Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xanje gun haydar ne . Anbani sakone nabashi mom tace Allah sarki haydar yaron kirki Allah ya yaye Masa wannan damuwar cikin farin cikin Adam yace amiin mom ama damuwar haydar daga yau tak'are da inzzin Allah..

" Mom natafi lokaci nak'uremin saina dawo.. mom tace Allah yatsare a dawo lpy

kalonsa dady yayi Yana Mai jinjina wanan kafin shaku,wa tsakani haydar da Adam...!

Koda Adam yafita baitsaya a ko Ina ba sai gidasu amininasa ..
'Sallama yayi Ammy ta amsa gasheta yayi ta amasa tace Adam ka dawo kenan to ya hanya ? Adam yace hanya Alhamdulillah Ammi tace Masha Allah
kashiga Yana ciki tashi yayi cikin sauri yayi ciki d'akin...!

Kwace yake akan gado sallama yayi yashigo d'ago idanusa yayi wada suka kada sukayi jah

Ya saukesu akan Adam k'arasawa yayi bakin gadon ya xauna a gefensa cikin xumud'i Adam yace al-bishirika kawar da xance haydar yayi yace yaushe ka dawo Dan, yasan halin abokinasa yaxunan xaita damusa da labaren wai duk Dan yaga yasashi cikin farin ciki

'Adam yab'ata Rai yace bansani ba nide so nake ka Amsa min da goro shima hayday b'ata fuska yayi Alankalin yace goro!!!

'Adam yace kasan naje gombe har nayi kwana uku to nayimaka tsintuwa ta soyayyah na hadu da ummeey xabura haydar yayi yamik'e yace da gaske kakeyi Adam?

'Adam yace haydar nahad'u da ummeey ummeey tak:ara kyau kaminninta ya canja har banganetaba!!!!

Tace taxo Kano har sau biyu naimanka ama bata gan kaba haydar ummeey alkawarika Bata yada ba takaini har gidasu muka gaisa da mahaifiyarta
Gashi tabani sak'o nabaka haydar karb'ar takarda yayi hannusa na rawa yabud'e ya fara karantawa yayi........




By ummeey muhammad lawan...✍🏻https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*

_*ZA6IN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_



_*Page 13 & 14*_


_______________ _*Assalamu Alaikum  gaisuwa Mai yawa  ga masoyina tare da fatan alkairi a gareka   haydar  nabaka malakin kaina harda ruhina  nasan baxan mace bamu ganaba  inanan xaman jiranka masoyina  gobe kaxo ban yarda  ka haura ba*_
_*Koda baka shiryaba  shukar dakayi haryanzu baici wani ya girbe ba!!!*_

Rungume Adam Haydar yayi cikin farin ciki  yace "in sha Allahu Ummeey na gobe xan amsa kiranki  zan ziyarci Gombe garin masoyiya ta.!


janye jikinsa yayi a jikin Adam  yace "nagode d'an uwana Allah ubangiji ya saka maka da mafifin cin alkairi ha'ki'ka kai kafi 'karfin aboki saide nakiraka d'an uwa "

Adam yace karka damu Haydar burina shine naganka cikin farin ciki yanzu sai muje musanar da Ammy ko.?

Tare suka fito suka nufi inda Ammy take zaune  Tana lazimin  Haydar yace  " Ammy "Ammy " albishiriki   yau ba'kin ciki na yatafi

"Farin cikina ya dawo gareni  Adam ya gamu da Ummeey  Ashe Ummeey tana can a garin Gombe.!

Itama Ammy farin cikine yakamata saka makon jin wannan labari
gashi kuma farin cikin d'an nata zai dawo gareshi
Ammy tace "toh saiku saka ranar dazakuje Gombe ko..?

kamun Adam yayi magana Haydar yace ai Ammy gobe  zamu tafi Gombe

Ammy tace "ai dakun bari zuwa jibi kaga gobe dadyn ka zai dawo daga Abuja 

" Eh Ammy nasani Amma dan Allah kibarni natafi gobe indan dady ya dawo saiki masa bayani

Ammy Bata musa masaba tace to Allah yakaimu gobe

Haydar ya dafa kafadar Adam yace Adam kaje kayi bankwana dasu mom domin kasan gobe samma ko zamuyi

Dariya Adam yayi yace "karka damu abokina baka da matsalla a wajena  fatanmu dai Allah yanuna mana gobe cikin 'koshin lafiya.    yace "Amin.

Ammy tace "Adam sannu da 'ko'karifa  Allah yasaka maka da mafifincin alkairi , Adam yace "bakomai Ammy ai Haydar d'an uwana ne..

" Banajin akwai wani abuda Haydar zai nema aduniyar nan inde har Ina da hanyar da zanbi ya malaki wannan Abu toh yaxamo min dolle nate maka masa  , Ammy burina shine  Naga Haydar ya mallaki ummeey , tuda itace farin cikinsa...!

Ammy za tayi magana Adam yace "Ammy nizan wuce gida.

Godiya Ammy tayiwa Adam sosai  sannan tace ya isar mata da gaisuwata gun mom d'inshi

Haydar yaraka Adam har bakin get  sannan sukayi sallama

Haydar ya dawo ciki  ya zauna kusa da Ammy yace "Ammy na wlh jinakeyi kamar mafarki nake.


Hira sukayi sosai shida mahaifiyar tasa wanda rabon da suyi irin wannan hiran har sun manta  itama Ammy taji dad:in ganin d'an nata datayi cikin farin ciki.

" Haydar zanso  ace kullum ka kasan ce cikin farin ciki  da kwanciyar hankalin zanso ace kullun nadinga ganika cikin farin ciki Haydar inaso kakoma kamar da d'inka.!


Murmushi yayi yace "Ammy na nayi miki alkawari kullun xaki ganni cikin farin ciki   Ammy xanje na kwanta kinga gobe san mako zamuyi.

Mi'kewa yayi yayiwa Ammy sai da safe ya wuce d'aki
Kwanciya yayi, lumshe idanusa yayi ya bud'esu yana murmushi  , Haydar ya 'kosa gari ya waye , barci barawo ne ya daukeshi kamar a mafarki yakejin kiran sallar asuba tashi yayi yashige toilet yayi wanka ya dauro al'wala  yatafi masallaci  koda aka idar da sallah yayi Addu'oin sa nan yayi gida dama tun dare yahad'a kayansa  fitowa yayi yayiwa Ammy sallama tayimasa fatan alkairi dafatan nasara a rayuwa.

Motarsa ya d'auka kaitsaye gidasu Adam yanufa.

Dama Kuma Adam yasanar da mahaifansa cewa zai raka Haydar Gombe

Yana insowa  'kofar gidan  wayarsa ya d'auka yakira Adam bai wani bata lokaciba yafito yashiga motar suka d'au hanyar Gombe.

Tuki Haydar yakeyi cikin kwanciyar hankali    kana ganin haydar xaka tabbatar dacewa yana cikin farin ciki domin hakan ya bayyana a fuskarsa

Karfe 11: 00  dai-dai su Haydar suka inso  cikin garin gombe.

Kai tsaye unguwar jeka dafari suka nufa   sunna insowa kofar gidasu Ummeey  yaro suka aika  yayi musu sallama da Ummeey  yace " inji haydar ne.

Yaro  ne yashigo yace "wai ana sallama da Ummeey inji haydar.

Ummeey dake tsakar gida Tana shara sake  tsitsiyar tayi.......

_*By*_
_*ummeey muhammad lawan.....✍🏻*_
_*'YAR AUTAR💃🏻 DASHEN🌲 ALLAH*_https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*

_*ZA6IN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_


_*Page 15 & 16*_

_______________Sake tsintsiyar dake  hannuta tayi  cikin hanzari Ta zari Hijjabinta tayi Wake

'Kara sawa Inda suke tayi cikin ta kun ta mai daukan hankali

Haydar da tunda  ummeey tafito yakura mata ido ko kiftawa bayayi  tabbas ya gane takun sawunta  fuskar tace kawai Ta canja Masa


'Kara sowa tayi garesu tare da sallama abakinta  haydar  daya mace wanjan kallonta  bai masan tayi sallama ba  Adam ne ya Amsa sallamar

Kallon-kallo  suke yiwa junansu   hawayen farin ciki ne suka zubo daga fuskarta hannu Haydar yasa ya tari hawayen

ta dur'kusa akan gwi woyin ta  d'aga hannu wa tayi sama tace ya Allah kai ka d'ai nake bautawa Kaine majibanci lamurana ya Allah kasa gurin Haydar naxamo mata!!!!

" Tsareta yayi da indanu cikin shau'kin son ta yace 'in sha Allah Ummeey  Haydar nakine  Abaya " 'kaddara tayi Nasaran rabamu  amman a  yanzu  muke da nasara akanta !!

wani sanyi Ummeey taji  Yana ratsa xuciyarta  gakuma wani shaukin  son haydar dayake shiga cikin xuciyarta

Haydar nasha wahalar a rayuwa  rashinka Babar musifa ce a gareni   tabbas kaid'in kakasance jinin dake gudana a jikina ne  tsawon wannan shekaru damuka d'auka bama tare da junna wlh ina rayuwane kamar wata mutun mutumin

' Tausayinta ne yakama Haydar ciki raunan niya murya  yace " Allah sarki Ummeey ha'ki'ka so ba 'karya bane  

Inaso kisanar dani dalilin barinku Kano,  kun bar Kano batare da nasan dalinliba

Kallon cikin kwayar idonsa  Ummeey tayi cikin sanyin murya tace

A ranar da kazo gidan mu domin muyi bankwana zaka wuce kaduna   Aranar ne aka sanar da Abbana rasuwar mahaifinsa 

Washe gari da sasafe muka kama hanyar zuwa gombe bamu dawo ba saida akayi sadakan uku nida mama muka dawo mukabar Abba acan  domin Abba yasanar da mama cewa sai anyi  bakwai zai dawo

Mun dawo Kano cikin alhenin rashin kakana domin ko munsha'ku dashi  sosai

Anyi sadakan bakwai  yayan Abbana abdallah yake sannar da Abbana wasiyar da mahaifisu yabarmusu cewa Abba yabar Kano  ya dawo mahaifarsa da xama  koshima zai huta da yawon hanyan da yakeyi

Abbana baiyiwa yayan nasa musuba yakar6i  wasiyar da  mahaifinashi yabar Masa  haka Abba ya dawo Kano yake sanar da mama 

Mama Bata tada hankalinta ba hasalima farin cikin tayi domin itama tagaji da yawon hanya da mukeyi

Ahaka mama ta kwantarwa da Abbana hankali har yasamu nutsuwa

Mama ne take sanar dani yarda sukayi da Abbana take najini ina jiri saura kadan nazube 'kasa batare dana shiryaba

Bakaramin firgici da tashin hankali nashiga ba tunanina baiwuce Ina xansamu Adam abokinka  nasanar dashi tuda kai baka gari..

Gashi nibansan innane unguwarku ba duk  zamana dakai bantaba tanbayarka inane unguwarku ba kuma kaima bakataba sanar daniba

Haka inaji Ina gani muka tarkace kayamu mukabar Kano   bayan mukoma gombe nakasa samun nutsuwa sakamakon rashinka  shine nanemi alfarma a gurin mamana akan tabarni naje Kano nemanka ko Allah zaisa nasameka

Mama ta amincemin tabarni haka nakama hanyar Kano  batare da Abbana yasaniba na sauka a gidan ka'war mama.
Aranar nasha yawan nemanka ama bansameka ba  haka na ha'kura nakoma gombe  cikin ba'kin ciki

Duk da hakan ban saduda ba haka nasake komawa Kano  nemanka Allah bai had'ani da wanda yasanka ba  sai a wanan lokaci , nayi takaicin hanani ri'ke waya da Abbana yayi.........

By ummeey muhammad lawan ( ummu Afnan).......✍🏻_Date:-_ 2022/11/08


*🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA👳🏼‍♂️*



               _NA_


*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN (Ummu Afnan)*


*💃YAR AUTAR 💃🏻DASHEN🍃ALLAH*



__For more inf... 08140801885__




Pages  17 & 18



_______________Haka na koma gida  ba tare da son rai na ba, tsawon wannan lokacin ina. rayuwa ne cikin 'kunci da tashin han kali.



Komai baya min dad'i cikin wannan duniyar, haka na mi'ka. lamarina ga ubangijina domin ko ina ji a jikina watarana zamu had'u.



Ta 'karashe maganar cikin kuka.



Tsan tsar ta shin han kali ne suka bayyana a tare da Haydar ganin hawayen dake zu ba daga idanun masoyiyar ta sa.



Cikin rauna nan niyar murya, Ya ce"Share hawayen ki rabin jikina na yi miki al'kawari daga yanxu. ba xan 'kara barin hawaye su xuba daga wannan kyakyawar fuskar taki ba"



"Adda Hawaye marasa adadi sun fito daga cikin idanun mu ba'kin ciki mara misaltuwa ya d'ar su a cikin zuciyar mu tsawon shekaru uku, mun shiga tashin han kali da rud'ani sakamakon nesa da juna da xuciyoyin mu su kayi.


Sai gashi Allah ya 'kara had'amu a karo na biyu"



Ummeey mu godewa. Allah kin ga ka d'an daga cikin ni'imar ubangijin mu, bayan mun d'au wasu shekaru bama tare sai gashi Allah ya sake had'amu"



Cikin 'karfin gwiwa Ummeey, Ta ce"Ha'ki'ka Allah shine abin godiya, Allah nagode maka daka nunamin wannan ranar da naga fuskar masoyi na"



Murmushi Haydar ya yi wanda ya 'kara fito masa da kyawun sa.



Ya ce"Adam kaga ikon Allah ko wai yau ga Ummeey ga Haydar"



Shima Adam murmushi ya yi, Ya ce"Ai ni yau rana ce ta farin cikin a gare ni yau gashi aboki na ya kasance cikin farin ciki bayan shekarun da ya kwashe yana cikin 'kun ci sai gashi rana tsaka aboki na ya dawo asalin Haydar d'in da na sani wanda kullum idan ka kalli fuskarsa xaka ganshi cikin fara'a damurmushi"



Murmushi Haydar ya yi, Ya ce"Nagode sosai abokina ba 'karamin. gudun mawa ka bani a rayuwata ba, kaine kayi sanadiyar samuwar farin ciki na.

Kullun burinka bai wuce a ce ka ganni cikin farin ciki ba, Adam kafi 'karfin aboki sai de na kira ka da Amini ko d'an uwa na jini"



Haka su kaci gaba da hirar su cikin farin ciki da annashuwa musamama Ummeey da Haydar wanda. Suke cikin shau'kin so.



Da xa'a tsaga cikin zuciyoyinsu babu abin da da za a gani in ban da tsan tsar 'kauna da shau'kin so.



Suna cikin hirar su sai ga Abba har xai wuce cikin gida sai kuma ya dawo baya.



Ummeey da ba tama lura da Abba ya 'karaso in da suke ba, ckin 'ba'cin rai Abba.



Ya ce"Keee! Ummeey me kike yi anan?"




Cikin firgici Ummeey, Ta ce"Abba sannu da dawo wa"



Dur'kusawa Haydar da Adam suka yi har 'kasa cikin girmamawa suka gaishe da Abba.



Amsawa Abba ya yi, y afara tambayar mai ya kawo su cikin jin kunya Haydar ya fara masa bayani.



"Abba ni ne Haydar. wanda ya ke xuwa gun Ummeey shekarun baya da su ka wuce"



Mamaki ne ya kama. Abba cikin sanyin jiki Ya ce"Ayya na gane ka mu shiga daga ciki"



Abba ya yi musu iso harxuwa cikin gida, haka su Haydar suka gaisa da Mama Ummeey ta kawo musu abinci da ruwan sha, sun ci abinci cikin farin ciki.


Shi dai Haydar duk in da Ummeey ta yi idonsa na kanta sai da suka gama cin abincin Abba ya shigo suka sake gaisawa cikin mutuntawa.



Jikin Abba ba 'karamin san yi ya yi ba, fuskarsa d'auke da damuwa ya rasa mai xai ce da Haydar domin shima shaida ne akan irin 'kaunar da su kewa junna su.



Cikin san yin jiki Abba, Ya ce"Haydar ina mai baka ha'kuri ka xo a 'kurarren lokaci domin kuwa kwana kakwai ya rage auren Ummeey na bata Muhammad d'an yayana Abdallah, ka yi ha'kuri Haydar hakan ta faru ba'a son rai na ba"



Ummeey dake gefe tana jin kalaman mahaifin nata take ta xube 'kasa a sume.





__By ummeey muhammad lawan (ummu Afnan)…✍🏻___Date:-_ 2022/11/09


*🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA👳🏼‍♂️*


             _NA_



_UMMEEY MUHAMMAD LAWAN ( UMMU AFNAN )_


_{YAR AUTAR DASHEN ALLAH}_



*DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION*


*D.A.W.A*

https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783


__For inf...08140801885__



Page  19 & 20



_______________ Cikin tashin  hankali Mama ta'karasa in da Ummeey take a yashe, jijjigata Mama ta fara yi taga babu alamar numfashi a tare da ita.



Fashewa ta yi da kuka tana fad'in, "Na shiga uku mai ya ke shirin faruwa dani, Ummeey  ki tashi na yi miki al'kawari muddin ina raye sai burin ki ya cika"




'Karasowa Haydar   ya yi in da take, dur'kusawa ya yi a gabanta  idanun sa na xubar da hawaye.



Cikin kuka, Ya ce"Ummeey ki tashi  zama dake babu mai hannani, idan kin ga ban aure ki ba   to tabbas  ruhi na ne  ya bar jiki na"



Haka Haydar ya din ga kuka yana sambatu.



Tashi Mama ta yi ta nufi in da randar su take, ruwa ta d'ebo a kofin tanu fi in da Ummeey take ta yayya fa mata ruwa.



A hankalin Ummeey ta fara bud'e idanuta  jin ruwa mai san yi na sauka akan fuskarta, ajiyar zuciya ta sauke mai 'karfi take abubuwan da suka faru suka fara mata yawo a 'kwa'kwalwarta.


Kallon Haydar d'in ta yi ta ga hawaye na xuba a fuskar shi  take tausayin sa ya kara kamata.



Yun 'kurawa ta yi ta tashi  ta nufi in da Abban nata yake     zaune babu alamar fara'a a tare da shi  murtuke fuska ya yi tsantsar 'bacin rai ne suka bayyana a fuskarsa.



Dur'kusawa ta yi  a gaban shi, Ta ce"Ka yafe min Abbana  bawai maganar da ka yi zan yi musu ba, Abbana bawai ina musu da kai bane akan  za'binka   na san ba xaka ta'ba za'ba min abin da xai cutar dani ba"


"Ka yafe min zuciyata ta kasa ha'kura da Haydar, Abba ka taimaka ka auran dani ga Haydar.

Abba idan baka aura min Haydar ba xan ha'kura da aure  har abada!!



Kallonta Abba ya yi cikin 'barci rai, Ya ce"Keee! Kin ga nayi miki kama da wanda xai yi al'kawari ya kar ya, to wallahi kin ji na ratse muddin ina numfashi a duniya  wannan aure babu fashi sai an yi shi ko da ko a ce idan an kai ki gidan xa a dawo min da gawarki ne"


Ummeey ba 'kara min firgici ta shiga ba,ta firgita kwarai da kalaman mahaifin nata  ta san shi yadda yake da tsauri akan ra'ayin sa.



Shi dai Haydar bai ce komai ba ido kawai ya xubawa Abba.



Adam ne ya yi 'karfin hali, Ya ce"Abba kayi ha'kurin mu barwa Allah lamarin  idan Allah ya 'kaddara Ummeey matar Haydar ce to babu mai hanawa, mu xamu wuce Allah ya xa'bar mana abimda yafi alkairi"



Mama Ta ce"Ameen ya Allah, amma dai ba Kano xaku wuce ba ko?"




Adam Ya ce"Eh da ke akwai kakata a nan d'in can xamu wuce  mu kwana"



Adam ya kama hannun Haydar su ka yi ficewarsu daga gidan Mama tana yi musu Allah ya kiyaye.



Ummeey na ganin fitarsu fashewa da kuka tayi.




Abba ko ko kallonsu bai yi ba dan shi yanxu haushin suma ya ke ji dan gani yake xuwan su babu alkairi a ciki gashi sun jawo 'yar tasa tana son bijere masa.



**
Koda Haydar suka fito daga gidan motar su suka shige Adam ne mai tu'kin babu wanda yace uffan kai tsaye  herwagana suka wuce…





_By YAR AUTAR DASHEN ALLAH......✍🏻_https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share

_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link


_*WHATSAPP LINK*_

https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA

_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*

_*ZA6IN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_




For inf...08140801885




*Page 21 &22*


______________Suna insowa gidan sallama sukayi inna ta Amasa sallam tare da fitowa daga dankin mamakine ya bayana karara akan fuskarta Inna

murmushi karfin halin Adam yayi yace sai Kuma kikaga nasake dawo wa ko toh wannan karon rakiya nayin ba gunki naxoba

Taɓe bakin Inna tayi tace to ai nima ban nemekaba toyaxu Mai yakawoka gidana ai saika koma gun wadanda kazo domin su

Tabarma Inna tashifiɗa musu zama sukayi suka gaisheta ta amsa

Cikin kulawa Inna tace Adamu ? aini dana ganka har gabana yafaɗi na ɗauka wanni abune yafaru naga jiya jiya kakoma Kano Kuma ance yau kadawo!


'Kallonta Adam yayi yace "kwantar da hankalinki Inna babu abuda yafaru

Wannan dakike gani abokina ne, yanuna Haydar dake zaune Inna ma kallon Haydar ɗin tayi tace " ayyah sannuko daƙyar Haydar ya iya buɗe baki ya amsa mata

Inna mushaƙu dashi sosai harta Kai ga bama iya boyyewa juna komai duk wanda yasani to yasan Haydar.

Inna ƙaddara tafaɗawa abokina wanda shine sanadi xuwan mu Gombe a yau

Take Adam ya kwashe duk abun dayafaru tun farko haɗuwar Haydar da Ummeey
Adam bai ɓoyewa Inna komai ba.

Kawai sai ganin Inna sukayi tana sharar kwalla domin Inna tsohuwar nan ce wacce tausayin abu 'kalilane yake sata zubar da Hawaye

Cikin tausayawa Inna tace sannu yaro hakika labarinka cike yake da abun tausayi

Shiko wannan mahaifin yariyar nan wanne irin mutu ne da zai nemin almakashi ya yanke ingiyar ƙaunar da Allah yadasata a zuciyar bayinsa

Wlh Ina tausayawa masoyan da sukeyin nisa cikin kogin ƙauna a zo ace rana tsaka za'a rabasu hakan yakan iya jawowa sanadiyar tar watsar zuciyoyinsu

Amma kayi haƙuri Haydar kada kamatsawa kanka, karasa kar sashin zuciyarka, kana lallashin zuciyar ka kabata hakuri Allah xai sauya maka da wadda tafita

Ɗago idanusa yayi wanda suka rine sukayi jaaa ya ɗaurasu a kan Inna yace "Inna bazan taɓa samun madadin Ummeey ba
barai har nayin tunani samu wace tafita, take tausayinsa yaƙara kama inna

A haka Inna taita rarashinsa Tana bashi labare daban-daban wanda suka shafi rayuwa duniya a haka harya ya ɗan samu nutsuwa a zuciyarsa kiran sallar magriba akafara suka ɗauki buta sukayi alwala suka wuce masalaci Basu dawo ba saida akayin isha'i ɗankin Inna suka wuce Inna takowo musu abinci

Amma Haydar yaƙi ci yace ya ƙoshi domin yarda zuciyar sa take masa ƙuna baiga alamar zai iya haɗiyar ruwa bama bare kuma har ya iya cin abinci

Babu yarda Adam baiyi da Haydar ba akan yacin abinci koda kaɗanne amma yaƙi

Inna ce tasa baki tace "haba Haydar kada kayin fushi da inkon Allah
kazamo mai karɓar ƙaddara a duk yarda taxomaka, ka godewa Allah domin shine ya jarabceka domin ya gwada karfin imaninka , dan Allah naroƙeka ka daure kacinye wannan jarabawar

Itafa jarabawa soyayyace daga mahalinci take, duk wanda baya samun jarabawa a rayuwa toh ya binciki kansa
maganganun Inna sunyi tasiri a kan Haydar take yaji zuciyarsa tayi sanyi godiya yayiwa ubangiji daya bashi inkon cin wanan jarabawar.

Yace "Inna nagode da tinatarwarki a gareni nagode da nuna kullawa da tausayawa da kikayi a gareni


Daɗi Inna taji dan gani ɓacin rai nasa ya ragu a zuciyarsa tace bakomai Haydar ai shi ɗa nakowa ne


Haka Haydar yasa hanu sukaci abinci ammafa yana cin abinci ne kamar wanda yake cin magani domin daurewa kawai yakeyi

Bawani cin abinci yayi da yawa ba yacire hannusa shima de Adam ɗin haka take a gurinsa ganin halin da abokin nasa yake cikin bakaramin tayar masa da hankali yayi ba sai yakejin jikinsa tankar wani marar lafiya


Tashi sukayi sukayiwa Inna sai da safe suka wuce ɗakin Adam, ɗakin tsaf yake an gyare dama Inna gwanace wajen tsafta ta gyara ɗakin tsaf kwanciya sukayi kowane su abu namasa yawo a zuciyarsa musamma ma Haydar dashi kaɗai yasan abunda yakeji a ransa
barci ɓarawo ne yayi awun gaba da Adam

Amma shi Haydar ko rintsawa baiyiba bai ankaraba saijin kiran sallar asuba yayi tashi yayi ya xauna sanan yatashi Adam

Sukayi alwala suka wuce masallaci basu dawo ba saida gari yayi Haske
Adam ya kalin Haydar yaga idanusa sun kunbura sunyi Jan

Yace "Haydar yaxu bazaka cire wannan abun aranka ba.

"Haydar ayau Ina mai baka shawara daka haƙura da Ummeey.


_*By. YAR AUTAR DASHEN ALLAH......✍🏻*_🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA🎅🏻


      NA


UMMEEY MUHAMMAD LAWAN
  (UMMU AFNAN)
💃🏻YAR AUTAR 💃🏻DASHEN ALLAH



For more inf...08140801885



Page  23 & 24


________________ "Tunda  har  Mahaifinta   yake in kirarin cewa Koda zata mutu  baxai Aura mata kaiba"
kaduba irin Maganganun da yake fada Wanda  kwata kwata bai dace ace uba yafadawa Yar'sa wannan magan ganu ba.

"Haydar  Mahaifin Ummeey yayin  fushi sosai  Ummeey  na cikin matsalla babba  kaga baxamuyi nasara Akansa  ba

Haydar inde har kaunar da kakewa ummeey ta gaskiyace toh ka kar'fafa mata  gwuwa wajen ganin tabin ummurnin Abbanta

Ka rarashe ta wajan ganin takarbin zabin Abbanta'
Shide Haydar baice  komai ba idon kawai ya xuba Masa.

"Ama kallamansa sunna Masa yawo a kwakwalwarsa

Zuciyarsa na tafar fasa kamar xata faso kirjinsa tafito waje  idan akwai Abun da yafi tsana A duniya bai wuce ace yarabu da Ummeey ba

'To ama Kuma Yaya xaiyi kadadara tariga da tariga fatan mafita dayace shine ya yarda da shawaran  da Adam din kebashi.

Haydar ya dau shawaran Abokinasa batare da  son ransa ba     wucewa yayin ya nufin inda suka anjiye motar su

budewa yayi ya dauko takada da bairo yafara

Please Login or Register in order to submit comment