Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake.

Ya gyara zama, cikin hard'e k'afafun'sa.

"Hak'ik'a naga a lamomin hankali, da nutsuwa da addini a tare dake Sumayya. Shi yasa Sulaiman, yana cemin ke ya zab'amin na a mince, musamman da naji yace ma kin yarda da aure na. Amma dai Ina jimamin, yin auren wucin gadi, da d'iyar Wanda nake ganin k'imar'sa da darajarsa a idanuna. Amma na kasa juya baya. I think, some thing is wrong with me."
Nace
"Kaji da shi." A zuciya ta.

"Amma fa wannan magana da mukayi, Ina so ta zama sirrin Mu, bana so taje kunnen kowa, saboda Mu ta shafa."
Nan kuma cewa nayi, a cikin zuciya ta.
"Ka makaro".
Yace
"Idan kina da a binda za'kice kema, kina iya fad'amin."
Abinda na iya cewa Kawai shine.
"UM!. Saboda naga al'amarin nasa, ya gagari cewa ta.
Ya sake, kallo na, yaga bani da niyyar cewa wani a bu, Sai naga ya tab'e baki, irin na jin haushi.

Ya fito da wayar'sa daga aljihu, naga yana ta daddannawa.
A sace na ci gaba da jefa masa kallo.
Tabbas Ancle Fa'izu Zai iya sace zuciyar ko Wacce mace. A kowani yanayi, kuma a kowani hali. babu shigar da bata yi masa kyau. Sai ya kan rink'a b'adda bami. Yau Sai kaga yafi jiya kyau. gobe, kaga yafi yau kyau.

Kawu Sulaiman da ya shigo, na fahimci, shi yake ta dannawa flashing a she, da naga yana ta daddanna waya, yayi ya tsaya .
Kawu na yana shigowa yace.
"Yarima har zaka tafi? Baka fa jima ba?"
Yace
"Ya zanyi to Sulaiman? Idan na zauna takaici Sai ya karni.Wannan bagidajiyar 'yar taka babu a binda ta iya Sai gidadanci. Tun d'azu Sai Surutu nake ni kad'ai, tak'icewa dani komai. Kallo nama ta kasa yi, Sai k'auyanci, take ta dokamin. Gaskiya ni bazan iya da ita ba Sulaiman.
Da yake Yasan halin Kayan'sa Kawu Sulaiman, banga ya nuna komai ba illa yace.

"Karkayi saurin rik'on'ta Yarima, had'uwar kuce fa ta farko"
Yayi saurin d'aga masa hannu
"Kaga, kar ka bata Wata Kariya saboda tana 'yarka. Tana sane. Yanzu da cikin k'awayen'ta ne, da tuni ka jiyo shewarta, Wai sunan ita 'yar jami'a ce, kyau a maidota primary, kuma a ji d'aya."
Raina Kam, naji ya sosu da furutan Ancle Fa'izu nacin fuska a gareni. Tabbas, halin'sa yana nan nacin zarafi, bai ragu ba ma, Sai k'aruwa ni a ganina. A gaban fa Kawu Sulaiman, Wanda Zai nemi aure na a wurin'sa yake min irin wannan wulak'ancin. Gaskiya Ancle Fa'iz baisan Wata aba Wai ka ra ba, ko kawaici, ballantana kunya.
Kawu Sulaiman ya dubi komai da aka kawo masa bai tab'a ba, yace.
"Yaya baka Sha ko d'an lemo bama. Me yasa.?"
Yace
"Ta banine? A jiyewa fa Kawai tayi. Wai look at her, batasan ma yaya zata tarbi bak'o ba? to Sai yaushe? Wannan 'Yar taka Sulaiman da gyararraki, ba gyara ba."

Ya juyo gareni ya watso min wani kallo mai kama da harara.
"Kinzo kinyi min wani dimkim dake. Sai a bin ya bashi 'yar dariya ya dara kad'an. "Sunan fa wani ganye Wai Shima dinkim. Sai ya sake sakin 'yar dariya da ban tab'a ganin yayi irinta ba.

"Ya kuma fa isheka haka haka, Yarima. Kai wani irin siriki ne Wai. Gaba na Sai aibatamin d'iya kake.Ko mutuwa ance tana alkunyar idanun iyaye.Wai kai bakasan Kawai ci ba, ko kunya.?
Bud'ar bakin'sa yace

"San'da a Kayi rabon su bana nan, ko zaka sammin taka?"

Ancle Sulaiman ya bishi da kallo Kawai, kamar Bazai taga ba, Sai yace
"Ank'i a sammakan, kasan darajar su ne."
Murmushi Ancle Fa'iz yayi.
"To, rik'e Kayan'ka, ka kuma maida wuk'ar. Ka Sani, ko nace Sumayya tayi zuciya ta daina gidadanci Kawai, shine Zai sa na sarara mata Wallahi, ba Sai ka tada komad'a bama." Ni dai daganan, Sulalewa nayi na barsu suna sa'insa basu Sani ba. Nace, sunfi kusa. Ga duk kan alamu suna irin wannan karawar, mai kama da wasa, a zahiri idan ka gansu.

Wannan nasan somin tab'ine a kan matsalolin da zan fuskan'ta idan nayi saken auren Ancle Fa'izu. Duk yarda zanyi kuwa zanyi, domin yakice auren.Sam! Ban shiryawa cin fuska ba, da tozarci da wulak'ancin Ancle Fa'izu. Wato Yariman kawuna.

Bazan yarda burina ya rushe ba. Tuni zuciya ta ta tsaramin, yarda nake son rayuwar aure na ta kasance. Rayuwa nake so, sosai ta soyayya da nishad'i da walwala, da farin ciki, da fahimta. Na tabbatar na auri Ancle Fa'izu duk sun rushe. Ballantana ma Wai auren wucin gadi, yake so nayi,Wanda Zai k'are kusa ne, nesa ne ban Sani ba, shi ya Sani. Abinda na Sani, ni Zai Cuta Kawai. Domin na tabbatar ko wani abu bai ratsa tsakanina na aure da shi ba, tilas ya sakeni kallon bazawara za'ayi min. Ban isa na goge tambarin zawarci a goshi na ba a idon mutane. Ga zato mummuna da za'ayi min a ce bani da hali ne. Dad'i ma samarina na baya suyi min dariya, da Allah ya k'ara, tun da ga zaton'su ni mayaudariya ce. Mak'iya na su samu hak'oran yi min dariya. Bani da abokin fad'a Sam. Amma duk Mutum nasan baya rasa masoya da Mak'iya.
Nasan kuma Kawu Sulaiman bashi da masaniyar nufin Yariman'sa. Nasan ko giyar wake yasha, bazai so nayi irin wannan auren ba. Dad'i ma naji daga baya, da yake bani da hak'k'in Yarima, gashi ya fad'a min k'udirin'sa kafin aure. Kenan na Samun hujjar ya kice auren cikin ruwan sanyi. Sai dai idan
Kawu Sulaiman bai ji ba. Dole kuwa yajin.

A d'akin Kawu Sulaiman, Ina rakab'e bakin k'ofa, shi ya fara magana kafin na fara,kamar yarda naso.
"Abinda kika yi, dole ya b'ataran Yarima, saboda shifa wayayye ne sosai, mai son harka ta Wayewa. Ballan,tana shi da ya sabayin hira da wayayya gogaggiya mai babban a ji irin Salima, dole ki sik'eshi.Bai kamata ki rikid'e masa ga siffar da nima nasan ba taki bace Sumayya .wani daliline a ranki, kika yi masa haka ko? Sannan domin k'arin kwab'a kika yi tafiyar'ki baku ko yi sallama ba. Menene damuwarki Sumayya?"

Wannan damar nake jira.

"Kawu, ni Wallahi halin'sa bazan iya da shi ba. Ko a makaran'ta tsoron karo da shi nake. Abu k'arami, Sai ya tozarta Mutum. Ka gani ma da idanun ka Kawu, gaban'ka ya rink'a yab'amin maganganu, ko nauyin'ka bai jiba.
Ya katseni da hannu.

"Da Kinsan Yarima sosai, da fahimtar'sa bazaki yi wannan k'orafi ba."
Na fahimci kamar Kariya kawuna Sulaiman yake bashi ma, shi yasa na fito masa da da Zancen da idan yaji, Sai ya zargeshi.

"Ancle Fa'izu fa cewa yayi aure na Zai yi na wani lokaci ya sakeni Kawu, saboda cikar burin'sa. Wallahi ya fad"a kaji na rantse."

Ga mamakina Wai Kawu nan nan ma bai damu da furucin Yariman'sa ba, da manufar'sa.

