Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayan hjyn sai ya matse lokaci guda.
Zaman kauye da zaman babban gida irin da muka baro a kauyen ya saka min wayau da saurin fahintar mutum lokaci daya.
Tun lokacin na fara fahintar akwai yar tsama a cikin wanan gidan ke nan itako wace ta kirani da yar uwar baba a lokacin sai cewa tayi da Dada hjy ga mutumiyar ta tashi tayi sallah naga ta damu da son ganin ku yasa na kawota ko hankalinta ya kwanta.
Allah sarki yar gidan Dada yanzun nake zancen ki a raina nasan kina wajen gwaggonki yasa ban daga hankalina ba ai ya jikin naki ya koma daidai yanzu ko Dada ta tambayeni cikin mika hannu gareni kamar karamar yarinya alaman inzo gareta.
Ban bata hannun ba don ganin ido yai min yawa a wajen sai zama da nayi a gefenta kafin na dago kai ince da jama,an dana sama ina wuni murya kasa kasa kamar ina tsoronsu.
Wai yatace mai sunan mama yar wajen garba dama tare kuke ashe da ita sai lokacin wanan dayan hjy dake zaune a kusa da Alh tayi magana cikin isa da takama da izza tace ina zaka ganta kuwa tunda komai sai an nuna makirci a kansa an nuna son kai nima tunda suka iso sai yanzu na ganta ai na daiji ance tare sukazo da ita dama.
Maimakon naji ta bata amsa sai naji tayi murmushi tana fadin kaiya ko in nuna ko kada in nuna kowa ai yasan cewa ita din jininace dai sai lokacin mijin nasu yai magana yana fadin.
Shout up please har agaban wa yan nan bakin yaran sai kun nuna halin ku na banza da alama ma yarinyar nan bata da lafiyane yadda na fahinta amma fitinan ku ya hana mutum ya fahinci komai.
Ina wuni Abba na kara maimaita gaisuwana gareshi kafin ya dan kallo a hasale yana fadin mamana anzo lafiya ashe bakiji dadi ba kuma a hanya Dada ta karbe da fadin aini abin ta ban tsoro nafito lafiya da yar mutane a hanya kuma ta nade min haka ?
Yanayine hajiya baba din ya fada kuma da kauyanci kinsan ba mota suka saba shigaba irin haka sai jakkai da rakuma dole taga abin wani daban tunda bata saba shiga mota ba ai .
Wanan hjy yar likuti mai masifa don sunan dana laka mata ke nan tun ban sauke kayana a kaiba lokacin duk da ina karama na fahinci magana ta dasa min don kawai yar uwar zaman ta taji haushi .
Sai naga itako bata damu ba ta daga tana fadin idan kinci abinci sai kizo kisha magani ki kwanta ta mike ta bar falon har takai kofa naji muryan Abba din yana fadin.
Maryam ke nan dai a wajen ki maman tawa zata sauka ke nan to ki kula min da uwata kinsan dai bani wasa da mai wanan sunnan a rayuwata tsuki naji anja daga gefen shi wanda yasa har na dago kai na kalli wanan bakar matar mai jiki dake gefenshi.
Sai naga yayi magana kasa kasa da sai shida ita zasu iya ji kaita girgiza tana fadi niba zancen ka nakewa tsuki ba nawane nan a zuciyata ta fada tana kawar da kai gefe daya.
Ganin hakan banyi marmarin tsayawa ba nima na mike don kada in bace wajen komawa part din nata muryan halimatuce ke fadin jirani muje zainabu jirani muje tare ta mike tana biyo bayana ban tsaya ba naci gaba da tafiya tabiyoni.
Wanan shine tushen bakin hassadan daya shiga tsakanina da wanan ahalin duk da ban masu komai ba amma saboda akidansu na bambanta tsakani yasa sukaga na zabi wace take jinin mahaifina sama dasu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[1/19, 19:17] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON BIRI

ZAINAB IDRIS MAKAWA


5️⃣
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Wai har naji dadi muryan halimatu ke fadin hakan lokacin da muka shigo dakin mai dakin tana cikin bayi batama san da shigowan mu dakin ba a lokacin.
A takure ta fito ta samemu zaune a waje daya har saida taja da dan baya tana fadin wai kune kunkoci abinci kafin ku zo muka girgiza kai alaman a,a.
Ai ba zaku kwanta da yunwa ba ta fada ta aje tawul din dake hannunta saman gado tana fadin bari naje na debo maku abinci ta fice daga dakin.
Kallon juna mukayi nida halima din kamar munafukai munyi tsuru tsuru damu zakice bamune muka gama daukin zuwa kano a jiya ba sai gamu kano ido ya raina fata don har na fara dana sanin zuwa a zuciyana ko.
Sallama tayi ta shigo dauke da plate shake da abinci ta aje muna a gaban mu ta juya ta fita halima ta kalloni tana fadin cikin kashe murya wanan tafi hjy can kirki kinji metace dani wai da Dada batazo damu ba ai tunda ba,a fara buki ba.
Da alama bata son baki ko bataso azo damu ba shigowan mai dakin yasa tayi shiru ruwa ta girke muna a gaban abinci tana fadin kuyi hakkuri ba kowa ke son shimkafa da dare ba amma shi aka basu umurnin yi yau.
Abincin dake girke din nakai ido na kalla jelouprice ne yaji hadin gajyen kabeji da caras da sauran tarkace sai nama manyan yanka guda hudu.
Duk haduwan abincin bai wani ban shawa,awa ba don lokaci guda gidan naji ya fita min a raina badon komai ba sai fahintar da nayi cewa mazauna gidan ba zaman lafiya a tsakaninsu don har mu baki daga zuwan mu abin ya fara shafan mu.
Saboda yanayin jikina na rashin sabo da mota ban ci wani abincin kirki ba sai halimatuce ta zauna ta kwashi abinta bandai da yunwar nama don zance gidan mu Alhamdullahi akan nama don har gobe baba na shiga kauye yayi kwanakinsa a can yana aikinsa mudai iyalinsane ya dawo damu cikin katsina inda gidansu yake muna zama don inganta rayuwan mu nan gaba da yan uwa suka inmasa yayi.
Amma part din mu na can kauye yana nan indan yaje nan yake zama sunso su mamaye wajen amma dole suka barshi da abinsa tunda sunsan yana zuwa lokaci lokaci kusan shi yafi rayuwa ma a can din.
Hakan yasa idan zai dawo zai dawo da nama man shanu nono da sauran tarkacen rugan dana kauye har sai inna tabawa mutanen arzikinta suma sun lakaci arziki a wajenta.
Wanan yasa banda kwadayin irin abubuwan nan nan shigowan mai dakin yasa na dan muskuta ina gyara zama saita kallo mu kafin ta mayar da dubata kan abincin dake gaban mu din aje tana fadin..
Ya kuma bakici abincin ba ko har yanzu jikin ne dai cikin sanyin muryan ayadda take magana cikin yanayin sanyi da kamala tare da mutumta mutum.
Naci gwaggo kalman ya fito min a baki don sanin cewa ita din alakar uba muka hada da ita don haka ta zamo gwaggona ke nan da ace ta uwace sai in kirata da mama ko wani lakanin daya danganta da uwa.
Murmushi ta sauke a fuskanta kafin tace dani toko jikin nakine bai sake ba har yanzu zaki kara shan ruwan shayi a hada maki kada ki kwanta da yunwa a cikin ki ta tambayeni cikin tsureni da idanuwanta daga inda take tsaye din gefen gadonta.
A,a nakoshi gwaggo na kara fada sai naji ta sauke ajiyan zuciya ta juya can kuma ta juyo tana kallon mu tace idan kun gama ga daki can a gyare kuje can ku kwant zakufi sakewa bisa ga nan din kema a nan zaki kwana ke nan ta tambayi halimatu din dake tattara dan kwaran shimkafan da suka zube a kasa.
Ta dago tana fadin ehh a nan zamu kwana tare don can inda dada take naji sunce kada a bata masu daki da kazanta sai ta sake murmushi tace kayya ku kananan yarane da zaku bata waje kuje ku kwanta ku huta ta fada tana fita ganin hakan yasa na mike nabi bayanta.
Dakine hadade mai kyau da katon gado da shimfida har da mirro a cikinsa tace kuyi zamanku nan abin ku har ranan da zaku koma kalman mun gode ya fito a bakina tace da akai maku me kuma gidan kune fa nan din .
Har takai kofa ta juyo tana fadim idan fankan yayi yawa kunsan dai yadda zaku rageshi ai muka amsa da mun sani ta fice ta barmu a dakin lokacin halimatu ta kalloni tana fadin wai matar arziki inda wacan muka samu kawai a gidan nan da iyalinta yaya zamuyi ke nan ?
Ya kuwa haka dai din zamu zauna a takure muma na fada ina bin dakin da kallo wai dakin baki ke nan kamar na wata mace don Allah halimatu ta fada nace wanan dakin ne na baki tace ehh,mana.
Bakiga ko acan cikin irinsa aka sauke mu ba amma naji yarinyar na fadawa uwar da turanci ko ta dauka ban bokone wai in babansu ya dawo amai damu boys quarter.
Allah ya kyauta yanzu damuwata shine inda zamu samu kayan canzawa tunda kayan mu suna wajen Dada mun barsu na fada ina dan dube dube gashi wanda na bata da amai bansan inda aka kai munshi ba.
Haka muka kwanta duk yadda halimatu taso muyi hira na kasa sakin jiki inyi haka din saidata fahinci cewa nayi barci ta kyaleni sai dana falko da darene na samu an kashe muna fitilan dakin halimatu na tayar ta rakani zuwa bandaki na kewa bamu kara falkawa ba saida safe da mai shiyan ta tayar damu daga barci don muyi sallah bayan hakan namu kara jin duriyanta ba kuma again.
Ban iya komawa barcin safe ba don haka dana gaji da kwanciya na mike na fito gidan tsit yake babu kowa ba wani motsin wani mahaluki kuma Allah ya taimaka naga tsintsiya a kofan dakunan na dauka na sharo ko ina na part din don zaka gane iyakar part din don a rabe suke falon gidan yana tsakiya daga sama kuma benene na maigidan a tsakiyansu sama.
Tsab na gyaro ko ina kafin nafito har ta waje main falo dinsu shima na gyarashi tsab na dawo dakin har lokacin halimatu tanata kwasan barcinta wanka nashiga rashin sanin heater a ban dakin yasa na watsa ruwan sanyi a jikina.
Na fito ba mai da zan shafa duk suna cikin jakata inna tayi min guzirinsu har kayan shafa na yan mata don na shafa ba sai na nema a wajen su ba inna ta saka min akayana.
Don inna irin mutanen nan ne masu kula da kansu suna rike kima da darajansu talaucin mu baisa ta zubar da kimanta ga kowa baka taba jin taje wajen wani yin karamin murya kan neman wani abin rayuwa daya shafi gidanta.
Haka kuma bata da lokacin zama yin kananan magana da mata kan saka kansu kan abinda bai shafesu ba har su daukarwa kansu zunubi donshine ba zakace ga abokiyar fadan ta a shiya ba indai innace.
Yaushema taje wani gidan balle ta saka ido ga abinda mutum keyi koda yaushe kake nemanta tana kofanta a zaune inda Allah ya ajeta dan dama kwana bibiyu zata shigata gaida Dada ta dan kumsa alheri takai mata shine kawai yawan fitanta a cikin shiya ita.
Daga dakin da nake zaune nayi zaman tagumi ina tunanen duniya najiyo muryan mai shiya tana fadin yau wani dan albarka na samu yayi min wanan aikin haka ?
Can na danji kara bude part din sai kuma ta dawo ta nufo dakin da muke din zaune ta turo da sallamanta nayi firgigit na juyo ina dagowa kamar mara gaskiya har kasa nakai ina mata ina kwana.
Ta amsa tana saye da hijjab sky color har kasa a jikinta sai dogon rigan daga ciki dake baiyana kansa lokaci lokaci ga kamshi na dan busowa a jikinta har inda nake take fadin kardai ince duk ke kikayi wanan aikin haka tunda safen nan.
Na dukar da kaina tace Allah yaiwa rayuwanki albarka da alaman tarbiyan da matar yaya ta baki ke nan kike nunawa ga halaiyanki ki kara tsare kanki kinji duk dan mutunci kallo daya zai maki yasan kin samu tarbiya yadda akeso.
Ta juya zata fita lokacin nace gwaggo cikin sanyin murya sai ta dagata ta hanyar juyowa tana fuskantana nace dama mai nake son in shafa nayi wanka maina danazo dashi yana cikin kayana a wajen Dada.
Au har wanka kinyi da safen nan injin dai kin kunna ruwan zafi na manta sam na kunna maku heater ai da nashigo jiyan ta fada tana kallon hanyar bandakin.
A,a ruwan sanyin dai na watsa na fada lokacin halimatu dake kwasan barci duk abin nan da mukeyi ta motsa ta mike firgigit tana gaida ita da kwana ta amsa kan ta juya ta fice a dakin.
Kizo ki karbi man ta fada bayan takai kofa halimatu kuma ta shiga bandaki na mike zuwa dakin nata na samu tana bincike abu a wardrobe din ta sai ga man shafi babban gora ta dauko tare da wani marron din dogon riga yar kanti material cikin irin kayan data kan tara idan sunyi tafiya rigan ya burgeta duk da bata da diya mace ita a rayuwanta.
Diyanta mazane shidda cip a duniya biyar a wanan gidan ta haifesu dayan wanda shine babban mahaifinsa ya rasu tun tana da cikinsa shima din irin auren hadin da zurian mu sukeyi akai masu.
Bayan ta gama wanka tana zaman zawarci saiga baba na kano kuma ya nuna yana sonta sai kuma aka kara dada auren gida a kansu din ashe rabon zuriane haka tsakaninsu sai gashi ta haifa mashi diya biyar duka maza.
Wanda ya kara haddasa kiyayya a tsakaninsu da abokiyar zamanta hjy malka wace ita ma dai din a cikin dangi take duk auren zamane a tsakaninsu amma kuma tunda zaman kishi ya hada a yanzu sai aka kawar da zumuncin aka kama hanyar shedan ana fafata zaman kisantaka zallah a gidan wanda har hakan ya shafi yaransu.
Bai tsaya a nan ba don har wasu dangi abin ya shafa ashe muma dai don muna yarane bamu san dawan gariba har muka yarda ta jamu zuwa sashenta wanda niko a lokacin kwadayin kiran yar uwar mahaifina take na kusa data furta min yasa na karkare yarda da komai nata.
Wanda hakan ashe baiwa hjy marka da yayanta dadi ba a take suka dauke mu munafukan bakinsu kamar yadda suke daukan duk wani wanda yazo ya danganta da hjy kubra din.
Wanan kuma shine dalilin zuwan Dada da wuri kafin buki don yana son aiwa abin tufka tun kan jama,an arzikinsa su taru su hautsana masa gida da kaidinsu na mata don yasan yan uwa da abokan arziki zasuzo sha,anin har wanda bai taba zuwa ba labari yakeji a yanzu zaizo yaga abinda ke wakana a gidan shima.
Ashe a daren jiyan bayan fitan mu sun fara fafatawa don ya gabatar da zancen a gabansu gaban Dada din don ko muna fita tace ashe har da yara sun iya munafunci to an riga da an kulla masu tun a gida kan suzo ga inda zasu sauka mana.
Lokacin ya juyo yana fadin wanan wani irin maganace kuma yaran nan me suka sani da zaki fara fadin haka akansu yarane fa wa yan nan kanana duka duka har yaushe suke wai ?
Dada da sai lokacin tagane me ake nufi tace Allah sarki wai su Abu take zance dama in hakane ai laifinane da muka iso baku gidan yarinyar ta jirkita da yawa naji tsoro nace a kira min dayan ku.
Akace ku bakwa nan sai Kuburah a gidan shine na aika tazo ta taimaka min da ita shinefa ta dauketa zuwa sashenta kinsan shi yaro karene inda yaga fuska can yake dama wanan ne dalilin kika gansu tare ai amma kayan su yana nan guna ai ko yanzu kinji nace ta bata magani kafinta kwanta ai.
Dada banda hakan shin akwai wani barene a cikin yaran nan don Allah ko banza yarinyar nan kakarsu daya da mahaifinta da ita kuburah zaki iya raba halakan dake tsakaninsune kome ,?
Ai gata gasu dama ni nauyi ta rage min ai yace baki san hakan ba tunda kin fassara hakan da wani manufa daga inda Dada ke zaune tace wai tsaya intambayeki marka.
Mu din ne nauyi yau a gareki da kike wanan zancen ko suwa kike nufi da nauyi a wajen ki ina dai nine sai diyan nan naku biyu da shakuwa yasa nazo dasu tun yanzu garin nan don su debe min kewa.
Kin fadi hakan tun yanzu inaga kin tara taron yan uwa an cika maki gida da jama,an arziki kuma kaga musa wanan yasa na daina zugan zuwa gidan ka dama don iyalinka har yanzu ba hankali ne dasu ba.
Hjy kin dai ji kin kuma gani da idon ki ni bansan yaushe malka zatayi hankali ba ta daina wanan bakin kishin data dorawa kanta kan kuburah.
Wanan yasa na matsa ki taso akwai matsala kin fara ko ganin inda matsalan take yanzu mikewa Nafisa tayi wace za aiwa auren don barin falon don ba zata iya juriyan jin abinda ke faruwa tsakanin iyayyen nasu ba lokacin.
Mahaifin nasu yace ki dawo ki zauna kiji abinda za a fada koke abin ya shafeki don gidan wani zaki bako dukkan maza zasu dauki wanan akidar ba ki sanni.
Simi simi ta dawo ta zauna tana turo baki kafin muryan Dada ya karde falon tana fadin wallahi marka kin bani kunya sai inje gidan dan uwanku indawo muna marmarin juna dasu kuko nan duk nazo da bacin rai nake barin garin nan kuma duk kece ummul,aba,isin hakan a gidan nan kuburah dai zuwa kikayi kika sameta sun zauna da zuciya daya da wace ta fara samu a gidan nan amma ke kin kasa hakan.
Bani ba kowa a cikin dangi ba maza ba ba mata ba tsoron zuwa gidan nan sukeyi don masifan ki da fitina bako bai zuwa baki samu sherin da kika lakaka mas ba kice yayi maki keda diyan ki.
Haka yaron nan Aliyu kin hana yaro shakat a gidan nan yau in Musa bai rike Aliyu ba duniya koda bai auri kuburah ba wakike son ya rikeshi a cikin dangi.
Yanzu kuma nime nace akan Aliyu hjy ta fada cikin hasala da dago kai tana aon jin ba,asin jefo Aliyu a zancen da sukeyi yanzu din.
Ai magance data shafi hakan malka uwar tawa zaki tsare da tambayan nan asheko ranki zai baci dani kiyi fatan ayi bukin yarki kina gidan nan na fada maki hakan ba yau ba.
Zan dauka na shaye duk wani hali naki amma banda wanda zakiwa uwata ko wani dan uwana a cikin sha,anin nan kai dagata don Allah Dada ta fada a cikin tsawa yasa ya tsaya.
Mikewa Dada din tayi da kyat tana fadin baidai zuwan mu dana yan uwanka da zasuzo daga baya ya kawo wanan kace nace ba a yanzu ?
To ku bari goben na dasafe zan saka yaran nan gaba mu koma katsina su kuma dangi zan gargadi kowa kada wanda ya kuskura ya tako sha,anin ku indai ina fada maishi yaji a cikin dangi.
Kuka sosai hjy malka din ta saka tana fadin nikan bakin jinina yakai haka yanzun nan kuma za a lauyeni har me nayi da za ace hakan a kaina.
Bakiyi ba marka yanzu na kara gane manufanki akan mu sosai burinki shine ki mallakemu kamar yayan ki sai yadda kika juya mu a gidan nan toba zai yuyu ba na fada maki.
Kama kanki a watse lafiya shiyafi don a yanzu ba mai daukar maki wanan bakin mulkin naki na kafirci kishi haukane koke kadaice farau tarda kishi a zauna lafiya.
Hannun Dada Nafisa ta kama suga shiga daki har lokacin Dada tana masifa Nafisa din tana bata hakkuri saboda tasan idan batayi hakan ba zata kwabewa mahaifiyar nasu kan bukinta din.
Mukan bamu san anyi hakan ba amma ita mai shiyan ta sani tun tana sintirin kawo muna abinci tana jin hayaniyarsu a lokacin.
Hakkuri irin nata yasa bata kula ba har wayewan garin nan kuma da muka tashi tasan akwai zance a kasa tsakanin abokan zaman nata yasa tayi shiru amma abin nacin zuciyar ta.
Ki karbi wanan ki saka don nasan yanzu basu bude part dinsu ba ina ai zai maki irin rigunan da nakan ajenevson haka rabonkine ya dan jima a dakin nan ban kyautar dashi ba.
Ki zauna nan ki shirya inkin gama ku dauki man kuyi amfani dashi ga kayan kwaliya a mirro duk dani ba wani kwaliya nakeyi ba amma ba zaki rasa abinda zaki amfani dashi ba a nan.
Tana fadin hakan ta fice daga dakin kitchen ta nufa don hada abinda zamu karya dashi din lokacin na bude roban man shafin na lakoto naji yana kamshin wani icce kamar saye ga laushi mai dadi a jikinshi kamar man bama da akecin ganye dashi.
Daga roban nayi ina kokarin karanta sunan man naga an rubuta naturalsense nayi nayi na fassara kalaman da hausa na kasa har nagama mulke jikina badon naso ba na rufe roban kada ta dawo ta samu ban gama ba na nufi mirro din a nan ma na rasa me zan shafa kayane birjit a wajen da bansan amfanin su ba lokacin.
Bayan na dan shafa na mayar da komai a inda na sameshi na saka rigan a take naga na koma kamar bani bace a gaban mirro din haka na daure na fito daga dakin zuwa inda muka kwana.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[1/20, 17:40] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON ,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Ranan bani gajiya da satar kallon kaina a jikin mirrow halimatu ba zatace ga tufafina ba don haka bata gane wanan din daga mai shiyan ua fito ba sai faman yabawa da itama takeyi akai da yayi mi kyau .
Har lokacin da hjy ta kawo muna abincin mu har daki kokone da fanke sai ruwan shayi kuma shi mukaci muka koshi lokacin halimatu take zancen wanka.
Kafinta shiga tace bari ta karbo kayanta wancan dakin

Please Login or Register in order to submit comment