Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kauye, sai sajewa dasu nan bai zamo min wahala ba ina dai kokarin kafa kafa da yan kannena a lokacin duk inda nake idona nakai gashi suna kiran mu da sunan yan bararo.
Saboda hasken mu da zubin mu daya huda jinin mu na uwa da muke kama da bararo din wajen kama ga tsabta koda yaushe kafan mu da kumshi na lalle har hannuwa inna ke kumshe muna don ta saba da hakan tunna kauye itama hakanne ko yaushe a cikin kumshi take gata fara sai abin yake muna kyau daga mu har ita din indan anyi.
Baba yai shawara da yan uwanshi kan bokon mu suka bashi shawara ya jefani secondary kawai zaifi don ya mace make girman diya mace baida wahala a yanzu.
Aka kaini makarantar yan mata na jeka ka dawo inda yawancin yan gidan namu suke karatu an min uniform da safa da jakkan tare da littafai guda goma sha biyu nayi murna ranan barcima banyisa sosai ba don daukim in gani school din.
Washegari aka kaini aji daya aka ajeni a kauye kuma ina aji hudu ne na daina don ba daukan karatun da wani ma,ana mukayi ba a can talla ko aikin gida yafi karatu muhinmanci a wajen iyayyen mu mata damu.
Allah ya gani ina da ra,ayin yin boko a rayuwana saidai daukan da akewa wanda ke boko a kauyen mu yasa nima na bar zuwa bokon don da waka nake zuwa dashi nake dawow ga yara kamar mahaukaciya wanan yasa na tattara na daina bokon ina zaman gida tare da inna.
Ashe ina da rabo sai gashi nice ranan zaune a aji cikin yan bokon da nake mafalkin ganina a cikinsu yau gani garesu muna cudanya atare dasu a cikin aji.
Nayi kamar sati da farawa suma Aiaha aka kaisu boko suka fara zuwa tare muke tafiya dasu dawowane baba yake zuwa ya daukosu donsuyi kankanta da bin hanya.
Yawan shiga gidan Dada ina kai mata abinci yasa shakuwa ya shiga tsakanina da ita don muddin na shiga zan tsaya indan mata aiki diban ruwa shara da dan wanke wanken kayan ta daba wani yaw bane dasu kayanta kuma in dauko in kawowa inna ta wanke mata in an gam na wanke in kai matasu a nade kamar an goge.
Wanan yasa muka yi wani sabo da tsohuwan na sosai har yakai ta roki baba in dawo da zama a wajenta amma baba yasawa idonshi tankwa ya hana hakan .
Ya fake da cewa itace idon gidan Dada uwar tayi nauyi a yanzu ita ke taimaka mata da wasu aiyukan Dada tace gaskiyane kuma fa da can da nan ai kamar dayane tunda tana shigowa kullum .
A haka maganan ya shashance amma inna cewa tayi aida baba ya badani din ba komai ta dingayi da kanta gasu Aisha sai suna kama mata ai.
Baba yace ke dai bari fake min baya jiran biri abu ga hannun maishi shine abinsa zamani yanzu ya lalace gidan Dada gidan kowane ni ko shigan nan ba kasafai nake sonshi ba kinsan zainab ba wai ta gama wayewa bane haka.
Yarinyace har yanzu tunda ko goma bata idda rufewa ba barta a nan inda muke ganin abin mu yafi muna alheri a wanan zamanin inna tace hakane kumafa.
A haka har ubangiji ya sauke inna lafiya ta haifi danta kyakyawa mai zubin mahaifinmu sak nan yan barka suke ta shigowa gidan mu don Dada ta aikawa kowa a unguwa sun samu labarin haihuwan.
Dada mutumiyar arzikine sosai zakice itace ta haifi baban mu da cikinta yadda take manu nan ko kishiyar uwace matar mahaifinsane shima baba ya rileta tankar uwa a gareshi.
Nan a gidan mu tayi waya da wani danta da take kira da Alh ta sheda mashi zancen haihuwan ya saka albarka bayan haka da kwana biyu saiga baba ya shigo yana fadawa inna yayansa dake kaduna zaune ya tura masa da dubu hamsin yayi hidimar suna har ragon sunna.
Ranan muyi murna sosai haihuwan nan na mama ya jawo muna arziki a gidan mu zance don ta dalilin haihuwan baba ya gyarawa mama dakinta aka sayo mata saitin gado da mirror har da wardrobe a gidan dillaliya aka kafa haka yasa koda yan kauyen mu sukazo sun sha mamaki sosai a gidan.
Ganin waje lafiyeyayye mai kyau da daukan ido mama tambai sai kallon ikon Allah takeyi zancen baba Ado yana dawowa a zuciyar ta da yace kaiya ai kin masu silan takewa ke nan a rayuwansu don wani hassada takine ga mai rabo gashi ko ta gani.
Don yau innace zaune a gidan simiti da bugon kwano sun zama yan birni janta ya kara fitowa hakama yaranta sai wanan abin ya kashe mata jiki dama gulma ya kawosu katsina suka fake da sunan zuwa suna don suga kwam.
Ko haihuwan farko macen kauye tayi bata taba samun wanan abin arzikin da gatan da inna ta samu haka a kauye da wanan bakin cikin suka koma gida kowa na fadin albarkacin bakinsa a wajen.
Aikuwa wayen garin dawowansu labari har yabi gari sun kwaso karya da gaskiya suna bada labari a gari kowa da abinda yake fadi a bakinsa don sun kwaso saida suka cika akori kuran fam zuwa suna sunzo da sunan kwana baba ya hada baki da driver yace ba zai kwana ba jin hakan dole suka mike ba shiri suka bishi suka isa a cikin dare sosai garin.
Anyi suna lafiya an watse lafiya aka barmu mu kadai a gidan namu sai yayun inna su biyu don ba tafiyansu daya da tawagan kauyen mu ba zasu tsaya su dan kwana biyuwa inna a nan su kara ganin inda muke.
Don haka koda aka watse bansha wahala ba don aikin komai su sukayisa karshema gidan Dada naje sai yamma lis na dawo gidan na dan kama masu shara dana sama dayansu tanayi.
Akwai school don haka washe gari na shirya nida yan kannena muka nufi school bamu dawo ba sai biyu da yab mintuna na shigo gida tun daga nisa na hango mota a kofan gidan mu haka na shiga gida ina kallon motan dake sheki a cikin rana.
Tun daga soro nake jin wani kamshin turare har nayi sallama na shiga gidan a dan innuwan gidan na samu su baba da bakonshi saman sabon tabarman inna an shimfida masu suna zaune a kai.
Har kasa na gurfana na gaidasu sai naji mutumin na fadin kai yar tawa ke nan ashe ta girmane haka gaskiya Abdullahi kasa ka cutawa rayuwan yaran nan a kauye.
Wa yan nan kyawawan yaran masu kyau zaka aje a kauye ka cuci rayuwansu gaskiya da haka ya faru ba zamu yafewa kan mu ba ga hakan Allah ya taimakemu dai mun samu kun dawo garin nan gaba daya.
Ni dai na mike na nufi ciki na gaidasu inna nan na nufi dakina na kwabe uniform ganin bako a gidan yasa ban fito yadda na sababa don na wanke muna uniform din mu.
Muryan wanan bakon dan uwan baba naji tare da babana yana kwala min kira da zainab baba kuma yana fadin zainabu ke zainabu daga dakin na amsa da na,am baba da sauri na mike na nufo waje naji baba na fadin kizo baban ku zai tafi yana neman ki.
Kamar farko yadda na gaishesu ko wanan karon haka na zube a kasa gabansu ina fadin gani baba bakon yace yata zan tafi nace kizo muyi sallama ina sauran yan uwan nakine ?
Ya tambaya nace suna cin abinci nan ya fara magana yana fadin na fadawa babanki ki maida hankali ga karatu tunda ance kina da kokari don wata rana mukai ga babban likita mace ko wata babban office a cikin zurian anmu amma fa kinsan hakan bai samuwa saikin dage da karatu kada a yi wasa maison wanan matakin baya wasa da cikar burinsa sai ya dage.
Kaina fara dagawa kafin na bude baki da kyar nace to baba yana sa hannu a aljihunsa yace ina son muyi alfahari daku cikon yayan da zasu daga muna sunan wanan gidannamu ko bayan ranmune kamar yadda muma a yanzu muke alfahari da bazar namu mahaifin daya rasu.
Insha Allahu baba yace daga gefen shi yace ungo karbi wanan ki sayi duk wani abinda baki dashi a gidan nan na karatun ki ga babanku nan na fada masa duk wani abinda za ace za a bukata gun karatun ki ya sanar dani tunda nan kaduna nake zaune.
Kudi ya ban masu yawa saina kada kai alaman ya barshi akul naji yace dani ni babankine idan baki sani ba uban mu daya dashi tare kuma mukai karatu dashi zaria shiyasa kikaga munfi shakuwa dashi a cikin dangi kaf ni ashi haka muke kamar aminai ba zakice mu din wa da kani bane idan muna tare.
Jin hakan ga kuma baba a gefe yana wani irin murmushi yasa na mika hannu na karbi kudin daga hannun dan uwan baba din tare da fadin nagode baba cikin yar murya yace babu komai aike din diyatace halak malak ba godiya a tsakanin mu.
Jeki baba yace har lokacin fuskanshi yana dauke da murmushi na mike da sauri nabar wajen na shige gun inna dake daki da bakinta ganin sunanan dakin yasa na dunkule hannuna ban nuna mata kudin ba a lokacin.
Bayan kujeran inna na labe banda sakin jiki idan muna da bakon fuska a gidan mu har nakan kagara bako ya wuce ya barmu mu kadai wani lokacin don nakan ji na takura dayawa.
Inna taje sunyi sallama ta dawo dauke da dan jajiririnta a hannu wanda kayan jikinsa bani gajiya da kallonsu saboda kyau yadda aka saka kayan sabanin sakan mu na kauye dana saba gani ana sakawa yara acan.
Kwanan bakin biyu suka juya suka koma ba wasu dangin can bane ga inna kawai dai don sun fito nahiya dayane suke zumuntawa junansu a nan abin gwanin ban sha,awa idan ka gansu tare.
Gidan Dada na koma da zama da suke nan sai yamma nakan dawo nan gida in zauna don ban yarda kafe shidda yayi ina waje hakan yasa muka dayi sabo da yan matan dake yawan shigowa gidan Dada din hira da samun abin tabawa don baka raba gidanta da dan abinda diyanta suke aiko mata.
Wanan yasa yanzu da bakowa a gidan mu kona dawo daga school ina gida zaune ina dan aiyukan gida sai suka fara dan shigowa gidan namu wurina muna hira a nan ina aiyukana kuma.
Zasu girme min sa,adatuce sai Nabila amma haka muke kawancen namu dasu har yakai ko islamiya ko boko tare dasu muke jerawa mu tafi a wajen su nake jin komai daya shafi family wanda ni ban ma gama sanin yan uwa ba sai yanzune nake sanin wasu.
Nan nake jin ashe yawa garemu akwai wa yanda basu zaune a garin amma sukanzo gida jefi jefi tare da iyalansu lokacin sallah ko wani buki haka idan ya taso a family.
Zaman mu a nan cikinsu yanzu bazance zaman dadi bane yadda nake fadin su a,a zama daine yanzu wanda yafi muna na baya cikin yanci da sallama babu tsana babu tsangwaman kowa akan mu.
Zama na kasanni na sanka zama na cin gashin kan kai abinda kowa ya samu bakinsa saidai babu saka ido irin na kauye na lungun su wance kaza akeci ko kaza aka dafa yau.
