Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rubutu kamar ha




Amincin Allah yatabata a garekin  ya ke ma abociyar kyau da nutsuwa akullun burina na inso garekin nasamu yardarki na nuna mikin son dana zautu da muradin bengenki kece wace nake burin malaka Amatsanyin matar Aure Ama kash!!!!
Kaddara taringa da tariga fata mafarkina baxan tabba tabataba burina baxai taba  ciki ba..

"Ummeey nah Ina son kixama jaruma  Mai karbar kaddara komai girmar ta
Babu yarda muka inya yaxamo Mana dole murabu da juna.

Ki dau wanna abu a Amatsayi kaddara mu Wanda bamu insa mutsa laketa ba

Ina Mai Neman Alfarma a garekin ki daure ki karbin zabin da Abba yayin mikin domin Abba yafimu sanin daide
Duk Dan' nagari burinsa ya kyautatawa mahaifansa.

har yasasu cikin farin ciki
"Biyayyyah ga iyayyen dole ne baxan son ace ta dalilina Abba yayin fushi da keba 

Ummeey xanjin dadin idan har Kika kasance daga cikin Yan"Yan da iyayyesu xasuyin alfahari dasu  ummeey na sadaukar da soyayyata ne domin ganin ciga banki a rayuwa xan barki ne saboda farin cikin Abba  fatana Dee Abba yayin Alfahari dake Ina yin mikin fatan alkairi da fatan nasara a rayuwa baxan tabba mantawa dake ba baxan manta halancinki gareni ba Ina Mai tabatar Miki dacewa da sonki xan koma ga mahalincina sonki yayimin tabo a zuciyata Wanda baxai taba gogewa ba nabarki lafiya ummeey sai watarana Allah ya hada fuskoki mu da alkarin  Allah yabakin ikon cika wa Abba burinsa ga number Haydar idan kina bukatar temako daga gareni karkiji kuyanta yanxu naxama yayanki  Kuma Dan uwanki najini bissallah ..


Dago kan daxaiyi suka hada indo da Adam

Mikawa Adam yayi yace Adam " gashi kaje gidasu ummeey ka aika yaro ya Kai mata Yana maganar jikin a sanyaye cikin tausayawa Adam ya karba wasikar budewa yayi yafara Karan tawa

Har karshe Adam ya karanta take yaji  tausayin Abokin nasa ya Kara shigarsa.

kalonsa yayi yace kwantar da hankalin ka Haydar nasan da ciwo a Rai ama komai xai wuce xai xamo tarihi

Allah ubangijin ya shiga lamarinka Amsawa yayi da amiiiin

Zuwa sukayi sukayiwa Inna sallama Inna tarakosu har bakin mota tayi musu fatan alkairi

Da fatan sauka lafiya haka suka wuce suka bar Inna cikin alhenin da tausayin halin da Haydar din yake cikin
Koda suka inso kofar gidasu ummeey yara suka Taran sunna wasa

Adam ne ya fito daga cikin motar yakarasa inda yaran suke sallama ya musu yace " Kai xona aike ka gidanan ka kaiwa ummeey mikewa yaron yayi ya karbi sakon Adam ya ciro sabuwa dari biyar ya mikawa yaron

Yaron ya karba  tare da godiya cikin farin cikin da jin dadi ya shiga gidan

Sallama yaron yayi ai ko ya cin sa.a Ummeey na tsakar gida Tana xaune ta kifa kanta a kan gwuwoyinta

Ta Amsa sallamar batare da ta dago kanta ba

Yaro yace Wai gashi ijin wasu muta ne suce abaki

Dago Kai Ummeey tayin da mamaki a fuskarta tace ni Kuma a kace kabawa

Yaro yace eh  karbar ta karda tayin ta bude idanuwanta suka sauka a kan rubutun Haydar  gabanta ne yafadin take xuciyarta tafara bugawa

Kamar xata fasa kirjinta tafiton waje fara karanta wa tayin Hawaye na kwarayan a idon ta

Cikin shashekar kuka tace shikenan narasa farin cikina na shiga uku na

Mama ce tafito jin kukan nata karasawa tayin da sauri ta fada jikin mama Tana cewa..






By YAR AUTAR DASHEN ALLAH...✍🏻🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA🎅🏻



          NA




UMMEEY MUHAMMAD LAWAN
  ( UMMU AFNAN)
💃🏻YAR AUTAR💃🏻 DASHEN 🌲ALLAH




For more inf...08140801885




Page  25 & 26




_______________" Mama Haydar  ya  barni  barina har Abada  shikena  mafarkina ya rushe  Kara fashewa tayin  tayi da kuka Mai ban tausayi

' Rarashin ta Mama tafarayi  tare da mata  nasiha Mai ratsa zuciya   

' Tadan samu sasauci dagane da radadin da zuciyarta  take mata..

Share  hawayen   dake  zuba a fuskarta tayin tace   kiyin hakurin Mama zuciya tace  take min zogi takasa jurewa a zabar radadin rabuwa da Haydar..

Tausayin tane ya Kara kama mama    hawayen da take boyewa ne suka xubo a kan fuskarta..

Daga kan da Ummeey  xatayi taga Hawaye naxirya akan kuncin Mama

Cikin tashin  hankalin tace  Mama kidaina  xubar da hawayenki  a kaina

Xubar hawayenki masifa ne a gareni

Hannu tasa tafara share mata Hawaye dake xuba a fuskarta..

Tace Mama hawayenki tsada gareshi a guna darajarsa  yafin  karfin zinare

Dan Allah mamana kada kibari hawayenki ya xubo Koda kuwa kan fuskar kine

Mama ki duba kingani inna murmushi Kuma hakan yasamo asalin ne tun daga kasan zuciyarta

Murmushi karfin halin Ummeey tafarayin Wai duk Dan taga ta kwantarwa da mama hankalin


***********

A bangaren Ango Kuma zaune yaken shida mahaifiyarsa

Yace momy  gaskiya ya kamata ace kinyin wanni abun akan wanan Aure da Abba ya keson  kaka bamin shi

Wai kamarni ace za.ayiwa Auren Dole
Kumama A rasa wace za a Auramin sai wacar kucakar

Nifa a duk family mu babu wacce natsana irinta

Kalonsa momy tayin tace  bazaka gane irin bakin cikin da yake damu naba akan Wanan Dan iskar Aure da Akeson maka

Nayin inya yina a kan ganin Abbanka ya janye wannan maganar Ama Ina yakin saboda taurin Kai irin nasa waishi a dolle  ga mai son kara kulla dankon  zumuncisu!!

Nifa Ina tunanin  baffa ka muhammadu asirin yayiwa Abbanka

Domin   iban Asirin ba  babu yarda za ayin ya nace yace Dole sai ya Auran maka wanan matsiyaciyar yarinyar

Kallon momy nasa yayi  gamin da cije lebe cikin takaici

Yace Ai ko wlh sai baffa muhammadu yayi danasani cusa Yar,sa gareni
Saina nuna Masa cewa zaran ba kalan yadin bane Koda An dinka bazan taban yi kyau ba

Murmushi momy tayin hadin da sauke anjiyan zuciya  tace My Son naci buri a kanka

Naci buri akan Aureka naso ace anyin  bikin inrin Wanda  ba taba yin irinshi ba  a cikin wanna kasar   Ama kash!!!

Sai gashi Muhammadu yazo Rana tsaka ya rusamin duk wani burina  a kanka


Kalon momy nasa yayi yace kwantar da hankalinki momyna  burinki bazai taba rushe waba

Zan Auro kalar matar da kike burin na Aura  za ayin bikin irin Wanda kike buri  za ayin watsi da Naira har sai kice ya Isa haka

Wanni dadine yaratsa zuciyar momy  take tajin duk wani bacin dake ranta ya kau  daga garenta 

tace my Son a ranar zan kasance cikin farin cikin  maran misaltuwa

Bude baki yayi zaiyin magana sai sukajin sallamar Mai gadin dauke da akwatuna a hanusa

Daga momy har Muhammad din babu Wanda ya Amsa sallama saima Bata fuska da sukayin 
gaishesu  baba Mai gaddi yayi ama ko kalonsa basuyiba bare har yasa ran xasu Amsa Masa.

dama in dasabo yariga da yasaba da halinsu haka yaita shugo da kayan  Yana gamawa yayi ficewarsa

Abba ne yayi sallama  yashigo dauke da far.a  a fuskarsa  muhammad ne Ya Amsa tare da fadin  Abba sanu da hanya cikin jin dadi

Abba yace yauwa kamar ko kasan Ina bukatar ganinka   gacan kayan lefe sun kamalla

Ina son a yaudina a kai kayanan anjima gwogwoka zatazo sukai kayan

kaikuma kaje kasamu kan,warka tafada maka Abubuwa  da suke bukata  Dan gane da bikin  kaga lokaci ya ta karatowa

Jiyayi zuciyarsa namishi zafin tankar Ana soka mishi mashi

Da kar ya inya amsawa Abba da toh

Momy ce taya mutsa fuska  tace amade baduka wanna kayan za.akai musu bako

Kallonta  Abba yayi cikin baci Rai yace mekike nufi da Wana maganar

Cikin takaici momy tace gani nayin kayan suyin yawa saikace wata Yar hamshakin Mai kudin za a Auro  alhalin Kuma Yar gidan matsiyatane

Cikin takaici Abba yace Yar Dan uwa nawa ne kike Kira  da Yar matsiyata to wlh kishi ga hankalinki

Muhammadu Dan uwa nane na jini yafi karfin kikirashi da matsiyaci

Kuma inaso kisani da ummeey da muhammad duka sun Yan,yanane
Matsayinsu daya ne a guna

Mikewa momy tayin cikin masifa tace kada kasake hada wacer matsiyaciyar da Dan,na Dan wlh ko makaho ya laluba yajin yasan Akwai banbanci a tsakani ..



By YAR AUTAR DASHEN ALLAH......✍🏻🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA🎅🏻



         . NA




UMMEEY MUHAMMAD LAWAN
          ( UMMU AFNAN)
YAR AUTAR DASHEN ALLAH




For more inf...08140801885





Page 27 & 28


___________________"Abba  Kam  shigewa daki yayi  ya kyaleta   tanata bambaminta shima Muhammad din cikin bacin rai  yayi ficewarsa   daga  gidan


Da misalin  karfe   3 : 40  Gwogo Halima ce ita da sauran Yan,uwa   suka nufi gidan yayanata


Momy dake fallo a zaune  tazuba  uban tagumi  abun duniya duk yabi ya isheta

Tana cikin Wana yanayine tafara jiwo hayaniyar mutane


Da sallama suka shigo fallo   Dakar Momy ta inya Amsa musu cikin daurewar fuska    tace ohh  Ashe kune 

Shiyasa naita jin hayaniya sai kace  wasu karnuka  cikin bacin rai Gwogwo halima tace kada kikuskura kikara budan baki kikiramu da karnuka wlh kishiga hankaliki  


Gwogwo  Asabe ce tace Dan Allah  Halima kubar maganar nan 

Mufa  Wana ranar Rana ce tafain ciki a garemu     kiga baidace Ace mutsaya Munata  sa isa da juna ba


Yakamata mu hanxarta mu dau kayanan mutafi kar  dare tayimana

Gwogo Asabe ne  Tak'arasa  Ida kayan suke  fara dauko kayan tayin  suka fara budewa suna dubawa


Kowa nagurin Saida yayi santii kayan Dan bakaramin kudin Abba ya kashe ba

Akwatiina Sha biyu kowane  a makare yake  da kaya      bude wata jaka sukayi sukaga  daleliyar waya sai daukar ido takeyi

Cikin jin dadi Gwogo Halima tace la kuga harda waya cikin kayan lefen  Suma karba waya sukayi suna xuxuta   irin kyau ta

Rabi ce tace Kai gaskiya  Ummeey tayin goshi Allah de yabada zaman lpy

Gwogwo Asabe ce tace ai dama can uwata  Mai sa.ce   da sa,arta take tafiya duk Wana da yarabeta saiya samu wanna sa,ar Kwoshewa sukayi da dariya 


Momy de nazaune a gun gaba daya haushisu takeji jitake kamar taje tarufesu da duka

Haka suka tarkata gaba daya sukayi waje motocisu Mai gadi da direba ne suka debo kayan suka sa a mota

Kai tsaye gidasu Ummeey suka wuce  dama mama tasan da zuwasu  itama  ta sanar da Yan,uwa da Abokan Arziki


Basu Bata lokaci ba suka inso gida  cikin girmamawa Yan,uwan mama suka tarbesu dama Kuma suba baki bane a gida domi gaba  dayasu  Yan,wa junna ne

Bude  akwaiina suka farayi kowa na kalon  irin dukiyar da aka zuba  a ciki

Haka mutane sukaita son barka  kowa nayiwa ummeey fatan zaman lafiya

Hauwa ce tashigo dakin cikin sauri  ta rugume Ummeey cikin farin cikin tace sister na kiyin goshi  kiga iri dukiyar da muhammad ya kashe  wajen gani yazuba mikin kayan lefe nagani nafada har da waya fa yasamiki  a ciki Kai amafa kemai sa.ace a rayuwa

Tureta Ummeey tayi daga jikinta  Ba,ta  fuska tayi tace nikuma kiga Wana kaya basa gabana

Jikin Hauwa ne yayi sanyi tace kiyin hakuri Ummeey   bawai nayi haka bane Dan nabata Miki Rai  saide a rayuwata nakaji farin ciki Ida Naga Abu alkairi a tatare dake

Girgiza Kai ummeey tayin tace duk iri dukiyar da Yaya muhammadu zai  kashe a kaina wlh bazasu taba sani farin ciki ba

Hauwa hijjabi ta tadauka tace kigani  sai gobe Dan Naga zance naki ba Mai karewa bane ficewa Hauwa tayi tayiwa mama sai da safe


**********************

Kano


Tuda Haydar suka kama haryar Kano  Adam yaketa fama Masa nasiha  suna shigowa cikin  Kano

Adam har gida yakai Hayda  suna shiga suka Tara da dady da Ammy suna hira

Gaishesu sukayi  ciki kullawa suka Amsa  suka musu Yaya gajiyar hanya

Ammy  ne  ta dubesu ciki kullawa ta ce  yanaganku haka jiki duk a mace kode Baku sameta bane

Shide Haydar kasa magana yayi   gani suyi shuru babu wada yabata Amsa
Ammy tace wai meke faruwa ne kusanar da mumana

Adam ne yayi karfin halin yasanar dasu duk abuda ya faru ..
Ammy da dady Suma basuji dadin  faruwa haka ba ama yayazasuyi  Basu insa su sauya Masa kaddara Saba

Haka dady da Ammy sukaita rarashisa akan ya manta da komai  kalamai iyayyenasa suyi tasiri a kansa  domi ko ya rage yawan damuwa da tunnani



Gombe

*****************
Muhammad ne  tsaye  a kofar gidasu  Ummeey  fuskarna a murtuke babu a Lamar far,a atare dashi

  yaro ya aika  akan yakira Masa  ita Bata wani Bata  lokaci ba tafito insowa tayi inda yake tare da  Masa sallama 

Bai Amsaba saima binta yayi da wani wulakantece  kallo  kasa tayi da kanta Tana wasa da Yan,yatsu hanuta

Ciki gadara  yace Mai kike bukartayi a bikinaki
Dago Kai tayi ta kalesa ciki sanyi murya tace a a bana bukatar komai

Bude motasa  yayi  ya ciro kudi masu yawa ya mika mata

Kin karba tayin  tsawa ya daka mata har Saida ta razana batasan lokaci da Tamika hanu ta karbaba

Cikin sauri ta wuce gida


*****************

A YAUNE DUBA JAMA,A  SUKA  SHEDA DAURI AURE

Muhammad Abdallah  Shu,Abu & Ummeey  Muhammad Shu,Abu   Abisa  sadaki Naira dubu dari dauri Aure da yasamu halatar duban jama.a daga sasan jahohi daba daba

Gidasu  Amarya yacika da jama,a sai hidima akeyi   kowa kagani zakasan Yana cikin farin ciki

Ama bada Ummeey dataketa Aiki kuka  hauwa sai rarashinta takeyi Ama Ina Taki tayin shuru

Abba ne yashigo yatura mama takira Masa ummeey
Shigowa daki mama tayi  kama hanuta tayi tace tashi muje gacan Abbaki Yana kiranki

Bin mama tayi suka nufi dakin Abba Yana zaune a kan kujera   durkusawa tayi a gabansa

Gyara murya Abba yayi yafara mata nasiha akan taji tsoro Allah tabi mijinta  nasiha Abba yamata Mai ratsa zuciya 

cikin kuka Ummeey tace  Abba namaka Alkawari  zan zamo Mai biyyayah ga mijina  bazaka tabajin wani Abu Mara dadi daga gareni ba 

Abba kayafemin duk wani abuda na aikata a gareka wada ranka bai soba

Cikin tsanyi jiki Abba yace  babu abuda Kika taba min tsakanina dake sai Adu,a Allah yamiki albarka Allah ya Baku zuri.a danyiba
Kara fashewa tayi da kuka

Kama hanuta Mama tayi suka fita daga dakin  mama tace da hauwa kuyi kushiya kuga gacan Yan dauka Amarya sufara zuwa

Mamaa ma hawayene keshiri zubowa daga idonta tayi sauri Mai dasu

Dakyar hauwa tasamu Ummeey tashiya  haka Yan,dauka Amarya suka shigo

Dakar  aka banbare Ummeey a jikin mama  kuka Ummeey takeyi sosai  mama ma kuka tafara 

Haka ummeey tanaji Tana gani  tabar mamanta  acikin motar ma Ummeey Bata dena kuka ba  suna insowa gida kowa yafito daga mota ama ita  Taki fitowa

Gwogwo Halima ce tajawota daga cikin motar  sukayi cikin gidan

Gidan ya tsaru sosai kowa sai Yaba kyawu gidan yakeyi  

Domi Muhammad bakaramin kudin ya kashewa gida ba

Mutane suka wawatse gida yarage daga ita sai hauwa......



By YAR AUTAR DASHEN ALLAH....✍🏻            NA

UMMEEY MUHAMMAD LAWAN
     ( Ummu Afnan)
"YAR AUTAR DASHEN AoLLAH


For more inf... 08140801885



Page 29 & 30

___________________"mikewa  Hauwa tayi tace Sister  ya kamata nima yazukan natafi gida kiga dare yayi

'Rike gyaleta   Ummeey tayin  tace  kema tafiya zakiyin kibarni a  cikin wanna gida nikadai
Takarashe maganar  kamar Mai Shirin yin kuku

Hauwa tace kiyi hakuri Sister  ya zamo dole  natafi babu yarda muka inya Aure  ya riga da yarabamu     

'kuka ne  Mai karfi ya kufce mata ciki kuka  tace kidena fadin haka   yin Aurena bawai Yana nufin  mu rabu da juna bane  ai shin Aure ba mutuwa bane  munana tare nidake insha Allah  itama Hauwa fashewa tayin da kuka suka rugume juna

'A haka de  Hauwa tawuce gida cikin Rashi jidadin rabuwa da Aminiyartata


**********************


Shiko  Ango jin Wana ranar yake kamar ranar mutuwarsa  Tsatsar  baki ciki ne bayane a fuskarsa
Isma,il ne yace  Abokina yakamata Ace yazuka kawuce gida   Amaryarka tanacan Tana jiranka

'Wani mugun kallo ya watsa masa cike da jin hashisa yace  in naje gidan uban mezamata  Kai kasan yanda natsani yariyarnan kuwa 

Isma,il yace nifa Muhammad banga ai bun  yariyarnan ba  Ummeey  Tana da kyau  Tana da ilimi Tana da tarbiya  duk wani Abuda  ake nema  a  gun mace to Ummeey tana dashi  

"Muhammad  Mai kake nema Agun Mace wada Ummeey bata dashi kada kamata ita dinfa jinikace    kajin tsoro Allah karike yariyarnan  tsakani da Allah idafa har kacutar da ita Allah bazai taba barinka ba


'cikin fushi yace takatta✋ Mallam  wanan Yar guntuwar nasihar taka bazatayi  tasiri a kainaba

Naga a lama Kai  bakasan Mai akenufi da Aure dolle ba  bakasan radadin dake tatare dashiba

Cikin  fushi yatashi ya shinu mota keey yayiwa mota  yafigeta da karfi har Yana tada kura
Isma,il bisa yayi da kallo yace Allah ya shiryeka Abokina  bazaka taba gane irin gatan da Abba yayi makaba sai nagaba 

'yana insowa gida hon yafarayin Mai gadine yazo cikin sauri  ya wangale geet din

Shigowa yayi    ya  kashe motar yafito Mai gadi ya gaisheshi  daga Masa hanu yayin
yayi shigewarsa ciki

kaitsaye dakinsa yanufa   dakin bakaramin haduwa yayiba  komai na dakikin farine kal  sai daukar ido yakeyi

Cire kayan dake jikinsa yayi ya wuce tolet  wanka yayi yafito ya wuce gaban Miro goge jikinsa yayi da tawul

  Mai ya shafa sana yafeshe jikinsa da turare masu kamshi  kaya barci yasa  ya haye kan gado wayasa  dake ta fama  Kara ya dauka  karawa yayi a kunesa

Yace  hello baby  y kk ?
Cikin shagwaba meenat  tace tooo gani na de kwance  cikin tunanika   zuciyata takasa samu nutsuwa

  idan natuna cewa yau zaka hada jiki dawata Yan mace baniba sainaji zuciyata tankar zata tarwatse  nakasa yarda da Alkawari daka daukamin


"Kwantar da hankaliki baby   ai babu wata Yan,mace dazan inya hada  jiki da ita   "Idan bakeba

"Kikara hakuri baby nan dawasu Yan,kwanaki zanje nasamu Abba  nasanar dashi kece zabina   yaje yasamu dadynki  a yin maganar Aure mu

Wani sanyi dadi taji naratsata  cikin fari  ciki  tace too baby kamar nan da wane lokaci  kena Dani gaskiya  namatsu Naga anyi bikinan kowama yahuta..

Muhammad yace aini nafiki burin gani Wana Rana ama karki damu kamar yau ne ranar zatazo kiji baby na   yaxu Dee barci nakeji zan inya cemiki good night

Cikin shagwaba Meenat tace ko nazo natayakane nasa sai kafijin dadin baci musamama idaka daura kanka a saman kirjina 

Murmushi Muhammad yayi yace   sauri mekikeyi baby  lokaci hakan yanana zuwa kamar yaune

Uhmm  ida nabiyeki sai mukwana  a haka  byeee kikulamin da kanki ilove you so much kashe waya yayi   wani fari ciki ne ke shigarsa  murmushi yayi yace

Meenat kekadance kike sani fari ciki Koda Ina cikin damuwa  Ina sonki Meenat


*********************

'Hauwa natafiya Ummeey  waka tayi tadauro alwala  tayi sallah tadade a kan salayan Tana rokon Allah da yabata ikon yiwa  mijinata biyayyyah  baci ne Mai nauyi yayi awun gaba da ita 

Bata farkaba sai da Asuba  tashi tayin tannufi bayin  dauro Alwala tayi  tatada Sallah
Tana indarwa  Alqu,an tadauka tafara karata Suratul Maryam

Agogo taduba taga karfe 6:30 rufe Alqur,ani tayi  tatashi tanufi kichin domin tamusu Abun karyawa

dubawa tayi taga duk wani Abuda Ake bukata nakayan Abinci akwaishi a kichin din

Dankalin tasoya da kwai sai farfesu kifin da ruwa tea Tana gamawa tashige daki


wanka tayi tafito  tazauna a gaban Miro  kwaliya tayi wada hakan yakara fito mata da kyauwu fuskarta

Bude Akwatin kayan lefenta tayi taciro wata doguwar riga baka Tasha adon siton


rigar tasaka tayafa dankwalin rigar a kanta

bakaramin kyau tayiba kichin Takoma tadebi Abinci inya wada zata iyaci 

Jerawa  kuloni tayi akan wanni hadadden tire 


dauka tayi tanufi dakisa  gabanta nafaduwa A hankali tamurda kofar tashiga bakinta dauke da sallama

Zaune yake a kan kujera ya daura kafa daya kan daya

Karasawa tayi Ida yake durkusawa tayi a gabansa ta ajiye tiredi dake dauke da Abinci  cikin girmamawa tace Ina kwanna Yaya.

Dago Kai yayi ya sauke idanusa Akanta take yaji wani sabo tsanarta yakara shiga zuciyarsa.

  ciki bancin Rai yace keeeeee.. ubawa yace kishigomin daki

Kasa tayi da kanta tace Abincika nakawo maka Naga baka fito bane  duban tiredin dake gabansa yayi hanu yasa ya dau  kofin dake dauke da TeA a cikin dagowa yayi yawatsa mata a fuska

Wani iri Kara  Ummeey tasaka sakamoko zafin dataji Akan fuskarta


Mikewa yayi yamatso daf da ita cikin kakausar murya yace a gidan uwarki nake cin Abinci dazakiyi tunani tuda nabar gida ba Mai bani Abici

konayi Miki   kama dawanda zaki kawowa Abu yaci to wlh duk ranar da kikasake shigomin daki saina ballaki

Zaki Fitamin daga daki Kosaina ballaki wawiya kazama

Hawayene ke zirya a fuskarta maganganusa sumata ciwo musamama zaginta dayayi a duniya babu Abuda tatsana  irin a zagin iyayenta

Fita tayi daga danki  a fallo ta zauna kifa kanta tayi a kan kujera  tafara raira kuka Mai tsuma zuciya.....




BY YAR AUTAR DASHEN ALLAH.....https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*

_*ZAƁIN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_

For more inf...08140801885



Page 31 & 32

___________________Bugu kofar da  Akeyine yasata daga kanta share Hawayen da suka Bata mata fuska tayi

tashi tayi tanufi bakin kofar hannu tasa tabude  Gwogwo Halima ne ita da Hauwa

Murmushi jin dadi tayi tace sanu da zuwa Gwogwo Sister kekuma sai yazu kikaga dama zuwa ko  Aini fushi nakeyi dake

Kallonta Gwogwo Halima tayi tace  yau Naga ikon Allah yaushe ma garin ya waye to da Asuba kikeso tazomiki gida

Hauwa tace kyaleta Gwogwo so takeyi nazo  da sasafe ya muhammad ya korani  dariya Gwogwo tayi

Ummeey Kalon Hauwa tayi ta wuga mata harara  Kara Kwashewa da dariya Hauwa tayi tace  Gwogwo kiga Tana harata ko saboda nazo gidanta

Dariya Gwogwo tasa tace Ai kunfi kusa babu ruwa na

Gwogwo tace kehaka ake tarbar baki bazaki bamu gurin zama ba

Ummeey Tace lla Gwogwo kiyi hakuri duk gawace tabi ta insheni da surutu tanuna Hauwa  Hauwa tace nikan karkimin Shari kede dama haka kike.

Zama sukayi a kujera  Ummeey takawo musu lemo da ruwa  sai a lokaci tatuno bata karya ba

Tashi tayi nufi kinchi tadauko kullolin data zuba nata Abinci ta ajiye a gabasu

Suna cin Abinci suna hira Gwogwo nabasu labarai  sukuma sai dariya sukeyi dama Kuma Gwogwo takware wajjan barkonci da bada dari


Muhammad dake zaune a dakinsa ya soma jiyo hayaniyar tasu tsaki yaja a ransa yace wato yariyarnan hartafara jidomin tarkace mutane a gidana

To wlh gaba daya sainayi maganisu mikewa yayi ya fito daga dakin kaitsaye falon nata yanufa


Gwogwo ko suna gama cin Abinci  tace zata zaga bandaki Ummeey tanuna mata inda bayin yake

Ta dawo tafara gyara gurin dasuka cin Abinci

Yana insowa inda take tsaye hanu yasa ya sharara mata wasu lafiyayu maruka Wanda Saida shatin yatsutsa yafito a kan fuskarta

tangaltagal tayi zata Fadi Hauwa tayi sauri tatareta kuka  tasaka Mai karfi wada yayi sanadiyar fitowar Gwogwo daga  bayin

Cikin sauri Tak'araso Ida suke  kalon  Ummeey tayin taga  Hawaye nazuba  a idonta gakuma shati maruka kwace a kan fuskarta

Kallon Muhammad din Gwogwo tayi cike da tuhuma ciki baci Rai Gwogwo tanunasa da yatsa tace Kaine kamareta ko?

Ciki Rashi girmamawa  yace eh nine  Ai dama duk Wanda ya sayin rariya yasa Dole tazubar da ruwa

Kunefa kuka dage akan gani saina Auri yariyarnan 
Bayan kusa cewa a tsarina babu Aure Yar matsiyata
Abbanta' ya hada Aurena da itane duk Dan yacin Arzikina
Ama wlh kuji naratse Nairata bazata taba  ciwu a gunshiba

Ciki barci Rai Gwogwo tace  Muhammad kaci Amanar zumuncimu Allah bazai taba barinka ba

Dakake ikirari cewa Yaya muhammadu ya baka Ummeey ne domi Arziki da Allah yabawa Mahaifinka

To kayi kuskure kajeka Tambayi Abba naka Arziki dakuke tikafo dashi kaida mahaifiyar taka to Yaya muhammadu ne silar Arziki Abba naka

Ama wai yau  an  wayi gari Dan, Yaya Abdallah shike cin mutunci Yaya muhammadu  wlh Ina jiyemuku ranar da kwai zai fashe

Daga mata hanu yayi yace dakata Gwogwo  inajin kuyarki ya isheni jin Wana surkule naki Mai kama da Tatsuniya

Nibamasa Mai ya kawoku gidana ba kodama An Aura min itane Daku dinga zuwa kuna cika min gida

Kalon Ummeey yayi a wulakance yace kekuma wlh idan kikasake bari wata tashi gomin gida sai nalahira yafiki jin dadi  Tsaki yaja ya wuce daki

Gwogwo  sake baki tayi Tana kalonsa mamaki ne karara a fuskarta  batataba tunani Rashi mutunci nasa ya Kai hakaba

Gwogwo rarashi Ummeey tafarayi tayi mata Alkawari za,ayiwa tufkar hanci zata sanar dasu Abba Akan a Raba Aure

Ama Ummeey taita roko Gwogwo akan kada tasanar da kowa tayiwa Abbata Alkawari bazai taba jin wani Abu daga garetaba

Dakar  Gwogwo tahakura  tashi sukayi zasu tafi ciki sanyi jiki Hauwa tace Sister Ina waya da akasamiki a kayan lefinki kidauko natura Miki WhatsApp kiga Zaki rage wani damuwar

Tashi Ummeey tayi tanufi daki bude Akwatin tayi taciro waya tamikawa Hauwa  dama Akwai sim akan waya

WhatsApp

Please Login or Register in order to submit comment