Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

best wajen saida laces takalma and bags, wayanda suka saya kaya daga wajenta can testify now rush and join WhatsApp group nata kuma kusayi kaya💃
https://chat.whatsapp.com/Fvbu8FNZxXTIA5oHt26Daj





Hana kowa yamata magana Ya Raheena tayi hakan yasa duk suka tafi da kanta ta kula da Alawiyyan ta shafa mata hot balm a waist nata da Ammi tabuga a table ta share mata baki tabata pain killers sannan ta kwantar da ita akan gado tana shafa kanta kawai tana kallonta, mugun tausayi Alawiyyan ke bata bini bini yarinyar tai kuka, ta juya tai chan, tai nan ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Wajajen 4 ta tashi da kyar ta mike bayi taje da zumin yin fitsari da alwala kawai saitaga blood, ajiyan zuciya ta sauke, tayi deep down kuma feeling relief batason tayi cikin AJ batare da sunyi aure ba, fitowa tayi jin hayanyiyan yaran Ya Raheena hakan yasa tafito suna chan falon kasa, hango wayan Bobo akan gadon dakinsu dayake a bude tayi hakan yasa taje dakin dasauri ta dauko wayan kawai saita kashe ta tura karkashin gado, yaran banda wayoyi sunada İPad sunmafi damuwa da iPad dinsu sabida game, Teddy gadon tadauka ta rungume she misses AJ so much, she miss kamshin turaren shi, she miss his touch, his smile, his hands a jikinta, she misses yanda yake magana da ita, yanda yake lallashinta, he is the only person aduniya daya damu da farin cikinta da bakin cikinta duka, idan har Allah yabata AJ batajin akwai wani abu dazata kara damun Allah akai yabata ba, tanason AJ sama da rayuwanta, tun ranan haryau basuyi waya ba kawai saita hau kuka ahaka Ya Raheena tashigo dauke da tray na abinci taganta ijiye mata abincin tayi tace “eat Cookie” batare data kalli Yayan nata ba tace “I want pad” juyawa kawai tayi yafice takawo mata pads da disposable pants a kwali karba tayi tawuce bathroom itama Ya Raheena tafice she don’t wanna talk to her yanzu harsai yadawo daidai.
**

Waiwaye Baya Kadan!
Wuraren 10 nadare AJ yakai gidanshi, sauka yayi yabude gate yashigo da motan yakoma yarufe yajuyo tun kafin yakai kofa yaga Khairat tafito da gudunta da bala’in farin ciki tayo wajenshi, chak ya tsaya dan baiso tai hugging nashi hakan yasa itama ta dakatar da kanta ta tsaya dab da shi jiki asanyaye ganin ko bude mata hannu baiyiba alamun she can hug him, ahankali tace “sannu da zuwa, ya aiki? Kadawo lpy”? Kai ya gyadamata yace “fine ya kuke Ya princess”? Yayi maganan yayi gaba tabiyoshi abaya feeling so happy ganinshi direct dakinta yashiga dudda Alawiyya na bacci saida ya dauketa ya rungumeta tsamtsam ajikinshi yana motsi, tsayawa Khairat tayi jikin kofa tana kallonsu bata taba sanin is
possible kaso yaro kaki uwarsa ba sai akan AJ, son Alawiyya yake kaman ranshi, wani awaje zai dauka soyayyan Maman ne ya shafi diyar amman gabaki daya ba haka bane, yanason yarda tahaifamai but ita Uwar bayasonta ko kadan, kusan 5min yayi ahaka da yarinyar sannan ya kwantar da ita yana patting back nata sannan yashafa kumatunta yajuyo dan ya fita, matsamai tayi yawuce yayi hanyar dakinshi tabiyoshi tace “nakawo abinci”? Girgiza mata kai yayi yace “a’a thank you” yana shiga dakinshi bayi yafada yayi wanka yafito yasa PJ kawai yafada gado, koda Khairat tazo ayanda ya kwanta ya baje yana baccin gajiya babu space dazata kwanta ma agadon, jiki asanyaye tajuya taso ta kwana awajen shi, she missed him alot wani zubin kwanciya kusa dashi tanajin duminshi is the only thing dakesa taji dadi azuciyanta dan tasan ba sonta yakeba.
Idan kika karanta this littafi baki biyaba ban yafeba! Wallahi ban yafemiki ba eh ke! Ban yafe makaba kaiba! This book subscription is 1k pay idan bazaki iyaba don’t read. Chat me up don saya by clicking on this link wa.me/+2347032934950
Wuraren 8 yadawo gidan daga sallan asubahi, Alawiyya yagani afalo tana wasa tana ganinshi tawani zabura dasauri yayi wajenta wani kalan daukanta yayi yace “oyoyooo my baby, Alawiyya na, Dady’s princess, My Queen” wasa yahau yima yarinyar ahaka Khairat tafito da cerelac dinta data mata karba yayi yabama yarinyar ta tsaya tana kallonsu kaman ta cinye AJ yakara kyau this 7days tafiyan dayayi, ya chanza yayi fresh a idanunta kodan bata ganshi bane oho, but he’s looking really good and awesome.
Daukanta yayi yatafi da ita dakinshi ya kwantar da ita akan gado ya shiga wanka kafin yafito harta kara bacci dan ta koshi, shiryawa yayi tsaf sannan yazauna gaban drawer nashi yadauki pen da paper dan shiru yayi saikuma ya juyo yakalli Alawiyya dake bacci ahankali yace “banson na cutar da Momy ki i know you will not like it” saikuma ya juyo yayi rubutu a paper ya linke yasa a envelop kafin yatashi yafito falo zama yayi kan kujera ya ijiye envelop din kan table, daidai nan Khairat tafito daga daki tayi wanka taci gayu dawata gown na atampa tace “akawo breakfast Baban Alawiyya”? Girgiza mata kai yayi anatse yace “come and sit” kallonshi tayi kafin tawuce kujeran daya nuna mata ta zauna tana kallon envelop din dayake kan table hakanan kawai taji gabanta yafadi, ijiyan zuciya AJ yasauke kafin yadago idanunshi yakalleta anatse yace “Khairat” ahankali tace “na’am” Ijiyan zuciya yasake saukewa yace “first of all I want to start by telling you sorry kiyakuri Khairat” hakanan kawai taji takasa magana abu yazo mata wuya kaman maruru ya tsaya chak, ahankali yace “Khairat you are a good woman and I respect you sosai, I will forever respect you and I am so glad Alawiyya has an awesome Mom irinki” yafadi anatse yace “My daughter is lucky to have a mother like you” yayi dan murmushi kadan sannan yace “that envelop bana baki shi sabida raini bane ko matsayin ki baikai bane no! Infact nabaki shi ne sabida ke mai daraja ce da kuma kima a idona and you don’t deserve ki zauna karkashin wanda baida feelings for you ba irina” yadanyi shiru kafin ya shafa fuskanshi yace “Khairat you don’t deserve a man like me you are too good, too gooood Khairat, I don’t wanna be selfish and just keep you a karkashina bayan nasan akwai lot of men out there da suna ganin this precious gem zasu dauka dagudu dan u are one in a billion, I am sorry Khairat but banson hakkin ki yamin yawa aka, I don’t love you one bit Khairat” daidai nan Khairat ta runtse idanunta hawaye na gangarowa ahankali tana nishi mai tiriri, saukar da kanshi kasa AJ yayi ahankali yace “for a whole shekara daya da rabi I’ve tried hard to teach my heart to love you but nakasa I don’t have feelings for you! I tried to see you for you but nakasa, anytime kika min wani abu i feel guilty, most of the time I feel guilty nama zauna naci lafiyayyen abincin dakika dafamin cus akanme zan wahalar dake nazauna naci abincin ki bayan bana sonki? For a year da kusan rabi bantaba zama nayi wani dogon magana dake ba, today is the first time nake having long magana dake haka, most of the time bana iya kallon cikin idanunki is either namiki magana ina kallon gefe ko ina kallon wani waje cus i feel guilty to look into a good woman eyes like you alhalin bana sonta, kar hakkinki yamin yawa Mom Alawiyya, ki yakuri Khairat ki gafarceni ki yafemin idan nataba miki wani kuskure but I want you to go out there and marry wanda ke sonki kike sonshi, our daughter kuma I want us to coparent her in peace and harmony, idan kinason ki riketa is fine I trust you zan barmiki ita ta girma a hannunki, idan kinason ni nariketa is all fine with me, you are just like my sister and forever nadaukeki a matsayin kanwata you can come to me regarding anything, I am sorry Khairat, kiyakuri kiyakuri but na sakeki saki biyu, inaso ki zauna kiyi iddan ki cikin gidan nan and you don’t have to worry about telling iyayenki zanje gidan Mama I will tell her daganan zan tafi gidanku nafada dakaina, kiyakuri Khairat and thank you for everything dakikamin including giving me Alawiyya the most amazing gift ever in my life, nayi freeing dinki yau” yayi maganan ahankali yana sauke kanshi kasa dan kukanta is breaking his heart sosai, ahankali Khairat tazubo daga kan kujera zuwa kasa takifa kanta akan table din takasa rike kukanta, tanason AJ, Allah ne yadaura mata sonshi dudda da aka musu süren bata sonshi but zama dashi yasa tagane he’s such a gentleman, he’s sweet, baya sonta amman baitaba mata wulakanci ko mugun kallo koya kyareta ba, wlh baitaba fada da ita daidai da sau daya ba yau shekara daya da rabi da auren su, baitaba mata ihu ko tsawa ba, ko baida kudi tace tanason abu baisamu ba dazaran yasamu zai sayo mata, baya sonta baya hira da ita babu wannan abotan tsakaninsu bayan wannan abu guda tal AJ baitaba mata na cutarwa ba she really really loves him, sakin yataba mata zuciya sosai.

Kasa jure yanda take kuka AJ yayi asanyaye yace “kiyakuri Khairat”kafin ahankali yatashi kawai yafice yashiga motanshi yabar gidan.


Naso nacigaba but let’s us take a moment of silence for our Dearest Khairat😭.

But kuna ganin hukuncin da AJ ya dauka ya kyauta??


Yakamata ya saki Khairat ko bai kamata ba??

Yacigaba da zama da ita dudda baya sonta??


Kuna ganin soyayyan Alawiyya yayi influencing sakin??

Kuna ganin in marriage soyayya should be both miji da mata na son juna otherwise arabu idan daya bayason daya??

Now my question to those dake cewa AJ bai kyautaba daya saki Khairat, why is it Okay Alawiyya tarabu da auren Alhaji sabida bata sonshi and is not Okay for AJ yasaki Khairat tunda baya sonta??? Oya kubani amsa.

See you next week Thursday cus drama is about to happen💃💃💃

EPISODE 1️⃣7️⃣



SUPRISE💃🔥

Kindly save my new WhatsApp number wa.me/+2347032934950
Dayan whatsapp number na ya sami matsala.
M Shakur😎


Gidansu AJ yafara zuwa, madaidaicin gidane mai kyau kal kal dashi yafadama Mamanshi komi dake wakana yadauka ma Mama zatamai fada duba da zai bata friendship nata da kawarta but to his biggest suprise batamai ba sai kawai tace “Allah sa hakane mafi Alkhairi katashi kaje gidansu Khairat” tashi yayi yawuce tabishi da kallo, bala’in tausayi yaron kebata sabida tasan yanda yaso Alawiyya yar makarantan su kuma har yau har gobe soyayyan ke dawainiya dashi gwanin ban tausayi, AJ kaman mahaifinshi yake mutane ne wanda idan sunso sunso kenan, har Babanshi ya mutu ita kadaice matarsa ko wata budurwa be karayi ba bayan ita, gashi AJ yagadoshi yakasa son wata aduniya, yakasa, wannan wani kalan jarababben soyayya ne haka, Allah kyauta, Allah yasani tanason Khairat sabida itama aurenta bai yu da wanda taso da bane, saisa sukai shawara su hada yaran, daya cutar da diyar aminiyan ta gwara rabuwan Allah ya zabama dukansu biyun abu mafi allhairi.


Yana gym dinshi misalin 9 nadare wayanshi ya shiga ringing ganin new number kawai jikinshi yabashi Alawiyya ne office nashi ya wuce daidai wayan ya katse yasake kiran wayan kafinma yayi ringing Alawiyya tadaga wayan asanyaye in that baby way tace “Hello” wani irin sanyi AJ yaji ajikinshi ahankali yace “at long last, I’ve been waiting for your call, wayan waye wannan”? Murya Chan kasa tace “na Bobo” kobata fadiba yasan yaron sister ta take nufi ahankali tace “ina yini” murmushi yamata yace “wannan muryan fa is somebody missing me”? Dan murmushi tayi for the first time tunda ta shigo gidan nan tace “alot” ijiyan zuciya yasauke yace “i miss you too Ajay, sosai! What happened bayan kin koma tell me everything?” Bata boyemai komiba tafadamai komi sosai ranshi yabaci yace “are you still having pains?” Ahankali tace “Ya Raheena tabani pain killers, ka nemomin Babana?” Tafada ahankali cus shine kawai abinda takeso yanzu, cikeda so AJ yace “am on it don’t worry zan nemo miki Baban ki indai yana raye okay” gyadamai kai tayi, ahankali yace “karki bari wani yasake dukanki run and hide inside okay idan wani na attempting tabaki, always call me idan kin sami chance, and eat, don’t play da abinci, you need strength” gyadamai kai tayi yace “kinci abinci yanzu”? Girgizamai kai tayi batare datai magana ba kaman yagani yace “mesa?” Shiru tayi ahankali yace “you miss the way I feed you?” Gyadamai kai tayi tace “uhnn, AJ I love everything dakakemin and I’ve missed all” murmushi yayi yay shiru yanason how Alawiyya talks like wata shagwababbiya and muryanta so calm, dan ijiyan zuciya yasauke yace “jawo abincin kinaci ina baki labari” daukan plate na abincin tayi yafara bata labari tanaci, bata taba cinye abinci datana gidan ba yau tass ta cinye bama tasani ba saida taji takai empty spoon baki tace “laaa” AJ yace “kin cinye ko” jin tafiyan Ya Raheena ta kashe wayan da gudu ta tura kasan gado shigowa tayi ta kalli tray tana mamakin yanda ta cinye abinci bata cemata komiba dai tace “good night” tawuce tafita daga dakin, tashi tayi ta kulle kofan tazo ta kwanta ta kirashi suka cigaba da waya dama a gym zai kwana kusan saida tai bacci ya katse wayan.

***

Yau Kwanan Alawiyya 6 agidan Ya Raheena, tun bayan day3 tagama MP dan dama ita 3days takeyi, Ya Raheena ta kira mai gyaran jikinta tana mata gyaran jiki wanda abin yadawo al’adan familyan su duk bayan MP sai an miki gyaran jiki kinsha magunguna an miki full body waxing, kinci kaza an miki wankan turaren jiki dana gashi nan da nan tafara sheki duk dare saisunyi waya da AJ yanzu ma cikin dare suke waya lokacin tasan Ya Raheena tai bacci babu wanda yace mata kala cikin yayyinta Ammi kuma bata kara zuwa gidan ba, hankalinta ya kwanta sosai abu biyu kawai ke damunta tana kewan yaranta sosai barinma taga yaran Ya Raheena na wasa sai kuma kewan AJ da bala’in sha’awanshi duk idan taji sha’awan tana kokarin kauda tunanin tai istigifari dan tayi alkawari bazasu karayiba sai sunyi aure amman abun sai gaba yake har saida jiya AJ ya lura from yanda take magana chan kasa tana sauke numfarfashi awaya, da kyar ya lallabata tai bacci.

Yau around 5 na yamma Ya Hamida tazo gidan tana sanye da suit dan daga office take hannunta rikeda wani babban bag tayoma Alawiyya shoping, Alawiyya na kwance akan gado aka turo kofan da sallama kasa kasa aka shigo hakan yasa ta dago kanta ganin Ya Hameedah ne dan turo baki tayi kadan tareda dauke kanta kawai tai kwanciyanta tareda juyamata baya itafa yanzu babu wanda takeso banda AJ arayuwanta haushin yan uwanta takeji sabida dukansu are selfish babu wanda yadamu da ita har yanzu sunki ma Ammi magana araba auren, maida kofan Ya Hameeda tayi tazo zata zauna daidai Ya Raheena na shigowa atare suka kalli Alawiyyan data juyamusu baya Ya Hameeda tace “ko gaisuwan ma bansamu ba Ya Raheena” murmushi kadan Ya Raheena tayi takarasa gaban gadon ta zauna tareda shafa bayan Alawiyya tace “stand up and greet Hameeda” ahankali Alawiyya tace “why will I greet her bayan tagama dukana, I want to be alone ku kyaleni” zuwa Ya Hameeda tayi dasauri ta zauna kusada Ya Raheena akan gadon tace “Talakawa ke irin attitude din nan kiga basuson kanninsu basa kula da su” dasauri Alawiyya ta taso takalleta tace “wallahi talakawa sunfi mu masu kudi komi, they have a rich heart, har yaran daba nasu ba suke sonsu, and they support each other, they support siblings nasu, masu kudi kanmu kawai muka sani, look at me today I have dukanku ku biyar but non of you could protect me, what is wrong about not loving Makamashi eh tell me? Ya Hameeda Ya Raheena tell me? Kufadamin can I force myself na soshi ne? Kun zaci inda inada ikon sama kaina sonshi da tuni bansamai ba kodan nacigaba da ganin murmushi akan fuskanku da tuni nasa muku, how can I love wanda I don’t love ku gayamin?” Tai maganan idanunta na kawo hawaye sabida abin namata ciwo tadan fuzar da iska daga bakinta trying to stop herself from yin kuka tace “da ace yau kune kannaina not just that ko ayanzu danake kanwarku i will do anything for dukanku wlh kuwa, but I am your kid sis baku sona you all doesn’t care about happiness dina, you all don’t care about rayuwata, inada ku alive healthy but duk kuna tsaye kuna kallon rayuwana getting ruined kunki daukan mataki akai duk randa na mutu zakuyi nadaman abubuwan dakuka mi……” Dasauri Hameeda tadaura hannunta kan bakin Alawiyya tana girgizamata kai tace “don’t say such words Cookie” ture hannunta tayi daga bakinta takai hannunta tadaura kan kirjinta tace “do the two of you have any idea menene zuciyanka yamaka nauyi? Ya Hamida my heart is sooo heavy, banajin farin ciki ko guda daya acikin zuciyana, da ina gidan mutumin nan har banso yadawo I hates him, I hate yana tabani, the sight of him is the worst site ever, bana iya kallonshi ba kaya ajikinshi, I can’t stand bakinshi close to mine yana sani amai, at a point I became suicidal Wallahi I wanted to kill myself…..” ta tsaya anan sai kawai tafashe da kuka sosai dake tsuma zuciya tace “I wanted to end it cus banso Ammi ta shiga matsala sabida ni relationship nata da Alhaji ya lalace, keken dana shiga was holding myhand ihu kawai nake cus fuskan Makamashi kawai nake gani a nashi da duka mutanen wajen ma I was able to recognize only one voice, the voice of the angel that save me” ahankali Ya Raheena tace “who saved you?” Ahankali Alawiyya tace “does that matter? For days bansan menakeyi ba I swear by Allah I had to see a psychiatrist yasani on 7 good days medication, Ya Raheena and Ya Hameeda I am telling you this ne sabida if anything should happen nan gaba kusan nasanar daku, ni kanwarku ce and hakki ne akanku to protect me, and guide me, banason Alhaji Makamashi, kada ku bari Ammi ta maidani wajenshi kar wani abu yasameni you guys should save me” yanda take kuka saiga hawaye akan fuskan Hameeda dasauri ta share itama Ya Raheena share fuskanta tayi da sauri sai kawai takai hannunta kan idanun Alawiyya ta goge tass cikeda so tace “kiyi shiru”Ahankali Alawiyya ta tsagaita kukan Ya Raheena ta nuna kanta tace “Alawiyya ina sonki sama da yanda kike tunani, Hameeda loves you as well, haka sauran yan uwanki, dukanmu muna sonki and we all care about you and about your well being, I know you Alawiyya, I see you and I see through you har hanjin cikinki ina gani, I don’t care about whatever kikayi da AJ dan ko zakiyi gardama zuwa nan da 2yrs I know kina wajen AJ for those 7days amsanki ranan da yanda kika kalli Ammi ya tabbatar min da hakan and I have something to ask you? Both ni da Hameeda are not here to tell you wat to do but muna nan ne to help you and to make you see things like an adult dakiketa claiming you are cus all I see a abubuwan da kikeyi is childishness” Ya Raheena tai shiru kafin ahankali tace “yau bari nabude miki ido and nabaki critical illustration of duniya and waye maza” tayi dan shiru tace “kinga Ammi ta hadu da Alhaji wato mijinki lokacin tana battling da divorce da issues nata da Baban mu dan yace zai karbe mu taki, ga financial crisis kuma, Alhaji was the first person daya bama Ammi aiki da wani gidanshi taboyemu sabida karya kwacemu hardai ta natsu tasa case din a court for custody, he helped Ammi da lawyers ahaka Ammi taci nasara a kotu tafara aiki, tazo ta haifi Layla, Zaifa and Habeeba” dasauri Alawiyya tace “waye Baban su”? Kafin Ya Raheena tai magana Ya Hamidata ce tace “bamu san….” Dasauri Ya Raheena tai blocking nata ta hanyar cewa “that is not wat we are talking about yanzu, Alhaji sent Ammi for wani 2yrs course a Qatar all that time datake Qatar muna gidanshi tareda Nani daya bamu masu kula damu, sannan akai akai shi da kanshi yana zuwa yana dubamu yayo mana shopping kaman babanmu all of us grew fond of him” Ya Raheena tadanyi shiru tace “Ammi couldn’t come back bayan 2yrs, she end of spending 5 good yrs though muna video call da ita bamu wani damuba muna cikin dadi wadata da komi babu me dukanmu Ammi tadawo mana dake lokacin kina 2-3yrs my God Alawiyya you are so beautiful” Ya Raheena tai murmushi, Ya Hameeda tace “bamu taba ganin cute baby like you ba in our whole life ke kin ganki gaki da kiba we were so happy to have a little sister, kinada farin jini sosai ke kinga farin jininki kuwa, Alhaji kullum idan yazo wasa yake dake kaman ya hadiye ki, akwai ranan birthday naki lokacin kina 11yrs Ammi taje dake office ki gaida Alhaji har aka baki kudi da sauransu daga ranan dai ni bansan ko shine ba but dai yace ke da Ammi ku koma Dubai ki secondary school naki daganan baki kara dawowa ba sai bayan kin gama, Alhaji shine gatan rayuwan Ammi, he’s her best friend, Alawiyya listen to me very well duk duniyan nan bazaki taba samun wanda zai soki tun kina small baby da akema komi kawowa this age ba irin Alhaji” baki Alawiyya tabude dasauri zatai magana Ya Raheena tadaga mata hannu tace “wait lemme finish bawai cewa nake kisoshi ba and ba gardama nace kimin ba” anatse Ya Raheena tace “as mace you have to be a critical and logical thinker, karki kalli abubuwa from just love angle Cookie look at things from other parts, now bawai ina cewa kibani amsan tambayiyin nan dazan miki yanzu bane but I want you to analyze it azuciyanki, first question kina ganin Ammi zata taba yarda duk runtsi ki rabu da Alhaji wanda yamata komi all labarin nan dana baki ki auri wani??” Tai maganan tana kallon Alawiyya dake kallonta tace “kinsan everything da Ammi ta mallaka ta sanadin aurenki ne? Takuma sanadin Alhaji ne, Ammi had a dream of becoming politician but bata da means din Alhaji made that possible, Kinsan kashe auren nan zaisa Ammi tarasa duk wani mukaminta aduniya? Muma yaranta mu rasa namu cus duk Alhaji ya sama mana this work, sannan ayi publishing family news namu a news channel, jaridu, social media ke ko’ina ma, do you want family ki and your mother to go through this mess sabida nonsense feelings din da you called love???” Ya Raheena tai shiru tace “now mu dauka kin bata relationship din tsakanin Ammi da Alhaji an raba auren, what if Ammi tace bazata taba yafemiki ba sannan ita ba mahaifiyar ki bace sannan mu sauran yaranta tarabamu dake ta hanyar yimana Allah ya isa duk wanda ya kara kulaki a rayuwarsa??” Ya Raheena tadanyi shiru tace “that’s my second question and again, kina ganin abangaren Alhaji zai barki? Sannan zai bar duk koma wani yaro ne daya shigo rayuwanki yasa kika rabu dashi? Alawiyya did you even know who you are married too? Kintabajin wayanda ake cewa su they’re above law??” Ya Raheena tadanyi murmushi tace “irinsu Alhaji ne ake cema they’re above law cus gwamnatin dake ruling yanzu a Nigeria tasa ce, dan gidanshi ne shine ubangidan shugaban kasan mu, ke bari kiji Alawiyya Alhaji zai iya hadama koma waye saurayin naki tarkon dahar yamutu yana gidan yari bazai fito ba ko anan kadai bakiyi 2 zero ba? Kega Mamanki ta yafeki sanma tarabaki da yan uwanki, saurayin da sabidashi kike haukan nan kuma yatafi gidan yari da bama’a barinki kiganshi tell me Alawiyya bakiyi asara ba? Baki zama stupid and gullible foolish girl ba?” Ya Raheena ta sauke ijiyan zuciya tace “well that’s my third question now bari muje kan Oga kwata kwata shi yaron ko saurayin ko who ever he is dayasa kike mana iskanci da hauka da hayagaga, first abu dazan tambayeki akanshi is how sure are you yana sonki 100 over 100 Cookie?? Cookie kinsan maza kuwa?” Ya Raheena tace “is he worth risking everything and everyone dakike dashi aduniya for him Alawiyya!”? Tai maganan

Please Login or Register in order to submit comment