Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayakuri kayakuri shikenan abinda zan iya fadi kaga wannan halin shine dalilin dayasa maza da yawa basason bama matayensu freedom har subarsu suyi sana’a dan wasu matan dazaran sun soma taba kudi shikenan sai sudinga jin kansu kaman giwaye suma yanzu sun faso, amman kabarni da ita zan kirata zan kira Mama kuma” ahankali yace “please kada ki sanarda Mama tana fama da hawan jini saisa nakiraki ban kirata ba” murmushi tayi tace “to shikenan amman dan Allah kayakuri” ahankali yace “to saida safe agaida yara” yakatse wayan yadade ahaka yau bacin ran yasa he wanna be alone ma inda bahaka ba zai iya kiran abokan shi yaji inda suke yaje yasamesu, yayi kusan 3hrs awajen sannan yatada mota yabar wajen.
Domin magana dani M shakur koso nasaki a group dina chat me up tanan wa.me/+2347012181461

Yana katse wayan Jamila ta danna mata kira wayan harya katse bata dauka ba akaro nabiyu ne tadauka tace “Hellooo Anty Jamila” cikin fushi Jamila tace “ke wace irin mahaukaciya ce Hadiza? Ni wlh I don’t even need to ask you nasan kene da laifi dan nasan kalan hakurin Nura tunda yau dakanshi yadaga waya yakirani nasan kin mai babban laifi” tsaki Hadiza taja dayasa Anty Jamila tasake baki, cikin fushi Hadiza tace “ohhh kiranki yayi yahada mini munafinci? To wlh zaizo gidan nan yasameni ina jiranshi” jin yanda yake magana kaman tana jiran wani saran wasanta yasa Anty Jamila tace “Hadiza are you okay kuwa? What has gotten into your head? Nuran kike magana haka akanshi?” Cikin fushi sosai Hadiza tace “Anty Jams bazaki gane bane, Nuri finds every little way to belittle me, nan Abuja ne fa ba kano ba but kullum so yake ina shiga kitchen namai abinci, a Abuja yan aiki ke girki matan gida relaxing take bayinta namata aiki, inada yar aiki ai nama baki labari wacce nace miki su Aman na sonta, ita ke kula dasu I am busy da shigo gida nawa yake so naraba kaina? Sai nasa yar aiki tamin wani abu yahanata yimin sabida shike biyan kudin shine nacemai yadena daga this month nizan cigaba dabiyanta sabida I should be the one in control of her, ina shago dazu yakirani wai Mamanshi zatazo gobe taga Dr kinji fa Anty Jamila sabida ya rainama kanshi wayau danni bai isa ya rainamin wayau ba, gidan nan belongs to two of us baida right dazai kawo koma uban waye into this house without asking permission dina, what did he take me for eh? Wlh wlh jiransu nake suzo goben dagashi harsu saina kuntata musu bakin cikin da bazasu kara marmarin zuwa gidana ba me akeyi da yan uwan miji banda hauka mtswwww” “Innalillahi wa innailaihi raji’un” Anty Jamila tafadi tana tafi da hannunta cike da mamaki tace “Hadiza giyar kudi ko giyar karatun wannan femi ah’ahhh Feminism ko oho dai ke damunki” Hadiza tace “feminism wai? I know my right I can fight for my right duk inda nake aduniya tunda mata suka gano this feminism sun samu yanci sun samu cigaba, a woman can stand aduk inda namiji ya tsaya aduniyan nan” “dalla rufemin baki sai idea bature yasa kin rasa mijinki tukunna zaki dawo hankalin ki” Anty Jamila tamata ihu tace “wannan ba shine tarbiyan da aka baki agida ba, keda mijinki can never be equal ko awajen Allah domin ko aljannanki na karkashin tafin kafanshi, mata dakika ganmu daga rib guda daya na maza aka hallito mu, kada ki mata, Allah yafadi acikin suratul Nisa’i aya na 34, Arrijalu qawwamuna Alan nisa, bari madai naja miki ayan gabaki daya
ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍۢ وَبِمَآ أَنفَقُوا۟ مِنْ أَمْوَٰلِهِمْ ۚ فَٱلصَّـٰلِحَـٰتُ قَـٰنِتَـٰتٌ حَـٰفِظَـٰتٌۭ لِّلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُ ۚ وَٱلَّـٰتِى تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهْجُرُوهُنَّ فِى ٱلْمَضَاجِعِ وَٱضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا۟ عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيًّۭا كَبِيرًۭا ٣٤

Men are the caretakers of women, as men have been provisioned by Allah over women and tasked with supporting them financially. And righteous women are devoutly obedient and, when alone, protective of what Allah has entrusted them with. And if you sense ill-conduct from your women, advise them ˹first˺, ˹if they persist,˺ do not share their beds, ˹but if they still persist,˺ then discipline them ˹gently˺. But if they change their ways, do not be unjust to them. Surely Allah is Most High, All-Great.

Allah ne yafadi da kanshi, idan kuma u are talking about rights da yanci ne tun zamanin Annabinmu ya kwatoma mata yancinsu idan wani yaji kina magana haka idan ba’asan Nura ba zaa dauka wani abu bawan Allahn nan yake miki, kin sami miji nagari bawan Allah shiru shiru mara magana kinamai irin abubuwan nan ke kinada baki kice sai da izinin ki mahaifiyarshi zatazo gidan danda tahaifa, matan da komu nan last week saida muka kirata muka mata yajiki wlh maganan ki yasama ina jin kunyan Nura, Hadiza sau nawa da ni da yarana harda Mama muke zuwa gidan ki every now and then duk wani abu dazai shigo damu Abuja gidanki ne masaukinmu we don’t even ask for permission sabida anzama daya, ace yau mahaifiyarshi zatazo for treatment na rashin lafiyanta kina maganganu haka ina imanin ki? Wani kalan tsantsan son kai ne wannan”? Cikin kunkuni Hadiza tace “ai dama side dinshi zaki dauka nasani mutum yana nema ya maidani yar aiki bazakice komiba ace nine zan shiga dakinshi na gyara namai girki bayan inada yar aiki mai yi” Anty Jamila tayi shiru na kusan 5min sannan tace “danace basai na sanar da Mama ba but Hadiza kinyi nisa Mama dole ta shigo zancen nan, yar aiki itane ke gyara dakin mijinki tamai girki? How many minute zai daukeki kima mijinki girki? Bawai nace yar aiki is bad bane ai ko ni inada yar aiki tadan taimaka maka da one or two things but that does not mean zaki barmata ragaman gidanki menene haka Hadiza ke kina ganin wayau ne hakan kin cika yar boko ko? Kin waye kinada kudi kinyi kawaye matan Abuja kema kin dauki sahunsu kirasa wanda zaki mawa sai mutumin da shine yabaki jarin mutumin that made u Hadiza” ihu Hadiza tayi tace “me aciki Anty Jams ai sai nabiyashi kudin daya kashemin nafara business din harda riba indai hakan zaisa yafita harkata yabarni na Sarara nayi yanda naga dama” dasauri Jamila tace “wai kinsan wane kike aure kuwa? Nura fa kampanin shi shike tashe yanzu ko su cosgrove abayansu suke, ga kyau ga aji ga hakuri baki tunanin yazo yahadu da wata kinamai haukan nan yakaro aure abinshi” har cikin ranta Hadiza taji maganan ya soketa dasauri tace “Nuri baida ra’ayin mata biyu tun kafin muyi aure yamin alkawarin ni kadaice matarshi har abada and Nuri baya taba karya alkawari, he’s a man of his words” dan murmushi Anty Jamila tayi tace “to inhar bakison alkawarin nan ya karye take care of mijinki ki sauke pride din nan youu are under him and u will always be, kidaina mai kallon keda shi are equal kina rainashi, keda mijinki can NEVER BE EQAUL, and Bari nagaya miki ki gaggauta gyarawa kafin Nura ya rufe babinki yabude sabon babi,_ saida safe kuma zan sanar da Mama yanda mukayi” ta katse wayan batare data karabi takanta ba shiru Hadiza tayi tana kallon wayan ranta ya mugun sosu da kalman kishiya. Da Yayanta tayi tsaki tayi ta yarda wayan gefenta tace “shiya isa yama mini kishiya, tsorona bazai ma barshi yayi wannan kuskuren ba, banda hakama mata basa gaban Nuri sai business kuma Nuri baida ma yawan sha’awa kaman nine saimuyi watanni bamubi takan shimfidan juna ba ninama fison haka dan ba haihuwa nakeson nakarayi ba inaso nai maintaining this body da shape shi aina zai taba samun kyakkyawan mata fara hausa fulani komi yaji irina” tayi dan murmushi tanajan bargo takoma bacci abinta.


MAISA WASU MATAN KE GANI SUDA MAZAJENSU ARE EQUAL????


💫MATAN?? Ko MAZAN??💫


✍🏻M SHAKUR

EPISODE 5️⃣
Ummi kwata kwata takasa runtsawa koyaya ta kulle ido ganin lokacin da Alhaji ke kallonta take, da yanda ya kula da ita dazun dinnan the same way yake handling su Aman that’s yanda yayi handling nata, abun yaki fita daga zuciyanta, the entire scene ya narkan da zuciyanta sosai dan har yanzu kamshin turarenshi takeji yanda yazo dab da ita, she can still feel dadin kamshin iskan bakinshi lokacin daya hura mata, mirginowa tayi daga dan katifan datake kai zuwa kasan tiles, sanyin tiles din yawani kara tsuma zuciyanta ta bude idanunta tana kallon POP sama fuskan Alhaji take gani wlh Alhaji akwai karisma da haiba dawani irin kyau ahankali tace “inama ya aureni” dawani kalan sauri tadaura hannunta saman bakinta kaman irin wacce tafadi taboo din nan, tayi aiki agidaje 4 wannan ne na 5 bata tabajin kaman mijin ko Alhajin gidan datake aiki ya aureta ba sai wannan sabida yanada mugun kirki, gashi da sanyin zuciya, sannan yanada natsuwa, yanada daraja mutane sannan yana son yaranshi sama da komi kawai mata ce baiyi sa’a ba wlh inda itace matanshi ko zaiga gata dan miji irin Alhaji da baida matsala hakan nan wlh kula zatayi dashi sama da yanda yake kula dasu Amal ma kula zatayi dashi kaman wani jariri tana bashi duk abinda yakeso aduniya, ahaka bacci yayi awon gaba da ita da tunanin Alhaji aranta.

Wuraren 1 yashigo gidan da kanshi ya kwaso duka kayan daya sayo dazu na cefene yakai kitchen ya ijiye komi sannan yawuce sama dan kwanciya.

As usual biyar yafito sanye da jallabiya tunda yabude kofanshi kamshi ya daki hancinshi ahankali yake sauka daga staircase harya karasa sauka kasa wutan ko’ina akasan akashe wutan kitchen ne kawai akunne ga kofan kitchen din abude wajen dinning yaje ya tsaya yana kallon kitchen din Ummi yagani tana girke girke daban daban ga su lunch bag na Aman da Amali akan island yau zasu school, tana sanye da Riga da skirt yana ganin kayan yagane su kayan Hadiza ne tun tana yammata sun kode sosai amman dudda haka sunma Ummi kyau that means tayi wanka kafin tashigo kitchen folding hannunshi yayi yana kallonta tundaga kan slippers green dake kafanta zuwa kanta dake daure da dan kwalin atampan jikinta, tanada tsayi sannan tanada hips dudda ba sosai ba but sunada curve irin yaran nan ne da suna samin kula zasu cicciko yanzu wahala ne yasa suke looking haka ma, dan lumshe idanu yayi yabude ya tsare fuskanta da kallo ahankali Yatambayi kanshi am I falling for this girl? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuya yawuce yafice zuwa mosque yana deep tunani shiba yaro bane yasan when zuciyanshi keson abu.

Wuraren 7 nasafe yashigo gidan Hadiza yagani a dinning taci gayu sosai cikin wani exclusive atampa ta buga dauri tanacin lafiyayyen breakfast chips da pepper soup sai shayi agefe, itakuma Ummi na tsugunne a tsakiyan falo tana feeding Amal a baki Aman na kusa da su daduk ta shiryasu cikin kayan makaranta suna ganin babansu da gudu sukai wajenshi. “Daddyyy Assalamu Alaykum Dady ina kwana” murmushi yayi yadauki kowannensu yamusu peck yashigo dasu falon yace “ku karasa breakfast yanzun nan school bus zaizo” basuyi musu ba suka koma, anatse Ummi da kanta ke kasa tace “ina kwana Alhaji” batare daya kalleta ba yace “fine” sannan yadau remote yana chanza tasha 8 zai fita hakan yasa kawai ya ijiye remote din yawuce sama ko kallon HADIZA baiyiba itama bata kalleshi ba saima karasa cin abincinta datayi tawuce tadauki car key tace “ki dafamin couscous da daddare ke” ahankali Ummi tace “to Anty, saikin dawo Allah bada sa’a” yatsine fuska tayi bata amsaba tawuce tafita tashiga motanta tabar gidan, bata dade da fita ba motan su Amali yazo Ummi takaisu suma suka wuce tafito tana gyara wajen taje dinning ne ta gyara inda Hadiza taci abinci sannan tawuce tana duba girkin datake ma Kakan su Amal dazata zo, tana cikin tuka tuwon Alkaman taji kamshin turare dasauri ta juyo hada ido tayi da Nura daya shigo kitchen din yasa wani blue gizna shadda wlh yayi kyau na bugawa a jarida faduwa gabanta yayi dasauri ta dauke kai ta saki muciyan a tukunya zata duka yace “cigaba da abinda kikeyi” batai musu ba tacigaba saikuma tadan juyo hada idanu suka sakeyi ahankali bakinta nadan rawa tace “kana bukatan wani abu ne Alhaji”? Dan girgiza kai yayi yaja daya daga cikin kujerun dake gaban island din yazauna yace “me kike tukawa”? Atsanake tajuya takalli tukunyan tace “tuwon Alkama, kace Hajiya da safe zata iso saisa nake mata nasan basuyi kari ba suka shiga hanya, itakuma sister ka zan dafa mata abu daban” yana kallonta yace “nikuma fa” dan kallonshi tayi ga mamakinta murmushi yasakan mata dasauri tace “breakfast dinka nakan dinning amman idan kanason wani abu daban ne zaka iya fadamin namaka yanzun nan” “hmmm!” Yasauke ijiyan zuciyan dashi kanshi baisan karanta yafito ba maganan yatabamai zuciya dan wannan ne abinda matanshi bata tabamai ba just look at yanda yarinyar nan tabashi girma da daraja da kima kome yakeso yafadi zatamai that king treatment shitake mai, kawai saiya dago yakalleta yace “dafamin shayi mai kayan kamshi” dasauri tace “to” zare muciyan tayi daga tuwon tadan diga ruwa ta rufe tarage heat din tawuce ta wanke hannunta tashiga hadamai shayi shikuma yaciro wayanshi yana tabawa dan kawai tasaki jiki amman wlh kusan kome takeyi idanunshi binta suke, nan da nan tahada shayin tadauko wani hadadden flask jug tazubamai tasaka a tray tadauki cup da spoon da sugar kaga yanda take plating zaka dauka taje culinary school ne nan ko tsabagren experience ne a aikatau, tadauko tray din tazo har gabanshi ta ijiye sannan ta duka tace “nazuba maka?” Ahankali yace “yes” mikewa tayi yana kallon hannunta farcenta farare kal dogaye masu kyau tazubamai tace “sugar cubes nawa zansa ko asa zuma?” Kaman wani yaro dan he’s just enjoying the way take neman permission nashi for komi this is luxury da baya samu yace “zuma” dasauri tajuya tafita daga kitchen din taje dinning tadauko zuma takawo ta zubamai sannan tajuya tadauki cup din tadaura kan tray nashi tajuyo tabashi kallon fuskanta yayi sannan yasa hannu ya amsa yace “thank you Ummi” wucewa tayi takoma wajen tuwon tashiga kwashewa kaman daga sama taji yace “waye Mudin kauye?” Juyowa dasauri tayi takalleshi hada ido sukayi yana kurban tea juyawa tayi tacigaba da kwashe tuwon tana mamaki a ina yatabajin takira sunan Mudi saikuma ta sauke ijiyan zuciya tace “tsohon miji na ne” dasauri Nura yakalleta yace “kin taba aure”? Gyadamai kai tayi tace “eh amman an dade tun ina shekara sha uku-sha hudu aduniya” yana kallonta yace “meya rabaku”? Tsayar da kwashe tuwon datakeyi tayi saikuma ta kalleshi yanda ya tsareta da ido yasa ahankali tace “dukana yake, kullum kullum duka, hakanan kaman idan bai dakeni ba bayajin dadi rayuwanshi, shine…..” takasa maganan tai shiru takai hannu ta goge hawayen dasuka zubo mata dasauri tajuya tacigaba da kwashe tuwo Nura yace “shine meya faru”? Ahankali tana kwashe tuwon tace “shine rannan dayamin wani bakin duka saida na haifo bakwaini, inada cikin wata shidda lokacin, amace yafito yaron, saida nayi jinya na kusan shekara daya inata fama da yoyon fitsari, Gwaggo na ta hadashi da mai anguwa akan saiya sakeni kuma abimini hakkina dan ya illata mata jika tun bayan haihuwan dole dayasa nayi ban warkeba, to da kyar yasakeni amman dudda ina rashin lafiyan yakan biyoni har gidanmu yamin duka har suma inayi, ko baizoba kullum cikin fargaba nake zaizo, Maman mu tarasu Gwaggo mu ce kadai garemu kuma batada karfi ta tsufa, ahaka dai na warke but ina cikin tsoro kullum, saisa dataji wata mata dake zuwa kauyenmu kwasan yara aiki taje ta roka da kyar akace za’a daukeni, to aboye aka fitar dani daga kauyen mu kada Mudi yaganni, tundaga nan nazo birni tun ban gane abubuwa harna gane yanzu nima, amman inaso nakoma kauyenmu naga Gwaggo na da kannina Salamatu tai aure harta haihu Maimuna da Ikilima ne za’ayi bikinsu kwanan nan kuma inaso naje amman Gwaggo na bataso nazo tsoro take kada nakoma kauye Mudi ya kasheni, yanzu ance yafi da zama takadiri ya gagari kowa, tsoron shi ake har mai gari, amman nayi kewan garinmu da gidan mu da Gwaggo na da kannina sosai bansan ya Allah zaiyi dani ba bansan kozan kara sa kafa a kauyenmu ba” tai maganan tana kai hannunta saman fuskanta duka biyun tadanyi sheshekan kuka mara sauti, shiru Nura yayi yana kallonta tabashi tausayi sosai ahankali yace “kinaso nakaiki kauyenku kiga yan uwanki”? Dasauri tazare hannayen ta dagakan fuskanta takalleshi da rinannun idanunta yanda ya tsareta da idanu yasa gently ta gyadamai kai, murmushi yayi yace “I promise zan kaiki kauyen ku, and namiki alkawari ba Mudi ba ko mudari yake bai isa yamiki kallon banza bama balle ya dakeki kinji” gyadamai kai tayi ahankali, murmushi yadan mata yace “kada ki kara kuka bayama fuskanki kyau” akunyace tai murmushi shima murmushi yayi yace “idan Hajiya tazo dazaran nagama kata katan asibitin ta zan kaiki gida ko” gyadamai kai tayi dasauri, tashi yayi yakalli agogon hannunshi yace “bari natafi daukosu nasan jirginsu yatashi yanzu kafin nakai airport sun sauka, kinason nasayo miki wani abu”? Yamata tambayan da saida ta kalleshi da mamaki ganin ya tsaya yakuma tsareta da ido tace “Amali tadameni tun jiya zatasha yoghurt babu yoghurt agida” jinjina kai yayi irin yaji din nan yace “ke me kikeso”? Sunnar da kanta kasa tayi akunyace tace “slippers wannan yakatse dazu na naneshi da wuka mai zafi saisa na iya sawa” yanda takejin kunyanshi na burgeshi sosai, anatse yace “to” yajuya zai wuce dasauri tace “Nagode Alhaji Allah kara girma, saika dawo Allah ya tsare” juyowa yayi yace “Ameen Hajiya Ummi” dasauri takalleshi wucewa yayi yafice yana murmushi mota yashiga, saida yafara tsayawa a super market yayi sayayya harda cream da shower cream mai kyau yasa mata da su turaruka da wasu abaya daya gani a super market din da idanu ya gwada tsayinta haka yabiya kudi yafito, haryakai airport labarin Ummi yake tunani yaushe kauye zasu dainama yara Auren wuri ne haka, yanzu sabida wani katon mugu aka koro yarinyar nan aiki, yayi traumatizing nata tun tana 14, small girl fa, hmmm Allah ya kyauta.

Daidai yana parking awajen parking wayan Amina nashigowa fitowa yayi daga motan yana daukan wayan yace “okay ku jirani a arrival din gani nan zuwa” wucewa yayi tun kafin su ganshi ya hangosu, wata tsohuwa ce fara mai zanen kalangu a fuskanta zaune kan wheelchair dawata budurwa da akalla zatai tsaran Ummi ke gungurawa ga akwatinan su kan cart a gefe tareda mutumin dake turawa, ahankali tsohuwan matan tadago idanunta dan taji alamun danta ajikinta hakan yasa sai waige waige take, ta baya yazo yahada idanu da Amina daya mata alamun kartai magana sannan yataho kawai Hajiya ganinshi tayi agabanta ya tsaya bai damu da airport sukeba tsugunnawa yayi yasa guiwowinshi akasa yana kallon fuskan mahaifiyar tashi data washe baki ganinshi tace “me haka tashi tashi kayanka zasu baci, yanzu kasan banda karfi balle na wanke maka” ahankali yakai duka hannayenshi yatallabo fuskan mahaifiyan nashi yace “bance kada ki kara ciwo ba eh Hajiya?” Cikin barkwanci tace “ai dazai tasomin saida nace kai rashin lafiya ka manta kashedin da Nura yamaka ne kakeso kadawo kuma” dan murmushi yayi duk rashin lafiyan Hajiya bakinta is always there baya fatan tai rashin lafiyan dazai hanata magana har abada In sha Allah. Rungumeta yayi ahankali yace “barka da zuwa Mamana, Allah yabaki lafiya Hajiya, Allah yasa kaffara ne” bayanshi ta shafa tace “Ameen Ameen ai naji sauke Amina ai bata kyautamini ba banso ta tadamaka da hankali ba wlh, tashi daga kasa kaga jama’a sai kallemini d’a suke yasa guiwa akasa” batare daya saketa ba yace “albarkan mahaifiyata nake so” murmushi tayi tace “Allah maka albarka Nura, Allah ya lura dakai kaman yanda kake lurada ni, Allah yasa yaranka sumaka yanda kamini Nura, yanzu tashi mutafi kaji dan albarka” anatse yace “to Hajiya” sannan yadago yabama mai cart hannu suka gaisa sannan yakalli Amina hannu yabude mata dasauri ta rungumeshi tace “Yaya ina yini” kanta yashafa yace “lafiya lau Autan Hajiya” wheelchair ya karbe yashiga tura Hajiya da kanshi har mota saida ya zaunar da Hajiya tazama comfortable sannan ya sallami mai cart suka shiga mota suka tafi, Hajiya sai kallonshi take ta madubi tanamai hira tace “amman kai rashin lafiya ne ko Nura? Naga kafada sosai”? Dan murmushi yayi yace “aiki ne wlh Hajiya” ijiyan zuciya tasauke tace “to Allah yabaku sa’a kadinga hutawa kanacin abinci akai akai kaji ko” “to Mamana” ya amsa yana murmushi, tace “nataho maka da danderu” baki yabude yadan juyo zai kalleta dasauri tace “kul maida hankali tuki kake” dan dariya yayi yace “Meenah ya akayi akabar Hajiya tawuce da danderu”? Dan dariya tayi tace “ba anga batada lafiya ba babu wanda yayi musu da ita” murmushi kawai yayi yace “inason Mamana Ameena sosai” Hajiya data washe baki tace “nima inason d’ana sosai” Ameena ta turo baki tace “Hajiya nifa” dan dariya Hajiya tayi tace “Inason ku duka akwai wanda ma yasamu soyayyata irinki Auta na” ahaka suna family hira sukakai gida Nura yace “specialist danai consulting yace zai ganmu by 12 yanzu zakici abinci kihuta anjima saimuje asibitin ko” yayi maganan tareda yin Parking yafito da ita sabida dakali da kafanta tayi tafiya tana rikeda shi suna tafiya ahankali Ameena biye dasu tana kallon hadadden gidan, bude kofa sukayi suka shiga ciki wani lafiyayyen kamshi yamusu sallama dasauri Ummi tafito daga kitchen tazo har tsakiyan falon ta duka tace “sannu da zuwa Mama, ya hanya ya jiki, Allah yabaki lafiya Mama, Allah yasa kaffara ne” washe baki Hajiya tayi tana kallon Ummi tace “waye wannan yarinyar mai ladabi ba irin su Auta ba da basu gaida mutane da kyau, ga iya addu’a, waye ita”? Dan murmushi kadan Nura yayi yace “Ummi sunanta” daidai Hajiya na zama, Hajiya tasauke ijiyan zuciya tace “jiki Alhamdulillah Ummi, sannu kinji Allah miki albarka tashi tashi ki zauna, ina Hadiza? Nasan jikoki na ana makaranta ina Hadiza?” Hajiya takara tambayan da zuciya daya tana waige waige neman Hadiza, cikeda hikima Ummi tace “tadanje tadawo wani uzuri yakamata amman tace na kula dake da kyau kome kikeso namiki” sosai Nura ke kallon Ummi yanda yarinyar keda hikima baitaba sanin zata iya fadan magana hakaba, dariya Hajiya tayi tace “ayyooo” kallon Amina data shigo da jaka Ummi tayi gateman biye da ita da kayansu da sauri ta tashi tace “kawo nakai miki daki jeki zauna kihuta kinsha hanya” murmushi Meena tayi tace “thanks” kai kayan sukayi sama sannan Ummi tadawo tashiga kitchen a tray tajera abincin Hajiya da ruwa a bowl mai kyau na wanke hannu tafito takawo har gaban Hajiya, Hajiya tace “Ayyah sannu da aiki Ummi, Allah dai yasa cimata ne dan yanzu bakomi nakeci ba, cuta batayi ba” tai maganan tana bude kulan ganin tuwon Alkama da miyan zogale dayaji ganye yasa Hajiya tace “laaaaaaa Hadiza tamin girkin nan kafin tafice” dasauri Ummi tabude baki zatace eh Nura yace “Ummi ta dafa miki Hajiya” kara kallon Ummi Hajiya tayi saikuma ta nunawa Meena Ummi tace “kinga girkin sa’onninki ko ke sai shegen kiwuya, wai wannan kamshi haka bari naci abincin nan akasa zan zauna ma” da taimakon Nura tazauna akasa ta wanke hannu takai abincin baki saita kalli Nura takuma kalli Ummi takara kallon Nura again tace “Ummin nan dai danake gani tai girkin nan”? Gyadamata kai Nura yayi sai kawai Hajiya tace “Allahu Akbar wlh tayi girkin yanda nakeso, kaga ba gishiri ba magi, sannan bata sakamin jan nama ba hanta da Koda kadai ne amiyan, cimata tamin kuma yanda nakeso, bani jakana Meena kigani” bata jakanta Meena tayi Nura ya karba, dasauri Hajiya tace “ciro duka kudin dake purse dina” murmushi yayi ba musu yaciro dubu goma da dari biyar ne ta karba tamikama Ummi tace “ga tukuicin ki dan kin dadada mini rai kinsa natuna na diyata Aisha mai bin Nura tana aure a eygpt ita kadai kemini abinci irin wannan taste din wannan tarban da akamin bazan taba mancewa da ita ba, nagode ko Ummi amshi kudinki” akunyace tace “Mama kibar shi ni nadafa

Please Login or Register in order to submit comment