Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiru inda naga suna saka kaya a drower dakin nabude nasakasu har yar jakkar kayana na warewa halimatun nata.
Data shigo na bata takoyi murnan hakan lokacin dana bata din don ta nuna farin cikinta sosai nan muka wuni muna taya mai shiyan girki har yamma muka shiga wajen Dada.
Tana zaune saman carpet data idar da shaf,i da wutir din ranan muka shigo ta dago kai ta kallemu gaida ita na farayi da Dada mun wuni lafiya ?
Ta amsa cikin dadin rai tana fadin ai nake tambayan ku dazun uwarku take fadin kuna can kuna tayata aikine kun karasa ko na amsa da ehh Dada halimatu wuri ta samu tahaye gado ta kwanta.
Ke kam anyi mashiririciyar yarinya duk wahalan ki kin kai na yar uwarkine da suka mayar kamar boyarsu ni inkin debe Kubura sai ince duk ta bar masu ko kawarda kara a gidan nan.
A,a Dada aiko aikin ta yaja muna alheri gashi har nima da ban masu komai ba nakai ga kala ukku masu kyau da tsada kaya masu kyau ta samo muna fa da batayi ba ina zama zai samo muna wanan alherin kuma ?
Ke arr ja,iri dayi banzane ke kiyi mana ko duniya da kayan cikinta zasu bata ba kumce ba na hana wanan bakin aikin da batazo wazaiyi masu shi ?
Dada ki bar halimatu kara zugaki fa takeyi tace aina fahinta basu dai son suga bakin mutum yayi shiru ke dai yar albarka mikon min tuwo naci tun dazun nake son in bude naga me suka kawo min koda yake kuburace a kitchen din banda matsala yau da bakin cimarsu.
Mata ki zauna kiyi girkin kwarai ba zata tsaya ba yau ko wuni gidan nan marka batayi ba inama har yanzun bata dawo ba wai suna wajen hada kaya can gidan da za akai yarta.
Banda lalacewan zamani ina uwa ina zuwa kallon jerem yarta kuma kisan zamani yaci baya a yanzu kunya ya fita idon mutane ni wanan abin kunya ina zan iyashi don Allah ?
Da dane ai tana gida ta saka yarta gaba tana kara mata huduba kan zaman aure amma kaiya haka zata dunkulata ta kaita solai solai kamar rukumi da kaya sai karyan arziki kawai ina aure zaiyi karko a yanzu don Allah.
Toke Dada mu ina ruwan mu da wanan zancen ki samesu mana ki fada masu kinzo nan kin tasamu gaba kina zuga fada kamar mu zamu hanata hakan.
Ban iya fadan ne kome ta fada a hasale wanda hakan yasa na tsoma masu baki nace a,a Dada don Allah dai kyale halimatu ba komai ne zakiga sunayi kice sai kin maganta ba don Allah ki kyalesu kila haka al,adan garin yake.
Tace kuma fa yar nan shiyasa nake sonki dan halin manya iyakata ko idon don kinji dazun mara kunyar yar nan ta fara zancen nazo ina takurawa rayuwansu ai.
Ki kyalesu Dada a rabu lafiya tunda haka suke abinsu kinga sai a zauna lafiya inma tayi maganan bari zasuyi halan wahal da kanta kawai zatayi.
Waini kike fadawa hakan to kaf dunsu gidan suyi kadan duk iya shegensu kyalesu nakeyi bani hauhuwan da wata tazo daga baya ta nuna min iko a kansa.
Mikewa nayi na dauko kayan abincin na dire a gabanta ina budewa kamshin man shanu ya bure dakin lokaci guda jin hakan yasa ta kallo miyan tana kura mai idanu.
Tuwon shimkafene miyar kuka da tantakwashi yaji kayan yaji gwanin ban sha,awa sai kamshi ke tashi na kara jawo plate gabanta ina fadin Dada biyo za a bude maki ?
Fara bude min gudan ta fada tana shafa wai addua a jikinta bayan ta gama yanka masifa yanzu na ba gaira ba dalili kan abinda bai shafota ba a daidai lokacin kuma wanan hjy ta shigo dakin.
Tan fadin hjy kin ganmu sai yanzu yau tun safe dana fita ban samu kaina ba mutanene yanzu basu sa gaskiya ko kadan mun bashi kudin kayan nan da dadewa sai jiya da mukaje kwasa yake son ya kawo muna wani zance kuma.
Sannu da zuwa mama na fada tare da gaida ita ta da mika hannu tana fadin yauwa yan matan hjy kuna nan kuna fama da rigiman tsohuwa ko ?
Ta kalli abuncin tana fadin yauwa ankawo maki abinci ko dama na damu wallahi na barku tun safe to ai dadin mutum biyu din ke nan a gida in guda bata nan daya na nan sai kiga gida ya rayu yadda akeso.
Jin hakan batace komai ba sai cewa da tayi ke Nafisa yau tana ta yabon ki kin mata aiki sosai kun shirya kayata nikan ina naga lokacin wanan yanzu.
Muryan babane shima ya shigo dakin nan muka zube muna gaidashi din har halima dake saman gadon ta sauko yake fadin ashe kina nan kina cin abinci yanzu nake maganan ki shigowa na kenan daga kasuwa.
An dawo lafiya ko Allah yayi albarka abinda ake nema Allah ya baku ya amsa da amin lokacin hjy ta juya tabar dakin ya kai zaune gefen gado ganin hakan yasa da sauri namike zan fice daga dakin.
Muryanshi naji yana dakatar dani ta hanyar fadin dawo ki zauna abinki ina kuma zaki mamana ba a binci zakuci bane ?
Dada tace wanan nawane nasu nacan gun uwarsu ai aini kubura ta kyauta min datayi min tuwon nan amma wanan hanjin da matarka ta dinga tura min kwana biyu ai saiya kaini asibiti ba shiri.
Kallon juna mukayi da halima muna kumshe dariyan mu ya dade a dakin yanawa mahaifiyarshi bayani kan bukin anan muke jin cewa ai mai mata zata aura ashe .
Da sauri Dada din tace aikaji ita kuma gun mai mata ta kare sunki auren hadi da zuria suka gada tun iyayye da kakani a nan kuma yanzu ta fada.
Aina fada mata tun farko daga ita harshi babangida din tunda sunki hadin da mukai masu yanzu banda korafi daga baya sai Dada din tace Allah dai ya gyara kundai bi ra,ayin diyanku kada ransu ya baci a nan .
Amma banzaci hakan ba gareku don ban taba tunanen wanan zamanin zaizo ya sameni da raina ba Allah ya gyara yace ya dan dukar dakai.
Muma dakin shiru mukayi kamar ruwa yaci kafin Dada tace dashi jeka huta da iyalin ka Allah ya bamu alheri ya mike da kyar da alaman wanan maganan ya dan tabashi lokacin.
Yana fita nace ci abincin Dada kar yayi sanyi tace to yar nan ke dai ta jawo abincin ta faraci halimace son jan magana ta sauko daga saman gadon zuwa kwabon abincin Dada ta tsami nama daya ta mike da sauri tana dariya.
Dada din tace ja,ira baki jin bakina tunda mai kaunata ta hanani yawan magana nace haka shine daidai ai Dada dinga sawa kowa ido wata rana zasu tunaki.
Ashe gaskiyane wasu yaran zuciyan manya ake dora masu ashekarun nan naki kike wanan maganan tankar yar shekara hamsin gareni Abbulle gaskiya ba karamin tarbiya da hangen nesa iyayyanki suka baku ba .
Da duk uwan zamaninan zasu diga lurar da diyansu alkibilan alheri da har yanzu duniya tana kwance tana barci yadda aka santa a baya amma kayya a yanzu mun aro wani akida mun yafawa kan mu na bata da sunan boko.
Naman ta dauko ta miko min na girgiza kai ina fadin a,a muma ansaka muna munci Dada wanan rabonkine ai wanda naci ma gashi ya lake min a hakori yana damuna yanzu.
Yarinya mai dabara karna matsa maki ki karba kikace hakan sai na dukar da kai ina dariya adaidai lokacin wanan karamar tasu data dan girme muna tashigo dakin babu ko sallama da waya makale a kunnenta tana fadin gani dakin ai nashigo.
Duk muka bita da kallo cikin mamaki wanan shigowan nata haka babu ko sallama itako sai cewa da tayi ehh gata zaune ai OK sai kawai ta miko min wayan dake hannuta din.
Ban karba ba sai dago kai da nayi na kalleta a cikin mamaki kafin na mika hannu na karbi wayan daga hannunta bayan tace a cikin tsawa ki karba mana sisterce ke son magana dake.
Na karba na kara a kunne na naji tana fadin sister ki shiga dakina cikin wanan jakkar da muka saka less din nan wanda nace zankai dinki ki dauko min gani kofan gida ki kawo min amma ki sak a leda fa.
Nace to anty ina mikewa namikawa mai waya abinta naji Dada na fadin wane kuma nace amaryance ke magana tace na dauko mata wasu kaya a dakintane.
Shine wanan ta shigo muna daki haka kimkau kamar me shaga coci bako sallama kina faman wani guntaci kamar gaban baya.
Wai dani kike Dada ta juyo tana fadan hakan baisa ta tsaya ba ta fice daga dakin kai tsaye nabi bayanta nima zuwa dakin Nafisa din inda ta aikeni .
Zakice ba dakin da muka gyara dazun bane yana kamshi kan dakin amma ga kayan da tayi amfani dasu a wanan yinin ta cire watse a dakin ko ina nayi mamakin hakan taya mutum zai debe tufafin amfanin shi ya watsar kuma ?
Nidai na dauko abinda tace din nafito bayan na dauki wani leda danagani saman kujera na saka aciki har na dan gwauta dakin sai kuma wani zuciya ya ban shawaran nasawa dakin key don kare mutuncina a gidan.
Hakan nayi nasameta a wajen saidai ban ganta wajen ba nan na tsaya dan dube dube ina neman inda take din naga an sako min wutan mota anyi horn saina doshi wajen don ina ganin yadda yan mata ke hira a mota unguwar mu don haka yanzu nasan wanan don tun ina mamakin hakan har na dmotar.
Dan nisa dasu na tsaya kadan sai naga an sauke glass din motan muryanta naji tana fadin ya kika tsaya can kuma miko min mana ta fada daga cikin motar.
Hakan yasa nataka zuwa bakin motar ina mika mata cikin ladabi kallo daya nayi masu na kawar da idona don yadda suke zaune din a motar ban taba ganin wasu mahaluki a hakan ba.
Yauwa yar kanwata shi kika dauko ko nace ehh anty ki duba ki gani ko shi din ne tana kokarin bude ledan yayin da kamshin su duk ya cika min hancina a wajen.
Muryan mutumin naji yana fadin wanance bakuwar bakatsiniyar tamu ashema yarinyace karama haka take da kwazon manya amaryata ta fada min kin mata aiki sosai yau dole in maki wani abu nima.
Yana kokarin tura hannunshi daya cire cikin jikinta cikin aljihunshi ya ciro kudi dabai tsaya kirgawa ba yan dari biyar biyar ya miko minsu yana fadin ai tunda kikeson matana nima ina sonki dole na yabawa kwazom ki.
Kallon kudin da yake miko min nayi na girgiza kai alaman a,a yace dakyau bakatsiniya kunya gareku badai tsoro ba ki karba aike kanwar muce ko nayi maki kama da dan yankan kaine da ba zaki karbi kudina ba ?
A,a wallahi aikai yayanane yanzu don nayi maku abinda kukaji dadi basai kun bani kudi ba to ki karba wanan kyautane tsakanina dake ai na dan kalli anty Nafisa din tace don Allah karba ki tafi kawai saina shigo.
Na mika hannu na karba ina fadin nagode najuya da sauri zuwa cikin gida do na fahinci bata jin dadin tsayina wajen yasa nasa kai nashige da sauri ciki.
Ganin halima ban fadawa kowa komai ba sai na cusa kudin cikin jikina saboda nasan halin halimatu din saida ta dan kauce nake fadawa Dada nace amma tace saita shigo zan aje harta shigo din in bata.
Don su ba,a shige masu gaba amma don mai nemanka yaba kaninka kudi shine kuma zaka karba inba komawa baya ba su basu gudun abin kunya dama ai waisu idonsu ya bude yanzu.


Yar uwa kiyi hakkuri da rubutuna yadda kikeso din ba haka tsarina yake ba idan zaki karanta ki karanta sabodake ba zanje lahira inkasa amsa tambayan da za ai mun kan rubutun nan ba.
Akwai masu rubuta rommatic novel saiki nema ki karanta hakan ba laifi bane novel dina yana tafiya bisa ga yadda rayuwan mu kan kasancene a tallakance don babu karyan arziki ko karyan al,ada aciki saidai idan na rubuta bisa kuskure don haka kiyi hakkuri ki barni hakan.
Saukin abin masoyana suna fahintar hausana da kuma sakona wanda nasan dole cikin kashi dari kashi biyar suna amfana da rubutu na don haka donke kadai kince wani abu bazai dameni ba haka tsarin rubutuna yake masu hankali ke gane sakona garesu koda yaushe.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[1/22, 09:09] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Buki kan ya soma don zance tun zuwan mu dai masu gidan basu zauna ba sukan inka debe hjy mum dake dan harkokin ta itama don shirin bukin don muna nan aka canza masu set din part dinsu dag daki har falo komai iri daya kalane kawai bambancin kayan.
Koshi saida hakan ya dan kawo rikici a tsakaninsu donko hjy malka tace kalan data zaba ke nan tun shego don me hjy mum zata daukeshi.
Ita kuma hjy mum tace ai bata san itace ta sayo masu kayan ba dama sai yanzu data fada in haka ba za a bari matsayin ta na babba ta dauka ba saidai baba ya bar kayansa.
Nan rikici sosai ya tashi saida Dada ta fito ta tsawata masu a cikin fushi tace ke marka ban gane me kike nufi ba a nan shin ba shigowa kikayi gidan nan kika samu Kubura ba.
Ko har kin mantane wai in tuna maki don ni komai yana cikin kaina kamar yanzu akayishi kada ki mayar da mutane wasu bican don kawai shi ya zama shasha kuna juyashi keda diyan ki yadda kuke so.
Tirkashi ranan kan naga fadan manya ba dadi don idan kana kusa kunnene kan girmi kaka duk da muna daki hakan bai hana miji komai dake wakana ba wajen.
Shi ya dawo daga kasuwa ya kashe wanan wutan daya hada inda yace don ya bata kudi ai basuyi za,a sayo wa yanda kalansu ya bambanta ba tun shago kudin komai iri daya ya basu don haka ta bari hjy kubura da itace babba ta fara zaba.
Dole ta dauki kalan milk din ita kuma hjy mum ta dauki ash color din aka zauna lafiya yan company suka jera masu kayan aka fitar da wanda muka sama akai sauyin su zuwa wasu dakunan.
Don haka wuni cur mukayi muna wanan aikin na gyaran part din duk da son jikin halkmatu ranan saida ta amfana ga aikin itama aka rutsa da ita.
Don bayan mungama na hjy mum kamar yadda mukaji yan gidan nakiranta muma muka kama nabar gwaggon da nake fadi da farko don ko nace gwaggo sai su kama min dariya kawai.
Wanan yasa nabar kiranta da gwaggo din nakama hhy mum yadda kowa ke fadi a gidan a yadda ta rikemu dole na mayar da hankali kanta yanzun ma na rage shigowa wajen Dada idan ba aiki muka rarage a part dinta din.
Bata da yawan magana haka mukan zauna zugun sai in akwai wuta ta kuna muna kallo wanda kallon ma dai wa,azine su tafi kamowa sai idan zata shige zata kai muna tashan da ake film mu kalla.
Zaune muke mun zubawa tv ido ana wa,azi akan sallah nan kan bamu da laifi gaskiya duk mu muna tsare sallah saudai kara fahintar hakki akan sallah din da yanzu muke sauraro a tashan da malamin keyi.
Talla sukaje irin na gidajen talabijin lokacin ta dan nisa tace damu yakamata gobe na kaiku wajen gyaran kai a wanke maku kai kuyi kitso har kumshi don idan sun fara shagalin bukin nan baku da lokacin hakan .
Daga inda nake kwance na amsa da to tace kawunan ku yana son kitso koba duk sati kuke kitso bane budan ba halimatu sai cewa tayi sai zainab ba ita da mamanta ta iya kitso duk sati take masu.
Kefa hjy ta tambaya cikin kallonta tace nikan gaskiya yana kai sati uku huduma banyi kitso ba ta fada tana dariya tace jam kina diya mace kike barin kanki babu gyara haka ko baku san kun girma bane wai ?
Muka kalli juna nida halima din tace kunyi sa,a kunzo lokacin kakanin mu sun mutu aida suna nan da yanzu ko wacen ku tana gidan mijinta tana aure.
Indai yadda nasan akidar gidan mune na da komu dai primary aka barmu mukayi zamana ikko ne nasamu har nayi secondary a can din ina batun shiga jami,ane Allah ya karbi ran mijina lokacin.
Zakice sa,arta muke wani lokaci idan mun zauna muna hira da ita amma saboda cika idonta a fuskan mu bamu iya sakewa da ita muna zance haka dan dama ma halimatu don ko lokacin itace tayi magana.
Tace haka Dada ta fada muna Allah ya jikansa ta amsa da amin nima na kara fada tare da dorawa da Allah yasa ya huta aljanna makoma a garesa tace amin .
Ban taba tunanem zan kara aure ba a lokacin amma abu ga mai magabata ban jimaba suka kara hadamu aure kuma da babanku nan ashe rabon yayan nan ne dama sai bata karasa ba yadda bahaushe kan fada din suce ya kashe shi.
Hjy mum ina suke ne wai bangansu ba mana Dada tace muna kuma kina da yara ai tace suna waje suna karatune dukkansu naso ko karamin abar min nan Alh yaki ya turaahi madina karatu .
Tunda ya tafishi har yau ko hutu baizo bama shiyasa yanzu aida nasameku nake jin kamar kada ku tafi wallahi don kuna debe min kewan kadaici sosai wanan zuwan naku.
Sai lokacin nayi magana nace wai mukan ai mun kusa komawa school ma hutun mu ya kusa karewa kai mai sunan hjy har ina cewa zanwa babanki magana ya bar min ke nan mu zauna tare.
Da sauri nace wai innata bata yarda ai shima baba nasan bai taba yarda da hakan wallahi bai yarda halimatu ta fada a karshe tace ranan fa da Dada tace ya bari ki dawo nan da kwana wajenta cewa yayi ai Dada tayi hakkuri.
Duban baya fakon biri sai meshi don Allah Dada tayi hakkuri ta barki a gaban innanku zaifi tunda kina shigowa ai ko wani lokaci.
Ninayi mamakima daya yarda kikazo din nan wallahi koda Dada ke fadin ai dake za,azo wallahi ban yarda ba saida kika fada min da bakinki cewa tare dake zamuzo.
Dariyan hjy mum din yasa muka kallota don bamu fahinci me takewa dariya a cikin zancen ba tagane me muke nufi tace shi yaya garba din yace DUba min baya fakon biri ?
Hakafa yacewa Dada lokacin nakasa fassara wanan maganan nidai na rike kalman kawai a bakina lokacin amma bansan ma,anarsa ba.
Aiba wani abu hakan ke nufi ba duba ga zamanin nan da yara basuji suma mutane baka yarda dasu abu a hannunka shine yake abinka ba,a hannun wani ba.
Irin hakan da mukan dan zauna tana sake muna fuska yasa muke jin dadi yanzu a gidan bamu ko zancen Dada da sai wani lokaci ma ta kekomu ta samemu zaune ko muna aiki.
Washegari din kuwa kamar yadda tace acan muka wuni wurin gyaran kai da kumshi dama ba dabi,ata bace karin gashi don Allah ya hore min suma har gadon bayata da acema ina saka mashi mai da ya sauko min sosai a baya amma kaina yana da santsi don haka shagon mai ya huta dani.
Da gashin kaina aka tsantsara min kitson bare bari mai kyau ga wani kamshi dadi na gargajiya mai dadi na tashi a kawunan namu da halimatu dai suka kwasa don tace ita sai ankara mata oulu a kai.
Su kuma masu wajen sukace hjy batace ai muna kari ba hakan yasa tayi fushi amma da aka gama kuma sai ta koma murna don sun iya kitso da kumshi kamar tsiya a wajen nasu na bare bari.
Hjy mum din tazo ta kwashw mu cikin motarta ni sai kallonta nakeyi ina mamaki don ban taba zaton ko tsamanin ta iya mota ba har tanada shima ashe saida naga ta fito da key munje mun sallami Dada mun fito ta danna key motar tayi kara tun kan mukai waje motar.
Yanzu ma din da yamma kuma itace tazo ta kwashemu komawa gida muna faman raba ido ba gida muka nufa gun tella mukaje ya dubamu bai auna muba ya dai ganmu kawai ya tambayi sunan mu ya danyi rubutu a wani littafi muka fito zuwa gida.
Mun kamo hanya gidane sai lokacin tayi magana don tunda ta dauko mu kamar ranta yana a bace don yanayinta daya nuna hakan har kana iya ganewa tace.
Zaku koma ku samu munyi baki fa don su Addal sun dawo dazun da safe bayan fitar ku duk da nima bansan da zuwansu ba sai ganinsu kawai nayi daga sama kamar anjefosu.
Sai ranan na yarda da damuwa nasa babba ya maida yaron dake yawan zama kusa dashi kamar sa,ansa ko amininsa don yadda hjy mum din ke fada muna magana lokacin.
Da farko halimatuce tace hjy mum wai Addle kuma tace ba Addale yake ba Addal don yana da sunan baba malam ne mahaifinsu babanku muke kiransa da Addal.
Sunan nake maimaitawa a zuciyana na rike sosai can tace akwai dai Allah yanzu don Allah ace an min adalci ke nan duk yaran mamanku malka ankosusu don bukin nan amma ni don son kai dan karamin akawo min shi na ganshi babanku yaki hakan don kuntatawa kawai.
A,a,a gaskiya ba,a kyauta ba kan na kallo halima din kafin ta zake nace hjy mum don Allah kiyi hakkuri Allah yasa rashin zuwansu shine alheri su kuma da sukazo Allah ya tsare ya kare ya mayar dasu lafiya tace Amin zainab naji dadin wanan maganan taki sosai wallahi kuma naji zuciyana tayi min sanyi sosai da wanan kalamin naki yanzu.
Nace wani lokaci ai mummy zamuga abu muna sonshi amma kuma hakan ba alheri bane tace kwarai tana nisawa zakice wata sa,armuce a lokacin tayi shiru bata kara magana ba har muka shiga gidan nasu tayi packing a inda ta dauki motar da safe.
Muka fito zuwa ciki dauke da wasu kaya data miko muna da zamu fito motan nan muka shige

Please Login or Register in order to submit comment