"Karki damu da Abinda ya fad'a. Ikon komai da tabbatar komai yana hannun ubangiji. Zukatan bayi, yana hannun ubangiji, shi yake sarrafasu yarda yaso. Saboda haka karki damu da komai. Ke ki nufi auren Ku, da kyakykyawan zato,da niyya mai kyau, da kuma kyakykywar addu'a zaki dace.za kuma ki a mintu daga a binda kike fargaba Sumayya. Ba kya gani, ko Mutum ne, ya nufeka da mugun nufi, kai kuma ka nufeshi da zuciyar alkhairi, sharrin'sa bayayin tasiri a gareka? Karki turje, kan wasu a bubuwa marasa tabbas d'in d'orewa, ki yasar da a binda yafi alkhairi a gareki, baki Sani ba. Ki dubama yarda k'addara take ta had'aki da Yarima, Ku had'u Ku rabu, Ku sake had'uwa.Sannan ni da nafi kowa son'ki a yanzu, ubangiji ya jarrabi Zuciyata da son ki auri Yarima. Kuma Sam, bana k'aunar a binda Zai kawo cikas a auren. Gani nake, Yarima shine kad'ai ni ya dace da rayuwarki a Duniya kaf Sumayya. Shine kuma Wanda nake jin Zai rik'emin a manarki ko bayan raina. Jikina ke fad'amin haka Sumayya. Sai auren ya gabato, zan fad'amiki dalilan da yasa na nace da aurenki da Yarima. Ban kuma damu da yana son'ki ko baya son'ki ba. Ke da kan'ki baki Sha Mamaki da ya amince da auren'ki ba? Aikin k'addara Kenan.Hakan na nufin fa, ke k'addarar cikin rayuwarsa ce. Wannan bai sheki ishara ba? In da na barki, kema auren rashin soyayya zaki yi da d'aya daga cikin masu son aurenki. Tun da haka ne, ki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya Mana. Ki auri Yarima domin dalilai da zan fad'a Miki su a gaba. Kuma ki yarda shi k'addarar rayuwarki ne, da bakisan me Allah ya shirya muku ba, ki aure shi saboda wannan. Ni dai ya fiyemin tarkacen samarin ki sau d'ari. Domin nasan komai a kan'sa, usuli da halayan'sa. Na gani, kuma naji a majiya ta gaskiya.Amma nasan ba lallai ki yarda da shi ba har zuci yanzu, saboda kallon wasu halaye na zahiri da kike masa. Amma a Kwai na bad'ini da bakisan da su ba. Shi yasa kike gani baza ki iya da shi ba. Tabbas zaki iya zama da Yarima, matuk'ar kika fahimceshi, kuma kika kiyaye a binda yakeso da wan"da baya so. Nasan ko baki gwanance ba, zaki iya koyawa zuciyarki, ki jure kiyi. Saboda kina da hak'uri da biyayya. Kuma ki Sani, idan ma kink'i auren'sa ba damuwa Zai yi ba, ba kuma hak'ura Zai yi ba da auren cimma Wata manufa ba. Wata Zai samu ya aura. To ita Watan kina zaton irinki ce mai kyawun zuciya da zata ceto shi daga yin kuskuren da yake son aikatawa, nayin auren wucin gadi? Ke kuwa nasan ko baki taimakeshi da komai ba, zaki taimakeshi, da nasiha da addu'a. Sanin kan'kine yin aure da niyyar Saki daga baya saboda Wata manufa, haramun ne. Kika yi kandagarkin hana afkuwar hakan bakiyi babban aikin Lada ba Sumayya? Naji jikina yayi sanyi Lis, da furutan Kawu. Tabbas Gaskiya ya fad'i , a binda nake shakkar yiyuwar, na yarda Ancle Fa'izu zai karb'i nasiha daga gareni, ko shawara. A yarda yake ji da kan'sa, ni kuma yake ganina a raine?
Kawu yace
"Kuma ki rink'a nuna kulawarki wurin mahaifiyar'sa, domin yana tsananin son'ta. Zan iya ce Miki nan ne sirrin farin cikin'sa. Ki soma d'ana tarkon'ki tanan. Ki kula, NAN FARIN CIKIN'SA YAKE.
ni na sake jaddada wannan a raina, har sau uku ma.
Da wad'an nan kalamai Kawu Sulaiman ya sake farauto Zuciyata ta a minta da auren Ancle Fa'izu. Amma fa ban daina farga ba ba, da zullumin auren. Tabbas ba domin na yarda da irin K'aunar da kawuna kemin ba, cewa zanyi farin cikin rayuwata ne baya so, yace na auri Ancle Fa'izu.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*





📱 10
________ Nayi sauri na fito daga d'aki, na karb'e tsintsiyar da Baba talatu, ta soma Shara da ita. Bata Musa ba, ta sakar min. Sai da na share ko Ina na cikin gidan tas!. Na had'o Kayan wanke wanke zan'yi Sannan tace"Ke dai Sumayya bakison kiga nayi komai, in dai kina gidan nan."
Nace.
"To, Baba Talatu, kina da kamata kiyi aiki? aiko tsari babu. Kiyi kwanciyarki, nayi aiki nayi kuma girki, Sai dai Kawai na kawo miki kici. In dai Ina gidan nan baza kiyi aiki ba."
Tace
"Koda a Kwai d'iya irin'ki mai kyawun hali, gaskiya k'alline. Kina da kyawun d'abi,a Sumayya, ga biyayya, ga tausayi. Ta Yaya kuwa bakina zai gajiya da sa miki albarka? da Fata na gari. In Sha'Allah Sai kin haifi masu binki, kuma Sai kin gwangwaje Miji na alfahari. Saboda kowa ya bud'i baki a kan'ki fata na gari ne. Addu'ar iyaye da 'yan uwa kullum bibiyarki za tayi tayi."

Tuni na saba da lafazan Baba Talatu dad'ad'a, kullum ne bata gajiya.

Tsawon kwana tara, ban sake ganin ko inuwar Ancle Fa'izu ba, ga wawtata farin ciki na Shiga sosai, a zatona ai ba zai iya dani d'in ba ne, kamar yarda yace, shi yasa ya janye.

A tsukin aka sake gayyatar k'ungiyar su Kawu sulaiman Kaduna united zuwa ga buga boll, cikin k'asar Enugu, za'su kara da club d'in Ranger's.
Nan ma su Kawu nane suka cinye. Ya bugo min waya, cike da farin ciki Yana mai shaidamin, dama sau biyu muna waya da shi, bayan tafiyar'su. Nasan da Ancle Fa'izu suka tafi, amma ko Zancen'sa bai yi ba, nima banyi ba.
Na fiddaran hakan, Sai ji nayi Ancle d'ina yace.

"Ga Ancle Fa'izu zan kai masa ku gaisa, kuma kiyi masa murna, domin shi Yaci Mana k'wallon nasarar guda biyu. Yana resting room amma na barshi yana shan mutuniyar tasa multina, bari na kai masa.

Da sauri nace
"Don Allah Kawu ka rabu da shi, basai munyi magana ba, kace Ina yi masa murna Kawai. Yace
"Zai fi kyau ki kira wayar'sa Ki fad'i masa. Idan baki da ita zan turo Miki. Nayi d'an Jim, daga bisani nace
"Ina jin nauyin hakan, Ancle. Naga shi ya kamata a ce yama nemi sanin lambata, ya kirani, amma bai yi ba. Shi yasa nake ganin kamar zan karyar da kaina idan na fara. Amma idan kace na kirashi, zan kirashin."

Yace
"A'a. Rabu da shi Kawai, na fad'a masa. Kinsan dai komai a kan'sa. Kinga kuwa komai ba zai shige Miki duhun menene dalili ba. Kinsan dole zaki rink'a had'uwa da irin haka, amma kiyi hak'uri wataran Sai labari kinji shalelen. Ni da shi mukayi 'yar dariya.

"Gaskiya Ina son Kawu Sulaiman, har bansan adadi ba, ko misali.

Kwanan'su d'aya tal da dawowa kawuna yace min.
"Sumayya, yau Yarima zai zo. Don Allah, ki kula a komai, kar ki bani kunya kuma. Ki canza"
Nace
"To, Kawu zan yi bakin iyawa ta" yaji dadi.
Na samu kaina da tsala kwalliya da ado fiye da farkon zuwan'sa sosai. Less nasa mai kyau, da nasan Ina kyau a ciki.

Har bakin k'ofar waje da yake tsaye na isa na tarboshi, saboda Kawu Sulaiman Baba ya aikeshi ya tafi, kafin fitowata wurin Yarima. Saboda haka kujeru na roba na Kawu na fito dasu harabar cikin wajen gidan kusa da d'akin Kawu dake kusa da k'ofar fita waje, da yake a katange ba'a hangen na ciki.
Kamar had'in baki, Yarima Shima Man less yasa na maza, kalar pink mai cizawa. Sun masa wani irin kyau Kam.
Duk da naje har bakin k'ofa na tarboshi cikin sakin fuska sosai, da sakin jiki da girmamawa, Sam banga ya sakarmin fuska ba. Ya dai dubeni, a dak'ile ya kau da kai. Tare muka jeru zuwa mazaunin Zaman, hannun'sa cikin aljihu, yana tafiyar nan tasa ta isa da jin kai. Naga Sai wani shan k'amshi ma yake, kamar Wanda aka tilasta Sai yazo wurina.

Kujerun da zamu zauna, suna fuskantar juna, kuma ni na a jiyesu Ina sane a hakan. Zuciyata ce naji ta soma k'ek'ashewa, daga fargabar da nake ciki ma na auran Ancle Fa'izu, saboda na hanga gabas da kudu da arewa, ban hango matsera ba, na tserewa auran. Shi yasa Kawai na Mik'a wuya, tare da nemo hanyoyin da zanbi, na k'ubuta daga tozarcin'sa da ya zama lazim. Nasan idan na ci gaba da nuna d'ari d'ari da shi, da Jan jiki, da alkunyar nan, to kullum gumamin takaici zai ci gaba da yi, shi ko a jikin'sa, ni zai bari da ciwon zuciya.

A tare ma muka zauna. Bayan na gaishe shi nace

"Yaya momi, da fatan tana lafiya "

Sai da ya fara da yi min wani irin salon kallo da Idanuwan nan nasa masu farauce zuciya. Amma na tabbata, babu manufar komai cikin'su.
Baki d'aya Sai naji yanayin komai nawa ya canza tashi guda. Wani irin feeling naji, da bantab'aji ba kan wani namiji. Gashi na jawa kaina, muna fuskantar juna bare na kub'uce.

"She is doing fine. Na barota lafiya Lau. Amma Yaya kikasan Momi?"
Nace
"Tun da nasan'ka ai dole na San'ta.

Yace"A'a ni kad'ai kika sani. Ita dai kinji sunan'ta wurin Sulaiman. Any way, naji dadI, da kulawar ki a gareta."
Karo na farko Kenan da na tab'aji ya nuna jin dad'i a a binda a Kayi masa a sanina.

Gudun kar na kuma laifi, nayi saurin cika cup da lemon maltina mai sanyi na Mik'a masa. Kafin ya karb'a yace
"Kinyi karatun ta nutsu Kenan!. Ban tanka ba.
Ya Mik'a hannu ya karb'a, Amma bai shaba, ya Shiga juya d'aya kwalbar lemon da ban bud'e ba.

"Yaya a Kayi, kika San Ina son lemon malt? aikin Sulaiman ne dai."
Idanun'sa na kan lemon yake surutan.
Ya shanye, ya sake cika cup ya shanye. Ya bud'e d'aya kwalbar ya cika cup ya Sha, ya a jiye ragowar a gefe.
"Da k'ishirwa na iso, Sai kika samu ladana kika yi a binda ya dace. Ina son maltina sosai a rayuwata. Na kansha kwalba uku Ku hudu wurin training ko gasar boll."
Nace
"Lallai kana son"ta da yawa."
"Ke baki son'ta?" Yace
Nace
"Kadai d'arsa min son'ta, ga yarda ka damu da ita."
Yace
"Look, ki fad'i opinion d'inki Kawai, ba ruwan'ki da zab'ina OK?
Naji rashin jin dad'in gwaliyar da yayi min, amma Sai na danne.

"Domin na tayaka son a binda kake so laifine.?"
Yace
"Kukure ne dai"
Kafin na wartsake daga wannan ya jefomin wani.

"Sumayya Wai addu'a kika yi min ne?"
Na waro idanu waje
"Wace addu'a zan yi Maka ni kuwa Ancle Fa'iz?"
Yayi harr da idanu ya sake kafeni da irin kallon d'azu, jin furucina

"Wallahi da da natafi, naci alwashin bazaki sake gani na ba, saboda gidadancin da kika nunamin. Amma bayan few days, Kawai Sai naji Ina son waiwayarki kuma. Naga kin canza yau, kina d'an tab'uka abu. Kenan komai da kika yimin rannan kina sane Kenan.?"
Bani da amsa, idan ma a Kwai bazai jiba. shi yasa na zab'i yin shiru.

"Kin a mince zaki jure irin Zaman aure N'a?"
Samun kaina nayi da juya idanu na rausayar

"Zan jure man, tun da na iya jure zafafan bulalanka goma, masu ratsa k'ashi da tsoka."
Sai ya d'an d'aga idanun'sa Sama, mai nuna a lamun ya tuno komai.

"A shefa kin tab'a fad'owa tarko na ko? amma wannan shafar mai ne, idan kika yi saken da kika sake fad'owa tarko na. Kinsan yanzu matsayi uku zan had'a a wurinki da an shafa fatiha.
Malaminki nake, Sannan Ancle,Sai na gaba mijinki." Da hannun'sa yake nuni, ta hanyar lank'wasasu.
"Haka ne?"
'Yar dariya na saka.
Yace
"Zakiyi ta gasken ne"

Ya tattaro, Nutsuwar'sa.
"Ina so ki fad'amin nawa. Zaki buk'ata na shirin auren'mu na biki, domin na tanadeki , banason auren nan ya wuce Wata guda fa. "
Da hanzari, na dubeshi. Duk nasan saboda manufar sa ne,da yake so ya cimma. Wani zafi,naji a k'irjina.
"Ka barshi, na yafe. Ni babu shagalin da zan'yi."

Ya jefa min kallon hadarin kaji.

"Kija Mani zargi ko? to bazai yiyu ba. Bazaki tozarta min aure ba, ko ba kya Sona , kuma ko banason'ki za'ayi shagali irin Wanda ya dace. Kije kiyi nazarin adadin kud'in da zakiyi amfani da shi. Idan na dawo naji. Dole ne , kima saddak'ar."
Shiru nayi, jin zai soma hawa dokin zuciyar'sa da nake tsoro.

Bayan sa'oi cikin kafeni da idanun'nan nasa masu narkar da zuciya.
"Kiyi min magana ko?"
Nace
"Zan fad'awa Kawu Sulaiman, idan na lissafa."
Ya kwaikwayi salon yarda na furta.

"Zan fad'awa Kawu Sulaiman idan na lissafa. To Wai meyasa zaki nuna bam bamci tsakanin ni dashi? Nima ba kawun bane?"
Da nayi shiru, ya tafa hannun'sa a hankali, ya kuma dunk'ule.

"Shikenan 'yar gidan Kawu Sulaiman, Sai naji daga gareki."

Ya ci gaba da lissafomin irin shirin da ya soma na auren. Lefema da Sadaki, da kud'in aure yace rana guda Zai kawo. Kenan Ranar d'aurin aure Kawai za'asa . Yarda yake nuna a fuwa da komai, Sai a zaci, wani auren soyayya za muyi da shi, na an matsu da juna. Bayan nan bana gaban'sa na Sani, ko na sakan na a gogo. Manufar'sa ya d'anawa k'ahon zuk'a.

Fargaba d'aya nidai ta ragemin, shine kar a zal ta fad'amin Ancle Fa'iz ya samu damar yi min cuta ta k'arshe. Shine burin'sa Yana cika ya sakenj, nazo na bud'e faifan Zaman zawarci. A binda nafi tsana Kenan a rayuwata, zawarci.. Jinake yi, har gabana na yankewa ya fad'i idan na tuno.

Nina shirya had'uwata da Nuriyya domin taji labarin da zai kid'imata. Wato na aure na da Ancle Fa'izu. Mutumin da ta k'wallafarai a kan'sa kamar ta zautu, wai yau shi yake shirin aure na. Inda a ke neman'sa yayi b'atan dabo..

Ta kuwa girgiza da jin komai. Nasan baza taji dad'iba, tun da ta nunamin irin son da take masa. Sai dai bani da zab'i face dole na fad'a mata, tun da babbar a miniyata ce dole taji. Ban sanar da ita sirrin komai ba, na dai ce Kawu Sulaiman ya had'a auran, amma ni a fargaba nake.idanunta naga yayi rau rau.

Tace"Sumayya al'amarin ubangiji ya shallake tunanin bayi. Tsakanina dake a wannan lamari addu'a Kawai, to yaya zanyi? bani da yarda zanyi Sumayya."
To nima d'in dabara ta kubce, bani da yarda zanyin da na barmata. Dani da itan da ya sacewa zuciya, duk rukuni guda muke. Babu Wacce ta rabauta da Soyayyar'sa, Sai ni da k'addarar auran'sa ta sauka a kaina.

"Ni haushi kike bani da kike Kiran Wai kina zullumin auren'sa. Kamar wannan zuk'ek'en saurayin za'a nok'ewa auran'sa? Wallahi da motsi a kan'ki. Ke koma ba na gari bane, ke dai ko baki tashi da ribar komai ba, kika tashi da ribar kyawawan fararen yara, ai kin gama da shi. Kasuwa ta tashima ai d'an koli yaci riba".

Ni kam haushi furucin'ta ya bani. Ana ga yak'i tana ga k'ura.
"Inaji ganin jarabarki ta son kyau da fari, Sai kin auri maye, nasan ko Kinsan mayen nema auren'sa za ki yi ".

Tayi 'Yar dariya.
"Tabbas!. Ko zai rink'a lasar kurwata kullum Ina suma na farfad'o zan aureshi in dai irin Ancle Fa'izu ne."

Na jinjina furutanta.
"Al'amarinki Sai dai neman sauk'i Nuriyya, amma ba waraka ba."

"Bani buk'atar warakar Dama"

Tace a daken'ta.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*





📱11
_______ A kwati shida set da kit d'aya Ancle Fa'iz ya had'o min na lefe. Ya zuba abubuwa kuma gaskiya masu tsada fiye da zaton kowa.

A tamfofi Holand manya guda goma ne. Bayan masu matsakaitan kud'i goma. Lesuna masu daraja guda goma ne. Shaddodi da material ma sunyi . Hakanan Takalma da jakunkuna babu masu rangwamen kud'i. Sai a jakar Kayan sarkoki' za'a sha kallo. Duk da babu gold, Sai da aka zab'a a ka darje wurin zab'o k'ayatattun sark'oki na cinyewa, launi launi. Tilas a ce isashshiyar mace da tasan kan sirrin iya ado da kwalliya ta zab'o.

Ni dai Abin yayi matuk'ar d'auremin kai, na yarda ya narkar da kud'i irin haka a auren da yafi kowa sanin manufar'sa da makomar'sa a gaba.

Hajiya Mariya tafi kowa, murnar zuwan aure na, inda tayi ta kod"a lefen tana labartawa ga wad'anda basu gani ba, tamkar kaina farau, kuma k'arau. Haka ma 'yan uwan uwa da ubana kowa Sai Sam barka da Fatan alkhairi.

Sati hud'u a kasa d'aurin auren. An tasheni tsaye an kuma tashi Kawu Sulaiman tsaye da kakana. Domin duk basu shirya ba suma, saboda basu zaci zuwan aurena a tsukin ba. Amma Kawu Sulaiman naga ko a jikin'sa. Murna yake sosai da zumud'in zuwan auren . Kuma dama komai Ancle Fa'izu yace ga yarda yake so a yi a kan aurena da shi, to ta zauna. Shi yayi ta nacin kar a d'aga bikin ma kamar yarda kakana yaso, saboda yasan Yariman nasa, bazai so ba Sam!..

A she kawu Sulaiman yayi tanadin'sa na aure na. Duk da yace min, suna Samun kud'I, shi da Ancle Fa'izu yanzu sosai a kan da a harkar boll, musamman ma Ancle Fa'izu da ya zama shine champion d'in su, duk yafi su Samun kud'i Amma na jinjina komai sosai da yayi min. Hidimar Kayan d'aki da komai shine mai kaso saba'in cikin d'ari a cikin 'yan uwa. Cikin hukuncin Allah komai anyi min na fita kunya. Ko saboda maraicina ne hagu da dama yasa kowa ya k'ure kan'sa wurin hidimtamin?

Bayan d'aurin aure na da Ancle Fa'izu da safe naji komai ya fice a raina. Jikina yayi sanyi, domin na tabbatar na Shiga hannu, Sai yadda ta kaya dani kuma.

A cikin wannan yanayin, Ina cikin k'awayena uku, da 'yan uwa Ancle Sulaiman ya turo yana

Please Login or Register in order to submit comment