Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarfata

kallonsa tayi tare da cewa "saukar yaushe?"
ta shi yayi ya mik'e tsaye ko kallon inda take baiyi ba,a cewarsa ai taraina shi ma shiyasa take masa wannan tambayar

ɗaki ya shige abunsa yabarsu anan ita da Umair


taji haushi sosai abunda Maan ya mata agaban yayansa, tashi tayi tafita ko sallama batayiwa Umair ba shi kam ko ajikinsa wayarsa ma yadauke yakira iraj suke ta hiransu kafin ya tashi ya koma d'aki achan ya sami Maan ya kafa ido akan laptop dinsa yana ta dannawa

waje ya samu ya zauna yacigaba da wayarsa
chan a bangaren iraj kuwa kwance take akan gado tana waya da Umair
"sweetheart wai yaushe zaka turo ne? Abba yayi min magana d'azu" "karki damu Baby surprising dinki nake so nayi"
"amma very soon kin kusa ki zama ta Umair Ulfat" yaƙara sa yana murmushi mai sauti

ɓangaren Maan kuwa gaba d'aya wayar da yayan nasa yakeyi ta dameshi ya sa karamar yarinya a gaba sai wani zance yake mata ,dan karamin tsaki yaja mara sauti amma duk da haka sai da Umair ya juyo ya kalleshi
"Babyna sai da safe i love you Ummuaah ya kashe wayan"

kallon Maan yayi yana nazari sannan yace" kaii Maan of the people dawa kake??"
"Allah yasa bada iyalina kake ba"yakara jefo masa tambaya ,ko kallonsa Maan baiyi ba,
ta sowa yayi da sauri Maan ya nufi ƙofa yana masa gwalo yabar d'akin
da sauri Umar ya biyo shi
"tsaya wallahi kafad'a min da Auntynka kake kowa" tuni Maan yayi gaba abunsa

d'ayan dakin yakoma
chan ma agyare yake komai tsaff kamar mutum yana kwana aciki
anan ya tub'e ya shiga bathroom ya watsa ruwa yafito yabi lafiyar gado ya kwanta .......


asuba ta gari Maan

🍇🍇
*kauyen Jaaka*
da sassafe inna wuro ta tashi tana fad'a wallahi ita an mata sata dan haka dole ita afuto mata kud'inta ko aga masifa da bala'i

ba wanda ya kula ta sai Labbo wacce tafito da buta a hannunta zata je band'aki
da gudu tayi kan ina wuro
"gashi nan "gashinan"
wallahi ta bangajeta tayi band'aki da gudu

Inna wuro salati ta rabka "innalillahi wa'innailahi raji'un Aisha ita da ƴaƴanta zasu kasheni"

safiya ce kawai tafito kasancewar gaba d'aya ta aurar da ƴaƴanta mata sai safiya da ado

"Inna wuro mai yafaru" safiya ke tambayar ta
fyace majina tayi a zaninta sannan tace "wannan shegiyar ce wanda uwarta ta tsine mata ce ta ke neman kash.... "aa dakata dakata" Labbo ta katse ta wanda yanzu ne take fitowa a band'akin

"a yaushe ne kikayi da inna ta cewa ta tsine min?"
"aa gaskiya njfa bana son haka karki sake"
nafada ina d'aga mata hannu

haba "wata babba dake anma kice wai antsinemin"

kallona safiya tayi
"gaskiya baki da mutunci Labbo ki bigeta sannan bazaki iya bata hakuri shegiya mayya er gidan matsiyac...tasss na wanke mata fuska da mari

" a hya"yayi"( baki isa ba ) wallahi kekam ki zageni na kyale ki

rankwashina naji anyi akai
cikin bala'i na jiyo zanyi masifa naga Samha ce fuska daure take kallona
"ki wuce d'aki yanzun nan" tafada a tsawace

"cikin gunguni na wuce d'aki ina zage_zage k'asa_k'asa karta jini dan wallahi duka zata min

"inna wuro tashi dan Allah kiyi hakuri yarinyace bata da hankali" Samha tafada ta na mik'a hannu zata d'aga ta buge hannun
"Aa wallahi karki tab'ani bansan me kika shafo ba karki gogan bala'i a jikina" tafada tana matsawa gefe

girgiza kai Samha tayi tana cewa allah yabaki hakuri sannan ta wuce murhunsu domin ta had'a musu karin kumallo

tuwon da suka ci na dare ta samu guntun tayi musu d'umame
jikin saniyar baffansu (Ard'o) taje ta tatso nono ta dashi sannan ta zuba a kwarya
ta zuba kowa nasa

na inna wuro ta d'auko takaimata
"inna wuro ganaki na kamalla"
"ajiye shi anan irin mayu kar muje muci guba dama so ake mu mutu aci gado"

Samha batace komai ba ta girgiza kai ta wuce d'akin Innarsu

a dakin Innarsu ta sami Fadwa tatashi sai kuka take Labbo kuwa tana zaune sai d'ige d'ige take ita a dole kwalliya take

" yarinya mik'o abinci a bawa Fadwa" inna tafad'a a kunyace saboda Samhan y"ar farice kunyar fulani take mata

abincin ta mik'o suka zauna sukaci sukayi nakk bayan su gama ne Labbo tace tatafi gidan su Ma'u adawo lafiya Inna tama ta itakam tayi gaba abunta

a Chan kwanar gidansu Ma'u ta had'a da Fatsume ai da wani mugun gudu da Banka k'ofar gidan su Ma'u tashige
suna tsakar gida
Ma'u ma ganin abokiyar shirmenta ta shigo da gudu ita ma ta kwasa sukayi d'aki a guje

Iya ta girgiza kai " Allah ya shiryeku"


a cikin daki ne sun b'uya a bayan k'yaure Ma'u tace "ke wai miya faru ne tana zare idanu"

dariya Labbo ta kwashe da ita sannan tace ke " Fatsume bala'i nagani fa"
" kinsan wallahi ban shirya dambe yanxu ba"


"tsaki Ma'u tayi wallahi Allah ya isana "
ke "yanxu duk gudun nan akanta ne"?

sai kuma ta fashe da kuka "wallahi nidai kin cuce mu mai yakai ki takalo mana Fatsume"

"yo k'addara mana"
kedai yanxu kikawo shawara yadda za'ayi da ita" inji Labbo

to "muje gidan su Feenarh muji yadda za'ayi..................








oumu khalil✍🏻🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON*


story & written


By



@ashoush_💞

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*

*PAID BOOK*

Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar 07069793061 ko ka kati a layin ,banda VTU

PAID BOOK

🍇 _Abdoul maneou_🍇

FREE PAGE 5to6
_____________Fitowa mukayi daga cikin ɗakin Iya muka sameta a waje
"zamu je mu dawo" adawo lafiya ta mana muka wuce lokacin da nazo fita daga gidan sai da na fara leƙawa waje saboda kar Fatime bala'i ta maƙale a ƙofa muna fita da riƙe mu ba shiri, da na leƙa na tabbata ba kowa, sannan na fito ina cewa Ma'u ke fito ba kowa fa,
muka kama hanyar gidansu Feenarh a hanya sai tsalle_tsallenmu mukeyi har muka isa k'ofar gidansu,
bulo na ɗauka na wurga cikin gidan nasu ,na kuma daukan wani na daki ƙofar gidan dashi,.

saiga Feenarh tafito da sauri"ke wai meyake damunki??" duk sanda kika zo da jifa ne zan gane kin iso?" tafaɗa tana tambayata
kallon tara saura kwata nayi mata sannan nace " so kike na shigo wannan mugun yayan naki ya dake ni ko?"nima na bata amsa ina tambayarta
"gaskiya yayanki akwai mugun hali gareshi" ina bata fuska nafaɗa dan har zuciyata yayanta mugune ,kallo na tayi bataji daɗin abunda nace ba, na kalleta nima nace nafaɗa,nikam
kuzo mutafi majalisar cin amana muyi shawara achan cewar Ma'u

