Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_


.......*_WASHE GARI_* kamar yanda na saba na tashi nai ayyukana da sauri-sauri. Ana idar da sallar asuba nai wanka. Breakfast ɗin Yaya Musaddiq na ɗauka na nufi kai masa kusan bakwai da rabi. Nako samu har ya kammala shiryawa. Tunda na shigo yake bina da kallo, basai nace komai ba nasan ya gama fahimtar yanayina ne. Amma sai na dake. Sai dai ina gaishesa maimakon amsa min tambaya ya jeho min. Baki na buɗe zance babu komai yay saurin ɗaga min hannu da faɗin, “Karma kimun ƙarya. Faɗamin mike damunki?”.
      A hankali hawayen da nake riƙewa suka silalo. Nima babu shiri na silale ƙasa ina mai fashewa da kuka. Duk abinda ke a raina tun jiya ne ya samu damar fitowa. Kafin ma ya sake cewa da ni komai na shiga faɗin, “Yaya kisan kai yayi. Da idona na gansa yana zare wuƙa a jikin mutumin ga jini face-face. A kunnena naji yana faɗin akai gawar wani anguwa a ajiyeta.....”
          A cikin matuƙar tashin hankali ya katseni jikinsa na rawa. “Waye wai? Ki min magana a buɗe Samraah Please wa aka kashe waye kuma yay kisan?”.
    Maimakon bashi amsa sai na miƙa masa wayata kawai. Amsa yay da rawar jiki. Yana ko dannawa da video ɗin ya fara cin karo dan ni bana sakama waya password sam. A matuƙar birkice ya ɗago yana kallona tun a fara kallon video ɗin. Idanunsa a warwaje na shiga razana ya furta, “Samraah Maash fa?”.
      Kaina na jinjina masa da sauri ina faɗin, “Shi yaya! shi! Mutumin nan azzalumi ne bana kirki bane kamar yanda duniya ke kallonsa. Zata iya yiwuwa ma kuɗin nasa bana ALLAH bane na jinin mutane ne”.
     Tuni zufa ta wanke Yaya Musaddiq. Cikin tashin hankali ya ce, “Bayan ni wa kika faɗamawa?”.
          “Mansoor ne kawai Yaya. Tun jiya nace mu kai ma hukuma video ɗin amma ya hana. Shine ma yace na baka ka gani dan mu haɗu da shi a gareji mu tattauna”.
     “Gara daya hanaki Samraah. Dan dole wannan al'amarin na buƙatar nazari. Maash ba anyhow mutum bane da dokar hukuma zatayi tasiri akansa cikin sauri. Inaga yanzu ba zama zamuyi ba tashi mu wuce. Bara na kira Mansoor ɗin ya fito shima gara muyi abinda ya dace da wuri tun kafin ya bar garin nan. Dan bai zama lallai a sake samun irin wannan damar ba duk da naji ya amsa miki wai kiyi hira da shi. Ga gari nan duk ya ɗauki zance harda masu faɗin ba haka kawai kikaje masa ba akwai asiri saboda yanda ya amsa ɗin babu musu a gaban duniya. Amma ni zuwa yanzu na fara zargin akwai wata a ƙasa kam, bana raba ɗayan biyu ya ganki sanda kike ɗaukar video ɗin nan, ko kuma ta cctv, dan Company kamar nasa dole asamu camaras tako ina”.
        Idanu na waro sosai na matuƙar mamaki, Yaya Musaddiq ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. “Samraah duk mai hankali dolene ya gane akwai dalilin Maash na amsa miki gayyatar da kikai masa cikin sauƙi. Dan bazai taɓa zama ya amsa miki bane kawai saboda kin jera masa tambayoyi. Kai ina dolene ma ya ganki fa, ya barki ne kawai bisa dalilinsa, sannan yazo a bainar jama'a ya amsa zaiyi hira dake, hakan na nufin akwai wani abu da yake ƙullawa”.
         Sosai na zubama Yaya Musaddiq ido, dan tabbas zancensa yasa na fara dawowa cikin hankalina yanda ya kamata. (Humm you are vary smart girl) kalmar daya fara ambata a kaina kenan. Tabbas wannan mutumin terror ne na gasken-gaske. Shin mi yake ƙullawa? Dan dolen dole akwai abinda ke ransa kamar yanda Yaya Musaddiq ya faɗa. Kai ina buƙatar ganin ma program ɗin jiya gaskiya.....
    “Kinga tashi muje, ba lokacin tunani bane yanzun”. Yaya Musaddiq ya faɗa cikin katse mun tunani. Miƙewa nai babu musu, dan basai na koma cikin gida ba dama....

       

       🤙❤️🤙❤️🤙❤️

   A ɓangaren Maash asubar fari ya farka, da ƙyar ya iya tashi saboda gaɓɓansa duk ciwo suke masa. Ruwa ya fara watsawa ya fito a gurguje ya kimtsa cikin wando da rigar polo. Koda ya fito su Hayatu suma har sun fito zasu wuce massalacin. A tare suka fita, bayan an idar da salla bai koma cikin gidan ba yace ma Tijjani ya fito da mota zasu je wani waje. Da sauri Tijjani ya shiga ciki, babu jimawa ya fito da mota, suma guards ɗinsa suka fito. Komai baice ba Hayatu ya buɗe masa baya ga shiga, shi kuma ya shiga gaba kusa da Tijjani. Jihar Jigawa suka nufa, a wani ƙauye dan akwai business ɗin da zai yi a wajen. Duk da dai da farko bai wani ɗauki abin da muhimmanci ba, sai da zasu je massalacin nan ne Hayatu ke sanar masa mutumin da zasuyi kasuwancin ya kira, kuma yana son suje da wuri ne.
       Yinin ranar guda a Jigawa suka cinyesa. Ko abinci bai sakama cikinsa ba garama su su Hayatun. Sai Black tea kawai yake faman sha kasancewar duk inda yake yana tare da flaks ɗin ruwan zafinsa a mota, sai kuma chocolate dan mayenta ne da haɗaɗɗun biscuits. Sai bayan la'asar suka dawo cikin Kano a matuƙar gajiye. Musamman ma shi duk da dai yaci chocolate sosai amma yana buƙatar dafaffen abinci, dan rabonsa da dafaffen abinci sosai tun shekaran jiya a Lagos. Ko zama a falon baiyi ba ya wuce bedroom, suma dai su Hayatun duk a gajiye suke, dan haka kowa ya nufi sashensa danya watsa ruwa. Bathtub ya cika ra ruwan ɗumi sosai sannan ya shiga ciki, sai da yaji ko inansa ya miƙe sannan ya ɗauraye jikinsa ya fita. Duk yau sau ɗaya kawai yay waya da Ummien sa. Ji yake duk kewarta ta damesa. Sai dai yanzu yasan koya kira bazai samu ba dan ba lokacin kira bane dan sallar magrib aketa kira. Shiri yay tsaf cikin kaya marasa nauyi. Ya baɗe jikinsa da turare sannan ya saka slippers da ke ajiye yay ficewarsa.
       Tun kafin ya ƙarasa fitowa cikin falon Hayatu dake zaune yana jiran fitowarsa ya miƙe da sauri. Dan tun ɗazun ya dawo daga wanka da yaje yayo shima a sashensa. Ya dawo ne da wuri akan batun cctv footage na jiya, dan yana ganin ya kamata su duba issue ɗin kar a samu matsala. Kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kansa, sai kuma ya nufi ƙofa a taƙaice ya ce, “Kayi alwala”.
       Cikin girmamawa Hayatu ya amsa da “Okay Sir”. Sai kuma ya saki murmushi yana mai binsa da kallo. A duniya boss ɗinsa da banne. Mutum ne mai abubuwan ban mamaki daban-daban. Ba kuma zaka tabbatar da hakan ba sai ka kasance a makusancinsa. ALLAH ya azurtashi da ni'imomi da yawa a rayuwa. Gadai ƙyawu kamar shine ya zana kansa. Ga dukiya, ga ilimin addini dana zamani. Yanada ƙyauta ga duk wanda ke tare da shi. Sai dai kuma hatsabibin kansa ne baifa mutunci a wasu fannin. Dan wani irin mutum ne a hagungunce da zaka iya ɗaukar lokaci baka fahimci alƙiblarsa ba. Ga taurin kam masifa da baƙar zuciya. Baya ragi ko ragowa ga duk ubanda yace masa kule. Yakan karya yatsar duk wanda ya nunashi dan baya ƙaunar raini. Shifa ko'akan business ana lallaɓa abokan harƙalla dan su dawo shi a garesa bai san wannan ba. Kana kawo masa hauka zai cireka a sabgarsa kawai. Sai dai baka isa tabbatar da waɗan nan halayyar tasa ba kai tsaye sai ka shigo gonarsa. Dan sumumu kasaune shi _*MACIJIN SARI KA NOƘE_*. A zahirinsa zaka ɗauka mutum ne mai sanyi da nuna halin ko'in kula, sai dai a kowanne motsi na cikin rayuwarsa a ankare yake. Domin indai brain ce ALLAH ya bashi. Irinsu ne ke juya akalar abubuwa a ƙanƙanin lokaci da kwanyarsu.....
        Firgigit ya dawo hayyacinsa jin kiran sallah. Da sauri ya shiga toilet ɗin falon ya ɗauro alwala ya wuce masallacin shima...

      Bayan idar da sallar isha'i suka shigo gidan. Sai dai Hayatu da Tijjani drivern sa sun rigashi shigowa. Dan su duka suna a gidan har baturiyar nan. Sai dai kowannensu yana a mabanbancin masauki da sai in shine ya buƙaci ganinsu zasu ganshin. Kusan mintuna goma suna a ƙaton compound ɗin gidan da ga jikin motoci suna hira sai gashi ya shigo shima. Ya ɗan dakata yay magana da masu gadi da suka kasance ƴan sanda har su uku sannan ya ƙaraso inda suke. Duk nutsuwa sukai kawunansu a ƙasa, baice da su komai ba ya wuce inda lafiyayyar ƙofar shiga sashensa take. Dan ta gilashi ce mai tsananin ƙyau da ɗaukar idon mai kallo. Gata golden daga waje sai walwali take kamar wani zinaren gaskiya. Da sauri Hayatu dake biye da shi ya buɗe masa ƙofar. Harararsa ya ɗan yi, Hayatu ɗin ya duƙar da kai ƙasa yana murmushi dan yasan laifinsa akan buɗe ƙofar ne tunda yana hanasu. Har ya shiga ya ɗan waiwayo. Driver dake ƙoƙarin komawa da baya ya dakatar ta hanyar faɗin, “Tijjani!”.
     Da sauri Tijjani ya amsa masa da “Na'am ranka ya daɗe”.
    Komai bai sake cewa ba ya cigaba da tafiyarsa ciki. Dan haka duk suka bisa. Duk da garin ba zafi ake ba, ba kuma sanyi ne mai tsanani ba dan ya fara bankwana falon a ƙanƙare yake da sanyin raɓar ac. Ga wani ƙamshi na musamman daya gaurayu da turarensa tamkar ba a jiya ne ya fara rayuwar cikin gidan ba. Zaune ya kai saman 3sitter. Kamar yanda ya saba zaman ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yanzun ma hakan yayi. Shiru kamar mai nazarin wani abu sai kuma ya ɗago yana ma Hayatu nuni da remote dake a Centre table. Remote ɗin Hayatu ya ɗauka da sauri, dan ko ogansa bai magana ba yana saurin gane karatun shirunsa saboda da hakan ya horesu tun farko. Dan shi bamai yawan magana bane sai idan shine yaso hakan da kansa. Sai kuma idan yana a gaban mahaifiyarsa ko mahaifinsa, shima a wasu lokutan ne yake hakan, sai ko Ammie. Volume ɗin tvn ya sassauta tare da canja tasha zuwa inda yasan yafi yawan kallo a irin wannan lokacin. Tasha ce ta addini, sai dai suna gabatar da duka programs ɗin su ne da turanci, hatta da wa'azi kuwa........✍️
        


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_


.......Gyaran murya ya ɗan yi idonsa akan Tijjani. Cikin sauri Tijjani da idonsa ke akan tv ya maido hankalinsa garesa. Kafin ma yace wani abu cikin muryar nan tashi kamar ta rowa ya taresa da faɗin, “Ina za'a samu abinci mai tsafta?”.
       Cikin girmamawa Tijjani ya ce, “Ranka ya daɗe akwai gidajen abinci masu inganci dake tsaftace abincinsu sosai a garin Kano. Harma da masuyi a cikin gidaje sai dai kawai ai order suna da masu delivery da zasu iya kawo maka har inda kake, ko aje a amso”.
       “Good. Sai ka samo duka gidan. Ka tambayi kowa abinda yake buƙata”
     “In sha ALLAHU yanzu kuwa ranka ya daɗe”.
   Bai sake cewa komai ba ya maida idonsa a television dan an fara gabatar da program ɗin da yay zaman kalla. Hayatu ne ya miƙawa TJ kuɗi masu yawa. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Nidai jallop rice da ƙirjin kaza nake so.”
      Dariya TJ yayi ƙasa-ƙasa yana ƙumshe baki dan karta fito. Sai kuma yayma Hayatu nuni da ogan nasu da ido. Kai Hayatu ya jinjina masa yana sake gyara nutsuwarsa da maida hankalisa garesa ya ce, “Sir za'a karɓo maka kaima ko?”. Shiru kamar bazai tanka ba, dan yamayi biris tamkar baiji ba. Sai kuma batare da ya kallesu ba ya ɗan kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai shegen ƙyau. Ya ɗan yamutsa fuska da jan siririn tsaki. “In dai bazai jima ba a samo min tuwon semo.. miyan kuka”. A tare suka amsa da girmamawa. TJ ya fita da hanzarinsa dan sun san baya cin abincin dare late, wani lokacin ma bai fiya ci ba. Yau ma suna ƙyautata zaton dan baici komai bane tun black tea ɗin safe. Haka yake abinci bai damesa ba, shiyyasa ga shi nan ko kaɗan baida wani tunbi, jikin ma badan yana haye-hayen waɗan nan tarkacen machines ɗin na motsa jikin zamani ba da zai kasance ne falen-felan.
TJ na ficewa Hayatu ya katse tunaninsa tare da matsowa inda yake. Da ga tsayen da yake kamar soja ya ɗan rissina yana fito da flash da ga aljihunsa da faɗin, “Sir ga cctv footage ɗin an samo”. Juyowa yay ya ɗan kalli Hayatu ɗin a yanayin jin daɗin hakan. Sai dai kuma ko kaɗan fuskarsa bata nuna komai ba tana nan a ɗaurenta tamau. Kujera ya nunama Hayatu. Zama yay yana ɗaukar laptop dake a Centre table ajiye ya saka flash ɗin jiki. Kafin ya miƙe yaje har gabansa batare da yayi playing video ɗin ba. Ajiye masa yay a stool ɗin daya jawo a hankali gabansa sosai. Sannan ya zauna a saman carpet kusa da ƙafafunsa yana shiga inda folders ɗin videon suke. Duk zubama screen ɗin laptop ɗin ido sukai. Cikin ƙwarewar aiki Hayatu ya zaluƙo video ɗin sashen da abin ya faru, tare da dai-daita lokacin da komai ya faru sai dai baiyi playing ba ya ɗan ɗago ya kallesa.
         A hankali ya furta, “Kunna”.
    Kunnawar yayi. Ko'ina ya fara nuna shiru babu kowa babu motsin komai. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai ga Samraah na bubbuɗe ƙofifi bayan ta fito da ga wani lungu da suka san restrooms na ma'aikatane a wajen. Yanda take taɓa ƙofofin tana ɓata fuska kamar zatai kuka zai baka tabbacin ta ɓata ne. Can cikin takaici ta fincike face mask ɗin fuskarta. Ƙyaƙyƙyawar fuskarta da babu zanen komai na kwalliya ta bayyana. Hayatu dai ya gagara haƙuri sai da ya furta “Masha ALLAH” a hankali. Dan ko makaho ya laluba fuskar Samraah yasan yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, duk dama eyeglasses ɗinta har lokacin yana a idanunta shi bata cire ba. Isowarta ƙofar da suke ciki ya sanya Hayatu waro idanu sosai, sai dai bai iya cewa komai ba. Ta buɗe ta ɗan leƙa. Sai kuma tai baya a rikice alamar akwai abinda ta gani. Wayarta data zaro tai danne-danne ta kanga tabbacin video take musu yasa Hayatu kasa haƙuri ya furta, “What! Sir itace kenan?”.
       Bai samu amsa ba, dan ogan nasa ko motsi baiyi ba har sai da ya kai ƙarshe. Fitowarsa, tsintar nurse mask. Har cigaba da video da Samraah tayi sanda suke fita da gawar mutumin. Cikin ƙanƙanin lokaci Hayatu ya gama haɗa uban gumi kamar wanda ke a filin kokawa. Shi kam duk da a birkice take video ɗin yaga matuƙar ƙarfin halin yarinyar nan. Motsin da ogansa yayi yasa hankalinsa dawowa jikinsa. Ya ɗan ɗago ya kallesa. Sai da gabansa ya faɗi ganin yanda cat eyes ɗinsa suka canja launi. Dan gaba ɗaya gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama ƴar siririya exactly yanda na mage suke komawa idan suna a cikin haske. Batare da ko kallon Umar ɗin ya sake yi ba ya miƙe ya fara tafiya. Sai da yaje gab da ƙofar bedroom ɗinsa sannan cikin dakiyar muryar dake tabbatar da ransa a ɓace yake ya furta, “A nemota duk inda take. A cigaba da bin duk wani motsinta daga nan zuwa sati biyu”.
