Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai yanzu na lura da ƙyaƙyawan yaron da ya ke tare da su, da wani k'aton abu a hannunsa (iPad),



kallon su Ma'u nayi na ce zo ku ji, matsowa su ka yi dukkansu, kun ga wannan to ƴan uwanmu ne ..................✍🏻




Hahaha ni kuwa nace kai Labbo banda ƙarya dai.



Abdul_Mani........ isn't for free Contact to Subscribe.......07069793061 na kusa gama free pages..✍🏻



🍇🍇
Oum Khalil🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON* 🍇



Story & Written

By

🍇@ashoush_💞


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
# *PAID BOOK*
Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar 07069793061 ko ka kati a layin ,banda VTU


PAID BOOK
🍇 _ Abdul maneou_🍇


FREE PAGES 13to14

__________ƙallon su Ma'u na yi, "kun ga wannan to ƴan uwanmu ne"



kallona suka tsaya yi dan tunda suke dani ba su taɓa zaton ce wa ni ina da wasu ƴan uwa ba,



"gaskiya Labbo ke kam akwai ƙar...." doke wa Feenarh baki na yi, ina ce wa "amma kin raina min hankali ni ce nake miki karyar?????".



Feenarh dai ta na riƙe da bakin ta da ya fara jini saboda bugun da na ma ta, Ma'u cikin zuciyarta take ce wa "kai Labbo akwai mugunta wallahi" dan ta san ko giyar wake ta sha bata isa ta fa da agaban Labbo ba'




tsaya wa mu kayi muna kallon mutane ma su baƙaƙen kaya, wasu daga bayan mu ne su ke ce wa, "anya kuwa ba aljanu ba ne??? ku duba wannan baƙaƙen abu kamar yan iska"




dariya ce ta kama ni, ɗan ma ba su san me ya faru dani ba, a yammacin yau din nan, da Allah ne ya san irin daɗin da za su ji,




daga can na hango Baffana ya na tawo wa, shida wa su daga cikin manyan garin, ta gaban mu su ka wuce, ina ta jin daɗi Baffana zai ga ƴan bunni (Birni) su gaisa,




🍇🍇
ABUJA
ɓangaren Maan da ya samu dakyar Daddy ya ce ya na da meeting, dawowa cikin parlon ya yi fuska a sake, "lafiya kuwa????" Ammurh ta ke tambayan Maan, "lafiya kalau Ammurh, Meeting din gaggawa ne ya ta shi" ya fa ɗa ya na wucewa upstairs,



girgiza kai kawai Ammurh ta yi, dan ta san Maan ƙarya ya ke ba wani Meeting da zai hana shi tafiya inde ya yi niyar aikata abu, kawai dai ba ya son zuwan ne, "Allah ya shirye ka Sadauki" Ammurh ta faɗa,




not too long Maan ya shirya cikin wa ni notch lapel suit maroon, ƙafarsa sanye da monk strap shoe baƙi, kai da ganin takalmin kasan na manyan mutane ne, sumar kansa sai kyalli man "SOULFLOWER CASTO OIL" ta ke,




k'amshin AMOUGE PERFUM dinsa ne ya fara isowa, a ƙalla turaren zai iya kaiwa 120k, Maan ƙarshe ne wajen wanka ga kyau ga kuɗi ya fito a asalin TYCOON ɗinsa,




tun daga sauƙo warsa daga upstairs zuwa downstairs Ammurh taƙura wa Maan ido, domin ta san ɗanta ƙarshe ne wajen kyau, har yaƙaraso batare da ta sani ba, kiss ya sakar mata a kumatu, tayi mur mushi, "You looks so cute son" Ammurh ta faɗa ta na shafa kansa,




shagwabe fuska ya yi "Ammurh ai kin fi ni kyau matsalar" ɗan dukansa tayi "Sadauki ba ka ji" ta faɗa ta na jan kunnen da "auuchhh, Ammurh dan Daddy baya nan shi ne yau ake ja min kunne???" Maan ya fada tare da turo bakinsa gaba,



"eh din" cewar Ammurh, "ina kuma za ka je ne Sadauki???",




"Ammurh ASIA, akan companynki da wasu zasu saka hannun jari aciki, and uncle Zaid yana son a can ja sunan Companyn zuwa, ALI ZAID AL QURAYSHI AND BROTHERS (AZAQ)"


"ya kamata ace na hallarci taron saboda ayi komai a gabana, ina son ganin yadda tsarin kasuwancin yake, zan ɗauki sababbin ma'aikata, ya faɗa hannun sa rike da na Ammurh,



karku manta masu karatu Ammurh da Daddy a Saudiya suka haɗu har sukayi aure,



ASALIN AMMURH

Manama Bahrain is situate between Qatar and easterncost of Saudi Arabia,
Umayyah Ibn Salman Isah Al Khalifa, balarabiyar ƴasar Bahrain ce cikin garin Manama, basa jin wani yare bayan larabci, bayan duniya ta waye da kasuwanci ne suka fara garen turanci a ƙasar, Ammurh ita ce ta uku agurin sarki Salman Isah Al Khalifa, Sarkin ƙasar Bahrain, yana da Zaid, Umaimah, sai Ammurh wacce ake kira da Umayyah, sarki Salman Allah ya masa yalwataccen arziki mai yawa da albarka, babu wata hatsaniya irin ta gidan sarauta a k'asarsa, ƴaƴansa sunyi karatu har matakin master's, a wata shekara da suka je aikin hajji acikin garin Saudiya, suka hadu da Daddy a wajen ɗawafi, soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanin su, lokacin da sarki Salman yaji labari yaso yayi gardama akan auren, amma kasancewar lamari ne na Ubangiji sai ya haƙura yabari tare da sa musu albarka, ba tare da ƴan uwanta sun so ba, amma kasancewar Daddy yana da kuɗi kuma a lokacin yana kan kujerar president na Nigeria, suka amince da auren, yatafi da ita ƴasar Nigeriya, lokaci_lokaci Ammurh tana zuwa duba ƴan uwanta, bayan da ta haifi Bashar ma taje, kuma a lokacin ne Maalik Salman al Khalifa yayi murabus yabawa ɗansa Zaid, sun je har naɗin saurauta tare da Bashar, bata ƴara komawa ba sai after ta haifi Abdul Mani, su kaje ta ga gida,
Lokaci_lokaci yaran Umayyah suna zuwa suna ganin danginta a ƙasar Bahrain,



Wannan kenan





ajiyar numfashi Ammurh ta sauke, "to Allah ya kiyaye son ka kula sosai, ina gaida Sitti da Abhu"



"to Ammurh zasu ji Insha Allah" Maan ya faɗa yana mik'ewa tsaye suit din jikinsa ya gyara sannan yafi ta,



a compound din gidan ya halu da Sarina tana shigowa cikin gidan, sanye take da riga da skirt ƴan kanti ajikinta,




da sauri ta nufo gurin da ya ke, ya na ganin haka ya dauke kai tare da shige wa motarsa, Guard ɗinsa su ka ja motar sai airport, kasancewar private jet dinsa da zaiyi tafiya dashi P.A baya nan kuma shi baison kowa ya tuƙashi,


"yallabai wanne airport za mu je?"
"station" ya bashi amsa, badan drivern ya san Abuja airport station ya ke nufi ba, shi kam da police station zai kai Oga" ya faɗa kasa-kasa dan wallahi ogan su akwai izza,




not too long su ka isa Abuja airport station, ba da jimawa ba jirginsu ya d'aga sai ƙasar Asia (Bahrain)




lokacin da sauƙa a airport already Hamad Zaid Salma, Al-Khalifa ya zo ɗau kansa, kasancewar sun san juna sosai, Hamad Zaid Salman d'ane a wajen Maalik Zaid Salman Al Khalifa,




da sauri Hamad yaje ya rungume Maan, cikin harshen larabci ya ke magana "kaifa haluk akhi??"( yaya kake ɗan uwa)
"bi khair wa'afiya" (ina lafiya kalau) Maan yaba shi amsa,



hannunsa Hamad ya k'ama su ka wuce ta wajen dogarayen da body guards din da suka zo taryen jikan Maalik Salman, wajen wata jibgegiyar mota ƙirar Aston Martin blue, su ka nufa aka buɗe wa Maan ƙofa ya shiga su ka nufi Manama Bahrain,



cikin palace din su ka wuce direct kowa ya fito taryen Maan sai zube wa suke suna masa jinjinar ban girma, hannu kawai ya ke ɗaga musu, daga ƙarshe ma share wa yayi kawai, inda sabo sun saba da halin Maan na rashin son hayaniya da magana,



"Oyoyo Abdul" Maan yaji an rungume shi taba ya runtse ido yayi, "ya Salam"ya faɗa cikin ranshi tare da ɗan ju yowa kaɗan,



"surprised" budurwar da take gabansa ta faɗa,
ɗan sakin fuska yayi kaɗan cikin harshen larabci yace mata "Ifraad ke kam bakya girma ne?? ɗan cika ni kaɗan mu gaida sitti"
Maan ya faɗa sound so tired,



Hamad ne ya harare ta shima cikin harshen larabcin da ɗan faɗa_faɗa yake cewa "ki sake shi mana, bakya ganin da gajiya a tare da shi??" cika Maan tayi ta wuce tana zumɓura baki,



wuce wa ciki su ka yi, babbar masarauta ce wacce akeji da ita garin, ba iya garin ba, da duk faɗin ƙasar gaba ɗaya, design ɗin masarautar da gwala-gwalai aka ƙayata ko ina na wajen,




wani ɓangare suka nufa,
wani kyakkyawan farin tsoho ne zaune kan wata kujera ta alfarma, yana sanye da fararen kaya tass da alkyabba ajikinsa saman kansa kuma hirami ne irin wanda karabawa suke sa kawa,



kana ganin wannan kyakkyawan datijjon za ka hango kamannin Ammurh a tare dashi,



"lale marhabun da jikana Abdul Mani Ibn Ulfat" datijjon ya fa ɗa ya na miƙawa Maan hannunsa,



jikin tsohon Maan yafa ɗa ya rungume shi, tare da ce wa
"na yi kewarka sosai Jaddi" wanda aka kira da Jaddi ya yi murmushi tare da shafa kan Maan yana ce wa "muma mun yi kewarka kwarai da gaske",




"ina tunanin zanyi magana da Ulfat yabar min kai nayi maka aure anan"




cikin sauri Maan ya ɗago ya na kallon Jaddi din, zaiyi magana sai Hamad yace "Jaddi ai ba shi da Mata"
"Madeeha zan aura masa" Jaddi ya faɗa,




mik'ewa Maan yayi tare da ce wa "ina Sitti??""




"gani abayan ka mai gida na" yaji wata murya ta faɗa daga bayansa, juya wa ya yi yana kallon ta tare da kwaɓe fuska,




"kinga dai abunda mijin ki yamin daga zuwa na ko??"
"rabu da shi, kishi yake yi saboda zan aureka"
Sitti ta faɗa tana jan sa kan wata kujera suka zauna,


gaggaisa wa su ka ƙara yi, suna tambayarshi Ammurh da sauran ƴan gida, daga ƙarshe dai shiru ya musu, ɗan ya fara gajiya da hayaniyarsu,



"Hamad ka rakashi ɗakinsa ya je ya yi wanka ya shirya" Sitti ta faɗa,



mik'ewa Maan da Hamad su ka yi suna fita daga ɓangaren Jaddi,
bayan fitarsu Ifraad ta kalli Sitti "wallahi ni kam ina son Maan"



cikin zallar mamaki Sitti ta ke kallonta, Ifraad gaba ɗaya rayuwarta irin ta yahudawa ce, sam ba bu irin kunyar larabawa a tare da ita,



"ba ki ce komai ba Sitti" ta ƙara faɗa ta na girgiza Sitti,
"ki same shi ki fa da masa kina sonsa"..................✍🏻



kuyi manage da wannan ayyuka sun min yawa,




🍇🍇🍇🍇🍇

ABDUL MANI ISN'T FOR FREE............. CONTRACT TO SUBSCRIBED.......07069793061



OUM KHALIL✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON*


Story & Written

By

🍇@ashoush💞


# *PAID BOOK*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*

PAID BOOK

Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar 07069793061 ko ka kati a layin ,banda VTU

🍇 _Abdul maneou_🍇
SECOND TO THE LAST
FREE PAGES
15to16
________ƙirjin ta da ya buga ta dafe, dan ta san ko giyar wake ta sha, ba ta isa ta kalli idanuwan Maan tace ta na sonsa ba,



Sitti ta yi mata haka ne saboda taja mata cin mutuncin agun Maan din, to wallahi ita kam ba za ta fada ba,




tana ga ma faɗan haka a ranta, ta miƙe ta bar wa Sitti gurin Fuuuu ta fi ce,





Jaddi wanda ya ke jin abin da su ke tattaunawa ya bi ta da kallo, yana girgiza kai,





ɓangaren Maan lokacin da suka nufi side ɗinsu direct bathroom ya faɗa domin yayi wanka, jikinsa tsami_tsami ya ke masa,





band'aki ne babba, kayan cikin bathroom din gaba ɗaya golden ne, ya haɗu iya kar had'u wa, jelly soap ne ajere kala_kala irinsu dove,liril,himalaya, Nivea,medimix kallon su ya ke ɗaya ba yan ɗaya domin shi har yanzu bai ga irin sabulun da ya ke son wanka da shi ba, dayan b'angaren ya kalla
oaras and alps natural body wash ya gani,



ajiyar zuciya ya sauƙe yana dan sakan murmurshi kaɗan,


.

Subhanallah fatabarakallahu ahsaneel khaleeqeen,Maan ƙarshe ne wajen kyau, murmushin da yayi sai da dimple ɗinsa ya lotsa wanda nima mai rahota ban tab’a gani ba sai yau,




ɗaukan Soap din ya yi, ya nufi jacuzzi ya shiga, ya ɗauki kusan 30 minutes yana wanka aciki kafin ya fito





ɗaure da towel ya fito a ƙugunsa, hannun sa ɗauke da wani yana goge ruwan da ya maƙale a sumarsa wanda tafara ta ruwa, bayan aski da yayi kwana biyu da su ka wuce,






Hamad ya gani zaune cikin ɗakin ya na danna waya,





wuce wa gaban wardrobe ya yi, ya ɗauko black cardigan tare da trouser, ya juya kasancewar ana sanyi a garin, Hamad ya tsura wa ido ya na kallon sa for some minutes,





ta gefen ido Hamad ɗin yake kallon sa, yasan Maan ba zai taɓa saka kaya agabansa Shiyasa yake wani tsura masa idanu,




gyara zama Hamad ya yi tare ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin ya ɗauke kai daga kallon Maan





"wallahi ba zan fita ba sai dai karka saka kayan nan" yake faɗa cikin ransa




Zuwa Maan din ya yi, ya tsaya a kan Hamad kamar zai shige jikinsa, yana rike ƙugu,
.

.

dariya ce ta zo wa Hamad, amma sai ya yi fuska, slowly ya ɗago kansa ya na kallon Maan ɗin da ya yi kamar zai afko kansa,




"E baka da hankali ne wai???"
"eh" Maan ya bawa Hamad amsa,




bai fi saura taki ɗaya a tsakanin su ba, dan Hamad har ya na jin yadda Maan yake taka ƙafarsa,



"eh lalle yau na yarda kai din, ɗan kan uwa ne" Hamad ya faɗa ya na ture Maan zai wuce amma ko gizau bai yi ba,





kallon Maan ya yi tare da ce wa "dalla malam ni ka matsa min na wuce, gardi kawai" ya faɗa yana wuce ta gefe ya fice,




"shhhhhhh" Maan ya ja iska daga bakinsa kamar wanda ya ci barkwano, daga ƙarshe ya taune lips ɗinsa ya na sa ka kayansa,




shiryawa ya yi, ya fito, as usual turaren dolce&Gabbana ya fesa,
ya nufi wurin da yaga kayan marmari, grapes kawai ya ɗauka ya ci kaɗan sannan ya mik'e ya fito gently ya ke tafiya cikin jarumta,




gurin Sarki Maalik Ali Zaid Salman ya wuce, direct apartment ɗinsa ya nufa, saboda Hamad ya sanar dashi baya fada,



"Assalamu alaikum" yayi sallama cikin vocal voice ɗinsa tare da tsananin kamewa, "wa'alaikumussalam ibni" wata masa ta amsa masa sallamarsa tare da cewa ɗana,




zama ya yi kan kujera ya na cewa "Barka da war haka juhan" cikin harshen larabci duk su ke maganar kasancewar sam su basa jin hausa,




gaggaisa wa su ka yi ba tare daya kalli Ifraad wacce tun shigo warsa ya lura ta na kallonsa, ko gaishe shi ma batayi ba,



"Juhan aina Abhi???" ( Juhan ina Baba yake) Maan ya katse mu su shirun da su ka yi,





"huma fil gurfa, ta faddali awwalan" (ya na cikin ɗaki da fari dai mu shiga) cewar Ifraad,



"taharak min huna" (ki matsa da ga nan) Maan ya faɗa ba tare ya kalle ta ba, ta ma gama rainashi wallahi, "I will deal with you" ya faɗa a ƙasa_ƙasa,





wucewa cikin ɗakin yayi ba tare da ya jira iso daga gare su ba, domin ba shida shamaki da ko ina agidan,




akan wata Lord raffels Lion chair, ya same shi zaune irin kujerar nan ta sarakai wanda su ka amsa suna sarakai, ɗauke da ƙur'ani a hannun sa ya na duba wa,



"Masa'ul khair ya Abhi"( Barka da rana baba),






cikin mamaki Maalik Ali Zaid Salman yake kallonsa, dan baiyi zaton har ya ƙara so ba,





"mata sata'ati?" (yaushe kazo??)
"sa'a eud ƙariban" (ɗazu nazo ban jima da zuwa ba)
"ayna akuka???" (ina ƴan uwan ka?)
"akh wani bi'aman" (ƴan uwa na suna nan lafiya)




bayan sun gama gaisawa, gyara zama Maan ya yi, ya na ce wa "ana tahadas ilayk" ( ina son na yi magana da kai Baba),
"ana astami'i ilayk ibn" (ina sauraranka ɗana),





"lina tahadath an al a'amal" ( ina son muyi magana akan kasuwancin ne)
" na'am min aljayid, al tahadath an al a'amal altijariyah" ( eh gaskiya ne ya na da kyau mu yi magana akan kasuwancin sosai) Maalik ya faɗa ya na gyara zaman sa tare da cewa "akbaratni walidatuk anak satuwazif muwazzaf judud" (mahaifiyarka ta bani labarin ce wa za ka ɗauki sababbin ma'aikata),





"eh Baba, uhibbu aliyahtijaj ala dabi'at tahrukatihim"( eh amma Ina so naga yanayin motsin su tukun na)
"masha allah Ibn mafi mushkila, ta'al alaq nazrat wastamtiii binafsik" ba damuwa ɗana, gobe za mu je tare da kai, ka ga komai da kanka),





sun ɗau ku san 20 minutes su na magana cikin harshen larabci, da ga bisani Maan ya bashi hannu su kayi sallama ya fito,




sallama ya yi wa Juhan ya fito, sumui_sumui Ifraad tana binshi a ba ya, da ga ƙarshe ma sai ta kamo hannun sa ta riƙe, su ka ci gaba da tafiya ta na masa hira, shi dai "eh a'a kawai ya ke ce ma ta,




Garden ya nufa a chan ya samu Hamad zaune akan rainbow acapulco chair ya na zaune, ya na sana'arsa ta danna waya,




kujerar da ta ke kallon sa shi ma ya zauna, da Ifraad a gefensa, ta na ma sa hira ƙasa_ƙasa,



🍇🍇
JAKA

a ɓangaren Labbo bayan Baffa ya shiga gidan sun jima aciki suna ta zance kafin su fito gaba d'aya tare da daddy,




gurin motocin su ka nufa tare da ce wa "Baffa ya shigo suje ya nuna mu su gurin"




shiga Baffa ya yi cikin dari_dari dasu,



Labbo ganin haka sai ta ce "yara_yara sai anjimanku" ta wuce gun motar, P.A ya kalle ta ke ina zaki???"
"aaaaaaaaaa cikin wannan kumbon mana" ta faɗa ta na nuna masa motar,





"haba yarinya, ai anan zamu barki tunda kin kawo mu"




"aradun allah baku isa ba, ansha man ƙarya, wallahi sai kunje dani" ta faɗa cikin tsantsan tijara da masifa ta na ƙan ƙanta idanu,





"nidai bana son haka wallahi, haka kawai na zo tare da ku cikin wannan akwatu mai tayoyi, shine kake son min baƙin ciki gaskiya a'a wallahi"





kallon ta P.A ya ke, kafin yayi tsaki ya wuce cikin motar su ka fara ja da gudu_gudu,




Ita kuwa Labbo ganin ha ka sai ta zura da gudu ta ɗale bayan motan ta na rike abun saman, tana ihuuu "yeeehhhhhhh daɗiiiii, jama'a kowa ya zo ya hau wallahi, ta faɗa cikin dariya,





jin abinda ta faɗa cikin sauri gagararrun yara irin ta su ka fara ha yewa saman motan suna ife_ife,





haka su ka zo har ƙofar gidan su Labbon sannan suka dur,o sun cika gun da hayaniya,





Labbo garin sau ƙowa ta, take musu bamban motan ya ɓalle,



zaro idanu tayi tace
"Hai hande mi boni" ( yau na shiga uku na) ko tunanin me tayi sai kuma ta ɗauki Bamban da ya ɓalle ta nufi P.A wanda shi kaɗai ta sani a yanzu tana cewa "karɓi abunku ya ɓalle, aradu sam_sam bashi da ƙarko"



P.A ji ya yi kamar ya shaƙeta, lallai wannan yarinyan bata da hankali,



ya buɗe baki da niyyar magana sai Umair yaɗa ga masa hannu, alamun ya barta kawai,




hararan P.A tayi kafin ta matsa kusa da Umair ta na cewa "hajji ɗan bunni (birni) ya shunanka??? shunana Manal Muhammadu Ghaly ...............✍🏻




muje zuwa


🍇🍇
*ABDUL MANI IS NOT FREE BOOK CONTACT TO SUBSCRIBED 07069793061






OUM KHALIL✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON*


Story & Written

By

🍇@ashoush_💞

# *PAID BOOK*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*

PAID BOOK

Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar 07069793061 ko ka kati a layin ,banda VTU

🍇 _Abdul Maneou_🍇

LAST FREE PAGES

17to18

__________Kallon ta Umair ya tsaya yi shi kam kamar wani statue, sai da ta ƙara ce wa ya " ya shunanka???" slowly ya d'ago ya na kallonta da tsananin mamaki a tattare da shi.




Girgiza mata kai ya yi, ya na ce wa sunana Umair ba tare da ya miƙa mata hannunsa ba,



"Yauwa to shannunka (sannun ka) ta faɗa ta na hard'e hannunta a ƙirjinta,




Can kuma kamar an tsikare ta, sai ta ƙara ma tsawa tare da ce wa "ko mu je na nuna muku wurin,



Yaya Ado wanda ya k'araso gun, da sauri Labbo ta na ganinsa sum-sum ta shige cikin gida, dan ba ƙaramin aikinsa ba ne ya jibagata, a taron bilwudari (bil"adama) ɗin nan ta faɗa cikin ƙunƙuni .




A tsakar gida ta sa mu Baffa ya fito daga hanyar ɗakinsa, dan har ƙarfe biyar ta yi,



"Baffa! Baffa!! muje a nuna wa ƴan burni abun mana" kallon ta Baffa ya yi "Uwata ki zauna a nan ki jira ni, ina dawowa".



bayan fitan Baffa wurin petroleum ɗin ya fita ya nuna musu, tare da labarta musu yadda abun ya faru,





Already dama Daddy ya tawo da masu aiki, bincika gun aka yi, danyen mai ne na petrolleim, wanda idan aka ce za'a tace shi, aciki za'a fitar da, gas, kerosine, dizel, da sauran abubuwan da su ke cikin petrol ɗin, idan hakan ta kasance kuwa ba ƙara min dukiya zasu tara ba.





bayan da su ka gama ga nin wurin, a take aka fara za gaye wajen da wayoyi na ƙarfe,





Baffa ya buƙaci da su shi go cikin gidan sa su ci abinci sai suyi sallah, ba suyi gardama ba su ka shiga cikin gidan ɗauke da sallama abakinsu.





Inna wuro wacce take tsakar gidan, kacha-kacha da ita a guje ta iyo wajen su, tiɓi-tiɓi ta zube a gaban Daddy ta na wkasar gaisuwa,




Baffa da ya ke wurin wata uwar kunya ce ta kama shi, duk yaji ya muzanta, ɗauke kansa da ga gareta ya yi dan ya lura da yadda take kallon aljihun Daddy da Abba.





Ɓangaren Baffa su ka wu ce, su ka zazzauna a parlonsa.




Babban Yaya sai kallon gidan ya ke ,tare da mamakin irin yadda gidam ya ke a tsaftace duk da kasancewar sa gidan kara.




Zama su ka yi da ga bisani Baffa ya fito, baifi minti biyu ba ya shigo lauke da ƙwaraye na nono a hannunsa da naman zabi a soye





Agaban su ya ajiye musu tare da ce mu su "bismillah" shiru su ka yi, "dan Allah kuyi hakuri da wannan ku sa mu ku ci, na san kunfi ƙarfin wannan amm......." Abba ya katse ma sa maganar sa tare da ce wa haba dai zamu ci inshaallahu.





tashi Baffa ya yi, don ya ba su waje ko zasu sake su ci abinci gidansa,



cikin gidan ya nufa domin ya samu Inna wuro yabyi mata magana akan rashin hankalin da tayi ɗazu,






a rumfar awakanta ya savmeta a tsaye, kai tsaye ya nufeta "innn......." ko ƙarasa ambatar sunanta baiyi ba ta d'aga ma sa hannu, ta na hararansa "nasan me za ka ce ku ma wallahi yanzu na fara, haka kawai ga duka ga cizo, ɗan arziƙin da mubke sa rai za mu yi mu tafi birni tsabar baƙin ciki irin na gaunati ta biyo mu zata kwace"




kyaketa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment