Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki wani kamshin dadi part din nata yakeyi kuma yana bude don haka nidake gaba na shigo da sallamata falon.
Ciki ciki ya amsa muna yana kwance saman doguwan kujeran falon jikinshi saye da farar jallabiya ta maza mai dogon hannu kafansa farare sun dan baiya ga gashin jikin nan nasa sun kwanta masa lub a kafafun nasa.
Ya dan dago yana amsa sallaman tare da fadin mai shiyan bata nan fa saiga hjy mum din ta shigo daga bayan mu tana fadin ki kai min wanan daki halimatu wanan kuma zainab ki aje nan in huta in bude mugani.
Mamakine ya kasheni lokaci guda ina kokarin tuno fuskansa in ba karya zanyi ba sune bakin da sukazo katsina wani lokaci har baba yai min bayanin su din nan.
Tabbas ma sune shi din ne dai dama dan hjy mum ke nan ake nufi kome ko kuma nan din ma yazone dai kamar yadda yazo muna latsina wani lokaci can lokacin bamu kai hakan ba girma.
Halimatu nikan wani suna kika kira dazunne ma ga yayan naku ina sulaiman din ta fada tana kallonshi yace cikin dan dagowa ya fita bansan inda yaje ba sai lokacin nace sannu da zuwa ya dan kalloni.
Da sauri nakai kasa ina fadin ina wuni anzo lafiya ya amsa cikin dan kura min ido kafin yace yar gidan baba garba ko ?
Itace ashe ka santa ya koma ya kwanta yana fadin wancan zuwan da mukayi katsina na santa kinsan lokacin sun dawo suna katsina tace ehh ai yanzu kam ya dawo gida ke nan .
Halima ta fito ta gaidashi itama kafin ta fice da sauri zuwa wajen Dada din dakin mu na shiga nayi sallah ban idar ba nake jin hjy mum din tana kwala min kira ni kuma ina sallah.
Saida na idar nazo na sameta ina fadin hjy sallah nakeyi kada lokaci ya shige azahar kawai nasamu nayi a can din dama zance ne ki debowa yayanku abinci ai na debo masa.
Na dan rakube ina fadin ayya sallah nakeyi bari naje gun Dada mu gaisa don zuwa yanzu hankalina ya fara komawa gida kan don ban taba tafiya nayi nisa da iyayyena da yan uwana ba sai wanan karon.
Da nazo gashi satin mu biyu muka rufe har mun zama yan gida a kano yanzu ko baba na kano ya dawo daga kasuwa baiji duriyan mu ba sai ya tambaya inasu mamana banjisu ba.
Wani lokacin idan hjy mun ne kusa dashi zata fada mai abinda muke inko hjy mah ce zata dan basar da tambayan nasa sai yasa murya ya kira wani daga cikin yayansa akiramu.
Gashi da halin arziki sai ince sukan haka zariyansu yake da alheri da kuma kula da iyalansu don duk dare baba na kano zai dawo da dan tsarababsa da za,a raba ako wani sashe nagidan.
Irinsu yought kilishi limu kaza da gadaden nama mai zafi tare da abin sha kuma sai kowa ya samu a gidan yaci bawai sai wanda yai ra,ayin bawaba kawai zai samu.
Tun shigana part din mukaci karo da wanan uwar feleken yar wurin hjy mai nuna kamar tana jin warin mutane idan aka hadu da ita din nan.
Nunani tayi da hannu tana fadin wai kece dama ban ganeki ba haka na dauka irin yan classic din nan ne ma a ina kukayi wanan gyaran hakane naga dayan ma yau ta canza sosai.
Ban iya bata amsa ba ina kokarin shigewa ga rainin wayau a na magana kina kokarin shige mutum ko ance kada ku fada munane kuma ?
Dan murmushin yake nayi mata ina fadin nikan ban dauka dani kike ba ai ku bansan wajen ba wallahi tunda ba garin na sani ba ni andai kaimu an muna hakan na shige dakin da Dada din take.
Halima na zaune tana cin abinci nace ke kuma ina can ina jiran kizo muci abinci har na idar da sallah banji ki ashe kina nan kinaci ke ban sani ba Dada tace kyale ja,ira ai na fada mata abincin ku yana can wurin uwarku dama.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[1/25, 15:44] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON ,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Alhamdullahi yan buki sun fara taruwa a gidan don iyalan baba na bauchi sun iso da na baba na zaria dake aiki a ABU zaria suma sun shigo don haka mun kara yawa a gidan.
Yinin yau aiki mukaci sosai a part din hjy mum don hakane ban samu fita inga bakin da suka iso din ba don suyan nama muka wuniyi ko ince na wuniyiwa mum din a kitchen dinta.
Wanda lokaci lokaci halimatu kan dan zagayo ta dan tayani kuma ta gudu don bata iya tsayawa ta soyashi kamar yadda nina tsaya nayi mata.
Itama mai aikin takan zagayo mu danyi tare kafin kuma ta kama wani tsabga sai wani lokaci ta lekoni don haka a wajen halimatu dake dan zagayowa nake jin komai.
Dakyat na samu nagama mun cika wani roba babba mai marfi nayi mata suyan yadda ba zai lalace mata ba wanan yasa na dade ina wahala wajen suyan yaji gishiri da maggi danake dan mirginashi kafin na soya don masuci hakana din.
Dakinta nakai roban can kurya na boye wanka nayi na dauro alwala don duk jikina ciwo yake min alaman yayi tsami a lokacin yasa na dan watsa ruwa na dauro alwala don in gabatar da sallolin dake kaina lokacin.
Bayan na idar ina wajen zaune lokàcin nake jin wata irin iska mai sanyi yana shiga jikina hakan yasa na mike na dauko mai nashafa don kada zazzabi ya kamani a lokacin.
Wani dogon rigan da anty Nafisa ta ban na saka a jikina rigan tayi min dagwas a jikina har ina mamakin yadda za,ace wanan kayan suyi mata ita tunda ta darani kiba da cika na yan mata sai kumani ga rigan yayi min daidai a jikina dana saka.
Duk da ina son hutu a lokacin amma hakana daure na nufi dayan part din wurin Dada da niyar inje can in kwanta sai kuma na samu dakin nasu da mutane.
Sallama nayi na shiga suka zubo min ido gaidasu nayi kafin suna amsawa na raba zuwa wajen Dada na zaune na manne a jikinta ta kalloni tace.
Ban sanki da raki ba badai wanan aikin da kikayi bane ya saukar maki da gajiya ko nace a,a Dada amma kamar zazzabi zazzabine ke son kamani yayin dana manna hannuna a gefen wuyana ina tabawa a hankali don naji zafib jikin nawa.
Wanan kallon banzan nasa ya watso min daga inda yake kwance saman carpet ya dan kishingide bashi ba dukkansu kallona sukayi lokaci guda.
Aiga likita kusa ki fadi abindake damun ki ya baki magani koya rubuta maki a in ma allurane duk yanzu sai a sayo ayi maki karamin ya fada yana kallon mu.
A takace nace lafiyata ai kalau kila gajiyace daice a kaina yasa nake jin hakan sai naga duk sunyi murmushi shi din dai ke fadin ashe kina da wayau yau da yarinya kinsha ihu din hannunsa akwai zafi sosai ya dan murmusa yace yaushe rabon da in maka allura kai ?
Wai wanan mugun kake zance dama ina zan bari ya makure yar mutane ya halaka masu ya yaje can dai ya samu wa yanda basu san ciwon kansu ba yayi ta zurnuka masu idan sun yarda.
Baiyi magana ba sai mikewa da yayi tsaye yana fadin kai Auwal kama min tsohuwar nan in mata allura ko bakin nan nata zai mutu jekaiwa ubanka musa dake kasuwa ko kaje kaiwa Audu ko garba kafin kazo kai mun.
Au har da zagi yau zaki fada kuwa don nayi niya babu mai hana in maki allura a gidan in ka isa ai gani gaka.
Gadan gadan yako harota saiga allura ya fito dashi daga jikinshi yace yau zamuga karshen cika baki don gaba daya saina dura maki wanan alluran a jikinki.
Ganin yadda ya nufota din yasa Dada ta dauka dagaske yakeyi tace yau zanga inda za a binne tsohuwa da ranta kuwa ya cakunata ya rike ta fara sallati tana kai mai duka tako ina tana zagi.
Tunda suka fara abin bai dago kai ya kallo inda suke ba sai kallon wayanshi da yakeyi jin hayaniyan yayi yawa ya dago yana fadin kai rabu da ita mana.
Wanan ai haukane idan kajin mata ciwofa ya zakayi hakan baisa ya sake ta ba bansan lokacin danace haba don Allah kada ka halaka muna ita mana.
Cak ya tsaya yana juyowa ya kalloni zanin Dada dake kokarin kwancewa a gabansu nayi saurin rikewa don nasan a rude take itako Dada sai dura mai ashar da takeyi ta uwa ta uba tana kira masa rashin tarbiya.
Ke ina wasa dakene ko rashin kunyan ku na yan kauye zaki kawo min a nan yanzu zan tatakaki wajen nan idan kika kara budan bakin nan naki mai wari a nan.
Badai bakina ba na fada ina kawar da kai gefe don na zuciya dashi iya makura don abinda yaiwa tsohuwar bana kai sake bane kokarin kai min mari yayi yaji an rike hannun nasa ta baya ya juyo a fusace yana fadin.
Ka sakar min hannu nayi maganin wanan karamar yar iskan haba dai meyasa kake hakane wai da wanan karamar yarinyar zaka tsaya kuma fada haka.
Sai yayiwa dan uwan wani irin kallo kafin ya kuta ya fice yabar dakin Dada tace mahaukaci sai turu kuce min ashe kara haukacewa yayi acan turai din yanzu.
Suka kwashe da dariya suna zolayan Dada din tunda ya bar dakin ban kara cewa uffan ba suma basu dadeba suka bar dakin kamar jira nake su fita na saka kuka sosai lokaci guda.
Hankalin Dada ya tashi tana fadin dama nasan za a aika hakan wanan yaron kan baisan arziki ba a rayuwansa daga maganan fatan baki gashi yanzu ya saka yar mutane kuka.
Duk lalashin da Dada tayi min hakan baisa nayi shiru ba saida ta fita can sai gasu tare da hjy mum sunshigo tana fadin kingata nan badon Allah ya gyara ba da dukanta zaiyine kome oho.
Ki taso muje part dina ta fada cikin bani umurni banki ba nabi bayanya zuwa part din ta dakin da muka sauka nayi niyar shiga amma naji tace nazo dakinta sai nabi bayanta muka shiga tare da ita.
Zama mukayi bakin gadon dagani har ta dan kura min ido na wani lokaci kafin ta soma magana ki bar kukan nan hakana mai sunan hjy nasan ba karamin abu bane yasakaki wanan kukan haka amma kinyi hakkuri don Allah.
Nasan an zaluncekine yasa kike wanan kukan amma shima ya kuru da bai kai ga taba jikin ba yau da ranshi yafi naki baci a gidan nan kuwa ta fada a cikin sanyin murya.
Ni gida nake son komawa mummy na fada ina sake barkewa da sabon kuka lokaci guda ta girgiza kai tace akan Hafiz zakice zaki koma gida yau.
Saida buki yazo gab zakice ke gida zaki tome akayi ke nan idan kin koma gida yanzu sai kace wace ba gidan ubanta tazo ba.
Nasan Hafiz baya da kunya ko sagarcine ke damunsa ohh komu mata yaushe kika tsaya shiga tsabgan mu balleshi namiji don Allah kiyi hakkuri ki daina wanan kukan haka.
Koda yake nasan bayin kansa bane iyayyensane dai basu yarda da hakan don sonsa ya rufe masu idanu basu ganin laifinsa su.
Da kyat ta samu na tsagaita kukana bankoma part din da Dada din take ba don nasan idan naje can zamu iya haduwa dashi wurin ni kuma ba zanso wata halaka kota gaisuwa ya kara hadani dashi ba kuma.
Nan nake zama wurin gwaggona inkin debe zuwa gaisuwan safe da nakeyiwa Dada din bayanshi yanzun na daina zuwa mata hira ga baki daya.
Wanda yasa Dadan ta fara korafin hakan har yakai tana biyoni part din hjy mum mu dan zauna idan tazo zakiji tace na biyo wanan matsorociyance data zama ta gudu yanzu gidan nan tana tsoron miskilin yayanta har ranan da har aka wuni ban samu lekasu ba yakai ta biyoni da yamma har part din hjy mum din.
Nan baba na kano ya dawo kasuwa akace tana wajen hjy kubura ya biyota nan din yana fadin Dada naje daki akace min ai kina nan Dada tace gani nan na biyo matsoraciyan nan Abulle ne kasan miskilin nan ya tsorata ta da shiga wajen mu tunda ya daga hannu zai mareta ranan ta daina zuwa inda nake.
Baba yana kaiwa zaune yakr fadin mari kuma Dada wa ke nan wai Hafiz wazai mara din wai tace gata nan don kawai tace mashi ya daina tsoratani shine nan ya dago hannu da niyar zai mareta saida mai sunan malam ya tareshi ya fita yana zuciyan banza don an hana ya mareta.
Aiko daya gane kurensa daya dora hannu akan jikin yarinyar nan don zan gwada mai daya suke da ita a gidan nan ita din ba bare bace a cikin gidan nan don itama mai galihuce kamar kowa a cikinsu.
