Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dawo Abuja Da Shirin Jibi In Allah Ya yarda zai yo parking Zuwa kano,domin ya kosa ya Daina Shakan Numfashi da Aneesa Yana Cikin Takura Sosai.




Ki biya ki karanta cikin Salama.



*Anitha..*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

  
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_
 
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*
       
*🅿�19*


*KATSINA*

"Achan katsina kuwa Haka Biki Ya Tashi Zuciyiyo Babu Dadi Dangin Umma sai maganganu Suke na An Tozarta Dan yar"uwansu Abba Kabiru yajama Umma Kunni kar karyaji Wata Mgana,Bayan Shida Abba garba Sun Kira Ya Muktar Suna mai Rantsuwan basu san Abunda Kasim ke aikatawa ba kenan da bazasu Taba Fara Shigemai gaba Aneman Aure ba,Sunyi Haka ne Saboda Suna Tsoron Bello Domin Ko Ranar Daurin Aure A bornon Tsoron Nashi ne ya Hanasu Wani Motsin Kirki.

Kasim kuwa Kwana Hudu Tsakani ya Tattara ya koma Kaduna,Shi Haruna Tun Washegari ya koma Kano,dama chan yake sun Rabu da Niyyar sai Sunyi Mgana ta Waya,Da zai Tafi Abba kabiru Yayi mai Fada Sosai kuma yaja kunnansa kan ya Fita Harkan Bello Kar ya Kuskura yace zai Dauki mataki Yaga dai Suma basun Fita bane Duk Ranar Daya makasu kotu yana da Hujjan da Za"a Dauresu har Igiya Tayi Rara bamai Sakawa a Sakosu.

Kasim Jin Abba Kabiru kawai yake kawai Don Mganarsa na Shiga Kunnansa ne tana Fita Domin yaci alwashin Daukan Fansa Akan Bello Domin Bazai kyale Wanda yayi Sanadiyar Kwacemai Aneesa ba,gashi sai kiran Wayanta yake Ba"a Dauka Ranar Dai da aka Daga Anty Nafee ce tamai Zazaga tace karya kara Kira domin Aneesa Tana Gidan Mijinta,Kwana yake Cikin maye Saboda baya Jure Tuna ya Rasa Aneesa Ko ya Hashim kafin su koma Abuja Shima ya Sameshi yayi ta mai Nasiha Ammh kasim Jinsa kadai yake bawai Domin maganganun Suna Shiga kansa ba.

Umma kuwa Da Abba Kabiru kemai Fadan ma yadaina Abunda yake Cewa tayi ya daina ma Danta Fada Ita yaronta baya Neman mata Sharri bello ya Kullamai kuma Allah ya isa Bata Yafe ba,Sai da Abba kabiru Ya Daka mata Tsawa kana ta kama Bakinta Mama Sahura kuwa Duk da Abun bai mata dadi ammh ko Jaje batama Umma Aranta ma Allah ya kara take mata Domin Tafi kowa Nuna son ya"yanta kafin Inna Rukayyah Ta koma kano sai da Sukayi da ita kan Zubaida Kwata Kwata Umma bata iya Siyasar Duniya shiyasa Ko Abba kabiru yake Girmama mama Sahura don ko da Take matar kaninshi Bata iya Gardama Dashi ammh Umma gaban Ya"yansa ma Tsinka sa takeyi

Zubaida Dai Ya Hashim ya Tarata suka koma Abuja Saboda Makaranta ammh Tayi kuka kamar Ranta Zai Fita Jin Aneesa ta Auri Bello Domin Ita harga Allh Haryanzu bataga Namijin Daya Riga yagama Tsari da Rayuwarta Irin Uncle Bello ba,Hakura tayi ta lallashi Zuciyarta ammh Tana ji Aranta bazata Hakura ba,zata Cigaba da Gwada Sa"arta Domin Aneesa babu Abunda Zata Nuna mata Daga Bangaren Jiki Zuwa na Fuska.

Zulfa ko sai da Tayi Zazzabin kwana Biyu Mama Sahura ce Tayi ta lallashinta Tana Nuna mata Gwara da Kowa ya Rasa Tsakanin ita da Zubaida,Ko da Bikin nan Da Suka Hadu haka Dinga Jifan Junansu da Mugun kallo kan Wanda baisan ma Suna yi ba, kuma kana uwa uba kuma Kowa na Bin Tsakin Uwarshi Ballema Mama Sahura da iya Kissa bata nuna Akwai Takun Sa"a Tsakaninta da Umma gaban Mutane Shiyasa sau Tari ko Taro ake Umma tafi Bada kanta Don Ita Zatayi ta yada Habaici Tana Zagin Mama Sahura Mutane suyi ta yabon Mama Sahura Domin bata Biyemata sai dai ma tadinga Fadin"Yaya kiyi Hakuri.."Kowa kuma Awajen sai ya bama Umma Rashin Hakuri Saboda ita Haryanzu batayi karatun Duniya ba.

****

Tunda Kasim ya koma Kaduna ya Cigaba Daga Inda ya Tsaya yan Wajen Aikinsu suna ta mai Jaje,Sani kuwa koda Suka Hadu shi yama kasim din Sallama ammh yaki amsashi,Tunda ga Lokacin Shima ya Fita batunshi,Domin kowa ya ganshi yasan bashi da Natsuwarsa Duk ya susuce ya lalace bawani gayu sai Tarin kasumba Wajen aikin ma Bai Cika maida Hankali ba,Kwana Biyu da Dawowarsa Haruna ya Biyo masa Suka Tafi Chan Wani Kauye Cikin Niger Delta Wajen Wani Boka Wanda kwana Sukayi Suna Tafiya kafin Su iya Sumai bayanin Abunda ke Tafe dasu Shi kuma yace Su koma su Sati daya tak..Komai zai kamallah basu bashi komai ba Domin ka"idan Aikinshi sai ya kamallah Ake biyanshi Haka Suka Juyo Cike da Farinciki basu damu da Wahalan Tafiya ba Haka Suka Sake kwana Suna Tafiya kafin su Dawo Hankalinsu kwance Suna Jiran Sakamakon Aikinsu.

*****

*Abuja*

Tuni ya gama Duka Shirinsa Na Tafiya kano agobe,Bai Sanar da Ya Muktar da Daada ba sai Daren Washegarin da Zai Tafi kana ya Shiga Shashen Daada inda ya Tarar da Anty Rahila da ya muktar nan yake Sanar dasu gobe zai Tafi kano,Su Hibba Suna Wajen Aneesa Sune Dama abokan Hiranta.

Cikin Murna Daada keta saka albarka Kafin tace"Daga kai Har Aneesa zaku barma na kewa ko,Zaku tafi lokaci Daya..".

Tamke Fuska Bello yayi kafin yace"A"a Bada ita Zani ba Daada Ita tana nan..."Wani kallo ya Muktar ya Jefeshi Dashi kafin yace"Bangane anan Zaka barta ba kabarma wa kenan..? Yafada Fuskarsa ba alaman Wasa ganin Haka sai Anty Rahila ta mike tace bari tazo Ta fice ta basu Waje.

Tattaren naman Saman Goshinsa yayi Waje Daya kafin yace"Me zataje tayi achan bafa zama zanje yi ba,Shima kamar wanchan ne Koyarwa Ne.."Harara ya Muktar ya Makamai kafin yace"Ok wannam Dalilin ne,zaisa ka Tafi kai kadai ka barta karfa ka kamanta Yanzu ba Da bane Kai Mijin Aure ne Aneesa kuma matarkace kuma Tana da Hakki akanka,Dole ka Tafi da Ita domin Babu amfanin kabar Matarka anan kuma kai ka Tsallake katafi Wani gari..".

Shuru Bello yayi kansa na Kasa Ji yake kamar yayi Bindiga Saboda Fushi Hura Hanci kadai yakeyi Zuciyarsa na Tafasa banda Tauye Hakki da Son Atakuramai ya Tafi da Aneesa tamai Uban mene..? Bai gama Tunani ba Daada tace"Ai mganar banza ma yakeyi...Dole ya Tafi da Ita in ta Zauna anan mezata mana,Kai Bello ka Tafi da matarka kajima na gaya maka.."Tafada kai Tsaye Haushi ya kamashi ya Dago yana Fadin"Daada bai zai yuyu ba...Nifa ba Wani Abu Takemin ba Da Zuwanta da Rashinta Duk Dayane plz karku mtsamin Na Tafi da ita zaku karamin Nauyi da Takura.."

Dakuwa Daada ta Makamai kafin Tace"Kaga Naka nan Bello mu kake Fadama Da Rashin Zuwanta da Zuwanta Duk Dayane Awajenta..? Bama son Mganar Banza Tafiya dai dole ka Tafi da ita kamaji na gayamaka bana son na karajin Wata mgana.."Rage girman Idanuwansa Yayi yana kankance su cike da Fushi a Harzuke ya mike zai yi mgana Ya Muktar ya Dakatar dashi da Hannu Lokaci Daya Shima ya Mike yana Fadin"Da Matarka zaka Tafi mallam...Dis is our Final Desicion..."Daga Haka ya Fice Daga Falon Daada.

Numfashi Bello ya Sauke yana Shafa Suman kanshi kamar ya Fashe da kuka Daada dake mai Mgana yamata Banza shima ya Fice Daga Falo cikin Fushi da kallo Ta bisa tana Tabe baki,Haraban Gidan ya koma ya Zauna Bisa mota yana Shafa Sumar Fuskarsa Yana Tunanin yadda Rayuwarsa Zata kare akano Shida Aneesa,Wacce Tun bayan Aurensu banda Sau Daya da suka taba mgana bai kara ko kallon inda take ba,kullun afalo Take kwana  babu Ruwanshi da Ita,Sau daya itama  Tataba Gaisheshi bai amsa ba,Daganan bata kara ba,Mganar Shiga Bedroom dinsa kuwa Sai da Daada ta mai Zazaga Domin kullun Aneesa nan take Zuwa Tayi Wanka kaya ma Tabar mai Sabbin Ta koma saka Tsoffin ta na gida Tun da baya barinta Shiga Dakin Dalilin Mganar da Daada Tayimai ne ya Daina Rufe Bedroom din nasa,Da Asuba in ya Fita Sallah Ta lallaba ta Shiga tayi Wanka ta Chanza kaya,ta Fito ta koma Falo kamar Wata Munafuka,Ranar Data Fara Shiga Saboda Shegen Gulman Aneesan Har ya Dawo Masallaci batagama Abunda Zatayi ba inda bata leka ba Saboda Gulma,yana Shigowa ya ganta gaban Dressing Mirror dinshi tana Fadi Cikin Ranta Ji kayan kwalliya kamar Wata macen,batama san ya Shigo ba,shi kuma yana ganin ta Daure da Towel ya koma Da baya yana Tsaki Falo ya koma ya Zauna yana latsa waya sai da Aneesa Tagama Kallen kallenta kana Ta Shirya ta Fito sai taci karo Dashi Dauke kai Tayi tana Tura baki cikin Ranta tana Fadin"Andai Cuceni Wlh...Saboda mugun Hali Tiolet ma in mutun zai Shiga sai yana Sata.."Yana kallonta ta gefen Ido bai tankamata ba Saboda sanin Bata ma kansa Rai kawai zaiyi,Kwata kwata Yanayin Rayuwarsu bai zo Daya ba gashi An Riga An Daureshi da Jijiyoyin Jikinsa,Ya muktar,Daada,uwa uba kuma Anty Rahila yana ganin Girmanta ga su Ya Ali Wanda bazai iya Cin Zarafin Aneesa ba ya gama duk iya hangensa bai gano ma kansa mafita ba

Haka Ranar Cikin Dare Cikin Aneesa ya baci taji Zawo Ta rasa ya Zatayi ganin Wankin Hula Zai kaita ga Dare yasa Ta isa bakin Kofar Bedroom din Bello tana Bugamai Cikin Barci yaji Muryanta Harda kuka Take Hadawa Wajen Rokansa ya Bude Domin Har tafara Zawon Awando,Saurin Saukowa Yayi Daga kan gado ya Bude Duk atunaninshi Wani abu ne ya sameta ko gama Bude kofar bedroom din baiyi ba ta Tureshi da Karfi ta Shige Ciki Cike da mamaki ya juya yana kallonta ta Fada Tiolet Aguje Saboda Sauri ko Rufe Kofar tiolet din batayi ba yana Tsaye yake Jin karan Zawon nata irin mai Fata Fata din nan ne,Yamutsa Fuska yayi Lokaci Daya yana Toshe hanci Saboda Warin Dayake Fitowa Daga Tiolet din Zuwa Cikin Dakin,ganin zai halaka da Wari ne yasa ya Fice Daga Dakin haryana ja mata kofa Bakinciki kamar ya kasheshi karshenta dai Ranar kan kujeran da Aneesa ke kwana ya karishe Daren Farkawa kawai yayi da Asuba ya ganshi kwance ya Dunkule Cikin Hijabin Sallarta Cikin Takaichi ya mike saboda kyamkyamiv ko Bedroom din Bai Leka ba ya Fice a masallaci yayi alwala Abunda bai tabayi ba Sallar Asuba batare Da yayi Wanka ba.

Ita ko Aneesa bata Dawo Hayyacinta ba sai da tagama barin Wuta,tayi floshing kana ta Tube kaya tayi Wanka Tana ajiyar Zuciya afili ko Fadi take kai kashi Rahma ne babu Abunda yafi kahi Daraja Wlh..,bata Fito ba sai da Ta Fesa Airfresher jin Bayin ya Chanza ganin bata ganshi adakin ba yasa ta kyakyale da Dariya tana Tuna Sanda ta Tureshi ta Shige Bayi,Kaya ta Sauya kafin ta Leko Falon ta ganshi Zaune kan kujera yana Hamma,Baya ta koma Harda sakama Kofar key Tana Dariyan Mugunta,cikin Ranta tana Fadin"Mugu yau kaima ka Dandana kwanan Falo,Ta ko Haye gado Harda Shigewa Cikin Bargonsa Tana Shakam kashim Turaransa Tana lumshe ido Cikin Lokaci kankani barci ya kwasheta bata Farka ba sai da Taji Yana Dukan Kofar tashi Tayi Tana mika Lokaci Daya take Fadin"Waye ne...?


"Tafada tana Kunshe Dariyanta Ransa bace yace"U better open d door Bf4 i loss my Temper..",Yafada Cikin Sanyi ammh Cike da Fada,Dariyarta ta saki yana jinta Tadaka tsalle akan gadon tana Dariya Sai da ta saka hijabi kana Ta Bude Kofar,ta Rabe a bayan Kofa,Shiga dakin yayi yana Hararanta Lokaci Daya yana Kara Toshe bakinshi Cikin Tsawa yace"Ke wata irin kazama ce zaki gama Amfani da Tiolet baki Wanke ba..? Yafada yana kara Rufe Hanci Abun ma Dariya ya bata ta kama baki tana Fadin"Ikon Allah kashin nan fa kowa nayi.."Hannu ya saka ya make mata baki yana Fadin"Sa'an wasanki ne ni...? Yafada yana Nuna ta da Tsaya baki ta Tura tana Sosa lebenta har ya Tashi,Hanyar Tiolet ya Nuna mata yana Fadin"Wuce maza ki Shiga ki wanke min Tiolet Tas,Zan Shiga nayi wanka kuma In kin isa karki Wanke Dakyau kiga yadda zan Dake.."Yafada yana Direct dinta da Hannu Wucewa Tayi Tana Kunkuni Tsawa ya Dakamata yana Fadin"Wai ina wasa Dake ne...?kinsan Allah zan Zaneki fa.."Yafada Lokaci yana yunkurowa ai da gudu ta Fada Tiolet din tana Hawaye Cikin Ranta tana Fadin mugu kawai,Haka ta Cire Hijabi ta Zage Ta wanke bayinan tas,ya koma yana kamshi kana ta Fito tana Haki Duk ta Jika kayanta Da Harara yabita kafin yace"Now get Out..Next time in kinji kazanta go to Anoder room don"t came back Here again...".

Tabe baki tayi ta Dauki Kayanta Dake saman Akwati Wanda ta Fito Dashi ta Fice Zuwa Shashen Daada Cikin Ranta kuma Dariyan Bello Take in ta Tuna yadda yake Toshe hanci afili tace"Ji yadda yakeyi sai kace shima baya kashin Waya sani ma ko Shima Zawon yake kamar nawa.."Tafada Tana Dariya Haka Dataje Shashen Daada tana mata Fada ammh Tana Dariya ta bata lbrin Abunda ya Faru Hartana kwatanta Yadda Bello ke rufe Hanci Ita kanda Daadan Sai da ta Dara Tana Girgiza kai Cikin Ranta tana Addu"ar Allah ya Shiryi Aneesa.

wai kuma duk wadanan Abubuwa kuma ace Dole sai ya Tafi da ita yana nan Zaune sai gashi Ta Fito Sanye da Hijabi Tana Dauke da junoir Hannunta kuma na Rike da Hibba Suka sauko Zuwa Shashen su ya muktar yana kallonsu har Suka Shige baisani ba ko ta ganshi itako batama lura dashi ba tana Shiga ta Hadu da alheri sai ta mika mata su ta juya ta koma Ta Fara Taka steps kenan taji taku mutum Abayanta ko Waigowa batayi ba Tadaga Hijabi da kafa ta Rumtuma da Gudu ta Shige Dakin Tana Dafe Kirji Tsaki yaja a Cikin Ranshi yana jin Takaichi kamar me,ko zama bata samu yi ba ya Shigo Falon bai kalleta ba illah Wucewa Dayayi gaban Tibi ya Dauki Remot ya Rage karan Cartoon din da ta kunna ma su Hibba,Takowa yayi Zuwa Tsakiyr Falon Lokaci Daya kuma ya juya Zuwa Bedroom dinshi.

Karamin Tsaki Aneesa ta Sauke kafin Ta kwanta Harda Juyamai baya bai damu ba Tunda ya Sake Juyowa ya kalleta ya Dauke kai yana Fadin"Ke ki shirya gobe da Safe zamu  tafi kano.."Yi tayi kamar bataji ba Ackin Ranta tace"Kaga ke mallam."Ganin Yadda Tamai ne yasa ya Hadiyeshi Fushinsa yana Fadin"Ke wai badake nake mgana  ba..ke Aneesa.."Sai Lokaci ta juyo tana Wani Tura Kirji Sauri kauda kai yayi yana Kara girman idanuwanshi yana Fadin"Kina jin Abunda nace..?..

Baki ta Motsa kafin tace"Hum..Me kace..? Wani Haushi ne ya kamashi Cikin Fushi ya Nufota yana Fadin"Ok bakiji ba ko..?bari nazo na Kara gayamiki ."jin Haka kuma ganinshi ya Nufota yasa ta Zabura ta Mike tana Fadin"A"ah Wlh naji naji..Ba cewa kayi gobe na Shirya zamu kano ba..? Tafada Tana Takurewa Jikin Kujera Fuska ya hade kafin yace"Gud...karki batamin Lokaci in ba Haka sai dai ki sameni achan..."yafada yana Shigewa Cikin Bedroom Dinsa da harara Ta bishi kafin tace"Baza"a je din ba.."Sai kuma tayi Sauri Ta Damke bakinta tana kallon Bedroom Dinsa da kallo Sanin yadda Kunnansa yake kamar na Maciji saboda ji.

****
Washegari Tun karfe 7:30am Bello ya gama Duka Shirya Shiryansa Abun da yabama Aneesa mamaki ganin Uban kayan da zai Tafi Dashi Jakunkuna Uku,mallam.Inuwa yazo Har Falon ya Dauka ya Saukan mai Dashi Zuwa Cikin Motarsa,kirar 4matic baka,kuma komai na amfaninshi ya Diba,ita azaton zasu gidan Anty Aisha ne,sai da ya barmata bedroom din tayi Wanka Ta Shirya Cikin Riga da Zani na Wani leshi mai kyau kalan milk da ja,ta sanya Jan mayafi da jan Takalmi kuma Duk Cikin kayan Auren da Kasim ya bata ne,Sai da ta Shiga Sashen Su Daada gaishesu ne Taji Daada na Zolayanta zasu barsu da kewa,Sai lokacin ta gane Tafiyan ba na Dawowa bane,Nan da nan Hankalinta ya Tashi Cikin Son tayi kuka tace"Daada chan zamu koma da Zama..?kai Daada ta Dagamata kafin tace"Chan mijinki ya samu aiki.."Bata rai Aneesa tayi Daganan kuma sai kuka Daada na lallashinta Anty Rahila dai bata mata mgana ba ganin iskancin na Aneesa nada yawa sai da Suka zo Tafiya ta gane kukan sabo ne itama sai da ta Share kwallah hibba ko da Junoir Haka Suke kuka Aneesa nayi Shikanshi ya Muktar ya sani Yasani zasu ji kewan Aneesa Hatta su Mallam Inuwa Sunji ba Dadi da Tafiyar Aneesa,Alheri da Jummai suma Harda kwallansu Aneesa dai Haka Suka Fice Daga Haraban Gidan Tana gaban Mota Tana Kukan Rabuwa dasu Daada,gashi Bello ya hanata Daukan kayanta Duka Akwatuna uku Ta Dauka yace takoma ta mayar dasu ta Dauko Daya Hala chan zata tare,waye zai Dinga mata Jigilan Zuwa da kaya yana maidamata,tana kuka tana komai haka ta maida akwati biyu Acikin yar Babban ta saka Duk Abun Amfaninta,bawai don zasu Isheta ba,sai don muguntar Bello Cikin Ranta ko Allah ya isa takemai domin ai Shi ya Diba kayansa Duka sai itane zai Hanata batasan ko Kwatan kayansa bai Diba ba,Wardrope dinsa maa baisan an Dibi kaya ba Saboda Tsabar yawansu.


Ki biya ki karanta cikin salama

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

 
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*


         *🅿�20*

Sun Fara nisa kukan Aneesa,yafara isar sa Dole ya gangara gefen titi ya faka motar Cikin Tsawa yafara mgana"ke kukan me kike ma Mutane...? Ko dai salon iskanci kine ya tashi..?ko kuma salon mutane suganki kina kuka Suyi Tunanin Sato ki Nayi..?

Ko kallonsa Aneesa batayi ba,illah Cusa kanta Datayi Cikin Cinyoyinta tana Cigaba da Shesshekan kuka Tsaki yaja kafin  yatada Motar yana Fadin"U better keep u mouth Shout in ba Haka ba wlh kinfi kowa sanina Sai na Watsaki Cikin Dajin nan na barki na kama gabana.."Jin Haka yasa Aneesa Tayi Dif sai dai na Zuciya sanin Halin Bello Tsaf zai Iya aikata Abunda yace don ba Mutumci ya cika ba...

Wajen 10am na Safe suka isa Gidan nasu dake Buk road,Megadin gidan Wani Bafullatani ne,mai kirki sai faman musu barka da Zuwa yake yi,Fitowa Aneesa Tayi Daga motar Tana karema Haraban gidan kallo Bello ko takanta bai bi ba ya Bude Booth ya kwashi jakunkunarsa ya bude Kofar Falon gidan ya Shige ya barta,don mugunta yasan fa bazata iya Daukan Akwatinta ba Ganin Tana jansa ne yasa Salihu maigadi wanda ya Fadamata Sunanshi bayan sun gaisa ya Dauka ya kai mata Falon Farko.

Aneesa Tsayawa tayi afalon Tana ta uban kalle kalle,Falon Farko Shi keda 1 bedroom da Kichen Guda Daya Shima duka ko"ina yaji kayan alfarma na Morewan Rayuwa,Wani korido tabi tana jan Akwatinsa sai gata ta bayyana awani katon Falo mai kyau da Tsari Wanda yaji Ubansu Rolay Chairs,Daga ganin Falon Zaka san Ankashe kudi,Kuma yafi na Farkon Girma,shi yana da wajen Dinning da Kichen mai girma sai Kofofin 2 bedroom Kusa da Juna,Tana Tsaye tana Faman Wurga ido Bello ya Fito Daga Daya Bedroom din yana Waya ya Fice ko kallonta baiyi ba,ganin haka yasa taja kafa Zuwa Dayan Bedroom din Shima ya Hadu karshe makeken Royal bed da Madubinsa,sai Wardrope babba da Tiolet,bata zauna ba ganin kura Adakin sai Ta Hau gyara wajen itace Har Falon da Kichen sai da ta Share tayi mooping Dayake ta samu Abun Shara agidan,Sake komawa Tayi Falon Farko ta gyarashi Shima Da Bedroom din Acikin Ranta tana Tunanin kila anyi Wajen don Baki ne.

Sai Wajen Azahar ta gama Tagaji Tubus Wanka ta Fada Tare da Dauro Alwala,cikinta Kugin Yunwa yake yi Domin bata karyaba rabonta da Abinci Tun Jiya Da Daddre,gashi kuma Tunda Bello ya fice bata karajin Motsinshi ba ta fito Falo ta leka ta taga ba taga Motarsa ba, kenan yayi Nisa ya manta da ita,gabas ta Saisaita ta Tada sallah ko kayanta Data so ta jera cikin Wardrope kasawa Tayi Saboda ta gaji Tana sanye da Wata Bakar Doguwar Riga tabi lafiyan gado Duk da yunwa dake damunta haka barci ya Kwasheta..

Bata Farka ba sai bayan La"asar ta Tatashi ta Dauro alwala tayi sallar la"asar,Yunwa yafara illatata Domin Jiri take gani in ta mike,kichen ta Shiga tana Bude bude ammh babu komai na girki sai kayan Tukwane dasu gas,har Fridge ta bude bakomai,fridge din ma Daga gani Babu Abunda Aka Taba sakamai Falo ta Dawo Tana Rangaji ta Zube bisa kujera tana maida Numfashi harda kwallanta,Shuru Shuru ba Bello sai Bayan sallar mangariba kana ya Shigo gidan Hannunsa da Lodoji guda Hudu manya,Lokacin Tana kwance nan kan kujera Saboda yunwa ma ta kasa Tashi tayi sallar Mangariba.

Yana Shigowa kallo Daya yayi mata ya kauda kai Cikin kichen din ya Shiga ya ijiyemata Duka Ledojin kana ya Fito Hannunsa Rike da goran Ruwa yana Fadin"Ga Abinci chan a kichen da Wasu kayan Cefenan,ban samu Lokacin Shiga kasuwa ba gobe in na Fita za"a saka komai Cikin Store.."Jin yace ga abinci can yasa wani karfi yazoma Aneesa ta mike da Hanzari Tana ganin Jiri kamar zata Fadi sai da Ta Rike bango da kallo ya Bita kafin yace"zaki dinga dafa Duk Kalan Abinci da kike so buh ke kadai Karki sake kice zaki yi girki dani don ni ba sa"anki bane,Su Daada ne suka matsa na Nataho dake amnh ni zuwanki da Rashinsa Duk Daya ne, so zaki iya Dafa abinci ki ke kadai sai ko megadi in zaki samai and kuma ki Duba komai kiyi list dim Abunda Babu ki bani gobe in na Fita zan Shiga kasuwa na Siya miki komai ga bedroom dinki nan Nima i hv my Own so karki Shiga Harkata nima bazan Shiga Taki ba Kowa yayi Rayuwarsa Am i Clear.."Yafada yana Kurban Ruwan Daga Tsaye ko jinsa batayi Sosai ta gyada kai Tsawa ya Dakamata kafin yace"Bakin ki na Ciwo ne.? Da zaki amsamin da kai.."Jikinta na Rawa saboda yunwa tace"Naji insha Allahu Zan kiyaye..."Juyawa yayi yana Fadin"Gud.."Daga Haka ya Shige Bedroom dinsa ya Rufo.

Dakyar ta iya karisawa Kichen din Tana laluben Hanya Saboda Yunwa ledar Farko ta Raruma nan Taga Take away din Shinkafa da Miya da Salat,sai Kaza Gashasshiya da Yoghourt,sai ruwan Faro mai Sanyi ai Aneesa bata tsaya wasa ba ta Zauna Dirshan Atsakiyar kichen din ta Tura Abinci gabanta ta Faraci ko Takan Cokalin Dake Ciki batayi ba Tana ci tana Hadawa da yoghourt,Sai da ta Shareshi Duka ta kuma Shanye duka yoghourt din ta jawo Ledan kazan itama taci Rabi ta Hada da Ruwa kana Tayi gatsa tana Shafa Cikinta kafin tace"Kai yau naji ta Babuwa..",Gaskiyan almajiri ne Dayace Yunwa bata da Hankali.."Take Fada Tana Dariya,sai da ta gama Hutawa kana Ta iya mikewa Dakyar Fridge ta bude ta saka Sauran kazan Tana Fadin'Na gobe don ba lalle bane ya Tuna Dani da Wuri.."Sauran Ledojin ta bude,kifi,Nama,kayan miya,green beans,Karas,Cabeji da Cray Fish,sai kwalin indomie guda Biyu,sai katan din Ruwa guda Daya Tana ga dai ya Siyo ne kafin gobe,Duka kayan Ta saka Cikin Fridge din shi kuma indomie ta barshi nan domin Store din yana Kulle ne sai Lokacin Ta iya Fitowa Falo tana Tura Ciki Hakikanin gaskiya Tayu Mugun Ci Daki ta koma ta Fada Tiolet wanka Tayi kana Ta Dauro alwala ta Fito tayi sallar Mangariba ta Hada da Isha"i Shafa"i da Wuturi tayi kana Ta Bude Akwainta ta Zaro Doguwar Rigar barcinta ta saka,sai dai ta Hau gado zata kwanta kana ta Tuna da,Abunda Bello yace ta Rubuta mikewa Tayi ta Bude Zip din Jakarta Inda ta Sako Littafanta Da Biro sai Qur"anin da Falmata ta Bata da azkar ta Yago Fallon Takarda Tayi Zaman Dirshan Akan gado ta Fara Rattaba Rubutu Wani Abun ma Harda mugunta su Semovita ne,wai harda aya da Dabino ta saka,wai na yin Kunun aya,hartagama Sai ta tuna da Abun Zobe Haka ta sake Rubutawa sai da ta Cika Takarda kamar Hauka,wani Abun ma Saboda Mugunta ta saka ba domin Tana ci ba,bata kwanta ba sai Wajen goma kana ta Nannade Cikin bargo sai barci.

*****

Karfe 7:3am na Safe ya Fito Daga Dakinsa Cikin Shirin Fita,Sanye Yake Cikin Wasu Ubansu American Suit,Ash And black,Ya matse Wuyansa da Tie baki kafarsa Sanye Cikin bakin Takalmi Rufaffe Na Fatar Damisa Haka Tsitsiyan Hannunsa Sanye da Agogo Baki na Fatar na kamafanin Rado,kallo Farko zakamai ka Fahimci Kwarjinsa Tare Dashi Wata karamar Jakar Briefcase ne Ahanunsa sai Wayarsa Dayake latsawa da Hannu Daya babban yatsansa na Sagale da key din motarsa.

  

karfe 8:00am yake da lecture din Yan level 1,Baya so yayi African Time Domin baya Cikin Tsarinsa,tun jiya bayan isowarsu  Fitan dayayi Cikin makaranta

Please Login or Register in order to submit comment