Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalleta ba ya rankwashe ta akayinta tare da cewa "Shad'iya"(uwar yawo) wallahi kika kuma binsu gidansu sai jikinki yafaɗa miki"yayi gaba abunsa

taji rankwashin,har sai da idonta ya cicciko da hawaye,main parlon su tawuce" shalelen Daddy meyasa meki?"cewar aunty Bintu matar Baban yaya"hmmm ai kema kinsan ita da waye ai,waccen boss din ne mana amma sa maganar aure shine ya huce akanta"Umair yafad'a yana mik'ewa akan kujera" zo nan autar Daddy"Ammurh tafaɗa tana mata nuni da cinyarta, shafa kanta Daddy yayi, ya haura sama yabarsu anan,hira suga cigaba dayi har wani lokaci daga bisani aka kira sallar asr, kowa ya tashi mazan suka tafi masallaci su kuma sukayi ciki

koda Maan yakoma ciki alwala yaɗauro ya fita shima ya sami jam'i bayan an idar da Sallah a jere suka fito suka shigo cikin gidan,
"innalillahi Maan kyakkyawa ne na ƙarshe dama dai aureta" wata ƙawar Sarina ta ke fad'a, tana daga barrender dinsu Sarina, gyaran fuska Maan yayi kuma ya cire uban gashin kansa da yake tarawa, gashinsa kwantacce har bayan ƙeyarsa,ga sajensa ma yakwanta, saboda ruwan da yayi alwala dashi,jallabiya ce yanzu ajikinsa,yana waya har sauran ƴan uwan suka wuce suka shiga ciki,shi yana waje tsayuwar mutum yaji a bayansa bai juya ba yacigaba da wayarsa, bayan ya gama wayar yasata a aljihu,yana juyowa idonsa cikin na Sarina yafard'a,gyara tsayuwarsa yayi bai cire idonsa acikin nata ba "bari na ga ƙarshen rashin kunyarki"yafaɗa ƴasan mak'o shinsa, Sarina tayi saurin sunkuyar da kanta,dan bazata juri kallon ƙwayar idonsa ba,yana da kwarjinin da mace bazata iya tsaya wa tana kallon ƙwayar idanunsa ba, hard'e hannunsa yayi a ƙirji ya ƙura mata ido for some minutes sannan yadauke kansa"do you need something?"kamar daga sama taji ya jefo mata tambaya, shiru tayi masa, ta gefen ta yaraɓa ya wuce,dan ya lura kamar bata da aikin yi ne,bai tsaya a parlon Ammurh ba ya wuce ɗakinsa,bayan shigowar su Babban yaya matarsa yakira su zo su tafi "Fannarh taso mu tafi"taji aunty bintu na faɗa,raurau tayi da idanunta kamar zatayi kuka ta girgiza kai "A'a aunty kuje ni yau awurin Ammurh zan kwana"
"uhnm"aunty bintu tafaɗa dan tasan kwanar zancen,ƴarta dake hannun Fannarh takarɓa taja hannun Mabruk tana yiwa Ammurh sai da safe,suka fice sukayi gidansu.


bayan tafiyarsu Ammurh tace"jeki ɗaki ki ɗauko tsarabar ki da yayanki yakawo miki"mik'ewa Fannarh tayi ta je ta dauko tsarabarta, "Luxury abaya's ne guda biyar" dogayen riguna ne masu kyau, aciki ko wacce kalarta daban,sai jeweles da bangle's da perfumes, abubuwa kala-kala aciki sai murna takeyi abunta, har taman ta haushinsa da takeji,
mik'ewa tayi ta je ɗakinsa knocking tayi masa "come in" ya faɗa shiga tayi da sallama a bakinta,da gudu ta jeta rungume shi"yaya nagode sosai Allah yasaka da alkairi Allah yakara budi"shafa kanta yayi "ameen" yafaɗa yana jan hancinta,da gudu taɗara fita daga daƙin,jijjiga kai kawai yayi,yacigaba da danne_dannensa,
daganan ya kwanta abunsa baijira dawowar Umair ba

🍇🍇
JAKA..................


