Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa "hey stop it" zare ido tayi kafin tace " me kace????" Farhan kam kansa yad'aga sama yana kallon Umair, "WHO IS SHE???"(wacece ita???)

kafad'a Umair ya ɗaga kafin yaja hannunsa zasu shige cikin gidan, da zafin nama, Labbo ta shige gabansu "ku tsaya dan Allah, menene SITAFIT, (STOP IT) naji wannan gwaigwai ɗin ya na cewa haka, ta faɗa tana kallon Umair cikin tsananin mamaki.

Ware ido Umair ya yi, yana kallonta shima domin sam bai gane me take nufi ba, Farhan ne ya yi dariya cikin yarinyata yace "Bro wai tana son cewa stopped ne fa" yafaɗa yana dariya sosai, gira ɗaya Umair yad'aga shima kafin yaɗan saki murmushi ya kalleta yana cewa "Stop ake cewa kinji, yana nufin kibari" daga kai tayi tana kallonsa, kafin ta wuce waje tana ƙunƙuni.

"dan wallahi yau sai naci uban gwaigwai ɗin nan da yamin dariya, shege da wani farinsa kamar ƙosai"

gurin masu aikin taje ta tsaya a kansu tana kallon yadda suke yi.

"ga ta can, ga ta can , taji ana faɗa daga bayanta" juya wa tayi domin ganin dawa ake, sai ta hango Fatsume bala'i da k'awayenta sun nufo wajen, cikin sanɗa ta juya ta fara tafiya domin taje ƙofar gidansu, sauri su Fatsume su ka ƙara domin a zatonsu guduwa zatayi, shan gabanta su ka yi, kallonsu ɗaya bayan ɗaya nayi "Sitaf" na faɗa ina ɗaga musu hannu,

turuss su ka yi gaba-ɗaya suna kallona, wannan ta kalli wannan, "ke dan uwarki me kikace???"
ƙawar Fatsume ta faɗa tana matso wa kusa dani, "Ubanki nace" nima na faɗa ina watsa hannuna alamun ban damu ba.

hannu takai jikina da niyar shaƙata "what are you doing here" (me kukeyi anan???) Farhan ya tambayesu yana daga ƙofar gida, kallonsa suke kamar sun sami TV ɗaya daga cikinsu ce tayi ƙarfin halin cewa "ina ruwanka" .

" Farhan Farhan" Umair yake ƙwala masa kira yana kiran sa, fitowa yayi yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya duk sunyi cirko_cirko suna kallon baiwar kyau,

cikin iyayi da kwainane da yanga Hinde ƙawar Fatsume tace "munzo ɗaukan fansa akan Labbo ne, shekaranjiya taya gama ƙawata kaya, sannan kuma waccen yarinyar ta gefe, Labbo ta cinye mata kud'inta saboda tace zata shiga mata fad'a, kuma bata shiga ba, ta gudu da kud'inta"

"gifff Labbo ta buge bakin, tana cewa Allah ya tsine uwar me ƙarya, yaushe na gudar mata da kud'inta????"

"ya isa kuyi hakuri, ga shi ku karɓi ƙudin bara na biya komai ya wuce" Umair ya faɗa yana cirowa dubu ɗaya acikin wandonsa, ya miƙa musu.

carafff Labbo ta kama kuɗin, aradun Allah ba zaka basu dubu ba, kuɗinsu naira ashirin ne fa"
"ina ruwanki to ai nine na basu" Umair yafad'a yana fizge kuɗin ya cilla musu, ɗauka su ka yi suka bar wajen da gudu,dan yau kam sun sami kuɗi.

binsu Labbo za tayi ta gudu, taji an riƙe mata hannu, tana juyowa taga gwaigwai ne, "ki ƙyalesu mana, kizo muje gida Yaya Umair zai baki masu yawa" .

washe haƙwarana nayi "kace Allah???" girgiza min kai ya yi kafin nima na juya na bishi,
munzo shiga ƙofar gida na sakar kasa rankwashi a kansa, "auuchhh" ya faɗa yana riƙe gun,
"me nayi miki" ya faɗa yana kallona, nima zare masa ido nayi ina cewa "wa ya ce kamin dariya..........."✍🏻





yawan comment yawan typing.....






Oum Khalil✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


🍇 *ABDUL MANI*🍇

🍇 *TYCOON* 🍇



Story & Written


By


🍇🍇@ashoush💕

FREE BOOK

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCINMU*

# COMMENTS & SHARE

🍇 _Abdul Maneou_🍇

PAGE 23 to 24

_________Zumɓuro bakinsa gaba ya yi, domin shi dai ba a dukansa agidansu, "gaskiya in dia kika ƙara min wannan abun to Yaya UMAIR ba zai baki kuɗi ba, kuma ai ance ba kyau zalun......" Buuubbb LABBO ta buge bakinsa, "amma yaron nan baka da kunya ko????? gaskiya ina ga baka da kunya, ni ɗin zaka ce wa azzaluma???" LABBO ta k'arasa tana ƙanƙanta idanunta tsabar masifa ta na cinta,

"Eh ɗin na faɗa muguwa azzaluma" a guje na bishi, shi ma ya runtuma cikin gidan da gudu muna ta zagaya wa, SAMHA ta fito ta na kallo na, "mutum ya daina kallona kurwata kurrr" na ƙarasa ina farfara mata ƙatunan idanuna.

K'wafa ta yi, kana ta cigaba da sabgarta, ni kuwa na k'ara runtuma aguje nabi GWAIGWAI, can ɓangaren shanayenmu ya nufa, ganin haka na kyalkyale da dariya, dan yau sai na kai shi gurin (MAALUU) ta harbeshi.

a hankali na fara siɗaɗawa ina shiga a hankali na matse jikina yanda zan shige can ciki ina binsa sai da muka je k'arshen ginin na wawuro shi ya goce, LABBO ta fali kasa warwass, tana ƙoƙarin tashi sai naji wani irin zafi ya ziyarce ni, wasu taurari su na wucewa a ta saman kaina, bata gane me yafaru da ita ba sai da ta taɓa leɓenta, taga jini yana biyowa, kana na ji kukan sanuwa a gefena, sannan na ankara da hangurma saniyar tamin a bakina cikin dauriya na miƙe ina jan kafata, domin na fito daga cikin garken shanun.

a ƙofar garken na tarar da SAMHA da su MA'U tsaye, suna kallona suka kwashe da dariya zamana nayi dirshan a kasa na kama kuka, dan wallahi na tsani ayimin dariya, ta shi nayi da hanzari nayi kan su MA'U ina ta zabga mata zagi "wallahi sai na rama, bazan yarda ba" na cakume ta da faɗa, ɓanɓare hannuna SAMHA tayi ajikinta cikin silent voice ɗinta,tace "sune suka buge ki hala????" .

"Ni dai ina ruwanki, ko basu bane sai na rama wayace a yimin dariya" ta ƙarasa tana hararta.

kama hannun FARHAN tayi suka zo wucewa ta gaba na, na takarkare na ɗima masa duka, ina cewa "shege GWAIGWAI mai hakwara, zai cijeni".

Kallona MA'U ta yi kafin ta ce "ke wai waye GWAIGWAI?????"
"ga shi can wannan farin yaron" sauƙe numfashi MA'U ta yi ta na ce wa "kuma fa haka ne sai yanzu na lura dan farinsa ya yi yawa" dariya LABBO tayi kafin tace "ke dallah ni da naji ma ana cewa da GWAIGWAI ne, sai ya dawo mutum kuma" ta ƙarasa faɗa tana zaro idanuwanta.

"ke LABBO kiji tsoron Allah waya gaya miki?????" tsaki LABBO tayi kafin ta sake cewa "ke da har cizo yake yi ma, da canhu ake kulle masa baki"

" kuma kizo muje ki tambayi yayansa ma kiji"

Jawo hannun MA'U nayi muka shiga cikin tsakar gidan, anan na samu SAMHA tana korawa Inna bayani, gaba-ɗaya juyowa sukayi suna kallona.


"Zo nan MANAL" naji Inna ta kirani, a hankali naje, kama kunnena tayi ta murɗe shi "Auuchhh INNA da zafi wallahi , kiyi hakuri bazan ƙara ba" .

"zauna muyi magana" Inna ta faɗa tana zaunar da LABBO kusa da ita,
"shekararki nawa yanzu???" watsa hannu sama tayi alamun bata sani ba, sai kuma tace "auuu na tuna haka da haka" ta faɗa tana dunƙule hannunta biyu guri ɗaya sannan ta ware uku, alamun goma sha uku kenan 13 .

"bazaki iya magana ba ne ko YAYA????" turo baki LABBO tayi gaba,
"ki nutsu kiji me zance miki, meyasa ke sam baki da hankali???" zare idanu tayi tana cewa "Kaiiii INNA wayace banida hankali kuma???"

"dallah yimin shiru ko na fasa bakin yanzu" zaro ido tayi tana kama bakinta alamun ta zuge,
"gaba-ɗaya gari ya ɗauka ko ina zancenki akeyi ana cewa baki da nutsuwa, kin fiya faɗa da neman tsokana, ko jiya da naje gidan biki sai cewa ake yayarki ta fiki kyau da nutsuwa, duk halinki ne ya jawo har yanzu yayarki ta rasa mijin aure, dan Allah ki rufa min asiri ki nutsu" sunkuyar da kai LABBO tayi, kana INNA ta cigaba da magana yanzu haka sauƙarki saura sati ɗaya amma ba abunda kike sai shirme" INNA ta cigaba da yiwa LABBO nasiha tana mata faɗa har BAFFA ya shigo.

kana shima ya ɗan ƙara da nasa, tare da tuna mata cewa ta fara tilawar karatunta.

sumui sumui ta miƙe ta fito daga ɗakin sai ka rantse da Allah gaba-ɗaya abunda aka faɗa mata ta ɗauka tass, fitowa nayi na samu SAMHA tsaye ga UMAIR a gefe, kama haɓa nayi na riƙe, ina jijjiga kai, "uhnm" na faɗa ina rabawa ta gefe na wuce, cikin zuciyata na ke cewa "Allah ya tona muku asiri, wallahi sai na gayawa BAFFA ashe iskanci kike da ɗan Burni, tusa ta kusa ta ƙarewa bodari" .

"keeee tunanin me kike" MA'U tayi tafi a saitin fuskata, firgita na waigo ina kallonta kafin nayi murmushi ina cewa "babu komai"
"to kizo muje mu karɓo hijab ɗin walimarmu a gidansu HINDE"
da sauri LABBO tace "yauwa muje, kinsan ina binsu bashi" kallona MA'U tayi da alamun tambaya "bashi kuma????"
"eh bashi jiya ɗan Burni ya biya su kulin da naci na siyan faɗa, dan haka zasu bani chanji, muje kawai"

Muka kama hanya har gidan su HINDE mu kaje, mu kayi sallama, "munzo karɓan hijabi" MA'U ta gayawa Maman HINDE, "ban ƙarasa ba ku dawo anjima" har zanyi magana MA'U ta ja hannuna, shiru nayi domin har na shirya abunda zan aikata araina.....


🍇🍇
MANAMA BAHRAIN

a ɓangaren Maan bayan fitar Guards ɗinsa daga ɗakin, Jallabiya ɗinsa ya zura, kana ya sami kujera ya zauna, ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ya na girgiza wa idonsa a rufe,
"Assalamu alaikum"
can cikin ƴasan maƙogoronsa ya amsa sallamar sa, ya na juya kansa ɗayan gefen dan bayason abunda zai sa shi magana yanzu.

"mtsww aikin banza wallahi komin juya kan da zakayi sai na shigo ciki" HAMAD ya faɗa ya na k'araso wa cikin parlon, zama yayi akan cusion yana cewa "summa sami'ina an sha'an say'an yahdus, nahadna wadakalna fi mizaj shay'i" (sai mukaji wani abu mara kyau ya faru kuma, hankalin mu ya tashi mun shiga wani hali) "yuqal innal musalahin dakalul makan ba'ada zuhura Baba, a tamanna ala yahdus shay' laka, wali sha'abik??"
(ance ƴan bindiga ne suka shiga wajen taron bayan barin Baba wajen??? ina fata babu abinda ya sameka kai da mutanen ka?) .

lakad ra'ayta kasir min alkanabil ala al BBC mu'akkar, li anna alhuras hunak kutilu jami'an" (ɗazu nagama gani a BBC an tashi Bomb dayawa, saboda masu gadin wajen duk an kashe su) sai yanzu MAAN ya ware idanunsa akan HAMAD jin yace an kashe masu gadin Wajen, tunda HAMAD yake ta zuba bai buɗe idonsa ba sai da yaji ankashe mutane, gauron numfashi ya sauƙe kafin ya buɗe baki slowly "lizalika attakazat kadwat kabiraat fi zalik, kullu da'amik fil funduk wa kullu shay"
(sai na ɗauki babban mataki akan wannan abun, sannan a bincika gaba-ɗaya camera's ɗin da su ke cikin hotel ɗin) MAAN ya na gama faɗin haka ya miƙe.

cikin ɗaki ya shiga kusan 20minutes, walking slowly ya fito sanye da Blue body hug a jikinsa yana gyara ɗaurin agogon hannunsa .

"sa'aud marratan ukra"
(ina zakaje kuma??)
"I'm planing a trip to Nigeria, as I told you, get a lot of information on it, I ll leave now" MAAN ya faɗa yana dukan kafaɗar HAMAD,

"But why would you go Fast????" (meyasa zaka tafi da gaggawa haka??) HAMAD ya sake tambayan MAAN,

"Will do something very important, but I ll be back on time.." ( zanyi wani abu mai muhimmanci amma zan dawo akan lokaci) ya faɗa yana jan ƙaramar trolley ɗinsa, zuwa waje.

"Don't tell anyone I ll leave untill I get home" ( karka faɗawa kowa zan tafi har sai na isa gida)

yana fita Guards ɗinsa gaba-ɗaya suka miƙe suka rufa masa baya, motocin suka shiga.

Suka basu wuta ba su tsaya a ko ina ba sai
INTERNATONAL AIRPORT BAHRAIN ICAO
babu ɓata lokaci jirgin su yad'aga sai NIGERIA✈️...............






Oum Khalil

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment