Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dacewa "Da farko ina yiwa dukkan mahalarta wannan fada rawa mai albarka Barka da zuwa, Bayan haka a yau ne dukkan jama'ata ke zuba idanu domin suga yadda za'a zartar da hukuncin kisa ga manyan'yan leƙen asirinmu, kamar yadda labarin ya wakana.


Sai a wannan karon ba haka al'amarin yake ba, domin kuwa abinda zan sanar daku zai yi matukar girgiza ku, yaku jama'ata kuyi sani cewa a daren jiya ne wani muhimmin sirri da na daɗe ina ɓoye muku zai bayyana a gareku.


Fiye da shekaru uku ina tare da Amintattun 'yan leƙen asiri a dukkan wani rukuni na al'ummar wannan ƙasa tawa, tun daga gidan sarauta, Unguwanni da kasuwa da ma manyan ƙasashen maƙiyan Addinin musulunci, kuma a kowa ce rana dukkan aiyukan da na sanya su ya kammala, ta wannan hanya ne a samu nasarar tarwatsa dukkanin shirin maƙiya.


Hanya ta biyu dana kawar da hakan shine gabatar da addu'o'i dare da rana tare da keɓaɓɓun mutane, domin kuwa babu wani abu da yafi ƙarfin addu'a, Ubangiji na iya canza dukkan abinda ake ganin ya gagara ta kowace fuska, amma sinadarin wannan canjin shi ne bin dokokin ubangiji (SWT).


Sannan wani muhimmin abu da mutane basu sani ba shine a kowa ne dare bana iya rintsawa da idanu na har sai na shiga cikin gari cikin ɓadda-kama ina mai sanya idanu akan aiyukan da na sanya shuwagabanni akansu, kamar yadda na saba wannan al'ada ne ajiya ina yin rangadi a cikin gari na shiga wata unguwa da ake ɗaukar matasanmu mayaƙan Mujahidul-Haƙ, Sai da nayi shiga da siffa irin ta Mujahidul-Haƙ sannan na samu shiga gidan sirrin inda ananne na ganewa idanuna Gaskiyar rahoton da ake bani akan Yan tawayen ƙasarmu.


A bisa wannan dalilai na yasanya Ni da kaina na ɗebi dakaru na shiga har cikin Daji na ceto rayuwar Ɗana yarima Affan tare da sauran jama'ar da akayi garkuwa da su, A cikin wannan daji ne muka samu nasara gano wani Ɗakin sirri da dukkan maƙiyanmu wato sarakunan kafirai,bokaye haɗe da Musulmi maciya amana ke haɗuwa suna ƙulla makirci da sharri, mun sha gwagwarmaya dasu ta hanyar fafata arbu tsakaninmu bisa taimakon Ubangiji muka samu sanar hallaka su baki ɗaya.


Anan ma mun samu waɗansu bayanai muhimmai wacce da ita ne mu kayi amfani wajen kame dukkan maci amanar mu a cikin dare kafin wayewar gari.


Koda yazo nan a jawabinshi sai yayi shiru Kuma idanuwanshi suka ciko da kwalla.


Al'amarin da ya jefa ruɗani a cikin zukatan al'umma kenan suka ƙara tattare hankulansu akan mai martaɓa.


Sarki ya ci gaba da cewa "Sanin kanku ne cewa fiye da shekaru uku wannan ƙasa tamu na cikin halin matsalolin tsaro da taɓarɓarewar matasan mu, daga lokacin da abubuwan suka fara gudana ina saka idanu tare da tattara hujjoji domin tabbatar da zargin da nake yi domin ya zamo gaskiya ba son zuciyata ba.


Sai gashi abinda nake zargin ya tabbata gaskiya, Daga cikin jerin mutanen dake hannu wajen jefa kasar mu cikin tarin matsaloli sun haɗar da Sheikh Ɗayyib babban malamin dake amsa fatawa a wannan ƙasa tamu da sauran biranen musulmi, sai Waziri Utbah,Hakimi urwat, uwar gidana gimbiya Huwailah,sarkin dogarai, sarkin fada,tare da sauran jama'a da yawa waɗanda zaku cika da matuƙar mamaki a yayin da kuka yi arba dasu a lokacin da za'a gurfanar dasu.


Sheikh Ɗayyib an kama shi da laifin yin fatawa waɗanda suka saɓa da magabatanmu wanda ta wannan hanya ne yayi amfani wajen zartar da hukuncin kisa ga dukkan Musulmin da ya saɓa da aƙidarsu ta Mujahidul-Haƙ tare da dukkan wanda zai tsananta bincike akan abubuwan da suke gudanarwa.


Kusan dukkan Musibun dake wanzuwa a wannan lokaci an samu ne ta hanyar Littattafan addini daya wallafa kuma ya sanya su a cikin addini domin su kawo rabuwar kawunan musulmi, sanin kanku ne cewa Babu wani hukunci da yazo a cikin alƙur'ani da sunnah da ya tabbatar da cewa koda musulmi yayi kalmar shahada a hallakashi idan ya saɓa wa wata fahimta ta wata jama'a a addini, Domin ubangiji shine masanin abinda ke wakana a zukatan bayi kuma shine ke yi musu hukunci.


Bayan wannan ma fatawoyinshi sun yi tasiri akan matasan mu wajen samun damar saɓa wa Ubangiji ta hanyar fakewa da rashin aikin yi har su karbi aƙidar Mujahidul-Haƙ, dake Kaɗaita musu aljanna da kyakkywan ƙarshe,


Waziri kuwa an same shi da laifin taimakawa waɗanda ke Safar mutane daga wannan birni namu ayi Garkuwa dasu domin a ƙarɓi dukiya mai tarin yawa da za'a bawa matasan Mujahidul-Haƙ.


Sannan kuka kuma ya taimaka sosai wajen kawar da ainihin Littattafan magabatanmu da ke da tsaftacciyar aƙida ta addinin Islama.


Sarkin dogarai kuwa ya cutar da al'ummarshi ta hanyar ƙarbar cin hanci ga dukkan wani bafatake daya shigo wannan ƙasa tamu, ta hanyar ƙarɓar cin hancin ne masu safarar mutane da shigo da miyagun makamai, da kayan maye suka samu dama akan mu, da kyale dukkan wani nau'in kaya da suka shafi wani attajiri ko Basarake, batare da an binciki mene ne ake ɗauke dashi ba.


Hakimi urwat da uwar gida kuwa sun ci amanar Allah da Annabin sa ta hanyar tallata saɓon Allah da yaɗashi cikin al'ummar mu da sauran laifuka,


Lokacin da kuyanga ihsan ajiya tazo fada domin ta sanar dani irin nau'in sabon Allah da ake gudanar a gidan sarauta shine urwat ya kurumtar da ita ta daina magana domin kada ta bada hujja, sai gashi ta samu lafiya kuma ta tabbatar mini da hakan tare da waɗansu hujjojin daga wasunta.


Daɗin daɗawa kuma


Dukkanin dai laifukan suna da yawa bazai yiwu mu bayyana su hakanan ba, domin annabin rahama ya hore mu da ɓoye laifukan yan uwanmu musulmi, domin kuwa da yawan laifukan dake yaɗuwa a wannan zamani na mu Suna da alaƙa da yaɗa alfashar da wasu ke yaɗawa da 'yan uwansu ke aikatawa


Bayan wannan kuma ina so jama'a su lura cewa bawai don kana cikin wata jama'ar ba ne Abin da zai sa kaga cewa kai babu hannunka a cikin wannan Musibun dake damun duniyar Musulunci ba, kowanne mu ana akaran kanshi yasan nau'in laifin da yake yiwa Allah to shi ma na iya janyo dukkan wata musiba kamar yadda dai muka sani cewa saɓon Allah SWT shine ke kawo gushewar dukkan ni'ima.


Kuma ku lura cewa tabbas Matsalolinmu mu musulmi daga kaɗan suka fara har suka haifar da manya, saboda haka kada ku taɓa raina kuskure komai ƙanƙantarshi.


Yayin da bayi suka aikata zunubi sai Allah ya saukar musu da Musibun da zasu kankare wannan zunubinnasu domin su haɗu da Allah (SWT) lafiya.


Da wannan dama nake roƙon dukkan jama'ata daga Nan fada kafin su koma gida su yiwa Allah alkawarin zasu daina duk laifukan da suke yi wanda tsakanin su da Allah ne kawai, tabbas ina da tabbacin Ubangiji zai dube mu ya kawo mana gyara a cikin wannan Rayuwa tamu, kuma mu riƙa kallon dukkan Musulmi a matsayin ɗan uwanmu kuma abu ɗaya ne ya haɗamu ita ce kalmar shahada,


Ko da kaga ɗan uwanka yana aiwatar da wani abu da ya saɓa da fahimtar ka to kayi mashi kyakkywan zato, domin baka san a ina ya samo hujjar yin hakan ba, saɓanin fahimta ba sabon abu ne a cikin addini ba


Kada mu zama masu bincike abinda ke zukatan al'umma,domin Allah shine kaɗai yasan abinda ke zuciyar bayinshi, kuma shi ne zai yi hukunci a gobe ƙiyama.


Kuma dukkan abinda musulmi zai yi bazai taɓa kafurtaba face ya yarda da abin azuciyarshi, don haka ne idan mutum ya yi abin da ya saɓa da fahimtar mafi yawan al'umma ake neman shi da ya tabbatar da Mene ne hujjarshi na aiwatar da hakan.


Kada muyi watsi da abin da magabatan mu suka rayu akai, kuskuren da sukayi mu nema su gafara wajen Allah.


Sannan dukkan abinda kowannen ku zai aiwatar yaji tsoron Allah a ciki.


Tsira da aminci Allah su tabbata ga Annabin rahama Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama da jama'ar gidanshi.


Lokacin da sarki Shaibat yazo Nan a jawabinshi sai fadar jama'a suka ruɗe da kabbara masu salati nayi, kuma kowa na ƙara jinjina wa sarki, bisa jawabinshi, suna masu cewa munyi yarda mun amince zamu gyara halayenmu da tsakaninmu da ubangiji,


a dai-dai lokacin ne aka shigo da waɗanda ake tuhuma da cin amanar addini.


Nan fa jama'a suka cika da matukar mamaki a cikin waɗanda basu yi zato da hannunsu a cikin al'amarin ba.


Suka shiga yi musu Allah wadai har sai da sarki ya tsawatar sannan komai ya samu dai-dai ta.


Duk wanda ya kalli fuskokin su waziri a wannan lokaci zai ga alamun nadama da da nasani, Da yawan su Har zubar da hawayen baƙin ciki da takaici su ke yi, wasu daga cikinsu ma har faɗuwa ƙasa suke yi suna cewa "Haƙiƙa mun tuba munyi nadamar abin da mu ka aikata muna neman afuwa.






Sarki ya ɗora da jawabin shi da cewa yanzu dukkan su za'a tafi dasu izuwa kurkuku, waɗanda a cikinsu suka cancanta a yanke musu hukuncin kisa zamu zartar waɗanda kuma waɗanda za'a bukaci tuban su, da waɗanda za'ayi bulala duk zamu zartar a sirran ce, nasan yanzu da kanku kun ganewa idanuwanku waɗanda suka nuna Nadamarsu dama waɗanda basu da alamun hakan, dukkaninsu zamu yi musu adalci


Da wannan nake yiwa jama'a fatan alkairi kuma na sallami kowa daga fada.


Koda gama faɗin hakan sai sarki ya juya ya shige izuwa gidan sarauta dogarai na biye dashi a baya.


Nan take aka tusa ƙeyar maci amanar addini aka nufi hanyar kurkuku, fuskokinsu cike da ƙunci da da na sani, ƙarƙashin jagorancin yarima Affan.


Bayan mako ashirin da biyar lamura sun fara dai-dai ta acikin ƙasar madinatul-barnawiy, jama'a na ta ƙoƙarin ganin sun daina saɓa wa Ubangiji (s'w't).


Sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba, sai gashi dukkanin kawunan ƙungiyoyin musulmi sun haɗu, zaman lafiya da aminci ya wanzu a ko ina albarka gami da ni'imomi suka mamaye al'ummar musulmi.
www.littafanyaki.com.ng




Kuma sarki da kanshi ya dunga yin hawa izuwa ƙasashen sauran Musulmi yana sai-sai ta musu matsalolin su, tare ƙone dukkanin Littafin addinin dake ɗauke da gurɓatattun aƙidoji, gami da ɗorasu bisa turbar gaskiya.


Karshe


Alhamdulillah




Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe


MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp number
08137237071
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment