Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun da ba koyon nayi ba"

"Kina Sha'awar koyon tuk'in mota?" Yace bayan ya rage sautin music d'in da yake tashi da hannu guda, guda kuma yana kan sitiyari yana d'an jujjuyashi.

Nace "Wallahi Ina Sha'awar driving."

Yace "To kuwa kin samu. Bari Muje filin koyon tuk'i na soma nunamiki daga yau." Ya juya kan mota, ya canza hanya Sannan ya k'ara speed, Sai gamu a babban wani fili babba, har da Wata mata ma da mijinta, Itama tana koyo.

Ancle ya nunamin komai a hankali, da yarda zan yi komai. Kamar wasa ya bani kan motar, ko tsoro bai jiba, yace na jarraba, amma yana kusa dani a gefena. Kafin na soma yace" Sai kin sa nutsuwa sosai fa, kuma ki cire tsoro, idan ba haka ba, zaki jima baki iya ba."

Tiryan Tiryan da na bi shawarar Ancle na kuma bi yarda ya nunamin komai, Sai gashi Ina tuk'in motar sannu a hankali. Sai da ya sani nayi round biyar na tafkeken filin wurin.

K'arshe yace " Sumayya, Stop the car."

Da na tsaya cak, yace.

"Kin burgeni gaskiya. Nasan duk in da muka sake yin fita uku ko biyar zaki iya mota. Abinda ya rage Kawai zai rage miki, hawa titi da lunguna, kinsan Shima training d'insa, dabam yake da na filin wuri irin wannan. Yanzu ki mai damu gida."

Na zaro idanu "Daga koyon farko? baka tsoron na tintsirar da kai a hanya, ko na yasheka a wani sak'on?" d'an Murmushi Kawai yayi, bai tanka ba, ya karb'i kan motar.


*******

Tun daga ranar kullum Sai mun fita a mota nida Ancle Fa'iz saboda koyamin mota. Mu kanyi yawace yawace kuma sosai a mota, bayan mun gama da komai. Bantab'a Samun farin ciki ba, zuciya ta ta rink'a haske tun da na auri Ancle, ba kamar na lokacin. Domin mun sake da juna da hira da annashuwa fiye da ko Yaushe. Amma dai har lokacin bansan matsayi na ba wurin Ancle Fa'iz. Ko da wasa banga alamun Wai Sona a tare da shi ba, duk da kulawar da yake bani fiye da baya, da kuma hira ta nishad'in da Mukan yi.

A k'arshe dai nike Jan mota na fita damu na dawo da Mu. Har takai ma yakan bani mukullin motar na fita, ni kad'ai a cewar sa, da haka zan k'warance. K'iyayya sosai kuma mai zafi, na ganta a wannan k'arni, tasu Momi da 'ya'yanta, amma nayi biris.

Da muka koma makaranta, Ancle ni ya bawa mukullin motar nake zuwa makaranta da ita. Shi ba kullum yake hawa, bai fi a Sati sau biyu ko d'aya ba. Domin idan ba wuri mai nisa bane, ya gwarace ya hau babur. Shi yasa motar kamar tawa. Idan Zai hau Sai dai ya karb'i mukullin a hannu na.

Nan ma, Ina wuta a jefani. K"iyayya ta ninka ta baya. To na lura Momi, kamar batason b'acin ran Ancle Fa'izu ma.Domin ran nan na gaji da fitintunin da suka yawaita Saboda hawa motar Ancle Fa'iz. Na Shiga d'akinsa nayi sauri na ajiye masa mukullin motar, na fito da niyyar na Shiga motar haya. Ashe Ancle ya ganni, Sanda na a jiye. Ya d'auko da sauri ya biyo ni, in da ya kira suna na na tsaya cak a tsakar gida. Yace "Banace kibar mukullin motar ko yaushe a hannunki ba? Me kike nufi da ajiyewa? Kina nufin motar haya zaki Shiga? Kuma idan zan hau, ai Ina yi Miki magana ko?"

Karab a kunnen Momi, dake shirin saukowa daga bene Dama jin muryoyin mu, ya Sata saukowar.

