Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki bazai iya Furtawa ba,kuma alkalami bazai iya Rubutashi ba balle har ya wallafa.

Dawowata yasa muka Bude Sabon Shafin Soyayyah bamu gajiya da juna gefe Daya kuma muna Kula da Danmu Muhammed Amin kamar mu lasheshi,Bama iya Boye Soyayyar damu ma Juna ko agaban waye kuwa,Ban yarda na bar kaina na lalace Daga Haihuwa Daya ba na mike ina gyara kaina Da Jikina Sanin Halin mijina mai son Ado da kwalliya kuma yana Bukatar kullum ya dinga jin Dadin wajen Harka yan"uwana suna Taimakamin sosai kuma na tabbata ko yau Baba ya Dawo gidan Duniya bazai Tirr dasu ba Saboda sun kula dani kuma sun bani kowani irin Gata

*****

Wata uku da Haihuwa ta Bello yagama Dukkan Shiryen Shiryensa sai dai kawai yazo yana Fadamin ya tura C.V Dinshi Tun last 8 month din Da suka gabata ya Tura ma jami"ar *CLARKSON UNIVERSITY NEW YORK* kuma Alhamdulillah sun Riga sun karbeshi Tun Wata Daya Daya gabata so ya tura musu Duka komai ta Email dinsu yanzu nan da wata Daya zamu tattara mu koma chan da albishir din Nima achan zan Cigaba da karatu na sun bashi gidan zama har illah masha Allah da Motar Hawa sai dai in Shine ya gaji ya Daina aiki Dasu.,Ammh sai yaki karban gidan ya neman mana wani mension mai kyau ya siyan mana komai ta Waya ya gabatar.

Wayyo Dadi murna ta cikani na Daka tsalle na Rumgume Mijina Saboda Farinciki Haka na Shiga Kiran yan"uwa da abokan Arzuka ina gayamusu suna Tayani Murna B.kaita da Salamatu Jibiya sun fi kowa murna,Duk d B.kaita tana Tunanin bazan samu zuwa Bikinta ba wanda aka sanya wata Biyar masu zuwa zata auri wannan dai lacran na Umaru musa yar'aduwa Universtiy.

Iyayena da yan"uwa sun fi kowa Murna Ko Ya muktar bai sani ba sai da muka je musu sallama Jinjina kai yayi yana Jinjina ma Kanin nasa wajen kwanya ya Tabbata kaf jami"o"in Dake cikin Duniyar nan ba wacce Bello zai nemi aiki da ita ta ki bashi Dama Gabadaya Da grade A yake Fitowa Shi kanshi Dayake yayan nashi yana Jinjina ma baiwar kanin nashi Sosai.

Daga Abuja Borno mukaje yi musu sallama Kwana Biyu mukayi Munje Maiduguri wajen Anty Nafee ammh bamu kwana ba,muka Dawo aranar Washegari kuma Muka Hawo Jirgi zuwa kano Anty yagana sai dai mukayi sallama awaya Anty Aisha dai Naje gidanta na Wuni Haka gidan Ammi wanda zuwa Lokacin Bello da kanshi yama Uncle Aminu mganar Raihana da Midibbo wanda ya kusa kamallah Military sch ya kusa Dawowa Itama Raihanar Ta kusa gama nata karatun su Baffa Hardo suka zo wajen Dangin Su Uncle Aminu suka nema ma Modibbon Auran Raihana,An saka Lokaci Wata Goma masu zuwa Lokacin Dukkansu sungama karatunsu Har Modibbo yafara aiki.

Mun gama Duka Shirye Shiryen mu komai namu ya kamallah ba Da wasu kaya bane zamu tafi sai Abunda Ba"a rasa ba,Jami"ar BUK tafikowa Damuwa da kuma Ganin Asaran Rasa Mr Bello,ammh basu da yarda zasuyi Tunda dai cigabane ya samesshi haka Daga Daliban Har malamai aka rabu ana kewar juna Uncle Aminu da Anty Aisha da Megidanta suka Rakamu Aiport Din Mallam Aminu kano Da karfe 8:30pm na Daren Ranar Asabar jirginmu ya Daga zuwa Birnin New york.

Mun Sauka a babban Filin Jirgi na New york a inda muka samu Taxi har zuwa cikin anguwar da Jerin Gidajen da Bello ya siyama suke wato *maahattan Midtown* gida ne mai upstsir mai kyau da Tsari mai Dauke da Falo da 2 bedroom Daga sama sai kichen da Dakin baki Daga kasa Daga waje sai aprtment haka wajen parking din motoci,Muna da makota Wadanda ke kusa damu,Daya barabiya ce karatu Mijinta yazo yi sai Daya kuma Yar Nageria ce ammh kuma bayarbiya ce Mijinta Likitane Shima aiki ya kawoshi Sunanta Adija Tunda muka zo kasar itace ta shigo muka gaisa naji Dadin samun Wani Dan kasata kusa dani.

Dama tun muna gida Nageria Yariga ya karbomin Resuit dina,Ban Fara karatu ba sai da Muhammed Amin yayi Wata bakwai kana na Zama Daya daga cikin Daliban makarantan Da Mijina yake koyarwa,ina karanta Biology,Muhammed Amin kuma Dashi nake tafiya Dayake makaratantar akwai Nannys masu kula da yara wajensu nake kaishi sai mun tashi tafiya gida mu karbosa mu Dawo gida Soyayya muke gudanarwa mai cike da Tsabta kamar zamu lashe juna.

Ban samu zuwa Bikin B.kaita ba sudai na Tura mata kudi masu yawa Gudunmmuwa,duk da Banjin Dadin Rashin Zuwana ba Bani da yarda zanyi ko ba domin komai ba Saboda karatuna...ga Kuma Mijina ban zan so na zama ina Rabamai Hankali ba ammh koda yauahe muna waya da yan"uwanmu da iyayenmu Lokacin da muka samu Shekara Daya a New york Anty Rahila da Ya Muktar suka kawomana Ziyara nan ne naga karamin cikin Jikinta yawon Bude ido suka zo Domin Hibba da JUnior Suna gida wajen Daaada.

*****

*SHEKARU UKU BAYA...*

Acikin Shekarun ukun Da Suka gabata bazamu ce komai ba sai Dimibin Godiya ga Allah,Domin Ababen Cigaba ne suka Lullube Duka Rayuwarmu,Duk da mun Kurbi Ruwan Rashi Sosai na Rasuwar Daada wanda shine Dalilin Zuwanmu gida na Farko Allah yasa Lokacin mun samu Hutun Makaranta mun ji Mutuwar Daada sosai barin ma Bello da ya muktar da suke ganin Tamkar Daada itace uwarsu da Ubansu,

Bamu koma ba sai da muka Tsaya Bikin Uncle Aminu Wanda suka Daidaita da Salamatu Jibiya muka Sha biki Tabi angonta Zuwa Lagos Raihana kuwa kaduna take Zaune ita da Mijinta Modibbo wanda ke aiki anan Heaquaters na yan sanda Dake Jahar kaduna suna Zaune Shida Matarsa Raihana,Munje mun yi musu kwana 2 har gidan Sani sai da mukaje nayi ma matarsa barka ta kara Haihuwa,Naje katsina gidan B.kaita na isketa da cikinta, Muhammed Amin kuwa yayi yawo ba inda baya zuwa,Sanah ma an saka Lokacin Bikinta da wani Ma"aikacin Costome Dake aiki a partacourt,

Da zamu koma New york bamu koma da Muhammed Amin ba muka bar ma su ya muktar Tunda ina da karamin ciki alokacin,Dawowarmu ko Wata Biyu bamu yi muka samu Labarin Rasuwar Abba kabiru damam Tun Zuwan mu Rasuwar Daada muka samu labarin yana halin Jinya sosai Tunda ga lalurar Data sameshi,gabadaya duka arzikisun ya kare wajen siyan mgani Hatta gidan da suke ciki sai da suka Saida Gidan Hashim suka koma da zama,Gashi bashi kadai bane domin Ramin mugunta ya koma ma Kasim Ya zame a bandaki kashin bayanshi ya karye yanzu Shine ke Rayuwa Bisa Keken guraku,Abokinsa Haruna kuwa Hatsarin Mota yayi Allah yamai Rasuwa komai nasu yagama karewa Shi kanshi Hashim din karfin Hali ne da Godiyar Allah ammh aikin kamfani Har yaushe zai Rikeshi Inda Allah ya taimaka Zubaida ta Samu miji cikin Abokansa ta aura Matansa Biyu itace ta uku tana Abuja ammh tana cikin Jin Dadin Rayuwa har ma tana taimaka ma iyayenta.


Bangaren Su Abba garba kuwa Abun yayi muni sosai,Suma komai ya kare ga cikin Shigen da Zulfa data Dauko musu bakin ciki kamar ya kashe Mama Sahura Inna Rukkayyah ce kadai Allah ke Rike da ita ta samu ta Aurar Da Hamdiya anan garin kano Ummu ce ke gabanta yanzu itace kedan Taimakonsu itama babu komai sai godiyar Allah,Bello ne kadai yazo gaisuwar mutuwar Abba Kabiru sai Alokacin yaji azuciyarsa ya yafe musu ko ba komai sunga Hukuncin Allah Tunda agidan Duniya Shiyasa wani lokacin da gwara ka bayyyana kan ka a gaban Hukuma ta yankema Hukunci,da ka zauna Hukuncin Allah ya Faru dakai tun agidan Duniya Haka Abba garba ke kuka yana Rokan Gafaransa,Kasim kuwa Duk yagama lalacewa yana Zaune Bisa Wheel chair din da Bello ya tashi akai,Yarsa kuwa Fauziya da Kudiran Allah ta Rayu ammh fa cikin kaskastacciyar Rayuwa, Rayuwa kenan nan yake Shaida musu shi ya siya Ragowan kamfanin mahaifinsu Dake Lagos wanda yanzu haka ya na nan yana aiki ta hannun manajan mahaifinsu Mr James,sunyi matukar mamaki Abun da kuma ya basu mamaki  Shikanshi ya muktar ya Jinjina mai kanin nashi sosai inda yace"Yaya bazamu bari...Komai na mahaifinmu ya kare ba...Zamu ji Dadin in muka Tsira Dako Da Abu Dayane.."Rumgume juna sukayi suna kukan Rashin Iyayensu.

Ba Dadewa da mutuwar Abba kabiru,Gidan da ya Ragema Abba garba cikin Dare aka tashi da gobara Dakyar suka Fita sai dai Zulfa ce dake cikin Daki ta kone sosai Asibiti aka kaita kwanta Biyu tace ga garinku nan Gidan kuma ko Tsinke ba"a Fitar ba komai ya gama konewa Wanda ba wanda yasan Daga ina gobarar da take,Mama Sahura tayi kuka kamar ranta zai Fita,Komai ya kare yar nata kuma Allah yayi ikonsa da ciki ajikinta karshenta dai Kauye suka koma Wato Jikamshi dangi Duk sun kare Gidansu na baya wanda yagama Zubewa suka samu Daki Daya Hashim ya tallafa musu suka gyara wajen zama saboda shima bashi da wajen da zai ijiyesu sakamakon Shima an ragemai matsayi acampany Dayake aiki Ya muktar kuma Bello yahanashi basu Taimako Yace ya kyalesu bazai iya karesu ba Hakkin Rai ne da kuma hakkin Dukiyar marayu da suka ci bazai barsu ba.

Aisha maiduguri Tuni tayi Aurenta agarin maiduguri wani Dan"uwanta ta Aura,dan kasuwa ne a kano yake kasuwanci yadaukota suka dawo kano inda yayi gida,Yariga yagama sanin labarin Abunda ya Faru da Aisha Tun Farko,sai bayan Rasuwar Mahaifiyarta ne tayi Auren ya"yanta biyu yanzu Saboda Mijinta yana da Fahimta yasa suke zuwa Har Abuja ganin Fauziya Suna mata alheri Aisha tayi kuka kukan Nadamar Rayuwarta ta baya da yadda Rayuwar yarta ya kasance,Yayanta ya riga yayi Rantsuwa Aisha bazata Rike Fauziya ba,Dangin Ubanta zasu Riketa Kasim kuwa yana kuka Yana Rokon Aisha gafara domin yana da Tattabacin Harda Hakkinta ya kamashi,Me zatace banda ta yafemai ko ahaka Kasim ya Tsaya Allah ya nuna mai Isharsa Zainab Alhaji isa ma Tuni tayi Aurenta Kasim dai yana Zaune yana Girban Abunda ya Shuka In ya Tuna Rayuwarsa sai yaji da ace Allah zai bashi dama daya Sauya Rayuwarsa ya dawo Nagari,sai dai kuma kash Lokaci ya Riga ya kuramai.

Danaji labari sai da naji ba Dadi acikin Zuciyata ina Addu"ar Allah ya Rabamu da Cin Dukiyar maraya da kuma aikata Abunda zai zo ya dinga bibiyar alhalinmu Ameen.

Ayanzu haka na kara Haihuwan Mai sunana Wato Aneesa kenan muna Kiranta Anee,sai kuma mai sunan Daada muna Kiranta Daadan,cikin Shekaru uku na haifesu ni kaina na san na Taka gwarne,B.kaita ta haihu namiji Hakama Raihana Sun haifi Little Aneesa,Sanah ma tuni har anyi Bikinta ta tare agidan mijinta Muhammed Amin kuwa yana Wajen Anty Rahila achan aka sakashi a makarata mukuma muna New york nida mijina da Ya"yana Lokacin har na kamallah karatuna ina Service ne.

*****
Ina cikin kichen da misalin karfe 7am na safe cikin kayan barcina Riga da wando masu Taushi ina Hadamana kalaci sakamakon yau Weeked ne Dagani har Mr Bello muna gida

Ina cikin Soyamana Fanke dama ina zuwa da abubuwan amfanina in mukaje gida Nageria naji Kukan Daada Da hanzari na Fito Ina Tambayan meke Faruwa,Ganin Anee tana Dariya Dauke da Choculate din da na bama Little Daada Dake zaune bisa kekenta na zama na gane Dalilin kukan ban tsaya bata Lokaci ba na isa kusa da Anee na make mata kai ina Fadin"me nagaya miki Don kaniyarki..?

Nafada ina jan kunnata,Baki ta bare,Ban tsaya Sauraranta ba na kwace mintin bakinta ina Fadin"Muguwa kawai...katuwar banza,wacce batasan kanwarta ba Wlh in nakara jin kukanta na Fito sai na lahira yafiki jin Dadi.."Nafada ina Turata baya ta Saka kuka kiris sai ta Fada Jikin Babanta wanda ya Sauko Daga sama yana sanye cikin Kayan Barci na pjms Masu Ruwan Toka,Yayi kyau ya kara kiba kamar ba Mr Bello da alama yana kara jin Dadi Sosai.

Riko Anne yayi wacce ke kuka Harda majina kamar wacce ake yankawa yana Fadin'"Me kuma tayi Tun safe kin Fara zaluntarmin ya..? Yafada yana Sharemata hawaye Ko kallonsu banyi ba na Duka ina lallaban littale Daaada na saka mata mintin Cikin bakinta kafin na mike ina Fadin"Dukan Min y"a tayi kajama yarka kunni Wlh in tace mugunta ce Dabi"arta zata sha Wuya ahannuna.."Nafada ina Huci Saboda Rashin ji Aneesa yafara isata wlh yarinya kamar bugun jinnu.

Mirmishi yayi yana Kara Rumgume Anee yana Fadin"Koma miye dai Kar a takura mana...Ai gado tayi.."Ina kallonsa nace" gadon wa...?gira ya Dagamin yana yar Dariya Mirmishi nayi kawai na koma kichen ina Ma iyayena Addu"a acikin Zuciyata saboda indai ko Hakane sun shaa fama dani sosai.

Ina cikin Juya Fanken Dake cikin Mai naji Hannunsa bisa cikina ya Rumgume ni ta baya ajiyar zuciya na Sauke lokaci Daya ya saka kansa zuwa wuyana yana Sumbata ta dan zillewa nayi yayi Saurin Riko hannuna yana Rikewa Lokaci Daya muna juya fanken atare Cikin Sanyin Murya yake Fadin"Hausawa fa sunce magaji mafiyi..Anee gabadaya kece sak daga kamaninku zuwa Hallayanku...So ki godemana yadda muka Wahala akanki.."Ban yi mgana ba illah Dariya Da mirmishi dana saki Lokaci Daya ..

Tare muka gama Kwashe Fanken Cikin mai cikin Sauri na kashe  gas din najashi wajen fridge ina Fadin"Me kace...? Waro ido yayi yana Fadin"Banyi mgana ba Madam Aneesa.."Dariya na saka kafin na Rike Kumatunsa ina Fadin"Na yarda Anee duk Kinjina ta Dauko..Ashe haka su ya Ali keji lokacin ina yarinya...Lalle..."Dariya yayi yana Riko kuguna cikin Sanyin Murya yace"Nima yakamata kigodemin nima kin bani wahala musamman makaratanmu ta Kwatar kwatashi.."Kirjinsa na Fada ina Fadin"Godiya kake so..? Kai ya Gyadamin,Dagowa nayi ina kallonsa kafim nace"Godiyarka ba irin tasu bace ..Kai naka na musamman ne.."Na fada Lokaci Daya ina sakarmai kiss akumatu kafin na Dago ina Fadin"Dis one is for my Uncle Mr Bello muhammed Jikamshi..'Na kara sakarmai wani a gefen kumatun ina Fadin"Dis one is for my Husband..."Na karshen na Sumbaci bakinsa mai Tsawo lafin na Dago ina Fadin"Dis one is for my B.love...Tanque For u love,Support and care...And a very big thank to u for been Thier for me...I love u so much..."Nafada ina fadawa kirjinsa na kamkamesa ganin kuka na neman kwacemin Kara kamkameni yayi yana Fadin"Thanks so much my Anee...Kedin ta musammance ina matukar sonki..."Yafada yana Sumbatar Wuyana cikin Fitan hayyaci na Dago kaina na Hade bakinmu waje Daya Cikin kwarewa muke Sumbatar juna Lokaci Daya muna Shafa Sasaan Jikin Juna,Dagani yayi sama na makale acikin Jikinsa muna Sumbatar juna,Kan Fridge din ya Dorani yana Salube rigar barcin Dake Jikina Nonuwana suka bayyana ya Saki bakina yana kallona cikin Fitar hayyaci yace"Nasha my Anee...?

Lum nayi da ido banyi Mgna ba na Tura kanshi ina Sakin Siririya kara Kamar wani karamin yaro yashiga Sarrafa Breats dina yana Shan Daya,gudan kuma yana wasa Dashi sai da ya Dauki mintina kafin ya Dago yana layin Ido yace"Na....go...de...."

"Nima anan zan cema masu karatu Nima NA...GO...DE..."

*TAMMAT BIHAMDULLAH..*


*Alhamdulillah..Godiya tabbata ga Allah (SWA)daya bani ikon Farawa Wannan Littafin cikin Aminci da yardansa,gashi kuma yau Allah yayi ikonsa na kamallah muku shi hakika Allah ne Abun godiya Salati kuma Aminci ya Tabbata ga Shugaban Hallitun Duniya Annabi Muhammed (SAW) Tsira kuma da Aminci suka Tabbata ga Ahalayansa da Sahabbansa Ameen...Fatana zaku Dauki Abunda ke Amfani cikin Wannan Labarin nawa ku watsar da mara amfani,ya kuma bamu ikon Daukan Darasin da muka karanta Kuskuran dake ciki kuma Allah ya yafemin ladan dake ciki kuma Allah ya Rabamana dani daku gabadaya Ameen*



_Godiyata ta mussaman ga Masoyanmu wadanda suka Siya littafanmu,mun gode Sosai Allah ya saka da alheri...Allah ya kuma ya bar zumunci Ameen ya Allah bakina yayi kadan wajen Nuna muku kalmar Godiyata Sai dai nayi Fatan Allah ya biyaku da gidan Ajannah Firdausi,godiya ta mussaman ga Masoyana na nesa Dana Kusa,godiya ta mussaman ga Malamai na marubuta da kawayena da yan'uwa ina godiya ga Kwarin gwiwanku...Allah yayi albarka ya kuma kara girma_


Fatan alheri....Fatan sai mun sake Haduwa cikin Sabon Novel din da zamu Rubuta muku Nida Sisinah Aisha alto fatan bazaku bamu kunya ba zaku nuna mana kauna wajen Rububin Siyan Sabon labarinmu wanda zai zo nan bada Dadewa ba Mungode


Daga karshe zan miki godiya ke mai Hannun Bera ko kuma masu hannayen beraye da kuke ta Sharing din wannan Novel din Into groups groups...Bazan ce miki komai sai godiya Allah ya saka miki da Abunda kikamin Sai dai kuma kisani akwai Ranar Tsayuwa Gaban Allah Ranar da Gabbai ma bazasuyi mgana ba Aranar zaki biyani Dukkan hakkin da kika Dauka nawa Dake da wadanda suka karanta basu Biya ba...


*Anitha...*
*Shakira..*
*Janafty..*
*Jamila umar...*
*intelligent writer's asso...*
*20/7/2020..*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment