Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya"yan ne ke Ci karkashin nashi ya"yan da Muka Tozarta Allah kenan.."Yake Fada yana Sauke Numfashi.

Kasim yace"Abba Tunda kun Tuba Shikenan,Shima Ya Muktar din ai ya yafe muku Shima kuma Bellon komai zai Wuce Nan da Lokaci kadan.."Zubaida tace"Allah yaya Daada nan ce ke Bala"in Sonshi Shida Aneesa ko Guda bata kaunar ya Tabasu.."

Cikin Mamaki Hajiya karima tace"Wata Aneesa kuma...? Tafada Tana Wasa da gashin kanta Gyara kwanciya Zubaida Tayi kafin tace"Kanwar Anty Rahila ce Daddy muktar ya Daukota Daga Borno Shegiyar yarinya ce Ta nan sai Zuba iskancinta take Ko Ballon bata Shakka,Mkrantar Dayake koyarwa ma Take ,Tare suke Tafiya kuma in sun samu Hutu su komo Tare.."

Baki Abba kabiru ya Rike kafin yace"Kaji ko... ? Itama Matar nashi So Take ya Auri kanwar nata Kinsan Yan Bornon nan ba Kyau Tuni zasu ja Hankalinsa.."Kasim Dake zaune yayi Dariya kafin yace"Kai Abba Daga mgana sai kace zai Aureta.."zubaida tace",Anya Abba basa ga maciji fa yadda kasan Annabi da kafurai Shi kadai ke iya mata Hukunci agidanan Daada Tayi Shuru ko Anty Rahila bata iyawa da Fitinar Aneesa kamar Mai Bugun Aljanu.."Dariya ta kara Kama Kasim Cikin Nishadi yace"Niko har naji ina Sonta Domin ina son mace mai Tsiwa.."

Hararansa Hajiya karima Tayi kafin tace"Toh mara kunya.."Mikewa yayi yana Sosa keya yace"Umma,Abba ni zan Fita zan Shiga Cikin garin Wajen Abokina Shamo.."Hajiya karima ce Kadai Tace mai adawo lafiya Shiko Abba kabiru komawa yayi ya Zauna yana Wani Nazari Acikin Ranshi.

****

_GRA-Katsina_

*ABBA GARBA HAUSE*

  
Suma Duka iyalan gidan Suna Zaune A kayatattacen Falon na Gidan Abba garba,Harda su Hamdiya da Ummu salma da Inna Rukayyah Wacce Suka zo garin Jiya,kuma Sunfi Dasawa da Abba garban Shiyasa Take Sauka agidanshi kuma Matar Shi Sahura Wacce Suke Kira Mama Sahura,Makiran Macece Ta iya Duniyanci Tasan yadda Take Hillatan Mutum Shiyasa Kaf yan"uwan Mijinsu sunfi yabonta Fiye da Karima Umma kenan,Shiyasa basa zama Waje Daya Duk da Abaya sunyi Amintakan Munafunci Tunda Rabuwan Mazajensu yazo kowacce Ta Koma Tsagin Mijinta Shiyasa Inna Rukayyah ke Sauka gidan Abba Garba kuma ko Taje gidan Abba kabirun Umma bata mata Wani karban Mutumci.

Zulfa ce ke Basu lbrin Irin Wulakancin da Bello yayima Zubaida sai Dariya Suke Sha Tun barema Mama Sahura Dake Mirmishi Cikin Kissa Tace"Kash..Banji Dadi ba.."Tafada Tana kallon Inna Rukayyah Wacce Ta kada kai Tana Fadin"Ai ni Wlh naji Dadin Hakan,Duk da Muma bamu Tsira ba Wajen Ja'irin yaron nan ammh gwara yayi mata Haka din,ko ba komai ni Nafison In ma Auren Bellon zaiyi ya Auri Zulfa Saboda Daga Kariman har yarta basu da Kunya sam."

Cikin Kissa Mama Sahura tace"Ah inna ba komai Ai Duk Dayane da Zubaidan da Zulfan Duka Namu ne,Fatanmu Dai Shine ya zabi Daya Cikinsu yadda bazai Auro na Waje Balle har tazo Taji Abunda ya Faru ta Zugashi ya Dauki Mataki bq.."Inna Rukayya ta Girgiza kai Tana Fadin"Hakane...Ammh ni nafi son ya Daidaita da Ita Zulfan,Ai mganar Gaskiya Su kabiru sunyi kuskure Babba,Rudin Shedann Dana Zuciya ya Debesu Kuma Tunkafin Su Fada da bakinsu mutane Su ke Zargi Saboda yadda Suka Hau Dukiyar Marayun,Kinga fa Haryanzu chan Jikamshi Gulmar Dake Tashi kenan.."

Mama Sahura tace"Umh Inna Wlh Alhaji baida Tunanin Kashe Rai,Duk Yaya kabiru ne Yaja Shine mugun Shi ya Dinga Forcing Dinshi har ya amince,Ammh Haryau kukan Nadama yake Yana kuma ganin Laifin Yaya kabirun Daya Dorashi kan Wannan Kuskuran.."

Inna Rukayya tace"Hakane Ai Shi kabiru akwai Hange Hange ne,Allah dai ya kyauta don ma Mun Samu Shi Babban bai Dauki Abun da Zafi ba Shidai Bellon Shine Naga kamar Yana da Wani Shiri ne.."Mama Sahura ta gyara zama Tana Fadin"Shine ai Inna Mukesi mu Jawoshi ajikinmu yadda ko Yana da Niyyar Wani Abu Sanadin Hada Surukanta damu Dole zai Hakura,Ko Zulfan ko Zubaida Duk Wacce ya Aura Insha Allahu Shima zai Manta komai.."

Jinjina kai Inna Rukayyah Tayi kafin tace"Hakane kam..Toh Allah ya bada Sa"a Kafin na Koma zanje Abujan Insha Allahu..."Da Sauri Hamdiya tace"Inna zan biki Banta ba zuwa ba.."Ummu Salma tace"kin ma isa Wlh Dani za"a Je.."Tafada Tana Hararan Hamdiyan Dariya Inna Rukayyah Tayi kafin tace"toh duk naji Gabadayanku Zamu Tafi Ba Dadewa zamuyi ba bai Wuce mu kwana biyu ba Dagachan zamu koma kano Saboda Hutu ya kare.."Jin Haka yasa Suka kama Murna Zulfa na gefe tana latsawa waya cikin Mirmishi tace"Daddy bai da Mtsala Uncle Bello ne Mai Damuwar Inna Shifa bai kaunar ganin Wani Daga Cikinmu Agidanman Saboda mu Har yaji yakema Abuja Mutum kamar Zuciyar kafiran Farko.."

Inna Rukayyah tace"Nagani Zuwana na Farko Diban Albarka da Yaron nan yamin kamar nayi kwallah ,muktar din na mai mgana ya gaisheni Wlh ko Waigowa baiyi ba ya Fice Da Hanzari kamar yaga kashi.."Tafada tana Rike baki Mama Sahura tace"Hmm Haka fa yakema Kowa Ko Su Alhajin basu Tsira ba baya gaishesu..."

Inna Rukayya tace"Gadon Zuciyar Bakaken Fulanin nan ne na Dangin Uwarsu.."Mama Sahura tace"Wlh Haka Alhaji yace.

Daga haka suka Cigaba da Hiransu Sama sama Duk dai Akan Bello ne da Irin Rashin Mutuncin Dayake ma Duk Wanda ya Fito Daga Tsatson Abba kabiru ko Abba garba.

*******

Kwanci Tashi babu Wuya Awajen Allah gashi Har Hutu ya kare,Tuni Daliban GGUSS kwatar-kwashi Sun koma Harda Wasu Daga Cikin yan Jss3 sun Dawo SS1 ciki Harda B.kaita Ita da S.jibiya Tun kwana uku da Yin Resume Suka Dawo Mkrantan Amatsayin Senoirs.

Aneesa ko bata da Masaniyar Komai,Duka gidan ba Wanda Yama Bello Mgnar Aneesa,ganin Tun Satin da Wuce Mallam Inuwa ya maida sa Sch Din sai Kowa ya sakankace kan,Bello ya Bar Aneesa Ta cigaba da Jeka ka Dawo,ko da Su B.kaita suka ga Me bello Jikamshi ya Dawo Shi kadai sai Suka Cire rai kan Aneesa baza ta Dawo ba jidda madaki da Suka Dawo suka Iske Suna Neco sun kusa gamawa Har Dakinsu Tazo Neman Aneesa suka Sanar da Ita Aneesa bazata Dawo ba,Hakika Yan Ajinsu Sun Dawo Da yawa yayinda Wasu kuma Basu Dawo ba,Dalibai dadama in Sukaga B.kaita da S.jibiya Sai sun Tambayesu Aneesa Su kuma Cikin kewa Suce Anee bazata Dawo ba Wasu Dayawa Sunji Dadi wasu kuma basu Ji Dadi Ba Domin Aneesa Ta zama Cele by Force Ackin mktantar Sabida bakinta da Kuma Tana kanwar Da Handsome man Mr.Bello jikamshi.

