Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gani yanda tayin wani mugun rama gaba daya yanayinta  yaacanja

              K'asa tayi da Kai Hawaye nakokarin zubowa daga idanuta muryarta narawa  tace Abba   akwai kudi a gunka kabani nasalamin Mai Naffee

   Abba yace kishiga ciki zanje nasameshin  shigewa ciki tayi  Dakar ta inya bude baki tayi sallama

Mama dake shara sake tsitsiyar dake hannuta  tayi kallon  Ummeey  tayi cike da tausayawa  hawayene suka zubo daga idanun  Mama
Karasawa tayi Ida  Ummeey take
Kama hannuta tayi tazaunar da ita a kan taburma  cikin murya Mai rauni Mama tace Ummeey  lafiya  Naganki da akwati kiga yanda Kika dawo saikace wace tashekara Tana jinya  Kode kiyin rashin lafiyane

Abba nasalamar Mai Naffee din gidan ya shigo Dan bazai inya fita ko inaba  gani Ummeey dayayi bakaramin tayar Masa da hankalin yayiba Zama yayi a gefenta..

Kallo iyayyen nata tayi taga gaba dayasu fuskarsu dauke da   damuwa 

A Ranta tace kowane halin zasu tsici kansu idan sukaji  ya Muhammad ya sakeni tausayinsune ya kamata

Abba ne  ya dubeta cike da kullawa yace Mamana lafiya kuwa Naganki cikin irin Wana yanayi

Hawayene suka zubo daga idonta a hankalin tabude bakinta  tace Abba ya Muhammad ya sakeni  yamin sakin uku Abba tuda ka Aura dani ga ya Muhammad  yake azabtar Dani  haka nake rayuwa a gidansa kullu cikin duka da zagin

An wayi gari abuda zanci yafi karfina a gidansa saka makon kwashe kayan Abinci da Momy tayi   

"Umma Hauwa itace  tasai da wayanta tamin cefane kayan Abinci ta aika Hauwa takawomin  hata magani  dazan sha. Hauwa ce tasayamin

"Wlh Abba nason ace mutuwa ce zata fitar Dani daga gidan ya Muhammad  kodan gani daurewar farin cikika  Abba naki sanar daku halin danake cikine  saboda banason hankalinku ya tashi   fashewa tayi da kuka

Itama Mama kuka tasa tace kagani ko Mallam  yariyarna babu iri rok'oka da batayiba  akan kabarta  ta Aure wada take Son ama kaki kace lalle sai zabinka

Gashina Kuma zabin naka Yana Neman kashemin Yar, kaduba yada Muhammad ya dawo min da Yar,  wlh daga shin har mahaifiyarsa bazan ya femusu cutarmin da rayuwar Yar,ta da sukayiba" !


Tsantsar bacin Rai ya bayana a fuskar Abba   yace  Mamana kuka ya Isa haka kishare hawayeki   kidau Wana abuda ya faru a matsayin kaddara  wada bamu isa mutsalakeba
    Mamana akwai wani Siri dazan sanar dake nangaba kad'a  Anane Zaki gane

dagani har yayana Abdallah  mun Aura mikin Muhammad ne don gani mun inganta rayuwarki
       Sai gashi abuda muke gudu shine ya faru


Share hawayenta tayi  tace Abba kadena bani hakuri nasan bazaka tabayin abuda zai cutar daniba Kuma wlh nadau hakan a matsayin kaddarata  kallon Mama tayi tace


Mama Dan Allah kidena kuka banason kisaka damuwa a ranki   komai ya riga da yawuce   Kallonta  Ummeeyn tayi Tanajin radadin a zuciyarta

Shikasa Abba    daurewa yake  danji yake Kamar ya zubar mata da Hawaye musama idan ya daura idanusa a kanta
             Yakanji zuciyarsa namasa k'una Anya kuwa zai inya yafewa muhammad   iri cutar da yayiwa Ummeey


Wayasa ya ciro ya Kira yayanasa  yake sanar dashi  sakin da muhammad din yayiwa Ummeey

  shima Abba bakaramin firgici ya shigaba saka makon  jin Wana mumunar labarin yasanar dashi yayi  gashina zuwa gidan yazu, sana ya kashe wayansa


...............Fitowa Abba yayi daga d'akinsa ya Taran da Momy zaune a fallo  tadaura kafa daya kan daya karasawa Abba yayi Ida take fuskarsa babu annuri  yace d'anki ya sanar dake  abuda ya aikata.......

Ya mutsa fuska Momy tayi tace  Alhaji in bada abunka akwai abuda My Son zai aikatane batare daya nemin shawarataba
    Inade akan sakin Wana yariyarce

to  ya sanar Dani ya mata sakin uku saboda bata da kunya batasan darajar  manyaba hanufa tad'aga tamari Meenat  saboda raini  Meenat sa,artace   to ko Mai Aiki gidasu tafi Ummeey daraja da kima

shikuma My Son yaga bazai inya Zama da itaba shine ya kad'ata gidasu sana yahada mata da tukunci duka  aini sonayi daya karya banza


Cikin bacin Rai Abba yace kun tafka babban kuskure daga ke har d'anki    zakuyi danasani a kan Abubuwa da kuka aikata

Fita yayi daga gidan ransa a bace Kai tsaye gidasu Ummeey ya wuce Yana insa ya Taran da Abbata a kofar gidan

Shiga cikin gidan sukayi Mama ta shifuda musu tabarma takawo Masa ruwa da Abinci
   Itama Ummeey fitowa tayi Durkusawa tayi  a gabasu tagaishe da Abba

Shikasa Abba bakaramin tsorata yayiba gani yada tarame talalace  gawani baki da tayi kiyi hakuri Mamana Allah baya barin zalinci shine zai bimiki hakinki akan wadanda suka zalinceki

     Shima Abba nasiha ya mata sosai  kudi yabata masu yawa da kyar Ummeey takarba nama Saida Abba yabata Rai sana takarba babu Abuda zatace da Abba saide San barka tutana karama Abba ke da'wainiya da ita harzuwa girmata



................. Meenat nasamu kullawa daga gun Muhammad din komai take bukata Tana samu daga gareshi    Momy tanemo musu Mai Aiki ita takeyi duk wasu ayukan gidan
       

    Abuda Muhammad ya lura dagane da ita batasan komaiba dagane da abuda ya shafin addini  batason yin sallah idan Kuma ya takura mata sai tasaka kuka  gashi shikuma  bayason bacin Ranta haka zai hakura ya kyaleta  ama Abu Yana damusa  gashi   ko wankan tsarki batayin saide  tayi wankata da sabulu 

Zaune suke a fallo suna kallo, tadaura kanta a kan cinyarsa sallama sukaji dago Kai Muhammad yayi  yaga Ashe Momy ce

Murmushi yayi yace  Momy barka da zuwa Zama tayi a kan kujera tace yauwa My son

Kallon Momy  Meenat tayi tace  Hy !! Momy y kk? Momy tace lafiya Lou Meenat y gida ?  Yatsina fuska tayi tace normal!!

   Ama Momy ya kamata idan zakizo kina  sanarwa Dan gaskiya banason Ana zuwa min gida batare da nabada izziniba

Daure fuska Muhammad yayi yace baki da hankaline Meenat  Momy nawa kike fadawa haka to kishiga hankalinki 

Kuka tasa tace baby nikakeyiwa hayaniya kasanfa banason anamin fada...




DAGA ALKALAMIN

Ummeey Muhammad Lawan
     Yar Autar dashen Allah_*ZAƁIN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_


https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*




FOR MORE INF...
08140801885



Page 77 & 78



_______________" Rugumeta yayi a jikisa I,m Sorry Baby  rainane ya b'acin  banji dadi maganar da Kika fadawa Momy ba

Momy zata inya zuwa gidana a duk lokacin da taga dama 
Turro, bakin tayi tace  nifa Baby banason a yawaita zuwamin gida  in Kuma Momy tanace sai tazo to gaskiya saide nabarma  gidanka '

Kallon Momy tayi tace , Sorry Momy  kizauna a gidanki Ida kina bukatar gani Baby  sai kikirashi a waya zaizo har gida ya sameki
               Dan banason ganin tarkace a gidana mikewa tsaye Momy tayi  cikin b'acin Rai tace amade yariyar nan baki da kunya
         Nida gidan 'Da,na  zakice sai nanemin iziniki agunki  kafin nazo to wlh kiyin kadan yariyar kibin a hankalin in kuma  bahakaba yazu , yazu zansa ya sakeki tuda baki da mutunci

        Kuka Meenat tasa tafara buga k'afafu  Baby kanajin   abuda take fadamin wlh bazan yardaba sai kadaukamin Matakin a kanta 
                Muhammad ' kasa ya kullule yarasa ya zaiyi da Wana lamari   ga ran Momynsa  ya b'acin sai banbami takeyi

Ga Meenat sai kuka take
jin kuka nata  yake har cikin ransa   please....Baby   kidena Wana maganar  tayaya Zan dau mataki akan Momyna  kikwantar da hankalinki yazu zata barmiki gidanki share hawayenki  kiga banason gani bacin ranki
Share hawayeta tafarayi tace to Baby tatafin yazu Dan nagajin dajin hayaniyar nan

                 Kallon Momy yayi yace Momy kiyi hakuri Meenat yariyace karama yarintane yake damunta  muje namaidaki gida 
          'Momy tsabage b'acin Rai kasa yin magana tayi  
Fita zasuyi daga Fallon Meenat tace Baby Ina zaka Kuma ?

Juwowa yayi yace zankai Momy gidane ama bazan dadeba Ina kaita zan dawo
        Kallonsa tayi karmar Mai Shirin yin kuka  cikin shagwaba tace  nifa babu idan zaka kabarni nikad'an a gidan

  gulma da ya kawota shizai Mai data
             Muhammad yace Momy kiyi hakuri kije gida nima inaxuwa anjima takaicine ya Kama Momy masifa tadingayi  zagin Meenat Muhammad sai hakuri yake Bata

Fita tayin daga gidan Rai a bance shikuma Ida Meenat din take yanufa sai wani cin magani takeyi rarashita yafarayi Dan a duniya babu Abuda yatsana sama da bacin Ranta



................... Yau kimani wata biyu kena da dawowar Ummeey gidasu tafara murmurewa kyauwuta ya fara dawowa Dan   Tana samu kullawa daga gun iyayyenata  

Fitowa tayi cikin shirita  ta iske Mama a tsakar gida  Tana wanke wanke tace Mama sanu da Aiki  dama Ina son zanje gidasu Hauwa ne   bata masan nadawo gidaba

Kallonta Mama tayi tace aiko da kinkyauta kigaishesu. Ummeey tace to zasujin insha Allah

Tashi Ummeey tayi tace Mama sai nadawo Mama tace a dawo lafiya
Tana fita gidasu Hauwa  tanufa  

Tana shiga gidan tatara da Hauwa a tsakar gida Tana wanki  karasawa tayi tarugumeta tabaya tare da fadin nayin kewarki Yar,uwata

Murmushi Hauwa tayi tace nima haka Sister wlh kulun cikin tunaninki nake  d'azuma Saida mukayi hiranki da Umma take Tabayana yaushe zanje nadubaki 

Ummeey tace Allah sarki Umma ai wlh sisters babu Abuda zace daku  saide Adu.ah

Keni banji motsin Umma ba kode batanane  Hauwa tace eeeh wlh Umma tafita unguwa gashi sai yamma zata dawo

Wai nikan Sister meye sirrine Naga kincanja bakamar Ranar danaje gidanki nagankiba wlh sister dana dawo gida kasa barci nayin  sai tunaniki nakeyi

Murmushi Ummeey tayi tace kiyin hakuri sister nasan namiki laifi ban sanar dake cewa nakai kimani wata biyu Ina gidamuba Aurena ya mutu  ya muhammad ya sakeni batare da wani Abu ya shiga tsakanina dashiba


Farin cikine ya lulube Hauwa tace Alhamdulillah  Allah nagodema daka cire k'awata daga cikin wanan k'angin   Ina rok'on Allah daya gagauta saka Miki  iri zalincin da ya Muhammad ya Miki
             
   Murmushi Ummeey tayi tace sister  zaifi kyau  mumanta da baya mutinkari gaba Allah Dee yasa inya bakin  wahalar kenan

Hauwa ta Amsa da Ameen Cigaba sukayi da hiransu cikin kwanciyar hankalin kamar karsu rabu   Ummeey batabar gidasu Hauwa ba saikusan yamma



                  BAYAN. WATA HUDU

..................Yau kimani wata hudu da mutuwar Auren Ummeey   kwance take a kan gaddo    zuciyarta cike da tunanin Haydar din  tunani take ta Inna zata fara nemansa  Dan a yazu bazata inya rayuwa  da kowane dan, namijiba idan bashiba

Zubur tamike sakamokon tu,nawa da wasikar da yaturo Adam ya kawo mata a cikin wasikar yasaka number wayasa  Ida yace idan Tana bukatar temako tasanar dashi

tashi tayi tabude wata jakar litatafai Ciro wasikar tayi hamuta na rawa tafara daukar number   Kiran layin tayi tajin ya danga cikin zazakar muryarsa Mai narkar da zuciyar yace.....


DAGA ALKALAMIN

Ummeey Muhammad Lawan

Yar Autar dashen Allah_*ZAƁIN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_


https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*




FOR MORE INF
08140801885


Page 79 & 80


_____________"HELLO!!!!! HELLO!!!!!
Sauti muryarsane ya dakin dodon kunanta wada hakan ya hadasar mata da farin ciki a zuciyarta

Ajiyar zuciya tasauke Mai karfi hawayen farin cikine suka zubo daga idanuta cikin muryarta Mai sanyi  tace  Haydar........ Ummeey ce sai Kuma tafashe  

Mikewa yayi tsaye ciken da mamaki yace Ummeey  Ashe dama zank'arajin  wanan zazak'ar muryarna taki wace take sani farin ciki Koda Ina cikin bacin Rai
Kukan Mai kikeyin kidena kuka

  kukaki nad'agamin hankalin kunuwan Haydar bazasu inya jure jin kukan  Ummeey ba
Share hawayenki Ummeeyna kisanar dani maike faruwa

Share hawayeta tayi tace Haydar nakirakane domin nasanar dakai  Aurena ya mutu nakai kimani wata hudu Ina gidamu

Lumshe idanu yayi ya budesu yayi a hankalin zuciyarsa cike da farin ciki Bude bakinsa yayin yace   Alhamdulillah Allah nagodema daka dawomin da farin cikina   dama inajin a jikina duk da anyin sanadiyar rabani dake watarana dolle Zaki dawo gareni

Allah bazai taba barisu suk'wacemin keba sai gashi cikin ikon Allah kin dawo gareni

Wani dadi Ummeey tajin Yana ratsa dukan sansan jikinta Murmushi tayi gamin da fadin hakika Kai masoyin gaskine   bayin gangancin baka   Amanar zuciyataba 

Yaushe zakazo Gombe  danyin
bayin ga shukar da tadade Tana  bukatar ban ruwa Ummeeynka  namararin kallon Wana kyakyawar fuskarna taka wace ke dauke da annuri a Koda yaushe

Murmushi yayi yace gobe Insha Allah Zan shugo Gombe !!!  Gombe  gari masoyiyata
       
              Lumsheee idanu tayi tanajin wani sanyi a cikin Ranta budesu tayi fuskarta dauke da  Murmushi tace Allah Ubangijin ya kaimu gobe da Rai da lafiya 
            Amsawa yayi da Ameeen sana sukayi sallama zuciyoyinsu  cike da son ganin junnasu  k'urawa waya dake hannusa yayi idon 
  gani  lamari yake tankar a mafarki


daga hanuwansa yayi sama ya Allah idan mafarki nake ya Allah kada kabani ikon farkawa yazu
           Murza idonsa ya farayi yaga abun a zahiri yake faruwa

  murmushi yayi gamin da fadin koyanzu  Naga ribar hakurina  yau ga Ummeey a  hanuna Ya Allah kaji Tausayina kada kabari tasake kufcewa daga gareni
              
              Kiran wayan  Adam yayi  Adam dake kwace a d'akinsa yaji wayasa na ringing daga wayan yayi dauke da far,a akan fuskarsa  hello, Haydar kana lafiya ?

          Lafiya lau nake Abokina Ina cikin farin ciki wada ya mamaye dukan sansan zuciyata   Adam Ashe rabon mutun bazai taba kubce masaba  Auran  Ummeey  deee baiyin Rai ba  yazu take sanar Dani takai kimani wata hudu a gidasu babu  Aure a kanta

Mikewa Adam yayi zaune cikin mamaki yace Haydar  kana nufin Ummeey bata da Aure Auran Ummeey ya mutu
                    Alhamdulillah duk da ba,a farin ciki  da mutuwar Aure ama  a wanan karo nakasance cikin jin dadin  dajin mutuwar Auren Ummeey
     
                      Ina tayaka murna Abokina  da dawowar masoyiyarka gareka  yanzu yaushe zamu Gombe
             Haydar yace nariga nasanar da Ummeey gobe Insha Allah muna hanya Adam yace to Allah ya kaimu gobe

          Haydar yace Amiin ama Dan Allah banason Rukkayah tasan  da maganar mutuwar Aure Ummeey Rukkayah Tana da kishin  sosai wlh mudin tasan Aure Ummeey ya mutun  to daga ranar nayi bankwana da farin ciki  a cikin gidana har yazu Rukkayah bata Dena fushi daniba saboda suna Ummeey danasawa yar'ta   Taki tafitar da Wana Abu a rainta.

              Wlh kishin Rukkayah har tsoro  yake bani Adam yace   kwantar da hankalinka Abokina  dazaran mun dawo daga Gombe zansamu Rukkayah zan mata bayani insha Allah komai zai tafin daide

Haydar yace nagode Abokina gobe karfe 8:00 zamu tafi Adam yace Allah yakaimu gobe kashe wayansa yayi  yanufin  gidan

Koda ya insa gida ya Taran da Rukkayah zaune a fallo tanayiwa Ummeey wasa itako sai kyalkyallewa  da dariya takeyin

Zama yayi a gefenta sanu da dawowa tamasa Amsawa yayi dauke da far'a akan fuskarsa  hannu yasa  dauki Ummeey

      Kallon Rukayyah yayi yace Momy Ummeey gobe inaso zanyi tafin  kallonsa itama tayi tace Allah yakamu gobe ama wane gari zaka  Haydar yace Gombe zani

          Gabantane ya fadin kallonsa tayi cike da tuhuma  mezakayi a Gombe bayan nasan baka da yan'uwa a can

       Ina da yan'uwa a Gombe Mana ko kin manta Kakarmu Inna  nacan tare da Adam zamu tafin
Zamu kaiwa  Inna ziyara kiga ai zataji dadin ko  Kallonsa take batare da tayin maganaba zuciyarta naraya mata Abubuwa daban daban
            

                     WASHE GARI

Damisalin karfe 8:00 Adam ya inson gidan Haydar Rukkayah gaishe da yayannata tayin fuska a hade Dan ita bata yarda dasuba gaba dayasu haushi yayan natane ya kamata

      Musamama da takalin  fuskar Haydar din taga sai murmushi yake sai kace wani sabon ango

Haydar yace Rukkayah zamutafi kikulamin  da kanki kikulamin da  Ummeey na  zamu wuce sai Allah ya dawo damu lafiya 

Dak'ar ta inya bude baki tace a dawo lafiya Allah ya kiyayye hanya  kwana nawa zakuyi 

      Haydar yace kwana biyu zamuyi    shuru tayi batare da tace komaiba 

Fitowa sukayi daga gidan suka shige mota suka dau  hanyan Gombe Haydar sai far'a yake bakisa yaki rufuwa

Damisalin karfe 12 :30 suka in son cikin gari Gombe  tsayawa sukayi a masalacin sukayi sallah
Anguwarsu Ummeey suka nufa
         Ummeey sai shirye shirye tarbar Masoyinata takeyi girki tayi musu shikafa da wake da Mai da yajin  sai kunu ayyah

Dan tasan Haydar din nata dason Abinci gargajiya zuwa tayi tashiya ciki shigar doguwar riga  kayan bakaramin kyau suka mataba  wayatane tayi Kara dauka tayi takara a kunenta  fuskarta dauke da murmushi Sallama tayi

Amsawa yayi yake sanar da ita suna kofar gida  kashe wayan tayi cikin sauri tanufi hanyar waje Tana fitowa tatar dasu  tsaye jikin mota kallon kallon sukeyiwa juna zuciyoyinsu cike da shaukin So 

wani kyau yaga tagara Masa duk da rama dayaga tayi hakan bai hanashi gani kyautaba  sallama tamusu sana tagaishesu Amsawa sukayi gaba dayasu suka Amasa.

a hankalin tabude bakinta tace  Haydar.... Ashe Idanuwana zasu Kara ganika" Allah nagodema  daka dawo min da masoyina a Lokacin Dana cire Rai dasamusa


Murmushi yayi yace Ummeey ai Mai Rai baya fitar da Rai daga rahama Ubangiji  kullun  inajin a jikina watarana Zaki dawo gareni burimu Zai cika namalakar junamu

     Saide akwai maganar da nakeson sanar dake Ummeey.... nayin Aure dago Kai tayi da sauri tadaura dara daran idanuta a kansa tace  Haydar kayi Aure?
    

  Eh nayi Aure Ummeey har Allah ya azurtani  da samun karuwa yar'mace

  Ummeey tace  natayaka murna   lale wanan matar takasance Mai sa,a

a rayuwa tasamu mijin daya tankar ya dubu  dazan ganta Dana Bata shawara tarike mijinta hanu biyu  Dan samu irinsa a fadin duniyarna sai Ansha wuya


Mamakine ya Kama Haydar  gani yada bata nuna damuwarta akan Auren da yayiba  lalai Ummeey tadabace a cikin mata

     Kallon Adam Ummeey tayi tace Adam Naga kayi shuru bakace komaiba murmushi Adam yayi yace  Mai zance Amaryamu ai Wana zance namasoyane
           Saide namiki wani albishin wada shi Haydar din ya manta bai fadamikiba 

Itama murmushi tayi tace Ina sauraroka 

Adam yace Ummeey  saboda irin son da Abokina yake Miki  ya dau alkawari idan Allah yabasa yar' mace zaisa mata sunaki

Sai gashi  Allah ya azurtashi da samu yar' mace Kuma yasamata sunaki

Wani dadi Ummeey tajin Yana ratsata tace  Haydar  Ashe kaunar  dakamin hartakai haka kasawa Yar,ka sunana

wayo dadin  zanso Naga Wana yariyar zason gani yar' masoyina   Allah yarayamin Mai sunana Haydar Kai masoyine nagaskiya Ina Alfahari dakai Haydar

Mushiga cikin gida kucin Abinci kuhuta shiga sukayi cikin gidan Ummeey takawo musu Abinci  zuba musu tayi a plate
        Basu wuri tayi Dan susamu sucin Abinci

Suna gama cin abincin sai ga Abba ya shigo mamane take sanar dashi zuwansu Haydar din  karasawa yayi Ida suke gaishesa sukayi cike da mutuntawa. an wanan karo Abba yajin dadin zuwasu Haydar din

  Adam ne yace Abba yauma  de musake  dawowane a kan maganar Aure Ummeey dan Allah Abba katemaka kabawa Abokina Auren Ummeey

Kallonsu Abba yayi yace na'amince zan bawa Haydar Aure Ummeey Ama Ina da sharadin  zaka turomi mahaifinka a gabansa 
zan fadamuku sharadina  idan kun Amince to Zan Baku Aure Yar,ta zufane ya karyowa Haydar Abba yace kakwantar da hankalinka Haydar Wana karo bazan hanaka Aure Ummeey ba saide idan kune kukaga bazaku inya Aurentaba...


DAGA ALKALAMIN

Ummeey Muhammad Lawan
Yar Autar dashen Allah_*ZAƁIN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_


https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*




FOR MORE INF
08140801885

Page 81 & 82


______________Adam yace toshikenan Abba  babu damuwa insha Allahu zamu sanar da Dady sak'onka  Kuma nasan Dady zai yarda da duk wani sharudanka matukar bai sabawa addiniba

Zamu tafin masaukimu zuwa gobe zamu dawo wata killama tare da Dady zamu dawo Abba yace Allah ya kaimu gobe

Atare suka Mike tsaye    sukayiwa Mama sallama Ummeey fitowa tayi daga d'aki domin tayi musu rakiya
Kallon masoyin nata tayi taga yanayisa gaba d'aya ya canja  gabantane yafadin cikin tashin hankalin  tace  Haydar  Wana karoma Abbana yakin Amince da maganar Auremu  koh wayooo Allah nashiga Ukuna  sai Kuma tafashe da kuka Mai cin Rai

Kallonta Haydar yayi gamin da fadin menene abun kuka anan bafa abuda kike tunanibane Abba ya Amince zai bani Aurenki.

Ummeey tace Adam dagaskene abuda yake fada kode akwan wata matsallane kuke boyemin

Murmushi yayi yace  gaskiya Haydar ya fada mikin 
Ummeey tace tomeyasa naga yanayiku gaba daya  ya canja  bayan ba a haka kuka shiga  gidamuba kushiga gidamu   dauke da far,a akan fuskarku
Kun fito Kuma fuskarku dauke da damuwa
       Dan Allah kusanar Dani Mai Nene dalilin canjawarku   

Murmushi Haydar yayi yace Ummeey Abba yace zai bani kee naturo Dadyna  ama Kuma akwai sharudan dazai kafa Mana

             Hankalina yatashine saboda bansa wane irin sharadin Abba zai kafamanaba yazu kishiga gida zamuwuce gidan Inna idan muhuta zankira Dady nasanar dashi  duk yada mukayi  da Dady zakijini zuwa dare 

Ummeey bazanbar Gombe ba har sai Abba ya baniken  An tsai da Ranar bikin sana Zan koma Kano

     Murmushi tayi tare da fadin Allah ya Amince zanso gani Wana Rana Mai cike da dinbin tarihi
           Ranar da muka Dade Muna mafarkin zuwata Murmushi yayi yace Zan wuce Ummeeyna saimuyi waya

Toh Allah ya tsare Ango Ummeey Dady  Ummeey  dariya yayi Dan har cikin ransa yajin dadin Wana suna data kirasa dashi
               Shigewa Mota Adam yayi tare da fadin idan nabiyema  Haydar saimu akwana anan batare da kasaniba Dan Naga kuna cikin shaukin son 
           Kallonsa yayi gamin da fadi wlh Adam Idan inatare da Ummeey mantawa nake da komai a cikin wanan duniyar
                Subar kofar gidasu Ummeey batare da son ran Haydar ba  gidan Inna suka nufa 

Inna tayi farin cikin daganinasu susamu tarba tamusama daga gun Inna
      Haydar ya Kira Dady yake sanar dashi  duk abuda ya faru bai Boyemasa komaiba   Dady ya Masa Alkawari gobe zazo yasamu Mahaifin Ummeey   farin cikine ya Kama Haydar  wada ya bayanna a kan fuskarsa

            Yasanar da. Adam yayi  yada sukayi da Dady shima Adam yajin dadin da Dady ya  amince zaizo gobe

    Dady yasanar da Ammy mutuwar Aure Ummeey Kuma gobe zaije Gombe nemawa Haydar din Aure Ummeey Ammy tayi farin ciki sosai tayi musu Allah yasaya alkairi.


                WASHE GARI

Damisalin  karfe 1:30  Dady yashigo cikin gari Gombe kira Haydar yayi yasanar dashi insowarsa Haydar da Adam  ne sukaje Taran Dady

Basu bata lokaciba suka nufin gidasu Ummeey dama Kuma Ummeey  tasanar da Abba Mahaifin  Haydar din nazuwa yau shima Abba yasanar da yayanasa   zuwasu 

     Abba da yayanasa suyi matukar farin ciki da zuwan Dady sun karbesa cikin girmamawa da karanci

shikasa Dady yajin dadin irin karamawar da yasamu daga gun su Abba
           Dady yace Alhaji  nide  sunana Alhaji Museen nine Mahaifin Haydar  Allah ya jarabin Haydar da son Yar,ka  wada kaddara tazo lokaci guda tarabasu    Haydar yashiga cikin mawuyacin halin sakamokon rasa Yar,ka da yayi

  Dan bakaramin son  yakemataba  sanadin hakan   ya harfar Masa da ciwo zuciya
mutsici kamu cikin tashin hankalin 

       Musha wuya sosai kafin musamu Haydar ya dawo hayancinsa 

            Jikin Abba yayi Sanyi tausayin Haydar din yakamasa lalai bai kyauta musuba yayi sanadiyar shigarsu cikin wani halin ya jefasu cikin garari to Yaya zaiyi dolle sumasa Uzuri shima ba,a son ransa ya aikata hakanba yayi hakane domin inganta rayuwar Yar,tasa  kallon Mahaifin Haydar din yayi yace...



DAGA ALKALAMIN✍🏻

💞Ummeey Muhammad Lawan💞
     🥰Yar Autar dashen🌲 Allah. _*ZAƁIN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_


https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_


Please Login or Register in order to submit comment