        “An gama Sir. Amma in baka manta ba ka bata damar yin hira da kai ma”. Hayatu ya faɗa cikin tsumar jiki. Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shigewa da yake yi kamar mai nazari, sai kuma batare da ya juyo ba ya furta “Zanyi tunani akan hakan”.
Buɗe baki Hayatu yay zai sake magana cikin nuna gamsuwa, sai dai harma ya riga yay shigewarsa shi. Hayatu ya rabga tagumi tare da faɗin, “Tab ƙyaƙyƙyawa kin shiga uku wlhy, bama ke ba duk zuri'arki kin sakasu a masifa. Ke miya kaiki shiga gonar da bataki ba. Aikata wannan aikin da ba'a sakaki ba, karanbaninki ya ɗebeki shiga fadar sarkin aljanu. Dan oga ALJANI ne irin ifiritan nan.” yana cikin wannan sambatun nasa TJ ya shigo da ledoji masu ƙyau an musu tambarin gidan abinci. Firgigit Hayatu ya dawo hayyacinsa tare da gyara yanayinsa. TJ da ma bai wani lura da halin da yake a ciki ba ya ajiye masa tasa ledar sannan ya ajiye wata a Centre table yana faɗin, “Wannan tuwon oga ne. Shi na tsaya ma sai da akayisa yanzu-yanzu gashi nan da zafinsa yanda zai masa daɗin ci.”
        “Ai wannan tuwon mawuyacine ya samu shiga kuma yanzu”.
    Idanu TJ ya waro a rikice ya furta, “Na shigangaɗi Hayatu badai na makara ba? Wlhy babu tuwonne amma matar tace zatayi da sauri tana da miya. Ni kuma naga tunda yace yana buƙatarsa yana so ne shiyyasa nace tayi da sauri...”
      “Kai ka kwantar da hankalinka badan ka daɗe bane ba kawai dai wani abunne daban ya ɓata masa rai. Amma bari na gwada faɗa masa ka dawo mugani”.
     Ajiyar zuciya TJ ya saki, duk da kuwa yanayinsa bai warware ba. Dan in har ogan nasu na cikin ɓacin rai ko damuwa suma sukan shiga matuka saboda yanda suka ɗauki al'amarinsa da matuƙar muhimmanci a rayuwarsu. Tashi Hayatu yay ya nufi hanyar bedroom ɗin nasa, sai da yay jimm a tsaye bakin ƙofar kafin yay knocking a ɗarare. Ko motsi ba'aiba, bai gajiyaba ya sake yi tare da sallama. Nan ma anja kusan minti ɗaya kafin ya amsa masa a daƙile. Sake nutsuwa Hayatu yay kafin cikin dauriya ya ce, “Kayi haƙuri Sir, dama TJ ne ya dawo, a kawo maka abincin nan ne”.
        “No! I'm okay”.
    Shiru Hayatu yay cikin nuna damuwa ƙarara a fuskarsa. Sai kuma ya sake raunana murya ya ce, “Please Sir, duk yau fa bakaci komai ba. Ko nace ma rabonka da abinci tun shekaran jiya a Lagos. Abu mafi saka Ummie damuwa a rayuwa shine ka kwana da yunwa. Dan ALLAH ko kaɗanne ka daure kaci, saboda nasan duk da bata tare damu zata ji a jikinta kamar yanda ta saba”.
      Wani irin cizar lips yay da ga zaunen da yake a bakin gadon hannunsa dafe da kansa. Hayatu ya matuƙar sanin lagonsa a rayuwa. Dan shine kaɗai yake iya bi da shi fiye da kowa bayan mahaifiyarsa. Hakan kuma nada alaƙa da sanin da yay masa tun ƙuruciya. Duk da dai shi ya girmi Hayatun da kusan shekara biyar ma, amma kasancewar sun tashi ne shi da iyayensa a cikin gidan kakansa da ya haifi Ummien sa yasa yay masa farin sani na gaske. Ya jima a gurin kamar bazai motsa ba sai kuma a daƙile ya furta, “Kawo nan”. Cikin sauri Hayatu yabar jikin ƙofar cike da farin ciki bawan ALLAHn kamar cikinsa zai kai. Babu jimawa kuwa sai gashi da tuwon. A can ya shirya masa shi saman table ɗin gaban sofa dake bedroom ɗin, har lokacin kuma yana a zaune bakin gadonsa hannunsa dafe da kansa. Yanayi ne dake nuna yana cikin zafin rai, dan Hayatu ya sanshi a rayuwa fiye da tunanin mai tunani. Ganin Hayatu ɗin baida niyyar fita yaja siririn tsaki yana ɗagowa, harararsa yayi da faɗin, “Ka tsaya gadi na ne sai naci ka gani?”.
         Ƙasa Umar yayi da kai yana ɗan murmushi. Sai kuma ya rissina tare da faɗin, “Ayi haƙuri Sir”. Daga haka ya fice a ɗakin. Wani tsakin ya sake ja sannan ya miƙe zuwa gaban sofa ɗin ya zauna. Hatta ruwan wanke hannu Hayatu ya tanadar masa. A nutsensa cikin yanayinsa na rashin gaggawa akan komai ya fara cin tuwon dan yana son tuwo sosai saboda fevorite food ɗin Ummien sa ne, ada sanda yana yaro idan tayi tace sai yaci yakan zauna yayta kuka shi bazaici miyan daddawa mai wari ba. Amma bayan wani lokaci da rayuwa ta canja kanta zuwa abinda bai taɓa mafarkin riska ba a cikinta sai ya maida tuwon fovorite nashi shima. Yaci kusan rabin malmala ɗaya ya ajiye duk da kuwa tuwon ya masa matuƙar daɗi,  sai dai bai cika son cin abinci late haka ba. Shiru ya ɗan yi zaune a wajen kafin ya tashi zuwa toilet. Brush yayi da sake gyara jikinsa ya fito. Ya samu Hayatu har ya shigo ya tattare komai harda sakama ɗakin freshener ya ƙara dai-daita masa ac. Komai baice ba ya rage kayansa zuwa na barci, sai dai maimakon kwanciyar zama ya sake yi a sofar yana ƙoƙarin kunna laptop ɗinsa, dan yana son ƙarasa harƙallar wani business ɗinsa kafin ya kwanta. Dai dai kuma mi hakan kamar neman gagararsa yake. Dan tunda ya kunna ya gagara danna ko keyboard ɗaya tunaninsa ma neman tafiya yake wani sashe daban. Da ga ƙarshe dai ya ture laptop ɗin gefe ya ɗauki wayarsa. Wata number da aka saka Dude ya nemo tare da danna kira.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)


_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_

......Kusan lokaci ɗaya muka iso garejin da Mansoor. Dan haka babu ɓata lokaci muka nufi cikin motarsa, dan nan ɗin zaifi mana zama sirri fiye da ko'ina saboda abinda zamu tattauna ɗin. Gaba Yaya Musaddiq ya shiga ni kuma baya. Sun gaisa da Mansoor cikin mutunta juna kamar yanda suka saba nima na gaishesa. Amsawa yay idanunsa a kaina ta cikin mirror.
       “Ya kamata ki huta da kukan nan Samraah. Sai kace kece kika aikata laifin nan. Kinga kuwa yanda idanunki suka koɗe”. Mansoor ne yay maganar cikin nuna damuwa matuƙa. Yaya Musaddiq dake saurarensa ya ce, “Ai ita haka take bata bin al'amarin rayuwa a hankali ka ganta nan. So take sai ta jama kanta wani ciwon muma ta sake sakamu a wata damuwar sannan”.
     Idanuna na cikowa da hawaye na ce, “Kuyi haƙuri Yaya ba haka bane. Wlhy na kasa mantawane da ganin gawar kawai. Amma in sha ALLAHU bazan ƙara ba”.
    “ALLAH yasa hakan” Yaya Musaddiq ya faɗa. Yayinda Mansoor yaja numfashi ya fesar tare da amsawa da Amin. Idanuna na share tare da ƙoƙarin yin magana wayar Mansoor ta shiga ruri. Tamkar an saita sai tawama ta fara. Kusan a lokaci ɗaya duk muka kai hannu domin ɗauka. Sai kuma muka kalli juna tare da sake ɗagowa duk muka kalli Yaya dake tambayar mu “Lafiya kuwa?”.
        “Daga office

Please Login or Register in order to submit comment