Aneesa Har party Ta Hada Bayan Komawar Bello Makranta Ita Da Hibba Suka chashe,Ashe Tungunne bata kare ba Duka Duka Satin Bello Daya Da Tafiya yama Ya Muktar Waya kan Ashiryama Aneesa kayan provisin da Abun Bukata Ranar Monday zai zo su koma Tare,Ya Muktar Cikin mamaki yace mai"Na zata zaka barta ta Fara Jeka ka Dawo anan Abuja.."

Cikin Gimtse Fuska Bello yace"No...Nan zata Cigaba Har ta Kamallah.."Daga Haka ya Datse Kiran,Ya Muktar Kuwa kai ya girgiza kafin yace"There is a War In Aneesa Taji Lbri ."Bai gayama Kowa ba sai Anty Rahila Wacce Ta nuna Taji Dadin Haka Ita ke Fadama Daada,Wacce Har Awaya Ta Kira Bellon Yana Jin Mganar Aneesa ne yace"Wlh Tallahi Daada...Mgana Daya bazan Chanza ba Aneesa Bazata bar Kwatar-kwashi ba sai ta kamallah Secondry Duka Tukunnah.."Tunda Daada Taji Haka batama bata ma kanta Lokaci ba Ta Kashe Wayarta.

Anty Rahila da Aneesan Direba ya Daukesu Suka Shiga Mall Suka mata Siyayyah ammh Data Tambayeta sai tace Borno Zata Tura ta ta musu kwana Biyu,Aneesa bata wani soZuwa barno ba Saboda Takuran ya Ali,gashi ita kuma bata wani Shaku da mama Falmata ba Tamafi Shakuwa da Hajiya yana,Ga dai Wanda Tafi Shakuwa Dashi Sosai nan Marigayi Alhaji Bukar Bulama...

Haka dai Suka Dawo Gida Aneesa na Kuncin Zuwa Borno,Daada da Anty Rahila ba Wanda yace mata Kanzil,Ranar Lahadi kuwa sai ga Bello ya Diro Abuja Shida Uncle Aminu Wanda Ita Aneesan bata ma san Zuwansu ba sai Wajen yamma Tana Falon Daada Suka Shigo Tunda Ta gansu sai Jikinta bai Bata ba,Tana gaishesu Aminu ne kadai ya amsa Bello Cikin Tsare gida ya kalleta kafin yace"Ki Tsefe kanki kiyi Kitso ki kuma Shirya Abubuwanki masu amfani gobe zamu Wuce Dake.."

Aneesa Ta zaro Ido Waje kafin tace"Zuwa ina kuma...?

Harara ya sakarmata kafin yace"Zuwa Makranta.."Wani Zabura Aneesa Tayi kafin ta Dora Hannu Akai ta Zumduma Ihu,Wanda Sai da Suka Toshe Kunnuwansu Daada Dake Daki Ta Fito da Sauri Tana Fadin"Lafiya...?

Tasamu Amsan Tambayanta ganin Aneesa malale Akasa Tana Kuka da Birgima Tana Fadin Ita babu Inda Zata Tafi sai dai Akasheta.."Uncle Aminu gefe yaja Aranshi yana Fadin"Yarinyar nan Yar bala'i ce.."Shiko Bello Belt din Kungunshi ya Fara Warwarewa yana Fadin"sai dai ki Mutu ko..? Lalle ko zaki mutu da duka,kinga sai na Dauki gawanki na kai makarantan Bushi girl kawai.."

Zaku ga chanjin kudin Novel Daga sama zuwa kasa hakan ya faru ne bisa Roko da kuma korafin wasu Daga cikin Fans dinmu,na cewa ana cikin wani hali na rashin kudi ne Duba da Kaddaran wannan yanayin Da Allah ya aikomana Shiyasa muka zauna muka ga ya kamata mu Duba ku Domin ko bakomai kun Nuna mana Hallacci da kuma kara wajen Siyan Duka Novels dinmu Muna godiya sosai Allah ya saka da alheri Ameen



*How to pay....â‚?200 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?400...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*


_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �350 ne,VIP �600, Single one �200 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_


*ANITHA..*

  
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞
       
           *🅿�10*

""Daada ce tayi Saurin Rikemai Hannu Tana Fadin"Kul karka Tabata...Ka barta Taji da Abunda ke Damunta yarinyarnan tace batason makrantan nan Bello mezai Hana ku kyaleta Tunda ba Mkarantan Shiga Aljanna bace.

Tafada Cikin Fushi,Bello ya kalleta kafin ya maida Kallonsa kan Aneesa Dake kara Saka Ihu Tana wani Fizge Fizge kafin yace"Dama so take akyaleta ta Dinga zama kara zube ba karatu,Ammh ta iya Rashin kunya ko..?toh Wlh bari kiji In kinga baki Tafi mkranta gobe ba,kin mutu ne kafin gari ya waye Abunda zai Dakatar Dani Kenan.."Yana gama Fadin Haka yayi kwafa bayan yaja Hannun Uncle Aminu Suka Fice Daga Falon Daada Ta bisu da kallon Mamaki da Al"ajabin Zuciya irinta Bello.

Cikin Sigan Lallashi Ta Isa ga Aneesan Tana Fadin"Tashi Anee bar Kukan hakanan,Megidan nawa ne In yayi mgana baya Chanzata sai dai kiyi Hakuri kawai.."Aneesa Tatashi Zaune Tana Share Kwallah Cikin Tura baki Da bata rai Tace"Ni bazan Je ba Daada..Ko za"a kasheni bana so akyaleni..."Tafada tana Shure Shure da kafanta kamar Wata Yarinya.

Shuru Daada Tayi mata Tana Binta da Kallo bata samu Zarafin Mgana ba Anty Rahila ta Shigo Ganin Aneesa Kwance kasa Tana Kuka Harda Majina yasa Tasan Kwanan Zencen Domin Kafin Shigowarta Sun Hadu dasu Bello Tsuke Fuska tayi ta karisa Gaban Aneesa Bayanta Hibba ne Cikin Haushi Tace"Meye Haka Aneesa..? Dallah tashi kibama Mutane Waje karatu fa zaki Tafi ba Wani Waje ba,Ammh kin Zauna kina ma Mutane kukan Banza.."Aneesa bata Saurareta ba sai ma kara saka Kuka Datayi,Ran Anty Rahila ya baci Ta kalli Daada Tana Fadin"shikenan Karki Fasa Don Ubanki,Ya Ali zan kira na Sanarmawa Daga za"a Taimake ki zama Mai ilimi ko wa kika ga yana zama ba Ilimi.."Tafada tana Juyawa Da Sauri Daada Tace"A"a Rahila Karki Kirashi Kyaleta Zata Hakura.."Da Sauri Aneesa Tace"Wlh bazan Hakura ba..Ni bazan Koma Ba Sai dai ko In Ya Alin yazo ya Kasheni.."Tafada Tana kara sakin kuka yiyiiii..

Takaichi Ya kama Anty Rahila takalli Aneesa Tace"Toh Wlh bazan zauna Dake ba Tunda kika ki Makranta sai dai ki koma Borno  Kuwa.."Tura Baki Aneesa Tayi kafin Tace"Ba inda zani Wlh Ina gidan nan.."Tsaki Anty Rahila Taja kafin tace"Baki isa ba...Tunda bakison karatu Toh Borno zaki koma Ya Ali ya samu Wani ya Aura miki Shi Tunda Kika ki Karatu Dole ki zauna zaman Aure..."

Kara Mikewa Zaune Aneesa Tayi Idanuwanta Duka Awaje Tace"Aure Kuma Anty Rahila..? Hararanta Tayi kafin tace"Eh Indai bazaki Koma Mkranta ba Toh Tabbas Aure Ya Ali zai miki kin manta mganarshi Ta karshe..."Shuru Aneesa Tayi Tana Kifkifta ido Daada na kallonta kamar Tayi Dariya sai ta kanne Cikin Hawaye Aneesa Tace"Ni bazan yi Aure ba.."Tafada Cikin Tsawa Zakuda Kafada Anty Rahila Tayi kafin tace"Toh ki zabi Daya ko karatu ko Aure.."Jin Haka yasa Aneesa Ta Mike Tana Fadin"Ni dai Wlh An Cuceni Allah ya sakamin.."Tafada kafin ta Zura da Gudu Zuwa Cikin Bedroom dinta Tana Kuka Daga Daada Har Anty Rahila Dariya Suka Kwashe Dashi kafin Anty Rahila ta Fice Tana Fatan Allah ya kara Shirya Aneesa.

