Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonki Sumayya. Zan iya bugar k'irjI nace Miki k'anwata, zan iya CE Miki kuma my Daughter duk dalilin Sulaiman. Really, ke matata ce, Amma a bakine ni a wurina, banda a aikace. Shi yasa bazan yarda na d'ora Miki wani nauyi nawa ba. Kema nasan bazaki so ba, ko zaki so, ni bazan so ba. Shi yasa tun farko ban b'oye Miki komai ba, ballantana ki Shiga duhuwa, idan kika ga ba yarda kika zataba.
Ko da yake Ancle sulaiman yace Wai NI DA KE MUN DACE. To ni ban kai hangen dacewar da yake nufi ba. Ko matakin benen soyayya bamu hau ba, yace MUN DACE?

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na biyu_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*



📱13
_______ Bazan yi Miki k'arya ba, nace Ina sonki, saboda kiji dad'i, kuma bayan k'aryar ma kuma ai da yaudara. Shawara ta, ki daure ki rink'a kallona a matsayin Kawu Sulaiman, hakan Zai kawar Miki da damuwar da zaki iya samun kan'ki a ciki, ko takura. Zai sa ki Samun sakewa da farin ciki a zaman Mu, idan kika da sawa zuciyarki hakan. Ki jarraba Sumayya, zaki tarar da a binda na fad'a Miki,zaki gasgatani."
Ni dai har ya fice, kamar gawa, na gaza yin motsi. Nasan shi ko a jinsa, game da furucin da ya furta min, saboda babu d'igon kuwa a tare dashi, wurin fad'in a bu, ko yin abun da yasa kan'sa. Tun da gashi bai b'oyemin komai ba, tun farko. Amma a bu nafi jinjinawa. Farko yace na rink'a kallon'sa a matsayin kawuna Sulaiman. Wurina kamar haramta halas ne. Shi Mijina ne, to don me zaice na rink'a kallonsa a matsayin Kawu na,da aure ya haramta a tsakanina da shi. Sannan ya dubi cikin idanuna yace yana k'yamatar Wai na soshi. Kuma Wai aure na dashi na fad'ene a baki ban da a aikace.

Banyi zaton za'ta kai Mu da nisa haka ba, domin zatona duk Wata d'awainiyar aure Zai bani damar nayi masa, iyakaci ya k'aurace min, tun da baya Sona.. komai Kenan bazan yi ba, hoto zan zama. Gaskiya da sake. Na dad'e a daren ranar ban iya Samun bacci ba, Ina tsara salo salon yarda zan fitowa Yariman kawu na, mai wuyar Sha'ani da tsadadden samuwa.

Idan yasan wata ai baisan wata ba. Nayi wayewar sanin komai, da iya komai. Zan fito masa duk ta inda bai zata ba. Kuma cewar da yayi na rink'a kallon'sa a matsayin Kawu Sulaiman zan kuwa fitine shi, duk shagwab'a da tab'arar da nake yiwa Kawu Sulaiman tun Ina yarinya, har girmana zai shata salo salo, bashi da k'orafi ko sababi, zan ce shi yaja. Da ace ban riga na aure shi ba, ya furta min kalaman nan, to tabbas zan yi zuciya na barshi. Amma tun da yayi saken da igiyar aure ta sark'emu, to wallahi bazan Hak'ura da shi ba, Sai inda k'arfina ya gaza. Bani ba, ko wacece ma a binda zatayi Kenan, in dai ta samu nasarar mallakar miki irin Ancle Fa'iz. Baza ta yarda ta canza shi da wani ba sai dai tayi k'OK'arin canza shi zuwa ga yarda takeso, idan zata iya, Ko taci layar hak'uri ta zauna da shi da halinsa.

A ranar dai nayi ta bak'i amma yawanci k'awayena na jami'a saboda su na gayyata a yinin biki na, saboda bana son tsofaffin k'awayena na secondry su San na auri malam Fa'izu, terere za'ayi tayi, ana kwazawa.

Daren ranar Ancle Fa'izu ya shigo falona, amma ba muyi hira ba doguwa. Duk yarda naso ya Saki jiki ya jima yak'i, ya kawomin uzurin wai a gajiye yake, na kuma karb'a. Ko minti biyar bai yi ba, yayi min Sai da safe ya wuce d'akin sa.

Da safe na a jiye bak'unci gefe d'aya, tun da nayi sallar a suba ban koma ba. Ancle Fa'iz nema ya tasheni sallar a suba bai San nima gwanar tashi bace k'arshen dare nayi nafilfili har zuwa a suba, to Sai yazo ya tarar dani zaune Ina lazumi, Sai ya juya.

Tare muka Shiga hada hadar girkin safe da su Khairat, duk da Khairat tayi tayi na bar aikin sayi nak'i. Ta Hak'ure, Sai gashi muna aikin tare cikin armashi, har 'yar hira mu keyi. Ita kuwa Muhibbat baya ga gaisuwa bata sake cemin komai ba. Bayan miskilanci, ma naga tana Fama da jin kai ainun, ko irin yanayin Yayan tane da ita ban Sani ba. Amma shi Ancle sanadin aure ya d'an sauya,tun da har yana 'yar hira dani. Ta yiyu ita ma ta sauya idan an Kwan biyu, amma fa a zatona.

Muhibbat dai tafiyar ta tayi ta barmu da aikin, kuma na lura sanadin zuwa na ne. Khalifa ne ya lek'o kichean d'in ya soma yiwa Khairat Maganar ta dafa masa ruwan wanka idan ta gama.Sai kuma yayi Jim, da ya ganni, in da ya sake bina da mayataccen kallo, Sannan ya Mik'o gaisuwarsa gareni.. Na amsa da sauri na kau da kai na ci gaba da a binda na keyi. Zuciyata bata sak'amin komai ba, game da Khalifa, Kawai banajin dad'in kallon da yake yi min ne, ko santaran nake babu aure. Ban Sani ba, ko shi kuma tasa d'abi'ar Kenan, ko kuma wani k'uduri ne a ransa. Amma yaya zanyi, tun da k'addara ta cilloni gidan'su.

Bayan ya tafi, Khairat tace "Yaya Khalifa ya cika matsawa mutane idan yaga a na aiki. Da da wutar nefa ma Sai na jona masa a Heater ko electric cooker. Amma tunda Yaya Fa'izu ma zaice na dafa masa ruwan wanka,, Sai Kawai na had'a musu wuri guda."
Nace"Bari na d'ora musu a gas cooker d'ina, idan yaso Sai ki d'ebarwa Khalifa nasa, kin San yanzu ruwan sanyi bazai zububa a jiki, dole Sai an d'an dafa, tun da da ragowar sanyi, tun da kuma safiya ce, Kije kiyi shirin makaranta, kar ki makara, naji kina tambayar lokaci, na k'arasa soya dankalin."

Tace "Gaskiya Kam. Kin hutashsheni ma, na gode Anti Sumayya. Dama na kusa latti Wallahi, wannan Yaya Khalifan Zai sake b'atamin lokaci. N'a gode."
Nace"Kai Khairat, Ina a bin godiyar, ai anzama d'aya."

Cikin mintina kafin ta shirya, Na dafa ruwa, ta Mik'awa Khalifa nasa. Ban bata na Ancle Fa'izu ba, nace na a jiye masa, duk da na fahimci ita ke yi masa wannan aiki, ba kuma fasa bata zai yi ba na Sani saboda ni. Ni kuma na Hak'k'ak'e aikin ya dawo hannu na duk runtsi.
Da na gama na zuba komai a mazubin da ya dace. Daga Sama na jiyo muryar Momi, nan nasan ta tashi Kenan.
Na nufi benen domin na gaishe su har Abban. Amma gyaran muryar Abban da naji yana saukowa daga benen na dakata. Saye yake da babbar riga babu ta ciki. Nan nasan iya k'ofar gida zai fita. Na tsuguna na gaisheshi. Cike da farin ciki sosai ya amsa, ya tambayi lafiyata da yarda na kwana."Allah ya shi albarka, ya Baku zaman lafiya 'yata." Ba kad'an ba naji dad'in addu'ar nan tasa. Ko ba 'ace ba,kana ganin sa kaga Mutumin K'warai mai karimci. Fara'a Kam a fuskar sa kamar gonar auduga.

Nasa kai da nufin d'aga labulen mai kauri da ba'a ganin na ciki, na tsinkayi maganganun, kuma farko Sunana naji an kira, shine dalilin da gabana ya fad'i Na kasa Shiga, in da maganganun suka tayi ta tururuwar Shiga kunne na. Muryoyin Khalifa ne da momi.

"Sumayyan ai babu laifi Itama Khalifa.Tana da hankali da nutsuwa ga alamu ga ladabi. Gashi tana karatu, amma banga alamun wayewar banza a tare da ita ba kamar wasu."
Yace
"Momi, bafa a saurin yabon d'an kuturu, Sai ya mutu da yatsu."
Ta karb'eshi
"Haka ne Khalifa Sai ya mutu da yatsu."

Ya sake cewa.

"Momi, nifa tun kafin ma na ganta na tsaneta. Da na ganta Sai nafi tsanarta. Kallon k'urillama nayi tayi mata, domin naga me Yaya Fa'izu ya gani, a jikinta har ya zab"i auren'ta, amma bangani ba. Momi mai kafirin wayoce fa Yarinyar nan, da iya kissa, daga zuwa har ta zama 'yar gida?anya bazata d'auke Miki hankalin d'aba a gaba?
Da bata ce komai ba ya zarce
"Momi amma fa Yaya Fa'iz ya kwafsa, kan a bu kad'an yayi wani auren huce haushi, kodai k'arawa kai haushi, tun da na tabbatar Salima kad'ai yake so a duniya. Laifin mominta ai
bai kamata ya shafeta bako?"
Nan momin tace" Shima ai ba Salimar yayi nufin b'atawa ba, nufin sa na kan mamanta, amma dole ita zata fi kowa jin ciwon hukuncin da ya zartar na yin aure.Nasan labarin bai same ta ba, tun da kaji shiru.Amma dai ya aikewa da iyayenta katin d'aurin aure, ta yiyu bata ji ba.Nima banji dad'in a binda yayi ba na zartar da hukuncin yin aure, a matsayin ramuwa. Nafi son sa da Salimar sau dubu. Babu yarda banyi ba, na hanashi auren nan, amma ya dameni da magiya da lallami, kullum har Sai da na saduda. Ni kunyar had'a ido nake da Salimar ma Wallahi. Yarinyar dake mutuwar son'sa, duk in da d'an uwan sa yake, Sai da ta nemi Sani. Bata gajiya da yi Mana d'awainiya, jikinta bai huta ba, haka ma kud'inta. Amma a ce sakayyarta Kenan? Gaskiya Sai yanzu nake jin ciwon auren ma, bayan anyi. Ko a waya kunyar Mu gaisa nake ji. Kasan Kusan kullum tana bugowa ta gaisheni."

Khalifa yaja dogon tsaki.

"Dole ma Yarinyar nan tabar gidan nan Momi, dole ya sallameta, ko bai shirya ba."
Momin tace"Wani irin furuci kake yi Khalifa? Kai ke auranta, ko kana da wani k'arfin iko ne a kan mai auranta? ai babu Maganar dole, tun da Shima ba sonta yake yi ba, yarda na fuskanta , kama hutar da kanka. Idan d'an koli Yaci kasuwa, ai gida yake komawa ko?"

Khalifa yace "Haka ne Momi. Ni dama babbar damuwata, kar ta ritsa dani. Saboda Salima tace za'ta samomin aiki na acounter a kamfanin babanta. Kinga idan auren ta da Ancle Fa'izu bai yiyu ba, ko taji yayi auren nan, Yaya kike zaton makomata Momi? Ni za'ayiwa buk'ulu fa. Ai dole na shirya munak'isar da zai Saki Yarinyar nan Momi, idan naga bashi da niyyar sallamarta da wuri."

Ban tsaya naji me momin zata ce ba, na juya a hankali na sauko, saboda idan na Shiga za'su tsargu. Idan kuma na ci gaba da tsayuwa, za'su iya fitowa su ganni.

Nayi zaune a d'aki, damuwa duk ta baibayeni. Maganganun Khalifa su sukafi zafafa k'wak'walwa ta. Bansan zan fuskanci Wata matsala ba kuma a gidan, bayan ta b'angaren Mijina da nake tunanin ita kad'aice da zan ji da ita. To A she bayan matsalar da nake da ita ta Mijina, duk gidan ma Ina da matsala da su, babu mai yi dani a she duk sun fison Mijina da Salima. Gaskiya naga Muhibbat Sai wani fizga fizga take min. Momi farin cikin Ancle, Fa'iz tace ta fison Salima sau dubu dani. To ko iya nan matsala ta ta tsaya, ai da aiki gagarimi a gabana. Ancle baya had'a kaunar momin sa da ta kowa. To ni kuwa da wanne zan soma? Ta Ina zan fara? Da yaya zan soma warware matsalolin da suka yi min k"awanya hagu da dama?.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*



📱14
______Duk da wad'annan matsaloli dake gabana, amma domin k'arfin hali Wai b'arawo da sallama, Zuciyata Sai rad'amin take da cewa
Sumayya karki kaya, ba"a sanin maci tuwo, Sai miya ta k'are, kuma mai zabarin nema, yana tare da nasara, wataran, musamman mai nagarta.

Ni dai nasan, bawai nacin son Ancle Fa'iz ko ya Soni, shine babbar matsalata ba. A ra'ayina, a tsarina, babu a binda nak'i jini irin a ce nayi aure ya mutu, Sannan a ce ma ban dad'e ba. Sam! ban shiryawa Zaman zawarci ba, ban kuma shiryawa amsa sunan bazawara ba. Domin Muddin wa'adin aure na da Ancle Fa'izu ya cika ya sallameni, ban isa na goge tambarin sunan bazawara a goshins ba.

Nasan samarina ma zasu samu labari, suyi min dariya, musamman Usman, daya da ya tab'a yab'amin magana da Karin magana, yace Wai k'arshen a lewa dai kasa ce, suna nan suna zuba ido kuma, suga k'arshen'ta. Shi zaton'sa wani mai iko sosai na samu na barshi.

Bayan wani lokaci, na koma na gaishe da Momi. Sam Banga wani sauyi a tare da ita ba, Sai ma bangajiya, da tayi min, da cewa, Wai taji nice jigon aikin komai, na Karin kumallon ranar. Khairat dama ita ta kwashe komai, ta kaiwa kowa. Nima har d'aki ta biyo ni dashi. Tace min
"Anti Sumayya, na tafi makaranta. Fuska ta cike da fara'a nace"To, a dawo lafiya, K'anwata." Khairat, ita ce na tabbatar tana k'aunata da zuciya guda. Kuma nima ta Shiga raina, tashi d'aya.

Har lokacin, banga Ancle Fa'iz ba, ya fito daga d'akin'sa ba. Bacci yake ko menene, ban Sani ba. Kamar na Shiga na gaisheshi, na kasa.

Na had'a ruwan wanka mai zafi dai dai dai, nasa turarrurukan wanka, na rufe da murfin babban bokitin wankan,mai kyau.

Sai da na gama shiryawa, na zauna a falo, Ina karyawa, Sannan na jiyo muryar Ancle Fa'iz shida Khalifa a tsakar gida suna magana. Nan nasan a she Khalifa, ba fita yayi ba. Kafin na farga naji sallamar Ancle Fa'iz. Amma daga bakin K'ofa ya coge, muka gaisa. Nace"Ancle ga ruwan wankan ka can fa na kaima bathroom. Kallona naga yayi, Sai yayi d'an Jim, kamar bazai ce min komai ba. Ni kuwa nasan shammatar'sa nayi, shi yasa na sashi a kwanar nazarin yarda zai yi da katsalandan d'in da nayi, na binda bayaso nayi. Wato yi masa d'awainiya ko Wacce iri.
Nace
"Ancle, Fa'iz kajini kuwa?"

Ya shafi, kyakykywar
bak'ar sumar'sa da take a kwance ta soma fesowa, daga askin da yayi mai suna SKIN, da yay masa kyau kuwa sosai.

Yace"Naji ki Sumayya."
Daga haka bai sake cewa komai ba, ya tafi. Nasan da bai a mince ba, zai fad'amin ba ya so, tun da bashi da rufi, ko alkunya.

Ranar nayi bak'i sosai. Baba Talatu da Hajiya mariya suka fara bud'e fage. Da Tsokanar wasa na tarbesu nace
"Ku kuma tsofaffun nan Sai yau za'Ku gamo kai, Ku ringid'o kuzo? Ko Ku lek'oni jiya? Kuma naga duk mazajen nan ku ai naga duk tsofe, babu sabbon jini, sun zama jagwal, ballantana kuce tarairayar'su tasa kuka kasa Samun lokaci."

Hajiya Mariya tayi 'yar dariya tace
"Shak'iyyar wofi. Kwana biyu dai munji kunne, da kika yi gaba, yanzu kyayiwa mijinki kuma."

Baba Talatu, tace"Sa'a ma kika yi muka zo yau. Dama idan dad'i yay wa Mutum yawa, Sai yace Allah kasheni na huta. Da Kawunki Sulaiman cewa yayi, kar muzo, a bari a d'ebi lokaci tukun. Kakan kine, ma yace Sai munzo mun zo mun duba masa ke lallai, duk da dai bake kad'ai bace ma a gidan, ko menene ai da mata 'Yan uwanki ko?

Naji nauyi, na saddakai k'as nace kuma. "Yaya Kawuna yake?
Baba talatu, tace"Dama nasan shine a layin farko. To Lfy Lau yace a gaisheki da kyau." Na yi murmushi kuma nace.

"Allah sarki tsoho mai ran k'arfe, Yaya yake, kina kulamin da shi kuwa? (kakana). Tace

"Tace" Ko ke albarka.Lfy Lau yake, yace na gaisheki."

Hira sosai muka yi, daga bisani, na kaisu wurin Momi. Momi ta karb'esu da daraja Kam, suka yi tama hira, har Hajiya Mariya tace da Momi. Ina Angon yayi, bamu ganshi ba?"
Momi, tace"Sun tafi ziyarce ziyarce, shida Khalifa, d'azu. Tace"Ai nayi zaton jin za muzo ne, ya waske, gudun kar muzo muyi masa d'iban Karan mahaukaciya,saboda ya Samu, Sabuwa, ya ya damu gefe." A kasa dariya, a tare. Hirar barkwanci tsoffin nan sun Shashi da Momi. Hakan yay min dad'I Kam, sosai. Nuriyya tazo a ranar, kuma da ita muka yi ta tarben bak'i har girke girke, duk da momi ta aiko da nata daron tace a bawa bak'i.

****

A Sati na na d'aya a gidan, Ina zaune gaban mudubi Ina taje kaina, Wanda yasha washing da retourching, Yana ta shining ya kwanta lab'am. Ba kuma wani tsawo ne da shi ba can, iya saman kafad'ata yake tsayawa. Ina kuma alfahari da a bina a hakan.
Half vase ce a jikina, da under wear na siket iya gwiwa, domin kwalliya na gama nasa turarurruka na jiki, zan saka kaya na Kenan, naji an banko k'ofa da sauri, an shigo. razana nayi, bawai ga yanayin under wear Kawai dake jikina ba ma, saboda nasan babu mai iya shigomin d'aki kai tsaye haka ba, domin ko Ancle Fa'iz Mijina iya kacin'sa falo, bai tab'a Shiga cikin d'akina ba.

Wanda na yanke tsammanin Zai shigo, shid'in ne ya shigo. Ancle. Sau d'aya ya dubeni, kuma duban sauri da ya shigo ya wuceni ya isa kan gado, ya zauna. Na Samu sauk'in razana, ganin shine. Naja dogon Hijab na sallata nasa, na sake kai duba gareshi, cike da Mamaki. Da ganin'sa kasan daga wanka ya fito. Silk d'in sumarsa da bata taru da yawa ba, jik'e take da ruwa. Zulaika ce gajera a jikin'sa, da towel fari, sol, da ya sak'ala a kafad'a.
Nace"Lafiya kuwa, Ancle?" Kafin yace komai, k'ofar d'akin da take a bud'e ya tashi ya jawo ya rufe. Sannan
Yace

"Mutum, domin ya shigo d'akin matar'sa laifine?"
Na girgiza kai
"Ko kusa, my Ancle. Gani nayi baka tab'a shigowar bane"
Yace"To, yau na shigo, then so what?"
Nayi shiru, Ina kallon'sa.

Ya sake zama kan gadona, ya cire towel d'in da ya sagala a kafad'a ya ajiye gefe

"Sumayya, wani a bune ya faru, nake so, Kije falo ki zauna, ko da Momi ta aiko kirana, kice bananan"
Toh! Wata Sabuwa Inji 'yan caca. Kallon da nayi masa galala, yasan tambayace zan masa na dalili, ya katseni
"Karki tambayeni dalili. Just ki aiwatar, kyaji komai daga baya. Yanzu babu lokaci, kiyi sauri Kije"
Na ja zani zan d'aura, kasan Hijab yace"Kisa kayanki Mana, tun da kin d'ebo. Kiyi sauri amma.

Bani da zab'i face bin umarnin'sa da nasan zai iya jefani matsala babba, idan a kasamu kuskure a ka gane gaskiya. Amma k'arya kuma ba'halin Ancle Fa'iz bace, ko mai amfani ce. Tun da yau yayi kuwa, nasan da akwai babban dalili, ba kuma k'arami ba.

Na Shiga kici kicin cire Hijab domin saka Kayan da sauri, duk da nauyin'sa da yake zaune a d'akin yasa nake komai a sanyaye kuma. Sai naga shi d'in ma juyar da kan'sa gefe yayi ya jawo wani littafi irin na ma'aurata zalla da Nuriyya ta sayomin yana dubawa.
Ban gama d'aura d'an kwali bama na fito, na jawo k'ofar d'akin na barshi a ciki.

Na fara da kunna kallo, domin Samun Nutsuwar yin basaja.Amma, zuciya ta cike da tararrabi take, na me yake faruwa. Fatana dai ko maye, kar ya ritsa da ni, wurin yiwa Ancle Fa!iz Mijina biyayya. Ko minti biyar kuwa, ban cika da zama ba, Sai ga Muhibbat ta d'aga labulen k'ofata tana daga tsaye k'erere, da jin isar nan da fad"in rai tace "Yayan Yana nan?"
Nace
"A'a bai shigo ba ai ."
Ta tsuke fuska" To, Ina zai Shiga Kenan?"
Nayi tsai, Ina kallon'ta Sai kuma nace

"Kin duba, d'akinsa baya nan?" Bata amsamin ba, illa tsaki da taja, ta Saki labulena ta tafi. Na d'an ji ciwon hakan. A binda na kasa tantancewa, ni take yiwa tsakin, ko kuwa rashin ganin Yayan nata.
Bayan mintuna da fitarta na Shiga d'akin, na sameshi, a kwance ma yake a binsa. Nace"Muhibbat tazo nace mata baka nan, Wai don Allah me ya faru ne?"
Yace
"Zan fad'a Miki, Jeki d'akina ki d'auko min Kaya marasa nauyi, shirt da jins, ko T. Shirt da troser da takalmi, da under's, a Kwai sababbi da ban bud'e ba under's, su za'ki d'ebo." Nace" Tom."

Da na fito a d'arare, nayi sa'a duk suna saman Momi, Ina jiyo hayaniya kuma. Na Shiga d'akin Ancle, a karo na farko. Gado ne Kawai da kwabar zuba Kaya,set, da kujerar zama. Na bud'e kwabar, duk na d'auko Kayan da ya sa na d'ebo. Wasu Kayan duk a hargitse, bayan da gogaggu a ciki. Nafi zaton wurin neman wani abu ya hargitsa.
Da na kawo masa, na d'ebo mayuka da turarurruka na jiki da na Kaya, da comb nawa. Domin ban d'auko nasa ba. Yace"Sumayya kwashe Turaren nan, banasa turare mai k'arfi, Sai mai sent, cool, irin nawa. Nace "To" kuwa na kwashe.
Na fito na barshi yana shiryawa. Da na fuskanci ya gama na kai masa Karin kumallo d'akin. Tea da soyayyan plantain ne da k'wai da Khairat ta kawomin.
Ya juyo Yana mai gyara botton d'in riga yace"Ke me zaki ci, da kika kwaso Break fast d'inki kika kawomin?"
Nace"Ancle, ai yayi min yawa dama, na Mutum biyu Khairat ta kawo."
Yace "Duk da haka, Kije ki karya, idan yayi Miki yawa kikai kichean a ba mabuk'aci. Ni a waje zan karya ma."
Ba haka na so ba, na maze amma, saboda na soma karantarsa, idan yace Bazai yi a buba, to fa rabu da shi Kawai. Na kwashe Kayan da ya cire da nufin wankewa ko ba lokacin ba. Na zauna a falo. Ya fito yace"Zan fita, ki rufemin d'akina an jima, mukullan suna kan tebur d'in ward robe." "Nace"To, Ancle"

Sai da ya lek'a tsakar gidan, yaga babu kowa Sannan yay wuf ya arce.
Nayi masa a dawo Lfy, Bayan ya Fice, bai amsa ba, shi yasa nasan bai ji bane.
Bansan me yake faruwa ba, amma Ina ta jiyo hayaniya a Saman Momi, da a lamu bak'ine.
K'arfe takwas na dare, Ancle Fa'iz ya dawo. Dama yakan lek'Oni, kafin ya wuce wurin Momi, idan ya dawo. Daga bakin k'ofar yace"Bari naje wurin Momi, naga yarda zamu kwashe da ita,Sai nazo na fad'a Miki kome ya faru, nasan kin zak'u. "

Yafi a wa d'ya, kafin ya dawo. Na d'ebo turare cikin show glass ya shigo. Kan kujera two seater ya zauna. Nima Sai nazo kusa da shi dab, na zauna. Nace"Nayi zaton kamanta fa"
Yace
"Yaya zan manta, Bayan ninace zan fad'a Miki. Ya kwantar da kan'sa jikin tudun kujera ta baya, cikin galabaitacciyar murya yace"Don Allah Sumayya ki daina saka wannan turaren d'akin mai k'arfi. Wanda kike sawa ma na jiki sent d'insa is high. Turare mai k'arfi har kaina yake hawa."
Na danne, ba dad'in da naji nace"To my Ancle, zan daina sawa na samu air freashner Kawai mai sanyin k'amshi na d'aki. Na jiki kuma zan saka iya body spray sansanya.

Yace"Koma wani iri kiyi amfani da shi, amma d'an kad'an zaki sa. Yayi a jiyar zuciya ya zarce.
Dazun Salima ce tazo gidan nan. Ina wanka naji sallamarta. Shi yasa Ina jin ta hau benen Momi, ni kuma da na fito daga wanka shine nayi sauri na shigo d'akinki. Saboda nasan Momi zata tilastani da cewa,na bita Muje wurin mamanta, saboda ta turo kirana har sau uku nak'i zuwa. Tayi laushi tayi nadama sosai, ni take ta zabarin nema nazo ta bani Hak'Uri na auri 'yarta, batasan ta makaro ba. In dai nine to Wallahi ba ta ma soma nadama ba.
Sai jiyan Salima da yamma ta samu labarin aure na dake, domin mamanta b'oye mata tayi a she a son samunta Sai an nemoni an dai daita komai, Sai Salima ta Sani, saboda tasan taga katin auren ma ba k'aramin hauka zata yi musu ba. To jiya ta samu labari, ta tashi hankalin su. Ta nemeni a waya na fad'a mata a binda mamanta tayi min. Kuka ta rink'ayi min sosai, Wai banyi mata a dalci ba da tun farko na rufeta. Wai ai babanta yana raye ai shi Sai ya d'aura Mana aure. Amma Yaya zanyi aure? Ina nake ta tsoma rayuwarta. Ko Ina zaton zata iya rayuwa babu ni. Ke surutai kala kala. Jiya ma cikin dare ta kirani a waya tana kuka da surutai. Gaba d'aya daren

Please Login or Register in order to submit comment