Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin nuna mamakinsa a fili. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Anya yarinyar nan kin san wanene *_MASH!?_* kuwa? Babu sauƙi fa a ɗaukar wannan alwashin naki. Ni dai ina gargaɗarki da kar kiyi wani abu mara ƙyau dan ALLAH. Idan kin samu dama kamar yanda kowa ke fata fine, idan baki samu ba ba faɗuwa bace. Dan haka be careful sweetie. Kar ki biye ta MD kujerarsa kawai yake yunƙurin saitawa”.
        “Karka damu, ni ba wani abu mara ƙyau zanyiba ALLAH. Kuma duk ma tambayar da zan masa ai sai na kaima MD ɗin ya duba. Kaima kuma zan baka ka gani kafin ma na turama MD ɗin har ma Yaya Musaddiq. Kawai dai ina fatan karya masa wannan alfaharin nasa ne”.
       Kansa ya jin jina min, ya ce, “To ALLAH ya bamu sa'a, dan zanfi kowa kasancewa a farin ciki ace kece kika karya ɗin kam. Dan har ƙyauta sai na miki na musamman”.
    “Tami?”.
  “A'a ai ba sai na faɗa ba. Yanzu dai ajiye ma wannan batun. Su Alhajina fa zasu zo wannan weekend ɗin. Dan haka yau ina buƙatar ganawa da Abba yaya za'ayi kenan”.
       Da sauri na juyo na kallesa, ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. Kaina na ɗauke cikin jin kunya, sai dai wani irin farin ciki ne ke ratsa ƙashina da ɓargo har ina jin yanda jikin nawa ke rawa. Amma dai nayi juriyar dakewa. Sai dai ban sake cemasa komai ba har muka iso. Tunda ya tsayar da motar na kasa wani motsi, mun kai minti biyu a haka shi kuma yana kallona kamar ya samu tv kafin ya saki ɗan murmushi mai sauti. “Wai kunyar ce dai Babie?”. Sake kauda kaina nayi gefe batare dana bashi amsa ba. Ya saki ƴar siririyar dariya yana ɗan dukar sitiyari, sai kuma ya juyo gareni yana faɗin, “ALLAH ya kaini randa zan cire wannan kunya dai kowa ya huta, dan bazanyi sakaci ba a daren farko zata kama gabanta. Anya baki haɗa jini da fulani ba Samraah”.
       Hannu na kai ga handle ɗin ƙofar zan buɗe na gudu sai na jita gam alamar ya saka lock. Kasa sake wani yunƙuri nayi, na kuma kasa juyowa dan har lokacin ina jin kallon ƙurullar da yake min.
   “Kayi haƙuri ka buɗemin, zancen ganin Abba kuma ya kamata ka fara ganin Yaya Musaddiq dai first nake ga”.
        Sosai ya sauke numfashi mai nauyi, sai kuma ya amsa da, “Okay hakan ma yayi, zan bari to sai gobe in sha ALLAHU na samu Yaya a gareji”. Daga haka ya buɗe min. Wuff na fice abina kuwa. Batare da ko sallama nayi masa yau ba na shige gida, har lokacin kuma ina jin idanunsa a kaina. Ina rufe ƙofar gate ɗin na jingina a jiki ina sauke numfashi, sai kuma na kai hannuna saman ƙirjina da ke bugawa da sauri-sauri. Murmushi na saki kafin na buɗe idanuna a hankali na ɗan leƙa gate ɗin naga ko ya wuce. Sai lokacin naga yana ƙoƙarin yin reverse. Bazan ɓoye miki ba ina matuƙar ƙaunar Mansoor wlhy Bilyn Abdull, soyayya nake masa mai ƙarfin gaske da bama zan iya misaltata ba, dan Mansoor ya mun abubuwa na halacci da dama akan soyayya da bazasu iya ƙirgiguwa ba, na tabbata da aure kawai zan iya masa godiya a kansu amma bada fatar baki ko soyayyar saman titi ba.
    
        Cikin gidan na shiga kamar yanda na saba, sai dai acan ƙasan raina ina ɗan jin tsoro-tsoro. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganin ban samu kowa a falo ba yau. Zuruf na shige ɗakinmu, in da na tarar da Bibaa kawai tana kallo a wayarta. Yanda bata amsa ko sallamata ba nima ban sake bi takanta ba. Wanka na farayi duk da kuwa cikin ƙyanƙyamin bayin nai haka, dan yanda ban wanke ba haka Bibaa itama bata wanke ba, sai ma datti da suka ƙara masa. Gudun kar lokacin sallah ya wuce min yasa ni saka doguwar riga kawai na saka hijjab na tada sallar. Na kai raka'a ta biyu ina sujidar ƙarshe kawai naji saukar duka kaina. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un wata irin azabace ta ratsa ni, amma na daure sosai na cigaba da sallata. Abinda kuma zai baki mamaki ba'a daina dukan nawa ba har na idar. Karo na farko kenan dana ɗaga hannu sama ina kuka da neman sakayya wajen UBANGIJI na, ina ƙoƙarin shafa addu'ar dai dai nan Abba ya shigo kamar wanda aka jeho.
       “Haba Jalilah minene haka? Baki da hankali ne tana salla kina dukanta”. Ya faɗa a matuƙar hasale yana riƙe bulalar. Basu ba hatta ni sai da na shiga shock, dan nidai nasan ba yau ne karan farko da Mum take dukana ba a gidan nan. Hasalima ta dakeni a gabansa a lokuta barkatai amma bai taɓa cewa komai ba. Bama ni ba, hatta da Yaya Musaddiq yasha shan duka a wajen Mum, yanzu ne dai ta daina sai zaginsa da baƙar magana. Hakama Hafizzullah, sai dai duk ni na fisu shan wahala kasancewar akoda yaushe ni ina cikin gida a tare da su....
        Mum ce ta katse min tunani na, dan cikin hargagi ta hayayyaƙo ma Abba a gabanmu. Idan ni bazata ji nauyina ba ai ya kamata taji nauyin su Babie kasancewar sa na mahaifinsu. Amma ko'a kwalar kwagirinta. Dan sai da takai ya koma bata haƙuri da lallashinta. Ni al'amarin nasu ma sai ya nema fasan kaina dan al'ajabi. Haka dai ya jata da ƙyar suka fice a ɗakin. Harara Baby ta watsa min da faɗin, “Shegiya mayya. To kurwar iyayenmu kur wlhy. Kuma indai Mum ce kaɗan ma ta miki wlhy, bari dai Abban ya fita duk da ma ko yana nan zata iya cigaba da cin ubanki, yanzu ɗin ma ta ƙyaleki ne kawai kiji da wannan tsamin jikin mtsowww makwaɗaitan banza da wofi anzo an cika mana gida an hanamu rawar gaban hantsi”. Daga haka ta fice kamar iska zata ɗibeta. Dan sam Baby bata da wani jikin kirki, ta girman amma na fita cikar halittar jiki sosai, wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka nice babbarta. Sai da suka gama zageni tsaf ita da Bibaa suka fita sannan na fashe da kuka, dan illahirin jikina raɗaɗi yake min sosai. Da ƙyar na iya tashi na zare hijjab ɗina, abinka da farar fata wasu wajen ma har sun fashe. Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeni, haka na kwana ina makyarkyata ga ciwon jiki. Duk kiran da Yaya kemin a waya ban ɗaga ba, har ya gaji ya daina kiran, nasan dai ya zata ko barci nayi ne...
       Humm wato Bily inada taurin kai fiye da yanda kike tunani. Zaki sha mamaki idan nace miki washe gari ma duk da dukan da naci haka na sake tsallakewa nai tafiyata wajen aiki batare dana ɗaga ko tsinke a gidan ba. Nasan dai nabar ƙura sosai, amma ko'a jikina nai gaba batare da na jira ko Yaya Musaddiq ba yau. Sai wajen 12 sai gashi yazo lokacin ina kwance zazzaɓi ya addabamin. Ruƙayya ce data lura da haka ta matsa min nasha paracetamol da ƙyar. Da Yaya Musaddiq ma yazo itace tazo ta kirani dan ta ɗan fita taci karo da shi shine tazo ta kamani muka fita.
     Kallo ɗaya na masa na duƙar da kaina. Dan sosai naga ɓacin rai tattare da shi. Sai dai shima yanayin da ya ganni naga ya ɗan raunana fushin nasa, dan muna isowa inda yake sosai naji ya sauke ajiyar zuciya yana mai furzar da huci mai zafi.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆_


........Sai da Yaya yayma Ruƙayya dake shirin barin wajen godiya sannan ya juyo gareni. Kallo ya ƙare min daga sama har ƙasa sannan cikin yanayin fusata ya ce, “Miyasa kike da taurin kai ne wai Samraah?. Yanzu ga abinda kikayi jiyan wace riba kikaci tunda kinfi kowa sanin halin matar nan?. Amma ke da yake ba'a taɓa faɗa miki kiji shine yau ma kika kuma. To ai gashi nan ta sake ƙulla miki sharri kala-kala ita da yaranta. Tun ɗazu ina gidan basu barni na fito ba sunata min masifa akan wai ni nake sakaki. Har Abban na saka sharaɗin ko dai ki ajiye aiki ki dawo ki cigaba da aikin gidan ko kuma ya aurar da ke ga wa wanda ita Mum ɗin ta kawo. Idan yaga shi zai barki yin aiki ki cigaba, amma albashinki dolene kema ki dinga rabawa biyu daga yanzu kina basu rabi ana haɗawa ayi cefane. Nama kawo masa batun Mansoor yaƙi ya saurareni sam. Wai shi bai san da wani Mansoor ba kuma bazai aura masa ke ba, wanda Mum ta kawo kawai ya sani kuma shi zai bawa dan yaron nada tarbiyya sosai, kuma shi ya gamsu da hakayensa....”
      Kuka na sakar masa mai taɓa zuciya. Hakan ya sakashi yin shiru ya gagara cigaba da magana ya zubamin ido kawai. Kusan mintuna uku ina kukan sosai kafin ya kai zaune kusa dani. A jikinsa ta gefe ya sakani kawai shima hawayen na cika masa ido. “Amma kin san bana son kuka ko Samraah”. Ya faɗa muryarsa na rawa. Ɗagowa nai a karo na farko ina kallonsa. Sai kuma na sake fashewa da wani sabon kukan ganin yanda idanunsa suka kaɗa sukai jazur gasu cike da hawaye. “Yaya ya kake so nayi, shike nan haka zamu lalace a yima waɗanda basu taɓa jin tausayinmu ba biyayya. Kullum burin matar nan wulaƙanta mu, Yaya tun fa ban isa iya aiki ba nake bautar gidan nan, amma ko sau ɗaya ba'a taɓa min adalci ba idan nai kuskure a yafe min. Kullum kuma a banayi nake. Su Baby na kwance. Yaya na gaji wlhy, ji nake kamar na gudu na bar gidan nan kawai....”
        “Shiii!!! Karna sake jin irin wannan maganar a bakin ki. Samraah ai wuya bata kisa. Da ace tana yi wlhy da bamu kai haka a rayuwa ba. Duk can baya baki ƙosa ba sai yanzu da aski yazo gaban goshi. Kwana nawa ma ya rage miki a gidan. Bama ke ba da kike mace zaki tafi gidan aure hatta ni da Hafizzullah in sha ALLAHU mun kusa bar musu gidansu. Gara kawai na tada gini na kamar yanda kike bada shawara mu koma can kawai. Amma dan ALLAH ina roƙonki kada ki sake maimaita abinda kika faɗa yanzu. idan kin gudu ina zaki? Ki daure ki cigaba da musu abinda suke so. Watarana sai labari ai. Maganarki kuma da Mansoor na yanke shawarar zuwa wajen dangin mahaifinmu, duk da sun watsar damu basu taɓa waiwayen mu ba tunda ɗan uwansu yabar duniya zanje na roƙesu su shiga wannan maganar a baki wanda kike so tunda dama sune ai da wannan alhakin ba Abba ɗin ba. Ki tashi kuma muje asibiti dan jikinki akwai zazzaɓi sosai.”
       Ɗagowa nai zanyi magana ya girgiza min kai alamar kar nace komai. Dole na haɗiye kuwa. Ruƙayya ya kira da wayata, yace ta tattare masa kayana dan ALLAH. Cikin mintuna kaɗan ko sai gata. Da taimakonta muka fita inda mashin ɗinsa yake. Ta taimaka min na hau muka wuce dan Mansoor yau baizo office ba sunje wani aiki Jigawa. Sai da muka fara tsayawa a camix aka dubani kafin mu ƙarasa gida dan nata roƙonsa kan bazanje asibiti ba, sanin da yay min na ƙin jinin asibitin shima yasa ya barnin mukaje camix ɗin kawai aka bani magani.

      Kamar yanda Mum ta shirya cin ubana shima Abba ya shirya hakan yau, sai dai a yanayin da Yaya ya shiga dani gidan ya saka jikinsa yin sanyi shi. Dan Mum ta fara min tujara da ƙoƙarin kai mari ya dakatar da ita.
   “Uhm Jalilah inaga ya kamata ayi hakuri ai, baki kula da halin da take a ciki bane? Kiyi haƙuri harta warke ni da kaina zan sauke mata taurin kan nan nata nayi miki alƙawari”.
     Wani shegen kallo ta watsa masa a fusace. Kamar zatayi magana sai kuma mita tuna oho tai shiru. Fuuu ta wuce bedroom ɗinta ta barmu tana faman huci. Wannan zazzaɓi dai shine ya ceceni a wannan rana. Washe gari kuwa duk da weekend ne asubar fari Mum tazo ta tadani. Bata damu da yanayina na har lokacin ban gama dawowa dai-dai ba. Nima sai bance mata komai ba na tashi na hau aikin da take buƙata, dan kwana biyun nan fa da banyi komai ba haka gidan yake zaune kaca-kaca. Kafin takwas na safe har brackfast na kammala haɗawa, na ɗauki na Yaya Musaddiq na kai masa. Na samu ya kammala shirin wucewa Gwarzo kamar yanda ya faɗa zaije. Ba haka naso ba, dan naso ace munje munga Hafizzullah kamar yanda muka tsara. Zama nai muka karya tare yana ƙara lallashina da mun nasiha, jinsa kawai nakeyi, dan gaskiya bazan iya haƙurin wani abun ba in har nayi wani. Amma dai zan rage taurin kan kodan shi. Ban bar ɗakin ba sai da ya ƙarasa shiryawa muka fito tare, yau zai dawo, amma ya musu tsaraba. Ciki na koma na samu mutanen gidan gaba ɗaya a falo zagaye da Abba. Sai dining dake kaca-kaca sun gama karyawa amma babu wanda ya iya kawar da ko cokali. Abban na gaisar, ya amsa min babu yabo babu fallasa, itako Mum bama ta amsani ba. Ban damu ba dan ba yau na fara ganin hakan ba ai daga garesu, na nufi ɗaki da nufin yin shirin islamiyya da nake zuwa duk weekend Mum ta dakamin tsawa.
       “K dan ubanki waye zai kwashe miki waɗan can kayan”.
    Ɗan jimm nayi a tsaye zuciyar na yunƙurowa, sai dai nasihar Yaya Musaddiq dana tuna ta sakani komawa cool. Batare da nace mata komai ba na nufi dining ɗin na shiga tattare kayan. Sauri-sauri na wankesu na fito, har yanzu suna a falon, ɗaki nai wucewata na shirya, na sake fitowa dai na samesu. Da harar Mum na fara cin karo, ɗauke kaina nayi kamar ban ganta ba, a ladabce naje gaban Abba na duƙa. “Abba zanje islamiyya saina dawo”.
        Kansa kawai ya jin jina min ya cigaba da kallonsa. Nima sai na miƙe. Mum dake watsamin hararace tai saurin faɗin, “Ya kake bata damar tafiya Abban Abbas, idan ta tafi ubanwa zai mana girkin rana? Islamiyya take zuwa ne ba yawon iskancinta ba”.
     Ƙoƙarin ficewa nake da sauri dan nasan zai iya dakatar dani. Amma a mamakina sai naji yana faɗin, “Baga su Baby nan a gidan ba suyi girkin su mana tunda sun ɓarar da tasu islamiyyar su....” daga haka ban ƙarasa jin abinda yake faɗaba nai wucewata ina murmushi. Wani lokacin idan Abban yay abu sai kaga kamar mai mutunci. Koda yake dama ba laifinsa bane ba, zama kawai ake ana shirya mana sharri a wajensa maybe ma harda asiri. Dan nikan ban taɓa ganin mijin dake tsoron ɓacin ran matarsa irin Abba ba. Oho koma dai minene su suka sani ina ruwana.. Tunda na isa islamiyya na samu ƙawayena biyu na manta da wata hidimar gidanmu. Sai ƙarfe huɗu muka tashi, anan nai sallar la'asar sannan na dawo gida. Abin dariya abin takaici, a galabaice na samesu wai babu wanda ya tashi yay girkin ana jirana, Abba dai ya fice sai su kawai. Sai Abbas dana samu a gidan shima ya shigo. Ko kallon inda yake banyi ba dan ni da shi bama magana. Haka na tuɓe uniform ɗina na shiga kitchen ɗaura musu girkin da suke jira ɗin. Abu mai sauƙi na musu nayi komawata ɗaki..
       Yaya Musaddiq bai dawo a ranar ba kamar yanda yace. Koda na kirashi a waya sai yace nai haƙuri bai samu kawu Musa bane a gida, su kawu Sa'adu kuma sunce dole ya jirashi. Mun ɗan yi hira mukai sallama saboda kiran da Mansoor keta faman yimin. Hira sosai mukasha da Mansoor, dan sai kusan ɗaya mukai sallama. A hakan ma ba kwanciyar nayi ba. Tambayoyin da zanma wancan mutumin nai zaman tsarawa, har biyu sannan na miƙe na gyarama su Bibaa rufa na ɗauro alwala. Nice ban kwanta ba dai sai kusan biyu da rabi, amma hakan bai hanani tashi da asuba ba yin ayyukana. 
 
         Washe gari da yamma Yaya Musaddiq ya dawo gidan. Na dawo daga aikan da Mum tamun rijiyar lemo wajen ƙawarta na samu ya dawo. Naji daɗi sosai, dan bamma shiga gidan kai aikar ba na zauna muka hau hira. Duk yanda sukai da su Kawu Musa ya sanar min. Sunyi faɗa sosai, da farko ma ca sukai su babu ruwansu. Shi Abban daya nuna musu shine dolenmu yaje ya aurar damu. Amma Yayan ya dinga basu haƙuru, da ƙyar dai suka haƙura, sun kuma tsaida shi kawu Sa'adu zai zo ya sami Abban.
Hakan kuwa akai, dan washe gari Litinin sai ga kawu Sa'adu. Lokacin mu duk mun fice wajen sabgoginmu. Shima Abban a office kawun ya samesa suka tattauna. Duk da dai a farko taso tayi tsami a tsakaninsu. Kasancewar kowanne yana son nuna ƙarfin ikonsa a kammu da kuskuren da ɗan uwansa yay masa. Bayan dai sunyi sama sun faɗo suka dai-daita kansu. In da da ƙyar Abba ya amince da batun Mansoor........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
Up*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒆𝒏_



.......Oho mu bama musan sunayi ba, dan lokacin da suke nasu bidiri ni inama can office ɗin MD na kai masa aikin daya saka ni. Kamar kullum yau ma a kwai mask a fuskata, sannan dogon hijjabi ne har yana jan ƙasa na saka. Dama dai shigar tawa kenan. Idan har ka ganni babu hijjab to abaya ce na saka kuwa. Amma gyale dai a jikina zan iya rantsuwar tunda ma mallaki hankalina na san kaina ban taɓa sakawa ba. To bamma da shi sam, sai ƴan madaidaita da nakanyi rolling idan zan saka abaya. Duk da yanda na suturta jikina bai hana MD zuramin idanu ba, dan shi indai kallone ya iya shi na masifa ma da UBANGIJI ya hanemu yi. Ni dai miƙa masa takardar nayi na maida hankalina akan wayata.
       “Wow! Kai Samraah sannu da ƙoƙari. Shiyyasa duk girman gidan nan ke na fara hangowa dan nasan bazanyi zaɓen tumin dare ba, saboda nai matuƙar yarda da basirar ki, kina da saurin ɗaukar abu wlhy. Sosai komai yayi, sai fatan ALLAH ya kaimu ranar kuma. Yanzu zuwa anjima sai kizo ki amsa kiyi printing nashi ko. Ki kuma je ki zama cikin shiri na musamman, dan wannan ranar muna fata ta zama ta musamman a garemu. Dan ALLAH kada ki saka dogon hijjabin nan tamkar matar limamin anguwa. Ki yi shiga ta ƴammatan zamani dan kin san irin manyan mutanen nan sunfi son komai na wayewa su balle shi matashi dake a ganiyar samartaka. Inda son samu ne ma ki saka sabbin kaya, ki samu makeup artist ta tsantsara miki irin kwalliyar nan taku ta zamani Please”.
       Yanda kuka san television haka nai galala ina kallonsa. To amma kun san tsiyar mutuniyar taku. Sai ban musa masa ba nayi murmushi kawai da faɗin, “In sha ALLAHU Sir”. Yako ji daɗi, dan tuni ya washe baki da jera min godiya. Niko sai nayi dariya kawai a raina. Kuga ɗan banza yana son iskantani kawai. Yo in ba son iskantawa ba taya zai ce nai irin wannan shiri dan kawai burge wani sakarai can da ban san ma a wace alƙibla yake ba, ta musulinci ko ta masu kaɗa ganguna. Humyim bai san halin ƴar Abdul-wahab ba ne ba, amma zan sanar da shi sannu a hankali. Office na koma na cigaba da harkokina. Bayan azhar kuma muka haɗu da Mansoor. Dan nifa da kuke gani na duk rintsi bazaka ganni office ɗinsa ba in ba a dalilin aiki ba. Dan tun farko daya fara nuna buƙatar hakan ta hanyar kirana wai nazo na samesa office na dakatar da hakan. Nama nuna masa anan fa aiki mukazo, ya kamata mu ajiye batun alaƙa gefe muyi abinda ke a gabanmu kamar yanda muka rayu a makaranta. Idan mun fita anan sai mu dawo da batun alaƙar. Mansoor mutum ne mai sauƙin kai da fahimtar abubuwa, sai in kana kallonsa daga nesa ne zaka fassarashi da girman kai. Ya fahimceni harma ya nuna jin daɗinsa da hakan. Bawai dan ina zarginsa da wani mugun haline nayi hakan ba. A'a nayine domin kare mutuncina da martabata ta ɗiya mace. Sannan kuma hakan da nayi zai ƙara bani kariya daga hare-haren irinsu MD da basu iya ɓoye maitarsu a fili ga ƴaƴan mitane.
       “Amarsu ta ango”. Daya faɗa ya sani ɗauke kai gefe ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yayi yana dawowa ta inda na maida kan nawa. Ƙaramar harara na sakar masa ina sake ɗauke kaina. Ya ce, “Tab irin wannan harara haka amarya ai sai kisa na zube ƙasa wlhy. Kinga adana min ita sai nan da ƴan watanni kawai,  kinga inma suma nayi dai ƙya farfaɗo dani da kanki babu wanda yaji ko ya gani ko?”.
    Dariya ya bani, amma kasancewar ba'a ganin bakin nawa sai nayi murmushi kawai na sake ɗauke kaina.
     
     ★ Alƙawarin ALLAH ya cika. Iyayen Mansoor dai sun kawo kuɗi gidanmu a ranar juma'a. Ranar ni naga baƙin halin Mum muraran. Dan zage-zage ta dinga yi da yima Abba masifa wai an munafunceta. Ashe bai gaya mata ba sai ganin su kawu Musa yasa ta fara tambayarsa abinda ya kawosu. Shine ya sanar mata iyayen wanda yake nemana ne sukace zasu zo yau. Takaici ya sakata zuba masa ido kawai, amma ta kasa cewa komai. Dai-dai isowar baƙi kuma sai ga abinci Yaya Musaddiq na shigo da shi da ruwa da lemo batare da tasan daga ina aka dafo shi ba. Shiko Yaya Musaddiq sanin halinta da yay ne ya sashi saka matar ogansa ta dafa abincin. To ranar dai munga tujara. Dan nima da ban san mike faruwa ba ina a wajen aiki ina dawowa na samu rabona. Baby kuwa banda kuka babu abinda take yi. Ni dai ko uffan bance musu ba, a wajen Yaya Musaddiq kuma naji komai yanda ya kasance. Iyayen Mansoor sun kawo 300k, amma su Kawu Musa sun barma Abba 200k su sun ɗauki 100k na ɓangaren uba. Hakan da sukai baimun ba. Dan kamata yay su su ɗauki 50k Abba 50k aba Yaya Musaddiq 200k dan nasan dai shine mai mun wahalar ba kowa ba. Ban dai ce masa komai ba muka ci gaba da hira. Dan banama sha'awar shiga gidan. Ko hijjabi na ma da zan saka a gobe idan ALLAH ya kaimu domin zuwa taron can anan ɗakin Yaya na gogesa. Sai kusan sha ɗaya na shiga. Baby kawai na

Please Login or Register in order to submit comment