Daga inda hjy mum ke zaune suna hira da Dada ta jefo baki tana fadin gara dai a tsawata mashi din don kasan halin Hafiz idan ya tashi zuciyarshi na banza bajin zancen kowa yake a gidan ba shi.
Idan ya isa ya taba ta ai gani hjy mum bata dadara ba sai cewa da tayi dashi gara dai din a tsawata mashi kansu don kada yazo ya takurawa yar mutane ko yanzu din ma a takure take wajen nan ai tunda ta daina fita ko ina sai nan part din kagako ba,ayi ba ai.
Bari zan gashi in masa kashedi akansu tace dadai yafi gaskiya ya jiyo wajena yana fadin haba uwata akanshi saiki daina fita ko ina ai nan gidan kune kema kamar ko wani da kike a gidan nan ai.
Hawaye na dinga saukewa ya tsaya ya dan lalasheni wajen kafin ya fita bansan ya sukayi ba da baba din halima daice ke fada min wai ya samu Dada yana fada ankai karashi wajen baba.
To yanzu kuwa zai saka kafan wando dani a gidan nan ke nan idan ya ganeni sai ya makeni ko a inane naja tsuki ina fadin ya kasheni idan yaso an fada mashi kowa mahaukacine irinsa ?
Washegarine kamun anty Nafisa don haka tun safe kowa yake busy a gidan duba ga yadda gidan ya kara cika sosai da mutane tako ina mutane sai zowa sukeyi na dauka part din hjy mum ba zai cika kamar na mai bukin ba sai gashi an kai ga bude sauran dakunan dake rufe a part din bakin katsina sun sauka ciki.
Don ita bangaren mai bukin yan gayu ire iren matan abokan baban kano da matan yan uwasa dake birni aka sauke a cikin part din su kuma yan gida anan wajen .
Don haka nike faman dawainiya dasu kome sukeso nice zasu kira su tambaya donko sun tambayi hjy mum zatace su nemoni don haka ko yaushe ina basy.
Dole ina kallon kowa nashiri don fita zuwa wurin kamun amma ni hakan bai samu gareni ba don ko wanka banyi ba ina faman dauko min da miko min ga mutane ga mutane da ganin iyaka.
Haka nayi ta daurewa ina komai sannu a hankali har yakai saura iyamu da hjy mum data tsaya shiryawa a lokacin sai wata da nake yawan yiwa dawainiya a dakin nata mu muka saura a part din don haka zamu rufe kafin mu dawo daga can din.
Na dauka zan samu su halima a waje amma kodana rufe kofan nafito kamar yadda hjy mum ta umurceni dayi saina samu babu kowa a wajen sai inta da wanan kawar nata a wajen.
Hayaniya gami da dariya danaji a bayana yasa na dan juya hjy mommyce tare da wasu abokanta suka fito suma a cikin shirinsu lokacin har hjy mum ta bude wani mota tashiga nan naga sunja sun tsaya cikin mamaki.
Kizo mu tafi hjy mum ta fada hakan yasa da sauri na dago kafa na samesu na bude motan nashiga ta tayar muka bar wajen wai ashe ban sani ba nan rigima sukeyi akan motocin maigidan saisu da shakikanaune suka san hakan.
Don abinda ya faru shine hjy mummy ta karbi mota daga hannun mijin datake ganin zatayi sha,anin bukin ta burge kowa a wajen har kishiyan nata tasha mamaki wajan .
Sai gashi ta fito taga hjy mum ta shiga dayan motan nasa dayafi tsada a gidan ta wuce ta barta nan gashi kuma itace ta zabi wanan dake wajenta don haka yanzu me zatace dashi kuma ?
Don bata taba zato ko tsamanin wayewan hjy mum yakai haka ba a ganinta don ita hjy mum komai nata a addinance takeyinsa bata faye irin rigingimun duniya din nan ba.
Gashi kuma tana zaunene bata kaiga ganin irin shigarta ba inda itama hjy mum din sam bataso hjy mummy din taganta a yanzu ba sai idan anje wajen ni kaina da yanzu na zamo yar koren hjy mum din ta kyashewa shigata na buje da rigan less daya fito min da suran matashiyar budurwa mai tasowa a jikina.
Wanda kalan light pink din less din yai matukar min kyau ga dinkin da ganinsa an kashe mai kudi sun min dauri dayake dan baiya kitson kaina hakan yasa hjy mommy jan guntun tsuki tana fadin.
Haukar banza wai hankaka maida dan wani naka ke nan ita ala dole ala tsiya yar nan take kokarin mayarwa nata abinda ba zai yuyuba ke nan kuwa a gidan nan ta dauko muna wata yar ta jefa muna gida don kawai kyashi da hassada mafarin duk abinda akaiwa yayana tace sai anyiwa wanan yar ke nan ko ?
Koda yake ma aikin banza idan mutum ya isa ya haifo ya macen mana mugani da ake min wai kallo adole itace mai yaya maza a gida yanzu ko ga yaya matan sun taso sun tsone idanu.
Kai hjy malka banga abin damuwa bafa wajen wanan bagidajiyan mata daba kowa yasanta bama sai yan tsiraru in fitsari banzane kaza tayi mana duk inda kika shiga dai dole akalleki a barta wani hadewa zatayi gaki a wajen.
Wanan ya karfafawa hjy mummy din gwiwa don dadata da na kut da kut dinta sukai mata saiga waya ana cewa suyi sauri an fara program din event din.
Ba can mukaje ba saida muka biya wani gida muka dauki wasu mata biyu muka koma mu uku a bayan motan kafin muka doshi wajen.
Karyan yan kano da son bidi,a wajen ya hadu da manyan da kananu kowa tana nuna halinta don bame bari a barshi baya wasu sunzo daga bangaren amarya wasu kuma daga bangaren ango haka wasu sunzone ta uwar amarya haka dai kowa da dalilin zuwanta wajen taron.
Tun shigowan mune kallo ya koma gun hjy mum din da yaranta suka sayo mata tsaraban lafaya tun daga Dubai don kawai su fidda uwarsu kunya basuji tsadansa ko kudin da zasu kashe ba a wajen sayan .
Haka nima a cikine bataji zafi ko kuashin dinka min ba don kawai yadda ta amince kuma ni din na zage ina fitar da ita nauyi da kunyan da bata zata ba a lokacin saboda kawai banso kaina ba nima.
Ance kaso kanka duniya taki ka haka kaki kanka sai duniya ta soka nako sheda wanan karin maganan don ko nagani ga halima da hjy mum din don sai tayi min abu kiri kiri tabar halimatu din.
Tun zuwan mu na sance jiki nakoma wajen su halimatun dake min wani kallon mamaki don bata sanni da wanan kayan ba gashi kuma ta ganesu a jikina.
Nan ta fara fadin kaji yan kyashan na mane da sarki banda wanan basu iya daukaka rayuwan mutum sai idan yana masu bauta ni ina zan iya wanan don ragar banza.
Duk da irin maganan ya bata min rai amma ban tsaya kulata ba saboda nasan halinta akwai kyashi da nuna hassada bata iya boye hassadanta ko ta hade kowa yasanta da wanan mugun halin.
Amsa daya nasan na bata shine ko hakan iyawane don wasu sun gwada sun kasa ko kuma hakan laifine kayiwa dan uwaka tsakani da Allah kuma yanzu ya zama laifi.
Hakana a dunkule mukai maganan hjy mum bata tashi burgeni ba sai da aka kirata tayi bayani a matsayinta na uwa irin addua da nasiha mai kashe jiki datayi ta watsowa mutane hakan sai ta burgeni har kasan zuciyata.
A haka dai taro ya watse bayan ansha bidia da sauran abubuwa a wajen tun kan a tashi ta nemoni muka dawo gida do makulin part din yana wajena.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/27, 20:17] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON ,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1️⃣0️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Mun dawo da wuri gida inda halimatu ta lake muka dawo da ita nan din ma ba zama mukayi ba don hjy mum din ta turamu makwabta mukai mata sakon hadin sinasir da zataiwa baki na karyawa da safe don hjy mum bata yarda tayi sanyi da bakin part din nata ba lokacin itama don tana iya nata kokarin gaskiya.
A hanyan dawowane kawai mukaga gari ya hade da hadari lokaci guda nakali halima nace kinga ikon Allah ko halimatu wai hadari aka shirya yanzu kuma .
Tace nima haka nagani Allah ya taimaka mun bar wajen taron nan da yaya zamuyi mu dawo gida yanzu garama ke hjy mum taje dake niko badon nayi dubaraba duba ga yadda mukaje na biyoki da bansan ya zamu kare a wancan wajen ba.
Sai ta kara daga kai ta kalli saman tana fadin da alaman amaryan nan zata shiga a sa,a irin wanan hadarin hakan inama yau za a kaita gidan miji aida ta more.
Ta more dame ruwan kome na tambayeta tace ke banson shakiyancin tambaya baki taba jin inza akai amarya akai ruwa ace tayi sa,an tafiya ba komai ?
Nikan ban taba ji ba sai yau a bakinki kuma wanan ruwan wata kila iskane kawai ke nuna alaman damana

Please Login or Register in order to submit comment