A fusace tace "Wai Fa'iz, motar nan kan ka ka sayawa ko Sumayya?"
Nan naga fuskar Ancle ta d'an sauya, zuwa ga yanayin jin zafin furucin Momi, amma a tausashe yace

"Momi ko kaina na sayawa, ai kamar iyalina na saiwa. Guntun gatarinka kuma ai yafi sari, ka bani. Rufin a Siri ce motar gida, domin tafi Shiga motar haya sau dubu ni a wurina." Nan naga Momi tayi shiru ta kasa mayar masa da martani. Ya Mik'omin mukullin motar na amsa a tsorace. Domin kuwa Momi tana da k'arfin iko kan d'anta da zatashi, yayi duk a binda taga dama. Na lura, a Kwai dai a binda yake taka mata burki a yanzu.

Kwana biyu rak da faruwar wannan, Ina zaune da yamma Lis, Ina karatun littafi, gefe a hannu na biscuit ne short bread, Ina ci a hankali. Saye nake da Kaya English wear masu kyau, masu a don fari da bak'i na nad'e kaina da bak'in yanki nayi rooling d'insa, gashin kaina da nayi parking ya fito tsakiyar rolling d'in da nayi.

Khalifa ne tsidim ya fad'omin falon, babu ko sallama. Bai tab'a shigowa ba Sai ranar

"Ina mukullin mota?"

Yace dani yana shigowa.
Na dubeshi a hassale.

"Wace motafa?"

"'Kuji mu da 'yar rainin hankali, a kwai Wata mota, bayan ta yaya Fa'iz?"
NayI masa kallon tara saura kwata, na bawa banza a jiya, na ci gaba da karatun littafina.

Ya kunnu sosai "Wani salon wulak'anci kika fito da shi na share mutane? Wai kin samu rana har da baje shanya? . Na d"aga masa hannu

"Kaga Khalifa, ja tsummar rayuwarka ka b'acemin da gani. Bazan bada mukullin ba, Sai naji shak'a na suma na farfad'o tukun. Baligi kamarka a ce bakasan Hak'k'in Shari'a ba, ka shigo min d'aki kai tsaye babu ko sallama,Sai kace ba d'an musilmi ba."

A harzuk'e kamar ya kaimin naushi yace "Ank'i a yi sallamar, gidan ubanki ne.?" Yana fad'in haka Kawai naga ya fad'amin d'aki . Tuni nasan aikin gama ya gama, domin mukullin kuwa ya d'auko, saboda a kan teburin mudubi na a jiye. Ya fito rik'e da shi Yana karkad'awa cikin jin Isa . Ya. jamin tsaki ya Fice.
Na dad'e zuciya ta tana ta tafarfasa saboda d'iban albarkar da Khalifa yayi min. Bayan gasa min magana, ya shigemin uwar d'aka sirrina yayi bincike saboda mukullin mota. Naci alwashin duk runtsi zan hak'ura da motar nan na zauna lafiya.

Ancle Fa'iz yana shigo min, ko zama bai yi ba yace "Waye ya fita da mota, banganta ba a farfajiyar gida?
A tak'aice banja da tsayi ba, nace "Khalifa ne"

Wani irin kallo Ancle yayi min kafin yace
"A wani dalilin zaki bashi mukullin motar? to karki sake bashi, na fad'a Miki."

Fargaba ta afkuwar rigimar da bansan iyakacin ta ba, da kuma ni zan zama a bar zargi, shi yasa na marairaice nace "Haba my Ancle, d'an uwanka nefa Khalifa, smma a ce bashi da isar amfanarta?"

Yace "Domin yana d'an uwana Sai a kace wajibi Sai yayi iko da a bina? Kuma babu izinina? For what reason?.

Zan ci gaba da lallashin sa, ya d'agamin hannu.

"Sauraramin Sumayya, babu ruwanki. Ya numfasa Sannan can yace "Wannan yaron Khalifa bashi da mutunci da kike gani. Wai ni zai dubi tsabar idona yace Wai ba girma na bane a ce matata tana hawa motata. Kenan nine dai dai da shi, da zan hau mota ya hau mota? to Wallahi bai isa ba, zai zo ya sameni Sai na Sab'amasa."

Duk yarda naso na lallashi Ancle gudun afkuwar rikici, bai ma tsaya ba, ballantana ya saurareni, domin ya hau taken nasa , Sai yarda hali yayi. (Zuciya). Na dafe kaina cike da fargabar a binda zai biyo baya kuma.

A daren ranar dai Ancle Fa'iz yazo ya sake dank'amin mukullin motar. Baice komai ba, kuma naga ransa a b'ace . Gudun kar na k'ara masa damuwa yasa na jinkirta fad'a masa k'udirina na hak'ura da motar, Sai washe gari.
Amma kafin nan, Momi ce ta katsemin hanzari. Shigowa tayi Itama kai tsaye falona tana huci.

"Munafuka, algunguma, kara da kiyashi. Ungulu da kan zabo. Dama masu iya magana, sunce idan belbela ta samu dama Sai tace masar ne garin ubanta. To Wallahi ba ki isa kisa 'ya'yana gababa. Tun da suke ko musayar yawu basu tab'ayi ba, amna sanadinki Fa'iz yaci mutuncin Khalifa gaya, akan mukullin motar da ba daga gidan ubanki kika zo da ita ba. To bani mukullin motar,ni na k'wace, ki turoshi nima yaci zarafina ya karb'a. Idan bakiyi haka ba, to baki isa k'aramar shaid'aniya ba ma kanwa kuma uwar gami."

Momi tak'i tsayawa taji mafarin komai saboda rashin a dalci. Iya cin zarafi tayi min a ranar, bayan ta karb'e mukullin motar. Bansan iya adadin zagin da a kayiwa ubana ba a gidan nan. Ubana da yake kwance cikin kabari baisan hawa da sauka ba. Wannan shi yafi komai soya min zuciya. Na kifa kai na Shiga razgar Kukan da bantab'ayin sa ba, tun da nazo gidan.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*



📱21
_______ Menayiwa Momi? ta Ina na kuskurota?.menene Laifina a kan mota kuma? Tambayoyin da najerowa kaina Kenan, bayan naci kuka na k'oshi. Kyautatawa da biyayya,ninninkawa nake a b'angaren Momi fiye da kowa, saboda son da nakewa d'anta. Hakan yasa take da Wata daraja ma mai tsada a Zuciyata. Amma gashi duk a binda nake, Momi bata k'aunata. Nina lallashi kaina, saboda bana so Ancle Fa'iz yazo ya tuhumi sanadin damuwa ta, kuma ni bazan iya duban cikin idanun'sa nace Momin sa ta b'ata min ba. Bazan iya ba.

To takaicin bi da bi, ya rink'a zuwar min, kamar Wacce iyaye suka yiwa baki suka ce Jeki kin gani. Domin bayan fitar Momi da kamar awa d'aya, Sai ga Ancle Fa'iz ya shigo min Shima, ransa a b'ace. Na dad'e banganshi cikin b'acin rai ba, irin haka, ko nace ma ban tab'a gani ba. Kuma wuri ya zauna yayi shiru Kawai. Na lura bai kula da yanayin damuwar da nake ciki ba. Na daure nace "Ancle Fa'iz lafiya kuwa kake? Wani a bu yana damunka ne?

Ya d'aga idanu a hankali, ya dubeni.

"Zuciya ta ce take ta kai kawo, tana ta jimamin yarda na rasa matsayi tashi guda a wurinki, da zan baki umarnin kiyi a bu, amma ki k'iyi.
Ya numfasa tukun ya d'ora da.
"Nace kar ki sake bawa Khalifa mukullin mota, amma shine kika bashi. Yanzu na shigo na ganshi yana gyarawa mota parking, da alamu dawowar sa Kenan daga yawon da ya tafi da ita. Zamana kike Sumayya, amma kika fifita farin cikin wani da nawa. Kika zab'i biyayya da kyautatawa ga wanina,da bashi da gurbin da ya can can'ta kiyi masa haka Sama dani. Why?" Ya k'arashe furucin cikin kasalalliyar murya.

Na sake Shiga Kam, sabon rud'ani. Ta yaya zan wanke kaina ga Ancle ba tare da kawo laifin Momi da na tabbatar ita ta sake bawa Khalifa mukullin motar da ta k'wace a hannu na ba. Tabbas, ko zan sanar da Ancle Sai ta hikima da tausasa kalamai, saboda kar na fito da laifin Momin sa a sarari, da ko bai nuna jin zafi ba, ni bazan ji dad'i ba. Sai dai ina bud'e baki zan soma magana, ya katseni a harzuk'e.

"Kar kice dani, komai,domin bazan yarda ma dake ba."
Ya tashi ya Fice a binsa,bai kuwa sake lek'oni ba a ranar. Hawayen da na tsayar, su na ci gaba da zubarwa. Da nawa zanji a cikin'su. Momi zargina take, Khalifa ma, haka, ga Uban gayyar ma, yazo min da tasa tuhumar. Kuma ta Ancle tafi tayar min ma da hankali. Ji nayi Sam,bazan iya juriyar da nake zato zan yi ba,na jure duk rigimar da zata tunkaro, saboda Soyayyar da nakewa Ancle Fa'iz da tasa nake nacin son zama da shi, duk da bai nuna a aikace, ni matar'sa bace, face 'yar tayin zama Kawai.idan so cutane,to hak'uri ance magani ne. to zan d'au hak'urin kawai,domin na zauna lafiya. Bazan yarda da k'uruciya ta ba, a gadar min da ciwon zuciya.Tak'i kad'an zan k'ara, idan naga a bin yaci tura, zan bar musu gidan'su Kawai. A she kuwa gab, yake da yaci turar. Wasa ma farin girki a she, matsala na gaba.

Dai dai k'arfe uku na dare, Khalifa ya sad'ad'o ya shigo min d'aki, bisa ga tsautsayi na sabon da nayi na rashin rufe k'ofata da mukulli daga ciki, Sai dai na tura ta Kawai, ga kuma fahimtar da Khalifa yayi, Ancle Fa'iz baya kwana a wurina. Wannan shi yasa ya samu nasarar yin a binda ya k'udurta a sauk'ak'e. Fitila ya fara kunnawa da ya shigo, haske ya gauraye d'akin Sannan ya ta sheni, ta hankar bubbuga filon da na d'ora kaina a kai. A tsorace na tashi. Na sake tsorata sosai da ganin Khalifa a kaina ya zubomin idanu. Na bazama na jawo softcotton blanket da na a jiye gefena, saboda irin Kayan baccin dake jikina na shan iska ne, saboda zafin da ake yi, a tsukun.

"Lafiya? Khalifa me ya kawoka d'akina cikin dare? Cikin hankalinka kuwa kake?

Ya zaro min idanu, irin na tsoratarwa.
"Na fikima wadatar hankali Sumayya. Ramuwa ce Kawai ta kawoni d'akin nan, saboda wai saboda ke Yaya Fa'iz ya cimin mutunci, cin mutuncin da ba'bu mahaluk'in da yayi min irin'sa. Nasan kuma ke kika zugoshi, to Wallahi kinyi kuskure babba,domin ni ba a takani a Sha!."

Wani irin tsoro ya kamani sosai, domin zatona Wata illar zai min, ko ya hallakani. Muryata na rawa nace.
"Khalifa, amma Sai cikin dare za'ka yi ramuwar? idan gari ya waye Kayi min komenene, amma don Allah banda yanzu."

Yace "Ina! ai Wallahi baki isa ba, yanzu zan rama. Ramuwar gayya tafi ta gayya ciwo. Ciwon da naji a zuciyata Sai na ninninka miki irin'sa. Ki bani had'in kai, na 'yan mintina ne zan idar da nufina na tafi, idan kuma ba haka ba, zan k'ulla miki sharrin da babu mahaluk'in da zai iya wankeki a duniya? sai kowa ya tsaneki, ni da yaya Fa'iz Kawai kika had'ani, ni kuma Sai na had'aki da kowa kin zama a bar k'ya mata."

Tuni na d'au hasken me Khalifa yake nufi,na kuma girgiza da mummunar manufar'sa, da ya rik'a a matsayin ramuwa. Nace

"Wallahi Khalifa bazan aikata aikin ashsha ba, ban aikata ma a baya ba, Sai yanzu da nake da nauyin hak'k'in aure a wuyana? ni ba halina bane. Na yarda Kayi min kowani hukunci idan kalmar hak'uri bazata ceceni ba, amma banda wannan manufar taka"

Yace "Ai ban baki zab'i ba. Kuma ramuwa fa nace zanyi, kuma ramuwar mugunta ai a binda Mutum kasan yafi k'i shi za'ka yi masa ka huce. Kuma nasan mijinki ma, duk da baya sonki, zai tsaneki ya sakeki take, idan ya sa ni." Yana fad'in haka naga ya nufoni.

Nayi zallo gefe a zabure.

"Wallahi zan fasa K'ara na tara Maka jama'a".

Yace

"Haka na fiso ai ki tara Mana ma mutane." Ya nufoni gadan gadan.

Na kuwa daddage na fasa Wata irin k'ara cikin kad'aitaccen daren. Na kuma fasa ta biyu da tafi ta farko sauti. Sai naga Khalifa ya tsaya cak.!

Ancle Fa'iz ne kuwa farkon shigowa, saboda d'akin'sa yana dab da nawa, dole yafi kowa ji. Da Khalifa bakin k'ofa yaje ya tare, domin kar na fita, Amma ganin shigowar Ancle, Sai yaja gefe guda, ni kuma jin Ancle ya kira Sunana yana shigowa falon da sauri, na antayo daga d'aki, bayan naja wani mayafina dake jikin hunger na lullub'e k'irjina. Yarda na taho karta na nufo Ancle Fa'iz Sai a zaci jikin'sa zan fad'a, Amma Ina zuwa Sai na tsugune k'as a gaban'sa Ina kuka. Ancle naga ya Shiga wani irin rud'u da yaga Khalifa, ya juyo da kan'sa ya dubeni. Ya zuba Mana idanu Kawai, ya dubeni, Sai ya dubi Khalifa kuma. Can yasa hannu ya d'agoni daga durk'uson.
"Ihun me kike yi? Me ya faru? Me yasa naga Khalifa a d'akin'ki?

Kafin na iya amsawa Sai ga Muhibbat,da khairat sun shigo, ai Sai na sake Shiga d'imuwar rasa ta Ina zan fara, saboda kunyar Jama'ar da suka soma taruwa, kuma duk Jinin Khalifa.lokaci guda naga idanun Ancle sun sauya kala, sun yi jawur, Sai a zaci ba'ainihin kalar su fari fat bane, masu bada launin shud'i shud'i.Khalifa kuma Kawai yake kallo cikin sauyayyen Jan idanun.

Cikin tsawa yace masa.

"Me ya kawoka d'akin Sumayya? giya kasha, ko wiwi, ko kuma hodar iblis, fad'amin."

A dake ya amsa."Sumul nake. Kuma idan Ina shan d'ayan su, ai kaine shaidar farko, Yaya Fa'iz."
"Karka fad'amin Maganar banza, idan ka tashi shan, Sani zanyi? Fad'amin a binda ya kawo ka d'akinta, ko nayi Maka illar da bazaka moruba Wallahi."

Bud'ar bakin Khalifa.

"Gayyatoni tayi da kanta. Kuma batun yau ta soma gayyatata ta ba, saboda tace wai baka sauraronta, baka bata lokacinta, irin na mace da Miji yau ma bore nayi mata, nace zan fallasa komai, shine tayi ihu, domin reshe ya juye da mujiya."
Muhibbat ta d'au salati, amma wani sakaran kallo da Ancle ya jefa mata, Sai ta d'inke bakin. Khairat dai bata ce komai ba, illa tagumi na tsantsar damuwa. Da k'yar na samu wani k'ololon a bu ya fad'amin da ya tsayamin a k'ahon zuci, saboda Shiga firgicin jin sharrin da Khalifa ya kallafamin.

"Wallahi Ancle K'arya yakemin. Ina kwance na ganshi a tsaye a kaina....

Khalifa ya katse da sauri.

"Ta d'an a dam za'kiyi min? Saboda kina tsoron hukuncin da zaki fuskanta?
Na sake fashewa da kuka. "Kaji tsoron Allah Khalifa...."
Ya sake katseni."To, tsoronki zanji idan banji tsoron Allah ba? ai tsoron Allan yasa na zab'I na Toni a Siri komai yazo k'arshe."
Shigowar Momi dai dai nan yasa na sake firgicewa, domin nasan al'amari ma ya gama lalacewa. Ga Khalifa ya hanani nayi bayani sosai har Momi ta shigo.K'arin d'imaucewar tawa ma, da na kasa gane gaskiyar sirrin zuciyar Ancle Fa'iz na yarda ko rashin yarda, game da mummunan sharrin da Khalifa ya k'ullamin, domin har Momi ta shigo ta soma magana baice komai ba. Da alamu bayan rud'ani, kansa ya d'auki zafi, b'ararraka caji Kawai yake tayi. Momi ta dubemu Mu duka tace

"Wai me yake faruwa a nan.? Ihu da surutai sun tsoratani da k'yar na iya fitowa, zatona ko b'arayi suka shigo ma, Sai da na tabbatar da muryoyi."

Kafin ma ta rufe baki Muhibbat ta zayyano, Khalifa ya karb'a ya k'arashe har da k'ari. Mugun
Kallon da Momi tayi min banyi zaton zan tsira daga shan maruka ba, hagu da dama, ko kuma saukar mahaukacin duka, irin na kawo wuk'a.

"Biri yayi kama da Mutum, kuma alamu a lamun somin hauka zub da miyau.Tuni na tsinke da al'amarinki dama Sumayya, zaki iya fiye da haka. Wato bayan kin tarwatsamin Zaman lafiyar yara, yanzu kuma kinzo kin gurb'atamin tarbiyyar yarona da na d'ebi shekaru Ina tarbiyya. To Wallahi hukuncin da zan d'auka a kan'ki ba iya ke kad'ai zai tsaya ba, har iyayenki, ko da yake baki ma dasu Sai kakanni, to har tsufansu bazan tausaya ba."

Cikin Kukan da da k'Yar yake fita saboda tashin hankali nace "Momi, Wallahi sharrin Khalifa ne, shine......"
Ta dakamin tsawa."Rufemin baki Munafukar banza,mai bak'ar a niya, da mugun hali, da mugun usuli."
Nan naga Ancle Fa'iz ya dubi Momi a hargitse, da alamun Furucinta ya Sosa masa rai sosai, Kawai ta tsira ne, saboda itan mahaifiyar sace.
Kuka na ya k'ara d'agawa, jin dad'in komai ya tafi yarda Khalifa keso, Shima ya dakamin tsawa.
"Rufemana baki, shaid'aniyar Kawai, haka kurum kin jefani halin halaka."
Ai kafin ya rufe baki, Ancle ya kwasheshi da wani irin wawan mari.Ai bansan Sanda na tsaida kuka na ba. Momi ma baki bud'e tayi tana kallon Fa'iz, haka ma Muhibbat ta wani zaro ido na Mamaki, haka Khairat. Shi kuwa Wanda aka Mara d'in dafe kunci yayi Yana kallon Yayan sa ido yayi tulu tulu, kamar zai rama, saboda k'uncin zuci
A zafafe Ancle yace "Matar tawa kake zagi kana dakawa tsawa? a gabana kuma? Lallai ka Isa tabbataccen Mara kunya, kuma Wallahi Sai na koya Maka hankali"

Nan Momi ta karb'a a fusace "Fa'iz, d'an uwanka Kaci zarafi ka tozarta a kan wannan 'yar iskar matar taka? to me yayi mata ma?ai kome yayi mata bai biyani ba. Wato Sam baka duba ma ga ta'asar da tayi, kai ta anzageta shine damuwarka ko?

Ya aro nutsuwa, da tausar zuciyarsa Sannan ya soma magana.

"Momi idan sumayya shaid'ani yace Khalifa ma shine, domin kuwa k'arfe d'aya baya amo, Sai da a bokin yin sa. Kuma in dai hukunci na gaskiya za'ayi to su duka za'a tuhuma, kuma a hukunta. Kuma in dai har an yarda Sumayya ita ta fara neman Khalifa, to kuma laifin'sa yafi girma, kuma yafi fitowa fili, domin kuwa d'akin Sumayya aka ganshi, ba ita aka gani a d'akin sa ba."

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*




📱22
________ Ga Wanda duk ya dubi Momi, zai ga alamun maganganun Ancle Fa'iz sun Shiga sun zauna Zuciyarta, amma saboda zafina da take ji, da tsana Sai ta sake tasowa Ancle Fa'iz da fad'a da bantab'a ganin shi tana yi masa ba cikin 'ya'yan'ta. Ina ganin kuma Muhibbat tana yiwa Momin rad'a a kunne da Ancle Fa'iz ya kau da kai. Tace a zuciye.

"Kar na sake jin ka dangantawa d'ana laifi irin na wannan banzar matar taka, rore roren tsiya. Yaro na Khalifa kin tsatstsene ita ta yaudareshi, idan ba haka ba me yasa da bai yi ba.? gaba d'aya ma Fa'iz ka fa canza daga d'an da na Sani, mai kishin 'yan uwan'sa da son su da tsananin son Momin'sa."
Ya dubi momin, cikin sanyaya murya.
"Ina nan Momi a sanin da kika yi min, fahimtata dai kika kasa yi." Ta girgiza kai.

"Ban yarda ba, Fa'iz, k'iri k'iri fa ka gani, amma ka zama makahon k'arya. Muhibbat tace min kasamu Khalifa da Sumayya, suna aikata fasadi, amma kak'i ganin laifin Sumayya Sai na Khalifa, har marinsa Kayi. Hakan na nufin a dalci Kayi, kuma ka damu da naka Kenan?"
Ai Ancle Muhibbat naga ya zubawa idanu cikin wani irin fushi, cikin tsawa yace mata
"Ke Yaushe kika zama shahararriyar Mak'aryaciya ban Sani ba?" Wata irin mangara ya kai mata, Momi ta Kare ta matseta a jikinta.ita ma ta ruk'unk'ume uwar.

"Kar ka kuskura, ka tab'amin yarinya Wallahi, domin ta fad'i gaskiya."
Idanun'sa suna nan Jazur, basu canza ba, ya fesar da wani huci mai zafi, na jin ciwon rashin damk'ar Muhibbat, na tabbatar da Sai ta d'and'ana kud'arta. Dai dai nan a ka soma Kiran sallar assalatu na farko.

Ancle yace
"Momi,k'arya Muhibbat ta shirya Miki. Ni idanuna ba suga komai ba. Da naji ihun Sumayya da na Shiga ma basa kusa da juna. Wannan kuwa ko kusa bai kai hujjar yin zargi ba in da adalci. Shaidar zina babbar al'amarice Momi, ko a musulunci sai an samu shaidu hud'u, kuma Sai sun gani ra'ayal aini. Ko uku ne, suka gani, d'aya yace bai gani ba, to sai sun Sha hukuncin bulalai. Kenan a Kwai had'ari ma ga ayi wa Mutum irin wannan zargi, babu shaidu. kuma ni ina da hujjoji uku da ban yarda ba. Na farko Me yasa Khalifa daya ce bore yayi wa Sumayya, domin tona a siri mai yasa bai riga Sumayya ba? ai Sai ya fito cikin daren ya tashi kowa ya Sani, amma Ihun Sumayya na neman a gaji, shi ya fallasa komai. Sannan na biyu a d'akin Sumayya fa a ka ganshi dumu dumu. Ko a Shari'a shine jagoran laifi. Na uku da kunne na naji hirar sa da abokin sa Tajo a k'ofar gida baisan na dawo ba, zan fito na dakata da naji irin hirar. A cewarsa wai Sumayya ta zame masa matsala na katangar Samun aikin a counter a kamfanin su Salima, saboda auren ta da nayi, nak'i mai da kai ga auren Salima, ballanta na ya samu aiki. kuma wai sai ya shirya tuggun da zan saketa. Tajo Inaji yana tinzirashi. Dama a bokan, naka duk baragurbine, shi yasa kak'i kintsuwa. Sam banyarda da kai ba Khalifa. Ko kotu a kaje Wallahi bazan bi bayanka ba, bayan Sumayya zan bi. Nine na farko daga cikin witness d'inta ko high court za'a."

Momi kuwa

Please Login or Register in order to submit comment