Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rigan barci da Hijabin ta Fito,

Keken da Matsar gefe tana Fadin"Kana jin barci..? Ya kada mata ido Tashi tayi tana Fadin"Toh muyi karatu kafin mu kwanta gobe da Safe kuma ma cigaba da lbrinmu ko..?Ido ya Lumshe mata Mirmishi tayi tana kallonsa Har ta Dauko karamin Qur"aninta Gadon Ta Hawo gefensa ta Zauna ta Bude Tana Fadin"Bismillah mufara ka dinga yin naka acikin Zuciyarka kaji ko.? Ido ya kada mata taciga ba da Fadin"Kullum mukayi Waya da Mamata tana Fadamin cewa na Laminzi karanta Qur'ni koda yaushe,Shi alQur"ani mganin kowani Waraka ne"

Kallonta kadai yakeyi kansa yayi gefe Bisa Filon Ta Bude Suratul Maryam Tana Fadin"Suratul Maryam zamu karanta.."Daga Haka tayi Bismillah ta Fara karatun cikin Siririyar Muryanta mai cike da gardi Cikin Zuciyarta tana kara godema Bello Domin Shi ya Jajirce Har ta samu wannan Ilimin,Kullum Suna karatun islamiya lokacin Suna Mkranta sai da tayi Haddan Talatin,kafin su gama Tana ta karatu Shima cikin Zuciyarsa yake binta Cike da Farinciki Saboda gajiyarvtafiya yasa Lokaci kadan barci ya kwasheshi bata sani ba sai Zuwa chan ta Juyo ta ganshi ya Bingire kai yana Sauke Numfashi Miyau ya bata Gefen bakinsa Mirmishi ta saki kafin ta Saka Gefen Hijabinta ta Share mai Miyan daya Zuba Saukowa Tayi Daga kan gadon Ta maida Qur"anin bisa Side Drower din gadon,Sake komawa Tayi kan gadon ta Zauna kusa dashi ta karanto Addu"ar barci ta shafamai Duka Jikinsa Itama ta Shafa,inda kafafunsa suke ta maida kanta Bayan ta rage Hasken Dakin,itama bata wani Dade ba barci ya kwasheta mai Dadi

Karfe 4am na Asuba modibbo Ya Shigo Shashen Daada Lokacin Daada ma ta Dade da tashi tana ta salolinta knooking din Dayayi Shi ya tada Aneesa Shiko Bello ya Dade Datashi Daga kwance,Aneesa kuwa cikin barci ta Cukwikweye Kafafunsa Ta yi Filo Dashi Bata sani ba gashi tasakarmai Nauyi,bai iya Motsa kafar ba,ammh Aneesa ta gajiyar dashi Tashi tayi tana Salati ta Kunna Hasken dakin karaf ko Suka Hada ido kafarsa ta bi da kallo Lokaci Daya ta Zaro ido ganin inda ta kwanta Har ya Tara Jini Tsausayinshi ya kama ta abunka da Farin mutum Shafa wajen Tayi tana Fadin"Am Srry Bansan na Danne maka kafa ba wayyo.."Lumshe ido yayi ya Bude yana kallonta itama shi take kallo tana Fadin"Yanzu shikenan ko Cutar dakai za'ayi bazaka iya mgana ba..? Take fada tana Dauke kwallar idanuwanta lokaci Daya ta Sauko Daga gadon Hijabin Jikinta ta maida wanda ya ya zame Saboda barci kofar ta Bude Modibbo ya Shigo yana mata Tsiyan Taji dadin barci da Baffalensa ta kasa tashi.

Bata mai mgana ba Mirmishi kadai Tayi mai,Ita ta Taimakamai Suka Daukosa Daga kan Katifa zuwa Bisa Wheelchair,Abun mamaki bai bata Jikinsa ba Modibbo ke Fadamata bai cika yin Fitsari ba ko wani abu sai ya kwana biyu saboda bai da ciye ciye,Toilet suka Shiga Dashi Modibbo na gwada mata yarda yake mai wanka Dagosa yayi ita kuma ta taimaka suka ciremai jallabiyan Jikinsa,Runtse ido Aneesa Tayi sanda ya Zare mai Boxers din jikinsa,saboda bazata iya kallonshi Naked ba,ko Kirjinsa kasa Kallo Tayi ganin ko"ina ya Cika da kananun gashi,baya ta Juya musu Sadda Modibbo kemai Wanka Shiko Tsiya yake mata yana Fadin"Ashe baki son ladan.."Rufe baki tayi tana Fadin"Ina so ammh sai dai na mai da kaya ajkinsa bazan iya ganinsa Ahaka ba.."Dariya Modibbi yayi yana Fadin"Ba"a wanka da kaya ai...Mijinki ne bawani Abu ba kuma lalurace babu yarda za"ayi.."Itadai batace komai ba Kuma bata waigo ba sai da ya gama mai ya gogemai jiki da Towel,Aneesa ta mikamai Boxer dinshi da Vest dinshi ammh bata Juyo ba Bello sai kallon bayanta yakeyi,Sai da ya sakamai kana yace"Sarkin Tsoro toh an gama.."Sai lokacin ta Waigo ita ta mai alwala tace Modibbo ya Tafi zata shiryashi yace"a'a bari ya Shiryasa sai su tafi masallaci tare..Fita yayi dashi Daga Tiolet din itakuma ta maida kofa ta Rufe ta Tube ta Shiga wanka bayan ta saka kayan Bello Cikin kwandon Wanki koda ta Fito Daga wanka Har Modibbo ya Shiryasa ya Turasa Zuwa masallaci Itama manshafawarta ta shafa na olive ta Saka Wani Riga da Sikat yan kanti na kamfanin DKNY,ta saka Hijabi ta Tada Salla Raka"atanul Firjir tayi kafin tayi sallan Asuba bayan ta idar tayi karatun Alqur"ani Har Zuwa Wajen bakwai na safe sai Lokacin Taji Muryansu Falon Daada bata Fito ba gado ta koma ta Haye ta kwanta sai barci bata Farka ba sai Wajen 9am na Safe Shima Anty Rahila ce tazo ta tasheta Kan tazo ya Ali zai tafi,Fita tayi Falon Daada sukayi sallama da Ya Ali yamata Nasiha sosai Yatafi akan Sati mai Zuwa Zasu dawo gabadaya hadda su Mama Yana,Ya Muktar da Tawagarsa,suka rakasa Har Airport kafin ya Wuce Fadar Shugaban kasa suna da Meeting.

Tare suka karya da Bello ita ta Dinga bashi abaki,domin yaki cin Komai ko an bashi sai ya ki karba,ammh Aneesa na Fitowa ya Daina bata rai,Bayan Sungama Karyawa ne Ta Goggemai baki ta Turasa Suka koma Daki ta zaunar dashi kan kujeran Madubi ta saka wani Abun Aski Tana Fadin"Nidai bari na rage maka wannan Gemun ya maida kai wani Tsoho da yarintarka..",Tafada tana Tura baki kallonta yake bai ce komai ba Tsab ko ta Rage mai tamai gyaran Fuska sai gashi ya Fito sak Handsome Mr Bello,Yana ta kallon kanshi Amadubi ita kuma ta Haye saman madubin tana mai Dariya,Bayan ta gama mai ta Kwashe gashin ta kai Cikin Tiolet Ta zuba cikin dustbin din tiolet din ta dawo ta Zauna Agabanshi tana bashi lbrai saboda Samun Waje na Aneesa Harda Tsatsuniya take bashi Har da lbrin Rayuwarta a Borno Da Irin Dukan Data ci Wajen ya Ali tana bashi lbri yana kallonta wani waje tayi Dariya wani waje tayi kuka wani waje harda bata rai chan kuma sai ta Tura baki tana bata Rai,Shidai yana kallonta Zuciyarsa tana cike da Farinciki in yana Tare da Aneesa Shiyasa koda Minti Daya baya son Tayi Nisa Dashi.

******
Bayan Sati Daya da Dawowar Bello,Har Aneesa ta kware Wajen kula da Bello,wanka ne kadai sukemai tare da Modibbo Wani Likacin ma kafin yazo tamai,sai dai bata Ciremai boxer dashi take mai wanka in modibbo yazo ne yake Ciremai ya chanzamai,ammh wani bashi abinci,gogemai baki da komai ita ke Wahala dashi,Tare suke kwana Wani Lokacin Daada ke kama mata su maidashi bisa gado in Modibbo baya kusa,ko Ya Muktar wanda shima ke iya bakin kokarinsa,Aneesa kuwa bata Nuna gazawarta Duk da tana da karancin Shekaru Kowa ita yake Tsausayi Domin Nakasan Miji ba"abu bane mai Dadi.

Baki ta ko"ina sai Zuwa gaisheshi Suke,Su Abba kabiru da Duka iyalansa sunzo Hakama Ya Hashim da matarshi da Zubaida wacce ta Kurama Bello ido cike da Tsausayin Halin Daya koma,Sai da ta Share mai kwallah Zulfa ko da Suka zo Acikin Ranta Hamdala take da bata Aureshi ba Da yanzu ita ce ke cikin Wahala kamar yadda Aneesa ke Dawainiya Dashi,Mutanen Borno ma Sunzo Mama yana,mama Falmata ya Ali,Ya Sunusi,Da matansu da Ya"yansu Duka Suka kwana Daya Suka koma,Sai ga Malaman Chan Jami"ar Bayero,sun sake Zuwa Dubashi har da Dn na Sch din,lalle Bello mai Mutane ne Hatta da Gungun Malamai da Daliban Mkrantan kwatar-kwashi Tare da Jagorancin Principal din Mkrantan Sun zo Dubashi,Haka suka Tafi da kukan Tsausayin Halin da Bello ke Ciki,S.jibiya ma tazo ita da Mamanta Suka Wuni Suka koma Anty Yagana ma tazo ita da Mijinta suka kwana Daya Suka koma Hatta da Sauran yan"uwansa da suka rage na Jikamshi sunzo Duba Bello kowa kuma da Abunda yake Fadi,ana bada Shawaran Ayi mai na Hausa agani ko Allah zai saka adace.

Anty Aisha Tazo Daga kano,itama da Megidanta Hatta da Inna Rukayyah ma tazo Dubashi,Kasim ne kadai bai zo ba Kuma Abba kabiru yamai Waya kan Bello ya dawo Gida yaje Dubashi yace Aiki yamai yawa in ya samu Lokaci zai leko nan ko bai da Niyyar zuwa yanzu Duk da yana son Zuwa yaga Halin da Bellon ya koma yayi Dariya Sosai ammh yanzu Lokaci bai yi ba yadai kusa Lokacin da Aneesa zata koma tashi har Abada.

Mutanen Adamawa sun zo,Mota guda suma Baffa Hardo,wani Tsohon ne wanda yake Mtsayin Yaya ga Daada ya Tsufa Domin gabadaya Kansa Farin gashi ne tunda suka zo ya ke kallon Bello yana Girgiza kai Sai da Zasu Tafi ya kebe da Daada yana Sanar da ita yaga Sihiri mai karfi Ajikin Bello saboda Haka su Dage da mai karatun Qur"ani da kuma Addu'o'i Shima zai koma yayi Nashi kokarin Daada tayi mamaki ammh sanin Baffa Hardo yasan irin wannan Abubuwa yasa batayi mamaki ba ammh yace tayi Shuru da Bakinta da Haka suka koma Adamawa,zuciyarsa cike da mamaki waye yama Jikansa wannan Mugun Asirin.



Ki biya ki karanta cikin salama...

*ANITHA..*
8/19/20, 11:20 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

            *🅿�25*

Baffa Hardo bai gayama kowa ba Shikadai yake ta bincikensa,a binciken da yayi ne ya gano Sihirin Dake jikin Bello mai karfi ne kuma bazai taba Barin Jikinsa ba sai An Hako Abunda Aka binne da rai acikin Rami,kuma babu wanda yasan ina aka Binne wannan Abun sai wanda ya Aikata mugun Nufin Nashi,ko wanda aka Biya yasa aka aikata ma Bello haka domin a nakasa Rayuwashi cikin Nakasa da kasawa

Sai dai ya kira Daada awaya ya Sanar da ita a nemi Ruwan zamzam rika karantamai Suratul Yasin,Falaqi kafa uku Nasi kafa uku,Qul"huwal lahu kafa uku,ayatul kurusiya da Amanar Rasulu kafa uku uku cikin Ruwan Zamzam din arika bashi ya sha kuma arika Shafemai jiki dashi Safe da maraice,Shima Dagachan nashi Bangaren ya Dage danashi Addu"an Har Aga Abunda Allah zaiyi ammh al"amarin ya wuce Misali,Sihirin mai girma ne anyi aiki akan Sihirin Sosai.

*****

Duka Wahalan Dawainiya da Bello Aneesa ce keyinshi Wani Lokacin sai in ta kasa ne take Kiran Modibbo ko Daada su Taimakamata,wani wanka ne cin Abinci wanke mai jiki in ya bata babu Abunda batamai,Cikin Lokaci kankani ta kara Zabgewa ta Rame kamar ba Aneesa ba ta kara yin baki saboda Wahala ammh ita ko Ajikinta Alokacin Takejin ma wani karfi na Zuwan mata,Babu wanda baya Tsausayamata ya muktar yayi yayi ta barshi Modibbo ya Dinga kula dashi taki dole aka kayleta Shima gogan bayason na Modibbo yafison na Aneesa,ko wanka ne in ba ita tamai ba baya sakin Fuska Ranar Haka zai Wuni yana bata rai In ko Aneesa ve tamai ko Fuskarsa tana bayyanar da jin Dadinsa,Duk da Shakuwar da sukayi su kwana tare su tashi tare bai sa Aneesa ta saba da kallon Wasu gangan jikinsa ba ko wanka zatamai da Boxers dinsa zatamai sai ta gama ta Runtse idanuwanta kana ta Zame mai wando kuma idanuwanta na Rufe zata Rufa mai Towel ta gogemai,jiki tana yi tana Runtse ido ita adole bazata kallesa ba Shiko sai dai ya kalleta yana Dariya acikin Zuciyarsa,ko abinci taresuke ci tana bashi tana mai Hira Wani Lokacin taita mgana ya Kuramata ido baya Ko son Kyaftawa sai tayi Fushi tajuya baya Tana Tura baki,sai ta Huce don kanta ta juyo tana Hararanshi Shidai yana ganin Rayuwa,Kullun Dare basu kwanciya sai sunyi karatun Qur"ani kafin su kwanta kuma ba laifi ita tana ganin Chanji Tunda yanzu ya Rage karkatar da kai da Zubar da miyau ammh bawai ya bari Duka bane,Ruwam zamzam kuwa bata mantuwa kafin su kwanta sai ta tofa Addu'o'i aciki ta Safemai Jiki dashi itama ta Shafe Ajikinta kafin su kwanta,kowa ya Fidda rai da Bello zai Taka itako Tana ji Ajikinta Cewa Watarana Bello zai Taka da Kakafunsa.

Sun Shaku da juna Tare da matsanancin Son juna batare da sun sani ba,In akwai Abunda ke saka Bello yaji Ransa na kuna toh Yaga Aneesa na hawaye ko kuma yaga Ranta ya baci yanzu nan idanuwansa zasu kada suyi ja yayi ta karkace kai yana zubar da miyau,Itama bata kaunar ganinshi Haka Wahala dashi take sosai,Haka zata zauna tayi ta bashi lbrai harda lbrin Irin Wasikun da yanmatanshi ke rubutamai,Su aikota dashi tana yagawa Tun Suna Mkranta,shiko bai iya mgana sai dai kawai ya sakarmata ido yana kallon Siririn bakinta wanda yake matukar Burgeshi yana Bala"in so yaga Aneesa na Tura baki Tana mishi kyau sosai Shiyasa yake kunnata sai ta bashi abinci yaki Bude baki ya tsaya yana kallonta yanzu zata Hau Turamai baki ko kuma tana mishi Hira ya lumshe ido kawai yana jinta yanzu zatayi Fushi Tatashi ta Haye gado tana Tura baki Shiko sai dai ya Bita da Ido yana Mirmishi Cikin Ranshi.

Ko Wanka fa Ta Fito inzata Shirya sai ta Juyar da kekensa Ya kalli Bango kana zata saka kaya Daga baya kuma sai ta dinga kallonsa tana Fadin"Rufe idonka kaji tunda nima banta kallon ka ba ."Dariya yake cikin Ranshi sai yayi kamar ya Rufe ido yana Satar kallonta ta gashin idanuwansa,Aneesa nada Surar jiki mai Rikita Duk wani Lafiyayyan Namiji mai Lafiya,Ranar da Bello yaci karo da Aneena Cikin Surarta kwana yayi Cikin Zazzabi da Ciwon kai Saboda kukan Zucci yana Tunanin Tabbas Watarana Za"a iya Rabashi da Aneesa Tunda bazata Dauwama Ahaka babu Abokin Debe kewa ba shi yana kwance komai sai dai ayimai bashi da lafiyan dazai kare mata Dukkan Hakkinta,Kwana Aneesa tayi kuka jin jikinsa yayi Zafi,sai da Safe Ya Muktar ya kira likita Daga Specialist hop Dr.barau wanda ke Zuwa Duba bello Kowani Bayan mako Biyu.

***
Wata Biyu da Dawowa da Bello, gida Yan"uwa da Abokan Arzuka suna iya bakin kokarinsu wajen zuwa Dubsshi Sani kuwa cikin kowani sati Daga kaduna yana Hanyar Abuja zuwa Duba bello,Kamar dan"uwa haka yake kallon Bello da Tsausayib yadda Rayuwarsa ta koma Haka,Barayin Borno kuwa suma Lokaci bayan Lokaci Ya Ali da Ya sunusi suna Zuwa Dubamu,Su Anty yagana kuwa da su mama yana koda yaushe cikin waya suke kowa zai bada shawaran acigaba da addu"a in da rabo sai Bello ya warke kamar bai taba ciwo ba.

Uncle Aminu ya Diro Daga Kasar Spain bayan yagama Duka Karatunsa,Kwanansa Biyu da Dawaowa ya Diro Abuja dama Bello na cikin Ranshi Tun Lokacin Daya Daina samun Wayarsa,wacce aka barta tana chan kano,Mugun Labri da kuma Halin Daya Tarar da Amininshi ya sakashi Zubba da kwallah,haka ya Durkushe gaban Wheellchair din Bello yana kamkame da Hannayensa yana kuka,shi kanshi Bello ganin Aminun ya tuna mai da Rayuwarsu ta baya Shima sai Hawaye,In Aminu ya kalli Bello sai yaji kamar ya Rushe da kuka haka ya Dinga Nunamai Hotunan da sukayi Lokacin suna rayuwa amtsayin malaman mkratan Kwatar-kwashi Bello na Share kwallah shima yana Sharewa,sai lokacin yaji lbrin Auren Aneesa da Bello Daada ke karantamai ya Dade yana mamaki da Jinjina a"alamarin Ubangiji ita kanta Aneeesa sai da ya Tsausayamata Domin Hakika dukkansu Ababen Tsausayi ne.

Kwana D'aya yayi ya juya kano ya labartama Ammi komai Washegari ya Dawo Tare da ita,Itama ta jinjina lamarin sosai sai da tama Bello kwallah tana Tuna sanda yaje gaisheta na karshe da kafafunsa,Itama tabama su Daada Shawaran bata jin Ciwon Bello na Asibiti ne su mike Tsaye ga Neman Taimako su kuma Dinga Tofamai Addu"o"i Suna shafemai jiki dashi basu kwana ba Aranar suka koma cike da Alhini.

Washegari kawai sai ga Anty Nafee ta iso Abuja Daga ni Har Anty Rahila munyi mamakin ganinta domin kowa yazo banda ita kuma ko awaya bata kira kowa ba Haka Aka Sauketa Cikin Farinciki Lokacin data shigo Shashen Daada ita da Anty Rahila, Ina Falon Zaune kan kujera Bello na saman Wheelchair dinsa ina bashi ruwa yana Shan Rabi,rabi kuma yana ta Zuba ta gaban Rigar Yadin dana sakamai Harda Hula,da hanzari na Dauki Tissue ina gogemai sai gata ta Shigo koda na gaisheta sama sama ta amsa tana karemin kallo Daada na wajen ammh bata lura da ita ba tafa Hannun takamayi lokaci Daya Tana Fadin"Innalillahi Aneesa kinga yadda kika koma kuwa kamar wata kwarangwal....Haba ina Adalci anan ace ke zaki dinga Dawainiya da katon gardi kamar wannan Da babu Abun mamora tare Dashi.."

Tafada tana Nuna Bello cikin Tabe baki,Ba Aneesa kadai ba Hatta Anty Rahila sai ta Muzanta Niko idona Tuni yaciko da Hawaye saboda naji ta tozartamin miji itakuma Anty Rahila kunyar Daada ne ya kamata Cikin karfin Hali Tace"Anty Nafee baki gaida Daada  ba.."Sai lokacin ta Lura da Daada Cikin Son baras da Zencen ta Zauna suna gaisawa da Daada wacce ta amsa mata Cikin sakin Fuska kamar Babu Abunda ya Faru nan ko Cikin Zuciyar Daada kwata kwata bataji Dadin kalaman Anty Nafee ba Tunda Bello dai lalura ce ta sameshi ammh ada kowa yasan Duk inda Namiji yakai toh Bello ya Zarce nan..

Shi kanshi Bello kallon Anty Nafee yake da Fararan idanuwansa yana narkewa da bacin rai,Gabadaya da Aneesa ta kalleshi sai ya bata Tsausayi Shima ba Haka yaso ba Komai ya Faru da bawa Daga Allah ne,Kama Keken Bello tayi ta turashi Zuwa cikin Dakinta Suka Bita da kallo Anty Nafee kuwa baki ta Rike tana bin Aneesa da kallo Cike da mamaki ganin tana so ta kara sakin wata mganar ne yasa Anty Rahila ta tattarata suka koma Shashenta karta kara kunyata ta gaban Daada,Allah ma ya taimaketa Muktar baya nan sunfita tare da Modibbo.

Duk yadda Aneesa taso ta Tsaida kukanta sai da ta Sakeshi Suna Shiga Dakin ta Zame bisa kafafun bello ta Fashe da kuka Tsurama kanta ido yayi wanda ke Daure da Dankwali Atamfa kitson kalaban Dake kanta sun zubo Daga kafadanta Zuwa bayanta,so yake ya Daga hannu ya dora bisa gadon bayanta ya lallasheta ammh bazai iya ba nan da nan idanuwansa suka kada sukayi jawur kawai sai ya shiga maida Numfashi sama sama alamun Bacin Rai da damuwa.

Sai tayi ya isheta kana ta Dago tana Goge Hawayenta,Kallonsa cikin Tsausayawa da Kauna mai Tsanani Cikin Muryan kuka tace"Kayi Hakuri da Abunda Anty Nafee tace..Har Abada ni Aneesa bazan taba gajiya dakai ba..,ai ba kai ka Dorama kanka ba Allah ne ya Doramaka saboda Haka ina tare dakai mutuwa ce kadai zata rabamu kaji karka damu don Allah..."

Bata ankara ba kawai taga Hawaye suna Zubomai mikewa Tayi Tasaka Hannuwanta Duka biyu tana Sharemai Hawaye tana Fadin"Bana so...Kabari nima in ina kuka sai ka bata rai,kadaina kuka kaji ko ina tare dakai mudum rai.."Tafada Lokaci Daya tana Gyaramai zaman Hulan kansa Mirmishi tamai tana Fadin"Don Allah kamin mirmishi ko Sau Daya Kaji B.Luv dina.."Tafada tana Sakarmai wani kallo,cikin idanuwansa yake kallonta Lokaci daya kawai taga kamar Yayi mata mirmishi Tsalle ta Daka tana Fadin"Wlh kayi min...plz dan sake min nagani.."Wannan karon lumshe ido kawai yayi ya bude yana kallonta,Dariya ta saki tana Kallonshi Cikin so da kauna tace"Kaga kyan da kayi yau..?Bari na maka Hoto kagani.."Wayarta ta Dauko ta Shiga Daukansa Hotuna kala kala,Ta zagayo ta bayansa Ta Dinga Daukansu Self tare,tana Dariya Sunyi bala"in kyau,Wajen tazo ta gabanshi sai Sikt dinta ya Sarke cikin kafafun keken kawai sai ta Dawo da baya ta Fada Bisa Cinyarsa,cikin kunya Ta Dago tana kallonsa Shima ita ya kafe da ido yana jin kamar su Dauwama Ahaka,kallonsa take cikin Wani Shauki mai wuyar Fassara bata san Lokacin data Sulalar da kanta bisa Kirjinsa ba tana Sakin mirmishi ita kadai Shiko Cikin Ranshi ji yake dama yana Da Hannu daya ya Rumgume Aneesa ko zai samu sauki radadin Daya keji acikin Zuciyarsa Sun Dade ahaka kafin tatashi tana kakkare Fuska wai ita kunya kallonta kawai yake cike da Sha"awa.

Acikin Bedroom din Anty Rahila kuwa Anty Nafee ce keta Fada tana Fadin mganganu wai Rahila na gani ana cutan Aneesa Tayi Shuru suma su Ya Ali sunyi Shuru da bakinsu,Ta kalli Anty Rahila tana Fadin"Kunfa san zamansu bazai taba yuyu ba Aneesa mace ce iya mace kuma mai lafiya,zama da Wannan Mijin nata a nakashe bazai yuyu ba tana bukatar kwanji Namiji da kuma Wanda zai bata kwan Haihu in akayi Shuru topah Haka Aneesa zata Dauwama tana Wahalan gardi ita bada Jin Dadin Aure ba kuma ita baga Haihuwa ba Wahala haka zata taru ta kasheta kuma in akayi Haka tsakani ga Allah ba"a mata adalci ba.."Tafada tana Gyada kai kamar wata kadangaruwa.

Anty Rahila Da Jikinta Duk ba Dadi da manganun Anty Nafee Tace"Kidaina Fadin Haka Anty Nafee Insha Allahu Bello zai Warke kuma da kike mganar Wahala dashi Aneesan ne Taki mana ammh Har mai kula dashi fa Muktar ya Dauko Daga Adamawa yana nan Tare damu Modibbo..."Cikin Kallon Banza Anty Nafee tace"Dillah yiman Shuru Sakarya Daga ke Har Aneesa baku da Wayau ita kuruciya kedamunta ke kuma fa..? Wato kar kiyi mgana aga laifinki ko..? Toh tsakani ga Allah ko Baba keda rai bazai bari acucu Yarinya ba Tunda Ita bata da Wayau mu sai mu kyale Rayuwarta ta kare ahaka yakamata dai aduba wannan lamarin gaskiya.."Itadai Anty Rahila Shuru ta mata bata kara mgana ba.

Ya muktar Dake kofar Bedroom din Anty Rahila ya Dawo kenan ya Shigo ya sanar da Anty Rahila zai Tafi Lagos yanzu sai ya iske suna mgana da Anty Nafee sai ya Dagata daga bakin kofar sai da yagam jin Duk manganun Anty Nafee,wanda sai da suka kusa sakashi kwallah,baya ya koma yana Dafe kanshi ba Shakka gaskiya Tafada In har Aka bar Aneesa da Bello ahaka ba"a mata adalci ba kuma an cuci Rayuwarta.

Shashen Daada ya isa ya sameta Cikin Bedroom dinta,ganinshi cikin Damuwa yasa ta dago tana kallonshi cikin Muryan Tsufa tace"Muntari lafiya kuwa..? kafita lafiya lau kuma ka dawo cikin Damuwa.."?
Gabanta ya koma ya Zauna yana Fadin"Daada na yanke wani Hukunci kuma ina Fatan zaki bani Hadin kai bayan kin Dubi Abun da Fuskar Fahimta.."

Cikin Gyada kai tace"Insha Allahu ina Sauraranka..?yayi jim kafin ya Sauke Numfashi yana Fadin"Daada Na yi Tunani na gani cewa bai dace mubar Aneesa Haka ba Ma"ana kwaruwace da Zalunci muyi Shuru mu barta ta Zauna da Bello don yana Namu ba..Bisa adalci ya kamata arabasu ta samu wani mijin mai lafiya ta aura Shi kuma mu cigaba da Kula Dashi,In Allah yasa yasamu lafiya Falillahil Hamdu ,in kuma Allah bai kaddara zai kara takawa kinga yan"uwanta bazasu sakamu cikin masu zalunci ba.."Yafada cikin son maida kwallarsa.

Shuru Daada tayi Tana kallonsa kafin ta murmusa tana Fadin"Hakane kam mganarka Muntari nima dazu nayi kuka cikin Raina Danaji wata mgana...Sai nake Tunanin Ada fa ba Haka Megidana yake ba lalurace ta Fadamai,ni yanzu Tunani Daya ya zaiji in muka ce zamu rabashi da Aneeea,Alhalin na Lura dukkansu sun Fara Son Junansu barin ma Shi da Baya son kowa kusa dashi sama da ita itace Farincikinsa..."

Tafada tana Share kwallah Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace"Nima na lura da Haka Daada..Bazamu iya godema yarinyar nan ba...Banta Zaton zata kula da Bello Haka ba,Tana mai Dawainiyar da ko Ni bana mai kamarta ammh Duk da haka Hakuri zai yi Modibbo ya cigaba da kula dashi,muna tayashi da Addu"a inda Rabon zai mike sai kiga lokaci Daya Allah yayi ikonsa ammh Dole suyi Hakuri Duka Domin bama kowani bangare Adalci.."

Gyafa kai Daada tayi kafin tace"Shikenan Muntari Allah ya Shigemana gaba..."Mikewa yayi yana Fadin"Ameen Daada yanzu zan Wuce lagos taron mu na Sojojin kasa,sai zuwa jibi zan Dawo,Zan kira ya Ali da ya Sunusi ta waya muyi mgana sai suzo mu hadu mu Warware komai in nadawo insha Allahu..."

Daada ta gyada kai tana Fadin"Shikenan hakan ma yayi...Allah kiyaye Hanya ya kuma Tsaremana kai sai ka dawo..."Da Ameen yake ta amsawa Har ya Fice Daga Shashen na Daada Dakin Aneesa yayi kooking tazo ta bude tana gaisheshi,amsawa yayi ya karisa ga Bello yana kallonsa Cikin Sha"awa ganin yadda Aneesa ta sakamai manya kaya,gabansa ya Tsaya yaDurkusa Lokaci Daya ya Riko Hannuwansa yana Fadin.."Anee ta gayamaka kayi kyau kuwa..? Yafada yana kallonsa.

Lumshe ido yayi ya bude yana kallonsa,Mirmishi yayi mai lokaci Daya ya mike bayan ya saki Hannunshi yana Fadin"Zan tafi lagos sai jibi zan dawo ka kula da kanka kaji ko .? Yafada yana Shafa kanshi,Rumgumesa yayi kafin ya sakeshi ya fice Daga Dakin Aneesa na mai Allah ya kiyaye Hanya.

Falon Anty Rahila ya koma ya kirata Awaya yace ta Fito Falo yana Jiranta sai gashi ta Fito Dauke da Junior bai wani Tsaya ba yadai yagamata ga inda zashi,suna mganar ne sai ga Anty Nafee ta Fito suka gaisa bai Nuna mata

Please Login or Register in order to submit comment