Ko saka ido akan mu,amulan miji da mata don zaman babban gida irin wanda muka baro a baya zamane na kai mutum wuta idan bawa baiyi taka tsatsan da duniya ba a wanan zaman .
Gashi zamane na shagala kamar ba gobe sam ba mai kawo mutuwa a rayuwansa yace wai a,a bari nabar kaza a kwai mutuwa ko wani lokaci zata iya riskana saidai shagala da duniya ana dukar daji da kafafu.
Ban daki wurin wanka da bahaya daya ko biyu ansan tashin wace ansan sunyi sunna da mijinta mai kishiya akwai yan tayata gani suna saka mata ido a kishiyanta su zasu fada mata sunga tayi wankan tsarki ko sunga mijin yayi wankan asuba.
Duk damu da baba ya dan kebewa inna wuri bata tsira da hakan ba don sai kiga mace ta fado mata wai a san mata waje ta kewaya don gulma har yara suke turawa yin wanan laccan ga junansu.
Saidai ni dana dan tasa a cikinsu Allah ya kareni ga hakan don iyayyena basu yarda insha cikinsu ballema a koya min wanan akidan na babban gida babban bala,i.
Don da zaran aka fahinci mijinki yayi wankan tsarki baiyi a dakin kishiyarki ba aiki ya samu a gidan yanzu zancen boka da malam zai tashi aje kuma a zageki tsakar gida sai kin tsargi kanki da kanki kan hakan.
Idan kuma ke kadaine gun mijinki tofa nan ma ba,a barki ba za a sakaki gaba dasherin cewa kullun kina mane a kafadan namiji kin hanasa ya karo maki kishiya kin mallakesa kin hana wata tashigo itama taci arziki.
Wanan jahar su inna ke nan su akewa irin shaguben nan don duk ranan da aka ganta da sabon kaya zakiji an fara dama hakan take so taci ita kadai daga ita sai yayanta bata son wata tazo aci tare.
Saida baba ya tsaya tsakar gida ranan yai fada kan kewayawan da suke zuwa yi sashen mu sanan muka samu sauki saidai baiwai sun bar zuwan bane sukan faki idonshi s shigo su kewaya din don gulma.
Kai gaskiya zaman babban gida a kauye ba karamin fitina bana yasa ko baki da baki idan kin shigo dole bakin zai bude sai kiga yar karamar yarinya tana ciwa tsohuwa mutunci a tsakar gida gaban yayanta da kowa.
Nikan nayi barka naji dadi da Allah ya kadarta iyayyena suka taso dani don da karshensa a gidan aure zai kamani ace anyi auren hadi tsakanina da wani can a dangi.


ZAINB IDRIS MAKAWA
[1/16, 12:13] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON BIRI

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Yau weekend ne muna gida bamu fita school misalin shadayan rana ina kwance daki naji shigowan baki gidan hakan baisa na fito ba don naji muryan mazane ba mata ba.
Can naji muryan baba yana kwala min kira cikin daga murya na fito da sauri ina fadin baba gani yana zaune sun zagayeshi saman tabarman da suke zaune akai.
Yace kinci gidan ku bakiga yayyunki bane baki bakizo kin gashesu ba na dago kai na kallesu sau daya saboda kwarjinsu ina fadin sannun ku da zuwa ina wunin ku suka dago suna fadin lafiya lokaci guda.
Jeki ki kawo masu ruwa ya fada cikin bani umurni na mike ina tafiya cikin yanayina na yanga da tun ina fociciyata hakan nake tafiya wanda yanayin jikina yasa hakan sai wanda bai sani ba ya dauka yanga nakeyi.
A fakaice wasun su suka bini da kallo ruwan leda na dauko na dire a gaban su kafin na mike da zumar barin wajen muryan babane ke fadin dakata kinji kinga wanan.
Ina jin hakan na juyo na mayar da hankalina gun baba din dake magana dani naga ya nuna min na farko dake gefenshi yana fadin wanan dan babankine dake Kano zaune yanzune na wancan gidan na kusa da Dada din nan.
Wanan kuma dan kanwar muce Jummai matar babanku Ahmed dake Abuja wanan kanninsa ne data haifa a gidan babanki Ahmed din.
Baba na fadin hakan sai naga na farkon ya danyi kasa da kai ya lumshe ido a hankali kamar zancen bai masa dadi ba yadda baba ya fadi zancensa a gabana amma shima din mahaifinsa dan uwan mune saidai Allah ya karbi ransane tunda cikinshi.
Saida yayi min bayanin su kaf dinsu kafin ya barni in tafi suna ta hiransu dashi wanda yawan hiran tambayane yafi yawa da baba ke masu.
A lokacin na sulale daga gidan na faki idon su nafice zuwa gidan Dada don ganinsu a gidan mu yasa banda sukuni a lokacin duk na tsawala da ganin mutane a gidan namu kuma bakin fuska maza haka.
Na samu Dada ita kadaice agidan hakan yasa na dan saki jiki na debe hijjab fura ta miko min a wani kwanon shan silver mai marfi na girgiza kai ina fadin a koshe nake Dada nagode.
Tace ja,ira dama nasan ba zakici ba ai wanan mara yarda a bakuwa kike shigowa mutane ke a kullun kinki sakin jiki har yanzu da kowa kaf a dangi na dan turo baki ina fadin haba dai Dada akwai wanda nake sakin jiki dashi bayan ke kafin ta ban amsa na mike shara nayi mata na gyara dankin har tsakar gida kafin na dawo na zauna a kusa da ita muna hiran harira jikanta dake zama da ita datayi tafiya zuwa kaduna.
Anan mukaji sallaman su sunshigo gidan Dada din gaba dayansu yadda na barsu zaune a gidan mu din haka suka jero su hudu suka shigo gidan.
Farinciki naga a fuskan Dada din kafin ta fara tafawa tana fadin lale marhabin da bakin turai kune a tafe haka da rana tsaka ashe da rabon zamu gana daku kuma.
Koda yamma muka iso badai kin ganmu ba ina ruwanki da time din shigowan mu sai naga ta kwashe da dariya bakinta da goro ya bata mata hakora ya baiyana a fili.
Cikin dariyan take fadin ja,iri har yanzu dai kana nan a yadda kake ashe kai kam turai din baisa ka canza halin naka ba dama ance kada ka kara a yadda kasan halin mutum a baya.
Zama yayi a gabanta ya dora hannayesa bisa cinyarta yana dan murza gwiwanta din daya dora hannunsa a akai ta tureshi tana fadin ja,iri kaga kada ka karasa tsohuwar mutane don Allah.
Ka zama wani jibgege da kai kamar wani zaki nikan ma wanan karatun yayo a can ko zamancin abinci tana fada tana kallon yan uwansa da alaman tambaya a garesu.
Dariya ya kwashe dashi yana fadin nifa Dada nazaci kin mutu tuni don ko dan tsaraban goro ban riko da sunanki bani don na dauka ko kin bi mijin naki ashe kina nan gyagyau din ki baki tsufa ba.
Wani harara ta galla masa tana fadin da yake ni ba uwarka bace ai dole ka fadi hakan dadin abin dai akwai wanda suke son su ganni a cikinku koba haka ba ta kalli na gefenshi din sai ya murmusa yana dukar da kai.
Dariya ya fashe dashi yana fadin tsiyata da tsohuwar nan bata son mutuwa ko kusa yanzu da jin zancen mutuwa duk kinbi kin rude kina batun sakawa mutane kuka.
Allah sarki kaine dai baka sonta nikan ai yanzu a kullum zaman jiran nakeyi da fatan cikawa da imani a zuciyata .
A,afa Dada kada ki ganta a yanzu ki dinga kwala muna ihu kina fadin azo a taimakeki nan sauran suka kwashe da dariya Dada dai ta mike tana fadin ja,iri halin dai yana nan ashe bari na kawo maku farau farau ku jika makoshi kafin mu gaisa .
A,a Dada kibar wanan farau faraun naki kada kisa cikin mu tsatsa ni dai kan bazan sha wanan abin naki ba don haka dawo ki zauna muyi fira kawai na yaushe rabo.
Tsayawa iyan tayi tana kama baki kafin tace Ja,iri bakai kadai bane ai idan bakasha ba wani zaisha ai a cikinku ya kallo yan uwan nasa yana fadin to ku kunji da mai son shan tsatsan kwanonta a yanzu cikin ku?
Wanan kan kam anyi ja,irin yaro a nan ga yayyunka basuyi magana ba sai kaine da bakin iyawarka kake zuba haka ya dan dago ya kamo hannunta yana fadin Dada nifa naga kin koma min wata yar caras hakan nan ko kin fara zance da zawarawa suka kawo maki namane kika koma hakan wai.
Haba ta kama tana sallati kafin tace kaji min dan kawai ko to ubanka Amadi daya dawo garin nan ina kun sani dan albarka shine kullun ake dafo min nama a gidansa ana kawo min na tausa don gidan ku kaje kaima kaci a can din.
Ni kan ka isheni ka hana mu gaisa da yan uwanka muyi yaushe rabo dasu ta koma ta zauna dayan ya kalleta yace Dada ina farau farau din kinsa mun saka rai kin kuma zauna.
To na iya ja,irin nan ya fara fadan kwano da tsatsa zan halakaku da shi haka ta kallo inda nake tana fadin kinga Abule tashi hado masu ruwa a tulun nan mai sanyi da wanan sauran furan sai na dan kallosu a sace na kuma mike zuwa yin abinda ta sakani yi din..
Nakawo nake jin tana fadin yanzu kan tunda kun karasa karatu ai sai zancen aure ga yan mata a cikin dangi ko wanen ku a bashi anma gama magana akai yanzu gabatarwa ya rage a gareku.
A take fuskokinsu ya sauya kafin shi fitsararen nasu ya kalli tsohuwar yace ku baku da wani zance sai na aure karatun dama ko kammalashi ba ayi ba zaki daukowa mutane zancen aure daga mun shigo duban ki ki kawowa mutane zancen wani aure a yanzu kuma.
Yana fadin haka ya mike tsaye ya kallo yan uwa yana fadin ku sameni waje don Allah tama bata min da wanan zancen Dada ta waro ido waje ta dafe kirjinta tana fadin shu,umi ba dai ka manta alkawarin malam akan ku bane tun yanzu.
Dona ambaci auren zaka dauki zafi dani da ba,a aure za,a haifekane dan kawai koba aure ya haifeka ba kai .
Ya kallo tsuhuwar yace ko zaki maidani ciki tunda kinyi bakin ciki a yanzu nazo duniya ta hanyar aure to ba zanyi ba ku rike duk yar da zaku ban na yafe akaiwa wani.
Nifa bari kiji Dada ba wanda zaimun wanan auren hadin naku na gado tunda ba Allah da Annabi sukace kuyiwa yayan ku hakan ba balle kizo min da wanan zancen daga saukana gari ko ruwa bansha ba na huta.
Yana fadin haka ya fice ta fara salati tana tafa hannaye kafin ta fara kuka irin na tsofi tana fadin kaji min dan kawai har yanzu ashe iskancin nasa yana nan yadda ya barmu girma baisa ya bar wanan halin nasa ba.
Sauran hudun suka kwashe da dariya suna fadin barshi Dada yayi maki hakan ne don kiji tsoro amma ai ba hakan halinsa yake ba inma haka yake ai zai hadu da uban nan kune ida yace shi dan banane.
Ina makure ina kallonsu kafin

Please Login or Register in order to submit comment