Anty Rahila na Komawa Dakinta Ta Iske Missed call din Anty Nafee,Nan take ta bi bayan Kiranta nan Suka gaisa Shine Take Tambayanta Ina ta Shigane Take ta Kiranta bata Daga ba..? Nan Anty Rahila ke bata lbrin Diramar Aneesa.

Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Kema Rahila kinso sakama kanki Damuwa ne,Ko Su Ya Ali Aneesa Ta gagaresu ballatana ke,Kawai ku Tarkato ta Tadawo Gida Tunda Taki karatu Su Ya Ali su samu wani Garaugarai Su Auramata taje chan Ta karata Tunda Bata da Mutumci.."Tafada Cike da Jin Haushin Aneesan Domin Tana Bakinciki yarda Rahilan Ta Dauki Aneesa Taso Ace Sanah Dinta Rahila ta Dauka Domin Duk Ciki batakai su Karfi ba Mijinta bai da Wani Hali Sosai.

Mirmishi Anty Rahila Tayi kafin tace"Kayya Anty Nafee,Kema kinsan Duk Wanda yama Anee Aure yanzu Wlh yajama kansa Domin karamar Bazawara zata zama,Bajin mgana take yi ba Yanzu dai Dole ta koma Makranta Bello ne Daidai da Ita.."Tafada Tana Dariya Tabe baki Anty Nafee Tayi kafin tace"Hmumm kamar Ta koma Sakara kawai ta samu gata bata sani ba,In Da ace Sanah ce kika Dauka Rahila ba Ruwanki da Damuwa kindai Santa yarinya ce mai Natsuwa kamar Uwarta Rahila.."Tafada Tana yar Dariya,Tsam Anty Rahila Tayi kafin tace"Ammh nake ga Da Aneesa da Sanah Duk Dayane Awajena Anty Nafee,Kuma karki Manta Aneesa Kanwarmu ce Auta take ga Baba kuma kafin mutuwarsa Ya bamu Amanarta ne,in muka barta tayi kukan Maraici Allah zai Tambayenmu. "

Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Toh..Toh Uwar Tsari da Mgana barni Haka,Muyi mganar dana Kiraki Saboda Ita bana Bukatar Jin Lbrin Aneesa.."Tafada kafin ta cigaba da Sanar da Ita Dalilin Kiran bata  damu ba Ta saki Jiki Suka yi Mgana Sanin Halin Anty Nafee din Tun Farko bata so ta Dauki Aneesan Tama Nuna Jin Haushinta Sosai,ko Mahaifiyarsu Hajiya Yana bata Nuna Jin Haushinta Domin Duka Dayane.

Aneesa kwana Tayi kuka Kamar Ranta zai Fita Babu Abunda ke Tadamata da Hankali sai Dutsen nan da Kuma Debo Ruwa,Kai Gabadaya Mkrantan ma Bata Kaunarta ammh ya zatayi Bello yasaka ma Rayuwarta Ido kya ce Shine Bukar Bulama,Ko ya Ali yadda yake mata wani Abu,gani Take yafi kowa iya  Shisshigi ,Toh in ba Haka ba,me Suka Hada Daga Yayarta na Auran Wanshi Itafa ta gaji da Wannan Ikon Nashi Allah sa Tagama Mkrantar Borno zata koma in ba Haka sai ya kara Sakamata Wani Tsaman.

Bata da yarda Zatayi Tana Kuka da Hawayenta Da Safe Aka saka Duka kayanta amota,Bayan Tayi sallama Dasu Daada,Bayan Motan ta Shiga Ita da Uncle Amunu Shi kuma Mallam Inuwa da Bello Suna gidan gaba Wanda ke Kallon Aneesa yana Kunshe Dariya Ranar ko Ya Muktar batama Sallama ba gani Take Hardashi Aka Hada baki Aka Maida ta Makranta Har Motarsu Ta Fice Daga Haraban Gidan Aneesa na Kuka Wiwi batayi Shuru ba sai da Bello ya Waigo yana Kallonta Cikin Dakewa yace"In baki kama bakinki ba...Zaki Sha Wuya ne yanzu nan.."..

Uncle Aminu kuma Kunnenta ya Murde yana Fadin"Bush gal,Banda Kauyanci Wata Mace kiga tana Gudun karatu,Zaki zama mara amfani Ko Aure kika yi In dai baki da Ilimi.."Tura baki Tayi Tana Kwallah Cikin Ranta ko Tana Fadin"eh din naji ina Ruwanka Mugaye Allah ya sakamin.."Take Fada Tana Share Kwallah Tundaganan Tayi Shuru sai dai lokaci bayan Lokaci Tana Share Kwallah..

Su S.jibiya sai dai Suka ga Aneesa Kwatsam Bayan Sun Dawo Daga Karatu Wajen karfe 2pm,wannan karon ma Hostel dinsu Daya Dr Karima part 1,Kuma Wannan karon ma Ajinsu Daya SS1a,Lokacin da Suka ga Aneesa basu gasgata ba sai ta Ta dago Tana kallonsu Tana Hararansu ga Hawaye na Zubomata ganin Haka yasa Suka Tabbatar da Aneesansu ne Suka Ruga Suka Fada Jikinta suna Ihun Murna,Da Farko Taki kulasu kuka kawai Take Sauran yan Ajinsu na Baya Duk Wanda yazo yama Aneesa mgana ko Kallonshi batayi Daga Baya Taga ba Sarki sai Allah ta saki Jiki,saboda ganin su B.kaita Tare Suka Tayata Shirya provision Dinta Cikin Lokarta Ranar ko pref basu Fita ba,masallaci ma basu Fita ba Cikin Hostel Suka yi Shi Sai Washegari Aneesa Tafara Zuwa Aji Domin Suna Zuwa Mr.Bello ya Damkamata Uniform dinta da Check dinta da Takalmin Mkranta da Jaka da Littafanta Sabbi,Hakanan Ta karba ammh Cikin Ranta bata gode ba.

Ranar Mkrantan Kwatar-kwashi Ta Dauki lbrin Aneesa Bukar Bulama ta Dawo makarantar Ranar ko Sai ga Jidda Tazo Wajenta Har Hostel tana mata Mitan Tana ta Sauraran Kiranta Karya Aneesa Tamata da Cewa Nombar ta bace mata ne Shiyasa Marairaicemata Jidda tayi Tana Nuna mata Irin Son Datakema Mr.Bello gashi Saura Sati Daya su bar Mkranta Ta mata Kokari,Gyadamata kai Aneesa Tayi da Cewa ta bata da Zuwa Gobe Insha Allahu zata san yadda Zatayi Da Haka Suka Rabu da Jidda Tatafi Tana Jin Dadi Itako Anesa Mirmishin Mugunta Take mata na zakici Ubanki ne,Bayan Jidda ma Iri iritan Sun Ta Zuwa Wajen Aneesa Suna mata magiya ita kuma tana Sakasu akwana Aranta tana musu kallon Wawaye.

Wannan karon Seniors Suna Saman Bene ne,Shiyasa Sai Wahalan bata kai na Baya ba,kuma ba laifi Sun san kan Mkranta sai dai Su kalli Sabbi Dauka in sunga suna iyayi,barima New Comers Jss1 Dariya ma Suke basu kafin Sati Sunci Kwal Ubansu Ko Debo  ruwa ma Aka barsu ya Ishesu balle Muguntar Seniors Abun da Zai sake Baka Mamaki Har Ss1 Dinsu Mr.Bello Shine Formaster Dinsu yana Lura da Aneesa Shiyasa Ko Taso Tayi Wasa Batayi Duk da yanzu ya Rage Wata Muguntar Akanta ganin Ta Dan Fara Hankali ba kamar baya ba.

Ranar da yan SS3 Zasu yi Candy,Ranar ne Dukkansu Suka Hau Saman Dutsen na Kwatar-kwashi Suka Debo Gayyayyanki da Sauran Abubuwa wasu da Aljanu Suka Sauko Aneesa Tace kamar Dole mezai aiketa ko Candy zasuyi Wlh bata iya Hawa Wannan Dutsen Domin yana bata Tsoro Haka Lokacin Zafi in ya Dauki Zafi Wuta yakeyi Da Kanshi Lokacin Sanyi kuma yana Fitar da Huturin Sanyi Wani Lokacin ma Bacewa yakeyi Kwata kwata ba Aganinshi.

Da Jidda Ta Mtsama Aneesa da Magiya sai ta Mata karya da Cewa Uncle Bello yace Taje ta Sameshi Haka ta Dingama Saura Acikin Ranta Tana Dariyan Mugunta,aiko kuwa Sunyi Nadama Domin Koran kare Bello yayi musu bayan yayi musu kaca kaca,Kowacce tasha Kuka kafin ta bar Makranta barin ma Jidda da Takejin Soyayyar Bellon Har Cikin Ranta Itakuwa Aneesa Boye kanta Tayi Har Suka bar Mkrantan.

*****

Tafiya tayi Tafiya Cikin Jin Dadi Da Akasinsa Domin gashi Har su Aneesa Sun Shiga Ss2 Abun da zai baku mamaki yadda Aneesa Bukar Bulama ta zama zakaran Gwajin Dafi Wajen Kokari Acikin Mkrantan Duk Dalilin Bello yanzu Aneesa Ta Daina Kukan Zuwa Mkranta Tunda ta Fahimci bello bazai Taba kyaleta ba,Tana Da Kokari Afannin Darasinshi dana Uncle Aminu Domin ita dasu S.jibiya Turanci Abakinsu sai ka Rike baki,Ahutun da suka samu ne na First Time Anty Rahila ta Haihu Ta Haifi Da Namiji Wanda Yaci Sunan Muhammed Suna Kiranshi Junior,Lokacin Haihuwan Duka yan Borno sun Taho Harda mama Falmata mahaifiyar Aneesa da Anty Nafee da Anty Yagana,da Anty Aisha Daga kano sai Matan Ya Ali dana ya Sunusi da Ya"yansu Harda Sanah Tazo wannan karon,Hakama bangaren Su Abba kabiru Hajiya karima tazo ita da Zubaida duk da Zubaidan Tana nan Abujan ne Wajen Ya Hashim tana Shekarar Farko A base University Zulfa ce Take Katsina Umaru musa yar"aduwa.

Zuwanan da Sukayi kowa yayi mamakin Yadda Aneesa ta kara zama sai dai Fa mai Hali baya barin Halinsa,Rashin kunyanta da Tsiwanta na nan bai barta ba Sai dai yanzu ilimi ya Ratsata ta Rage Wasu abubuwa kamar su Faduwa akasa tana Kuka da Wasu Abubuwan,ko da Sunan sai da Takai Zuciya nesa Ammh Haka Anty Nafi ta Dinga kyaranta da Anyi Abu sai tace samun Waje ne,Har Sanah ma Ta iya kallon Banza Saboda Tana Da Girman Jiki tana ganin ta kamo Aneesan Aiko taci Ubanta Don Aneesa bata Daukan Raini gayamata tayi Ita kanwar Uwarta ce ba abokiyar Wasanta ba,Saboda Haka ta Shiga Taitayinta,Dole Ta Shiga Natsuwarta Sanin Halin Aneesan Ko Lokacin Data zauna agidansu bata da Sauki balle yanzu da Girma ya kara kamata ta kara zama yan"mata sosai.

