Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motsin mutum agefensa yasa shi d'agowa ahankali yana kallonsa Umar ne.

Wai brox meke damunkane?

Nayi kusan minti goma atsaye a kanka bakamasan nazoba duba jarida kakeyi amma hankalinka baya kai meyasa ne?
Wannan wanne irin aikine?
Idan zai takura maka kawai ka ha'kura dashi shine yafi haba kai kad'aene me aikin ko cewa akayi dole sai kai kad'ai zakayi??


Murmushi kawai Aliyu yayi sannan yace.
To sannu parrot kai ko gajiya bakayi.
Yaqarasa fad'a yana murmushinda baya barin fiskarsa


To idan kanaso na kyaleka fad'amun meke damunka???

Dan Jim yayi sannan yace

Kasanni jami'in sirrine Wanda banda iyayena daku babu Wanda yasan hakan,duk azaton mutane Ni dankasuwane tamkar mahaifina to yanzu abinda yasa kaga hankalina yatashi shine
Kusan watanni takwas kenan aka kawo aikin nan ofishina to saboda rashin lafiyarda kake yawanyi shiyasa Sam banmaida hankalina to last week shugabanmu ya kirani yace hukumomin 'kasashen waje sunce lallai sunbamu watanni biyu kacal mugama aiki inba hakaba zasu kar'bi aikin daga wajenmu to abinda yasa ma sukabamu saboda sunga a 'kasarmu ne ake aikata abin
Babban tashin hankalin shugaban 'kasarnan shine yasan muddin aikin yabar hannunmu zasu 'kara rainamana 'kasarmu wadda muke alfahari da ita ,

Yanzu halinda ake ciki shine sunce basuda kwararren jami'i kamarni idan nayi wata biyu ban'karasaba zasu koreni daga aiki tareda 'bata takarduna shine dalilin dayasa kaga hankalina yatashi.

To brox aikin menene haka da aka daukeshi da tsauri?

Ajiyar zuciya Aliyu yayi sannan yace........


*****************


Da sauri tami'ke tabi ta gefenshi ta wuce ba bukkarta ta nufa ba kai tsaye bukkar su Yemi ta nufa tana zuwa ta zube ajikin maman Yemi tafashe da kuka
Da 'kyar maman yemi tasamu tayi shiru sannan ta tambayeta abinda ke fad'uwa

Cikeda ba'kinciki tayi mata bayanin komai
Bisaga mamakinta kawai saitaga maman Yemi
Tana murmushi sakin baki tayi tana kallonta yayinda hawayenta suka tsaya chak!

Cikin son kwantar mata da hankali Maman Yemi tace.
Marcy ba babanki bane yamiki ciki kidaina zargin hakan"

Meyasa kikace haka bayan kuma naga shaida da idanuwana??

Mai makon tabata amsar tambayarta sai tayi murmushi tareda cewa.
"Tashi ki koma bukkarku kinji dare yayi"

A'a Ni anan zan kwana gaskiya.

Ta 'karasa fad'a tana share hawayenta

"Kin manta gobe bikin shekara kuma tunda safe za'azo akaimu cikin gari kuma kinmanta idan mukashiga garin bazaki sake ganin mahifiyarki ba har sai ranarda kika haihu??
Meyasa bazakije kimata sallamaba?

Kafinma ta rufe baki Marcy ta mi'ke da gudu tanufi bukkar mamanta
Tana zuwa ta fad'a jikinta ta rungumeta hawaye na kwaranya daga idanunta yayinda maman murmushi kawai takeyi tamkar me cikaken hankali.

Kuka take tana faman surutai

Meyasa wannan garin suke haka wannanfa ba rayuwace me kyau ba me yasa zasu rabani dake banda Abu mafi soyuwa a xuciyata kamarki mama,bazan iya barinkiba mama in a so kisamu lafiya inaso naji muryarki mama inaso ki rungumeni a 'kirjinki inji d'umin jikinki bawai Ni na rungumeki kina tureniba sai yaushe ne zanga haka sai yaushe.?
Ta'karasa fad'a tana fashewa da kuka
Da sauri kuma ta saketa takoma kan Babanta ta rike hannayensa

Baba kace tayimin magana kahana arabani da mahaifiyata kataimakamin kune jigona daku nasaba yanzu idan na mutu wajen haihukumafa shikenan ban mutu awajen mahaifiyataba shikenan ko gawata bazaku ganiba.

Zuwa yanzu gaba d'aya muryarta ya dashe fiskarta tayi jajuz dukda bata kasance farar fataba wankan tarwad'a ce

Hawayen fiskarta yashare sannan yace.

"Ki kwantarda kinji bazaki mutu ba kuma bazaki haihuba"

Da sauri ta matsa hannun shi
Baba mekake cewa ne haka kaifa kace inada ciki kuma Cikina yana girma kamarna masu ciki kuma yana motsi .

"Tabbas zaici gaba da girma kuma zaicigaba da motsi kuma zakici gaba da ciwo kamar yadda kikeyi har sai ranarda Yemi ta haihu"

Waji jirine taji yana kokarin kayarda iita dukda azaune take gaba d'aya kanta ya kulle batagane meyake nufiba Sam saboda batada nutsuwar ganewan.

"Ki saurareni da kyau kiji abinda zance miki bansaniba ko yau ne had'uwarmu dake na 'karshe amma zangaya miki komai har sanadin ciwon mahaifiyarki Wanda shima shiri ne na sarkin garinnan"

Dan Jim yayi sannan yace .

"Maganar cikin ki shirine kawai nawa ba bu wani ciki domin tun kina jaririya nayi miki shirinda ba Wanda ya isa ya miki ciki harsai na warwareshi Wanda sai yau na wareshi saboda nasamiki ciki Wanda azahiri akwai shi amma a ba'dini babu shi."

Zuba masa I do tayi domin ita haryau bata fahimci zancenba jikawai take
Abinda tagane kawai ciwon mamanta shiri ne na sarkin garin to meyasa zai mata haka kan wanne dalilin????



*_tooo kuxo kubawa Marcy amsar tambayoyinnan domin. Ni wannan sonjin kokop na Marcy ya iheni haka_*

Thanks you masoya muhadu a next page

_Leemarht Yar pillonku_πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


*_next page loading.............._*πŸ“πŸ“πŸ“
[4/18, 8:27 PM] Leemarh Phillo: πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ

*A WANI GARI*

πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ

*NA*

*_Leemart Yar pilloh_*🌲





*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________________*
Β©πŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻

_Aβ€’ Wβ€’ Aβ€’_

_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsapp
*_________________________________________*



*_page 10_11_*



Mi'kewa yayi yanufi 'kofar bukkar sai'da ya tabbatar babu kowa sannan ya dawo saida yafara bata ruwa tad'an sami nutsuwa sannan ya fara bata labarin komai


*TUNA BAYA*


Kamar yadda kikasani sunana Bunna na tashi bansan iyayena ba sai dai mutanen nan garin bantashi naga suna wani addiniba haka bansan tarihin iyayena ba haka nake kara zube wannan dalilinne yasa nake rayuwa acikin daji Wanda hakanne yasa nasan sirrin dajinnan sosai yazamto inabada magani ko wanne irine banda na mutuwa,
Lokacinda nakai shekara ashirinne nayiwa wata yarinya ciki itama kamarnine batada kowa a wannan garin shiyasa bawanda yatayata murna haka har sarki yagane akazo aka kaita gidan sarki daga nan bamu 'kara haduwaba saida ta haihu Sarki yadaura mana aure aka kawo min ita
Aranar nayi mana bukka muna rayuwa cikeda 'kaunar juna muna tattalin junanmu kasancewar mumsan bamu da kowa sai kanmu da yaronmu,

Yaronmu shekararsa biyar watarana wata mata ta haihu a gidan sarki saita mutu kasancewar yawanci a gidan sarki yake zama to agabanshi matar ta mutu hakanne yasa sarki ya d'auke yarinyar aka kaita dakinsa shi kuma yaronmawa yabisu a baya kafin akai jaririyar ramin yara ya d'aukota yakawomin nikuma hankalina yatashi saboda karyayi laifi shiyasa naje da kaina namaida jinjirar wajen sarki amma sarkin nan Mara imani Yakama yaronnan agabana yamasa yankan rago sannan aka dauki gawarsa aka had'ada na jaririya aka kai ramin yara"

Kukanda ya kufce masane yasa shi tsagaitawa itama Marcy kukan takeyi jin abinda akayiwa yayanta.

Sha'kar hanci yayi sannan yaci gaba da bata labari.

Acewar sarki tunda dai har yayi haka to nangaba zai iyasamai I do akan harkokinsa shiyasa yamasa haka saboda masu son yin abinda yayi su kiyayi aikata hakan,

Fad'ar irin halinda matata tashiga a lokacinma bata bakine ganin yadda tadamu ne yasa nace mata zanje innemo ramin yara aduk inda yake nasha alwashin taimakon duk wani jariri da akajefa ciki

Saidai tamkar yadda kikayine nasha matu'kar wuya amma bangane raminba daga baya ma naga ne babu wani ramin yara kawai yaudarace irinta sarkinmu

Dasauri Marcy ta dafe 'kirji tareda zaro many an idanuwanta abinda ya katseshi kenan tad'an tsagaita

Baba kace ba ramin yara to ina ake kai jariran idan and'auka?

Murmushin ya'ke yayi sannan yace

Ki saurara kiji da kyau"

Lokacinda matata tasamu ciki nabiyu saina daina barinta acikin gida na ke shiga da ita daji saboda cikin yazo mata da matsaloli sosai kuma maman Yemi 'kawartace itama tana nata laulayinne wata rana nafita Ni kad'ai a lokacin safiyane sosai Ashe bayan fitana anyi haihuwa wacce tarasun ta mutu saboda yara 'kanana ne dole sudinga mutuwa wajen haihuwa shine akarako sarki bakin jeji zai jefa yaron a ramin jarirai agabana yayi komai kuma lokacin ne naga ne ba wani ramin jarirai a garinnan kawai yaudararmu akeyi ganin naganshi yasan kuma zan iya tonamai asiri shiyasa ya jefeni da sandar tsafinshi take taxo ta bugi gabana nazama ba namiji ba yadda bazan 'kara amfanuwaba,

Sannan yace idanna tona zaikashe matata da cikin da take dauke dashi ganin zai iya aikatawa yasa nabarshi nasan akwai ranarda asirinshi zai tonu,

Tunda ga ranar nafara binciken yadda zan kasaarashi nakawo 'karshen wannan zaluncin da ake mana,

Saidai rashin lafiyar matata yakan d'an dakatar dani,

Wata rana munfita daji nida matata lokacin cikinta ya tsufa sosai cemin tayi dole saina kaita 'karshen dajin taga kwalta saboda ita bata ta'ba sanin akwai wasu masu rayuwa bayanmuba shiyasa nakaita,

Kafin mu 'karasa bakin titin ne ta tirje na'kuda ta kamata anan dole natsaya na jinginar da ita abayan dutse na tafi Neman wani ganye dayake maganin na'kuda,

Banyi nisa da inda takeba naji kukan jariri acikin duhuwar ganye nasan ba matata bace domin ina ganinta harna kauda kai zan wuce matata tayimin alamu da intaimakawa jaririn dukda tafita daga hayyacinta,

Da sauri najuya na nufi duhuwar INA bud'awa naga mace kwance da jariri Sabon haihuwa ko kaya bayida da alqma awajen aka haefeshi a lokacin ko motsi matar batayi tasuma,

Daga ita har jaririn na daukosu nadawo wajen matata lokacin ciwon tad'an lafa mata ita ta taimakamin muka gyara jaririyar Dan macece nayiwa matar dabaru ta farfad'o saidai da alamaBata gama dawowa hankalina bansan meya kawota wajen ba suturarmu ma ba iri d'ayace da tataba matata har tsoron ta takeji nafahimci hakan ta yadda take jabaya
Ahaka na Goya matar na dauki matata ahannu na nufi garin da ita jaririyar kuma nadaurata akan matata ba 'karamar wahala mukashaba dukanmu banzo bakin gariba saida dare Dan haka a daji muka yada zango ita kuma matar nabata maganinda zatayi kwana uku tana bacci nakaita cikin bukkarmu naxuba mata ganyaye yadda bazaka ta'ba cewa da mutum ba saidai babban tashin hankalin shine INA komawa bakin daji naga matata rai yayi halinsa ko haife d'an dake cikinta batayiba haka na rungume jinjirar matar nan a 'kirjina na tona rami na binne matata na koma bukka da safe gari ya kideme da muranar haihuwar Yemi Dan haka akazo Neman matata ganin batajeba

Kowa idanyaganni da jariri ina kuka zai yayi baya domin tunani nake tayadda zan ku'butar da jinjirarnan ta matar nan domin idan nace Y'atace aka haifa matata ta mutu za'ace za'akaita ramin yara .idan nayiwa sarki bayani zaisa akasheta har uwarta shine abinda ya 'kara d'aga min hankali sosai,



Ltake dabara ta fadomin nafara buge buge da ihun cewa sai anfitomin da matata domin ansacemin matata

Sanin cewa ana Satan matan mutane idan sun haihu yasa aka fara ihu ana cewa anemomin matata ,

Sarki yasa ashiga daji a duba ko zaaga wad'anda suka d'auketa ,

Nikuwa bandaina kukaba da buge buge kuma nahana kowa daukarki saboda karma suga farar fata domin bamuda farar fata a garinnan ko jaririne ba'kine idan suka ganki asirina zai iya tonuwa.

Dasauri Marcy tarufe bakinta

Kana nufin mahifiyata ba matarkabace?
Kuma bakaine mahaifinaba ??

Fashewa ta 'karayi da kuka tanabin jikinta da kallo ganin fatarta irinta yan garin ba'ka dukda bata kaisu ba'kin ba amma batayi kama da farar fataba

Da sauri tad'ago kanta tanabinshi da kallo idanunta na tsiyayarda hawaye.

To baka fadamin yadda mahaifiyata tasamu ciwontaba kodai tun lokacin haihuwarne?

Murmushi yayi kafin ya girgiza mata kai alamar a'a

To kafad'amin zuciyata zata fashe ka warwaremin komai.

Taqara fashewa da kika







Wash yaupa nayi typing daywa wallahi dole xan taqaeta labarin nan saboda gabatowar azumi bansan ko zangamaa ba kafin azumi

Nagode muku muach

*_Leemart Yar pillo_*πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

*_next page loading.............._*πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
[4/19, 3:35 PM] Leemarh Phillo: πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ

*A WANI GARI*

πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ

*NA*

*_Leemart Yar pilloh_*🌲





*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________________*
Β©πŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻

_Aβ€’ Wβ€’ Aβ€’_

_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsapp
*_________________________________________*






_page 12_13_




Cikin damuwa Aliyu ya d'aga kanshi yace.

Wato ansamu sanarwa sirri ne cewa anayin safarar jarirai ana shigowa dasu cikin 'kasarnan kuma ba iya jariran 'kasashen waje ake kawowaba no harda na nan kasar.

Cike da mamaki Umar yake kallonsa

"Jarirai kuma tome akeyi dasu?

Tsafi tsafancesu akeyi amaidasu kud'i zallar kud'i wasu karasa kishin kai sune masu bada goyon bayan hakan a 'kasarnan.
Yanzu maganar danake maka shine angano farkon dajin da 'kauyen yake saidai yafi a 'kirga ana tura jami'ai dajin domin shiga garin saidai hakan ya gagara duk fad'in dajin ana kewayawa amma basu ta'ba samun garin ba amma antabbarda lallai akwai garin da akeyin wannan abin
To garinne aka turani kuma Ni kad'ai saboda kwarewata dukda ansani Ni kad'ai ne saboda ana zargin akwai munafukai acikin jami'anmu,

To binciken danakeyi shine samun hanyar qauyen,
Abinda yasa kaga kodayaushe inatakurawa kaina da aikin shine naje farkon dajin nasaka camerar tsaro ta yadda zata haskamin duk wani Abu dazai gifta ta wajen amma abin mamaki shine ko tsuntsu banta'ba ganin ya giftaba,
Kuma muna samun rahoton cewa anacigaba da wannan abin yanzu ba jariraine kawai ba har yara ana kawowa.

Babban damuwa ta yadda zangama aikin nan cikin watanni biyu kuma bawai nasan garin bane a'a saina nemo garin sannan inshiga inyi abinda ya kaini,.
Amma nayanke shawarar zuwa da kaina gobe saboda naduba ko Allah zaitaimaka nasamu.


Cikeda da damuwa Umar yake kallon Aliyu sannan ahankali yace.

"Shikenan Allah yataimaka yasa kayi nasara Amma dukda cewa Ni ba jami'in sirri bane tare zamuje goben kashirya komai na mutum biyu kai Dan uwanane duk abinda zaisameka myasamemu tare karka manta Ni soja ne dukda banfara aikiba amma na horu ko ba kai bane zan iya bada rayuwata domin da'kile duk wani zalunci a 'kasarnan da izinin Allah saimun kawo 'karshen duk wani azzalumi dayake cikin 'kasarnan 'ina alfahari da 'kasata


Kafin Aliyu yace wani Abu ya juya yawuce cikin gida saboda yasan zai iya dakatar dashi shikuwa jiyake tamkar shi akabawa aikin an Dan haka yawuce yabar shi dafe dakai

Ajiyar zuciya Aliyu yayi cikeda kwarin gwuiwa yami'ke yanufi cikin gidan shima yana tunanin yadda za'ai Abban ya amince a tafida Umar wannan aikin me had'ari ganin yadda yafi 'kaunarshi fiyeda sauran yaran har Ayshat datake mace batayin ta'baran da Umar yakeyi.


Afalo yasamu su Abban nasu suna fira da sallama ya shiga yagaida Abban sannan ya zauna akan Capet kasancewar duk girmansu indai Abban ko UMMI suna kan kujera tosu a 'kasa zasu zauna.


Yaushe ne tafiyar taka??

Kamar daga sama yaji maganar Abba


Gobe ne.

Shiru Abban yayi sannan yad'ora mai da addu'o I

Cikin Dan in ina yace

Abba kaji rigimar Umar ko wai dole tare dashi zanjeharyatafi shiryawama


Visa mamaki saiyaji Abban yace.

"To kuje mana ai namiji ne sonda mukemasa bazaisa mu mai dashi sakaraiba yarona jarumine ai kyan namiji kenan ba ja baaya bazan hanashiba Allah yabaku nasara"

Kafin Aliyu yace wani Abu Umar ya rungume Abban yana dariyar farin ciki shima Aliyun dariya yake


Aliyu ne yace to Abba kayiwa ummi bayani da kanka kaji

To shikenan Ku tashi kufita kuhad'a abinda zaku buqata dukda bawai aikin bane baki D'aya

Mi'kewa sukayi suka wuce dakinsu cikeda farincikin zasu tafi tare


*****

Baba Dan Allah kafad'amin to menene ala'kar ciwan mahaifiyata da haihuwar Yemi kuma kace tsafine taya zanfiskanci komai kafitar dani

Murmushi yayi sannan yace .

"Har daresanna wad'anda aka aika suka dawo yayinda har lokacin nake kuka kuma sau d'aya nabaki madara aranar aka fara kiranki da sunan matata Marcy haka Yemi Ranar kwana na uku ne nasan aranar mahaifiyarki zata tashi nafita da zummar Neman matata kamar yadda nakeyi kullum na rungumeki munfita daji saida hankalin mutane yadan kau naje nadauko mahaifiyarki nakaita daji har lokacin bata tashiba saida duhu yafara shiga sannan na ciccibota nayi gidan sarki da ita nafad'amai a daji naganta take yace gobe za'a yankata a jefar saboda ba 'kabilarmuba CE cewa yayima namun dawace ta chanza halitta tazo dantakashemu

Ganin yadda na had'e rai yasa yasha jinin jikinsa na cewar zan iya tonamai asiri harna bud'e baki zanyi magana saiya ja hannuna yayi d'akinsa dani yace karna yadda na tonamai asiri inba hakaba zai sa akashemu duka
Nikuma nakafe muddin aka kasheta saina tonamai asiri shine yaji tsoro kad'an ya amince da hakan amma Ashe yaje gidansu Yemmi ya d'ebi jininta ya had'a wani tsafi dashi nafita daji ina dawowa natadda mahaifiyarki na wannan halin

Had'in da akayi da jinin Yemi yace harsaita haihu sannan zai karye kuma yayiwa Yemi asirinda bazata iya haihuwaba

Nine Dana fahimci hakan na karya asirin harta samu ciki ba 'karamin wuya nashaba saidai sai bayanda nakarya Nagano cewa akwai matsala saidai matsalarce bansaniba."


Shiru yayi yana sauraren sautin Ku kanta

Ahankali yacigaba da cewa

"Kidaina kukannan haka kisaurareni"

Katseshi tayi da cewa.

Baba bakafad'amin ina ake kai jaririba?

Yanxu kuwa

Idan andauki jaririn anraka sarki 'kofar gari shi kuma yana tafiya ba sosai ba saiya shiga wani hanya ta cikin duhuwa a kwai dogarinsa awajen saiyabashi jaririn shi kuma yadawo to hanyar dake cikin duhuwar kai tsaye gidan sarki yakoma a cikin gidan akwai daki Wanda nannane matattarar duk wani tsafinshi kuma akwai ba'kin fiska Dan ake gani sunashigowa masu irin fatarki"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace

Amman baba meyasa baka ta'ba shi gaba ka kawo 'karshensu ?

Murmushi yayi sannan yace.

"Inba sarki ba babu wani Dan 'kabilarnan da zaishiga yafito a Raye shiyasa mahaifiyarki datashigo yanemi kasheta kema badan abinda nashafa miki ajikinkiba da daga fatarki zai gane ki,kinga dalilin d'aya haukata mahaifiyarki kenan saboda kar wataran ta tonamai asiri,duk satar da akeyi a garinnan shine sila damuwar da tamin yawace tasani farashan wannan giyar danakesha "


Tagumi Marcy tayi tana jin wannan labarin tamkar almara a kunnenta

Ajiyar zuciya tayi sannan tace .

To Baba taya za'a kawo 'karshen wannan zaluncin da akeyi a garinnan yaushe wannan duhun zai gushe haske ya zo??


Cikin 'kasa da murya yace kece
Kece zaki kawo 'karshen komai dalilin wannan cikin najikinki kenan saboda dole zaku koma gidan sarki da zama kuma achan dakin yake sannan ke ba jinin garinnan bane xaki iya shiga saidai akwai kasada amma ki kwantarda hankalinki INA tareda ke a komai adarennan zan fad'a miki yadda zakiyi"

Girgiza kai Marcy takeyi hawaye na kwaranya a idonta....



*tirqashi*


*_Leemart Yar pilloh_*πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


*_next loading........_*


_comments and share please_

πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ

*A WANI GARI*

πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________________*
Β©πŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻

_Aβ€’ Wβ€’ Aβ€’_

_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsapp
*_________________________________________*
Β  Β  Β Β  *NA*

*Leemarht Yar Filloh* πŸŽ„

_masha Allah,Alhmdulillah hak'ik'a banida bakin gode muku ina matu'kar godiya bisaga addu'o'inku gareni naji dadi sosai nagode da kaunarda kukenunamin
Masu kirana da masu message dama wad'anda basu samun damar hakanba ina matu'kar yinku love you AllπŸ’πŸ’πŸ’_


*_Alhamdlillah Masoya a wani gari da naso nagama littafinnan kafin axumi amma kana naka Allah na nashi Insha Allah wannan shine na 'karshen page saikuma bayan sallah idan Allah yasa munada rabon gani_*


_nasadaukar muku da wanann page din All makaranta a wani gari ina godiya Allah yabar Kauna_*



*_Page 13_14_*



Cikin kwantarda hankali yace
"Yanzu kisaka wannan layar a 'kugunki karki yarda ta fad'i saboda idanda ita bazasu gankiba aciki amma idan babu ita zasu ganki ne su kasheki, idan kika shiga d'akin saikibi yamma zakiga wani kogo an an cIkin kogon gunkin tsafin yake karkiji tsoro 'konashi kawai zakiyi kinji amma kisa nutsuwa a ranki kicire tsoro tabbas idan kikayi hakan kin ku'butarda rayuwar yara harma da manya kuma kintseratarda rayuwar mahaifiyar"

Wani zazzafan hawayene ya fad'o mata Take taji zuciyarta ta harzu'ko mata tabbas zatayi
Take tace masa

Shikenan baba na amince.

Murmushi yasake sannan ya mi'ka mata layar
Kar'ba tayi ta d'aura san'nan tace

Amma Baba mamata fa bakaganin idannayi hakan zasu gane kuma suzo Su cutar dakuba.

Murmushi yayi san'nan yace ranarda mukaji Yemi ta haihu alokacin zata dawo hayyacinta zand'auketa mugudu chan bakin daji ko kwana nawane zamaujiraki anan har kifito inaji ajikina zakiyi nasara"

Amma Baba mutanen garinan fa ??
Murmushi yayi sannan yatare
Dukansu 'yan uwanmune bazamu ta'ba guje musuba zamu dawo cikinsu amma sai komai ya lafa,sonake mahaifiyarki tasami lafiya naji asalinku menene asalinku da tishenku na maidaku cikin danginku shine abinda zai kwantarmin da hankali"

Rungumesa tayi ta fashe da kuka
A'a Vaba bazan iya rayuwa bakaiba Kaine bangona abin jinginata Kaine mahaifina inasonka ina tare dakai.

'Dagota yayi tareda share mata hawaye da hannunsa san'nan yace

"Ranarda kika fito daga ciki zanhad'a miki maganinda zakiyi wanka fatarki ta dawo dai_dai kuma zaki saka wani kwalli idanuki yadawo fari Tass irinna mahaifiyar"

To Baba ta ina zanfita??

Ta cikin kogon zaki mi'ke zai kaiki har bayan gari"

Amma Baba idan banganku bafa ???

Zama ki ganmu Amma koda baki ganmuba kisawa ranki muna Raye kuma zankulada mahaifiyarki"


Fashewa tayi da kuka sannqn ta rungume Mamanta saboda tasan dagayau zaiyi wuya tasake ganinta.


To ki kwanta kafin azo tafiya daku kikula da kyau kinji ko!

Ko damar amsawa ma bata samuba saboda yadda zuciyarta ke dukan uku_uku

Anan jikin mahaifiyar tata bacci ya d'auketa cikeda mafarkin da tasaba kamar kullum


************



Cikin ikon Allah UMMI ma ta amince da tafiyarsu tare amma saida sukaje chan ofishin nasu yasaka hannu aka amince san'nan suka so suka fara shirin fita kasan cewar dare yayi


Washe gari suna fitowa daga masallaci suka fito domin tafiya harda su ayshart gaba d'aya daga kaga idanunsu zakaga tsantsar damuwa saikace tafiyar kenan alhalin dubawa kawai zasuje suyi ayau su dawo kafin su tafi asalin garin


Addu'o'i sosai sukayimusu abakin dajin tareda fatan alkhaery harda jami'an tsaro aciki

Said a suka shige cikin bishiyoyi suka daina ganin su sannan suka juya suka shiga moto cinsu suka tafi


Tafiya suke sunad'an fira kutsawa suke sosai amma babu alamun zasuga gari ko kauye kai ko gidan tsuntsu basu ganiba nan suka yi sallah sukaci abinci san'nan Aliyu ya kalli dan'uwan nasa


Umar kaganin kuwa ba chanza hanya zamuyiba inaji ajikina garinnan ba'a setin nan yakeba saboda kaga masu binciken suna kwanaki suna tafiya amma basu ta'ba ganiba inaganin mu chanza hanya ko Allah zaisa mudace .


'Dan shiru Umar yayi san'nan yace
"Abinda za'ayi kawai shine kabi kudu nabi arewa tunda ga waya saimuna tuntub'ar junanmu muji halinda kowa yake ciki"

Wani irin kallo Aliyu yabishi dashi na bakada hankali san'nan yace

Babu inda zakaje 'kafata 'kafarka duk inda zamu shiga mushiga tare kamanta gargad'inda Babanka yamin Akankane?to wallahi ba bu inda zakaje muje ko ina tare

Murmushi yayi kafin yace tom shikenan naji yanzu ina zamuyi?

Murmushi Aliyu yayi san'nan yace
Kudu zamuyi mubi nan muganiko zamu dace.

Mi'kewa sukayi suka nufi kudu tafiya suke amma har sukayi sallar la'asar basuga komai ba bare wani gari harsun yanke shawarar juyawa domin su koma gida kamar daga sama sukafarajin motsi kamar ana tunkaro wajen kuma kamar tafiyar montane

Mamaki ne yakamasu suna tunanin taya mota zata shigo wannan hanyar batareda tayoyinta sun huhhujeba domin hanyar cike take da 'kayoyi masu kauri dogaye

Da sauri Aliyu yaja hannun Umar suka shiga cikin duhuwa kasancewar ga duhun rana datazo fad'uwa shiyasa baza'a lura dasuba suna nan tsaye har motar tazo ta wucesu ko 'kirar motar ma basu ganiba

Bayan wucewar motarne Umar yayi murmushi san'nan yace
Tabbas munakan hanya domin duk yadda akayi wannan motar daga chan take yanzu gashi rana tafad'i bazamu iya gane hanyar data biyoba kasancewar ga duhu kuma ba halin kunna fitila mu haska karsu ganmu

Yanzu kawai mu juya mutafi gida shine zaifi "


Kallonsa Aliyu kafin yasaki murmushi yace.

Kai ka koma amma ni zancigaba da kutsawa nafasa duba hanyar zanje innemo garin kuma zanyi abinda yakaini domin tabbas idan mukabarnan hanyar zata 'bacemana idan kuma muka dace zamusaka sheda to za'a gane wasu sunbiyo wajen.


A'a bazai yuwuba duk inda zakaje muje tare muje naga hanyar akwai wadatar koramai ga kayan marmari zasu ishemu rayuwa amma bazan bari nima katafi kai kad'aiba"


Murmushi Aliyu yayi san'nan ya karb'i wayar hannun Umar yahad'a da tashi ya Ya zubasu a wajen yaja hannun Umar suka matsa chan inda babu duhuwa sosai suka kwanta bayan sun tabbatarda babu wani abin cutarwa a ciki


Wash kuyi haquri plx

*_masoya a yi Ramadan lapiya Allah yasadamu da Alkhairan dake ciki Allah yayi mana maganin wannan annobar ameen ya Rabbi_*


*Leemart Yar filloh_*πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


[5/24, 8:46 PM] Phillo: πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ

A WANI GARI

πŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺπŸŽͺ


*NA*

*_Leemart Yar pilloh_* πŸŽ„



*_Bismillahirrahmaneerraheem_*


_inayiwa yan'uwa da abokan arxiqin murnar barka da sallah patan anyi sallah lapiya allah ya maemaeata mana ameen Allah yajiqan wadanda muka rasa marasa lapiyanmu Allah yabasu mukuma Allah yakaremu ameen allah yatsayar mana da wannan annoba haka ameen_

*_LOVE YOU ALL_*





*_Page 15-16_*



Suna kwanciya saboda wahalar dasukasha na tafiya yasa wani nannauyan bacci yad'aukesu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment