Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su mike da kamshinsu nabisu da kallo har suka fice daga gidan bayan sun ajewa Dada din alheri sukai gaba sai gashi tsohuwar ta koma fadin yan albarka sun gado mahaifansu wajen alheri.
Yaki zoki kirga min kudin nan na boye kafin yaran banzan nan su dawo su wawashe min tare muka kirga kudin dubu goma sha biyar tana faman saka masu albarka.
Ta cire dubu daya ta miko min tana fadin ki karbi wanan kyasai foda sha wanan kuma daure min shi dakyau na tura a lalita kafin su dawo su gane ina da kudi a dakin nan.
Kaina girgiza kafin nace a,a Dada ki barshi nayafe rankwashi ta kai min a kai tana fadin ko uwarkice ta hanaki karban da sauri nace a,a Dada kawai ki barshi ta dangwara min kudin a jiki ta mike tana cire zip din lalitan bujenta irin na tsofi na mika mata kudin dana daure din ta tura a cikin aljihun nata.
Mikewa nayi ina fadin Dada barin koma gida kada baba ya nemini ban fada mashi zan shigo nan ba na fito na barta tana fada dani akan me zance za a nemeni bayan ansan banda wajen zuwa kaf unguwa sai wajenta.
A kofan gida na samu baba zaune da kanwata sadiya da dan ledan awara daya saya mata nake gaidashi yace dani daga wajen Dada ko nace eh baba naga gidan da bakine naje can.
Murmushi baba ya sauke a fuskanshi yana fadin banda abinki zainab ai duk yayyunkine wa yan nan kusan abu daya kuke dasu rashin sanine kawai don baki saba dasu ba tun farko.
Murmushi na sauke a fuskana ba tare da magana ba na shige gida inna tana zaune saman kujera yar tsuguno ta mata na shigo da sallamana ina gaida ita.
Gunsu na nufa ina lakatan fuskan yaro nace maizuka inna wai wanan yaron naki baya gajiya da shan nono ko yaushe nono a bakinsa .
Ta dago cikin haraea tana fadin ke bakya gajiya da cin abinci wayayi maki wani zance balleshi wanan meya samu har ya zuka bayan kun kwashe komai tundai ke na saka yar dariya ina cire hijjab din dake wuyana direct gun wanke wanke na nufa.
Ina wanke wanken muna hira da inna jefi jefi akan islamiyan mu nake bata labari har yakai nagama na kife na dauki tsintsiya na share gidan tas kafin na dauki bucket na dibi ruwa a randa na nufi bandaki don in watsa ruwa ko ya ruwa yake da sanyi kuwa don mun saba tun a kauye.
Bayan mun shirya har kannena muka fito don zuwa islamiya a daidai wanan kofan dake rufe ko yaushe na hango dandazon su ban daga ba ban kuma kallo inda suke ba haka muka shigesu zuwa islamiya.
Wa yancan yaran badon a kauye suka taso ba da yanzun sun fi kowa a family din nan shanawa don yaran gasu gwanin ban sha,awa dasu wallahi.
Kai uwarsu ce suka kwaso wa yan nan yaran akwai tsabta daga gefensu wasu ke fadin wai yarancan suna da girman kai basa gaida kowa fa yara kanana dasu amma sai girman kai.
Haba dai wa yan nan yaran me suka sani wani girman kai dayan da duk tsayinsu wajen kowa na fadan albarkacin bakinsa sai wanan ya furta daga hakan kuma bai kara tsunkawa ba ya juya shigewa yayi ya barsu a wajen.
Tunda na samu nabar wajen naci gaba da sauri ban tsaya ba na shige islamiya a kusan kullun mune farkon shiga islamiya har ma yanzun da abokan tafiyana sukai tafiya.
Har muka tashi islamiya gabana sai faduwa yake ba komai yaja min hakan ba sai ganin wa yan nan matasan da baba ya kira da yan uwana duk da naji su din yan uwanane amma hakan bai hanani tsoron suba.
Kodon shigar tufafinsu da yanayinsu da ban saba ganin shigar haka ba ga mutane don ko a nan katsina akasari irin shigan mutanen hausaw suke shiga wando da rigan jamfa amma wa yan nan gasu fara wasu chaculate color amma haka suke a tsuki dasu ba maiyiwa wani fada a cikinsu gashi ba zakace ga babba ga karaminsu ba komai a tare sukeyinsa.
A gaban mu motarsu tazo ta wuce mu sai muka samu mutum biyun su kofan gidan Dada sun faka motar dayan yakai bakin masalaci daga nisa kaina yana duke kasa yake fadin don Allah yan matan dada karbo min ruwa wajenta nayi alwala.
Sam ban dauka dani yake zance ba sai kokarin shigesu nakeyi kaina na dukr a kasa sai dayan dake gefen mota a tsayene yace ke yarinya dake ake magana koke kurmace bakya jine ,?
Jin hakan yasa na dago kaina ina fadin ayya banzata dani yake ba ai don Allah kuyi hakkuri baiko tsaya bin ta kaina ba hakan yasa na nufi wajen mai miko min butan na karba daga hannunsa tare da dan rusunawa na girmama a gareshi kansacewarshi na gaba dani.
Ya karba yana min turancin daba fahinta kwakwalwata zaiyi ba Dada tana zaune tana jiran ayi kiran sallah na shigo da sallamata ta amsa min tace kishiyata badai yanzun kuka dawo daga karatun Allah ba ?
Yanzune Dada sauri nake in karasama gida wanan bakin birni din sukace na debo masu ruwan sallah a nan tace shu,umai ni yanzu na kare zancensu a raina har ina zaton ko sun wucene ma don ban kara jin duriyansu ba tun dazun da suka fice.
Ni dai na debi ruwan nakai masu ruwan ya karba tare da furta kalman thanks ya juya nima na kama hanyan gida ina sauri kada a kira magariba ina waje kamar yadda iyayyena suka horemu dayi kullum.
Ina shiga gida daidai ladanin masalaci yana dauka loudspeaker zai kira sallah wanda wanan karan ke fara fadakar da nusulman unguwa lokacin sallah yayi.
Innace zaune da danta dake goye a bayanta tana jiran kiran sallah sallama na kara yi ina gaida inna din saidai bata amsa min ba bayan fadan data tareni dashi da fadin.
Meyasa bakya jini ina kika tsaya har aka kira magariba baki shigo gida ba sai kannenki da kika turo min suka shigo su kadai kallonta nayi a dan maraice nace ban tsaya ba inna tare muke dasu wa yan nan bakin da baba yace yayyun mune sukace in debo masu ruwan alwala a gidan Dada.
Ki dai kula ta fada taja buta ta fara alwala ganin hakan tunda na saba jin wanan kalman ba saudaya ba ba sau biyu ba a bakin inna din wanda bazance ga ma,anarsa ba a kaina yasa naje dakin mu na debe hijabin kaina na fito na dauki buta na zaga ban daki.
Bayan na idar da sallah na shafa addua ban zauna ba don nasan abinda zanyi basai an tuna min ba madafi nashiga na dauko kwanon silver da muke cin abinci na zubawa su sadiya.
Kafin na koma dakin inna na dauko shimfidan baba na shimfida har filo da yar redion shi da yake sauraren jakkar magori dashi da sauran shirin radio kaduna idan ya dawo daga sallah don bai kara fita idan ba wani kwakwaran dalili zai fitar dashi ba sai kuma Allah ya kai muna rai washegari yake fita kuma.
Bayan naga ana tayar da sallah na shiga nayi a nan na dan jima ban fito daga dakin ba har saida baba ya shigo naji yana tambayana na amsa ina fadin gani baba na fito ina gaidashi.
Yake tambaya kinci abinci kuwa nace yanzu zanci baba ina biya karatun mu na yaune kada ya shige min mallam yayi min duka gobe mai sunan iya banda abinki ai sai ki fara cin abincin kafin ki zauna karatu.
Na juya zan dauko abincin naji inna na fadin ai kasam halin ta da naku naku cin abinci sai ta saka mutane yin magana kafin ta zauna taci don sabo da wanan mugun halin a rayuwanta.
Zance nafi jin dadin baba bisaga innan mu don baba yafi inna lalaba mu ita inna koda yaushe a cikin tsawa take muna kamar yadda wasu uwaye mata kanyiwa yayansu wani lokaci.
Ballema ni da kusan don ina yar fari a wajenta take nuna kara a kaina ko banza koba kowa haka muke yar tsarguwa da inna din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[1/17, 21:35] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FAKON,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA


4️⃣
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE AGAREK SHI HAKKI, BA ABIN WASA BANE , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


A zatona sun bar garin don washe garin lahadi ko kofa ban taka ba har islamiya banje ba don mun tsaya wanki da kitso da sai ranan lahadi mukeyi don inna ta camfa kamar yadda yake ga addini.
Bata wanki ko kitso ko tsifan kai ko yankar kumba ko sharama dole dai akeyinsa don jin da tayi malamai na fadin cewa ba a son mutum yayi komai daya shafi rayuwa a wanan ranan idan baya zama dole ba.
Wanda rashin sani da kuma akidan nasara yasa a yanzu mun take hakan muna aiwatar da abubuwan mu kai tsaye tunma daurin aure a yanzu harda wanda ba aikin gwaunati yakeyin ba sun mayar dashi wanan ranan ta asabar sabanin jumma da kakannin mu suka fiyi a da ayanzu a sabar din akeyinsa.
Sai yan tsirarune da suke da fatawan hakan akai suke zaban kyawawan rana da Annabin ya koyar damu suke abunuwa a yadda addini ya koyar damu yinsa din Allah yasa mu dace Amin.
Safiyan Monday mun fito zamu school daidai gaban gidan nasu na hangoshi a tsaye gaban wata jar mota kirar jeep da a lokacin bansan sunnanta ba ya jingina jiki da bayan motar yana tsaye.
Jikinshi yana saye da koriyar riga ta maza da akaiwa rubutu da manyan haruffa an rubuta VERSECE sai yar wandon maza fari mai aljihauya da yawa manya da ake kira cryzy ya dan wuce gwiwa har hakan ya baina santala santalan fararen kafafunshi waje da gashi ya dan rufe ga hannayensa saye da wasu zubba da biyu da suka karawa hannun nasa amarshi.
Ganin hakan da yake wanda kallo daya nayiwa yanayinsa na dukar da kaina kasa da sauri don kada na kwashi zunubi garin kallon kwam dinsa don nasan hakan ne zamana da yan matan gidan namu da nakanji kallo daya sun haddace abinda ke jikin mutum sin fada gashi nima a yanzu na iya hakan.
Magana suke da wani baban mu karami dashima muke kiransa da baba karami amma yanayinsa kamar yana sakar muna murmushine don mu din ya kurawa idanunsa muna tafe.
Sai naga ya juye min kamar mutanen kasan su inna da yan cikin tv da nake gani yanzu masu rawa da waka a wasanninsu din nan.
Ina kwananku nayi masu cikin dan rusinnawa da muka saba dashi tun a kauye idan zamu gaida mutum iya abinda na iya furtawa ke nan garesu sai naji muryan baba karami yana fadin yan buko har zaku tafi ke nan da safen nan ?
Ai gara suyi sammako zaifi masu abinda naji ya fada ke nan da hausa badon haka ba sai ince ko baijin hausane din zama a kasan turawan da ake fadin sunayi yanzu.
Kuzo ku karba kalman daya fito bakinsa ke nan sai naji kunya ya lulubeni gashi muna da tarbiyan cewa a,a ga mutum farat daya idan ya nufemu da alherin abinda yake ci idan mun riskeshi.
Toga wanan babu komai a hannusa ya kumace muzo mu karba yaya ke nan zanyi jin hakan yasa naja na tsaya ina kada kai alaman a,a sai baba karamine yace dani kuzo mana ana magana daku.
Tuni naji kunya ya lulubeni lokaci guda a wajen yayin dana dan sada kaina kasa cikin kunya na tako zuwa garesu din ina rike da hannun kanne na dake rike dani har zuwa wajensu din.
A daidai lokacin ya tura hannu cikin aljihun wandonshi ya fito da kudivyan dari biyar biyar guda uku ya miko min da sauri na sake girgiza kai ina fadin mungode suyi yawa baba ya bamu hamsin hamsin musai abinci muci.
Kai amma yar nan da wani zance kike ana batun dari biyar meya kawo zancen wani hamsin can kuma karbi don Allah kin tsaya kinawa mutane shirmen banza.
Shiko murmushi yayi yana fadin kinga kanwata karba ku kara ai harda na gobe na baku kinga baba ya huta baku gobe ke nan idan ran mu yakai koba haka ba ?
Jin hakan yasa na dan rusunna na mika hannu a cikin ladabi na karbi kudin a hannunsa tare da furta mungode na juya muka tafi har kafana yana hardewa waje daya.
Kwata kwata raina baiso karban wanan kudin ba gaskiya don inba Allah ya gyara ba nasan sai munsha fada a gida tundai ni har mukaje muka dawo suna cikin littafin dana sakasu a ciki.
Sam na manta da zancen su saida yamma da baba ya dawo gida sune zaune da inna suna hira naji yana zancen kudi abin ya fado min a rai daga inda nake tsaye nace lah .
Jin hakan yasa suka kallo inda nake duke ina wankin uniform din mu na school nace na manta in fada maki inna dazun da safe da zamu tafi school wanan yayan din da sukazo ya bamu kudi wai mu kashe a school shine na aje sai yanzu na tuna dasu na tsame hannu na wanke na nufi daki na dauko littafin dana adana kudin a cikinsa banko tsaya kidayawa ba don a zatona kwara ukune ya bamu kowa guda guda ashe ba haka bane.
Don ina bude littafin kudin suka watso kasa shar sabbi dasu mikaku sukai fale fale a kasa hakan yasa na fara sanin sunfi kwara uku ashe yadda nake zato.
Muryan innace ke fadin waya baku kudi haka masu yawa kika karbo ina jin hakan na dago da sauri na kallo inda inna din take zaune kafin naji baba yace dakata muji ai wanda ya bata.
Tunda har bata kashe ko kwabo a ciki ba aiba zamu fara mata fada ba sai munji ba,asi akai na hada kudin daya watse na dago ina fadin dazun ne da safe da zamu school mukaga wanan da kace su yayan mune faein nan dogo tsaye da baba karami suna magana.
Shine da muka gaidasu yace muzo mu karba muyi breakfast dashi nace ya barshi ka bamu hamsin hamsin sai baba karami ya kama min fada wai ai shima yayan mune don haka mu karba shine na aje na manta da muka dawo in nuna makine inna .
Amma aina hanaki karban abin mutane ko haba Rukkaiyatu kibi zancen nan a sannu itama ta sani ai na hanata hakan amma ai kinji tace babansu karami yasa ta karba don haka ai mata uzuri .
Da alaman inna bata gamsu da hakan da baba yace ba son yadda naga ranta ya baci har fuskanta ya nuna hakan a fili sai naji baba yace dani aje kudin kije abinki nagane ko waye mai sunan malam ne Aliyu ko tunda kince fari dogo shine ma dai fari sosai a cikinsu ai.
Bayan nabada baya baba ya rage sautin muryanshi yana cewa ina din ki dinga bin yarinyar nan a sannu tasan abinda takeyi ai tunda kikaga duk da abin kwalam a school din baisa ta kashe ko kwandala a cikin kudin nan ba gashi kuma a karshe ta kawo muna duk dai bamu sani ba ai tana amfani da zancen mu ke nan a kanta.
Malam tsoron zamanin nan nake ji a kauyema an yaudari yaro da kudi balle nan da yake birni abin ne sai ana tsawatawa haka ai nasani amma ki sani Rukkaiya insha Allahu Allah zai kare min zuriata dana musulmai daga masheranta.
Ban taba aikata zina a rayuwanta ba ko makamancin haka in Allah ya yarda Allah zai kare min zuriata da yardan sa insha Allahu amma fadan yana da kyau garesu sai dai a hada da nasiha.
Ai kinji hankali bai tashi ba don nasan yaron natsetsene baiyi hakan garesu da wani manufa ba sai da niyar alheri irin na yan uwantaka a tsakanin su dan uwatane donshi na kyale aida nine zan fara fadan karban da tayi din.
A haka rayuwa ke tafiya damu a sannu a hankali ayanzu nasan duk wani dan uwa na kusa dana nesa har matan babanin mu maza dake zaune wani gari izuwa yanzu dai nasansu gwargwado sai wanda baizo ba na gansane ban sani ba.
Gashi shakuwan mu da Dada yasa suma din sun sani sosai don yanzu mun shaku da ita fiye da dacan da mukazo rashin sabo yana sa ina mata make make narashin sabo a tsakanin mu.
Saidai cikin hikima da nuna so da kauna irin na tsofi har Dada ta saye min zuciyana dagani har iyayyena a yanzu banda wani zance sai nata a bakina itama kusan hakan.
Don duk cikin jikoki tafi yarda dani da kuma kamar sakani a rai bisa ga kowa wanda nasan shakuwan dake tsakanin mune ya kawo hakan.
Hakan yasa da tafiya kano ya kama Dada ta bukaci baba ya barni mu taka mata baya nida halimatu jikinta dake wajenta baba baiki ba don dama yana da burin hakan nakai ziyara ga dan uwansa dake masa korafin yana masu rowan mu bai bari muna shiga dangi a san mu.
Shiri sosai Dada takeyi na tafiyan mu din don a bakinta nake jin cewa buki za,ayi nan da sati biyu a gidan baban nanu dake can zaune kano din kusan duk dangi zasuzo wanan bukin don shine karo na farko da zai aurar da yarsa mace don maza basuyi aure ba saboda karatu.
Itama yar nasa da ake kira da anty baby naji Dada tace ta tsaya karatune yasa ba ai mata aure da wuri ba sai yanzu data kammala zatayi aure.
Mukan a bangaren mu ba wani shiri illa zaban yan tufafin mu mu goge sai kuma kitso da kumshi wanda inna da kanta ta zauna ta dandasa muna kitso har siifa a kafafun mu nida halimatu din.
Mota sukutum baba na kano ya aiko da za a dauki Dada din dashi don haka ba wani matso matso ko guna mu hudu ras aka dauka tare da baba karami da yabi gayyan Dada din zuwa kanon .
Gidane babba wanda mallakin baba na kano dinnne don dan kasuwane sosai shi a kware market din kusan kowa yasan sunnansa don yayi fice a kasuwanci kuma ya karbeshi sai hamdala.
Nasha wuya sosai a hanya don amai dana dingayi wanda warin mai da nashaka da sanyin AC motan suka hade lokaci guda suka haifar min da aman don da farko kaina ya fara juya min sai kuma sanyi saiga amai duk na bata jikina dashi.
Allah ya kare na riko dan leda a ciki na dunkule nayi tayi sannuko nashashi a wajen Dada yafi cikin kwado a lokacin don ta nuna damuwanta sosai ga hakan daya sameni.
Har take fadin data sani da bata zo dani ba ta daukoni lafiya hannun iyayyena gashi tun ba akai inda za ajeba yar mutane ta fada a wani hali a hannunta.
Hakan yasa muna isa bata tsaya takan taron da ake mata ba ta mayar da hankalinta akaina tana fadin ku kama yar mutane don Allah ta jigatar da yawa nan matar da suke kira da umma tazo tana fadin ya akayine meya sameta Dada ta fara fada masu wahalan danasha a motar.
Bata tsaya sanya ba ta wuce dani sashenta ruwan masu dumi ta hada min ta kaini bandaki don inyi wanka ta nuna min yadda zanyi ta fito nakoji dadin wankan don naji jikina ya dan sake gaskiya.
Ina fitowa na sameta zaune saman gadonta ga kayan tea a gefenta yana tururi a cikin kofi muryan ta a cikin sanyi take fadin ki sauya kayan jikin ki kafin ki sha ruwan shayi ga kayan ki nan na karbo maki a wajen Dada.
Karban kayan datake miko min nayi nawane amma kuma sabbine ai hakana na karba na daure na sauya tana zaune saidai tsabgabta takeyi bani take kallo ba ban tsaya shan tea din ba taga na tayar da sallah inayi.
Saida na idar na fara gaisheta ta dago daga karatun littafin da takeyi tana karba min gaisuwana tare da fadin kisha ruwan zafin zai taimaka maki.
Banki ba na dauki kofin shayin na dan kurba nan ma sugar naji yayi yawa saboda iyayyen mu basu saba muna da sugar ba ko kadan asalima muda muka fito kauye inamu ina sugar inba karya ba.
Amma saboda dan danon shayin da yai min dadi ga kanshin kayan yaji na tashi a cikinsa haka na daure na shayeshi tas na aje kofin burodin daine banko kallesa ba.
Gabin na aje kofin yasa ta dago kai tana fadin ki kwanta ki dan huta ko jikin zai dan sake idan kin tashi na danyi wani rau rau sai naga tayi dan murmushi tana fadin baki sanni ba ko idan yaya Garba ne ai zaki sanshi ko ?
To ki sani in ma baki sani ba kaf gidan nan nafi kowa kusa dake wajen alaka don kakan mu daya da ya garba sune suka haifi iyayyen mu rashin sanina da bakiyi ba yasaki kasa sakin jiki dani ko ?
Jin hakan yasa na dukar da kaina kasa nasan ko wani halaka ke garemu ashe ba karami bane babbane tsakanin mu da ita amma a lokacin ba zance ko ita wacece ba a garemu.
Saidai jin kalamin bakinta yasa dole na kwata a makure adakin nata dayaji kayan alatun zamani a cikinsa irin na zamanin lokacin.
Barci nayi sosai duk da farko a tsorace nake ga hankalina yana wajen Dada datayi nisa dani a wanan katafaren gidan mai girma ta ina zanje Dada ko halimatu a wanan gidan mai dan karen girma.
Banina tashi ba sai wajajen yamma lis koshi itace ta tayar dani don magariba daya gabato a lokacin don haka ta tayar dani daga barcin dana dan samu nayi din.
Bandakin na koma ban fito ba saida na tsabtace mata shi gabin ba wani datti a part din kada bukuntana a dakin ya takura mata ko a gida kuma da bandakin mu yake na kauyawa muna yawan kula dashi balle nan din da yake na yan birnine garesu.
A gagauce nayi sallah la,asar wanda ba,a dadeba akai magariba sai bayan sallah isha,i naji umma tace dabi muje ta kaini wajensu Dada don taga hankalina na gunta.
A falo muka samesu zaune har baban kano din daya dawo daga kasuwa tare da iyalinsa dasu Dada din dasuke baki a cikinsu mun samesu a cikin raha da annashuwa koda Umma tayi sallama fuskan

Please Login or Register in order to submit comment