Falmata har Acikin Ranta Taji Dadin ganin Aneesa ta kara Chanzawa ko bata Nuna ba Kowa ya kalli Fuskarta zai gano Tana Cikin Farinciki Awannann Zuwan ne Har suka zauna da Aneesan Suka danyi Hira saboda kwata kwata babu Shakuwa Irinta Uwa Atsakaninsu Domin kaf Ragamar Kuruciyar Aneesa Alhaji Bukar Bulama ne keda Hakki Akanshi Shine yasan Komai na Aneesa Saboda gatan Datasamu Awajensa,Wananan Hutun taso Zuwa gidansu B.kaita da S.jibiya sai bata samu Hali ba Saboda haihuwan Anty Rahila din,Sai ta bari sai da suka kara samun Hutun Second Term kana ta Roki Anty Rahila da Daddy Suka barta,Salamatu Jibiya suna Dutse ne da Zama Mallam Inuwa Shi ya kai Aneesa Ta Kwana Daya agidansu S.jibiya Kana ita da Aneesa Suka Tafi katsina gidansu B.kaita Hakika kawaancen Kawayen Junan Abun kallo ne Duk da Kullum Cikin Yin Fada Suke barinma B.kaita da Aneesa basa Iya zama Waje Daya batare da Sunyi Tsiya ba,Kwansu Biyu Akatsina Direban gidansu B.kaita na Yawo Dasu Cikin gari Dayake bayan Mallam Inuwa ya kawota sai ya koma,Iyayensu duk sunajin Dadin kawancensu Sosai Tunda Dukkansu yara ne masu Tarbiya da Hankali Ko Tsiya Tatashi Tsakanin B.kaita da A.bukar bulama in tana so Ta Harzuka ta tace mata yar Baka,ko kuma tace mata Tana son Uncle Bello yanzu Aneesa zata Birkice Tafara Tsiyarta B.kaita ta Biyemata Suyi ta kasa Hali ba Ruwansu bai Hana Kuma anjuma ka gansu Tare ba,Sai da suka Dawo Ta Dutse kana Baban S.jibiya ya sanya Direba ya Maidota Har Abuja Booth Dinta Cike da Kayan Arzikin da Iyayen kawayenta Suka Hada mata bayan Ta Dawo ta kwana Biyu Suka Tafi Borno Ita da Anty Rahila da Hibba wacce ke Mkranta yanzu a British International School Abuja Suma sun Samu Hutu ne sai Muhammed Junor  Ajirgi Suka Tafi Borno Wanda Suka Shafe Sati Daya,Anty Rahila ta Koma Ammh sai ta bar Aneesa Da Hibba Anan Suka karisa Hutunsu kafin su Dawo Abuja.

Zuwan da Aneesa tayi ne Wannan Karon ta Sauka Dakin Innarta Falmata badomin komai sai Domin Tafara Hankali ta Fahimci Uwa ta Wuce Wasa,Kuma Ita Din wani Jinshiki ne Ashe Falmata na Sonta kawai Hallayarta ne ta Tsana da Kuma kawaici Haka ta Dinga ina zata saka Da Aneesa,wannan Hutun kam su Ya Ali basu  yi Ciwon baki ba Kullum kuma godiya sukema Bello Domin Yayi Abunda Su baza iya ba Ya Dawo da Aneesa mai Hankali Ilimi ya Ratsata ba kamar Baya ba,sai dai yaransu suna cin ubansu bata Raga musu Duk wanda yashi ga Gonarta Dafashi Take ba Ruwanta Balle Hibba da Tsokana in Ta Tsokanesu Suka Daketa Har Dakin Uwar yaro zata Bika ta Daka Uwarshi bata isa Tayi mgana ba in ma Tayi Toh yanzu Aneesa Zatace Suma haka babanninsu uka nadeta kamar Jaka Dole ta rama kan ya"yansu Tunda bazata iya Ramawa kan Su ba.

Bataje gidan Anty Nafee ba Ita Datake Aure aMaiduguri Anty Yagana tabi Ibadan Ita da Hibba bayan Tazo,wajen Sati Tayi musu achan Mijin Anty Yagana yana ta Tsokanarta suna Tuna mata Abunda Tayi sai dai Tayi Dariya kawai batacewa komai,Toh me zatace Ita kanta Tasan  Aneesa Tayi Lokaci,Tasani lokacin Akwai yarinyata yanzu kuwa ba laifi Budurci ne yagama gauraye Jikinta Shiyasa Tabar yayin Wani Abun Ammh Fa Tura baki da Kunkuni Aneesa Bata Daina ba sai dai Wanda yafi karfinta bai Shiga Harta ba yanzu bakin nan zai yi Tsini kamar zai Fado kasa

Sunsha Hutu Sosai Kafin Mallam Inuwa yazo ya Daukosu bayan Sun Dawo Borno,Kafin su Tafi Haka Anty Nafee tazo Tana ta yada mata da Mgana wai saboda Ita bata dashi Shiyasa taki zama awajenta,ammh sai gashi ta Zauna Wajen Rahila Tunda Mijinta wani ne Akasar Gabadaya kuma yana da tarin Dukiya Shiyasa Koda tazo batayi Tunanin Zuwa Wajenta ba,Aneesa na Jinta ta mata Kunnin Uwar Shegu Domin ba Tun yanzu ba tasan Babin da Anty Nafee ta ijyeta taso ta zauna Wajenta tadinga mata Bauta

Please Login or Register in order to submit comment