oumu khalil✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON*

Story &written


By

🍇@ashoush💕

*PAID BOOK*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
*PAID BOOK*
Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar 07069793061 ko ka kati a layin ,banda VTU

🍇 _Abdul maneou_🍇

FREE PAGES 9to10

*JAKA*
________ɓangaren Labbo kuwa sassafe na tashi, naje ƙofar gida ɓangaren da akayi tonon ruwan har a kasamu petrol, nake ƙarewa kallo "in bandama an raina mana wayo taya za'a ɗauke mana rijiyarsu zan gani ai" ina gama faɗa na juya cikin gida


A tsakar gida na zauna ina yan gunagunai, da naji motsi kaɗan zan tashi da gudu naje na leƴa, har sai da su Samha su ka fito naji nutsuwa ta zo min, kallona tayi "wallahi kin samu matsala yarinya" ta faɗa tana min dariya

"Eh naji koma miye" naƙarasa ina aika mata harara, tsintsiya suka ɗauko suka wuce wani ɗakin kara da yake gefe, suka share tass suka gyara

Ina zaune ina kallonsu dan ko tsinke bazan ɗauka ba, tunda dai rijiyar da na tono za'a kinkime a dauke, "kaji karya" Safiya ta katse ni tana zaro ido jin abinda Labbo ta faɗa

"Ke ki kama kanki ba dake nake ba" ai kuwa Safiya sai ta riƙe kanta tana cewa "na kama"
dariya Samha ta kwashe dashi "kinji kunya wallahi, gurin da baki san ma an tona ba, shine kike cewa wai harda ke"

idanu na ƙura mata kamar ina neman wani abu a jikinta, a zahiri tunanin irin muguntar da zan mata nakeyi,ni zata kunyata agaban su inna wuro "yau kinshiga ukunki"nake faɗa a cikin zuciyata,

ita dai taga ƙaramin bakina yana mul mul mul amma batasan mai nake cewa ba, tashi nayi ina karkaɗe zanina, sashin Baffa na nufa ina cewa "Baffa yaushe en birnin zasu zo wai?"ɗakinsa na leƙa baya nan,sai na wuce waje abuna,

shagon Halliru na nufa "a bani a lewa mai guda biyu" kallo na yayi yana cewa "wacce alewace haka?" kaga Halliru "wannan alewar fara daya a sama da guda ɗaya a ƙasa" dakyar Halliru yagane kwatance na yabani alewa na juyo gida,


a hanya na haɗu da Kaltume wace zan shiga wa fada yaya Ado ya kamani,

"Labbo! Labbo!!"
suka kira suna na, kallon su nayi "to ya akayi?" wata daga cikinsu ce tayi karfin hali "dama Kaltume tace wai kibata kudin.... " bata gama faɗa ba na doke bakinta, na juyo ina kallon Kaltumen " ke to naci dubu sai ceto, kinga wannan alewar aradu da kuɗinki na siya"

anan nayi tafiyata na barsu, sun kafe ni da idanuwa suna kallona har na bacewa ganinsu

a chan ƙofar gidanmu na had'u da Ma'u da Feenarh, da sauri suka nufo inda nake, tafiya na cigaba da yi, Ma'u tarik'o ni "haba Labbon Inna da Baffa, kiyi hakuri wallahi muma ba'ason ranmu muka gudu ba" "eh wallahi da gaske muke Labbo" ita ma Feenarh ta fada, haƙuri suka cigaba da bani "naji to na haƙura" yeeeh "kokefa shiyasa nake ƙaunar ki Labbo, baki da fushi" dariya nayi ni kam a dole ance bani da fushi "kunsan me??" "a'a suka haɗa baki" "yau ƴan birni zasu zo su tafi da rijiyar gidanmu" "kaiii haba dai??" "Allah wallahi, kuzo ma muje gidan, ku gani da idon ku" biyo ni sukayi muka tafi har cikin gidanmu, suka gaida Inna Muka fito, Inna wuro sai harara na take nikuwa yau bata ita nakeyi ba, wuce wa mukayi muka zauna wajen garken shanmu muna ta fira


"Assalamu alaikum Baffa yana nan??"
wani yaro yayi sallama, shareshi mukayi kamar ba muji ba, daga ciki safiya tafito da gudu
"waye??" tafaɗa tana leƙawa "kicewa Baffa ana kiransa agurin mai unguwa" ya juya yatafi koma wa safiya tayi, tana faɗawa Inna wuro ana neman Baffa, tsaki tayi "zoki wuce baza'a faɗa ba" ita dai Inna wuro bata goyon bayan abunda Baffa yake niyyar yi shiysa take ta bakin ciki tun daren jiya,


ko da naji abunda Inna wuro tace, mik'ewa nayi nashiga sashin Baffa da sallama abakina, a zaune na sameshi da ƙur'ani a hannunsa yana karatu "Baffa mai unguwa yana kiranka" "tohm uwata" Baffa yafaɗa yana mik'ewa, a tare muka fito dashi ya fita nikuma na koma gurin su Ma'u


🍇🍇
ABUJA
wajen ƙarfe 10:30 Maan ya farka daga baccin da yake, addu'ar tashi daga bacci yayi, ya miƙe ya shiga band'aki, wankansa ya silla fess dashi, ya d'aura alwala yafito

al'adar Maan ce baya zama babu alwala ajikinsa, ya saba da haka gaban wardrobe ɗinsa ya nufa, wata jiƙakƙiyar gezna ya ɗauko kalar sararin samaniya (Sky blue) sai sheƴi take da alamun ba'a taba sata ba ma, gaban mirror (madubi) ya nufa yayi shafe-shafensa, ya juya yasaka shaddarsa tare wrist watched dinsa ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa, ya feshe jikinsa da turaren royal blue, gently ya fito daga ɗakinsa, a hanyar parlon Ammurh suka haɗu da Umair "a'a mutum na mutane sadauki na Ammurh, you look so gogeous"
"thank you" Maan yafad'a yana miƙa masa hannu suka gaisa, shima Umair din gezna ce ajikinsa ruwan k'asa yayi kyau, shima ba baya bane wajen kyau, kasancewar duk da Ammurh suke kama,

Maan farar fata zai nuna masa da katon jiki, a tare suka jera,har cikin parlon
a saman dining suka samesu suna breakfast dan sun gaji da jiransu,
"Good morning Daddy" su ka gaida Daddy
"Morning,how was your night??" "Absolutely Good" suka faɗa a tare, Umair ya juya ya kalli Ammurh kema bari ayi miki yarenki "Sabahul khair Ammurh"
murmushi Ammurh tayi "bikhair mashaallah ibni"
Maan kam sumbatar ta yayi a kumatunta ya koma ya zauna, Fannarh ta saka masa fried potatoes da fried egg, sai tea, basa cin wani abu mai nauyi a breakfast, shima Umair zama yayi aka zuba masa, cikin natsuwa gaba ɗaya suke cin abincin,

bayan sun kammala Daddy ya kallesu, Bashar "yakira yace yafito yana hanya,kai Baba da Umair kutashi kuje wajen mota ganin nan zuwa" da sauri Maan ya d'ago yana kallon Daddy Jin ya ambaci sunansa, ganin yadda Daddy ya ɗaure fuska yasashi yin shiru.

mik'ewa sukayi shida Umair Ammurh tana musu "adawo lafiya"

a waje Daddy yasamesu suna jira, Maan ya ɗaure fuska kamar an aiko masa da saƙon mutuwa

ringing din waya ne ya katse wa Daddy maganar da yake niyyar yiwa Maan, ɗaga wa yayi, he take almost 10minutes yana waya, daga bisani ya kalli Maan "kana da meeting yau dasu dr.poll sai ka zauna ku tattauna Insha Allah next time zaka je kaga tsarin yanayin aikin.

Maan kamar amma sa bushara da gidan aljanna, da sauri yafito a motar yana zakud'a kafaɗarsa tare da d'agawa Umair hannu, "Safe trip bro" sanna yaje yayi hugging din Daddy ya wuce, cikin motar Daddy ya shiga
gateman ya buɗe musu gate driver ya cinna hancin mota kan kwalta zuwa Airport.

lokacin da suka isa anyi settling din private jet ɗinsu shiga kawai sukayi jirginsu yad'aga sai Jigawa state


Within 40 hours private jet ɗinsu ya sauƙa a Dutse International Airport (ICAO)

daga government house aka ɗauki motoci aka tare su, kasancewar Governor Aliyu Ulfat ƙanine ga Daddy, babu ɓata lokaci suka isa gidan His Excellency A Ulfat (Abban Sarina) yana da mata biyu d'aya a Abuja ɗaya a Jigawa

Hajiya Rahma itace matar Aliyu ta biyu yaranta biyu Farha & Farhan sa'anun Fannarh neh,

Sun samu tarɓa ta mutunci a gurin Hajiya Rahma, abubuwan ciye-ciye a kawo musu kala-kala sai da sukaci sukayi Nakk sannan sukayi sallar zuhr, suka ma shirya domin hanya
suka ma hanya


"Yaya Umair dan Allah zanje nima" "yeah nima zanje" Farhan ya karɓe maganar Farha "A'a kuyi zamanku akwai gajiya a hanya" "Please yaya dan Allah??" "okay to sai dai muje da Farhan, next time idan Maan zaije sai yaje dake ko?" ya ƙarasa yana kallon Farha, "a'a ni wallahi yaya Maan bazai je dani ba zaiyi tafada a hanya tafaɗa a shagwaɓe" shik kuwa Farhan sai gwalo yakeyi Mata, da kyar Umair ya mata wayo ta haƙura,

Daddy yana shigowa gaba ɗaya suka miƙe har Babban yaya wanda yaƴaraso yanzu daga gidan abokinsa,

Babban Yaya ne ya kalli Daddy yace "Daddy ba a jet din zamu je bane??"
girgiza kai Daddy yayi
"A'a Bashar kasan ƴan ƙauye ne a garin, kar su tsorota da mu" Umair da yaƙaraso hannunsa rike da Farhan yace "Daddy Maan yace ya turo guard ɗinsa da suke COMPANYN TRIACTA NIGERIAN LTD"
bai gama rufe bakinsa ba wasu jibga-jibga motoci suka fara shigowa, wanda zasu iya tafiya a sahara, AVANZA ƙirar Toyota, P.A ne ya fito yana cewa Daddy "Oga ne ya turo su" shiga motocin sukayi suka ɗauki hanyar Kiyawa Jaka......



🍇🍇
Oumu Khalil✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI🍇*
🍇 *TYCOON*



Story& Written

By


🍇@ashoush_

*PAID BOOK*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*

# *PAID BOOK*

Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar 07069793061 ko ka kati a layin ,banda VTU

🍇 _Abdul Maneou_🍇

STILL FREE PAGES
1️⃣1️⃣ to1️⃣2️⃣

___________Motocin da Maan ya turo mu su, gaba ɗayan su, su ka shiga, su ka kama hanyar Kiyawa Jaka,


*********************
🍇🍇
JAKA

bayan Baffa ya isa wajen Mai Unguwa, ya yi sallama su ka gaggaisa da jama'ar wajen, ya sa mu waje ya zauna,



Mai Unguwa ya yi gyaran murya "Malam
Muhammadu Ghaly (Ard'o) na kira ne domin na ƙara tuna maka, yau mutanen da na ba ka yanki da cikin gonarsu za su ƙaraso, ɗuk batun dai, bai wuce akan albarkatun ƙasa da aka samu daga ƙofar gidan ka ba, numfasawa ya yi kaɗan, ya ƙara cewa "abinda na ke so da kai kar ka damu idan sun bukaci filin su, to ka da ka yi gardama ka ji?"



Ard'o da kansa ya ke sukunye har yanzu bai d'ago dashi ba, sai da mai unguwa ya kuma ce wa "akwai wani fili na, da yake can gaba da na ku sai ka koma can, idan har mutanen sun bukaci ka ta shi" kallon mai unguwa Addu'o'in ya yi yana miƙa masa hannu "nagode sosai, bari naje na sanar da mai ɗakin na wa yadda mu ka yi, su kuma Allah ya ka wo su lafiya" ya faɗa cikin hausar sa da bata gama ƙwari ba,



bayan fitar Ard'o Mai Unguwa ya jinjina kai cikin jimamin ta shi Ard'o da za'ayi agidan,



hakan sam bai masa dadi ba, da ma sauran mutanen garin da su ke fadar mai Unguwar,




Lokacin da Ard'o ya dawo gida, kai tsaye b'angaren sa ya nufa, ba tare da ya amsa sannu da zuwan da Samha take masa ba,



gaba ɗaya yana cikin yanayi na alhinin zuwan wannan ranar, amma to ya zai yi tunda ba filinsa ba ne, ya za ma dole su tashi,


"Assalamu alaikum" Samha ta yi sallama ɓangaren Baffa, ɗagowa Baffa ya yi yana kallon Ƴartasa,



"Wa'alaikum mussalam" ya amsa ma ta ya na mata nuni da inda zata ajiye yar langar da ta ke a hannunta,



"ki ce da Innarku ina nemanta, ki fadawa Inna wuro ma "to Baffa" Samha ta amsa ta na barin ɗakin,


a hanya ta haɗu da Inna, ta sanar da ita Baffa yana kira, ta wuce sashin Inna wuro don ta gaya mata,


"Salamu alaikum" shiru ta ji ba'a amsa ba, sai taƙara ce wa "Assala ...."
"ke dallah rufa mana baki" Inna wuro ta katse ta, ce maki nayi ban ji Sallamar ba ne, za ki cika mi ni kunne, ta ƙarasa faɗan maganar ta na hararar Samha,


ta rasa gane me yasa Ƴaƴan A'isha su ka fi nata kyau da haske bayan ubansu ɗaya,


"kiyi haƙuri Inna, da ma Baffa ne ya ce a kira ki" Samha ta faɗa ta na sunkuyar da ƙanta, dan ita wallahi sam ba ta iya wannan hayaniyar da su Labbo su ke yi ba,


"ina uwar ta ki??" Inna wuro ta katse mata tunanin da ta ke, cikin rawar baki Samha ta ce, ta...ta..taaa wuuce gaba"


"mtsww wannan ai munafurci ne, akan me ba za ki zo ki fada min ba, sai da ki ka gayawa uwarki" Inna wuro ta fara bambamin faɗa,


Labbo da take zaune ita da su Ma'u suna ta dukan wani ɗan Taure suna dariya tafara jiyo hayaniyar Inna wuro,


"ina zuwa" ta cewa su Ma'u da ɗan gudunta taƙara sa shiga gidan, daga nesa ta hango yadda Inna Wuro take ta nuna Samha,


"meyake faruwa anan din neh??" Labbo take tambaya tana tana isowa wurin,


"uwarki ce take faruwa" Inna wuro ta bata amsa, "a'a dakata, a gaskiya nifa bana son wasan da babu dariya, ya dai da zagin iyaye, a'a wallahi gaskiya karki ƙara,ahto"
Labbo ta faɗawa Inna Wuro haka tana ɗaga hannunta tare da cuno bakinta gaba,


"yoo miye laifin Addah anan??? nidai banson haka gaskiya a gyara" nafada ina ta harare_harare, Samha ta jawo hannu na "zo mu tafi, "a'a Adah kedai cika hannun na tambaye ta dalili"


jana Samha tayi muka bar gurin, Inna wuro sai bala'i takeyi,dama idan banyi mugun hali ba, ban cika yar gidan A'isha ba,


sai da tagama zage_zagenta sannan tayi ɓangaren Baffa,


a tsakar parlo ta sami Baffa da Inna,harara ta aikawa Innan mu tana cewa "Allah wadaran naka ya lalace,Yara gaba-daya babu tarbiyya" kallon ta Baffa yayi sannan yaɗauke kansa,dan yanzu ba wannan ne a gabansa ba,



gyaran murya Baffa yayi, sai da yafara musu nasiha, sannan yace "dama na taraku anan saboda na sanar daku, yau mai wannan gurin zaizo, idan yabuƙaci mu tashi zamu ta shi mukoma gaba da nan chan filin mai gari,



"kutmarrrr in an isa shegiya nake, wanne tsinannen ne zai tashe mu anan???? a'a wallahi da sake" sunkuyar dakai Inna tayi " wai kekam lafiyar kuwa??" Baffa ya tambayi Inna wuro daga faɗa Miki abu, sai kihau zagi??? ki kiyaye bana son haka, kutashi kutafi" Baffa yafaɗa sam ransa babu dadi,


koda Inna wuro tafito zahe_zage take tayi, ita wallahi bawani ɗan iskan da zai fitar da ita agidan nan, sai da a kaga zasuyi kuɗi,sun tara tattalin arziƙi sannan ace su tashi, bazata saɓuba bindiga a ruwa,


Inna kam ɓangaren ta ta nufa tana kiran sunan Samha, domin su ɗan tsince takarcensu, da babu yawa,



**********************


ɓangaren su Daddy koda suka shigo Kiyawa,wata hanya suka ƙara nufa, ko kwaltar arziki babu a hanyar burji ne gaba ɗaya,



Umair tun yana hira da Farhan har yagaji yayi shiru dan wallahi, idan motar ta ɗanyi tsalle har kansa buguwa yake da saman motar, Farhan dai yayi shiru baya cewa komai.



Daddy dai mamaki gaba-ɗaya yagama kashe shi dama akwai irin wannan hanyar acikin wannan ƙasar??? yake tambayan kansa, shidai Babban yaya baya cewa komai, dan indai irin wannan hanyar ne yasa ba dasu,



after 2hours
daga dutse suka isa cikin garin JAKA, garin ko ina korayen ciyayi neh, da shuke_shuke abun sha'awa,


tunda suka hango manyan motocin AVANZA,
Yara suka fara gudu kowa yana ta kansa domin ya tsira da rayuwarsa, yau ƴan bille kai sun shigo garin, sai gudu ake Manya da Yara, domin wannan sabon abu ne a wajen su,

"miye yafaru???" Labbo wacce tarako su Ma'u hanya take tambaya,
"yan bille kai neh suka shigo" zaro idanu nayi kamar zasu fado ƙasa,
"ta ina sukayi???"
"ta chan gurin ne" yaran suka faɗa suna gudu.



hannu na ɗaura akaina "wayyo Allah shikenan mun banu mun lalace, mu gudu nace wa su Ma'u" aikuwa kafin nagama rufe bakina, gaba ɗaya suka runtuma da gudu, Ma'u kam har tafara ɗigan fitsari, muna cikin gudun muka haɗu da motocin su Daddy,



"Wayyo Allah gasu nan wallahi" Feenarh ta faɗa suna yin reverse suka juya baya da gudu, ni dai naƙame ko motsi na kasa yadda kasan shuka ni akayi, yau tawa taƙare,



wani guri suka samu sukayi parcking,
kallon garin Umair yakeyi kowa ya watse babu kowo, tun shigowar su garin ya lura ana gudu, koda suka tambayi wasu Yara inane gidan mai garinsu sai suka fece da gudu,



kallonta Babban yaya yayi da kyau, from head to toe, farar yarinya ce agabansu mai dogon hanci, fuskarta V shape ɗaauke da ɗan mitsitsin bakinta, gashinta a kwance lub_lub har gaban goshinta, ɗagowa yayi ya ƙurawa fuskarta ido,yana kallon blue eyes dinta yana ƙara mamakin kyan yarinyar a wannan ƙasurgumin ƙauyen,



an ɗau kusan minti biyu babu wanda yayi magana, Labbo babu adduo'in da batayi, kulhuwallahu ahadu,.....wamin sharrin gasikin iza wakaba, me Farhan zaiyi Inba dariya ba, wayarsa ya ɗauko yafara ɗaukanta video,




"Uhnmm uhnm" Daddy yayi gyaran Murya, yana matsawa kusa da ita, wayyo innahu min sulaimana,,wa innahu......tsiiiiiiii naji wani abu mai ɗumi yana biyowa ta sawayena,



tsugunnawa nayi a kasa na rike ƙafafun farin Babban mutumin da yake gaba na, "dan Allah Oga kayimin rai, wallahi kaina ko naira biyar bazaiyi, ba shi da nauyi kajiko??? gum gum shine ƙarar buga kanta da tayi wai dan Daddy yaji Fanko ne ya haƙura ya ƙyale ta,



murmusawa Daddy yayi sai yanzu ya fahimci nufin ƴan garin na gudun da suke, wato sun zata ƴan yankan kaine, shine suke gudu, tab lalle akwai aiki agabansu,


ƙara matsowa Daddy yayi yasa hannu yariƙe ni,
"dan Allah Alaramma Alhaji Malam kamin rai" nafadɗa ina ƙara fashewa da kuka ina matse k'afafuna, kar futsari ya zubo, ina ta nadama abinda yasa banbi su Ma'u ba, dan Annabi da Annabi kuyi haƙur,



"Mtsww" P.A yaja tsaki yana daka mata tsawa,
"hey shut your mouth off" yafaɗa yana zare mata jan idonsa, kama bakina nayi ina ɗaga masa kai, banma san me yake faɗa ba, nayi jaga_jaga da fuskata da hawaye ga gumi, kallo na yayi da kyau sannan yace "gurin mai gari zaki nuna mana, mu baƙi ne munxo mudu ba gidan Malam Muhammadu Ghaly (Ard'o)"


shiru nayi ina zare idanu,sai yanzu fa na tuna Baffa yace zamuyi baki ƴan burni (Birni) kallon sa nayi nace "kune wanda zaku kwarfi man fetur??" jijjiga kansa yayi, aikuwa sai na kwashe da dariya har ina tsugunnawa ƙasa, na taso na miƙawa P.A hannu mu tafa,kallona
yakeyi da jan idonsa, sai nayi saurin ɗauke hannun na maida baya,



kallona gaba ɗaya suke yi da alamun tambaya
"anya lafiya ta kuwa???"


bayan na tsagaita da dariyar na kalli baƙin basamuden da ya ke gabana, (P.A) "kashh wai kune dama??" jijjiga kai kawai P.A ya yi, su dai su Umair ikon Allah kawai ya ke gani,


"ware dillan ( kuzo mutafi)" na faɗa ina kallonsu "ki zo mu shiga can" P.A ya faɗa ya na nuna min mota,


"a'a idan na shiga shegiya na ke" na faɗa ina murguɗa baki tare da zare idanu, shi ma zare mun ido P.A ya yi, dariya na yi ina wurga hannaye na gaba, "mu je kawai da wasa na ke ni ma" na faɗa ina washe musu bakina, motocinsu su ka koma gaba ɗaya, ni ma nabi bayan wannan baƙin mutumin, gaban abunda ya kira mota ya kai mu, na tsaya ina shafata, ƙofar motar na riƙe ina ja amma taƙi buɗewa,



kallonsa na yi "to ka ce mata ta buɗe min na shiga mana" zagayo wa ya yi ya buɗe min murfin motar ya ju ya, sai da na shafa kujerar na zauna ina takure jikina,



kwatance na fa ra musu muna bin hanya-hanya, mutanen garin sun fara fitowa daga maɓoyarsu, don har labari ya kai musu ƴan birni ne suka zo, ana ta bin motar da gudu,


a can kwanar gidan Mai Unguwa na hango su Ma'u, ta window na zura kaina, na ɗaga hannu na, na daki ƙeyar Feenarh ina ce wa "shegiya na dawo na zauna" kallon gefe na na yi na ga wani mai bindiga, haƙuri na bashi ina dariyar yaƙe na ka ma bakina na riƙe,



"yauwa mun zo" na faɗa ina kiciniyar buɗe murfin ƙofar, abun buɗewar na samu na banƙareshi har sai da ya karye, na zare idanu, ta window na duro da abun a hannuna, P'A na ga ya za gayo ba shiri na wurga abun, da hanzari na matsa kusa da su Ma'u, ina ɓoye hannu na a bayana, shi kam bai ma lura da ni ba,



kansa a sama shi da sauran mutane ma su irin kayansa, suka je suka tare ko ina na ƙofar gidan mai gari,


a hankali Daddy da Abba suka fara fitowa, sai Babban Yaya da su Umair, da sauran abokan tafiyarsu, su ka shiga gidan Mai Gari,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment