Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faru da ita acan sai ta faɗa masa bazata munafuncesa ba. Kajimin yaro fa dan ALLAH”.
         “Humm Aunty kar kiga laifinsa. Dan dama abin da kamar wuya ace ya fahimta kai tsaye. Amma dai kam al'amarin akwai ɗaure kai”.
       “Bana wasa ba ma. Inda shi wani ne dan ALLAH basai ya haƙuraba, idan ma ya matsune yay auren dole a goben basai a ɗaura da Waleeda ba. Nasan dai Daddynta bazai ce komai ba wlhy”.
      Idanu sosai ƙanwar tata ta waro waje. Sai kuma ta ɗan murmusa da faɗin, “Kai Aunty wannan ai babbar magana ce. Ni dai abinda nake gani anan kawai addu'a ce tafi dacewa. Sannan kisa a ranki in sha ALLAHU abinda zuciyarki ke ayyana miki bazai zama hakan ba.”
      Baki kawai Mamy ta taɓe batare data sake cewa komai ba.....

       💢💫💢💫💢💫💢💫💢

   *_RANA BATA ƘARYA BILYN ABDULL. MASU IYA MAGANA SUN CE SAI DAI WAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA_*. Na yarda da batun masu hikimar zance. Domin kuwa nima da kaina na yarda wannan rana tawace kam. Sannan in har Mum na amsa sunan uwa a gareni to taji kunyar kuwa. Dan halayyar da take nunawa yasa dangin mahaifinmu suka gagara haƙuri sai da suka yayyaɓa mata magana. Dan har Kawu Lurwanu na iƙirarin mata dukan tsiya. Yaya Musaddiq ɗin da take gani aba komai ba a gareta ne yayta basu haƙuri da kareta har aka samu ƙurar ta lafa. Gida ya gama cika danƙam da mutane. Dangi na kusa dana nesa sun nuna halacci. Ga abinci kala-kala anyo daga Gwarzo batare da an zaman jiran sauraren na nan gidan Abba da kunya ta sakashi kawo buhun shinkafa a jiya da dare ba, sai wasu ƴan kayan miya cakwat da nama a baƙar leda abin zakkunya dai.
        Kafin goma na fito shar dani a amaryata. Ga ƙunshin da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya ta rangaɗa min a daren jiya ja da baƙi yay masifar fitowa kamar kaci. Duk da gyaran ƴan kwanaki akai mun na fito fes dani kamar fure a tsakkiyar lu'u-lu'u. Wani cotton lass ne a jikina lemon green ɗaya daga cikin kayan da suka kawo jiya aunty Zakiyya ta ciro min. Dan duk kayan da zanyi hidimar biki dama sai da Mansoor ya ɗaukan mukaje tela ya gwadani tun kusan wata biyu da ya shige. Aiko ɗinkin yay masifar zaunamin a jiki. Sai wata stones sarƙa mai ƙyalƙyali da walwali tamkar diamond na gaskiya. Awarwaraye zobba da komai sunji a hannayena. Ta sama gashina da a daren jiya shima yasha wanki daga ƙanwar mijin Aunty Zakiyyar dai dan aikinta kenan shima sai ƙyalli da ɗaukar idanu yake. Bayan ta gama tsaramin kwalliyar da naita zame-zame a farko aka naɗa min ɗauri na azo a gani. Nan take hasken camara na waya ya shiga kai-kawo a kaina. Nanfa wasu sukace sai sun turama ango fa. Ciki harda Hafizzullah. Ban tanka musu ba face murmushi kawai da nake yi........✍️
        


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*







*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_

____________

_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._

_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_

_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._

_kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_

______________


......Daga can tsakar gida kam taro yay taro gida ya kacame da hayaniya irin ta biki, anan ɗakin ƙawayena na zagaye dani. Wasu na hotuna wasu na kwalliya, wasu na hirarsu akan batun dinner da za'ayi bayan an kai amarya. Dan can gidan su Mansoor ɗinne suka shirya. Kiran da Yaya Musaddiq yazo yamin ne ya sakani saka gyale na rufe har fuskata. Shine ya kama hannuna har falon baƙi. Tunda muka fito kuwa gidan ya sake ruɗewa da buɗe-buɗe. Ni dai kaina na ƙasa a cikin gyale dan haka kawai sai naji ina jin kunya kowa.
      Ban ida daburcewa ba sai da muka isa falon baƙi. Dan ganin kaf kawunaina na ɓangaren uwa da uba harda Abba. Sai gwagganni da innoni suma dai duk suna nan na kusa sosai. A tsakkiyarsu Yaya Musaddiq ya kaini ya zaunar ƙasan carpet. Shima sai ya nema waje ya zauna.
       Kawu Musa ne ya fara min da nasiha mai ratsa jiki. Kafin sauran ma su dinga karɓa ɗaya bayan ɗaya. Daga baya suka koma faɗa da gargaɗi, yayinda ni kuma nike sharɓan kuka ta cikin gyale. Dan babu abinda ya tadamin hankali sai jin muryar Yaya Musaddiq na rawa alamar karaya sanda yake min addu'ar zaman lafiya a gidan aurena. Abba ma dai yamun tasa a taƙaice, daga baya kiran wayarsa da akai ya nema excuse ya fita, da alama kuma kiran da akai masan nada matuƙar muhimmanci ne. Dan naga sai da ya fara magana da Kawu Musa suka miƙe tare suka fita. Fitar tasu bai hana iyayena cigaba da mun nasiha ba, sai da suka gamsu sun min yanda suke buƙata kafin suka sallaman Inna Hauwa ta kamani ta maidani ciki, dan mazan zasu wuce massalaci ne daga can kuma za'a ɗauro aure. Dole sai da aka sake min kwalliya bayan nayi sallar azhar saboda na ɓata fuskar dan kukan da nasha. Kaya na canja zuwa wata shadda da taci uban aiki da stones sai walwali take yi. Ga ƙamshi irin na amare ƴan ƙwalisa ina zubawa. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar nan. Lokacin da ƙarfe biyu ke cika maza suka fara dawowa alamar an ɗauro auren gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri. Wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da jijiya har ina jin wani kalar sanyi-sanyi duk da kuwa uban zafi ake zugawa a gari kasancewar watan azumin Ramadan na kawo jiki. Ƙawayena sun shiga min shaƙiyanci da buɗa a saman kai, sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba. Shin murna da farin cikin mallakar matashin saurayi ƙyaƙyƙyawa ɗan ƙwalisa mai cikar kamala da dattako irin Mansoor ne, ko kuwa fargabar rabuwa da ƴan uwana biyu ne da ke a cikin tarkon wancan terror ɗin. Bily a lokacin sam na kasa ganewa. Na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa. Sai ma wani sabon bugun zuciyar da na sake ji sakamakon shigowar aunty Zakiyya kamar a firgice tana kiran Gwaggo Gudidi data shigo tana miƙamin fura a kofi da aka dama wai na sha. Koda Gwaggo ta tambayeta lafiya, sai tace mata su Kawune ke kiranta kuma sunce tai sauri dan kamar dai akwai wata matsala. Da saurin kuwa ta fita alamar itama tana a cikin ruɗanin ne..
       Na cigaba da zama kamar butun butumi a tsakkiyar ƙawayena daketa hotuna abinsu batare da su sun fahimci kamar akwai abinda ke faruwa ba. Muna nan dai shiru hayaniyar gidan na sake ƙaruwa alamar mutane na sake cika gidan ƙananun magana suka ɗan fara fitowa. Sai dai anƙi a fito da komai a fili ana ta son basar da mutane dai. Abinda ya ɗan fara tsayamun a rai shine rashin zuwan Mansoor gidan. Dan a burikanmu akwai zuwa hotuna bayan ɗaura aure da yace zasuyi shi da abokansa da kuma ni da ƙawayena da ƴan uwana. Amma dai zuciyata nata tausata akan masa uziri, dan maybe mutane sun masan yawan da hakan bazai yiwu ba ya cika wannan alƙawarin. Wannan tunanin yasa na danne zuciyata na ajiye wannan batun a gefe.
      Isowar masu kiɗan ƙwarya bayan sallar la'asar yasa Inna Hussaina zuwa ta fita dani a ɗakin ni da ƙawayena. Sosai gidan ya cika da mutane har sai da naji ƙwalla ta cika min ido. Dan ban san munada taron dangi har kamar haka ba da zasu iya nuna wannan soyayyar garemu a irin wannan ranar. Ko a wajen kiɗan ƙwaryar ma duk da ba rawa nake ba tsaye kawai nake tsakiya ƙawaye na da ƴan uwana masu rawar zagaye da ni sai da dinga shigowa ana min liƙi, wasu kuma sukanyi hoto dani a waya harda masu video. Kusan ƙarfe biyar sai ga Gwaggo Magajiya riƙe da hannun Yaya Musaddiq da Hafizzullah wai sai sun min liƙi. Kallo ɗaya na musu su duka biyun na fahimci sunyi kuka. Dan idanun Yaya Musaddiq jajur suke. Na Hafizzullah kuwa har sun kumburo saboda shima fari ne kamar ni, dan mu biyun munfi Yaya Musaddiq haske. Hankalina ne ya tashi a take nima idanuna suka ciko da ƙwalla ina binsu da kallo. Amma sai suka ƙi yarda mu haɗa ido sai liƙi da sukemin kawai ana ihu kawunansu a ƙasa suna murmushin da ni kaɗai na fahimci na yaƙe ne. Duk yanda naso riƙe kukan nawa hakan ya gagara, bamma san sanda na riƙo hannayensu su duka ba cikin nawa. Dole suka kalleni a tare. Kukan na sakar musu kawai na faɗa jikin Yaya Musaddiq. Shima sai Hafizzullah ya ya rungumemu mu duka biyun ya saki nasa kukan. A take wajen yay tsitt, wasu na ganin mun birgesu da fassara abin namu da tsananin shaƙuwa ne da soyayyar juna. Wasu ko da suka san wani abu dake ɓoye sai suke jin tsananin tausayinmu da jin karaya suma. Nan take aka ringa tuno alkairan iyayenmu da musu addu'a. Dole dai Yaya Musaddiq ya jamu muka fita daga filin. Nan Gwaggo Gudidi ta jamu zuwa ɗakinsa ta dinga lallashinmu da mana nasiha. Haka kawai maganganun nata sai suke ta min kai da kawo dan na gagara fahimta da fassara wasu nikam. Kiran Yaya Musaddiq da akai a waya ne ya sashi miƙewa ya fita. Babu jimawa ya dawo yay kiran Hafizzullah. Anan ne Gwaggo ke tambayarsa lafiya? Sai yake sanar mata zasu maida kayan can gidan ne dan an gama kwashesu. Cikin nuna gamsuwa tace, “Oh to hakan yayi, bari na tattara su Zakiyya su sameku acan yanda aikin zaiyi sauri. In sha ALLAHU ai yanzu zakaga an kammala”.
      Da to ya amsa mata yana ficewa. Hafizzullah ya canja riga suka fice. Babu abinda na gane a zancen nasu, amma na gagara haƙuri sai da nace, “Gwaggo kodai akwai abinda ke faruwa ne? Naga sai magana kuketa yi kamar a ƙudundune?”.
         Kai tsaye tace min, “A'a babu komai ƴar nan. Kinga tashi mu koma ciki dan da anyi magriba zaki yi wanka a wanke wannan fentin da aka cika miki a fuska. Koda masu ɗaukar amarya dai sun zo ɗin sai dai mu yazam mune muka jirasu basu zasu jiramu ba”.
    Banda tacewa face bin umarninta. Tunda dama nasan dai ya kamata a kainin da wuri kodan dinner da su Mansoor suka shirya. Amma kwalliya kona wanketa dole a sake wata basai munje can gidan ba kuma aita dibi-dibi nasan Mansoor da ƙosawa akan abu, sam baya son jira. Acan ƙasan zuciyata kam ina jin babu daɗi saboda rashin ganin duk jama'ar gidan a cikin sha'anin bikin nawa. Dan yaran duka babu wanda na gani har Auta da su Yaya Abbas da Nabel da shi banama zaton yazo gidan yana makaranta. Gara ma ita Mum ɗin bayan ɗaura aure sanda Yaya Musaddiq yazo ya fita dani ɗin nan zuwa falon baƙi na ganta ita da wasu ƙawayenta a tsaye sunata faman dariya da alama akwai abinda suke tattaunawa a tsakaninsu.

       ★★Bayan nayi sallar magrib kamar yanda Gwaggo ta faɗa aka haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito da taimakon Gwaggo na kimtsa jikina. Ta kuma tsareni sai da naci abinci da wani nama na musamman mai romo a cikin kula. Naman yayi daɗi dan haka na saki jiki naci sosai, koda tace sai na cinyesa ma ban musaba na dage na cinye nasha romon. Hakan yasa cin abincin bai armashi ba garan sosai. Tun ina kallon agogo harna daina. Sai dai a raina inata mamaki, dan tara dai-dai ya kamata ace muna a wajen dinner. Amma gashi anan har taran yama wuce ba'a kaini gidan su Mansoor ba balle ai batun zuwa dinner. Bily kar kiga kamar na cika zumuɗi ne fa. Kawai dai bana son naga an saɓama Mansoor alƙawari ne, to amma yaya zanyi, sai sanda aka kaini. Matsalata kawai da babu waya a hannuna.
     Muna nan zaune Gwaggo na ƙaramin nasiha kusan goma saura akace su Yaya Musaddiq sun dawo sai a fito da amarya ga motoci sun zo. Sai a lokacin kuma naji duk na rikice. Nanfa na saki musu kuka. Duk yanda akaso na miƙe naƙi nai hakan har sai da Kawu Musa da kansa ya shigo yana faɗa sannan. Kuka nake sosai har numfashina na shiɗewa. Amma babu wanda ya saurareni, sai ma gaban Mum da aka kaini na roƙi yafiyarta. Cikin taɓe baki tana wani fisge-fisge ta ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya sai aje aita haƙuri, dama ita rayuwa ai haka take babu tabbas...” ganin tana neman sakin layi Gwaggo ta kamani muka fito. Abba ma an sake kaini na masa sallama. Yaya Musaddiq kam ya rufe kansa a ɗaki yaƙi yarda. Nasan kuka yake, dan haka nima na ƙara ƙarfin nawa kukan ina tutturjewa, amma babu wanda ya saurareni sai dai wasu nata bani haƙuri wasu na tayani matsalar ƙwallar aka fita dani. A rikicen da nake yasa bamma san kala ko adadin motocin da suka zo ɗaukata ba. Ni dai kawai an sakani a motar da ƙamshin da take yaso sakamin razani a zuciya, sai dai kuma rashin ƙarfinsa sosai da ruɗanin da nake a ciki na rabuwa da ƴan uwana ya hanani bama abin muhimmanci. Gwaggo Gudidi da Inna Magajiya ne tare da ni, sai gaba Ruƙayya ce ta office ɗin mu data zame min kamar babbar ƙawa ita da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya........✍️


_🤭Uhummm inji mai ciwon haƙori._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_

_______________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

_______________

.......Har muka iso kuka nake sosai, haka dai aka fita dani kaina a lulluɓe. Ina jin mutane nata yaba gidan. Hakan baisa naji wani abu daban ba saboda nasan gidan Mansoor kam tabbas yayi ƙyau da tsari. Sannan babu laifi babbane. Da addu'a na shiga kamar yadda Gwaggo ta bani umarni. Dan motar da aka ɗakkoni ce kawai dama ta shigo har cikin gidan. Sauran duk a waje suka tsaya. A falo aka ajiyeni kamar yanda Inna Magajiya tace. Mutane suka ɗan shishshiga kitchen da inda ba'a rasa ba. Bedrooms dai a rufe suke duka biyu dake a gidan kamar yanda naji suna faɗa. A karan farko na ɗan ji mamaki, dan nasan bedrooms huɗu ne a gidan Mansoor. Amma dai banda tacewa, bayan mutane sun gama zazzagawa suka fita dan dare ya farayi za'a maidasu gida. Sai da kowa ya fita sannan Gwaggo ta kama hannuna ta kaini bedroom da naji tana faɗa bayan ta buɗe da makulli, anan ne na gane ashe keys ɗin na hannunta sune dai suka hana mutane shiga wai dan kar a ɓata tunda dare yayi babu damar zama a gyara min. A bakin gado ta zaunar dani, tana sake jaddada min kalmar haƙuri, haƙuri dai da duk abinda zan gani, dan shi aure ibada ne bawai wasan yara ko nanaye kamar yanda mu yaran yanzu muke tunani ba. Ni dai kuka kawai nake zabga mata. Tadai samu ta zame jikinta ta gudu ta barni. Kuka na sake fashewa da shi irin mai cin rai da zuciya ɗin nan, harna zame na kwanta a gadon batare dana sani ba na cigaba da kukana.
       Tun ina darzar kuka da tunanin Mansoor zai iya shigowa har al'amarin ya fara bani tsoro. Dan gari yay wani irin shiru sai kukan karnuna amma babu Mansoor babu labarinsa. Kai komai ya fara canja min daga yanda nake tunani da hasashensa. Dan daga jiya zuwa yau komai da nake gani ba irin tsare-tsaren Mansoor ɗina bane. Komai yana zuwa min a banbancin abinda muka tsara. Mi hakan ke nufi, Mansoor ne ya canja komai a yanda na sanshi ko yaya al'amarin yake ne?. Banda mai bani amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyi na. Dan haka na cigaba da kwanciya a wajen ga ciwon kai mai tsanani na ratsani, kafin ma wani dogon lokaci na fara rawar sanyi. Ina jin yanda wata iskar hadari ke tasowa da ƙarfin tsiya amma na kasa ko motsi. Haka na cigaba da kasancewa a wajen na tsawon lokacin da ban san adadi ba har barci yay awon gaba dani batare dana farga ba....

        Hasken rana irin mai kashe idon nan ne ya addabi fuskata. Dole na buɗe idanuna da sukai min wani masifar nauyi saboda kukan da nasha. Ganin a inda nake nada banbanci da inda na saba ya tuna min da mike faruwa. Zumbur na miƙe zaune ƙirjina na luguden daka. Ɗakin na shiga bi da kallo, madaidaici ne ba wani ƙato ba can. Sai dai kayan sun masa ƙyau cas. Abu na farko dana fara lura da shi sam ba irin fentin gidan Mansoor bane ba, kuma bedroom da Mansoor ya nunan a matsayin nawa randa mukazo ƙatone sosai. Ƙirjina yay wata irin girgiza. Sai dai tunawa da banyi sallar asuba ba yasa na tattare komai zuwa gefe na miƙe. Ƙofar da na gani da nakema zaton bayi ne na nufa. Nan ma dai ba irin toilet ɗin gidan Mansoor bane. Kai ƙwalwar kaina fa na neman juyewa. Amma dai na sake ƙoƙarin dakewa nayi alwala na fito. Akwatin dana gani saman bed side drawer na buɗe, na samu hijjab kamar yanda nai fata, dan haka na nutsu domin gabatar da salla..
       Ina idar da sallar na miƙe kamar zararriya, dan kaina gaba ɗaya a juye yake da komai. Fitowa nai gaba ɗaya daga bedroom ɗin. Ganin wani dake a kusa da shi yasa na buɗe na shiga nan. Gabana ya faɗi. Dan babu komai a ciki sai ƙatuwar katifa irin wadda ba'a sanyawa a gadon nan. Sai wani ɗan ƙaramin akwati mai shegen ƙyau. sai takalma haif cover suma dai masu ƙyau sosai, a saman katifar da agogo da waya kusa da shi, sai can gefe kaya ne da aka cire shadda honey color data ciza sosai. Ga wani ƙamshi na musamman dake tashi har ina jin kamar nasan ƙamshin, amma dai na hana zuciyata hasasowa. Fitowa nai ƙwaƙwalwata na sake birkicewa. Falo ne dake tsaka tsaki, shima dai yayi ƙyau da kayan da aka jera masa, saukar idanuna akan wanda ke zaune daga can cikin ɗaya a kujerun dining ya saka zuciyata wata irin girgizar da ya rage kaɗan ta biyo ta bakina ta fito. Karkarwa jikina ya shiga yi, irin wadda bamma san na cigaba da tafiya ba cikin matuƙar sassarfa. Har na iso gaban dining ɗin bai ɗago ba. Yanata danne-dannesa a laptop hankali kwance. Ga mug dake ta turiri alamar shayi ko coffee a ciki.
     “Wanene kai? Miya kawoka nan? Ina ka kaimin mijina?”.
   Tambayoyi uku a jere suka fito a bakina dake rawa. Kamar baima jini ba, ko nace bai san da zuwana wajen ba. Dan ko motsi baiyi ba balle ya ɗago ya kallan, aikinsa kawai yake hankali kwance cike da ƙwarewa.
          A matuƙar harzuƙe hawaye masu zafi na rige-rigen sakko mini cikin daka tsawa na ce, “Da kai nake magana malam!!”.
   Cak ya tsaya daga danna keyboard ɗin laptop ɗin da yake yi. Nasan kuma yanda nai tsawar ne da matuƙar ƙarfi ga jikina na girgizar tashin hankali da ɓacin rai. Na sake zabura zan masa wata tsawar ganin nan ma bai amsa min ba yay wata irin juyowar da ta saka ni yin tsalle a lokaci guda da zuciyata saboda tsabar kiɗima. Sai gani rijif a ƙasa wanwar.
       “Ba'a min tsawa”.
    Ya faɗa a dakensa cikin silent voice ɗin nan nasa na gadara babu alamar damuwa da halin da yaga na shiga kuma. Sai ma ɗauke kansa da yay ya sake maidawa ga screen ɗin laptop ɗin. Yaraf kake jina na ƙarasa zubewa ƙasa gaba ɗaya. A hankali sai kaina ya fara juyawa, yayinda lips ɗina ke wata masifaffen rawa ina nunasa da yatsana da shima ke rawar. Tun ma ina banbance tsakanin haske da duhu har hakan ya fara neman gagarata. Tuni na tafi luuu ƙasa gaba ɗaya alamar ina neman suma. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba sai farkawa nai na sake gani na a inda na faɗin yashe. Da ƙyar na iya miƙewa hannuna dafe da kaina dake faman juya min. Kai tsaye inda nasan yana zaune na kai idona. Wayam babu kowa daga shi har laptop ɗin nasa. Sai mug ɗin nan na shayi kawai ajiye. Falon na juya ina sake ƙarema kallo. Yanzu kam ni kaɗaice a cikinsa da alama, sai zuciyata ke ayyana min kodai mafarki ma nake yi ne? A gaskiya sai dai mafarkin kuwa, dan wanda idona ya ganarmin a gidan nan nafi fatan ya kasance a mafarkin ne. Kasa daurewa nai, cikin layin juyewar kai tamkar wata ƴar maye na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton hanyar fita ce. Da ƙyar na iya lalubar handle ɗinta na buɗe, cikin yanayin dishi-dishi na dinga bin harabar gidan da kallo, ba wata babba bace dan bata wuce ɗaukar motoci uku ba suma a ɗan takure. Motar da nake ƙyautata zaton an ɗakkoni a ciki jiya kawai ce

Please Login or Register in order to submit comment