Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su fito tare kamar yanda ta mata alƙawari, maybe bata sameta ba ta shiga nemanta, ko kuma ta sameta a lokacin da take bude-buɗen ƙofar ko ma ɗaukar video ɗin. Dan inba haka ba babu yanda za'ai tai ɓatan dabo gareta. Hasashe na biyu lokacin da take faɗa maka ko wani ya jiku. Cikin biyun nan dole ɗaya ya tabbata, kuma duk inda zancen ya fito to tabbas an samu Maash an fargar da shi komai shiyyasa yasa ake bibiyarta.”
       Cikin jinjina kai Mansoor ya ce, “Tabbas hasashen ka zai iya zama gaskiya Yaya. Amma ni a wannan gaɓar ma sai hankalina yaso rabuwa biyu akan wasu dalilai. Maash bawai ƙaramin mutum bane. Kana ganin ya aikata wannan kisan ya kuma san ya aikata har wata ace ta ɗaukesa a hoto mai motsi ya sani kuma ya zauna sakaci. Duk da yanda muke tunani abinda masu hannu da shuni ɗin nan suka tsana a rayuwarsu shine su binne wani laifinsu amma ya zama yana a hannun waninsu ko waninsu ya sani. Zakaga suna gaggawa wajen ganin sun daƙile komai. Idan lissafina yayi dai-dai wata fa kusan ɗaya kenan da faruwar komai. Kana ganin zai zaman ɓata lokacine akan wani bibiyar Samraah bayan yana da hanyoyi masu yawa dama zai karɓi video ɗin a hannunta batare da wata gargada ba. Karfa ka manta har hira yazo anyi da shi kuma itace tai da shi, randa aka saki hirar kuma ƙura ta tashi sosai da kace nace ɗin mutane harda masu cewa akwai alaƙa tsakaninta da shi, nasan dai kasan komai ba sai na sake maka bayani ba. Na kawo wannan hujjojin ne saboda bana son mu shagala da yawa a kan shine wanda kuma ke son ƙulla tsiyar na gefe. Kuyi haƙuri MD kansa na cikin zargina. Dan na jima da fahimtar yana son Samraah na hauka, randa kuma ta kai musu kayan saka bikin mu ya tabbatar ma da kowa hakan. Sai ƴar uwarku Baby. Tana sona matuƙa, wasu dalilai ne suke dakufeta, naji a majiya kai ƙarfi cewar tai alƙawarin sai tabi tako wace hanya domin ganin auren nan namu bai yiwu ba, dan tana da babban plan akan haka akwai kuma mai bata ƙwarin gwiwa ta bayan fage. Saboda yima kanta alwashin indai itama bazata sameni ba sai dai su rasa su duka. Da farko na ɗauki zancen shirme kawai irin nata na ƴan shaye-shaye, sai dai wannan abin na yanzu ya fara haskomin da gaske zata iya komai fa. Dan haka musa hankalinmu jikinmu domin tabbatar da ko wanene”
        “Shaye-shaye kuma? Wai babyn ce ke shaye-shaye ko wa?” na faɗa ina kafe Mansoor da idanu. Murmushi kawai ya mun da faɗin, “Hum Samraah kenan, ke dai ALLAH ya shirya mana zuri'a kawai”.
     Yaya na kalla a firgice, sai naga shi babu alamar mamakin zancen akan fuskarsa. Kasa haƙuri nayi sai da na ce, “Yaya kenan kaima kasan tana Shaye-shayen?”.
    Sai da ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya furta, “Na sani Samraah. Na kumayi iya yina na ganin ta daina amma hakan ya gagara. Na lurar da Abba amma ya nuna sharri nake mata. Tun daga nan na tattarasu na watsar”.
      Zancen ya matuƙar girgizani gaskiya. Kamar yanda sosai maganar Mansoor tayi tasiri garemu ita game da MD da Baby da zasu iya sakawa a bibiyeni. Dan duk abinda ya faɗa gaskiya ne. Ni komai ma sai naji ya sake susuce min. Amma duk da haka Yaya yace bazamuyi sakaci da duka ɓangarorin uku ba. Zamu saka ido za kuma ku ɗauki matakin daya dace da kowanne. Dan haka zamu kai report wa yan sanda akan ana bibiyata, amma bazamuyi batun video ba fa, zamu bar ƴan sanda suyi aikinsu, idan ma Maash ɗinne da ga baya idan fito da videon ta kama sai muyi hakan. Nanma mun gamsu, kun kuma bashi goyen baya, duk da ni dai naso ace tun yanzu muka fidda video ma wa yan sanda. Amma ban san dalilinsu na son a ɓoye video ɗin nan kamar wani suna tsoronsa.
      Kwana biyu dayin haka aka kawo lefena da ga gidan su Mansoor. Akwatina har goma sha biyu shaƙe da kayan alfarma na gani na faɗa. Babu wanda zaice lefen nan bai birgesa ba. Sai dai anga tsagwaron hassada daga Mom dan ta kasa haɗiye komai. Harda zage-zagenta wai ai saurayin Baby ne na kwace da asiri. Kuma ba kowa ke kawo min asirin ba sai Gwaggo Gudidi. Abu kamar wasa dai sai da aka kwashi rigima. Dan ƴaƴan Gwaggo Gudidi duk sun zo suna gidan. Rikici akai sosai na gaske. Lokacin Yaya Musaddiq shi baya gida. Yana wajen aiki, kamar dai wancan karon ya damƙa komai hannun matar ogansa aima baƙi abincin tarba da kayan maƙulashe. A wajen aikin ma ba zama yay ba shi da Mansoor suka fita police station wajen batun ƴan sanda. Sun shigar da report tare da bada lambobin mota har uku dana basu.. Suna can har aka gama rikin nan kowa ya kama gabansa dan su Gwaggo ma sun ɗauke lefen nawa daga gidan sun wuce da shi can gidanta. Acewarsu barinsa gidan Abba bazai yiwu ba su Mom zasu iya salwantarwa saboda basu da isashen mutunci. Ashe ko hasashen su Gwaggo yay dai-dai. Dan su Mom sun shirya mummunan ƙudiri kuwa akan lefen nan aka ɓata musu shiri. Wannan yasa suka huce kaina sanda na dawo. Dan bana gidan ma ni ina gidan wata ƙawata ta islamiyya. Duk yanda naso daurewa na kasa. Ranar sai da nai kuka sosai da jin kewar iyayenmu. Daga ƙarshe nai alwala nayi nafilfilina tare da miƙama UBANGIJI kukana. Wannan ɓacin ran dana kwana da shi yasa banyi aikin komaiba a gidan. Sai ma shiri da nai tunda farar safiya domin wucewa gidan su Joy ko zan rage damuwa, amma zan ɗan fara zuwa office saboda saƙon da MD ya turamin jiya da dare kusan 12 kan dan ALLAH yana son ganina a office yau idan babu damuwa. Jin yace abu mai muhimmanci ne yasa na amince zanje ɗin, kuma bana ma son yinin gidanmu a yau ɗin sam. Na fito na leƙa ɗakin Yaya sai na samu ya fita. Nayi mamakin fitar tasa ta sassafe yau. Amma sai nai wucewata akan zan kirashi awaya. Zuwa da rana sai na samesa a garejin dan ina son mu ɗan tattauna wani abu.
         Napep na samu na shiga. Mun fara tafiya inata ƙoƙarin kiran numbern Yaya sai naji an kira sunana. Da mamaki na ɗago ina kallon wanda ke kusa da ni dana samu a napep ɗin, ganin babu wata alama data nuna shine yay kiran sunan nawa na kalla mai napep shima. Shima kuma babu alamar shi ɗin ne. Cikin takaici da jin haushi na sake ƙoƙarin maida kaina ina mamaki. Sai kuma aka sake faɗin, “Samraah!”. A fusace na ɗago yanzun kam. Kafin na samu damar cewa komai naji abu a fuskata. Yuuuu naji kaina ya fara mun. Cikin zabura nai yunƙurin dira daga napep ɗin sai dai na kasa hakan. Dan cikin ƙanƙanin lokaci jikina yay wani masifar nauyi na silale jikin kujera idanuna na lumshewa. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba kuma......✍️


_Duk da nasan Maash ya bada kwangilar bibiyar Samraah. Amma nima zancen Mansoor ya fara sakani a cikin ruɗani. Amma bana son ku ruɗe kumuje zuwa dai, dan har yanzu fa wasan ma bai fara ba. Yaya Maash ne da wannan aika-aikar ko kuwa MD? Zai iya zama Baby ma fa. Kai Mom ma ba barinta zamuyi ba. Shin waye yay kidnapping Sam-G🤥🤔?._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_



......Tunda suka tashi Mom taga Samraah batai aikin komai a gidan ba ta ƙara harzuƙa. Lallai yau dolene taci uban yarinyar nan dai-dai gwargwado har sai taga ubanda ya tsaya mata a gidan nan. Fuuu ta nufi ɗakin barcinsu tunda tasan yau weekend bata fita aiki. Sai dai me wayam babu Samraah. Sai auta da Bibaa dake barci. Da farko tai tunanin tana wanka. Dan haka ta koma falo tai zaman bala'i tana jira. Bayan kamar mintuna goma sai ga Bibaa ta fito tana miƙa da alama tashinta kenan.
       “K koma ko kiramin yarinyar nan Samraah”.
     Da ɗan mamaki Bibaa ta ce, “Ai bata ɗaki Mom.”
    “K ban san iskanci ki duba toilet mana ina zata je”.
   “ALLAH Mom bata toilet yanzu fa na shiga bayin na fito. Kodai tana kitchen tana aiki?”.
             A ɗan ƙufule Mom ta ce, “Tunda ni makwauniya ce ko. Dalla fita nasan tana ɗakin shegen can shima munafukin na biyu. Jeki daga shi har ita ki kira min su”.
     Babu musu Bibaa ta amsa da to. Sai dai babu jimawa sai gata ta dawo wai ɗakin a kulle yake. Dai-dai nan Abba ke fitowa da ga ɗakinsa. Tambayar mike faruwa yayi dan tun ɗazun yake joyo hargagin Mom da ga cikin ɗaki. Aiko a cikin tsantsar masifa take sanar masa. Ɗan jimm yay kamar ba zai ce komai ba. Sai kuma ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga neman Yaya Musaddiq. Bugu biyu kuwa ya ɗauka. Daga can ya gaida Abban cikin girmamawa. A daƙile ya amsa masa kamar yanda ya saba. Kafin ya ɗora da faɗin, “Kai kuna ina ne?”.
     Da mamaki Musaddiq ya ce, “Abba ina gareji. Akwai wanda zai zo ya ɗauka motarsa ne shiyyasa na fita da wuri”.
          “Uhhmyim ita Samraahn tana tare da kai kenan?”.
    “Samraah kuma Abba. Ni kam mi zaisa na taho da Samraah nan. Tana nan a gida ai na barta tunda yau bazata je aiki ba”.
    A harzuƙe Abba ya ce, “To bata nan”.
      Sosai zuciyar Musaddiq ta wani harba. Muryarsa na nuna alamar rawa ya ce, “Abba kamar ya bata nan. Ina Samraah zata je da sassafen nan bayan bata da office yau?”.
    “Sai ka tambayen tunda yawo nake da ita a bayana”. Daga haka Abba ya yanke wayarsa. Hankalin Musaddiq yay masifar tashi batare da yasan dalili ba, tunda ta saba duk inda zata ko baya gida sai ta kiransa ta sanar masa a waya. Dan haka babu arziƙi ya baro gareji da fatan ya zo ya samu Samraah ta dawo. Dan tunda Abba ya katse wayarsa ya maida akalar kiran kan Samraahn amma wayar na shiga anƙi a ɗauka. Daga baya ma aka kasheta duka baki ɗaya. Wannan kuma ba halin Kandalarsa bane ba, balle ma ace shine yay kiranta da kansa...
     Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan, inda ya samu har lokacin Mum nata masifarta. Al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai har sha biyun rana babu wani bayanin Samraah. Tun kowa na ɗaukar komai wasa har la'asar babu wani bayani. Zuwa lokacin anata buge-bugen waya wa ƴan uwa amma kowa sai yace bata je ba. Hakama ƙawayenta duk da Musaddiq yasan ita bamai yawan biye-biyen gidajen ƙawaye bace, ƴan uwan ma wace ala cika. Har gidan su Mansoor an sani zuwa sannan. Zuwa kusan biyar na yamma sai ga ɗayar wayarta an samu, wanda ya ɗaga ya tabbatar musu tsinta yayi. Harga ALLAH kuma ya yarda zai basu ne saboda yaga hoton Samraah ne a fuskar wayar. Hankali tashe Mansoor da Musaddiq sukaje inda ya kwantata yake, dan su ne dai keta faɗi tashin. Su Mom sunce basu yarda wani abune ya sameta ba sai dai idan yawon tazubar ɗin data saba tafiya ne ta tafi. Dan haka sukai burus da komai kamar basu san mima ake ba. Garama Abba yakan yi ɗan zugumm alamar tunani. Da Mom ta tsikaresa da hira kuma sai ya ware.
    Mansoor da Musaddiq sun amso waya tare da mask ɗin Samraah da eyeglasses ɗinta da aka tsinta. Ya kuma kaisu inda ya tsinta ɗin mutane kuma da yawa sun bada shedar tsintar yayi da gaske. Dan abun ya faru ne a idon mutane kusan uku dake sana'a a dai-dai wajen. Kasancewar suna fitowa da safe sosai suma. Sai dai sunce sunga wata napep da mota blue sun tsaya a wajen amma basu san mi sukayi ba, sai da suka wuce ne wanda ya tsinta wayar yake ganin abinda ya tsinta ɗin. Kuma yay magana da su bai ɓoye ba. Zuwa yanzu kam hankalinsu yakai ƙololiwar tashi, dan haka take suka kai report a station mafi kusa. Dalilin Mansoor nada ɗan halinsa tun a lokacin aka shiga traicing ɗayan layin Samraah. Dan kuwa wayoyinta biyu ne, kuma duk manya ne. Ɗaya tana amfani da ita saboda aiki, ɗaya kuma abinda ya shafi family ɗinta da ƴan abubuwanta ne a ciki. To ta aikin aka ajiye aka tafi da waccan. Har dare babu wani cikakken inpometion mai gamsarwa, zuwa sannan kuma dai tashin hankalin Abba ya fito fili. Dan Gwaggo Gudidi tazo tana faman kuka da faɗin lallai a binciki su Mom sun san inda suka ɓoye Samraah. Tunda kowa yaji dama abinda Mom ɗin ke faɗa a jiya gaban kowa. Mom zata hayayyaƙo maƙwafta da suka shishshigo suma suka nuna lallai akwai ƙamshin gaskiya a batun Gwaggo Gudidin. Kamar wasa kuwa sai ga rikici ya ɓarke. Dan zuwa gab da magrib su Musaddiq suka zo anguwar da ƴan sanda. Nanfa hankalin Mom yaso ya fara tashi, sai dai tana ta ƙoƙarin dannewa ita a dole kada aga gazawarta..
       Tambayoyi ƴan sanda suka musu har Auta ba'a bari ba. Mum kamar a ruɗe take amsa komai, dan haka ɗan sandan da case ɗin ke hannunsa ya dasa mata ayar tambaya. Sai dai bai ce komai ba suka wuce akan zuwa safiya zasu iya dawowa kosu nemesu a can station ɗin su.

💫 (✧✧)✨(✧✧)✨(✧✧)💫


Sannu a hankali na motsa idanuna da sukai min matuƙar nauyi da ɗaurewa. Sai kuma na shiga buɗesu sannu-sannu, a wani ɗaki mai ƙarancin haske na tsinta kaina alamar yamma tayi. Dan kiraye-kirayen sallar magrib ma naketa jiyowa. Ƙirjina ne yay wata masifar bugawa. Nai saurin ambaton ALLAH ina sake lumshe idanuna da sake buɗewa. Tabbas ta tabbata anyi kidnapping ɗina. Da ƙyar na iya tashi kasancewar duk jikin nawa babu wani ƙarfi. Ga wani irin fitsari da nake ji. Jiri-jiri dake neman kwasata yasa da ƙyar na iya dafe bango na miƙe. Lalube na shigayi ko zan samu wani haske. Cikin ikon ALLAH na samu makunar fitila. Idanuna dake lumshewa da buɗewa na sake warewa da ƙyau. Ɗakine babba sosai. Sai katifa a ƙasa ƙarama irin ta ƴan makaranta, akwai bargo da filo an kuma shimfiɗa bedsheet a kanta. Gefe kuma handbag ɗina ce sai leda mai tambarin gidan abinci har guda biyu a kusa da ita. Tare da ledar ruwa guda. Da ƙyar na iya jan ƙafata zuwa ƙofa. Na shiga ƙoƙarin murɗawa amma sai na sameta rufe gam. Inda labule yake ma sake nufa da ƙyar dan nasan bazai wuce window ba, na turesu da ƙyar. Ita ɗince kuwa, sai dai a rufe, nai ƙoƙarin na buɗe da ƙyar. Amma ƙarfen da akai adonta da shi ƙanana ne sosai ta yanda ko hannu bazai fita ba ma. Sosai zuciyata ke rawa yanzun kam. Ban haƙuraba na sake nufar ɗayar, nan ɗin ma dai irinta ce. Inda ke da kamar ɗan corridor na nufa, amma sai na samu ƙofar bayi ce a wajen. Naga hakanne sakamakon buɗewa da nai. Bamma san sanda na silale a wajen ba na saki wani irin kuka mai tsuma rai da girgiza zuciya. Na jima zaune a wajen ina kuka kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Kafin na sake miƙewa da ƙyar na shiga toilet ɗin. Fes yake babu wani datti. An kuma ajiye wadataccen sabulun wanka, omo, toothpaste brush, sosan wanka. Kai harda kayan wanke bayi. Babu dai abinda zaka nema ka rasa daya shafi hakan. Alwala na ɗaura batare da nabi takansu ba, zuba ruwan alwalar a jikina ya ƙara taimakawa naji na ɗan warware. Anan ma sai da na duba window sai dai yayi sama sosai koma ƙarami ne. Haka na fito na dawo ɗakin. A saman tabarma dake gaban katifar malale nai sallar azhar da la'asar har magrib. Sake kife kaina nai a wajen na sake buɗe sabon shafin kuka. Nama rasa ina zan kai tunani na. Kamar wadda aka zaburar na zabura inda bag ɗina take. Da sauri na buɗeta na shiga laluben wayata jikina har wani mazari yake tsabar yanda nake a ruɗe. Ganin kamar laluben ma baya min kawai na zazzage komai na cikinta burina kawai wayata ya faɗo, amma babu ita babu alamarta, sai ƴan kayan shafana dana zuba lips gloss ne kuma da fauda sai ƙaramin oil misk da face mask guda biyu da bana rabo da ita a jaka akoda yaushe. Bamma san na sake sakin wani wahallen kuka ba a wajen tare da zubewa ƙasa daga ni har bag ɗin........✍️





_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_



.......Kusan mintuna biyu ina zabga kuka, kafin na sake jawo jakar da tarkacen ciki dana juye ƙasa duka zuwa gabana. Sake zazzagawa na koma yi kamar wadda ta zautu. Ko abinda keda alaƙa da waya babu a cikin duka wayoyina biyu. Amma na kasa yarda, sai ƙara zazzagawa nake da ɗaɗɗaga kayan dana zazzage kamar wata mai neman barimar ɗan kunne. Sai da dai zuciyata ta tursasani akan babu ɗin da gaske sannan na sake fashewa da kuka tare da yin wurgi da jakar. Haka na kasance a wannan daren babu wata nutsuwa irin ta cikakken mai hankali a tare da ni. Sai dai koda wasa ban mance ambaton UBANGIJINA ba. Gab da asubahi wani wahalallen barci yay awon gaba dani, ban tashi farkawa ba sai kusan bakwai da kwata. A firgice na miƙe na nufi toilet na ɗauro alwala. Bayan nazo na gabatar da salla koda na idar a wajen na cigaba da zama na fara karatun Alkur'ani a hankali jikina duk babu ƙarfi, dan akwai yunwa ma tare dani, jiya gaba ɗaya banci ba ban sha ba. Nafi awa ɗaya da kusan rabi a wajen naji ana ƙoƙarin buɗe ƙofa. A zabure na ɗago daga cusa kaina da nai cikin ƙafafuna dan a haka nake karatun. Kallo ɗaya mai shigowar yamun ya ɗauke kansa, yana sanye da mask baƙi kamar yanda komai na jikinsa ke baƙi, dan hatta hannunsa akwai safar hannu baƙa. Ya kuma toshe idanunsa na baƙin eyeglasses da babu abinda zan iya ganewa ko gani nashi. Irin ledar dake ajiye a ɗakin ce a hannunsa. Batare da ya tankamin ba ya ajiye ya ɗauki ta jiya dako kallonta banyi ba ya nufi hanyar fita abinsa.
      Muryata na rawa nai saurin dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Wanene kai? Miyasa kuka kawoni nan? Mi kike buƙata da ga gareni? Wani laifi na muku ko kuɗin fansa kuke nema?”.
     Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Ina kammala faɗa kuma bai tanka ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sake kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawaye na gangaro min da gudun tsiya. Lallai ina a tsaka mai wuya, gashi bamma san wanda zan iya zarga ba. Dan gaskiyar Mansoor ne. A wannan gaɓar hatta da Baby da MD kai har Mom da Abba kansa ni zasu iya shiga lissafina ma. To amma ni abinda ke damuna waɗan nan mutanen da duk na lissafo idan sunyi hakan gareni duk miye ribarsu? A yanzu ba kaina kawai nake tausayi ba  ƴan uwana da halin da zasu shigane ke matuƙar tada min hankali fiye da komai. Ga Mansoor shima. “Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki ka kuɓutar dani da gaggawa. Kasa kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya a zukatan ƴan uwana da masoyana da ni kaina. Duk wanda bashi da laifi akan wannan al'amarin ya ALLAH ka hanashi shiga wahala. Mai hannu a ciki UBANGIJINA ka hanashi damar cutar dani koda yayi niyyar hakan a gareni”. Zamewa nai a hankali na sake kwanciya ina mai cigaba da karatun Alqur'ani na. A haka barci ɓarawo yay awan gaba dani tunda dama bai isheni ba. Ga kaina na wani kalar masifaffen ciwo.
      Barci nayi sosai, dan ban tashi farkawa ba sai da naji ƙarar an buɗe ƙofa. Firgigit na miƙe kuwa ina murza ido. Mutumin ɗazu ne dai kuma kamar ɗazun fuskar tasa a rufe. Wata ledar abincin ya sake ajiye min da wata babba fara ita kuma yanzu ma ya sake ficeewarsa batare da yamun magana ba ya sake kullenin. Kwata-kwata yanzu ma hawayen nawa sun kasa fitowa. Da alama zuciyar ta fara dakewa. Salloli da nake jiyowa anatayi a masallatai yasa na miƙe a hankali. Jikina sai ciwo yake tako ina. Na tabbatar harda rashin wanka dan ni mutum ce mai son yawan wanka a rayuwa. Kuma ko yaya idan banyi ba sai na dinga jin babu daɗi. Naso na daure kada nayi, kamar yanda nake ƙoƙarin hana kaina cin komai, dan ko ruwa sai a wajen alwala nake ɗan haɗiyarsa. Amma na kasa hakan dan wani ƙyanƙyamin kaina nama fara ji, harma zuciyata na wasi-wasi akan yin salla da su. Ledar kayan na janyo na shiga fiddosu. Dogayen riguna ne har biyar duk marasa nauyi da bazasu takurani ba. Sai hijjab biyu manya. Harda su b&p shidda-shidda. Sai kayan barci har uku da man shafawa da turare. (Ko wanene wannan anyi cikakken ɗan iska ma wlhy. Wato komai anyisa akan shirine, babu kuma alamar zan bar nan ɗin a kusa tunda harda tanadin kayan sakawa). Duk a zuciya nake wannan tunanin. Cikin jin ban aminta da ɗakin ba na ɗauka doguwar riga ɗaya da b&p na shiga toilet. Wanka nayi da ruwa masu ɗumi dan akwai hitter a toilet ɗin. Sai naji jikina ya rage nauyi, hakama zuciyata. Na ɗan ji ƙarfi da nutsuwa har ƙwaƙwalwa ta na iya sarrafa tunani yanda ya kamata. Brush shima nayi na ɗauro alwala na sake fitowa. Banbi takan mai da abinci ba na koma na kwanta a katifar na lumshe idanu kawai ina mai faɗawa duniyar tunani.....

       ✨💞✨💞✨💞✨

    Zuwa safiya labari ya fara karaɗe gari da social media. Abinka da sananniya musamman ma a watanni biyun nan da sunanta yay amsa kuwwa a lungu da saƙo sakamakon abinda ya faru a wajen taron buɗe Companyn Maash da kuma hirar da tai da shi. Ta wani ɓangaren kuma wanda basa harkar yanar gizo sun santa ne a dalilin shirin da take gabatarwa ta hanyar rediyo. Duk wani wanda ke a office ɗinsu hankalinsa a tashe yake. Musamman ma MD da ƴan sanda suka gano shine mutum na ƙarshe daya tura mata text message akan yana son ganinta. Dan haka a ranar Monday ɗin ƴan sandan suka gayyacesa office ɗin su. Gefe kuma gasu Mom suma an tattare zuwa station saboda abinda sukaita faɗa a

Please Login or Register in order to submit comment