tafiya mukayi Chan wani waje da ake cewa majalisar cin amana muka shige wata 'yar bukka mu ka zazzauna a ƙasa Feenarh ta kalleni tohm yanzu mai za'ayi ,
gira d'aya na daga nache" oho"
Ma'u tayi saurin kallona "gaskiya ke dai ƴar iskace ya ma za'ayi wai kice mana oho"
Feenarh ta ƙarbi zancen da cewa "nikam ina ga kawai zanje nabawa Fatime bala'i haƙuri kawai in yaso ta daken a wuce gun inb......"kan bala'i idan kin isa shegiya nake ,kuce bani bace jikar A'i "
na katse wa Feenarh maganarta ina ta hura hanci ni a dole ta ɓata min rai
"dallah kutashi mutafi anfasa sulhun ,dan halak kafasa" na fita a fusace amma sai nayi turuss saboda ganin Fatime a gabana tana kallona bata rai nayi zan wuce ta jawo rigata kiiiii tadawo dani baya ta na cewa "ke dawo nan "
"ba ruwanki dani ban shiga harkarki ba"nafaɗa mata haka,
wata dariyar rainin hankali ta shek'e da ita "wallahi yau kwananki yak'are domin kuwa sai na ci ubanki la'ada waje" tafada tana kara finciko rigata,
karar gudu naji daga bayana ina juya naga su Ma'u ne suka arce suka barni,,
"lallai yau ku taro wa kanku masifa" nafada araina ina k'wafa
sauƙar bulala naji ajiki na ina d'ago wa naga Fatime tana niyyar kaimin wani gashi yara sun fara taruwa ,kamar ni uwar daba za'a kama a daka a hanya ,
fincikewa nayi zan tafi tak'ara jan rigata
berettt rigata ta ɓarke
"kutt idan kin isa Allah ya tsinemin"
na fada raina a bace nayi kanta da duka ta ko ina nake dukanta, dan zuciyata ta ɓaci duk wani fitsarata bana son ataba mutunci na ,
kwarfo ƙafarta nayi saboda naga yadda yaya ado yakeyi mana nida safiya,
wanwar tafaɗi akasa sai da na mata dukan da ko tashi bazata iya ba sannan nayi tafiyata,
ina ayyana irin bala'in dasu Ma'u suka saka kansu a ciki

gida nakoma abuna na samu Baffa a ƙofar gida na gaida shi sannan nayi cikin gida
a tsakar gida na samu Fadwa tana ta wasa daukanta nayi ina mata wasa mukayi cikin ɗaki..


🍇🍇
ABUJA
MAITAMA ESTATE

cikin bacci Maan yake jin wani abu mai laushi yana tab'a masa jiki
yasan ba kowa bace Angelina ce ƙara gyara kwanciyar sa yayi ya juya mata baya ,ita ma da taga haka sai ta hau kansa tafara tattakashi rabuwa yayi da ita ,farcenta,
ta ni tsama sa acikin duvet ɗin nasa
"auuchhh " yafaɗa ya na mik'ewa zaune jawo ta yayi jikinsa yana shafa gashin jikinta
"what do you need"? ( mekike buƙata) yafaɗa yana cigaba da shafata, daga ƙarshe ya sauƙo daga kan gadon ya had'a mata madara yabata "oyya maza kizo Kisha madara"
ya wuce bathroom brush yayi sannan yafaɗa bathtub yayi wankansa tsaff sannan yafito as usual kamar yadda yasa ba shirin sa
baƙar armless yasaka agaban rigan ansaka dolce gabbana da short nica,
sai da yabata lokaci sosai wajen gyaran sumarsa sannan yasaka bandana akansa yaɗauko angelina suka fito.

a parlo ya sami yan gidan gaba-ɗaya kowa ya hallara amma har yanzu bai ga Fannarh ba,
zuwa yayi ya rungume Daddy yana cewa "good morning Dad"
"morning son" Daddy yafad'a yana shafa kansa,bata fuska yayi a shagwabe yace Daddy kaina yana nuna masa gyaran gashinsa,
kallon sa Daddy yayi sannan ya girgiza kai
"Allah ya shirye ka" dubi abunda kake kamar wani Fannarh, bangaren Ammurh yakoma ita ma yagaida sannan ya mik'a wa Umair hannu suka gaisa.

cikin nutsuwa Ammurh ta zuba wa Daddy abinci a plate sannan ta sawa kowa, ta koma ta zauna suka fara ci tare da bismillah babu wanda yayi magana,

Daddy ne yafara kammalawa yakoma main parlon ya zauna ,
sai Maan ya tashi Ammurh ta kalleshi badai harka k'oshi ba cikinsa yashafa yana lumshe mata ido,murmushi tayi tana ɗauke kai, sannan ya koma inda Daddy yake,
kallonsa Daddy ya nacewa bari nayi maka ta mutanen mamanka "akbirni" (bani labari)
Daddy yafad'a
" to alhamdulillah komai yana tafiya yadda yakamata "
shima companyn abubuwa suna tafiya normal saboda jiya ma nayi magana da manager ɗin ,yace bawata matsala
"amma abinciken da akayi on 23rd July akwai wani ƙauye a Jigawa da za'abuɗe Companyn ƙarafuna a wajen "
"bayan haka ma akwai wani ƙofar gida a cikin ƙauyen da akace suna tonon ruwa ansamu petrolleim a ƙofar gidan ". Daddy wannan aikin ka ne yakamata kaje ka gano yadda abubuwan suke tafiya"
"amma ni yanzu akwai wani zane da nayi yau nakeson zuwa naga wajen sai afara aikin buɗe wajen shima" Maan yafaɗa yana mik'ewa tsaye,

" son idan ka fita kaje ka gaida Abbanku shima jiya da daddare yadawo Daddy yafad'a yana hau rawa sama,
"okay Dad"
kiss ya manna wa Ammurh a chick dinta sannan yafita yana tafiyarsa ta jaruman maza

koda yafita side ɗin su Abban Sarina ya nufa kai tsaye yashiga parlon tare da sallama, a dining area ya samesu suna breakfast suma,ga Sarina zaune a kusa da Mami ko kayan baccinta bata cire ba,tana ganin Maan ya shigo tafara mik'a tana gantsare ƙirji ɗauke kai yayi daga kanta ƙasa_ƙasa yace "ƴar iska" sannan yaja tsaki
fasawa zuwa dining area din yayi ya zauna a parlo Abba da ya hango shi yace "a'a Babana bismillah taho mana" shafa sumar kanshi yayi "a'a Abba ina jira ka gama ne ai"
"Babana zo mana" Abba yafad'a yana yafito shi da hannu,
tashi yayi yaƙarasa kusan Abba yana miƙa masa hannu suka gaisa
"ya aiki Baba"?
"alhamdulillah Abba ,andawo lafiya??"
"lafiya kalau alhamdulillah Baban Babansa" Abba yafad'a yana murmushi"
"bismillah Abba yafad'a
"a'a Abba yanzu nagama breakfast "yafaɗa yana duba wrist watched ɗin hannunsa , Abba zan fita shine na leƙo mugaisa"
kallon Mami da take ta had'e rai yayi ,tab'e bakinsa yayi sannan yace" Mami barka da safiya" yana ɗauke kallonsa akanta,
"lafiya ,ashe kadawo kuma"? bai amsataba yace "Abba sai anjima yafita ko kallon Sarina baiyi ba ,dan ya lura yarinyar kanta yana rawa,

da sassarfa yafito a parlon yana ɗan sauri wanda idan ka kalleshi zakayi zaton tsabar girman kai ko ƙud'i yake sashi haka '
wajen motarsa yanufa (land cruiser) ƙirar Toyota ash babbar mota ce kamar jeep , guard dinsa gaba ɗaya suka dashi suka shiga mota suka bishi, abaya convoy sukayi as usual duk inda suka bi ana binsu da kallo dan manyan motoci ne duk wanda kagani yahauta to ƙusa ne, na Nigeria
a dai dai central bank of Nigeria yayi packing, wayarsa ya ɗauko ya danna kira chan ƙasan mak'oshinsa yace na iso sannan ya ƙatse ƙiran within 3 minutes sai ga wani saurayi ƙyakykyawakamar Maan din yafito da suites a jikinsa , yana ganin motar yagane dan yasan Maan yana son irin wa,ƴannan motocin, zagaya wa yayi front seat ya zauna yana miƙa masa hannu "Maan nee!!! Maaan nee !! "
yafad'a yana dariya musabaha sukayi,
"mutum na mutane kashigo kenan "? idon Maan akan titi yace "eh" achan ƙasan mak'oshinsa,dan shima Fahad akwai magana kamar Mus'ab

wuse 2 ya nufa achan yakeson buɗe sabon companyn motarsa,
"ina Mus'ab ɗin?" Maan ya cillowa Fahad tambaya
"nayi magana dashi d'azu yace mu samesa a wajen" girgiza kai kawai yayi,lokacin da suka iso direct cikin filin wajen suka shiga ,ga ma'aikata sai kai da kawowa suke ana ta aiki,daga wani ɓangare wani dogon saurayi kamar Maan din shima yafito hannunsa cikin aljihunsa gurinsu yaƙaraso ya miƙa musu hannu suka gaggaisa,kamar minti huɗu baya ,yakashe wayan yana kallon Maan
"mutum na mutane shi ma yafada yana k'ara miƙa masa hannu,hararasa Maan din yayi sannan ya ɗauke kai
"malam ni dai kawai muje kanuna mana yafaɗa a gajarce dan yasan Mus'ab da surutu tsiya,tafiya suka fara yi ana nunawa Maan yanayin yadda aikin yake tafiya shikuma hannunsa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon komai da komai bayan angama nuna masa suka fito domin su koma gida ,Musabaha suka kuma yi da Mus'ab yana kara maimaita masa inshaallahu yau zai shigo yagaida Ammurh,
mota suka shiga shida Fahad suka wuce guess house din Maan din,

Maan yad'auko sketch board dinsa ya cigaba da zane_zanensa, chan sukayi sallar zuhr daga bisani suka fito Maan yaraka Fahad har gida amma bai shiga ba
"ina gaida Mamma" cewar Maan to "zataji Fahad ya amsa sannan yashiga tangamemen gidansu..


🍇🍇MAAN🍇🍇
sunan Maan yasamo asaline daga abokansa Fahad da kuma Mus'ab sai wata Gundo friend dinsu ce tun suna primary lokacin da ake musu bayani akan human body kuma ga Abdul_Mani Ulfat basu iya faɗan sunan Mani ba, sai suke ce masa Maan har sunan ya bishi,
har bayan su gama makaranta tare suke har lokacin da suka je Oxford University a England sannan ne kowa ya kama course dinsa inda Maan yake karantan BIT,shikuma Fahad BSc Computer ya karanta,shikuma Mus'ab artichect duk sun riga Maan gamawa sai suka dawo gida ,koda Maan yaga ma karatu sai ya koma ɓangaren artists&architecture yayi masters ,Bai tsaya ba har sai da yasamu transfer daganan zuwa NETHERLAND achan yaƙara karantar business sosai, yayi PhD akai sai suka riƙe shi achan tare da bashi chief manager a wani companyn royal dutch shell a matsayin professional designer a Rotterdam, har yaƙara samun matsayi avue entertainment alterations and redevelopment a matsayin architect yana da certificate daban_daban a ɓangaren shiysa yayi zamansa a amsterdam yatara dukiya da baisan adadin ta ba..


🍇🍇
KAUYEN JAAKA
maƙogoro na har ƙaiƙayi yakeyi saboda tsabar masifa datake cin cikina ina ta mita" wallahi idan naka ma su Ma'u mai kwatarsu sai Allah a hannu na" Inna tace ta kalle ni mai yafaru"? tana riƙe hannu na "ke daga ina kike haka rigarki duk a barke?"
"Ban mata ƙarya ba nace "faɗa mukayi da Fatime shine ta tsaga min"
Innarmu tana da sanyin hali kama hannuna tayi ta zaunar dani kusa da ita..........



oumu khalil🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON*🍇


Story & written

By


🍇@ashoush_

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar 07069793061 ko ka kati a layin ,banda VTU

PAID BOOK

🍇 _Abdul maneou_🍇

FREE PAGES 7to8

___________Zaunar dani tayi kusa da ita tare da cewa "ki saurareni Manal ita rayuwa komai a hankali ake binsa, ba zafafa shi ki riƙa sawa zuciyarki salama, ni bana ƙaunar wannan zafin zuciyarta ki kinji ko?" daga mata kai nayi tace "Allah ya miki albarka" "ameen" nace ina mik'ewa Inna takira suna na juyo wa nayi ina kallonta, ta kunce haɓar zaninta ta ciro wata lankwasashiyar ashirin ta bani, na fita dandali wasa


achan nasamu su Ma'u ko kallon inda suke banyi ba, wajen wata mai ƙwan talaka na nufa, na siye na goma, nakoma kan ice na zauna ina ta cin abuna, ta gefen ido nake hango wa yanda Ma'u take ta lasar baki, araina nake cewa ƙwaɗayayya bazakici ba kuwa

bayan nagama kakarkad'e zani na, na tashi nakama hanyar gida, ina tafiya ina ƴan waƙe-waƙe na, nayi hanyar gidanmu, bayan natafi ne Ma'u ta kalli Feenarh "kinga Labbo tayi fushi ko? duk kece kuma kika jawo sai da nace miki mu jira ta, ko mu fuskanci Fatime tare amma kika ce mu gudu, yanzu muje mu bata hakuri" biyo bayana sukayi domin su tarar ni ko da a hanya ne, ni kuma lokacin da na kama hanya ko tsaya wa banyi ba, sai da na ga wani guri ana dambe naje na tsaya ina kallonsu, wani tunani ne yafado min, nayi saurin cewa "nawa zakibiya na shiga" ina mik'a mata hannu, hannun zanin ta ita ma tafara kuncewa zata dauk'o naji an jawo hannuna, juyo wa nayi zan mulmulo ashar idona yafad'a cikin na Yaya Ado, tuni naji jikina ya ɗauki rawa, cikina har kara yake kululuuuu.. hannu na yakama sai da mukaje kusa da ƙofar gidanmu, ya ciri bulala yafara zane ni ina tsalle ina kuka, wallahi bazan sake ba kayi hakuri na tuba, amma baiji ba sai da yamin lilis yace gobe nakara zagin Inna Wuro sai yayi kacha-kacha dani

anan yabarni ina sharce majina, bangaren baffan mu na wuce ina ta ihu "meyasa meki uwata?" "yaya ado ne naƙara sa ina kuka"zaunar da ni yayi a kusa dashi "to uwata ayi haƙuri a dinga haƙuri da manya kinji ko?"eh "Baffa"yauwa Allah yayi miki albarka" "ameen" nafaɗa na miƙe
"mama na"yakira sunana,juyowa nayi na dawo na zauna kaina a sukunye,allo yad'auko yayi rubutu aciki ya wanke yabani"kiyi bismillah kisha kinji ko?" tohm"na kafa kai a kofin na shanye tass na bashi kofin ina masa"sai da safe"
"Allah ya tashe mu lafiya" daganan"kituro min Innarki tare da Inna wuro"tohm Baffa

ɓangaren Inna wuro nafara bi na ɗauki dutse na bugi ƙyauren ƙofarta dashi,Safiya ce tafito "wanne shege ne wannan yake buga mana k'ofa?"labewa nayi a wani ɗan lungu cikin duhu,sai da tazo daff na samu na zabga mata mari a fuskarta "kice ma Innarki Baffa yana kira,na wuce abuna zuciyata tayi wasai saboda na rama dukan da yaya ado yayi min akanta,ɗakin Innarmu nima na wuce,Samha tana gefe zaune ita da Fadwa sai gwaranci take mata,Inna"kije inji Baffa"kallona Innayi tayi ta girgiza kai"Allah ya shirya minke"tafaɗa tana mik'ewa

fita tayi daga ɗakin, komawa nayi kan gadon karanmu zan kwanta Samha ta ja kunne na "meyasa bakyaji ne?? shekara 13 (sha uku) amma har yanzu babu alamun hankali a tare dake,wacce irin yarinyace kekam?? Allah ya shirye ki" tafada"ameen inda gaske kike"nafaɗa ina murguɗa mata baki, gadon na haye na juya mata baya,ina ƙana nan surutai har bacci yadauke ni

chan chikin bacci nake ji Inna ta na cewa"Baffa yafad'a mata za'ayi baƙi daga wani gari,zasu zo su duba man petrolleim dinda a ka hak'o,idan sun tashi su gyara wancen ɗakin dayake ƴofar gida,ai zumbur na mik'e ina cewa"Inna su waye zasu zo wai? ai man fetur din mu zasu kwashe?wallahi bazan yadda ba" na ƙarasa ina turo bakina gaba

"kashh wai yarinyar nan lafiyar ki kuwa? anya baki da aljanu?? dole nafaɗa wa Baffanku ayi miki rukiyya,kwanciya sukayi suka barni,nima na kwanta ina ayyana irin badaɗalar da zan gudanar akan man fetur din ɗofar gidanmu

🍇🍇
ABUJA
Maan daga inda yasauke Fahad supermarket dinsa ya wuce (Bestbuy) da ke nan cikin Maitama,packing yayi,yafito yana gyara ɗaurin wrist watched dinsa,gently yake tafiya har ya isa cikin super market ɗin,cashiers ɗin gurin gaba ɗaya suka tashi suna masa sannu da zuwa,amsawa yayi, wani daga cikin cashiers din ya bishi domin ya nuna masa manager, wannan shine first time daya kawo musu ziyara, upstairs suka hau, manager ɗin yana zaune yana danna waya, ƙasa-ɗasa Maan yayi sallama,amsawa managern yayi jiki yana rawa, yallaɓai ga guri ka zauna bismillah,zama Maan yayi cikin dakakkiyar Muryar sa yace"abashi Footage din yaga,ɗauko masa akayi danne_danne yayi aciki sannan ya miƙe hannun sa acikin aljihunsa,ya miɗawa manager hannu,ɗaya daga cikin cashier's din ne ya buɗe masa ƙofa yafito,hannu yasa a aljihu ya ɗauko rafar dubu ɗaya yabawa cashier din da yaraka shi,batare da yaduba ba ko nawa ba ne,yasa kai yafita,ko godiyar da yake masa baiji ba.

wurin motarsa ya nufa yana ɗaga yatsaya ɗaya P'A ɗin sa ya biyo shi, back seat yashiga ya zauna yayin da P''A ya shiga front seat yaja motar don su ƙarasa gida,basu wani daɗe ba suka iso gida,a gajiya Maan yashigo ya tarar da Babban yaya yazo (Bashar) da hanzari ya shiga parlon gaba ɗaya suna cikin parlon harda matar Babban yaya,sallama yayi musu yana zama kusa da Ammurh,"hai Allah Ammurh na,nagaji sosai"shafa kansa tayi "sannu Baba ai kayi kokari daga dawowarka,sai kafara zirga-zirga"

hannu ya mik'awa Babban yaya suka gaisa yana tambayarsa"ya aiki,Maan ɗazu Abba yake cemin gobe zaku je kuga wannan Companyn ko??"girgiza kai Maan yayi cikin vocal voice dinsa yace "i don't think gaskiya ba lallai na je ba, I have a lot to do" Umair da yake zaune chan gefe sai yanzu yayi magana "kafiya lalaci wallahi,miye abun wahala a aikinku kuma?'
"Ai duk wannan abun mu yakamata munayi'"sai kuma suka fara musu kowa yana fadan wahalar aikinsa,shidai Maan sama_sama yake amsa wa,sallamar Daddy ne ya katse musu hirar,bayan sun gaisheshi ya zauna,ya kalli Umair"d'azu antura gidansu yarinyar da kake nema,inshaallahu sati uku masu zuwa aka saka ranar auren,sai afara shiri ko"kallon Maan Daddy yayi"Son saura Kai ko?"da sauri Maan ya miƙe yana gyara wuyan rigarsa yayi side ɗinsu cikin tafiyarsa ta kasaita,gaba ɗaya suka bishi da kallo kwata_kwata Maan yatsani zancen aure bare akai ga budurwa,
fira suka cigaba dayi Babban yaya yana ƙara yiwa Daddy magana akan tafiyar da zasuyi gobe,shi Maan daga baya sai yaje tunda yana busy,a dai dai belcony din ɓangaren Ammurh da nasu ya hadu da Fannarh,kallon tsaf ya mata sannan ya kawar da kansa,koda taga haka tasan bawasa,sunkuyar da kanta tayi kasa" ina wuni yaya" ba tare da ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment