Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dan jima kafin ta dawo dauke da jakkunan kayan namu data dauko muna saida ta aje take fadin.
Anya ba gida zamu koma ba kuwa zainab don naji Dada na fadin kada mu yamutsa kayan mu tafiya zamuyi yau din nan ina ganin wani abu ya faru jiya bayan mu yadda naga ran Dada abace dana shiga.
Inma gida zamu koma zanfi son hakan ai halimatu don ni sam yanzu kanon ya fice mun a raina danazo kuma sai naga ta kalleni tana dariya kafin tace dani kuma dai ?
Yanzu har kano din ya fice maki a raine kuma daga zuwan mu na dan bata rai kafin nace gidanne sai a hankali halima tunda naji me wa yan can sukace daku jiya ai.
Kedai bari ga wanan ita babu ruwanta sai haba haba da takeyi damu a nan wanka ta shiga kafin ta fito na mike na gyara gadon har daki ta fito tana santin bandakin kafin kuma ta fara zancen man shafi na nuna mata wanda na shafa ta dauka tana wani dubawa kafin tace.
Nifa irin mayukan nan ban faye son shafasu ba nafi ganewa ainihin vessiline dina in shafa yafi kama jiki nayi murmushi na mike na bude jakata na dauko mata wanda take son shafawa din na mika mata.
Kuje ku gaida mutanen gidan muryan mai shiyan ke fada muna hak daga koda muka amsa da to lokacin halima tagama shiri muka nufi part din don ita tasan hanya niko shiga banyi ba tun zuwan mu din.
Ina kallon part din baida bambamcin tsari dana wanda muka kwana iya bambancin kayan alatune kawai da wanan yafi wacan dashi kuma ba gyara gasu duk sunyi kura a jiye wajen da suke.
A haka har muka kai daki da Dada ke ciki mukayi sallama muka shiga Dada din na zaune ita kadai a dakin muka gaida ita take tambayan jikina nace da sauki.
Dan shiru ya biyo baya wanda hakan zai nuna maka cewa bata cikin yanayin dadi a lokacin can ta dago tana fadin kuyi hakkuri baku karya ba har yanzu ko ?
Halimatuce tace tun wani shekara Dada mukan munsha koko da shayi har da fanke tun dazun mun kumayi wanka kafin mu fito.
Ai kaji kaji abin su wa yan nan suna nan sunata faman barci kamar masu barcin mutuwa wai sai yanzune suka tashi ake neman abin karyawa din.
Duba min don Allah wai har tana fada don me zakuje wajen kubura ku kwana baku tsaya a nan ba ko in kun tsaya uban wa zasu baku yanzu da kun kwana nan din ?
Ai har fada tayi dama kan hakan Dada halimatu ta tambaya sai Dada din tayi mata wani irin kallo mai kama da ina ruwanki taja bakinta tayi shiru ni dai ina gefe zaune ina raba ido kafin in mike ina fadin bari na gyara maki dakin Dada.
Ban jira tace ba na mike na hau gyaran daki sai gani har dogon corridor dinsu har falonsu har suka sameni muna gaisawa ba laifi don banga komai ga yaran matan ba saidai uwar.
Da dakyar ta amsa gaisuwan nawa ta wuce saida nayiwa komai kal saboda sabon zama da tsabta har ita babban Nafisa take fadin.
Kece kika gyara wurin nan haka na dago cikin gajiya ina gyada mata kai da sauri naji tace a zozozo don Allah idan kin gama sister kin huta kizo mu shirya dake kinji gaskiya kin burgeni.
Ban zauna ba tsakani da Allah da zuciya daya kamar yadda uwata tayi min tarbiya haka na gyara masu muhalinsu ya koma yana sheki tas don dole hjyr nan tazo har dakin Dada muna zaune halima nawa Dada dariya abin karin data kasaci .
Don doyace aka soya busai busai sai taliya aka kawo mata tace ba zataci ba ita kan cikinta ya baci don haka mu muci nace nikan na koshi halimatuma tace itama a koshe take sai ga hjy din tashigo tana fadin.
Sannu yar nan kece ke kadai kikai wanan aikin haka har ina batun nayo hayan ma,aikata wallahi su gyara min wajen sai gashi karamar yarinya haka tazo ta gyara min shi tasa Allah yayiwa rayuwa albarka.
Dadace ta amsa da amin aishi da na kowane don baka san inda zakaci alherinsa ba abinda uwarta ta koyar dasu ke nan ita kan bata kyataci diyanta ba wallahi don ko yaushe zaki shiga gidansu sune a tsaye har kananun kannenta zaki samu suna dan aikace aikacesu a cikin gida.
Yasa ko ko yaushe gidan nasu ko abinka ya fadi kasa zaki iya dauka kici do tsabta karyane kije gidan maryama kice kinga kazanta a gidansu.
Wayancewa hjyn tayi kamar bata san gugan zanan da Dada ke mata ba tace ai kinga ta huta gashi yarta ta nuna hakan ai yanzu .
Fitan hjy nima na mike nace ina zuwa halima nabar Dada na fadin sakarai kin zauna don son kai kin lalata kanki da yayan ki kuma ki hana ayi magana kina takama da bin bokaye sakarai kawai.
Part din nan na koma jug din da ak zuba muna kunnu na daukowa dada da sauran fanke na zubo a leda tayi damke muka hade da hjy sai na dan rude guilty,conscious ya kamani nake fadin .
Dama Dada ce bata iya cin doyan da aka kai mata ba da taliya shine na dauko mata kunnun nan tace a,a shine baki fada min ba aje wanan din bari na baki me zafi ki kai mata yar gidan Dada.
Wani dan flask ta kawo tare da dan kulanshi ta mika min na fita dashi na kai mata na dire a gabanta saiga tsohuwa ta shiga saka min albarka a take tana fada tana zukan kunu hadi da fanke ta shanye kofin kokon ga baki daya.
Banje gaiyatan da anty Nafisa din tayi min ba a ranan don ko ana azahar na mike na koma wajen hjy inda muka kwana wace nake kira da gwaggo a lokacin gyare gyare nayi mata sai gani har kitchen dinta ashe kowa nada kitchen dinsa a part dinshi.
Nan ma na gyara mata shi tas sai magariba lis na samu kaina a gajiye na koma wajen su Dada ta kalleni tana tambayana ina kika shigane kin gane uwarki kina can ko ?
Nace gyara nayi mata shiyasa na dade kin huta nace ke kan kin huta da Allah bai sako maki son jikin banzan nan na yayan zamanin nan ba uwarku ta hutar daku wallahi.
Meye cikin son jiki da lakacin matan zamanin nan banda zancen banza aiko gashi aure baikai ko ina ba zakiji ya mutu don lalaci da son jiki mace ko yaushe tana makake da waya tana dariya a daki kamar me hira da aljannu ita kadai.
Koke yanzu sai kiji dadin jikin ki ba zancen dibgewa a gareki sai kaji ka tashi wasai washegari don ka motsa jikinka ka hana wani cuta samun wajen da zai makele maka a jiki har yai maka illa.
Aiga wanan sakaran da bata da wayau kwance ta wuni tana lalaci anan ko dan kara bata iya nunawa ba dai ta tashi ta biki kuyisa a tare dai itama ta samu wanan albarkan da ake saka maki a,a ta saba da kwanciyan lalaci tana bin gado .
A hakane har wai kike da saurayi hakan zai aureki ko shara baki iya ba balle ki masa abincin kullun ina maku kwantace da halin yarinyar nan amma kunki wai ku gata tana zagin halimatu dake kwance saman gadon.
To aini bata fada min inzo muyi bane hakimatun ta bata amsa daga inda take Dada ta tare da fadin ke arr ita waya fada mata ta tashi tayi niko ubanki dake gida zaune.
Haba Dada har da zagan muna uba dai kan wanan maganan na fada ina zama gefen halimatu din itako cewa tayi ai kinsan dada idan bata zagi uban mutum ba bata huce haushinta akan mutum.
Nikan bam aikin banza ga mutanen da basu san darajanka ba su daukeka dan kauye ko nakasashe na kasa dasu tunda ina da uwata da ubana wallahi banyi haka kawai in karar da karfina ga banza saboda su.
Dada na fadin kinji ko kinji girman kai irin na dan arewa kaiba kowan kowa ba tusan galadima amma ka dauki girman kai ka dorawa kanka don fadin anta.
Yayin da ni kuma nake fadin ayya halimatu gidan uban mune fa idan mun masu abu shine ragewa ko kasawa innan mu kance mu kyautatawa duk wanda ya tsofe muna idan yana bukatan taimakon da mukafi karfinsa ta hanyar bada karfin mu tunda bamu da abin basa sai hakan ya zamo muna alheri a karshe.
Innan ku kukace Abu inan ku ai ta dabance don ta tarbiyantu ta kuma baku tarbiyan kuma don ta fadi hakan ai ba abin mamaki bane idan kunyi hakan.
Kawai sai jin sheshekan kukan halimatu din mukaji hakan yasa na juya da sauri cikin mamaki din ban taba zaton zataiwa kalamin Dada kuka ba don a kullun haka suke cikin rigima da juna wai a cikin itace mai daman yar uwartama da muka bari a gida sunfi kwasan rigima da Dada din donshi tace bata zuwa sai yan gida zasuzo ta biyosu don halin Dada din.
Haba keko don Allah meye haka kuma azo a samu daga zuwan mu kinawa Dada kuka haka na fada cikin jiyowa ina taba mata kafa jin hakan yasa ta dan rage sautin kukanta tana fadin.
Ke bakiji zagin ta take min bane tana nufin uwatce bata da tarbiya bata bamu ba daga can kuwa Dada tace na fada tana dashi din ne ta baki ko me ?
Fadan nasu dariya ya bani don inda sabo a yanzu na saba ganin fadansu fiye da hakan ma tun agida kuma nan da nan su shirya nace kai amma halimatu akwaiki da wani zance kema.
Yanzu aiba a hannun umma kike ba a hannunta kike inma batacine ita ta bataki ai da zaki tsaya zuciya haka tace ai bata ganin laifinta saina umma ko yaushe.
Dada tace nace uwarki nakara fadan uwarki din ke kuma kodana daukota ta dawo wajena aida hakoranta tab a baki na daukota nace kwantas tsohuwa kada fadan ya koma nawa kuma kingani Dada bata da gwani a wajenta nima gashi tana shirin sauke min nawa yanzu.
Shigowan wanan amaryan dakin yasa mukai shiru banda Dada dake masifa ta kalli Dada din tace ke kuma waya tabaki kike masifa budan bakinta sai cewa tayi ai dole in masifa yarinyar banza zata raina min wayau.
Ku halan baku san halin Dada bace kuke biye mata kunsan fa kishiyoyinta basu nan yanzu ku zata mayarwa da kishin kuyi ta fada da ita ko bakuji labarinta ba lokacin mijinsu malam yana raye.
Labarin arziki ba nikan lafiya muka rabu da yan uwana ki tambaya ki kara bamuyi irin wanan bakin kishin zamanin nan na iyayyen ku ba.
To nikan bari in fita kafin a sake min layi nawa ya sameni ta fada tana juyowa wajen Dada din ta kallo inda nake tace sister banganki ba kuma nace ehh anty na bari nagamawa su mamane sai gobe da safe idan Allah ya kaimu sai nazo na gyara maki hankali kwance.
Tace hakan ma yafi ko kinzo kin samu ina kwance ki kwankwasa min zan tashi na bude maki tunda nasan da zance daga can mukaji muryan Dada na fadin sannu kwamishiniya watau ma kinsan da zancen ko daba zaki bude kofan ba ke nan.
Wanan kam anyi yarinyar kawai a wajen nan sister don Allah kada ki manta kinji nace to anty tafice tana dariya muka bita da kallo dada na fadin haka za a gidan mijin solai solai ba asan komai ba sai daukin ayi aure ake fadi a baki.
Wai dama itace zatayi auren na fada cikin tambaya lokacin Dada din ta mayar da kallonta gareni tana fadin itace mana ba ita bace babban yar ita marka duk haihuwan marka din ai matane sai dan namijin na biyu sauran duk mata gashi a karshen nan ta sake namiji shi kuma gashi ta sake masa ya taso wani sakarai dashi haka.
To Allah ya shiryamu baki daya na fada tace amin ai zaki sanshi ba kwanaki sunje can inda nake ba da sukazo mukai ta kwasan rigima dashi dan kawai.
Tsofi kan akwaisu da zagi gaskiya komai kayi zagine wajensu nake fada a zuciyana muryantane take fadin ai kinsan ita kubura mijinta na farko rasuwa yayi yayi hatsarin mota hanyar iko ya mutu.
Shine data gama wanka wanan baban naku dama gasu yan uwa gasu abokai saiya mayar da ita dakinshi don dan lokacin yana da mata daya suka zama su biyu.
To shigowan wanan marka din gidan yasa har ya rabu da ita ta farkon yar makwabtan muce can katsina ita dai kuburah dince data zamo ta gida ba yadda zatayi dole ta barta har aka kai yanzu ciki ba dadi ga zaman nasu.
Shiyasa jiyan nan naci mata mutunci iya son raina dama ina da cikinta tun kan abinda tayiwa mai sunan malam yaro marayan Allah kice ba a taimaka masa don son rai irin na marka.
Mukan ba zancen mu bane don haka ban tsuka ba saima halimatu da naji tace dani aida gani sai tayi izzan tsiya dama bakiga yadda take kallon mutane a hankade ba.
Ni hakan yasa ko zuwa sukayi katsina bani shiga gidansu idan basun shigo gidan Dada sun rutsa dani ba in gaida su kowa na complain akanta gashi ance tana da saurin dafawa mutum sata idan yaje wajensu.
Nace me ?
Halimatu shine baki fada min in kama kaina ba naje ina gyara masu waje tace karanbanin ki na tsiya zainabu nifa nan kingani duk wani zancen Dada baisa inyiwa kowa aiki.
To shine me ko zaki hanata ita da takeyi samun albarkane komai tsiyan marka da iskanci ba zatacw yan nan tayi mata sata badai ko har meta aje da zai tsonewa Abulle rai takai ga tabawa ban ga wanan abin ba gidan nan.
Ni ban hanata ba ai ta fada tana murguda baki ta kawar da kanta gefe daya nace a raina in ma bata hanani ba ni zan hana kaina ai bandai tsunka ba balle nawa ya sameni a wajen Dada.
Saiga hjyn da muke dakinta tayi sallama ta shigowa Dada da abinci har kasa takai ta gurfana tana fadin ga abinci hjy tace sannu yar albarka har kin hada girki.
Ta danyi murmushi tana fadin tare da yata mukayi hjy ashe yar nan ta iya aikine haka itafa ta tuka min tuwon nan kwasan ledane kawai na karba nayi don da alama bata iyasa ba.
Dada ta karbe da fadin saina kwano kwaso zube da muka iya mukan shita saba dashi a can ba ruwan mu da cin tuwo a leda kamar yarbawa donsu muka sani da da kwasan tuwon leda idan suna buki.
Sai gashi yanzu kuma yaran mu kun iya wanan tabi,an nasu har makun darasu hjy idan ka kwashe a ledan ne yafi kyau da kuma karko amma a kwano sai yayi saurin lakacewa yayi sanyi nan take kuma.
Ayyo haka zancen yaje ashe Dada ta fada tace ku kuka gane hakan mukan bamu sani ba shiko mukai taba mahaifanku kuma basu korafi.
Cigaban zamanine hakan hjy yanzu kan idan mace na wancan kwasan naku saima a dauketa kazama a nan jin hakan yasa na dan dago kai na kalleta kadan na sada kan nawa kasa.
Ta kallomu tace yan matan Dada ko a kawo maku naku nan da sauri nace gwaggo bari nazo na daukar muna na fada ina mikewa tsaye da sauri nabita na karbo muna abincin.
Wanda zamuci har mu rage sabanin wanda hjyn su Nafisa ta kawo muna shimkafa da wake da salat sama wanda dada bataci ba wanan din yanzu taci sosai har wanda muka raga tana fadin a je zatayi saura dashi da safe ta karya.
A nan part din kuwa taliya suka sulala shine abincin darensu wai tunda baba ba a bangaresu yake ba ranan shi zasuci su kwanta hakana.
Ranan sunsha tsina wajen Dada yafi cikon kwando don sai fadin take saboda lalaci ga abinci amma saboda kyiuya mace bata iya tsayawa ta girka don lalaci.
Karfe tara mukaiwa Dada sallama zamu kwanta take fadin har zaku barni jifa Dadan nan kamar bake bace kika ishemu da fada tun dazun yanzu kuma munce zamu kwanta kin koma fadin har zamu tafi.
Koda muka shigo part din yana rufe amma muna murdawa ya bude muka shiga ashe mai part din tana falo wajen maigidan a lokacin.
Sai muna batun mu kwantane mukaji muryanta tana fadin har kunshigo sannunku da dawowa nayi mamakin jin hakan a bakin babban mace kamarta saidai dana tuna hali kowa da nasane na kyale.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[1/21, 22:25] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON ,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Washegari ban ma san hjy din tana turaka ba nidai na tashi kamar jiya nakama gyaran waje har zuwa kitchen dinsu da yanzu nasan lungun da yake shine can karshen part din.
Sai kofa da zaka iya budewa kayi wasu aiyuka a baya wanda ba cikin part din yake ba shi bayane fili sai bakin famfo dake wajen da wasu abubuwa dai haka.
Ba inda bangyara ba a wajen komai tsab don na tari sa,an asuba babu jin zafin aiki saboda a kwai ni,ima a lokacin aiki yana da dadi.
Takwas da rabi har nagama wanka na saka yar dogon rigan atamfam rubata a jikina irin dinkin mu na yaku bayi da zai nuna nidin ba wata bace.
Ko dakin Dada ban shiga ba na nufi dakin Nafisa din kwankwasawa uku na samu ta bude har ina niyar komawa baya a lokacin ciki magagin barci ta taso tana fadin wai wayene haka dan Allah ?
A raina nace tirkashi tana bude kofan take fadin wai kece dama ai kofan ma ban rufe ba sabodake don shigowarki na barta bude.
Bayanta nabi take fadi kinga wanan kayan ta nuna min tarin kayan da aka jibge saman kujera tace wanan kada ki fara tabashi amma na cikin closet din nan don Allah gaba daya ki gyara min su ki hada ko wani da dan uwansa har gyalen ma.
Duban tarin kayan nayi a raina nace tirkashi wanan duk kayan mutum gudane haka yaushe har mutum zai tsaya sakasu don Allah wanan irin abu haka ?
Wasu manyan ghana most go ta jefo min guda ukku tana fadin ki jera minsu a cikin nan amma don Allah na less daban buje da riga daban sai na zannuwan suma daban.
Na,amsa da to saidana dan nisa na fara yin yadda tace takoma ta nade a cikin bargo nan dai naci gaba da aikina abu wasa wasa har yakai ta tashi tana kallona daidai nagama jera zannuwa din zan fara na less ina dagowa naji taja tsuki daga bayana.
Hakan yasa na dan juyo tace kin ganene dinga nuna min akwai wa yanda zan cire dama kin hada wanan dinne nace ehh to ki fara wanan haka dole ta mike tare muka hada kayan da ita don nikan yafi karfi na.
Saukin abin takance dani ai wanan zai maki ko idan nace ehh sai ta nuna min gefe daya na aje da haka har muka karasa da kyat komai nata da takeso saida muka hada a dakin nan tsab mukayi packed dinsu a waje daya tasa na daure wanda ta bani cikin wani zanin gado gefe daya.
Ashe gwaggona ta taso taga har tayi aiki bataji durina ba ga alaman nayi aiki kuma don ta samu komai tsab a kitchen din ma na gyaroshi tsab har yakai taje daki bata ganni ba yasa taje dakin Dada nan ma banciki.
Saida ta kawowa Dada abin kari take tambayana don halimatu tana bandaki bata samu tambayanta ba Dada ta tsoratata da cewa bakiga Abulle ba tun safe ?
Ina ta shiga ni safiya a garin nan kuma sai gashi wai ana nemana halimatu tace ba tana wajen antyn nan ba ke Dada kin mantane da tace yau da safe zasuyi aiki dakinta hakan yasa Dada ta samemu dakin tana masifa.
Lokacin ma mun gama ina gyara kulle abinda ta ban tace don Allah Dada ki rage wanan fadan yarinyar nan ta gaji da yawa wallahi tun safe muke abu daya da ita ni nama gode maki wallahi dakikazo da ita ai da bansan yadda zanyi ba.
Ehh kyace hakaman tunda ga jaka na kawo maku ko to bari kiji bata karawa kowa wanan aikin wahalan kinji ke kuma na fada masu.
Haka na kinkimo kayan data bani din muka fito da Dada lokacin Dada tace wanan fa badai wanki bane kuma tace aiki tambayeta na juyo cikin muryan nan nawa nace Dada bani tayi fa.
Owoo yanzu naji batu ashe kinsan ya kamata na dauka halin banzan dai zaki gwadawa yar mutane kuma tunda ba sanin ya kamata kukayi ba ku.
Ke dai akeji yanzu ta fada tashige bandaki ta turo kofan da karfi zamu shige wurin Dada dayan ta fito tana yauki tacewa dada din duk kin hanamu barcin safe yau wajen masifan ki .
Saida ta juyo ta kalleta tace saiki kira ubanki ya koreni gidansa tunda na hannaku barcin hasara barcin safe tana fadin hakan muka shige daki.
Zance zuwan Dada gidan gaskiyane kamar ya takurawa yan gidan gaskiya don yadda take basu amsa gatsal zaka gane babu shirin arziki a tsakaninsu da ita.
Zakace ba irace kakarsu data haifi mahaifinsu bama don bata raga masu ko kadan da sunyi mata take basu amsa take a wajen kusan haka halinta yake ko banza saidai nasu din yayi yawane nagani.
Nikan dana rugumo kayan zan nufi masaukin mu dashi muka hade da gwaggon mu cewa tayi dani bayan nagaisheta wanan kayan na meye kuma ?
Cikin dukar dakai nace wanan antyn da zatayi aurene taban su ta mede baki tana fadin nasan tarkacen tsunmakarane ko ke me zakiyi dasu kuma bandai tanka ba na shige dakin dasu na zauna ina dan dubawa daya bayan daya .
Ni dai ani kan kayan sunyi min gaskiya ba laifi ina na taba saka less me kyau irin haka aina samu na shiga buki na fada a raina.
Wanda naga bani so suna ajewa halimatu don nasan zatayi korafi ban bata komai daga ciki ba kala ukku nacirewa halimatu din na kwashi wanda na zaba har na halimatu buuu nakaiwa gwaggon namu ta gani.
Sai cewa tayi suna da dan dama dama ai kin gode nidai naja bakina nayi

Please Login or Register in order to submit comment