Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai Suka gaisa cikin sakin Fuska,yana Sauri ne Tawagarsa na waje tana Jiransa ya Fito ya Shiga mota suka juya Zuwa Airport yana cike da Tsausayin Kaninsa da kuma yadda Zaiji in yaji Hukunci da ya yanke.

Daada bata gayama kowa mganar ba Tayi Shuru da bakinta Anty Nafee kuwa Kwana biyu tayi kafin ta koma maiduguri akwanakin Datayi kuwa sai da Aneesa ta gaji da ita haka ta sakata Daki tana mata Fadan wai bata hankali ne haka takeso ta karishe rayuwarta cikin Wahala bata biye mata sai dai tayi ta Tura mata baki In ko ta ganta tare da Bello ta dinga sakin mata mgana kenan tana fadin yana Nakashasshe bazai kyale mai lafiya ba,Abun dai ba Dadi Daada na ganin komai bata mgana Wani Lokacin Daki ta ke shigewa tana Share kwallah Shiko Duk wannan baya damunsa Abu Dayane ke cin Ransa kada aace za"a rabashi da Aneesa in ko Haka ta Faru bayan ciwon jiki harda na Zuciya zai iya kamasa.


*Kibiya ki karanta cikin Salama..Ke da kika Siya kike Fitarwa da ku da kuke karantawa baku Biya ba Bazan ce komai ba Illah Allah ya bada Sa"a ammh ki sani! na sani! mun sani!.kuma ku sani..! Akwai ALLAH.*

Zakuman Uzuri Vips may be zuwa Dare kujini Tsint Saboda wata Sabga data tasomin..Nagode

*Anitha...*
8/19/20, 11:21 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

  
*Wattpad:Janafnancy13*


*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

           *🅿�26*

Tun ya muktar na lagos kira ya Ali sukayi magan kan in ya dawo Don Allah yana son ganinsu shida ya Sunusi in kuma ba damuwa Harda su mama Yana saboda Muhimmancin mganar,Jin Haka yasa Ya Ali yace karya damu insha Allahu Da zarar ya dawo zasu zo.

Bai dawo ba sai da ya dauki tsawon kwana biyar kana ya Dawo Abuja ranar Daya Dawo ya kira ya Ali ya sanar Dashi inda yacemai insha Allahu ya Saurari Zuwansu.

Abba hardo ya kira Daada yace ta aiko Azo akarbi Ruwan zamzam din Dayama Bello addu"a aciki adinga zubamai cikin Ruwan wanka Kuma ya zama Ruwan shanshi,kullum kuma da Daddare in zai kwanta Ashafemai jiki,insha ALLAHU za"a samu Nasara Ahankali kowacce gaba zata Dinga saki Cikin Jin dadi Daada tayi tamai Godiya

Muktar na Zuwa gaisheta ta labartamai yadda Sukayi da Baffa Hardo Shima yaji Dadi Sosai,Yaso yaje da kanshi ne sai kuma ya Ali yamai wayar gobe suna Tafe shiyasa yafasa ya Tura mallam Inuwa,modibbo ya bisa Zaije ya kwana Biyu ya Dawo,Tare da Dauko Takardun Makrantansa wai Aikin Dan Sanda yake son yi Shine Ya muktar yace ya Daukomai Takardunsa.

Washegari sai ga ya Ali da ya Sunusi sai Mama yana da Mama Falmata Zuwan yabama Aneesa da Anty Rahila mamaki Tunda su basu san meke Faruwa ba,Sukansu Iyayen na Aneesa Sunga Ramarta da yadda Duk ta lalace,Mama falmata kuwa cikin Ranta tana Fatan Allah yabama Aneesa Aljannah Dalilin Jinyar Mijinta,Cikin Ran Mama yana kuwa karfin Halin Aneesa take ganin Yadda Tana yarinya karama ammh ta iya Dauke laluran Bello,wanda ko alama bata barinshi da kazanta Ko cikin Wani Hali koda yaushe zaka Sameshi cikin kyawawan Kammani Yana zaune bisa wheelchair dinsa.

Sai da suka ci abinci kana Aka Zauna Zaman Dalilin Zuwansu afalon Daada Nima muna cikin Daki Nida Bello ina karantamai wani Littafin Hausa mai Suna Ajininsa yake na Zulaihat sani kagara Anty Rahila tace na Fito Nazo tare da Bello Ya muktar na son mgana damu Daga ni har Bello sai da muka kalli Juna,dama ni cikin raina Tunda naga Zuwansu Mama yana Lokaci daya dasu Ya Ali jikina yayi sanyi Haka shima Cikin Ransa yana ta Fargaba Allah sa ba Tunaninsa bane zai Tabbata...

Hijabin sallah ne na Zumbula,ina kallon Bello wanda ya kafeni da ido Ajiyar Zuciya na Sauke kafin na karisa ta bayanshi na Shiga Turasa Zuwa Falo gabadayansu suka sakarmana idanuwa har muka kariso Tsakiyar Dakin kusa da Daada na ijiye Bello ni kuma na koma Kasa Kusa da Anty Rahila na Zaune kaina na kasa,Daga chan kuwa ido kadai Bello ya sakarmin Lokaci Daya kuma yana karye Wuya.

Ya muktar ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Alhamdulillah naji dadin yadda muka taru lokaci Daya..Mama da Fatan zaku man afuwa na taso ku Daga gari mai Nisa ni ya kamata ace nazo toh saboda muhimmancin mganar da kuma Halin da Bello ke cike yasa Na zabi kuzo nan mu tattauna mganar.."Kowa gyada kai yayi cike da gamsuwa mama  yana ce tace"Ayyah babu komai Baban Hibba Yanayin Aiki ne...kana ma kokari Allah ya saka da alheri.."

Gabadaya suka amsa da Ameen,Aneesa kanta na kasa tana Wasa da gefen Hijabinta Mama Falmata ma kanta na kasa batace komai ba wanda ya damu sanin Hallayarta na kawaici da Rashin son kwaranniya.

Cikin Gyara murya Ya Muktar ya cigaba da Fadin"Na taramu ne Dukkanmu Awannan wajen Domin Mun riga da mun zama yan"uwa Dalilin Auratayya daya Shiga Tsakaninmu Harda Zuru"a.."ya Ali yace"Hakane kwarai.."Jinjina kai ya muktar yayi kafin ya cigaba da Fadin"Dalilin Hakane naga ya dace muma Junanmu Adalci,bako wace mgana bace Illah Mganar Aneesa da Bello.."

Dam! Gaban Bello dana Aneesa ya Fadi lokaci Daya,Atare suka kalli  juna Lokaci Daya cikin Wani yanayi kowa na lura dasu barin ma Daada dataji har tafara tara kwallah cikin Mamaki ya Ali yace"Aneesa kuma...? Kardai Wani Iskancin tayi domin Nasan mai hali baya fasa Halinshi sai dai yayi lambo yagamin Wani Dibar albarkan tayi ma bawan Allah dake Zaune ba lafiya yanzu naci Ubanta wlh.."Yafada cikin Fada dama shi akwai Saurin Fushi.

Baki Aneesa ta Tura kwallah na Taruwan mata a ido wato ita haryamzu bata girmi Duka Hannun Ya Ali ba,Bello Dake kallonta Duk ransa ba Dadi Ya Sunusi ne yace"Zata aikata kasan Haka take akwai lambo Cikinta fal iskanci kedai kam bansan yaushe zaki hankali ba,Baba bai bar gidan Duniya ba sai da yagama Sangartaki.."ya fada yana Nuna ta shima Lokaci Daya yana Hararanta.

Dukar dakai Aneesa tayi cikin Ranta tana Fadin"Toh ni me kuma nayi.."Ya muktar ya katsesu da Fadin"Ashsd..Meyasa kuke Hakane...? Bafa laifin datayi Wlh Aneesa tafi kowa kula da Bello Acikin gidan,gabadaya Shikanshi in ba ita tamai wani Abun ba sai ga yana bata rai..Babu Abunda zamu ce mata sai godiya da Fatan Allah yasa ta gama da Duniya lafiya.

Suka amsa da Ameen Mama yana tace"Ai daman Aikinta ne ta kula da Mijinta kuma inda tasan Dimbin ladan da mace take samu wajen kula da mijinta ko jinyarsa data kara zage damtse ina Fatan Allah muma yaraba mana ladan damu.."Tafada cikin barkwaci aka amsa da Ameen Ana Dariya.

Cikin Jimami Ya Muktar yace"Ina Nufin kan makomar Aurensu ne..,Ina Tunanin Ya dace ace mu zauna muyi Duba kan Rayuwar ita Aneesa,kada mu tauye mata Hakki kamar yadda na Dauke bello kani gareni itama tamkar kanwata take gareni...Zan so mata Abunda zan so ma kaina na Zauna nayi dogon Nazari da Tunani na Fahimci zaman Bello da Aneesa waje Daya amtsayin Ma"aurata bazai yuyu ba,Akwai kwaruwa aciki,shi bashi da lafiya bazai iya Sauke mata Duka Nauyin Daya Rataya Awuyansa na Aure ba,ita kuma macece mai lafiya dole watarana tana Bukatar abokin Rayuwa wanda zai Sauke mata Hakkinta da wannan dalilai na yanke Shawaran mu taru anan domin na sanar muku Bello zai saki Aneesa,saboda ta samu damar samun miji mai lafiya ta Aura..."Yafada yana Shanye kwallar idanuwansa lokaci Daya yana kauda kai bayaso Bello ya Zuba masa manyan Idanuwansa.

Mganar ta Daki Zuciyar kowa Tun ballatana Bello da Aneesa,wanda ta dago a razane tana kallon Ya muktar wanda yayi kasa da idanuwansa,Shima Bello shi yake kallo cikin wani Dukan Zuciya da Rauni mai Tsanani kokarin motsa bakinsa yake ammh yakasa mgana sai kuma ya maida kallonsa kan Aneesa Wacce ta Rufe bakinta Hawaye na Zubomata Lokaci Daya tana girgizamai kai ganin Idanuwansa sun kada sunyi jawur lokaci Daya kuma sun Fara tara Ruwan kwallah,Daada ma kanta ta Sadda tana Share kwallah Mama falmata ta Dago tana kallon Aneesa da Bello lokaci Daya taji Sun kara bata Tsausayi Aneesa yarta ce ammh Tana mata kwadayin samun Aljanna dalilin Auren Bello Dake kanta.

Ya Ali ne ya sauke ajiyar Zuciya kafin yace"Wannan mgana Daka Fada Hakane Muntari Aduka mganganunka Babu na Banza...Kuma Abun adubane sai...",Tim suka ji karar fadowar mutum,Da gudu Kowa ya mike suka Nufi Bello Dake kokarin tashi ya Fado daga kan keken,kafin su isa Aneesa ta rigasu isa cikin Kuka da Fitan Hayyaci ta Rarumosa Lokaci Daya ta Fashe da kuka sai kowa ya tsaya yana kallonsu.

Kan Cinyarta ta dora kansa Lokaci Daya Hawayensa suna gangarowa ta gefe da gefen kumatumsa,Da ido ya kafeta itama Shi take kallo tana Fadin"Kaji ko zasu rabamu..? Sun manta kaima abaya ba haka kake ba! Kana tafiya kamar kowa..! Kana Mgana kamar kowa! Kaci abinci da kanka..Bayan ka zabi Duk Abunda kake so..! Ka saka kayan da Ranka keso..! Komai zakayi na Rayuwa yau da kullum kana ma kanka ne..! Basa Tunanin kaima Allah ne ya Dora maka..? Bazan bari su Rabamu ba Ina tare dakai Muddim rai.."Tafada tana Kara Rumgumshe,lokaci daya tana Sharemai Hawaaye

Ba wanda magaganun Aneesa basu kashemai jiki ba,Barin ma Daada da Anty Rahila hawaye Sukeyi Cikin Tsausayin Halin da Bello yake ciki,Mama falmata Dake tsaye taji Zuciyarta ta karye kawai sai ta Durkusa gaban Bello Ta Riko Hannunsa tana Fadin"Kana son zama da Aneesa..? Kallonsa ya maida kanta Lokaci Daya ya gyada mata kai Cikin Taruwan Hawaye,mirmishi tayi kafin ta saka hannu ta Sharemai Hawaye tana Fadin"Kadai na kuka..Bamu zo nan,domin mu Raba ku ba..Ba kasafai nake shiga Sha"anin Aneesa ba,ammh yau tsausayinka yasa na Shiga,koda Aneesa bata son zama dakai zan Tursasa mata ta Zauna dakai Muddin Rai ballatana itama tana son zama dakai saboda Haka,ku zauna tare  Har Abada ina muku Fatan Rayuwa mai cike da Farinciki har gidan Aljannah Firdausi.."Tafada itama kwallah na Zubomata Daga Aneesa har Bellon Fuskarsu Ta Nuna Farinciki kawai sai Aneesa Ta Shiga Sharewa Hawaye tana Fadin"Nagode mama...Yau ce Rana ta Farko da kika Taba Shiga Sha"anin Rayuwata...Kin kuma Shiga alokacin Daya kamata..Nagode mama.."Take fada tana kuka lokaci Daya da Dariya.

Gabadaya kowa sai da Kwallah ta kawomai cikin idanuwa Ya Muktar baya ya juya yana Share kwallarsa,Anty Rahila ce ta matsa Kusa da Aneesa tana Fadin"Anee tashi na kama miki Shi mu maida Bello kan kujera.."Tafafa Tana Share kwallarta itama,cikin sauri Aneesa ta mike Anty Rahila da Daada Har da Mama yana Suka taimakamata suka maidashi kan kekensa,Aneesa bata rabu dashi ba, kusa dashi ta Zauna Lokaci daya tana Kamkame hannunsa Guda Daya,shima lamgwabe kai yayi miyau na Zuba Daga bakinsa ammh Cikin ranshi Farinciki ne.

Jikin kowa asanyaye ya koma ya Zauna ya Ali ya Saki Ajiyar Zuciya yana Fadin"Tabbas Mama Falmata tayi gaskiya...Ko abaya bamu da Niyyar Raba Auren Aneesa da Bello koda itace ta Nuna batason zama dashi..Muktar kayi hakuri Duka Hujjojinka masu kyau ne ammh karka damu mu mun yarda Aneesa tacigaba da Zama da Bello amtsayin Mijinta,in ya warke Alhamdulillah in ma bai Warke ba toh Taji ta gani Dukkansu sun yarda zasu Rayu da Juna Ahaka ka cire Tunanin Cutar da wani Allah da Zuciya yake amfani.."Ya muktar ya Share Hanci yana Fadin."Bansan da wani baki zan muku godiya ba...Kun mana Abunda yan"uwanmu suka gagara yimana...Allah ya saka da alheri ya kuma bar zumunci dama ina alhinin  yadda Rabuwar Aneesa zata kaya da Bello domin Dukkansu sun Shaku da Juna.."

Daada ta muskuta tana Fadin"nima Haka Muntari..Zuciyata na cike da Tsoron Faruwar Haka..Domin bayan Mutuwar Jiki,harda Mutuwar Zuciya zata iya kama Bello Aneesa Allah yayi miki Albarka..Mama falmata sannu da Kokari.."Tafada tana Share kwallah mama falmata batace komai ba,illah ma ta kauda kai kawai tana kokarin maida kwallarta.

Nan kowa ya tofa albarkacin bakinsa Lokaci daya kuma suna bin Aneesa da Bello da kallo wacce ke gogemai baki da gaban Riganan jikinsa na kanfamin Armani,da gefen Hijabinta tana mai mgana kasa kasa,cike da tsausayi Ya Sunusi ke fadin"Duk Abunda kaga Allah yayi shi...toh ka saka ido zai nuna ayarsa Afili."Yafada yana kallonsu shi da kanshi yakeji acikin ransa wanda yayi sanadiyar raba wannan ma"aurata toh Allah bazai barshi ba.

Ana Shirin tashi taron,Domin su ya Ali sunce bazasu kwana ba,Aneesa tace"Don Allah ina neman wata alfarma..."Gabadaya suka kalleta suna jiran mganarta Ya Muktar ne yace"Wata alfarma kuma Anee..?

Bello ta kallah kafin ta maida kasa tana Fadin"Ku mana alfarma mu koma gidan mu na Kano da Zama,zamu fi sakewa achan...Shima kuma zai fi jin dadin hakan domin yana kaunar garin kano sosai.."Tafada tana kara Kallon Bello ido ya Lumshe mata Alamun Hakan yayi daidai.

Ya muktar yayi Shuru kafin yace"kano kuma Anee..?Baki tunanin zamanku anan cikin yan"uwa kamar baifi ba.."Kai ta girgiza kafin tace"Yafi mana ya muktar ammh ka kalli Fuskarsa zaka ga yana Farinciki sosai..Don Allah kar kace A"a kaji.."Tafada tana Hada hannuwanta cikin Sauri Daada tace"Mganarta gaskiya ne,Matsayin mata da miji suke kuma Zaman Aure suke..Bazasu daumawa tare damu ba..Ka barsu su koma kano,kila Yafi jin dadin chan zama waje daya ba Dadi.."

Ya Ali yace"Hakane..Kuma Hakan zai ragemai wasu Tunanin kullum kana Zaune waje daya.."Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Shikenan...Ammh Dole Modibbo yabiku Har Zuwa Lokacin da zan nema mai police militry sch Jos,lokacin kun saba da garin sosai.."Daada tace"Hakan yayi ma..Allah ya Kara lafiya.."gabaya aka amsa da Ameen sai da suka rufe taro da Addu"a kafin su tashi matan suka Shiga ciki sukayi sallar azahar,mazan kuma suka Fita har da Bello Zuwa masallaci wanda ya muktar ya turasa,Suna Dawowa suka su Fito,bayan Mama falmata ta kara bama Aneesa wasu addu"o'in tace ta yawaita karantamai Amanar Rasuli kafin ya kwanta Tafiyar Jirgi sukayi daman kuma da Zasu koma ma Jirgin suka bi Zuwa Maidiguri Dagachan zasu Shiga mota Zuwa Borno.

****
Wannan Dalilin shi ya karama Aneesa da iyayenta kima acikin Zuciyar Daada da Ya Muktar sukaji Duk Duniya basu da kamarsu su Abba kabiru ne dama ya muktar ke jawosu inta Bello ne ko Daada ko Ajikinsu suma sai suyi wata ko kira basu yi ta waya ba Yanzu Hankalinsu ya kwanta suna ganin mai basu mtsalan yana kwance ba lafiya babu Abunda zai iya yi Shiyasa lokaci daya Shifa da Abba garba Suka cire fargaban watarana Bello zai iya maka su ga Hukuma Tunda bashi ma da lafiya ta kanshi yake.

Hashim ne ke zuwa dubashi in yasamu lokaci shima ba sosai ba,matarshi ko Sau biyu ta taba Zuwa Zubaida kuwa sai D'ayan datazo bata dawo ba dama son bana Allah da Annabi bane na tsabar kyanshi ne,kuma yanzu Babu amfani Tunda ba ma mora,sai dai bare ne ke tafe Zuwa dubashi kowa na kawo nashi Taimakon,Sani da Aminu sune aminin kwarai ga Bello cikin kowani sati suna Hanyar Abuja Duk da Aminun zai Fara Koyarwa da University of lagos kwanan nan ammh hakanan yake Fizgan lokaci yana Zuwa,kasim kuwa ko Sau daya bai taba Zuwa ba,Duk da yana da lbrin duk halin da Bello da Aneesa ke ciki,abakin Abba kabiru ko Hashim sai ya kirasu yana Dukan Ruwan cikinsu Har Ya Muktar din yana ma haka ya kirashi yana Tambayanshi ya Bello..? Aneesa na nan tare dashi,Abun yana matukar bashi Haushi ganin Shuru Target din shi bai yi aiiki ba,shiyasa yayi lambo yana kara Tunanin ya kamata kota karfin tsiya ne Aneeea ta Zama tashi,wacce ta ma manta da wani Hallita wai kasim.

Tun washegarin Tafiyar su Ya Ali Modibbo da mallam inuwa suka Dawo,da sakon Baffa Hardo Aneesa Aka damkamawa bayan an mata karin bayani,gefe guda kuma tana ta Shirin komawarsu kano haka kurum takejin gwara su koma chan suyi zamansu kamar zasu fi jin dadi,Kayansu ta riga tagama Shiryamusu Sauran kayanta ma Ashashen Bello taje ta kwaso,duk da bata Diba da yawa ba,Tunda suna da Wasu achan ana gobe zasu koma chan ta yima Bello aski ta gyaramai kai da Sajensa ta askemai gashin jiki tas,itama tayi Tsifa Alheri ta mata kalaba,bayan angama tazo tana Nuna ma Bello ya Dinga kallo acikin ranshi yana ta yabawa Sabawar datayi Dashi yasa take Fahimtar wani Abu Game dashi in yana son Abu ta Fuskarshi take ganewa toh Ranar ma ta gane yana son ta bar kanta abude karta maida dankwalinta,haka kota Zauna sai in zata Fita ne sai ta saka Vail ta Rufe kanta.

Washegari suka koma kano Ita da Modibbo da Anty Rahila da Daada ,hibba da junoir suka rakasu,Tuni Modibbo yazoma Ya Muktar Da takardunsa shikuma yayi mai alkawarin zai cikamai burinsa,Ya muktar bai bimu kano ba,Ranar ma yana Zaria yazo Jaji passing out,Tun kafin suje Aminu ya kai  kanwarsa Raihana taje gidan ta gyara ko"ina hatta kichen duk angyara an zuba sabon cafane an zubar da wanda na bari Duk sun Rube,abinci kuma Ammi ta Dafo suka zomana Dashi bayan mun Sauka Salihu Maigadi kuwa baki har kunne yana ta kwarara ma Bello Addu"ar samun lafiya.

Basu samu komawa Aranar ba sai Washegari ammh kafin su wace sai da suka biya gidansu Aminu suka gaida Ammi kana suka Wuce su kabar ni Daga ni sai Modibbi wanda muka sauke cikin Bedroom din Falon Farko koda Suka tafi ma Bello na Haraban gidan Uncle Aminu da Modibbo sun Fita dashi Suma sun saka Fararren kujeru suna hira Lokaci Daya suna Shan iska ko Bello baya mgana ammh kallo Daya zakamai ka Fahimci yana cikin Farinciki.

Niko ina cikin gida ina Jeramana kaya Cikin Wardrope tare da wasu kayayyakinmu,Duka Ruwan Addu"an munzo dashi harda su na Fito dasu Kusa Tunda Amfanin kullum ne,bayan na gama kuma na Fada kichen nema mana Abunda zamu ci daddareg gefe daya kuma Hankalina kwance Tunda Bello na tare dasu Modibbo..


Ki biya ki karanta cikin Salama...



*Anitha..*
8/19/20, 11:22 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

 
*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

        *🅿�27*

Farar Shinkafa Na dafamana da Miyar ganye,sai na Dafamana Zobo na saka cikin Fridge,kafin na karisa girkin ya riga yayi sanyi Fruit na yankama Bello Domin yafi sonshi sosai.

Bello saboda ganin Uncle Aminu ne yasa ya bari Modibbo ya bashi abinci har ya karba,shikanshi Moddibon yana ta mai Tsiya,Sai dai kawai ya sakamai ido,Nan suka Wuni tare Ko sallah zasu tare suke Tafiya da Bello daya ke akwai wani masallaci nan kusa damu nan suka turasa suka je,sai yammh kana Uncle Aminu yamana Sallama ya tafi kan gobe zai dawo suyi sallama da Bello jibi Zai wuce lagos.

Washegari dayazo mai sallama bai Tafi ba sai da ya Daukesa suka Fita cikin gari shi da modibbo Sun dan jima kana suka Dawo gidan,Bayan Uncle Aminu yayi muna sallama kan sai bayan Wata Daya zai dawo ammh kanwarsa Raihana zata dinga Zuwa tana taimakamin Tunda tana gida bata Zuwa ko"ina Tun bayan candy dinta,Ba wata babbace kamar sa"a tace ko zan girmeta bai wuce da Wattani ba,kullum zata zo mu wuni tare muyi girki tare tatayani na gyara gidan muna yi muna Hira Dayake babu Ruwanta tana da Kirki sosai,ta gayamin cewa School of Hygen take son Shiga da Zarar Result dinsu ya Fito,Ni kuma nace mata namu ya Fito ban Duba bane dayake na abayanmu suka Rubuta nasu jarabawan kenan ina gabanta da Shekara Daya kenan.

Rayuwarmu muke gudanarwa cikin Farinciki Sosai Nida Bello,Raihana da Modibbo na Debemana kewa,Mu zauna muyi ta Hira Bello sai dai ya Dinga bin mu da ido,Sai yammah tayi kana Modibbo zai maida Raihana gida amotar Bello Dayake Tun Muna Abuja Mallam Inuwa ya koya masa Tuki,Bama cikin matsala Nafara maida jiki na,duk ba Ban koma kamar da ba,shikanshi Bello ya kara kyau sai dai Ramar Jiki kawai na ciwo,Koda yaushe y muktar cikin kiran mu yake awaya yana tambayanmu ko muna cikin mtsala,hakama Daada itama kullum cikin kira suke suna tambayanmu lafiyanmu Hankalinsu ya kwanta jin muna cikin Farinciki ba wata mtsala.
 
Haka zan tsala wanka nayi kwaliya Shima namai gayu Modibbo da Raihana suyi ta kashemana Hotuna suna mana Dariya,Niko a jikina domin na gama Sabawa da mijina Fiye da kowa na Duniya Sirrinsa nawa ne Hakama Sirrina nashi ammh haryanzu bana iya kallonsa Tsaf sai dai na dinga Runtse Runtsen ido Ranar bayan na gama mai wanka zan ciremai gajerun wando na Runtse idanuwana cikin Mistake hannuna ya taba mahood dinshi jin na taba abu kamar icce ya sani bude ido Abunda na gani ne ya Tsorata ni na Kusa sakin ihu jikina na kyarma sakinsa nayi Na Fita Daga Tiolet din Da Sauri kirjina na Bugawa Ranar wankan daban karisa mai ba kenan modibbo ya karisa mai ya shiryashi,kuma Haka na Wuni ban bari mu hada ido ba duk ko na cin kallona dayake yi,Kullum Dare kuma bana kwanciya sai munyi karatun alqur"ani bayan mungama sai na Shafemai cikin da Ruwan zamzam din da Baffa Hardo ya aiko mai dashi,,in zamu kwanta gefe nake kwanciya,ammh saboda ina da mugun barci kafin gari ya waye na gama hayowa cikinsa na kamkamesa ko Tunanin bai da lafiya bana yi toh ina na sani Tunda Cikin barci ne sai gari ya waye na Dinga Dariya ni kadai,kuma bai hana gobe na Sauya wajen kwanciya ba ammh Duk da Haka sai na isa gareshi,na saba kwanciya ina Juye juye Kamar wata yarinya.

Muna yawan Fita Yawan Shakatawa Nida Modibbo da Raihana Watarana ma har gidan Ammi muke zuwa mu Wuni sai yammh mu dawo duk domin muyi keeping Bello company kuma Abunda na lura yana jin Dadin Haka,wani lokacin ma Restaurant muke zuwa muci abinci ayita kallonmu ana Mamaki ga Mutum har mutum aamh babu Lafiya,masu tsausayi kuma suna tayamu addu"a acikin Ransu,Cikin Haka ne Watarana muka Fita Shooping bayan mun je wajen Siyan ice cream,tunda ina bala"in son kayan sanyi,harda gashshiyar kaza,da Kifi ina sonshi sosai domin modibbo na Fita ya siyomana watarana

Shopprite muka je bayan mun gama Siyan ice cream sai muka Shiga Al-pen store,Raihana da Modibbo na baya ni kuma ina gaba Ina Tura Wheel chair din bello,jikina sanye nake da Doguwar Riga kirar bahrain,Baka nayi Rolin da Vail din Rigar karamar jakace Rataye agefen kafadata,sai kafata tana sanye da Ruffafen takalmi mai kyau da Tsari Fuskata babu kwalliya ammh nayi kyau sosai,hannu na sanye da agogon Fata na gucci,Bello ma na Shiryashi ciki wata Shadda saky blue sakamakon Ranar Jumma ce,Riga da wando dinkin zamani kansa kuma na aza mai Hula zanna bukar kafarsa kuma Takalmi ne baki budadde na Fatar damisa,Hannunsa sanye da agogon Fata na kamfanin Rado,Kallo daya zakamai sai ka kara saboda yadda yayi kyau sosai Fuskarsa Na fitar da Annuru kyau da koshin lafiya.

Muna tafe ina Duba Wasu jerin turaren miski,na Sunkuyar da kaina ina Fadin"Na siya mana miski..? Na fada ina kallonsa Kallona yayi kafin ya Lumshe idanuwansa,dariya nayi kawai na Daga hannu zan Dauko ni ban ma Lura da mutanen dake wajen ba sai ji nayi ance"Wanake gani kamar Mr bello..."Aka Fada Daga gabanmu cikin Sauri na Daga kaina ina kallon mai mganar Ido na Zaro ina kallonta Lokaci Daya nace"Anty Jidda madaki.."

Nafada cikin Bayyana mamakina,Hankalinta na wajen Bello sai kuma taji muryata cikin Sarkewa Numfashi tace"Anee...Aneesa Bukar Bulama u again..",Tafada tana nunani cikin Farinciki muka isa ga Juna muka Rumgume,Cikin Fara"a Ta Dagoni tana Fadin"Anee kin girma fa sosai yanzu anyi hankali ko..? dariya nayi mata ina gaida wanda suke tare har su Modibbo suka kariso hannu na ta Rike tana Fadin"Meye haka Anee..? Yana ga Mr bello kuma bisa Wheelchair..?

Tafada muna kariswa gabansa niko sai binta da kallo nake ganin ta kara kyau ta zama babban yarinya,kafin na bata amsa Modibbo yace mata"Ayyah...Baya da lafiya ne Tun bayan wata Takwasa Da suka Suka wuce yake Rayuwa Ahaka.."Ido jidda ta Zaro tana kallon Bello lokaci Daya tayi kasa Agabanshi idanuwanta na Taruwa da kallo cikin Sarkewar murya tace"Innalillahi meya sameshi Hatsari yayi..?

Na girgiza mata kai kafin tace"Ba daya...Daga dare zuwa safe ya tsinci kansa cikin wannan Hali watansa uku akasar india an Dora misa Gwaje gwaje da kuma Ayuka har guda biyu ammh kuma babu wani cigaba shiyasa aka dawo dashi gida ana gwada na Islamic har Allah yasa a Adace..."Hawaye suka zuboma jidda ta dago tana kallon Saurayin da Suke tare Hannunshi ta Riko tana Fadin"Habibi Da"iman kalleshi shine Mr bello dana ke baka lbrin He si my Fisrt luv shina fara so

Please Login or Register in order to submit comment