k'asan gada suka wuce.
Tafiya suke hankalin ta na kan titi shi kuma yana kallan titi yana tuk'in sa a hankali, parking taji yayi sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunanin duniyar da ta tafi dan a zahiri kallan titi take amma a zuciyar ta wani tunanin take daban ta kalle shi tace, "Lafiya ka tsaya?". Juyowa yayi ya kalle ta yayi murmushi, "Hiii" aka fad'a ana kallan ta daga k'ofar Napep d'in, zatayi magana kenan aka fesa mata hoda a fuska ta lumshe ido ta zube akan kujerar, Wizzy ya kalli mai napep d'in yace, "good job" ya fad'a yana yi masa jinjina.

Murmushi mai napep d'in yayi yace, "Godiya nake Oga". Cak Wizzy ya d'auke ta ya saka ta a mota ya d'auki hanya a guje.

***********

Tsaf ya shirya cikin dogon jeans black mai zanen fari ya saka riga fara mai ma6allai a gaban rigar ya kawo farar picap ya saka a kansa, wayar sa ya d'auka tare da jakar sa ta tafiya ya fito daga d'akin nasa, a hankali yake sakkowa daga saman yana yi yana kallan agogo dan ganin ya kusa missing flight, cak ya tsaya tare da komawa baya yana kallan Amina da take zuba wani ruwan magani a cikin miyar agusi d'in da take ajjiye a akan dining table d'in, wani irin takaici ne ya kama Zaid tsanar ta ta sake yi masa dirar mikiya lokaci d'aya, a fusace yake sakkowa daga saman yana wani irin wuci kamar zaki, ganin sa ya saka ta firgita tayi baya da sauri tana b'oye maganin a zanin ta, bai jira wani abu ba yana k'arasowa ya d'auki miyar ya watsa mata a jikin ta, ihu Amina tayi sabida miyar da zafi tana zazzage rigar ta, sakin flasks d'in yayi a kan tiles d'in kafin ya juyo a fusace ya nuna ta da yatsa yace, "In kika sake wani abun ya sami mahaifina zan iya kashe ki" ya fad'a yana zaro mata manyan idon sa wanda suka koma jajaye sabida b'acin rai da k'unar zuciya.

Daddy da ya jiyo ihun Amina ya fito da sauri ya sakko k'asan, cak ya tsaya yana kallan ta jikin ta duka miya ga Zaid ya saka ta a gaba yana nuna ta da yatsa, "Zaid!" Daddy ya kira shi a fusace yana kallan sa da b'acin rai a bayyane a fuskar sa. "Zaid meyesa baka da kirki ne? Me yake damun ka? Uban me Amina ta tare maka ne a gidan nan ka sako ta a gaba haka eyeee,? Inda mahaifiyar ka tana raye wani yake mata irin abinda kake mata zaka ji dad'i?" Daddy ya fad'a cikin fad'a yana nuna shi da yatsa. Kallon sa Zaid yayi yana jin wani irin b'acin rai yana taso masa daga k'asan zuciyar sa tsanar Amina kuwa dad'a nitso cikin zuciyar sa, a kanta kad'ai Daddy yake masa fad'a har haka ya za'ayi bazai tsane ta ba, "Bata hak'uri" maganar Daddy ta katse masa tunani.

Da sauri ya d'ago kai ya kalli Daddyn nasa jikin sa ya soma wani irin rawa dan shi a rayuwar sa sam bai san wani abu wai shi hak'uri ba, bai tab'a bawa wani hak'uri ba sai dai shi a bashi koda shine bashi da gaskiya k'arfin ikon sa yana sakawa a bashi hak'uri, "Kayi abinda nace Zaid" Daddy ya sake fad'a cikin murya mai amo yana kallan Zaid, Saurin dafe kan sa yayi yana jin wani irin jiri yana neman d'aukar sa, jikin sane ya soma wani irin rawa kamar an jona masa wutar lantarki, "Ka bata hak'uri Zaid in ba haka ba zaka had'u da b'acin raina wanda baka tab'a gani ba."

Bakin sane yake rawa yana so yayi abinda Daddy yace amma ya kasa bakin sa yayi masa wani irin nauyi wanda bai tab'a yin irin sa ba, "baza kayi abinda nace bane Zaid?" Daddy ya sake fad'a a tsawace yana kallan sa da b'acin rai.

"I'm....so..rr...y" ya fad'a a rarrabe cikin rawar murya, yana fad'ar hakan ya wani runtse ido kamar wanda ya aikata babban sab'o yana yana girgiza kai, "Abuja" abinda ya iya fad'a kenan sanyayeya juya a fusace ya fita daga falon.

"Musa! Musa!! Musa!!!". A guje ya Musa ya tawo jikin sa na rawa dan yadda yaji muryar Zaid d'in ba k'aramin rud'a shi yayi ba, "Na'am gani" ya fad'a yana dan rank'wafawa, bai magana ba sai bud'e motar da yayi kawai ya shiga ganin hakan shima Musa ya shiga suka nufi hanyar airport, tunda suka shiga yake jan tsaki fuskar sa a tamke kamar koda yaushe sai wuci yake yana girgiza kai, in ya tuna ya bawa Amina hak'uri sai yaji kamar yayi hauka sabida takaici da bak'in ciki.
Koda suka k'arasa baiyi magana ba ya bud'e motar ne kawai ya fice ya shiga ciki, da kallo Musa ya bishi kafin yace, "Oh albasa batayi halin ruwa ba".

Daddy kuwa yana fita ya matsa kusa da Amina ya rik'e hannayen ta duka biyun yace, "Kiyi hak'uri dan Allah insha Allah hakan baza ta kuma kasancewa ba, na rasa abinda yake damun Zaid a kanki amma zan kamo bakin zaren kada ki bari abinda ya faru ya dame ki dan Allah badan ni ba". Share hawayen da suka ciko mata ido tayi ta d'an yi murmushi tace, "Babu komai kar ka damu, da ka sani baka yi masa tsawa ba kasan yanayin jikin sa yanzu sai hakan ya tayar masa da ciwon sa." Ajiyar zuciya Daddy yayi dan shima tunda yayi masa tsawar yaga yadda yanayin sa ya canja jikin sa yayi yake tsoron Allah yasa kada hakan ya zama silar tashin ciwon Zaid, "dole ne na tsawatar masa sabida kar ya sake kuskuren aikatawa nan gaba in yaga yayi ba'a yi masa tsawa ba gobe ma kuma yi zaiyi, babu abinda zai same shi ki kwantar da hankalin ki."
"Duk da haka sabida yanayin ciwon sa ka daina masa irin wannan tsawar." "Amina kowa fa yana da fushin nan, kowa yana da zuciya amma mu muna sarrafa ta yadda ya kamata shi waye da bazai sarrafa zuciyar shi ba? Komai fushi haka rayuwa zatayi,? Dole a dinga tsawatar masa yasan ba komai ake samu ta fushi da zafin zuciya ba, kiyi hak'uri dan Allah. " "Haka ne, bara naje nayi wanka na canja kaya na" ta fad'a tana zame hannun ta daga rik'on da yayi mata ta wuce d'akin ta tana wani irin murmushi mai kama da murmushin nasara.

Wayar sa da tayi k'ara ya saka ya ciro ta daga aljihu ganin mai kiran ya sanya gaban sa fad'uwa dan indai kaga kiran sa to ba alkhairi bane ba, "Hello Yaya" ya fad'a a sanyaye. "Ka rik'e hello d'in ka Abubakar, ashe d'an ka bashi da mutunci? Ashe bayan shaye-shaye har da daban ci yake yi bamu sani ba? Tsabar tsinancewa irin ta Zaidu mu zai saka y'an daba su yiwa dukan tsiya dan kawai munzo gidan su,? Sun fasa min baki shi kuwa Bala ma sun targad'a shi a hannu kaga kenan nan gaba kashe mu zai saka ayi". Shiru Daddy yayi yana sauraran sa jikin sa duk yayi sanyi, "To sai ka aiko da kud'in magani tunda d'an iskan d'anka ne yayi mana wulaqanci." Ajiyar zuciya Daddy yayi yace, "Allah ya baku hak'uri insha Allah zan kawo shi ya baku hak'uri." "Ku rik'e hak'urin ku bama so amma dole ka aiko da kud'in magani". "To zan turo insha Allah". "Ka kyautawa kanka" ya Fad'a yana katse kiran.

Ajiyar zuciya Daddy yayi jiki a sanyaye ya koma sama yana tunanin halayyar Zaid, ya rasa a ina ya d'auko wannan halayyar tasa.

Saukar sa a airport na Abuja bai jira driver ba kawai ya d'auki drop d'in taxi ya tafi gidan su da yake mai tama, a k'ofar gidan ya sauka ya bawa mai taxi d'in kud'in sa shi kuma ya nufi gate d'in gidan yayi knocking, dake mai gadin gidan yasan da zuwa sa yayi sauri yazo ya bud'e yana yi masa sannu da zuwa, a ciki ya amsa kafin ya shige cikin gidan yana wata irin tafiya cikin k'asaita, direct inda yake mallakin sa a gidan ya nufa ya bud'e ya shiga, falon yana nan tsaf a gare sai k'ura kad'an, d'akin ya wuce ya ajjiye jakar hannun sa ya fad'a band'aki, wanka yayi tare da alwala ya fito ya shirya cikin jallabiya kofi colour mai hula a baya, sallah ya tayar bayan ya idar ne ya fito ya shiga kitchen.

Kettle ya kunna ya dafa ruwan zafi ya had'a tea ya dawo falo ya d'an kad'e inda zai zauna kafin ya zauna ya fara shan tea d'in a hankali, sai da ya kammala sannan ya d'auki key d'in mota ya sauko dan ya bawa Mai gadi umarnin a wanke masa motar sa da take gidan, yana fitowa ya shiga motar aka bud'e masa gate ya fita ya nufi unguwar Zone 6.
A dai-dai wani d'an gida plat mai kyau ya tsaya tare da danna horn d'in motar tasa, mai gadin gidan lek'o yaga motar da bai sani ba sai ya kulle k'ofar ya fito, sauke glass d'in Zaid yayi ya kalli mai gadin tun kafin yayi magana yace, "Kace mata Zaid ne" ya fad'a a dak'ile yana Kawar da kansa gefe.

Cike da mamaki mai

Please Login or Register in order to submit comment