Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baffa ya yi, ya nufi ɓangaren Inna ,dan ya san inya tsaya anan za'ayi ba dai_dai ba, ya kasa gane me ya ke da mun Hasse, kwata-kwata yanzu bata masa biyayya.





Cikin daƙin Inna ya shiga aciki ya sa meta zaune ta yi ta gumi, ga Samha agabanta ta na sa wa Fadwa kayanta,




"Nyalli jam Baba am" (ka wuni lafiya Babana??)
"Jam ƙalau Bingel, a jamo??" (lafiya ƙalau yarinyata, kina lafiya??)
"se jam kalau" (lafiya kalau) Samha ta ba shi amsa ta na miƙe wa don ta basu waje ɗauke da Samha a hannunta.





Fitowarta ya yi dai-dai ta fitowar Umair wanda ya fito da jarkar faro a hannunsa ya na wankewa.




idonsa bai sauƙa a ko ina ba sai cikin na Samha, dum! dum!! dum!!! a ta ke gaba ɗayansu zuciyoyinsu su ka buga, wanda Samha har sai da ya kaita ga runtse idanuwan ta.





"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta mai kowa mai komai, wanda ya tsara wannan halitta ba tare da taimakon kowa ba, tsarki ya ƙara tabbata ga Ubangijin Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallama, Masha Allahu lakuwatta illa billah".





Umair ya ci gaba da tsarkake Ubangijin al'arshi, domin tunda ya ke bai taɓa ganin kyawu irin wannan ba, duk za gayen ƙasashen turawan da yake yi,





walking slowly Samha ta fara ta fiya ta na ɗauke kanta cikin kunya daga kallonsa, bayanta ya bi da kallo ya na ƙara ganin tarin baiwa da Ubangiji ya tara a mazaunan ta,





"Astaghfirullah" ya yi saurin tuba, saboda abunda zuciyarsa ya fara ayyana masa "kaii umair kasan me kake kuwa???" zuciyar sa ta tambaye shi,




Shima ba shi da amsar tambayoyin da zuciyarsa ta ke masa saboda ha ka sai ya ɗaga kafaɗarsa tare da koma wa ciki,





Ɓangaren Baffa bayan sun tattauna da inna sai ya fito domin ya koma sa shinsa, anan ya same su har sun kammala cin abinci suna zaune suna ɗan hira jefi-jefi,





da sallama ɗauke a bakin Baffa ya shiga cikin ɗan parlon nasa da ya ke shinfiɗe da darduma,




Mik'ewa su ka fara yi domin suyi haramar tabfiya kar dare ya yi mubsu a hanya,




Daddy ya miƙa wa Baffa hannu yabna ce masa, "game da wannan aiki da za'ayi, ba zanyi gaggawar ta shinka agidan ka ba, yadda ka tara ƴaƴa, tashinka anan zai saka shiga wani yanayi, saboda haka Malam Muhammadu kayi zamanka tare da iyalinka acikin wannan gida nabar maka halak malak"




"Kuma inshaallahu idan Abdoul ya dawo zai zo ya ga ginin da ya kamata ayi maka, yanzu ga wannan ka riƙe zu wa wani lokaci" Daddybya faɗa ya na mik'o masa rafar ƴan dubu_dubu ba tare da ya ƙirga ba,






Hannu Baffa ya mi ƙawa Daddy cikin tsananin farin ciki, Daddy ya gama yi masa komai a duniya "Allah ya saka da alkairi Alhaji nagode Allah yaƙara buɗi ya ƙara ɗaukaka, ni kuwa da me zan saka maka???"





"karka damu Malam nayi duba da yanayin mu'amulat ɗinka ne shiyasa na maka wannan abun saboda ka cancanci haka agurina, kuma wata rana nima zan zo neman abu agunka, yanzu ga d'ana zai zauna tare daka, na kwana biyu idan ya ga ya nayin aikin sai ya dawo"





"to to to ba matsala ya zauna tare damu ba matsala, nagode kwarai da gaske Allah ya nuna min lokacin da zaka nemi abu aguna kowanne iri ne zan maka bi'izinillahi rabbi"





Hannu Abba ya bashi suka gaisa, su na ƙara yi ma sa sallama, a tsakar gida su ka haɗu da Inna wuro, "a'a yallaɓai har kun fito ta faɗa ta na washe masa yalayen hakwaranta,





"eh mun fito" Abba ya bata amsa tare da sa ka hannu a aljihu ya na miƙa mata, carafff Inna wuro ta warce,
"angode Allah ƙara arziki" tafaɗa ta na ɗaure kuɗin a haɓar zaninta,




Abba ya waiwayo ya kalli Baffa wanda ya ke ci ke da takaicin ta, "ita kaɗaice iyalin naka????"
"a'a akwai ƴar uwarta, A'isha" Baffa ya kwalowa Inna kira,





cikin ladabi Inna ta
amsa tare da fi towa cikin nutsuwa da kamala har ƙasa ta tsugunna ta na gaida su Daddy da Abba,



cikin sakin fuska su ka amsa suna tambayar ƴaƴanta,




Baffa ya kira Samha wacce take ɗauke da Fadwa ta na tsaye wajen su Manal "Na'am Baffa am" ta amsa,





"ku tawo tare da uwata"
"to Baffa"
"ke Labbo kizo muje inji Baffa"
mik'ewa Labbo tayi daga wurin wasan nata ta biyo Samha, har ƙasa su ka tsugunna su ka gaishesu




cikin jin dadi Abba yabkama hannun Samha da Labbo ya ɗago da su, yayin da Daddy yakarɓi Fadwa a hannu ta,




Hannu Abba yasa a aljihunsa ya na miƙa mu su kuɗi, a tare su ka haɗa baki "mungode Baba" ba tare da sun karɓi kuɗin ba,



kallon Baffa Abba ya yi ya na cewa "Malam Muhammadu ko kaine ka zare musu ido su ka ƙi karɓa???" murmushi Baffa ya yi, ya kalli Samha ya na ce mata "Jaboi mana Inna am" ( karɓi ma na uwata)
sunkuyar da kai Samha tayi, ta karɓa m usu ta na godiya sosai,





Ganin haka da Inna wuro tayi, sai ta hankaɗo safiya ta na cewa "jeki kema abaki, wawiya gasu chan ana basu ke kina tsaye sha sha sha"




kamar daga sama aka jefota haka su ka ga Safiya, cikin tsananin mamaki su Babban yaya su ke kallonta, hannu Daddy ya sa a aljihunsa ya d'auko ya bata ita ma ko godiya ba tayi ba ta kama hanya ta juya,





shikam Abba tuni ya kama hanyar ƙofar gida, ganin haka gaba-d'aya su ka bishi abaya,





Cikin motocinsu su ka shiga, bayan sunyi sallama da Baffa, Umair kuwa ya d'auko jakarsa a boot tunda zai kwana biyu, ganin haka sai Farhan ya fara kuka shima sai ya zauna tare da Uncle.




Cikin hargowa Abba ya doka masa tsawa "kawuce cikin mota nace"





murmushi Baffa ya yi ya na ce wa "Allah ya baka yawan rai ka bar shi ya zauna tare da ɗan uwansa a nan ɗin in yan ason hakan, babu wani matsala"



"shi ke nan "Son ga Farhan ya zauna tare da kai" Abba ya kira Umair ya na faɗa masa, cikin jin dadi Farhan ya rungume Abbansa, ya na waving hand ɗinsa har su ka wuce....




🍇🍇
MANAMA BAHRAIN

a ɓangaren Maan lokacin da su ka zauna akan acapulco chair ɗin nan, Ifraad nata masa hira, tan a ba shi labari sai yaji wayanshi ta yi ƙara alamun saƙo ya shigo wayarsa, slowly ya miƙa hannunsa ya ɗauka ya na buɗe saƙon kamar haka..

_Bienvenido al momento,recibimos su mesanje del dr pol sobre una empresa que quiere compartir acciones con usted, hace tiempo que nos mandan mensajes pero no no decimos nada, telo diremos y decidiremos excepto que necesitamos tenerlo en tus manos, Oga tenemis que verte espero eschcuchar de usted_

FASSARA

_Barka da wannan lokacin, nine dr.pol mun samu saƙo daga wajen wani mutum, a game da wani Company da ya ke son sa ka hannun jari a ciki, sun daɗe da turo saƙon amma bamu ce mu su komai ba, mun sanar da su sai mun faɗa ma ka munji shawarar da ka yanke, sai dai muna buƙatar sa ka hannunka, Oga ya kamata kazo muna buƙatar ganinka, muna tsammanin amsar ka._ ~Dr.poll~



Maan ya na gama karanta message ɗin ya sauke ajiyar zuciya, da ma ya san dole Mr. Richard sai ya bibiyeshi, amma ya zama dole ya samo mafita,




abunda yaji ne yasa shi da wowa daga duniyar tunanin da yake ciki, Ifraad ce ta sakar masa kiss a gefen wuyansa, kallon ta yake cikin tsananin mamaki, gently ya miƙe daga zaunen da ya ke ya na sanya hannunsa cikin aljihunsa, ya fara tafiya cikin jarumta da haiba.




Ya na saka ƙafarsa a bangaren sitti, wayan ta sake ƙara, d'ago wayar ya yi domin ya ga wanda ya ke kiransa "ARMAAN MAALIK" ya furta cikin dakakkiyar muryarsa,
slowly ya ɗaga kiran "habariyako?" ( ya ka ke?)
"iku nyingi rafiki yangu" (kwana dayawa abokina) "habari za asubuhu" (wallahi lafiya kalau)"ulimwengu wa kweli"(gaskiya kasamu duniya) "mwaka jana nilionekana kwenye gazeti la habari (shekaran jiya na gama ganin hotonka a news paper)"hatahivyo" (haba?)Maan ya fad'a kamar bai san komai ba, "umekuwa mtu tajiri sana" (wallahi ka zama wani babban mai kuɗi) "asante mungu" (mun godewa Allah)
"tafadhalinipigie" (dama kira na yi mu gaisa), "ninawasalimu Ammurh na baba" (ka gaida Ammurh da Daddy)
"nitawaambia" (zan gaya musu) "kwaheri"
(sai an jima) "okay bye" Maan ya fad'a ya na zura wayar cikin aljihunsa.



Arman Maalik abokinsa ne sosai a AMSTERDAM su ka haɗu da shi ya na matuƙar ƙaunar Maan, murmushi Maan ya yi tuno wa da wani abu da Arman din ya yi.




ya na cikin wannan tunani ya ji an rugume shi ta baya "kalaty" da sauri ya d'aga kansa jin an kira shi da wannan sunan "Madeehaaaaaaaaaa" ya furta "yeah it's me..............." ✍🏻





🍇🍇ABDUL MANI ISN'T FREE BOOK CONTACT TO SUBSCRIBED.........07069793061......✍🏻






OUM KHALIL✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON*



Story& Written

By

🍇🍇@ashoush💞

#FREE BOOK

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCINMU*


🍇 _Abdul Maneou_🍇

PAGES 19to20

___________"Madeeha" ya furta cikin zaro idanu, murmushi ta sakar ma sa tana cewa "yeah it's me" ƙayataccen murmushinsa ya saki yana zare ta daga jikinsa, dan shi wallahi wannan ɗabiar ta larabawa sam_sam ba ta wa ni burgeshi.






Kyakykyawar yarinya ce sosai doguwa bata da jiki sosai, za ta kai kusan 22 years,





Tana riƙe da hannunsa su ka shiga har cikin Babban parlon masaurautar,




"a'a lale marhabun da madeeha yau ku ne a gidan likita bokan turai???" Sitti ta ke tambayan madeeha.




"Eh Sitti ni ce wallahi, kin san munata fama da ma rasa lafiya, yanzu ma zuwa nayi, zanyi wa wannan yaron injection" ta faɗa ta na nuna Maan da ya tsanta,



Da sauri Maan ya waiwayo yana zuba mata ashe color ɗin idanuwansa, "tab lallai nayi sake "Maan ya faɗa yana k'ara haɗe ransa kamar bai taɓa dariya ba, shifa ya tsani raini wallahi.





Gently ya miƙe daga inda ya ke a zaune, ba tare da ya sake kallon wajen da su ke ba, dan ya lura da ga ita har Sittin sun raina shi.





Tafiya ya ke cikin kuzari irin na ingarman na miji, yana ɗan hadawa da sauri, akwai inda ya ke son zuwa saboda gobe ne za'a halarci taron su na Companyn Ammurh.




Wata siririyar hanya ya bi wacce za ta sada shi da da garden ɗin gidan, gently yake tafiya, ya na ɗan danna wayar da ta ke hannunsa, kafin daga baya ya d'auko Bluetooth ya maƙala a kunnensa.





Baifi 4minutes da tsayuwa ba wata mota ƙirar ferarri fara tayi parking a gabansa.




Sai da ya gama danne_dannensa kafin ya nufi motar, wanda yake ciki da hanzari ya fito ya buɗe masa motar, ya shiga su ka fita daga ɓangaren.





"Hahahahaha kakkausar murya mara dadin saurara naji ya na dariya, "Alhaji Saminu kar ka damu kanka akan wannan yaron, na faɗa maka sai mun ga bayansa daga shi har ubansa" cikin jin daɗi wanda aka kira Alhaji Saminu ya kalli abokin maganar tasa yana cewa "wallahi da sai nayi ɓarnar dukiyata, duk ranar da akace min mun hallaka yaron nan da ya tsone mana ido" .





"na faɗa maka karka damu nasan me za mu yi domin bani da wani buri daya wuce mu hallaka shi, yanzu a binciken da nayi, ance yaron baya ƙasar nan"




"Tabbas yaron nan baya ƙasar, shekaran jiya ya wu ce Asia"
"Ubansa fa?????"
wa ta murya da ban tayi tambayar,
"ai ubansa ba zai mana wahalar kashewa ba, nafi son na fara kama yaron da hannuna"


haka wa ƴan nan mutanen suka cigaba da hirar yadda zasu hallaka wani yaro.




A ɓangaren Maan bai dawo palace ba sai 10:30 ya shigo duk ya gaji, cause tun da ya zo garin bai yi tafiya mai nisa kamar wannan ba,





A partment ɗinsa ya wuce ba tare da ya jira Hamad ba, ya faɗa kan gadon sa, bacci ɓarawo ya ɗauke shi,



washe gari Maan ya tashi cikin shirinsa na zuwa taron da za'a gabatar a safiyar yau ɗin.





sanye ya ke da classic fit suit royal blue, ta cikin kuma sky blue, ya na sanye da necktile ash, ƙafarsa sanye take da black loafer shoe, sumar kansa ta fito sai sheƙi ta ke ya shafa mata, pomegranate seeds oil, yau adon na musamman ne, Maan ya fito a asalin halfcast ɗinsa, ka na ganin sa ka ga jinin larabawa, calmly ya fara ta fiya cikin jarumtarsa, ya nufi ɓangaren Sitti.






k'amshin turaren sa na versace eros su ka fara ji, saboda ko ba a faɗa mu su ba, sun san waye ya ke amfani da irin wa ƴan nan tura rukan.





Wurin jaddi ya fara zuwa, su ka gaisa, kana ya nufi gun Sitti, ya bata side hug, tare da ce wa "ni kam na fita"
"ba za ka tsaya ka ci abinci ba??"
"eh sai na dawo" ya faɗa ya na gyara zaman rigarsa,
"adawo lafiya mai gida" Sitti ta faɗa ta na waving hand ɗinta.





Land cruiser ɗinsa aka kawo masa fara, tare da guard ɗinsa da za su bishi don tsaron lafiyarsa, bai wani ɓata lokaci ba ya shige cikin motar sa, driver ya ja su ka nufi Sofitel Bahrain Zallaq Thalassa sea& Spa Hotel, domin a chan zasu gabatar da taron kafin zuwa Companyn su.





Sofitel Bahrain Zallaq Thalassa babban hotel ne aƙasar Bahrain wanda suke ji da shi a ƙasar domin ya na daga cikin ƴan farko_farko da ake lissafa wa a garin hotel ɗin yana tsakiyar swimming pool ne ya yinda sauran wurin ya ke zagaye da korayen bishiyu, da shuke_shuke iri_iri abun gwanin sha'awa da burgewa, ko a Bahrain ɗin ma in kai ba wani ne ba, ba ka isa ka ta ka wajen ba.





Slowly drivern Maan ya sa mu waje yayi packing, ya yinda duk wurin manya_manyan motoci ne na manyan mutane da su ka halarci taron, ko wa ya zo Maan kawai ake jira,walking slowly yafito daga motar ya na tafiya cikin ƙasaita ya fito hannun sa ɗaya cikin aljihunsa yana taku irin na jaruman maza.




yana shiga cikin hall ɗin gaba-ɗaya sai aka dawo da camera's ɗin kan Maan kowa yana so ya ɗauki rahoto, dan wannan shine first time da Maan ya halarci taron su a ƙasar Bahrain





Cikin haiba da kwarjini ya nufi cikin tsakiyar taron ya na ɗaga mu su hannu, yau fuskansa a sake ta ke ba kamar ko yaushe ba, loud speaker aka miƙo ma sa, cikin vocal voice ɗinsa ya ce "Assalamu alaikum warahmatullah ikhwani wa akhwati,aba'wal ajdad, ba'ada tahiyatul islamiyya,arhab bil jami'i huna" (bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci ina yi wa ƴan uwana maza da mata, iyayena da kakannina, ina yiwa ko wa barka da zuwa wajen nan) .




"la shay'i yaquduna ila huna, da'una faqat naj'al anfusana su'ada" (ba komai ne ya tara mu anan ba sai dan taya kan mu farin ciki)




" fadilan an taqadim musa'adat ɗari'ah li ikwanina min bashar Allah zina hum ad'ilun
an a'amal, du'una najma'a baynal quwwa walsulb linaraa, nahnu nusa'id shababul ad'ilun an amal,wakayfa maata aba'uhum lakad rahalu, wallazuna hasalu ala darajatul ilmiyat lam yahsalu alaamal" (mu bada taimakon gaggawa ga ƴan uwana samari wanda ba su da aikin yi, domin mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin mun taimaki rayuwar samarin da basu da aikin yi, da wanda iyayensu su ka mutu, su ka barsu, da wa 'yanda su ka gama degree ba su sa mu aikin yi ba).





"washaksa yaqif ala mustawal madarasatul sanawiya, ja'al jami'i ilayna lil taqyim" (da wanda su ka tsaya a ma takin karatu na sakandire, kowa da kowa ya zo domin mu tan tance shi) "ma'a idamil qiyamat bil amali ra'ee, ala ratib 1,000,000 dinar bahriniyyun, kullu shahrun ilam, ma'a ishtirakatihim 500000 kullu usbu'u Minal usbu'ah" (ku ma za mu ba su aiki mai girma, akan albashi ki manin dinare million ɗaya, a duk wata na duniya, a ko wanne sati na mako zamu ba su ki manin dinare dubu ɗari biyar na bahraini)



yeeeehhhh "Maaan" "Maan" "Maan" "Maaannn"
"wahazal rajul, wahazal rajul, shaksu minan nass ,nahnu nataqif nahnu nataqiff" (wannan shine mutum, wannan shine mutum, mutum ne na mutaneee mun yarda mun amince).



Gaba ɗaya gurin ya ɗauki sowa da ihu na samarin da suke wajen suka fara ihu suna kiran sunan Maan suna cewa sun yarda sun amince, haƙiƙa a cikin samarin dasu ke ƙasar Bahrain babu wanda zai ce bai san Maaan ba, musamman ma bahrain.




d'aga musu hannu Maan yayi alamun suyi shiru, gaba ɗaya sai suka yi tsitt su na sauraransa, slowly ya buɗe ba ki ya ce "amal ayuqalil haza min mu'idal biɗalat fi waɗani al Ummi????" (ina fata haka zai kawo cigaba da raguwar rashin aikin yi a ƙasar mahaifiyata???" )




"na'am,na'am" (eh ,eh) shine abinda mutanen da ya ke wurin su ke faɗa da sauri da sauri.




"ta'al wad'alaq sarahani sa'ati 10" ( kuzo gobe da k'arfe goma ku sameni)
"nujud" ( nagode)



Boom..... bommm...💣 boommmmm 💥

shine ƙaran wani abu mai ƙarfi da ya gigita wa su da ga mutanen, su ka tashi a firgice.........✍🏻💥



# zaku ga Ina using yare acikin novel d'in, to tsarin ne haka🙏🏻🙏🏻



comments &share





Oum Khalil✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


🍇 *ABDUL MANI*🍇

🍇 *TYCOON* 🍇


Story &Written


By


🍇@ashoush_💕

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*

# COMMENTS & SHARE

*FREE BOOK*

🍇 _Abdul Maneou_🍇

NOTE EDITED🚫
PAGE 21 to 22

________A ɗi mauce mutane su ka fara juyawa domin su ga abunda ya tada musu hankali, cikin zare idanu suka ha ɗa baki su na faɗin "Bomb" ihu su ka fara yi, cikin jarumta MAAN yace "kowa ya yi shiru akwai ma fitar da zan baku, ku ma ku kwantar da hankalinku"

Sauƙo wa ya yi daga steps ɗin da yake kai, ya kalli JOHN VICE P.A, a gefen sa, ya nace masa "open the ground door" shiru P.A ya yi domin sam bai gane wacce ƙofar ƙasa zai buɗe ba, gashi mutane sai hayaniya su ke, kallon MAAN ya ƙara yi tare da cewa " Sir ban......... " cikin tsawa da zafin zuciya MAAN yace "open the door below" ya faɗa yana yin ball da wata kujera da ta ke gabansa, cikin sassarfa ya nufi wani switch ɗin lifter elevator, cikin hasala ya danna abun, a take wata ƙofa ta buɗe,

juyowa ya yi, gaba-ɗaya yana kallonsu within 2second, da ƙarfi ya buɗe bakinsa yana ce musu "Akruj bi sur'ah wanzur" (kuzo ku fita ta nan da sauri) ya faɗa yana nuna musu wani k'aton elevator da akayi shi acikin ƙasa, buɗe wa elevator ɗin yayi domin yabi dasu ta ƙofar da take ƙarkashin ƙasa, shine hanyar da zaibi kawai ya kuɓutar da taron jama'ar da suke wurin.

Da gaggawa mutanen suka fara nufar elevator ɗin suna shiga yana sauke su ƙasa, ba kajin komai sai ƙarar harbe_ harbe da ta cika cikin Babban hotel ɗin da ƙarar tashin Bomb,
sai da yatabbatar duk sun sauƙa ƙasa sannan yace da Guard ɗinsa gaba-daya su wuce,

tsuru_tsuru su kayi suna kallonsa, ga ƙarar harbin sai matsowa take,
ƙarar Bomb ce taƙara tashi gini ya zubowa mutum huɗu acikin Guards ɗinsa, da zafin nama ya ƙarasa wajen yaɗaga musu ginin .

cikin tsawa da ƙaraji yace "i Said get the hell away from here" ya faɗa musu idanunsa gaba-daya sun kad'a sunyi jajawur farin idonsa yayi ja kwayar idanunsa kuma ta ƙara rinewa zuwa ash,

Jiki a sabule suka juya suna shiga cikin elevator ɗin John wanda shine a matsayin P.A yanzu tunda Babban P.A yana Nigeria ya matso zaiyimagana....shuuu.Fuuuuuuuuu ƙarar bullet ya wuce ta gaban fuskan MAAN kafin yaja baya a gaggauce.

cikin zafin nama ya hankaɗe JOHN, kana ya fizge shi da gudu suka shige elevator kafin yarufe ya barsu anan, elevator din yayi ƙasa dasu ta under ground,

koda Bandits ɗin suka shigo sai su ka ga kamar babu mutanen da suka gudana a wajen, kallon_kallo suka fara yi a tsakaninsu, kafin su girgiza kai suka sawa gun Bomb, suka fice da sauri don kar akamasu.

"shhh shhh shhh " shine karar sautin da yake fita daga bakin MAAN iska yake ta fitarwa ko zuciyarsa zata rage tuƙuƙin zafi da take, tafiya yake cikin zafin zuciya da haiba, domin har sautin takun sawunsa anajin yadda yake bada sauti dum dum dum ajikin kasa,

taka ta yake kamar a haka zai huce zafin zuciyarsa,
cikin palace ɗin ya shiga ba tare da ya amsa ko gaisuwar da Maids ɗin gidan suke masa ba,
side ɗinsa ya wuce kai tsaye, tun daga bakin ƙofa ya fara cire kayan jikinsa yana watsi da su, kafin ya wuce bathroom ya sakar wa kansa shower yana sauƙe ajiyar zuciya,
"who is behind this????" yake tambayan kansa shiru yayi ya shiga tunane_tunane kafin ya furzar da iska mai zafi ya janye jikinsa daga ruwan da yake zuba ya kashe shower din ya fito,

a cikin ɗakinsa ya samu gaba-ɗaya Guards ɗinsa sun sunkuyar da kai sun hard'e hannayensu,

ko kallon su baiyi ba ya ɗauke kai ya wuce wardrobe yana jawowa wata mulk jallabiya ɗinsa ya ɗaga zaisa sa, sai JOHN ya ce "sir everything that happens isn't our fault, to protect your safety is our job, we will all give our lives for you"

Cikin kufula MAAN ya tawo wajensa tasss tassss ya wanke shi da mari idonsa yayi jajur,
"youre not serious JOHN, you're crazy, and you're going to be smashed" ya faɗa yana saka hannunsa cikin sumar kansa yana hargitsata, "unbelievable people have come to killed me, and you wanna ruined your life" ya faɗa yana nuna shi da yatsansa,

"get out immediately" MAAN ya faɗa yana nuna musu ƴofa, ƙin fita suka yi domin sun san yau ran ogansu ya ɓaci, kuma yanayin haka ne duk dan saboda ya tsare lafiyar su.

SADIO ne yayi magana "sir we are....... " MAAN ya d'aga masa hannu ya na cewa "i Said outtttttt"
fita suka yi gaba-daya daga ɗakin nasa jiki a sanyaye, suna fita yaja gajeren tsaki ya na gwada yanda JOHN yayi magana,
"Mtsww sir muna nan ne saboda muba da rayukanmu akanka" ya gama gwada yanda P.A yakeyi, kafim yace "crazy JOHN"

guads ɗinsa murmushi kawai su kayi suka girgiza kai suna jin abinda ogan nasu ya faɗa..........



🍇🍇
JIGAWA
JAKA

bayan tafiyar su Daddy cikin gida Baffa ya wuce ya sami Inna wuro yana ta faɗa, "a'a dakata Malam idan wa'azi kake sonyi sai kabari ai ga ƴarka sallamammiya tana nan zatayi sauƙar Qur'ani sai kaje kayi wa'azi achan" Hasse ni kike fad'awa haka?????".

"nafaɗa maka din uba na ne kaii???" ta faɗa tana aikawa da Baffa harara, jijjiga kai yayi yabar gurin domin shi sam bazai dake ta ba, wannan haramun shi kuma baya cikin maza masu dukan mata, ɓangaren sa ya wuce duk ransa babu daɗi,

"kedai kinji asara wallahi in banda lalacewa Baffanmu kike faɗa wa haka??? shiyasa ni ma bana ragar miki, muna zaune dake amma bamu san zuciyarki ba"
Labbo wacce ta shigo yanzu take faɗawa Inna wuro haka,

"ke... ke... dawa kike Inna wuro ta fafurota da takalmi aguje Labbo ta ranci takare tayi ƙofar gida har tana hankaɗe Umair wanda yake ƙoƙarin shigowa yanzu, har taso tayi wucewarta amma sai taga wani k'aton abu a hannun wannan gwaigwai ɗin da yake riƙe da hannun Umair,

haɓa ta riƙe tana kallon Farhan, kumatunsa ta ja tana latsawa, bige hannunta yayi yana

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment