Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiya ban samu bacci ba fa. Kiran waya, babu Hutu. Lallashin Duniya nayi domin ta fahimci bawai na barta Kenan ba, Ina sonta, kuma Ina da burin auren ta, amma da sauran lokaci. Kuma auren da nayi duk Sabida ita ne, domin idan ban tauna tsakuwa a ya taji tsoro ba, al'amari Bazai gyaru ba. Amma Salima fafur ta kasa fahimtata. Da gaji na kashe waya. Shine fa kika ga tazo da safen nan, Wai mamanta tazo ta tafi dani, saboda ta gigita nutsuwar su."

Duk da fargaba ta rufeni da jin a binda ya faru, da nima zance ya shafeni dole. Cikin taushin murya nace
"Ancle, Kayi Hak'Uri Mana kai ma. Tayi nadama fa maman nata. Kuma naga burinka Kenan. Kayi Hak'Uri."

Ai gani nayi, ya Mik'e zaune sosai ya dubeni.

"What? Nayi me? Wai nayu Hak'Uri yanzu? Lallai Yarinya baki sanni ba, labarina kike ji."

A raina nace"Ban dai gama sanin ka ba.

"Wa'adin da na yankar mata Wallahi Sai ya cika. Ina son Salima. Ina son 'yarta fiye da zaton su. Amma Wallahi ban shirya auren'ta yanzu ba, ko da kuwa za'a tattaromin kud'in masu arzik'in k'asan nan a bani a matsayin gudun mawar aurenta. Wallahi bazan aure ta ba Sai wa'adin da na d'ibar musu ya cika.

Nan nasan lallai Ancle Fa'iz ya wuce sanina da karatuna. Zuciyar da Kawu Sulaiman yace yana da ita, ta wuce zatona. Amma a hakan kullum zuciyta k'ara zarmewa take a son sa, duk da zahirin halayan'sa masu wuyar Sha'ani da juriya, suna dad'a tallata kan"su da kan"su. Wannan bai hana Soyayyarsa k'araci gaba da hab'aka a raina ba. Wuyarta Mu kwana Mu tashi, nayi ido hud'u da shi, naji muryarsa kuma.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*




📱15
______ Zan iya cewa, tun da daga ranar nan, gaba d'aya naga gidan sun sauyamin fuska, idan a ka cire Khairat, da Ancle Fa'iz. Amma Khairat ta d'an ja baya dani kad'an a kan da. Ta yiyu kashedi a Kayi mata, saboda ko magana zata yi min zan ga bata da nutsuwa. A kan matsalar Ancle fa da Salima na zurma wannan rigima. Saboda Momi tayi iya yinta Ancle yak'i saukowa a yi sulhu shida maman Salima. Domin burinta Kawai yazo ta bashi hak'uri ya auri Salima. Shi kuma yace ba yanzu ba, bashi da ra'ayi Sai lokacin da yayi ra'ayi. Momi da kan'ta tasan halin d'an ta, idan ya kafe a hak'ura, idan ba haka ba, to lamari b'aci zai yi. K'arshe ma a yi uwar watsi, yace auren ma baza'ayi ba ya hak'ura da ita. Da wannan dalili Momi ta danne zuciya tasa masa na mujiya. Wato ido. Amma a dame take game da lamarin, saboda wurinta a ke kamun k'afa, ita kuma ta kasa yin yadda suke so ga Ancle. Shi yasa Sai a Kayi haushin kaza huce kan dami, ni fushin a ka juyeshi a kaina, saboda su so suka yi ya sakeni ya auri Salima a lokacin, tun da sun zo neman sulhu. Shi kuma Ancle sunga bashi da niyyar, hakan. Sun fahimci baya nunamin Wata kulawa,ko ta aure. Domin kowa ya Sani, baya zaman minti biyar a d'akina, ballanta na Wai ya kwana ciki. Amma kuma babu wani fitintunu na rikici tsakani na da shi, duk da borar da na zama. Ina girmamashi, da yi masa biyayya dai dai gwargwado. K'alau muke zaune ba'ajin ko tari na na Wai muna ko da da musu. Wannan shi ya zamo k'arin umda da ya had'u da na bijurewar sa ga auran sa da a ke so yanzu da Salima, a kace Ina wuta a jefani. Alhakin komai kamar gani suke a wuya na yake, nice sila.

A tunani na inda a dalci basa yi min haka ba. Matsalar Auren Salima da Ancle tun kafin a San Ancle zai aure nine. Ya kuma fad'i hujjar bijirewar sa ga Momi. To don me zan zama a bar juyewa haushi? nima a barni naji da kashe wutar gabana Mana, da suma sun San da ruruwar ta. Zaman aure na da Ancle Fa'iz ko a suna ma bashi da takwara, ko mahad'i.

Ban ware girki na ba, har lokacin tare muke yi da Khairat na gidan duka. Wani zubun ni keyi, amma Ancle bayaci momi ke yi masa nasa shi kad'ai kullum.
Momi ta kirani har saman ta, naje na gurfana cikin sababben ladabi da nake mata, ko uwata albarka, domin jiki na har rawa yake, saboda tsabar biyayyar da nakewa Momi idan ta Sani a bu. Idan nasan tana son a bu ma, bana jira, Sai ta Sani, yi nake.

Cikin d'aure fuska Momi ta dubeni."Sumayya daga yau, bana son ki sake saka hannunki cikin girkin gidan nan, ki rink'ayin naki.Dama Fa'iz Nike yi masa, Kinga iya cikinki zaki dafa. Na fad'awa Fa'iz ma zaki soma girkin ki."

Nace"To, Momi"

Naci gaba da tsuguno, koda sauran umarni, da naga tayi banza dani, na Mik'e na janyo sanyayyun k'afafuna nayi waje.

Ancle bai min zancen girki ba, momin ce ta sake kirana tace"Nayi magana da Fa'iz yace kome kike so, na amfanin girki wurina zaki amsa, tun da ni yake bawa komai idan ya sayo."
Nace
"Momi, ai ba sai na karb'a ba, tun da Ina da Kayan garata da komai na girki."
Ta zabgomin wani kallo na baki isa ba.

"Na Sani d'iyar tajiri, 'yar na gada. To, hak'k'in Mune ciyar dake. Babu ruwan Mu, da Wanda aka kawo daga gidan tsoho. Namu za'kiyi amfani dashi."
Ni Kam Mamaki ya kamani ma, Na menene a bin zafin a ciki. Ai duk domin a amfana dashi aka kawo garar.
Na sanyaya murya nace.

"Allah ya huci zuciya, Momi, ayi a fuwa, tuba nake. Zan rink'a karb'a.Duk da haka komai na Aikin gidan Nike yi. Wanke wanke Shara, wanke band'akuna da Kayan k"amshi. Amma fa banyi fari ba, bata hanani ba dai. Khairat girki ne nata. Muhibbat Sai taga dama take sa mata hannu, kuma Momi bata yi musu gyara ba.

Daga nan damuwa ta soma Samun gurbi a Zuciyata. Gani da yalwar kud'i, ga Kayan a binci a store, da a ka kawomin komai a Kwai, amma Wai kullum Sai naje wurin Momi karb'ar komai, kuma idan naje, Sai an min wulak'anci kafin a bani, musamman idan Khalifa da Muhibbat, suna wurin. Habaici, da zambo da tsaki, nafi shansu ma.
Gaba d'aya Momi ta canza min. K'iyayya muraran ta fito min da ita. Ko kirana tayi, ban ji ba,ko na kuskure wani a bu, to zagine. Banza ,shashasha, sauna, d'iyar matsiyata, wannan sunaye nane,da Momi ta rad'amin daga baya. Sam bata Kiran Sunana ma. Kullum a mai laifi nake,da nayi da banyi ba, Sai an k'irk'irar min.
Khalifa da Muhibbat sun fi takuramin. Bani da 'yancin fitowa tsakar gida Sai Habaici, harara da tsaki. Amma Khalifa idan shi kad'ai ne, kulani ne Kawai bayayi, Sai dai idan Muhibbat tana kusa, ya samu 'yar uwa Sai suyi min taron gayya. Khairat idan tana kusa, a fuska Zanga ta nuna damuwa sosai a kan a binda suke min. To sai dai bata yarda zata yi da su, sun girmeta. A Kwai Sanda tayi magana a kan bai dace ba a binda suke, suka hayayyak'o mata. Khalifa ma saura k'iris ya kai mata duka Muhibbat ta Kare. Yace mata a gabana. "Wallahi, kika sake yi Mana shishshigi jikinki Sai ya fad'a Miki. Kuma Sai na fad'awa Momi, zagon k'asa kike mana."
Tun daga lokacin, Sai take jan jiki, da taga sun soma yi min iya shege.
Sunan da suke kirana da shi, Wai 'Yar jiran k'ofa. A bin nufi, ni Salima nake yiwa gadon wuri, kafin tazo. Wato bani da wani amfani face kula da muhalli suke nufi. Jin sunan ya zamemin jiki, domin suma shi suka rad'amin ko kirana za'suyi, bayan na Momi da nake ji da shi kuma.

Duk da naga gabar suke dani ta sosai, ni har gaishesu nake, idan basu kulani ba, amma babu sauk'i Wai ciwon Arne. Ko sallama nayi musu basa amsawa ma.
Rannan Khalifa ya biyo Muhibbat a guje suna wasan banza, ni kuma zan wuce rik'e da plaks da kofunan tea biyu na glass, na fito daga kichean zanje na wanke su, Muhibbat da gayya ta bangajeni da k'arfi na kife, plaks ya fashe da kofuna, ni kuma bakina ya d'an fashe na k'ume da garu, kafin na kife amma Muhibbat ko ta d'aga kai ta dubeni ballantana tace sannu. A gaban Momi, aka yi, domin ta lek'o ta Sama tana yiwa Khalifa magana, Amma bata yi magana ba, kuma ko sannu. Hak'urin dai da nayi ban tanka ba, saboda naga kullum k'ara d'aukar zafi a ke dani. Ta yiyu, so a ke na tanka a yi b'atacciya. Domin ko washe gari da naje gaishe da Momi, bayan ta amsa da k'Yar, na Mik'e Sai Muhibbat da take kusa da ita taja tsaki tace"Aikin banza, isar ba'a isa ba. Mace Sai nacin jarraba, ba'a sonki, amma kin manne."

Ban d'aga kai na dubeta ba, na fito. Momi naji.

Sati na uku Kenan za'a Shiga da aure na da Ancle Fa'iz. Ji nayi komai yayi min zafi. Baki d'aya naji gwara nayi komawa ta makaranta, duk da hutun da na karb'a saura kwana biyar ya cika. Babu wani a bu da yake d'ebemin kewa a gidan. Ga kuma damuwar wulak'ancin da a ke min. Ni kuma bazan iya fad'awa kowa ba nawa, ballantana Ancle Fa'iz da dangin sa ne kemin. Nasan bai Sani ba, tun da komai Sai bayanan a ke min, duk da ba wani Sona yake ba, ballantana nace suna shakkar ya Sani ya d'au mataki, Sai dai Kawai sun San shi mai zafi ne da baya d'aukar Wargi ko wani iri, ko yaga anyi wani a bu da bai da ce ba, batare da ya taka zazzafan burki ba.
Sam hutun ma da na d'auka na aure ma nayi da na Sani, domin bai min rana ba, Sam. Sannan babbar damuwa ta Kawu Sulaiman yak'i zuwa ballantana naji sanyi. Domin ganin sa da hirar sa mai kwantar min da hankali, kan mantar dani damuwa ta, da maraici na.

Ancle Fa'iz ya kasa bani lokaci, ko Yaya da zan jarraba salo ma na soma Jan hankalin sa gareni, ko da daga hira ma gajeriya a bin ya faskara. Kullum cikin uzuri yake, idan na nemi hakan. Banyi zaton Zai yi tsaurin samuwa haka ba gareni.
Amma kuma duk Sanda Zai fita, ya kan ce me nake so ya sayo min, nace babu komai.Abinda nake son ya gaza.Komai ya sayo d'aurina dabam. Kuma komai ya sayowa su Khairat Sai ya sayo min. Wannan ya tabbatar min rukuni guda ya a jiye mu.
Randa na hak'k'ak'e zan fad'a masa komawata makaranta, ranar ya shigo da robar madarar roba biyu a hannunsa, ya Mik'omin d'aya. Daga tsaye bai zauna ba, Sai yace"Bari naje na nemi Ado coach d'in Mu, naji ance yanzu yazo bana nan, ba domin shiba kwanciya zan yi na gaji.
Ban yi mamakin gajiyar da yake yawan cewa yayi ba, saboda nasan Boll ya buga, ko training. Amma uzurin sa na kullum da baya yankewa, shi yafi ban Mamaki.
Har ya juya, Sai ya dawo yace min

"Ki rink'a rufe k'ofarki da daddare Sumayya. Naga har na kwanta a bud'e take, me yasa?"
Nayi masa wani salon kallo nace"Bacci ne, yake kwasheni ban Sani ba."

Yace"Yace "Saboda me?"
Nace"Saboda bani da a bokin hira"
Ya gyad'a kai."Kin raina a bokan hirar takine. Gaki da book's na gani, ga Kayan kallo ai sun isheki."
Nasan jahiltar manufata yayi, yana sane. Nace cikin narai narai da ido.
"Wad'an nan ba'a bokan hira bane face d'ebe kewa. My Ancle kaifa kace na rink'a kallonka kamar Ancle Sulaiman, amma Sam baka bani lokaci irin nasa. Baka hira dani irin sa. Anya za'ka maye gurbinsa? Kullum Sai kace kana da uzuri. Na Shiga d'an Kukan shagwab'a kamar na gaske. Ni Wallahi bazan iya wannan rayuwar ba. Kullum ni kad'aI kamar mayya.Karabani da Ancle d'in dake min hira yana Sani dariya da wasan nishad'i, kai kuma kak'i hira dani. Ni gida zan tafi yau ma.
Yarda nayi zaton zai d'an lallasheni ko Yaya, ai Sai ya bud'emin wuta.

"Maza maza tashi, ki tafi, karki bari k'uda ma ya rigaki. Ni zaki fad'awa Wai damuwar sulaiman gareki? to duk Soyayyar da yake Miki ai bazai iya aurenki ba, Kenan no reason da zaki rink'ayin wani prouding a kan'sa har da Wata tutiya. Kuma tun da haka ne me yasa baki zauna can ba, yayi ta sangartaki yana shagwab'aki da soyayya, karki auri kowa, tun da, Soyayyarsa da kulawarsa ita kad'ai ke gamsar dake."
Na yarda Ancle Fa'iz ya iya yanka maganganun ramuwa na cusa haushi, idan kan kara a Kayi masa, shi kuma na itace yake.
Raina kam ya b'aci da jin furutan'sa. Kenan babu inda zanji San yi a gidan. Da sauri na Mik'e na Shiga d'aki na janyo gyale na da takalmi da jaka. Na fito. bada niyyar fita na fito ba, jarrabawa zan yi naga Zai barnin na tafi. Yana nan zaune in da na barshi. Ya bini da kallo, Yayin da na yafa gyalen, nasa takalmi, nayi kamar banganshi ba, nazo zan fita. Wata tsawa ya dakamin har Sai da jikina ya d'au rawa. Bana ko kokwanto su Momi sunji.
Ya nunani da yatsa.

"Wallahi, kika tsallake tudun k'ofar nan kika Fice Sai kin raina kanki." Nayi tsuru tsuru dani, kamar Wacce ta yiwa sarki k'arya. Sai kuma na dawo turus na zube kan kujera na Shiga rera kuka na rufe fuskata da gyale Ina ta sheshsheka, a zahiri rantsewa za'ayi na gaskiya ne, Amma a bad'ini na k'arya ne.
Ina k'yallaro shi, Sai jijjiga kai yake, Yana Jan kwafa da Ina Kukan, tabbas naga 'Yar damuwa a tare da shi, naji yace"Haka siddan Ina Zaman zamana na jawa kaina d'aukakkiya.
Jin furucinsa, Sai na k'ara sautin Kukan. Ya dubeni yaja tsaki, tsam Sai naga ya Mik'e yace

"Kyayi ke kad'ai ."

Yasa kai ya Fice. Yana fita na tashi na Shiga d'Aki nasa Kayan bacci. Kyakykyawar Riga ce silk Mai k'aramin hannu doguwa, nasa da hular bacci mai kyau. Na kishingid'a bada niyyar bacci ba tukun. Damuwar da naga Ancle ya d'an Shiga sanadin Kukan da nake da yake zaton gaskene ta farantamin. Da wannan na soma fahimtar wani sirri nasa da zan iya cin nasara a kan sa wani lokacin. Sam bayason a na yi masa kuka musamman na wata damuwa haka na fuskanta.
Ban sa rai da Zai sake waiwayata ba a daren, Sai jin sallamarsa nayi a falo yana Kiran Sunana.
"Sumayya! Sumayya!!.
Naki amsawa Ku ma nak'i fitowa, domin so nake ya shigo d'akin. Kuka ma naci gaba dayi kamar dama can aikin Kukan nake.
Babu shiri ya fad'o d'akin. Da alamu shirin baccin yayi Shima. Riga ce ta bacci yasa da dogon wando pure cotton mai taushi, irin Kayan. Sunyi masa kyau ainun. gaskiya Ancle yayi a rayuwa iyaka.kamar yarda Nuriyya ke yawan fad'a. Sai da ya tsaya a kaina na sakanni Yana kallona Kawai, Sannan ya tsuguna a gabana, murya k'asa k'asa yace
"Wai Sumayya menene damuwarki? Haka Kawai kina neman ki d'agamin hankali. Me kike so ne?

Cikin shagwab'abb'iyar murya nace"Bakaine kace bazan tafi gida ba."
Ya kuwa sake k'uluwa yace
"Bazakije gidan ba na hana,kuma ko Kukan jini za'kiyi. Ke ko kunyama ba kyaji k'atuwar budurwa kamarki ki rink'a acting irin na yara, k'anana, har kina kuka saboda sangarta ko? Ko da yake goyon kakace dole kiyi. Ga Sulaiman kuma ya sangartaki. To Any way ni bazan d'auki sakarci ba Wallahi, tun wuri ki Shiga taitayinki."
Nayi dib! Ko uhum ban sake cewa ba, face mitsitstsike idanu.

Shiru ya ratsa wurin na mintoci, Sai Iskar Sama dake motsi Tana wulwulawa tana bada iska madaidaiciya mai dad'I, sakamakon d'an yanayin zafi da ya shigo a tsukin.
Ko tausayina yaji, Sai kuma ya tausasa murya Maimakon kausasawa da fari.
"Sumayya, ni Banga a binda Zai sa ki rink'a damun kanki ba. Da a ce tun farko na munafunceki, to shine za'ki damu kanki, idan kika ga wani sauyi. Amma haka siddan ki rink'ayimin tuhumar da gangan? Me na yi Miki? Kullum fa Sai na tambayi me kike so, menene damuwarki, amma duk ban fita ba. Kinsan manufar auren Mu, kin a mince, to me yasa zaki rink'ayi min bore bayan anyi.?
Naga shiru ba mafita bace, gwara na fad'amasa burina ko zanyi sa'a ya a mince, daga nan k'ofar farko ta bud'e.
"Ancle nifa buk'atata ka rink'a yagar min lokaci, muna hira ko Yaya, na samu mai debemin kewa. Su khairat da kake cewa muyi hira basu da lokaci kullum suna kan hanyar makaranta, Boko da islamiyya. Dare kuma Kowacce d'akinta take Shiga, saurin bacci ne dasu. Momi kuma kunyarta nake ji, bana iya sakin jiki muyi hira sosai."
Nayi dace yace"To, zan jarraba yarda kike so, Amma fa ni ba ko Yaushe nake son hira ba, karki zamemin BBC, uwar watso kanun labarai. Dariya furucinsa ya bani, har nayi ta fito fili, saboda yanayin da ya furta. Shima Sai naga yayi 'yar dariyar.
"Ke dai 'Yar tawaye ce rigimammiya, mai fuska biyu kuma. Kin rikita mutane da kuka, kuma kin dawo kina yimin dariya ko? Warki ne ni dai dai k'ugun kowa." Yanayin da muke ciki, da yanayin lokacin, ya sanyayamin zuciya sosai. Naso mukasance daren Ranar da faranta ran juna irin na ma'aurata, koda iya hira, amma Ina!.Mikewa Ancle yayi. Nikuma na tuno da a binda nake son ce masa.
Nace"Am, Ancle"
Ya juyo"Ina jinki Sumayya." Nace"Gobe nakeson komawa makaranta. Yace"Sai yanzu za'ki fad'amin?"
Nace"To, na bari, Sai Jibi?"
Yace"No, Kije goben, tunda kin niyyaci hakan.
Daga nan yayi min Sai da safe ya fita. Inajinsa ya b'amemin k'ofar sosai.
Na kuwa kasa bacci. Da nayi juyi, Sai na hango Ancle Sanda ya tsuguna gabana, ya zubamin kyawawan Idanuwan nan nasa masu hasken blue masu kashe gab'b'ai, yanamin surutai a hankali. Gaba d'aya kasa Dai daita nutsuwata nayi a lokacin. Komai nasa mai ruruta wutar k'auna ce, ga ma'abocin kallonsa. Nasan shi a lokacin babu komai a ransa, burinsa ya shawo kaina Kawai.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*___________________________________*

📱17
_______ Ranar Wata alhamis, Ancle Fa'iz ya shigo da daddare ya sameni ni kad'ai a falo zaune nayi shiru. Mutan gidan duk suna saman Momi ana ta shan hira, da kallon TV. Ya shigo ya zauna, bayan nayi masa sannu da zuwa yace" Sumayya Wai zaman kad'aici menene ribar sa? Sai kiyi ta jan jikinki da mutane, kina ware kan'ki why?" Na d'aga idanu na dubeshi bansan me zance ba. Shi duk zaton sa nike jan jiki da mutan gidan, saboda baisan komai da yake faruwa ba. Na yarda a je a hakan, gwara ya zargenin da na zama nice ta farko da zan soma kai masa k'orafi a kan Maman sa da 'yan uwan sa.
Musamman Momin sa da yake ji da ita matuk'a.

Na daure nace"Kasan fa ni kunyar Momi nake ji."

Yace da sauri "Kinga do Allah ki daina irin wannan gidadancin. Kunyar lafiya? Shike nan Sai kice lalllai Sai dani za'kiyi sabo, ni da ba mazaunin gida ba? Ki gyara wannan hali naki please."
Nace "To". Laifin da ba nawa ba na amsa. Naci sa'a ranar ya zauna wurina, ya d'an d'ebemin kewa, nafi zaton tausayi na bashi, na kad'aicin da nake ciki babu kowa.

A hankali, a hankali kusanci da jituwa ya soma Shiga tsakanina da Ancle Fa'iz. Mukan jima muna 'yar hira, musamman da daddare, Saboda lokacin yafi zama a gida. Ya kan jima a falona, amma kallo yafi yawa a kan hira.

Ancle Fa'iz baya son kowani film Sama da kallon boll , Sai film d'in china. Dole na koyawa Zuciyata son,su duk da bana k'aunar ganin su, basu dameni ba. Amma har kud'i nake sawa na sai C D, saboda shi. Duk da Shima d'in yana sayowa. Duk wani a bu da na san ya naso, tanadar'sa nake yi na tarbeshi da shi, saboda sa'ar da na samu yana shigowa falona ya zauna.

A bin dai da bayaso nake yi, shine narka da shagwab'a. Narka da shagwab'a nake yi masa muraran cikin Mu'a mala ta da shi, musamman idan Ina son yayi a bu yak'i. To shi kuma wannan ce ba ya so, domin bayan k'orafi har hantarata yake yace

"Ke tafi can ki bani wuri, bani son tab'ara. Wani lokaci ya cuno baki yace. Duk Sulaiman ne, ya sangartaki ya shagwab'aki saboda mugunta, domin yasan gidan wani za kije bashi zaki k'warzaba ba.
Wani zubin kuma ya kance "Bari dai na baki wuri ba dani ba wannan tab'arar, Wanda ya sangarta ki, shi zai iya d'auka. To nan na kaishi gargara Kenan, domin ficewa yake ya barni. Duk da bayaso, ni kuma ban daina ba, domin ni kuma ta haka nake so na Shiga jikinsa da zuciyarsa Mu shak'u. To daga baya ma Sam daina k'orafin yayi da ya gaji. Sai dai yayi min shiru, yayi ta danne dannen wayar sa, ko ya shareni ya d'ora idon sa a kan TV, ko ya lumshe ido kamar mai son yin bacci. Idan na kai shi bango kuma ya mik'e kawai ya Fice, Sai yak'i shigomin kuma Sai yayi min ban iska na wani lokaci, ranar da na kai shi gargara Kenan.

Ban ja baya da komai ba, saboda damar da na samu daga gareshi, nayi ta shigo masa da abubuwa iri iri,duk da ina shan kyara, wani zubin, banayin zuciya, domin kuwa ni mai nemace kuma wataran bazai yi ba.

Wata sa'ra dana d'auka, idan zai yiwa kan'sa a bu, Sai nace Sai yayi min, ko munyi tare. Yana da wani a bin yanke farce mai kyau, duk ranar juma'a yake yanke farce da shi. Na kance ya kawo nayi masa Sai yak'i. Ni kuma Sai na takuramasa nace Sai yayi min ban iya ba da kaina. Farkon randa na soma damun sa da magiya, ya jefomin kallon tara saura kwata yace.

"Wai da can wa yake Miki? Ko domin Samun wuri? Nace"Baba Talatu ce. Yanzu kuma bani da kowa Sai kai Ancle, ka taimaka." A ranar fafur yak'i yi min. Amma daga baya ya soma yi min, saboda bak'in naci. Ni bana zuciya, Sannan ga binbinin magiya da kwantar da kai, ta haka naci nasara kan Ancle da murd'ad'd'en halin'sa.

*******

Babbar nasarar da na samu, tasa na k'ara k'aimi. wani lokaci ni da shi a falona, na tsiri tsifa saboda ganin arhar damar ga Ancle Fa'iz. Da. na soma nace "Ancle don Allah tayani tsifar kai."

Ko kallona bai yi ba, a fusace yace"Sumayya kina nema fa ki raina ni da yawa. Nine ma zan yi Miki tsifa?." hakuri na bashi a nan, saboda naga ya d'auka da zafi.

Ban daddaraba wani lokaci muna tare muna kallo na sake tsirar tsifa. Ina cikin yi nace. "Wash!. Ya waiwaye ni."Me ya faru?" Nace"Wani ciwo ne a yatsana da naji, garin tsifa gashi ya yanki wurin"
Yace"Garin Yaya kika ji ciwo?"

Nace "Jiya ne Ina yanka nama".

Yace" Sannu, ya kamata ki rink'a kula."

Na faki idon'sa nayi murmushi. Nace "Ancle don Allah ka tayani, kaga gobe mai kitsona zata zo, kuma ciwon hannu na bazai barni na k'arasa tsifar ba. Please za'ka tayani my Ancle?"

Yace

"Sai dai nayi Miki aski, ni shi na iya Kawai."

"Haba dai aski. Yaya zan yi aski Ina mace dani." Naci gaba da marairaicewa. Yace"Sumayya Wai ni bawan kine kome?"

Na fik'e murya irin ta d'a,a nace" Haba! Haba!!. ai ko a shirin wasan kwaikwayo, dole a ce da Mijin iya Baba. Darajojinka sun girmi haka tuni, Mijina."

Ya sassauto, domin naga ya d'an Saki fuska. "To, nawa za'ki bani na Lada?"

Na marairaice "Haba, my Ancle. Ina Daughter guda sukutum Sai na biya"

Yace "Idan baza'ki biya

Please Login or Register in order to submit comment