Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

books ɗinsa a gefensa barbaje alamar homework yake barcin ya kwashesa. Ɗagashi nai na maida kan katifa. Sannan na tattare books ɗin na ajiye masa gefe bayan na duba abinda yake. Yaron akwai brain, inba ni ba babu mai zama damuwar koya masa homework, sai idan Abba. Wani lokacin ma sai kika yayi da kansa kafin ma na dawo, sai dai na ɗan masa gyararraki kawai. Wanka nai ƙoƙarin shiga, sai dai bayin duk an ɓata shi, nasan Bibaa ce zatai wannan aikin ba wani ba. Na rasa mike damun kan yarinyar nan, amma zan koya mata hankali. Tanada ɗakinta ita kaɗai amma tsabar shaiɗanci tace tsoro take ji a can, shine Abba yace ta dawo nan mu zauna wai sai ta ƙara girma. Da farko na ɗauka haka ɗinne, sai daga baya na fahimci Mom ce ta sakata yin hakan dan ta dinga ɗaukar rahoton duk motsina tana kai musu. Tun wani lokaci da naji tana faɗama Mom wayar da mukai da Mansoor nagane hakan. Bayin na sake gyarawa sannan nai wankan. Harna fito na gyara jikina banji motsin kowa ba. Ba'a wani ɓata falonba yau sosai, dan haka na wuce kitchen. Shi kam yana nan jibge da kayan wanke-wanke tun daga kofunan kalacin safe har na rana da sukaci. Kaina na girgiza ina mai jin tausayin Bibaa da Baby a rayuwa. Dan ita Mom gani take gata take musu bata san kashe musu rayuwar take ba, haka kullum da rayuwar take a gidan, idan nai aikin safe na fita babu abinda suke kaudawa har sai na dawo na sake yi, badan nima na zama jan wuya ba abincin rana ma sai na musu na saka a kula. Sai da na nuna musu nima tsagerar kaina ce sannan, shiyyasa kullum basu da abincin rana a gidan sai taliya ko cus-cus ko macaroni, indomie. Sai idan akwai stew ne zakiga sun dafa farar shinkafa. Stew ɗin kuma zakiga dole nice zanyita, Mom taƙi yarda a ajiye mai aiki wai ita kishi, randa nayi aure to naga ubanda zai zo ya musu. Kwanikan na fara tattarewa na wanke, ƙafafuna duk sunyi tsami saboda tsaiwa. Haka dai na daure na kammala na maida komai muhalinsa sannan shima kitchen ɗin na shiga gyaransa. Ƙaramar indomie na dafa guda biyu, na raba biyu naci tawa anan na juyema auta tasa a plate. Har lokacin babu wanda ya dawo, mamaki ya sake kamani da tunanin ina sukaje haka ne?.
      Har akai sallar magrib sai mu kaɗai a gidan. Sai bayan an idar Abba ya shigo. Fita mukai ni da auta daya tashi muka gaishesa. Na wuce na kawo masa ruwa na koma ɗaki abina na barsu anan falo. Sun fita sallar isha'i nima zan kabbara tawa naji hayaniyar shigowar su Mom. Banbi takansu ba na tada sallata. Sai da nai har shafa'i da wutiri sannan na fito musu sannu da dawowa. Kaya na tarar barbaje a falon kashi-kashi. Na sakawa dana kwalliya harda na ciye-ciye alamar dai daga kasuwa suke. Ganin hankalinsu baya kaina dan ko gaisuwar ma da kai Mom ta amsa min na juya na koma abina ina mamaki, dan tabbas da kuɗin Yaya na jiya akai wannan sayayyar kenan. Jinai raina ya ɓaci matuƙa, dan haka na fito na wucesu. Yanzun ma hankalinsu babu alamar yana kaina. Ta ihun murnar kayansu suke kawai. Ɗakin Yaya Musaddiq na nufa, yana tsaye da alama yanzu ne yake dawowa massalaci. Ganina rai ɓace ya sashi faɗin, “Jikin ne?”. Kaina na girgiza masa ina kaiwa zaune. Cikin zafin rai na ce, “Wlhy Yaya zancen kuɗin sarƙar nan shirine kawai. Ko kasan matar can yau kasuwa suka shiga ita da ƴaƴan nata gasu can sun baje kaya a falo kamar za'a buɗe kanti. Kasan kuma babu yanda za'ai hakan ta faru Mom ta iya kashe kuɗin sarƙar nan a banza haka da gaskiya ne”.
       Murmushi mai sanyi Yaya Musaddiq yay hana kaiwa zaune kusa dani. Cikin sauƙaƙa murya tare da riƙo hannuna cikin nashi ya furta, “Cool down sweetheart. Sune a ƙasa ai. Bakiji shata na faɗin ku gargaɗi mai gina ramin mugunta ba. Ni nasan dama koda an ɗauki sarƙar ma bata kai ta kuɗin data faɗa ɗin ba. Amma ba komai ALLAH zai bamu wasu. Yanzu ma Abba ya bar ɗakin nan”.
       “Miya faru ya shigo?”.
Na faɗa cikin mamaki tunda nasan dole akwai dalili. Hannuna ya saki yana miƙewa da ɗan taɓe bakinsa. Ya zare jallabiyarsa ya ajiye sannan ya koma ya zauna dan jikinsa akwai dogon wando da t-shirt fara. “Yazo ya sameni akan wai tunda yaga inada kuɗi ni ne ya kamata na miki komai na aure. Dan shi gaskiya yana a cikin damuwar rashin kuɗi. Saboda hakane ma yaƙi yarda su tsaida rana a randa iyayen Mansoor suka zo. Amma da yasan har inada wannan kuɗin haka aida an kammala komai. Dan haka zai kirasu suzo weekend ɗin nan a tsaida ɗin. Na kuma bashi aron 200k zuwa ɗan wani lokaci zai bani..”
       “Kuttt! Amma mutumin nan ko! Wai mike damun Abban nan ne?. Dama ko bai faɗaba waye ke jiran wani abu da ga garesa mtsowww aikin banza. Sannan kuma bashin ka amsa zaka bashi Yaya?”.
    Murmushi Yaya Musaddiq ya saki mai haɗe da dariya, sai kuma ya girgiza kansa. “Kai wannan yarinya masifaffiya ce ke wlhy, wanda basu sanki bane kawai suke miki kallon mai haƙuri. Ni ALLAH har ma na fara tausayin Mansoor bawan ALLAH shi gashi da sauƙin halin tsiya”.
    Baki na tura ina faɗin, “Kai Yaya nice masifaffiyar?”.
      “Ta bugawa ma kuwa a jarida kandala. Wani lokacin da idan kina abu sai naga kamar ma kece Yayar tawa. Shiyyasa Hafizzullah ke cewa da kece Mamanmu da mun shiga uku”.
      Dariya na ƙyalƙyale da shi. Na ce, “Masherancine yaron nan ai. Dan ALLAH Yaya weekend ɗin nan muje mu gansa tunda wancan ya shuɗe. ALLAH ina kewarsa”.
        “Karki damu zamuje in sha ALLAHU. Dan na kammala masa ma siyayyarsa.”
     Cike da farin ciki nace “Yauwa Yayanmu, kuma Babanmu. Yanzu dai yaya mi kacema Abban?”.
       Sai da yay murmushi ya ce, “Mizan ce masa kuwa Samraah. Na gaya masa kuɗin dana bama Mom ɗin jiya ne kaɗai dama a wajena, sai abinda ya rage baifi saura dubu arba'in ba nama cire wani abu a ciki na haɗama Hafizzullah provision. Dama na tara wancan kuɗinne dan na basa shi da Mom ɗin su rage hidimar biki. Ga kuma abinda ya faru yanzu. Ina gaya miki sai kawai ya hauni da faɗa. Wai to wlhy sai nasan inda zan nemo wasu kuwa. Dan shi dai baida wani kuɗin yin hidimar nan bai kuma da hanyar samunsu. Inba hakaba kuwa sai dai a kaiki gidan mijin a haka.. inada yake shiga dai bata nan yake fita ba.”
       Wata shegiyar dariya na bushe da ita harda kwanciya ina hawaye. Yaya Musaddiq kuwa yay sagale yana kallona. Sai da yaga dariyar tawa ta tasamma ta hauka sannan ya ce, “Samraah kin samu motsuwar kai ne?”.
      “Babu wani motsuwar kai wlhy Yaya. Show ɗin ne yay matuƙar burgeni. Su Abba an lallaɓo aci banza. Banza bata samu ba, shine ya ƙare da borin kunya. To waye ya faɗa masa na damu a kaini da kayan ɗaki? Ko cokali ma kada su saya waye zaiji kunya”.
        “Shirme maganinka ALLAH kenan”. Yaya Musaddiq ya faɗa yana girgiza kansa. Da sauri na ce, “Yaya gaskiya fa na faɗa. Ni wlhy ban damu ba amin kayan ɗaki ko a kar ayin. Badai muna son junanmu ni da Mansoor ɗina ba”.
     “Baki da kunya, a gabana kike cewa kuna son juna”.
    Hannu nasa na rufe fuskata ina dariya. Shima sai ya shiga tayani...

        Washe gari koda na kammala aikina na shirya na fito na samu Abba a falo na gaishesa bai amsa min ba. Ko'a kwalar rigata nai ficewata. Yaya ga ɗaukan muka wuce ina bashi labari ina dariya. Shi kam murmushi kawai yayi yace “ALLAH ya ƙyauta”. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya gidan Abba babu daɗi sai haƙurin UBANGIJI kawai. Yayinda a waje aiki ke caja kai kuma. Kamar yanda mukai shiri ranar asabar muka tafi Katsina ganin Hafizzullah. Ƙiri-ƙiri Mom ta nuna baƙin cikinta akan hakan. Ta shiga zuga Abba wai ya hanamu zuwa. Sai dai Yaya ya nuna musu babu abinda zai sakamu fasawar. Haka dai muka tafi Mom na banbaminta na rashin gaskiya. Hafizzullah yayi matuƙar farin ciki da ganinmu. Dan harda kukansa na murna. Ya rame saboda karatu, naita tsokanarsa nikuwa muna faɗanmu da muka saba. Tare da shi muka yini. Da zamu wuce masauki kuma ya bimu akan shi tare damu zai kwana. Nan ma raba dare mukai muna hira kafin su koma ɗakin Yaya Musaddiq su kwanta ni kuma nai kwanciyata ni kaɗai muka sha waya da Mansoor dake bani labarin an shirya komai tsaf gobe in sha ALLAHU za'a tsaida date. Jinai duk wani iri, amma a ƙasan raina ina farin ciki da hakan. Koba komai ai zan samu ƴancin kaina. Na kuma samawa ƴan uwana. Dan insha ALLAHU Hafizzullah gidana zai koma, Yaya kuwa zan cigaba da dagewa akan yay aure..........✍️
         

_Kandala ta malam Mansoor 😘_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_


........Washe gari kamar yanda Mansoor ya faɗa muna a hanyar dawowa gida ya turamin saƙo na jerarrun kalaman godiya ga ALLAH. Tare da sanar min an tsaida wata ɗaya kacal, nanda kwana talatin in sha ALLAHU na zama mallakinsa. A gidansa zanyi azumin watan Ramadan. Duk da naji farin ciki ban maida masa reply ba, dan ina cikin mood mara daɗi na rabuwa da Hafizzullah. Shima mun barosa harda hawayensa. Munko samu gida cike da kayan sweet, biscuits da drinks a falo. Harda su goro sai akwatina guda biyu. Yanda babu wanda yay min magana akan kayan nima banma kowa ba. Sai auta ne ke faɗamin Uncle Mansoor ya gaya masa kayana ne. Sai kuma habaicin da Baby keta saki ranta a ɓace. A kallo ɗaya da nai mata kuma na fahimci tasha kuka. Ban kulata ba dan ba itace a gabana ba. Washe gari Monday na wuce aiki da wuri. Bayan mun dawo na tarar da Gwaggo Gudidi tazo daga Dawanau. Kakace a wajenmu, dan ƙanwar kakarmu ce, mahaifiyar su Abba da mamanmu kenan. Ba sosai take zuwa gidan ba saboda wulaƙancin da Mom ke musu. Mu kuma Abba baya barinmu zuwa wajenta, garama Yaya yanzu daya mallaki hankalin kansa yana zuwa abinsa. Yanzun ma shine ya kirata ya gaya mata komai ganin Abba baida niyyar saka danginsa ko ɗaya a batun auren nawa. Ƴan Gwarzo kuwa sun kwashi nasu kason kayan da za'a rabama mutane sun wuce dasu tun jiyan, dan bamu samesu ma a gidan ba. Nayi murna ƙwarai da ganin Gwaggo Gudidi. A take na shiga hidima da ita dan naga babu alamar ko abincin kirki ma an bata. Duk da hararar da Mom ke mun banbi takanta ba na shiga hidima da kakarmu. Bayan sallar isha'i kuma Yaya ya sayo mata kayan ƙwaɗayi yazo ga zauna muka sha hira. Dan dole Abba ma yazo ya zauna akayi da shi shima. Mom da ƴaƴanta kuwa kowa yay shigewarsa ɗaki sai Auta da uwar gulma Bibaa kawai a wajen. Bamu tashi a falon ba sai sha biyu. Abba ko tun sha ɗaya matarsa tazo ta tasashi suka shige ko kunyar Gwaggo Gudidi bata ji ba balle mu ƴaƴa. Shimfiɗata na barma Gwaggo, dan Yaya Musaddiq ya kawo mata babban bargonsa. Zan kwanta a ƙasa tace na hawo kan bargon. Badan naso hakan ba na hau dole. Sabuwar hira muka buɗe da ita har sai ɗaya sannan barci ya kwasheta. Niko alwala na tashi nayi nai nafilfilina kamar yanda na saba sannan na kwanta. Hakan kuma bai hanani tashi uku da rabi ba na shiga ayyukana. Kafin kace mi na kammala, dan har abinci naima Gwaggo na saka mata a kula nakai ɗaki dan nasan ba lallai da rana a bata na kirki ba. Gashi ban dawoba lokacin. Kalacin ma isashe na ɗiba mata. Itako tanata mitar yanda nake wannan uban aiki ga fitar safe kuma. Ni dai bance komai ba face murmushi kawai. Yau kam Yaya Musaddiq ya shigo gidan domin gaisheta. Ya ajiye mata kayan shayi da ƙaton bread ɗin ta harda soyayyan ƙwai. Albarka ta dinga saka mana sannan mukai mata sallama muka wuce dan kar mu makara.
Gwaggo Gudidi itace ta raba komai na kayan sa ranar nan. Har maƙwafta sai da tasa Auta ya kai ma kowa gida-gida. Sannan dangin su ta ƙulla na kowa daki-daki. Wanda ke anan cikin Kano ta saka Yaya Musaddiq ya kaita ta kai ma kowa. Na Gwarzo ma tare sukaje takai duk na ɓangaren danginsu dai. Yaya Musaddiq ma da Hafizzullah ta ɗiba musu. Nima komai sai da ta ɗiba min. Hakama jama'ar gidan kowa da nashi. Kuma kowa zai iya rabama abokan arziƙinsa idan yaso. Amma sai Mom tai biris da nata anan falo har Gwaggo ta wuce bata ɗauke ba daga ita har ƴaƴanta. Abba dai ganin Gwaggon yasa shi zama ya ƙuƙƙula ya fita dasu wai zai rabama abokansa da ƴan wajen aikinsu. Ya raba ko bai raba ba oho masa.
       A ranar da nakai ma ƴan office ɗinmu kowa ya sake sanin alaƙata da Mansoor, dan wasu basu ɗauka gaske soyayya muke ba saboda yanda muke komai cikin taku. MD kuwa ai kamar zai mutu. Dan masifa yayta zubama kowa a wannan yinin babu gaira babu sabar. Har dai ƴan uwana ma'aikata suka fahimci kishi yake yi. Ni dariyama ya bani wlhy. Mansoor kam yaji daɗin abinda nayi, dan bai ɓoye ba sai da ya sanar min. Murmushi kawai na masa nidai. Bayan an tashi aiki ya buƙaci kaini naga aikin gida da ake ƙarasawa. Amma sai nace masa ba yau ba ya bari weekend zai fi. Shima ya yarda da shawarar tawa. Dan haka ya maidani gida. A ranar ne kuma na fahimci wata farar mota na binmu a baya. Duk da naji tsoro sai banyi magana ba, nace bari dai na tabbatar. Ganin munzo titin shiga layinmu motar ta wuce yasa na sauke ajiyar zuciya har Mansoor na kallona.
     “Lafiya irin wannan ajiyar zuciya haka kamar wadda nai shirin sacewa. Ko tsoro kike kada na wuce dake ne?”.
        “Ai kaima bazaka fara hakan ba sai an baka”. Na faɗa cikin kauda kai ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yay da sake faɗin, “Hakane. Amma da zama a taimaka a banin yau zanfi kowa farin ciki. Maybe ma na ƙara samun ƙarfin aikin yanda ya kamata”.
      “Humm” kawai nace na buɗe motar na fice ina murmushi. Godiya na masa kamar kullum. Yanata son mu haɗa ido amma naƙi yarda da hakan. Sai ma na wuce da sauri na shige gida abina. Amma na maƙale jikin gate ina leƙansa. Yaja kusan minti ɗaya idonsa a gate ɗin fuskarsa da murmushi kafin ya tada motar ya wuce...

      ★★★

   Abubuwa kullum ƙara tsamari suke a gidanmu. Dan kullum al'amarin Mom da yaranta gaba yake yi. Ina sake samun tsangwama da hantara fiye da baya a yanzu sakamakon wannan batun auren. Yayinda Baby ta fito da maitarta akan Mansoor yanzu. Shi kansa ya fara nuna min tana matsa masa. Ashe tun da can ma da bata fiddo abubuwanta fili game da shi akwai abinda take shakka daga garesa, na kuma fahimci wani babban sirrinta ne ya sani duk da yaƙi fitowa fili ya faɗa min.
        Sam ba'a wani shiri irin na aurar da ƴa a gidan, musamman ma mace da bikinta ke da yawan hidima. Ko kaɗan hakan baya damuna. Dan nasan Yaya Musaddiq tsaye yake akan al'amurina ta bayan fage. Dan yanzu kusan duk sati zakiga Gwaggo Gudidi tazo mana. Da alama akwai abinda sukeyi ita da Yayan. Duk da madai ashe shi Mansoor ya samu Yaya akan shi baya buƙatar komai na gida duk zai zuba. Ni shaidace akan abinda ya faɗa ɗin domin ya kaini naga gida. A randa mukaje ɗin kuma na sake kama motar nan na binmu. Hankalina ya tashi fiye da ranar, amma nai jarumtar dannewa saboda kada na tada hankalin kowa. Nayi kuma alƙawarin saka ido sosai dan na tabbatar shin da gasken binmu ake kokuwa zargina ne kawai. Tun daga wannan lokacin na saka ido fiye da koda yaushe. Babbar magana kenan wai ɗan sanda yaga gawar soja, nako tabbatar bibiyata akeyi ɗin. Dan harna haddace Number motar duk da dai mai ita kan canja ne kusan da kala uku, sannan ita kanta motar wani lokacin bada ita ake bina ba da napep ne. Al'amarin ƙuruciya irin nawa da wauta, maimakon na sanarma ko Yaya ne sai nai tunanin kada na tada masa da hankali, gara na fara sanin wanda ke bibiyar tawa dai. Wannan ɗammara dana ɗauka tasa na fara ƙin daina bin yaya na koma shiga napep. Hakama Mansoor wataran sai na ƙi biyosa, ina amfani da yanayin da yake ciki na busy yanzu akan shirin biki. A ranar farko dana fara yin ƙundun balar tarar motar nan sai aka gudu. Karo na biyu ma haka. Ganin haka na sake himma dan a ganina tsorona ake ji. A karo na uku na haɗa kai da ƴan ƙato da goran anguwarmu a ɓoye akan idan ma fita su bini a baya. Na basu numbers na motar da ake amfani da su har kala uku. Abin zai baku mamaki, dan kamar mai motar nan ya fahimci abinda nake ƙullawa ranar sai bai bini ba. Tsahon kwana uku haka na ƙara yarda yaji tsorone na sallami ƴan ƙato da goran. Sai me a randa na sallamesu a ranar na cigaba da ganin motar kuma. Raina yakai ƙololuwar ɓaci. Na fara zargin MD ne kemin hakan ko kuma Abba ko Mom ko Baby. Kai har Mansoor sai da na zarga, to sai dai kuma shi danmi zai sa a bibiyan bayan kullum muna tare. (Bincike) zuciyata ta ayyana min. Ban gamsuba, dan in bincikene ai iyayensa ne zasusa ai musu. Sannan bata wannan hanyar ba, anguwarmu zasu je. Amma duk da haka sai nace bari na gwada kowannensu.
Da Baby da Mom na fara. Sai banga wata alamar hakan ba daga garesu. Shima Abba haka. Sai kawai na koma kan Mansoor. A randa na taresa da zancen ina magana cikin tsiwa kan basai fa yasa ana bibiyata ba zai san halina. Idan bincike yake son yi a kaina yazo ga ƴan anguwar dana tashi cikinsu tun ƙuruciya har girma mana. Amma sakawa ana bibiyata kamar son firgitar da ni ne. Tare da nuna rashin aminci a tsakanina da shi. Sagale yay yana kallona da mamaki, sai dai bai iya cewa komai ba harna fita a fusace. To ashe daga nan bai zame ko ina ba sai wajen Yaya Musaddiq suka tattauna akan hakan. Lokacin da Yaya Musaddiq ya dawo aiki yay kirana ɗakinsa.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_


.......Da faɗa ya faramin tare da turkeni kan saina faɗa masa dalilina na jifan Mansoor ɗin da waɗan nan kalaman. Da farko naso dojewa. Amma ganin yanda ya birkicemin a yanayin da bai taɓa ba bamma san na saki layi ba na zayyane masa komai. Tashin hankali na gani sosai a tattare da shi. Ya sake balbaleni da faɗa cikin ruɗani.
        “Amma Samraah baki da hankali. Yanzu wannan abin na faruwa da ke tsahon sati biyu amma kika ja bakinki kikai shiru sai yanzune kike faɗa. Shima badan kunyi haka da Mansoor ɗin ba da bamu kamo bakin zaren ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Samraah baki da wayo, wlhy sam baki da wayo. Dan tabbas bana raba ɗayan biyu mutumin nan ne yasa ake bibiyarki. Dolene ma ya gano kin ɗauki videon nan. Wannan abin shi nake gudu tun farko daman, shiyyasa kullum nake cikin tunanin mafita ashe nima nayi sakaci...”
        “Yaya ban gane ba. Wai kana nufin wancan mutumin mai ɗaure gashi Maashi yake komi ma oho masa”.
      “Idan bashi ba wanene Samraah. Tabbas dole shine zaisa a iya miki irin wannan bibiyar. Samraah kodai kinyi wani yunƙurine a kansa batare dana sani ba, dan na sanki da shegiyar wautar tsiya”.
     “Wlhy Yaya ni babu abinda nayi, kaima kasan kuma bazanyi komai ba sai da saninka. Ka tambayi Mansoor ALLAH ne shaidata shima shaidatane. Daga office bana zuwa ko'ina sai gidan nan. Weekend kuwa islamiyya ce kawai ko Malam Umaru zai tabbatar maka da hakan shima. Toni wanema yunƙuri zanyi tunda kunce nabar komai a hannunku. Wlhy ko video ɗin tunda na adanashi ban sake waiwayarsa ba balle ma na kalla har wani yaji ko ya gani. Hatta da Mansoor ranar yake cemin ALLAH ya kiyaye yana rage abubuwa ya goge video ɗin nan, da ace banda shi a wayata da an samu matsala. Amma dan ALLAH na sake adanashi kada nayi sakaci tunda na sanshi shi da goge-goge a waya na tsiya.”
           “Nasan baza'a samu matsala daga gareki ba Samraah. Amma dole mutumin nan yanada cctv camara ai, idan kuma mai yawan bibiyar abubuwane to tabbas anan ya gano shine yasa ake bibiyarki. Ko kuma wani ya ganki. Ina dai zuwa bari na kira Mansoor yazo ya same mu”.
    Ban iya cewa da shi komai ba. Sai faɗawa duniyar tunani kawai da nayi. Harya kammala wayar bamma sani ba. Cigaba yay da kai kawonsa alamar haɗa lissafin abubuwa. Cikin abinda baifi mintuna talatin ba sai ga Mansoor yazo. Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi suka tafi massalaci. Sai da aka idar suka dawo ina ɗakin Yaya ɗin dai har sannan. Mansoor na gaida daga haka suka shiga tattaunawa danni gaba ɗaya zuciyata bata tare da gangar jikina. Sai da Mansoor yaymin tambayar ni da waye muka je restroom ɗin a ranar? Dan tambayace da ya kamata ma ace sun min tun a waccan ranar amma basu yi ba. Saida na sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci sannan na sanar musu ɗaya daga cikin securitys ɗin da suka bada tsaro a ranar ce. Na sake maimaita musu yanda mukayi. Sun sake tambayata bayan ita ban haɗu da kowa ba? Sannan itama ɗin sanda ta tafi yin wayar bata dawo bane nemana?.
         “Eh gaskiya ni dai banga ta dawo ba, kasancewar ma hankalina ya tafi akan abinda ya faru ban sake bi takanta ba. Dan haka ban san miya hanata sake komawa ba. Kuma ni gaskiya bana jin nama sake ganinta har aka tashi”.
       Kallon juna Yaya da Mansoor sukai. Cikin ƙarfin hali da nuna tashin hankali Yaya Musaddiq ya ce, “Anya kuwa security ɗin nan bata koma ba a lokacin. Idan lissafina yayi dai-dai, ta koma domin

Please Login or Register in order to submit comment