Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_


........Daga ajiye Samraah gida ya wuce shima. Sama-sama ya amsa gaisuwar maigadin su ya shige ciki. Shi da ɗan uwansa a duk sanda suka dawo gida idan sun fita sukan fara shiga sashen iyayensu ne, musamman ma shi da akance yanada ƙulafucin uwa. Amma yau sai hakan ya gagara garesa. Dan ko motar tasa yau a gab da sashensu ya ajiyeta. A falo ya samu yayansa kwance cikin kujera yana kallo, hannu kawai ya ɗaga masa nan ma yay shigewarsa ɗakin barcinsa. Da kallon mamaki Attahir ya bisa. Dan abune da bai saba gani ba. Amma sai ya ɗan girgiza kai da sake maida kansa ga tvn da yake kallo, zuciyarsa na ayyana masa maybe ya gaji ne. Ya cigaba da kallonsa da tunanin idan yay wanka ai zai fito ya nema abinci, amma shiru kake ji har magrib na neman yi. Tsam ya miƙe ya nufin ɗakin nasa, ya ɗanyi knocking, kafin ma a amsa masa ya tura ya shiga.
A tsaye ya samu Mansoor na faman kai kawo. Yay masa kallon tsaf sannan ya ce, “Kai wai lafiyarka ka kuwa? Ka dawo ma mutane kana ɗacin rai ka kuma shigo ka rufe kanka a ɗaki. Ko har ka fara tunanin auren ne? To bakai kace kana so ba, kama jirani kayi tsalle ka dire kai ba haka ba.....”
Ganin Mansoor bai maida masa murtanin tsokanar ba yasa Attahir yin shiru, gabansa ya ƙarasa tare da dafa kafaɗarsa. Cike da kulawa ya ce, “Baka da lafiya ne Kiddo?”.
Kai Mansoor ya girgiza masa.
“To mike damunka?”.
“Yaya babu komai fa. Kawai bana jin daɗine”.
Jimm Attahir ɗin yay yana kallonsa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Okay shike nan. Shiga bayi kai alwala mu wuce massalaci. Dan kar Dad yay zaman jiranmu”.
Kai kawai Mansoor ɗin ya jinjina masa yana nufar bayi. Attahir ya bisa da kallo har sai da ya shige. Shima kaɗa kansa yay ya fita yana ji a ransa ƙarya Mansoor ɗin ke masa. Duk da shi mutumin ne mara son hayaniya. Amma idan suna tare baka banbance wannan halin nasa na rashin yawan magana. Dan suna rayuwa ne tamkar abokai ba wa da ƙani ba. Sun tashi ne kamar ƴan biyu, komai nasu a tare yake. A halayyane kawai zaka iya banbance su. Dan tabbas sun banbanta tanan ɗin.

Koda suka fito domin tafiya massalacin sun gamu da Dad ɗin su. Shima dai da mamaki yake kallon Mansoor ɗin. Harma ya gagara haƙuri ya ce, “Kai dama ka dawo gidan kabar Mamanku natama mutane shelarka?”.
Kan Mansoor a rissine ya ce, “Dad amin afuwa na dawo ne kaina namun ciwo”.
“Dole kai ciwon kai ai wannan hidima da kuka sha. Ku muje massalaci za'a tada salla”.
Binsa sukai gwanin sha'awa suka fita har maigadi. Koda aka idar da sallar ma basu fito a massalacin ba har akai isha'i. A tare yanzu ma suka dawo gidan, kai tsaye ainahin sashen gidan suka nufa su duka. Sashene babba kuma mai ƙyau, dan komai yaji na ababen more rayuwa. Lallai gidan su Mansoor suna da kuɗi suma ba laifi. Dan idan wani ne ma zai iya cewa yafi ƙarfin aikin da yake yanzu, duk da kuwa yana a babbar kujera ne. Amma kuma aikin jarida hubby ɗinsa ne tun yana yaronsa. Sannan mahaifinsa nada babbar alaƙa ma da wajen aikin nasu, dan yanada hannun jari mai ƙarfi a cikin companyn. Shigowarsu dai-dai da fitowar ƴammata biyu masu kama da su Mansoor ɗin sosai daga wani ɗaki. Cike da murnarsu suka nufo Mansoor ɗin suna masa sannu, sai jera masa tambaya suke akan Maash. Amma a mamakin kowa ko a yaƙi ya furta, sai ma zagayesu yay ya wuce saman kujera ya zauna yana faɗin, “Malami kun isheni da surutu”.
Babbar ce ta ɓata fuska tana kallon Dad ɗin su. Ya ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar sunfi kusa. Sake ɓata fuska tai sosai. Ta ce, “Dad kallafa yanda yake basar da mu. Shi dama Yaya Man idan baiso abu ba ya iyama mutane wulakanci”.
“To yayi fitinanniya.”
Wata mata dattijuwa ta faɗa tana fitowa a hanyar dake tabbatar da kitchen ne, itama dai kama take sosai da su Mansoor ɗin. Hararar yarinyar tai da nuna musu hanyar data fito. “Ku wuce kuzo ku fiddo abinci. An gaya muku kowama irinku ne da shegen surutu. Yaro yaje aiki ya gaji kun wani sashi gaba dolene sai ya baku labarin abinda ya farun? Idan son gani kuke miya hanaku zuwa”.
“To an taɓa ɗan lelen Mamy”.
Cewar Attahir na ƴar dariya. Murmushi Dad shima yayi, yayinda Mansoor ya miƙe ya nufeta yana harar Yayan nasa. Yana zuwa gab da ita ya bata side hug, tare da kamo hannunta ya sumbata. A marairaice ya ce, “Mamy barsu kada ma kanki yay ciwo”.
Kansa ta shafa fuskarta da murmushi. Kafin cikin kulawa ta ce, “Yaushe ka dawo?”.
“Tun ɗazun ya dawo yau baya yayinki ne kawai Mamy”.
Attahir ne ya faɗa yana kaiwa zaune a kujerar dining dan su Islam sun kammala jera abincin. Hararsa Mansoor yayi, tare da faɗin, “Mamy ƙyalesa so yake kawai ya haɗamu. Kaina fa ke ciwo amma nasha magani”. Yay saurin faɗar haka ne dan yasan yanzu zata iya ruɗewa. A hakanma tuni fuskarta ta nuna damuwa. Dan sai tattaɓa kan nasa take, daga ƙarshe dai ta ja hannunsa suka koma saman dining ɗin tana jera masa sannu, abincin ma a baki ta bashi dan kowa yasan ɗan gatan ta ne a gidan. Daurewa yay kawai ya ɗan ci abincin dan karta damu, amma gaba ɗaya hankalinsa na'a kan Samraah, babu abinda zuciyarsa ke hango masa sai yanda take a firgice har sanda ya ajiyeta a gida.....


Bayan sun kammala cin abinci duk yanda Mamy taso suyi hira Mansoor bai cewa komai, zata nuna damuwa Dad ya dakatar da ita akan ta barsa yaje ya huta dole akwai gajiya. Mansoor yaji daɗin samun wannan damar, dan haka ya miƙe ya wuce sashensu. Yana shiga bedroom ɗinsa wayar Samraah yay ƙoƙarin kira. Cikin sa'a kuwa bugu uku ta ɗaga. Sai dai a yanda yaji muryarta na fita a shaƙe ya tabbatar har yanzu tana a cikin damuwa. Daɗaɗan kalamai ya shiga jera mata da lallashi akan ta kwantar da hankalinta. Ba shi yace mata zasuyi wani abu ba. Bafa itace ta aikata laifin nan ba da har zata takurama ranta haka suma dake tare da ita ta sakasu a damuwa. Sosai lallashin nasa yay mata tasiri, dan haka ya yanke kiran yana cewa bari yay shirin barci zai kirata video call. Yana yanke wayar Attahir na shigowa ɗakin, yanda ya kafesa da ido ya sashi duƙar da kansa, fatansa dai ALLAH yasa baiji wayar da sukai da Samraah ɗin ba.
“Mike damunka Mansoor?”.
“Yaya nace maka babu komai”.
“Ƙarya kake yi. Idan kuma zakama kowa wannan ƙaryar ni kasan bazaka mun ba. Dan nasanka fiye da yunwar cikina. Koka sanar min, ko yanzun nan naje na kira maka Mamy da Dad maybe su ka sanar musu”. Ya ƙare maganar da juyawa kamar zai fita. Da sauri Mansoor ya riƙosa yana girgiza kansa. “Please basai ka kirasu ba. Ba wata damuwa bace mai yawa fa”.
“Kasan dai bama ɓoyema juna damuwarmu. Karka fara daga yau to”.
Numfashi mai nauyi Mansoor ya sauke tare da ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana harhaɗo ƙaryar dazai sanar masa dan bazai taɓa faɗa masa gaskiyar zancen ba tunda yayima Samraah alƙawarin haka.....

        ★💫★💫★💫★💫

          “Sir dan ALLAH kada ka saka kanka a damuwa. In dai batun yarinyar nan ne dai-dai yake da kaɗawar iska mai wucewa. Ita ta isa ta saka abinda bakayi niyya ba. Waye ubanta a ƙasar nan? Har micece ita a aikin jaridar ma. Yarinya ce fa ƙarama fitik”.
       Idanunsa dake lumshe ya buɗe a hankali. PA ɗin nasa dake magana ya zubama su kusan sakan arba'in. Sai kuma ya sake maidasu ya lumshe a kasalance. Dai-dai nan drivern sa yay sallama a ƙofar katafaren falon. PA ɗinsa ne ya amsa. Sai kuma ya bashi umarnin ya shigo dan yasan kayan boss ɗin nasu ne dake a mota ya kawo. Cike da tsantsar girmamawa yaje Centre table ɗin gabansa kuwa ya ajiye. Sai kuma yay ɗan jimm a duƙe kafin ya ɗago yana nuna wata jaka. “Sir wannan wani mutum ne yanzu nan ya kawo wai a baka. Naso ƙin yin hakan amma kausasan kalamansa suka daƙileni. Dan ya tabbatar min ƙin baka ɗin zai zama kuskuren da bazan yafema kaina ba kaima kuma bazaka yafe min ba. Dan saƙon nada amfanin da idan na wofamtar da shi dai-dai yake da gina harsashin tarwatsaka. Amin afuwa shine ya faɗi hakan”.
       A zabire PA ɗinsa ya furta,  “What! Wane ɗan iska ne haka. Su securitys ɗin gate kuma suna aikin mi ya shigo cikin gidan nan, kai kuma ka zauna sauraren wawancinsa, are you mad?”.
       Shiko gogan ko motsi baiyi ba. Sai idanunsa da ya ɗan buɗe kaɗan a ƙasa-ƙasa yake kallon drivern nashi da su. PA zai sake magana ya masa alamar ya barsa. Hakan yasa driver tashi da sauri ya fita ya bar saƙon da aka nannaɗe a cikin leda mai ƙyalli. Sake maida idanunsa yay ya lumshe kawai. PA da hankalinsa gaba ɗaya ke'a kan saƙon sam ya kasa nutsuwa, ganin ogan nasa baida alamar bashi umarnin ya buɗe suka miye a ciki ya furta, “Sir ya kamata musan minene a ciki. Dan bamu san mi mai saƙon ya taka ba har yake irin waɗan nan kalaman.” shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya kaɗa masa kai alamar ya buɗe ɗin. Jikin PA har rawa yake wajen ɗaukar saƙon. Kamar ƙyaftawar ido ya gama buɗesa ledar da aka nannaɗe sa. Sai dai kafin ya ciro abinda ke'a cikin kwalin da aka naɗe ɗin text message ya shigo wayarsa. Kasancewar wayar mai muhimmanci ce dan ta business ce ya ɗauka dan ya duba saboda akwai saƙon da dama suke tsammani. Rubutu ne da bai wuce words ɗari ba. Dan haka ya fara karantowa.
           Sosai jikin Hayatu PA ke rawa yana mai ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Sir tabbas hasashenka ya zama gaskiya. A kwai wanda ya gammu, kuma tabbas shine mai face mask ɗin nan. Dan gashi anan ya turo saƙo?”.
Idanunsa ya ɗan buɗe batare daya tanka ba yay masa alamar miya faru?. Cikin rawar jiki Hayatu ya fara karanto saƙon a fili kamar haka.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_


........*_Barkan ka madubin wannan ƙarni. Ba sai na cikaka da gaisuwa ba, bari na tafi kai tsaye kawai. Ina buƙatar naira miliyan ɗari biyar daga gareka. Kuma cikin gaggawa. Idan ba hakaba, a daren yau zan rusa duk wani tanadinka da tunƙahonka da videon dake hannuna ta hanyar yaɗashi a social media. Kasan dai kisan kai ba abune mai sauƙi ba. Musamman ga mutum irinka sananne mai tarin magauta da masoya tako ina. Na baka awa arba'in da takwas. Idan kunne ya ji jiki ya tsira._*

         Ya jima bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kwance jikin kujerar kansa a sama kaɗan. Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima ji ko fahimtar abinda PA ɗin nasa ya karanto masa bane ba sam. Yaja kusan minti uku PA nata kai kawo kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili. Zaune ya tashi da ƙyau, sai dai a nutsensa yake abin mamaki. Goran ruwa dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa. Sai da ya shanyesa tas sannan ya jefar da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na biyu yana sake nutsar da kansa, sai kuma kamar wanda ya tuna ya dubi PA ɗinsa. “Ina buƙatar duka cctv footage na company a daren nan?”.
      Cak Hayatu ya tsaya da ga kai-kawon da yake, sai kuma jiki a sanyaye ya ce, “Sir ka manta mun duba sanda muka shiga kafin faruwar abun amma basayi duk an kashesu”.
         “Hakane, amma kamar na kunna ukun farkon nan.”
      “Yes yes tabbas kuma hakane fa Sir. Wlhy sai yanzu na tuna. Aiko ko wanene wannan zaici ubansa.” baima jira umarnin ogan nasa ba ya fice da sassarfa tamkar zai kifa ƙasa duk kuwa da dare ne a lokacin. Dan kusan sha ɗaya ma ake nema, saboda bayan an tashi a taron company sun bu sarkine kamar yanda ya buƙa. Bayan sallar magrib suka bar gidan sarki, maimakon gida suka wuce wajen wani abokin harƙallarsa dan haɗuwar ta sirrice, sai goma saura suka nufo gida. Gashi yanzu ana harar sha ɗaya da wasu mintuna.

        Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga falon ya nufi bedroom ɗinsa. Tamkar mai hasashen ganin wani abu sai da ya gama kalle kowacce kusurwa da lungu da saƙon na ɗakin sannan ya kai zaune a bakin katafaren lafiyayyen gadon. Sabon gida ne fil dan yau ne ya fara shigarsa. Anyi aikin gininsa tare da Companyn nasa ne. Bai cika son zaman hotels ba a rayuwarsa sai in har ya zama tilas a garesa. Ta wani ɓangaren kuma gorin mutane akan kullum yana cika bakin shi ɗan Kano ne amma ko gida baida a arewa ma gaba ɗaya ya sashi ginin wannan gidan da ko makaho ya laluba yasan an kashe kuɗi. Dan yanda companyn ya haɗu shima gidan haka ya haɗu matuƙa.
         Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane. Abubuwane kawai suke masa kai-kawo a rai da suka faru a wannan yinin. Kallon komai yake tamkar wani film ba zahiri ba. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba. Amma na yau ɗin na musamman ne. Dan duk sunzo masa a bazata. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan. Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba?. Amma dai bari ya jira P.A ɗinsa da sakamakon da yake buƙatar gani kafin ya tsara komai akan mizaninsa. Da ga haka ya miƙe yana mai fara zame kayan jikinsa domin shiga wanka...

        Yaja tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe ash color sabuwa dal. Dan yanda take wani maski-maski zai tabbatar da hakan. Ƙaramin towel da a hannunsa ya kai kan jiƙaƙƙiyar sumar kansa mai tsaho data kwanto masa a fuska sosai, hakama ta bayansa kai kace bai haɗa jini da babaƙen fata ba balle ma har a kirashi da suna bahaushe. Tamkar ba shi kaɗaine a ɗakin ba. Fuskar nan a tsuke babu alamun rahama a cikinta. Duk da tun fitowarsa wayarsa ke tsuwwa alamar kira na shigowa, yay biris da ita tamkar bai ji ba. Sai ma ƙoƙarin nufar ƙaton mirrorn dake a ɗakin yayi abinsa. Tuni Hayatu ya shirya masa kayan shafe-shafensa a mirrorn, dan zaiyi kamar 1week ne a cikin Kanon kamar yanda yake fata. Hand dryer da aka ajiye a saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, sumar tasa ya fara busarwa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala gyarata alamar ya riga ya saba da hakan. Kafin ya ɗan shafa mansa sama-sama tare da sprays masu shegen ƙamshi kala har biyu sannan ya nufi doguwar wadrobe data cinye bango guda. Ta farko kawai ya buɗe, anan ko yaga kaya kusan kala goma duk ƙananu, sai ƴar akwatin da yazo da ita da suit kala uku a ciki. Yasan kayan dake a shiryen duk aikin Hayatu ne. Batare da yace komai ba ya ciri farin pyjamas mai shegen ƙyau da laushi, sai boxer shima dai sabo. Tsaf yay shirinsa tare da sake komawa gaban mirrorn yay sabon wankan tsadaddun turarurrukansa na barci da ƙamshinsu ba'a magana kamar ba dare ba. Tsaki yaja a hankali yana hararar wayarsa da ke cigaba da tsuwwa babu ko ƙaƙƙautawa. Ya san mai kiran nasa, dan ita kaɗaice take karya dokarsa akan hakan. Duk wanda ya sanshi yasan yanada doka a akan kira, dokar kuwa itace in har kamasa kira 1 bai ɗaga ba ka bada mintuna kamar biyar sannan ka sake. Idan nan ma aka samu akasi bai ɗaga ɗin ba to ka haƙura kawai, idan shi ya samu lokaci zai iya ya kiraka, idan bai biyo ba kuma ka ɗauka kiran naka baida muhimmanci ne. Wayoyinsa duk a hannun Hayatu suke. Wannan ce kawai yake riƙewa saboda Ummien sa. Gaban gadon ya ƙarasa in da ya yasar da wayar, cikin ƙara ɗaure fuska ya ɗauka dan yana son ta barsa. A daƙile ya kai wayar kunensa sai dai yaƙi cewa komai. Sai da yaja kusan sakan hamsin ya ce, “Thanks”. Kawai yaja bakinsa yay shiru. Kasancewar bai sauke wayar ba zai tabbatar ma da har yanzu magana ake daga can, dan sai wani yamutsa fuska yake da sake tsuketa kamar mai jin warin mai maganar. Kusan minti biyu ya sake furta, “Zanyi barci”. Daga haka ya yanke kiran gaba ɗaya. Wayar ya wurga a saman gadon tare da jan tsaki mai ƙarfi ya haye gadon yay kwanciyarsa. Kai kace ma baida wata damuwa a rayuwa. Sai da yay addu'oi barci sannan ya lumshe idanunsa. Kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamar yayi barcin.....


     ●´⌓`●●´⌓`●●´⌓`●

           Duk yanda nagaji na kasa barci. Sai faman juye-juye nake abubuwa na dawo min tamkar yanzu suke faruwa, dan ma ƴar wayar da mukai da Mansoor ta ɗan sani ƴar nutsuwa. Ganin ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa na tashi na ɗaura alwala. Salla na farayi, sai da na kwashe kusan awa ɗaya da rabi sannan na zauna ina istigifari. Kamar a mafarki naji wayata na verbration. A gogo na kalla, ƙarfe biyu da kwata. Mamaki ya kamani, dan ko Mansoor baya kirana a wannan irin lokacin, kuma ma ai munyi waya duk da dai yace zai sake kira video call amma bai kira ba, ganin lokaci haja yasa ban damu ba. Dan duk tsawon wayarmu baya wuce daga tara zuwa goma. Jin an sake kira bayan ta katse na yunƙura na ɗauka. Abin mamaki Mansoor ne. Ɗagawa nai hankali a tashe, a tunanina ko wani abu ya samesa. Amma sai naji yaymin sallama cikin taushin murya. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sannan na amsa masa.
“Dama naji a jikina zaki iya kasa barci, kiyi haƙuri Yaya ne ya ɗauke hankalina shiyyasa ban sake kiran ba. Haba Babie dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan. Ai ko ke kika aikata laifin nan sai haka”.
     Numfashi na sauke a hankali. Cikin sanyin murya na ce, “Ni ban kasa barci ba fa, na farka ne kawai”.
              “Uhhm yau kuma halin daba naki ba kika aro, to ai bai miki ƙyau ba dan baki iya ƙaryarba tunda ga harshenki yana rawa”.
     Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, sai kuma nakai kwance ina faɗin, “To amin afuwa gashi na kwanta. Amma kaima miya hanaka barci?”.
        “Saboda mahaɗin zuciyata batayi ba”.
       “Humm”. Na faɗa kawai ina murmushi. Shima ina jiyo sautin nasa murmushin. Mun ɗan yi shiru na wasu sakannin kowannemu na sauraren saukar numfashin ɗan uwansa. Kafin ya katse shirun da cewa, “Kin sanarma Yaya Musaddiq abinda ya faru ko?”.
      “A'a”.
   “Miyasa?”.
“Kawai dai”.
“Aiko Babie ya kamata ya sani. Dan ko zamu iya ɓoyema kowa shi banda shi. Maybe ma ya ƙaremu da shawara ai. Dan wlhy har yanzu ni kaina duk a kulle yake”.
       “Hakane zan sanar masa gobe in sha ALLAHU. Amma ni dai dan kaƙi ta nawane. Hukuma kawai ya kamata mu miƙawa ai”.
     “Baƙi naiba Samraah. Ina son ki fahimci wani abu. Mutumin nan fa ya wuce duk inda kike tunani a ƙasar nan. Yanzu koda mun miƙa video ɗin nan ga hukuma kina ganin zasu hukuntashi ne. Ko kin manta yanzu a ƙasar nan tamu KUƊI ne ke magana ba GASKIYA ba. Shi kuma ALLAH ya bashi su, Samraah Maash fa zai iya juya Africa a tafin hannunsa ta yanda yaso bama Nigeria ba. Ke hatta da ƙasashen masu jajayen kunnuwan yanada ƙarfin faɗa aji sosai fiye da yanda kike tunani ta wasu fannoni. Sai dai su banbancinsu damu zasu iya hukunta duk wani mai laifi koda shi wanene? Amma a ƙasarmu ba haka bane. Ko wanda bai kama ƙafar Maash ba zai iya shallakewa in har da kuɗi. Kiyi haƙuri dai mu nema mafita mai ɓullewa. Mu kuma samu jajirtaccen ɗan sandan da zai iya yin duk abinda ya dace batare da kuɗi sun iya tankwarashi ba saboda gaskiyarsa. In dai Maash ne bazamu ƙyalesa ba sai an ƙwatoma mutumin nan hakkinsa”.
        “ALLAH ya tabbatar to. Na kuma gamsu da bayaninka.”
     “Masha ALLAH dear, yanzu dai zan shigo gobe in ALLAH ya kaimu ki biyo Yaya Musaddiq gareji mu haɗu acan dan ina so mu tattauna da gaggawa mu nemo mafita kafin Maash ya farga. Saboda babu yanda za'ai ace babu camaras a wajen nan duk da Companyn bai fara aiki ba sai Monday”.
      Sosai zancensa ta ratsani dan har sai da na tashi zaune dingangan. Amma na gagara cemasa komai saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri........✍️
      

_Tofa masu karatu yanzunne fa ainahin wasan zai fara. Dan da alama mun gama sharar fage zamu tafi mataki na biyu a labarin. Wa kuke tunanin ya rubuta saƙon nan? Sannan karku manta a cctv footage fa Samraah za'a gani. Shin ko itace dai ta rubuta saƙon? Ko kuma wani yaji sanda take faɗama Mansoor yay amfani da damar? Ko kuwa ba ita kaɗaice ta gani ba? Shin minene dalilin Maash nayin kisan nan ma wai? Wanene aka kashe?..... Kai kai kai cakwakiya ce fa iya cakwakiya a labarin nan. Amma dai ina son jin amsoshinku a comment section. Yau har masu laɓe su fito inba haka ba gobe babu posting sai bayan salla🚴🚴🚴._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A

Please Login or Register in order to submit comment