Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirana. Na Shiga d'akin'sa da sallama, yana zaune gefen katifa, ya nunamin kusa da shi daga gefe yace

"Zauna, Sumayya, magana nake so muyi."

Na zauna, na juyar da kaina gefen k'ofa da mutane ke wucewa 'yan uwa, Jifa Jifa, daga waje zuwa cikin gidan, ko daga ciki zuwa waje, saboda k'ofar d'akin bud'e take, ana hangen Mu.

"Yaya naga baki da walwala ne? Kina da Wata damuwa ne, Sumayya.?"
Nace muryata na rawa.
"Allah Ancle banason nayi nesa da kai. Wallahi auren ya ficemin daga rai. Bazan iya jurar na wayi garin Allah banganka ba, kawuna. Don Allah ka taimaka a sahalcemin auren nan."

Yayi murmushi, ba tare da ya nuna damuwa da furutaina na sokonci, da kuskure gami da wawtaba.

"Sumayya, hak'uri zakiyi. Ko ba jima ko ba dad'e dole Mu rabu Sumayya. Babu yarda za'ayi Mu dawwama tare.Aure shine cikar darajar mace, shi yasa nafi kowa farin ciki da auren'ki. A yau zan cika alk'awari na fad'a Miki dalilan da yasa na aura Miki Ancle Fa'izu, ko kya rage damun kan'ki, kafin kiga zahir kema da idanun ki ki tabbatar..

Yarima Mutum ne mai gaskiya kuma kaifi d'aya ne a magana, bashi da fargaba ko tsoro wurin tsage gaskiya, ko kad'an.
Kinga mai irin wannan hali, za'ki sameshi da rik'on a Mana. Babu mai rik'on a Mana kuma Sai Mutumin kirki.

Babbar d'abi'arsa da tafi burgeni, shine bashi da ZARA.! Wato kule kulen 'yammata, daga wannan a koma wannan, yarda yawancin a bokan'sa naga wasu suna da irin wannan hali.

Zan iya rantse Miki, Sai kyawawan mata guda goma su wuce ta gabansa bai kulaba, saboda ba mai ra'ayin kule kulen 'yammatan bane. Macen da yake so, shi ita kad'aice a gaban'sa.

Duk namiji mai Zara, za'ki sameshi da d'auka da a jiyewa. Kome kike Tak'ama da shi, da yaga Wacce ta fiki, tauraruwarki zata dushe, yayi k'ok'arin barinki ya kai mata hari. Kuma namiji mai zara, kullum cikin hange hange zai kasance, ko aure yayi matarsa ba za ta tab'a gama gamsar da shi ba.Kenan daga nan, k'ofar matsaloli sun bud'e. A yi hattara mata.

Namiji Mara zara kuwa zaki sameshi da tsayawa ka'in da na'in a kan guda d'ayan nan da ya keso, Wata ba za ta yi ta d'auke masa hankali ba. Kuma ko k'addarar aure ya ratsa zai yi, to bazai rink'a auri Saki ba. Yau ayi gobe a Saki. Kuma namiji Mara zara, zaki sameshi da son matar'sa da kulawa da ita sosai da kishin'ta. Ki Sani suffofin Yarima fa nake wassafamiki, cikin rukunin namiji mara Zara.

Mutane da yawa fassara d'aya suke yiwa Yarima, shi yasa har Sukan manta da wasu d'abiun'sa kyawawa masu wuyar samu a zamanin nan. Kuma nafi kowa sanin Yarima da fahimtar'sa cikin a bokan Mu. Shi yasa muka shak'u tamu tazo d'aya.

Tuni na fahimci cikin halittarsa ne wannan d'agawar da jin kan da za'kiga yanayi. Amma a zuciyar'sa babu wani nufin yanayin hakan ne da nunin d'agawa na yafi kowa wani a bu haka nan d'abi'arsa take. Amma idan kika fahimceshi sosai, kika fuskanceshi, kika samu kan'sa Kuna Mu'amala ta d'asawa, to za'kisan Yarima a wasu juyin Mutum ne a bin so. Yana kirki Sumayya, amma fa Sai Kinsan makamar iya zama da shi za'kisan hakan, har ki yarda.
Nasan ke damuwar ki babba, babu soyayya tsakanin Ku. To ki Sani, anayin aure babu soyayya kuma a sameta daga baya. Kuma a na yin aure da soyayya daga baya ta gushe. Kinsan in'da matsalar take?"

Na girgiza kai a hankali.

"A cikin d'abi'a matsalar take Sumayya."

Nace "Ancle Yaya a bin yake ban fahimta ba."

Da sauri yace

"Yauwa 'yar albarka, wato kowan ne da Wanda ya dace dashi ya aura wurin d'abi'a, shi ake kira da Sab'awar halaye. Kinga kamar a kan'ki keda Yarima. Babban a binda yasa nake ta jaddawa ma Kenan a raina na cewa KE DA SHI KUN DACE.
Farko Kinga Yarima yana da zuciya sosai. Ke kuma kina da hak'uri. Ba komai ne ma yake b'ata Miki rai ba ke.
Yarima yana da d'an rik'o da rashin saurin yafiya. Ke kuma kina da saurin yafiya, da mai da komai ba komai ba. Kafin ma a nemi a fuwa kin yafe, tun da kin ma manta an b'ata Miki ma.
Yarima Yana da d'an zafi, a wasu Mu'amalolin. Ke kuma kina da sanyi sosai. Sau tari Yarima bashi da son magana, Sai ki bashi sunan miskili ma kai tsaye. Amma a wani tsukin Sai kiga kamar bashi ba, har hira Sai kusha. Amma dai rashin son hayaniyarsa yafi yawa. Na fuskanci ke kuma kin iya zama da mai irin wannan halin. Kin iya da halayen mutane wurin zama. Kuma nasan za'ki iya da wannan halin nasa mai kama da miskilanci Shi yasa nace KUN DACE.

Wannan shine Sab'awar halayen da ake so tsakanin ma'aurata, domin Muddin Mutum ya had'u da mai irin d'abiar sa a komai, to ba za ta yi kyau ba, ko kad'an, tamkar BOM a ka dasa, dake buk'atar lokacin tashin'sa yayi, yayi bindiga. Kema ki auna a bu d'aya rak!.ace mai zuciya, ya had'u da mai zuciya, Yaya kike zaton makomar?"

Nace

"Ai Sai a binda aka gani Kawai na rigima my Ancle."
Yace k'arshen furutan'sa
"Ai Sumayya, wurin Sab'awar d'abi'u a ke sanin an dace, amma ba'a wurin Samun mai kud'I irin kaba, komai kyau irinka ba, ko ilimi da sauran a bubuwa da akayi tarayya a cikin'sa. Wata soyayya ma a waje iskace, Sai anzo an zauna, 'yar manuniya ta nuna na halayya da za'ayiwa juna dai dai, Sannan soyayya ta gaskiya zata maye gurbi. Shine an dace da juna, da kuma Soyayyar. Me yasa kike ganin, anyi shaharar riyar soyayya da anzo zaman auren Sai yak'i dad'i kuma.?"

Kawu Sulaiman yayi gaskiya. Na fahimci komai Kam, daki daki. Ya kamata kuwa ma'aurata kafin suyi aure, su fahimci irin d'abi'un Wanda za'su aura, koda da bin cike ne, domin a San an dace da juna kar Sai an Shiga a fad'a cikin matsaloli.

Dole naso Kawu Sulaiman, sosai ya hanamin kuka lokacin da zan yi. Ya kuma sharemin hawaye lokacin zubar'su. Na fad'I hakan ne, saboda dangin babana da su ya dace Sufi tsayamin a aure, cogewa suka yi, kuma babu a binda suka yi min, Sai k'afafuwa suka kawo a Kayi biki da su, maza kuma d'aurin aure. Ko ganin k'asa ta rufewa Mahaifina idanu ne, suka watsar dani? tun da ko nemana ba sayi. Da babu Kawu Sulaiman a Sha'anin aurena, da bansan irin tozartar da zanyi ba. Har sark'ar gold Kawu ya bani a ranar k'irar dubai. Nasha kuka da zamu rabu da kawuna, in da duk jarumtar'sa Sai da ya share k'Walla Shima.



An Shiga👇

JIGON LABARIN..... 🏡

**********************💞

______ Unguwar magajiya cikin garin zariya, cikin wannan unguwa gidan'su Ancle Fa'izu yake. Nan kuma zan zauna cikin gidan'su, tun da ginin'sa bai hattama ba, da saura sosai, saboda babban gini ya kamfatowa kan'sa da Zai jima bai kammala ba, tun da bashi da samu na sosai da sosai da Zai kammala da wuri.
Gidan nasu, babban gidane sosai, amma irin fasalin ginin dane dashi, kamar shekara talatin baya. Fentin da kayiwa kafatanin gidan yayi kyau, duk da ba k'erarren bane. Babbar k'ofa d'aya ce ta bak'in k'arfe ta Shiga gidan.

Khalifa, shi yake bima Ancle Fa'izu, d'akin'sa za'a fara tararwa da an shigo harabar makeken cikin gidan. Muhibbat, ita ke bima khalifa, d'akin ta na can gaba da nasa.A Kwai kuma wani falo madaidaici da ya Shiga tsakanin'su a rufe yake amma ruf, da alamun babu kowa. Khairat, ita ke bima Muhibbat, d'akin'ta yana jikin na 'yar uwarta.

Wanda ke gaba da na khairat, falona ne babba mai d'akuna biyu. Kuma da usuli, anan khairat da Muhibbat suke a tare, sanadin zuwa nane suka barmin wurin, saboda yafi Yalwa, shi zai dace da a marya Irina. A Kwai kuma wani fallen d'akin gaba da nawa, nan Ancle Fa'izu yake, Amma da usuli Shima d'akin'sa kusa da na Khalifa yake. Duk daga baya suka canza tsarin komai, saboda auran.

Bangaren hannun daman hagun d'akunan dake zagaye da da farfajiyar gidan benene gajere da zai kai ka b'angaren iyayen Fa"izu, nan suke gaba d'aya. Gaba da benen kichean ne babba na Momi. Gaba dashi store mai daici, shi ya zama kichean d'ina, bai ma cinye komai ba, tun da Deep freezer ta bata samu Shiga ba, Sai Friedge da yake shi k'aramine. Daga bayan benen band'aki ne, gaba dashi ma wani ban d'akin ne.
Gaskiya, komai nasu ya birgeni duk da ba masu arzik'in bane, Amma na lura a Kwai soyayya da rayuwa mai ban Sha'awa a wurin iyalan gidan, kamar yarda Sukan su iyalan gidan suke kyawawan gaske. Duk mahaifiyar"su suka d'auko, Amma Khalifa shi ya baud'e.


Bayan sun wawashe kyan na gado sun barshi da kad'an, Sai ya fito kuma bak'i. Amma daga baya da naga Mahaifin"su, Sai naga a she shi ya biyo sak"! Kamar ni Kenan.'Yan uwan mahaifiyata sun cemin Wai Mahaifina na biyo, Wai da na biyo mamata khadija, da Sai nafi haka kyau. Toni godiya na kewa mahaliccin halittar, domin nasan nafi wasu. Kuma babu mai dubana yace min mummuna. Ina nan a tsakiya. Idan ba'a yaba ba, to kuwa baza'a kushe ba.
Idan Mutum yana duban na k'asa da shi, to bazai yi butulci ba, domin Duniya kafi, a fika ne. Idan Mutum kullum na Sama dashi zai rink'a dubawa, to ba zai zama mai godiya da tawakkali ga ubangiji ba. Kuma ni ban yarda a Kwai mummuna ba. Sai mace taso zata zama mummuna, in dai tana la'akari da wasu da suka fita tana sarewa, tana k'ask'anta kan"ta, to baya zatayi tayi.idan mace ta yarda ita mai kyauce Itama, to kullum k'ara kyawun zatayi, domin zata kasance ne ko yaushe cikin yin a binda zai k'ara mata kyau.

Ra'ayin Sumayya ne.

Ni dai, tun da aka kawoni d'akina a ka watse, banyi tunanin komai ba Sai bacci. Kukan da na Sha, yasa b'arin kaina ya matsamin da ciwo, nasan babban maganin'sa irin na Kwan'ta nayi bacci. Sam banyi tunanin Wai na jira Ancle Fa'iz ba, ban sa rai da zan saka shi a idona ba.

Bani da bashin salla, har shafa'i da wuturi na sauke kayana. Tun da na Kwan'ta ban tashi farkawa ba, Sai uku da rabi na dare . Da Saura sallar a suba. Na jero addu'oi na fito rik'e da torch light mai haske, domin na kasa bacci kamar kullum. Fargaba da rashin sabo na sabuwar rayuwa. Kona koma bazan iya ba sosai saboda kar na makara a sallah. Na fito domin duba a gogon falo.Falon babu kowa wayam. Amma naga an rufe k'ofar falon da na sayo kad'an, an rufe sosai. Wannan shi ya bani tabbacin Ancle Fa'izu ya shigo, bayan nayi bacci.

Dab da sallar a suba na koma bacci na kamar mintina arba'in na farka, saboda ban saba bacci ba a lokacin. Falo na na fito, da nufin na je na d'auro alwala, domin anyi sallar a suba.

Sararo nayi, saboda ganin kuma Ancle Fa'iz kwance kan kujerata kamar mai bacci. Singlet ce a jikin'sa, ya rataye rigar Kayan' jikin hannun' kujerar. Na tabbatar bayan sallar a suba ya shigo, tun da d'azu k'arshen dare bangan shi ba, baya nan......😱
_______________________`_



Anyi mai wuyar, tun da
an shigo JIGON...... labari....Mu had'u a gaba Fan's😀.....

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*




📱12
_______ Hannun'sa da yasa ya rufe fuskar'sa shi yasa na kasa tantance bacci yayi, ko idanun'sa biyu. Sai dai da nazo zan wuce na fita, Sai Jinayi yace "Ina zaki?" Idanun' nasa , dai a rufe yake da na juyo na kalleshi.
"Alwala zanje nayi" Nace.
Shiru yayi.

Bayan naje nayi alwala na dawo, na tarar kuma bayanan. Al'amarin' nasa Kam da d'aure kai.

Ya sake shigowa bayan gari, yayi haske sosai. Yana saye da rigar wandon shaddar da yasa d'azu, milk colour.
Dams Ina zaune a falin nayi zugum. Tunani kala kala sun lullub'eni.
Yace dani
"Ranki ya dad'e. Da ya shigo mukayi arba. Ban tab'a ganin'sa cikin nishad'i ba da walwala irin na ranar.
Nayi murmushi nace
"Ancle ai Sai ku wannan." Daga nan na rusuna na gaisheshi a ladabce.

Ya d'an nade rigar'sa ya zauna a kujerar dake gefen tawa, ya juyo yana kallona yace.
"Sumayya ake kika kika can,can'ta da a baki kambun sarauta guda. Irin wannan harkar Hutu haka? Tun jiya kika yi kwanciyarki da wuri, har na shigo baki Sani ba. Da a suba ma na shigo na k'wank'wasa jikin gadon'ki domin kiyi sallah, bakisan a nayi ba. Ni kuwa Ina na samu wannan hutun jin dad'in?

"Kai d'in dai kai ka dace da rik'e kambun sarauta Ancle. Ko a sunan da a ke kiranka da shi, an an yarda anbi. Yarima fa kake.!
Murmushi yayi, da ya k'ara masa wani sihirtaccen kyau, ya Saki Zancen, domin yaga nayi baki, har na fishi hujja.

"Kije Ku gaisa da Momi, domin muna gaisawa take Tambayata ke, Wai Yaya kika kwana, nace k'alau, Amma Kije taga zahir dai."
Naji sanyin dad'I da momin'sa ta soma damuwa da al'amarina. Nace"Yanzu Dama nake tunanin naje na gaishesu, ita da Abba, to ban Sani bane, ko sun tashi daga bacci, ko basu tashi ba."
Yace
"Ai mu nan gidan, in Dai muka tashi da a suba mukayi salla, to Bama komawa bacci. Idan ma a Kwai mai komawa baccin, to nine, kuma ba kullum ba nima, Sai San'da bani da uzurori da yawa. Amma Kije Ku gaisa da momin, shi Abba ya fita yau da wuri, Amma an jima Zai dawo.

Na dubeshi, cikin rausaya idanu.
"Ancle, Muje Kayi min jagora, kaji?"

Yace cikin bud'e min idanuwa
"Kina da larurar makan'ta?
Nace"Ko d'aya.

"Then, why kike so na jagoranceki?"

"Kunyar Momi, nake ji Allah."
Ya gyad'a kai "Kina da aiki a gaban'ki Yarinya. Amma fa bazamu jera ba Gaskiya, Sai dai ki bari nayi gaba, ki biyoni a baya."
Duk da bansan k'asadin'sa ba game da haka ba na hak'ura da hakan, saboda tuni na soma fahimtar'sa, Ancle Fa'iz, mutum ne shi da bashi karb'ar uzurin magiya ko roko, shi yasa ma ban soma ba.
Sai da na bada sa'oi tukun na bi bayan'sa

A harabar tsakar gida na had'u da Muhibbat Tana Shara, muka gaisa, amma dai banga sakin fuska sosai a wurinta ba.
Ita kuwa Khairat, Tana kichean Tana had'in Karin kumallo, domin k'amshin soye soyen'ta ma ya kauraye gidan.
Da yake, Ina d'an hangen'ta, duk da Bata hangoni ba, na k"arasa bakin k'ofar kichean d'in muka gaisa, nayi mata sannu da aiki cike da fara'a saboda naga fuska a wurinta. Da fara'a sosai ta amsa tace. "Yauwa Anti."
Yarinyar tashi d'Aya ta shigemin zuciya. Da alamu zatafi Muhibbat kyakykyawar Mu'Amala. Idan kuwa haka ne, Sai nace ta gama tako sa'a a matsayunta na 'ya mace. Domin kuwa ba k'aramar kyakykyawa bace Khairat. Kyau da hali, kuwa ai sai mai sa'a kan sa'a, d'ai d'ai Ku ke had'a duka.
A zaune dirshan na samu Ancle Fa'iz a falon Momi, kuma a gaban momi, yana shan tea. Duk da jin shigowa ta, bai cira kai ya dubeni ba, face momin da ta zubamin idanu, Tana k'aremin kallo a hankali. Ban kuma yi Mamaki ba, saboda jiya da a ka kawoni wurinta da daddare fusKata a lullub'e take har muka baro wurinta. Yanzu ne Kenan zata k"aremin kallo sosai.

Bayan na zube na gaisheta tace "Sumayya, yau kin wayi gari, a sabon wuri, Yaya a kaji da kewa?"
Kaina sunkuye cikin ladab nace "Momi AI bani jin sauyin komai, tunda Ina tare daku, kamar Ina gida ne.Ku iyayena ne, su khairat kuma 'yan uwa nane.

Na lura furucina ya faranta mata, a fuskarta na Karan'ta. Momi da Ancle Fa'iz suna kama sosai, har kalar fatar fara tas, mai sofanen jajaja, da kuma k'wayar idanun mai haske da yawa, da har yake bada launin shud'I shud'I. Duk da shekaru, sun d'an hauta kasan ta zuba kyau na lokacin k'uruciya, domin kuwa har yanzun Yana nan, sauyin kad'an ne, na turawar shekaru. Tabbas barewa bazata tab'ayin gudu ba, d'anta yayi rarrafe. Momi ta kalli Ancle Fa'iz da yake karyawa a nutse, tace

"Sumayya ga karin kumallonku can Khairat zata kai muku, kuma ga mijinki yazo ya dirarwa nawa, ai Sai ki matso Ku cinye Kawai tare, Khairat ta k'aro muku"
Kunya naji ta kamani, domin bazan iya wannan aiki ba gaban Momi. gashi kuma bazan iya bijirewa umarnin'ta ba.
Ancle Fa'izu kub'utar dani yayi da yace.

"A'a Momi, wannan ai yama k'are, ko bai k'are ba, gwara a kawo mata nata. Ni yau girkin ma na khairat, maleji nake yi da shi, duk ta cika magi. Can Yana cikin ci yayi saurun furzar da wainar k'wai.
"Magi, na tauna Momi, me ya samu Khairat haka?".
Momi ta dubeni tayi 'yar dariya.
"Sai kinyi kamar kina yi Sumayya, domin kin had'u da Miji mai tsirfa da k'orafi, ko Yaya aka kuskure. Ni na faraci kafin shi aMMA banji wani magi ba. Gishiri ne ya fito d'an kad'an. Kuma baiyi yawan da za'a yi k'orafi ba ko kad'an."

Nan ne naga ya d'aga idanu ya dubeni da sababben kallonsa Mara manufar komai yace
"Sumayya, karfa Zancen Momi yafa kid'imaki, duk da Gaskiya ta fad'I, Amma nasan baza'ki iya dani ba kema. Shi yasa girki iya cikinki za'ki rink'ayi idan kin soma girki.
Ya dubi Momi kuma
"Momi, kwanon a bincina fa Yana nan a wurinki kamar da, saboda Kinfi kowa sanin yarda nakeson d'and'anon a binci ko Yaushe.Khairat ke kamanta irin girkinki, to naga Itama ta soma shiriricewar yin girki irin na Muhibbat, yau a bu yayi kad"an gobe yayi yawa, to Itama na yafe ta, randa duk ba kya gida baki samu damar yimin girki ba Momi, waje zanje na samu Wanda yayi min na saya wallahi."
Banga wani sauyi ba Sam, a fuskar Momi, game da furucin d'anta, duk da tace
"Kadai biyo hanyar da bazata b'illemaka ba Fa'iz. Kayi aure, Amma aka da kwanon a binci? Kana dai da aiki a gabanka"

Ko kunya yace"Ja ma kuwa Momi, Amma nasan zan iya ne."
Ire iren wannan baisoma damuna ba, saboda nasan manufar auren da mukayi shi a zuciyarsa . Amma ni a Zuciyata, aure ne nake ji munyi mai manufa kyakykyawa, irin Wanda a keso. Shi yasa ni a binda zan maida hankali a kai, shine na Yaya zan janyo ra'ayin'sa gareni na canza masa alk'iblar da yake fuskanta.

A hanyar saukowa daga bene mukayi kicib'is da Khalifa, in da ya dakatamin yaja baya, domin na wuce. Shine farkon ganina da shi, Shima haka. Ta yiyu wannan dalili naga Yana yimin wani mayataccen kallo Sama da k'ASA. Nasha mur, saboda duk namiji mai wannan hali na kallon k'urilla, haushi yake bani.Amma duk da haka, bai sauya da k'uramin idanu ba, Sai fara'a da ya sake sakima Yana washe Hak'ora, a haka muka gaisa, ya haye saman Momi. Ni kuma na sauko, na nufi d'akina, in da naga Muhibbat Tana wanke wuri da tsintsiya. Nayi mata sannu da aiki, ta amsa cikin wani salo na I sa. A Raina nace, wannan miskilaNCI ta d'orawa kan'ta, ko kuwa haka yanayinta yake.? Bani da mai bani amsa, shi yasa dole Sai munyi nisan zama da ita zan canki amsa.

A kan kujerar da Ancle Fa'uzu ya tashi ta falona naga tsadaddiyar wayar sa a kife. Mantawa yayi, ko a jiyewa yayi yana sane bansani ba. Halin nawa nayi, na d'auka, domin ganina yanzu Ina da hurumin tab'a Abin Ancle Fa'izu, tun da Mijina ne.

Numfashina Sai da ya tsaya cak! na wucin gadi, ganin Wacce ke kan fuskar wayar Ancle. Duk da ban tab'a ganin ta ba, nasan ita ce. SALIMA.

Kyawunta da a ka kod'a to zarta ma da na ganta.

Wani irin Kishi naji ya ziyarci Zuciyata mai rad'ad'i . Shine shaidar farko da yake nunamin na tsundima tsindim a kogin son Ancle Fa'izu Wanda nake yaudarar kaina da da cewa Bana son'sa. Duk da nasan Salima yake so, ni auransa Kawai na rabauta da shi, babu zuciyarsa kuma sanadin dai salimar. Hakan baisa na daina jin ciwon kishin sa ba.
Salima tafi kama da irin larabawan Lebanon d'in nan, da basu cika haske ba da yawa, Sai tsagwaron kyau. English wear's tasa, Wacce ta matsemata jiki, surar halittar ta ta d'iya mace, duk ta nuna. Kanta kuma babu d'an kwali ta Saki yalolon gashinta ya zubo gadon baya,wani kad'an ta gefe ya zararo kan k'irjinta. Na sake kallon ta a Hoton na zumburi baki, na jin haushi. Sam shigar zub da darajar da tayi ta bawa namiji har ya zame masa mudubin dubawa a waya kullum ya sik"eni, bawai iya Kishi bane. Saboda Kayan da Gani masu tsadar gaskene, Amma masu nuna tsiraicine Gaskiya. Shi kuma Ancle soyayyace ta rufe masa idanu ya biye mata ya iya s jiye Hoton a fuskar wayar sama, bansani ba.
Sau tari wasu matan, suna ganin tallata surar jiki ga namiji Wayewa CE da k'arin janyo soyayya. To Wallahi k'Arya ne. Na k'Arya ta ni Sumayya. Bayan janyowa kai zunubi, ragewa kai daraja da k'IMA ne matuk'ar babu aure gib'I kuma sukewa kan'su sosai. Ko namiji bai nuna ba, ko bai hango aibi ba a lokacin to a gaba kuwa za'a karb'I raddi Wallahi.
To ni Ancle Fa'izu ya fita laifi a wurina, da har Hoton ya zauna a fuskar wayarsa, ko Yaushe Kenan da shi Zai fara tozali, idan ya d'auki waya. Tabbas giyar soyayya ta bugeshi yayi Yana sane, Bawai a ce bai hango illar hakan ba. Bansan Sanda nayi Jifa da wayar ba jikin bango saboda Kishi da haushi. Jikake tus! Na d'auka naga glass d'in ya fashe. Na d'ora jikin TV stand. Nasan masifa ce Kawai zan Sha. Iya ka Kenan.

Duk da Khairat ta kawomin break fast , ban karya ba, Sai da nayi wanka na shirya cikin kwalliya da ado sosai. Na zauna na karya. Har lokacin Ancle Fa'iz Yana wurin Momi.

A shiryen sa ya shigo min, Shima yayi wanka yasa shadda ruwan goro, hartin d'in gajera ce iya gwiwa. Sunfi yi masa fiye da Wacce ya cire. Duk da sirrin kyawun ba'a Kaya yake ba,a halittar ne.
Yana shigowa na dake, saboda laifin da nayi masa. Wayar tasa kuwa ya Shiga nema .

"Ba nan na bar wayata bane?"
Mik'Ewa nayi tsam naje na d'auko inda na a jiye. Har na Mik'a masa naga yanayi min wani salon kallo, da alamu na tuhuma ne, kafin daga bisani ya d'ora idanu a kan wayar yayi tozali da ta'asar da nayi. Ya sake dubana.
"Garin Yaya kika fasa min waya?"
Na sunkuyar da kai nace.
"Garin tsautsayi ne Kayi hak'uri Ancle." Na koma na zauna a bina.

Ransa b'ace yace" Garin ganganci Dai kika fasa min waya Sumayya. Me ya kaiki d'aukar wayar dake a jiye? Lek'en a Siri ko maye?"
Naji shigar furucin'sa amma na dake, saboda Nina jawa kaina. Kawu Sulaiman ya Sha yi min nasiha na daina tab'a a binda banawa ba, musamman na sirri, nace Sai na gani, gudun fad'awa rigima, saboda binciken da nake yi masa a d'aki. Na k'ara bashi hak'uri, nayi masa tayi da tea da nake Sha duk da nasan yasha, duk domin kau da Zancen ya wuce. Kuma babu dad'I daga auren Mu a ce mun soma Samun Sab'ani.

Ancle ya I so gareni, ya zauna gabana, kamar tea d'in zai Sha, amma Sai naji yace

"Sumayya, me yasa kike Kishi a kaina?".
K'warai Gaskiya ya fad'I, kishin yafi kaini ga hakan, Amma bazan so yayarda ba, duk da ya d'ago, shi yasa nace
"Wajibine mace tayi kishin mijinta.
Ya sake jefomin tambayar da ta hargitsani.

" To, Kina so na ne?"
Nayi k'OK'arin sarrafa kaina.
"Ai ko da so ko babu so, mace zatayi Kishi a kan mijina". Da sauri yace
"That's not true. Sai da SO ake yin Kishi. Nayi Mamaki da a d'an tsukin Nan da zuciyarki ta iya Sona. Ke Kinga na can canta kuwa?"

Na kasa iya cewa komai, saboda Sani a gaba da yayi, ya tsareni da idanun nan nasa masu sace zuciya farat d'aya.

"Idan za kiyi shawara dani tabbas zance kiyiwa zuciyarki shamaki da soyayyata, domin Bata da amfani a gareki Sumayya Sam!Sam!!. Kece mace ta farko da bazan so, ki kamu da soyayyata ba. Kamar yarda nake kallon su Khairat, haka nake

Please Login or Register in order to submit comment