Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma sai ta kasa shirin a gabansa sai daya dakin
ta shiga ta karasa shirinta ta fito cikin doguwar riga.
Tsarki ya tabbata ga Allah, wannan yarinya da
kyau take ga iya diresin kamar aljana. Abun da
Haidar yake fada kenan a zuciyarsa. Har ta zo
gabansa ta durkusa ta ce, "Sannu da zuwa yaya." Ya ce, "Yauwa jawahir kin ci abinci? Ta girgiza kai
ya ce, "To me kika ci.?
Ta ce, "Yogourt da ragowar naman daxu. Ya ce,
"Shi ne zai rike miki ciki? Me ya sa kike son sakaci
da cikinki ne?
Me ya sa baki girka kin ci ba.?" Ta ce, "Ai gani na yi ba ni kadai ce a gidan ba.
To in ban da abinki jawahir ke da gidanki sai an
girka an ba ki? Ke da na san ki da kyankyami, za ki
rinka cin abincin me aiki ne?" Ta girgiza kanta, ya
ce,
To kin gani ki rinka girkinki kina ci kin ji ko.
Yanzu me za ki ci, ko za mu fita muje mu sayo wani
abin ne ko kuma mu je gidan abinci.
Ta girgiza kai, "A'a zan girka wani abu yanxu
Ya dube ta ya ce, "Dare be yi miki ba. Ta ce, "A'a ba
komai. Tun da ta soma magana yake jin wani abu, zil-zil yana tsarga masa don jin dadin muryarta da
shaukin begenta. Ya mike ya fita jikinsa a sanyaye
kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya fito ya hau
samansa sai ya tarar da Kausar a kwance a kan
gadonsa tana nishi. Ya isa kusa da ita da saurinsa
ya ce, "Lafiya?" Menene ya faru? Ba yanzu na barki a dakinki ba. Ta ce, "Wallahi fama nake yi da ciwon
mara tun safe daurewa kawai na ke yi ka daure ka
kaini asibiti yanzu."
Haidar ya ce, "Yanzu ya dace mu fita asibiti mu bar
jawahir ita kadai a gidan? Kausar ta ce, "Haba
Haidar me yake damunka ne me zai same ta, ba ga masu aiki nan a gidan ba, ko ka fi so ni na kwana
ina murkususu?"
Ya ce, "To shikena tashi muje. Lokacin da suka fito
don tafiya sannan jawahir ta fito falon za ta shiga
kicin wannan shi ne karo na farko da jawahir ta ga
Kausar ita ma Kausar ta ganta. Ba su yiwa juna magana ba sai Haidar da ya ce zamu fita yanzu
zamu dawo.
Jawahir ta shiga kicin kamar ba ta ji me yake cewa
ba, suka fice jawahir ta zauna a babban falo ta
kunna kallo, salkamar da taji ce ta sata saurin
juyowa. "Lalala Bilki yau ke ce a gari?" Gaskiya ba ki da alkawari, ni na za ta ma kin manta da ni."
Bilki ta ce, "Haba jawahir ya zan yi na manta da ke,
kin san tun ranar da muka zo nan gidan Haidar ya
kore mu nake jin tsoron kada nazo na jawo miki
wata fitinar. To sai da na ji labarin aurensa na so na
zo sai na ji tsoron kada ya cire min kafa daya shi ya sa na hakura na fasa zuwa.
Jawahir ta ce, "Yanzu ya aka yi kika zo?
"Uhm ke dai bari, tare muke da direba munje gidan
kawar Hajiyarmu kusa da ku ne na ga ba zan iya
wuce gidanki ba.
Jawahir tayi murmushi, "Amma gaskiya na gode na kuma ji dadin zuwanki, don akwai labari da labarai
ma sai dai ga shi dare ne da za ki daure da kin zo
min da rana mun wuni muna hira.
Bilki tayi ajiyar zuciya ta ce, "Kina ganin in na zo
babu wata matsala ko Haidar yana nan."
Jawahir ta ce, "Ba komai wallahi ba zai ce miki komai ba.
To shi kenan jawahir na fita kin ga dare ya yi sai na
zo din
"Okey Bilki na gode don Allah ina sa ido kada fa ki
ki xuwa."
"Insha Allahu zan zo" Tayi sallama ta tafi. Jawahir ta soya indomie da kwai ta gasa masa kifi
ta hada masa lemon kwakwa da madara ta zuba a
jug ta cilla masa kankara ciki ta jere komai a kan
tebir din falon ta shiga sashenta ta ci na ta ta watsa
ruwa ta wanke bakinta ta je ta yi kwanciyarta. Sai
goma na dare su Haidar suka dawo. Kausar ta wuce dakinta Haidar kuwa ya nufi tebur din da
abinci yake don yunwar da yake ji tun break din
safe da ya yi a dakin jawahir.
Ya bude komai ya ci ya yi kat, ya rinka shan lemon
kwakwar nan yana nishadi a kasan zuciyarsa
kuwa sai shiwa jawahir albarka yake. Da ya gama ya murda kofar dakinta yau ma a rufe gam, ya
koma dakinsa yau ma ya kwanta yana murkususu
da ya rufe idonsa kyakkyawar surar jawahir yake
gani. Ga wata muguwar sha'awarta da tayi masa
mugun kamu haka ya rinka juyi yana murkususu.
Sai da asuba ya tashi ya yi alwala ya yi Raka'atainil Fajri ya yi ta karatun Alkur'ani ya yi addu'arsa ya
shafa. Ya dade yana lazimi sannan ya sauko falon
kasa ya zauna ko zai ga jawahir ta fito ya samu ya
ganta ko zuciyarsa ta lafa da tsananin radadin
kaunarta.
Ya yi sa'a kuwa ta bude kofarta ta fito tana sanye da abaya da karamin farin hijab, da ya sha adon
bakin les, tana rike da carbi a hannunta ta yi kyau
kamar ita ta yi kanta.
Duk motsin da tayi sai komai na jikinta ya motsa.
Yanda jikinta yake girgiza shi yake dada motsawa
da Haidar sha'awarta. Jawahir ta yi mamakin ganinshi a falon, don haka
ta karasa gabansa tayi saurin xubewa ta gaisheshi.
Ta mike ta nufi kicin idonsa na kanta.
Ya ce, "Jawahir" Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya
ce, "Don Allah idan break za ki hada ki hada da
mu."(HMMM GASKIYA JAWAHIR AKWAI HAKURI DON NA TABBATA A IRIN KISHI NA MATA BA KOWACCE XATA IYA GIRKI TA BAWA KISHIYAR DA ITA BA XATA YI BA).
.
(((((((SALON SO))))))
:
(((((PART 26))))))
:
. Ta yi dan dum kamar ba za ta yi magana ba sannan
ta ce, "Kai da wa?"
Ya ce, "Ni da Kausar"
Ta ce, "Ko a musulunci dakin da ka kwana nan ne
yake da hakkin yi maka abinci. To amma tun da
hakan ba ta samu ba ni ya zama dole na hada maka, amma ita kuwa wadda ka ambata ban ga
dalilin da zan girka mata wani abu na ba ta ba, don
ba zamanta na ke yi ba, kuma ni na ajiyeta ba.
Kafin ya ce, wani abu ta juya tayi komawarta dakin.
Jawahir bata fasa hada break din ba don idan tayi
kamar za tayi fushi sai ta tuno abubuwan da Anti Maryam ta gaya mata to sai ta daure tayi ko ba
komai yanzu tana ganin nasara don kulawar da
Haidar yake yi mata ba kaman a farkon aurensu ba.
A babban falon ta shirya masa komai ta koma daki
ta tsala wanka ta yi kwalliya ta gani a fada da wani
tsadadden material ta yi kyau har ta gaji da kyan, ta sha adon gwala-gwalai kamar ka sace ka gudu.
Kamshi ne yake tashi a kowacce kafa ta jikinta. Ta
fito falon Haidar yana bisa tebir yana break shi ma
ya sha tsantsarerren adonsa da shiga ta alfarma.
Yana hango jawahir ya fara sambatu a zuciyarsa,
"Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi kyakyyawar halittar yarinyar nan, ko yaushe zan
ga fuskar da zan latsa jikin yarunyar nan, har na
gani gado daya da ita? Kai wannan rana da na
suma dan dadi Tina daya daga cikin 'yan aikin
Kausar ne ta zo ta
kama kafar benen Haidar za ta hau, jawahir kuma sannan ta fito daga sashenta shi ne ta doka mata
tsawa, "Ke zo nan
Tina ta taho jikinta na rawa ta durkusa kasa a
gabanta, jawahir ta ce, "Uban wa ya ba ki ikon
hawa benen nan? Ko dakin sa'anki ne a ciki? Me za
ki yo? Wa ya aike ki?
Tina ta ce, Anti ce ta ce na hau na share.
Jawahir ta ce, "Wacece Anti?"
Tina ta ce Kausar Jawahir ta ce, "Ke dabbar ina ce
ko na ce
mahaukaciyar ina ce da za ki zo ki haye dakin megida?
Ko ku hudu aka auro ne ban sani ba? Tina ta
girgiza kai, "To wallahi ki sani wannan ya zamo na
farko na karshe ko falon nan kada na kuma ganin
dayar ku ta zauna a ciki, da kun shigo ku yi wajen
uwar dakinku ko kuma ku yi zamanku can bangaren masu aiki don ni ba zan yarda da
kwashe kwashe da tarkace ba.
Tina ta ce, "Ki yi hakuri Anti zan kiyaye gaba."
Jawahir ta ce, "A'a ni ba Antinku ba ce, ga Antinku
can wadda ta kwaso ku ta zo ta zube ku. Ya kamata
a ce kuna gidan mazajenku kuna bautar aure amma ga shi kuna zaune kuna bautawa wata
katuwar banza, don kwadayi, wato kun fi
kwadayin abun duniya da rahamar Ubangiji ko?
Tina ta girgiza kai, jawahir ta ce "To ki gayawa
ragowar 'yan uwanki ku yi kokari ku fito da mazaje
a yi muku aure ku je can ku samu 'yancin kanku ku yi wa Allah bauta.
Tina ta rissina tana cewa, "Mun gode Anti insha
Allahu za mu gabatar da masoyanmu. Jawahir ta yi
mata izinin tafiya ta fita. Haidar yana zaune yana jin
su ko ba komai
zuciyarsa ta yi dadi da kalaman da ya ji jawahir tana yi yana alfahari da hankalinta. Gefe daya kuma
yana tunanin ko dai jawahir ta fara son sa ne don
ya ga kamar tana kishinsa, to Allah ya sa haka ne.
Kausar ta bude kofar sashenta ta fito tana yamutsa
fuska ta dokawa jawahir harara ta nufi wajen
Haidar tana yamutsar fuska irin ta marasa lafiya ta ce, "Darling cikina fa ya ki daina ciwon kuma sai na
rinka jin kamar yana harbawa ko cikin wata biyu
yana fara motsi ne?
Haidar ya kamo ta ya zaunar da ita kan cinyarsa,
"Kausar
kada fa ki wahalar min da baby, ba kya son cin abincin ne yunwa ce take sa shi motsin dole bude
bakinki na ba ki, ki ce. Ta bude ya zuba mata,
"Yauwa kausar ko ke fa ai gwanda ki ci.
Jawahir ta ji wani katutun bakin ciki da kishi ya
tokare mata makoshi, lallai ma tsanar da mutumin
nan yake yi min ta kai tsana, duk tsawon lokacin da na dauka a gidansa ya kasa kusantata amma daga
zuwan wata har ya ba ta ciki, wallahi ba zan yarda
ba sai dai a yi wacce za ayi."
Ta nufi gun su gadan-gadan a lokacin da Haidar ya
sa mata cinyar kaza ke nan a baki jawahir ta
tankwabe tare da dankar wuyan Kausar ta ce, "Wallahi sai ta yi amansa, ai ni ba baiwarta ba ce da
zan yi mata girki ta zo tana ci."
Haidar yayi yayi ta sake ta taki shi kuwa ya fitar da
hannu ya shara mata mari. Jawahir ta yi saurin cika
Kausar yayin da ta dafe kuncinta zafin marin ya
gigita ta inda ta rarumi faramtin tangaran me nauyi ta kwadawa Haidar a gabansa tuni Haidar ya dafe
wajen ya kwalla kara ya zube kasa.
Hankalin jawahir ya yi mutukar tashi da ganin halin
da Haidar yake ciki sai ta sa kuka na shiga uku
yaya, Yaya don Allah kayi hakuri wallahi ba da
sanina na yi maka ba, Yaya ka yi hakuri ka tashi na tuba na daina ba zan sake ba. Kausar kuwa kofa ta
nufa ta kirawo megadi da yaron gidan suka kama
shi suka sa shi a mota ta shiga ta tuka motar suka
tafi asibiti. Aka kama shi aka shigar da shi daki
suka tsayar da Kausar a waje can likitan ya fito ya
ce ta je ta nemo dan uwansa namiji. Kausar ta mike ta shiga motarta ta yi gidansu Haidar.
Ta yi salllama falon inda ta samu Abbansa da Anti ta
durkusa ta gaishe su ta ce, "Daman Haidar ne ba shi
da lafiya har an kwantar da shi a asibiti shi ne na zo
na fada
Cikin hanzari Abba ya mike ko direba bai jira ba ya fita ya hau motarsa ya tafi inda Kausar ta shiga tata
motar ta rufa masa baya. Anti ta ce mata, "Duk halin
da ake ciki ta yo mata waya ta gaya mata. Ta ce to.
Lokacin da su Abba suka isa sannan Haidar yana
bacci don haka Abban ya wuce office din Doctor,
likita ya mike tsaye ya mikawa Abban hannu suka gaisa, sannan suka zauna. Likita ya ce, "Daman
Alhaji larurar da take damun Haidar ce abin babba
ne. Cikin firgita da dimauta Abban ya ce, "Me ya
same shi? Likitan ya ce, "To dai a bincikenmu mun
gano
buguwa ce mai tsanani ya yi a gabansa wadda har ta jawo masa mutuwar gabansa, don ba shi da
wani kuzari da zai iya kusantar mace bare ya iya
biya mata bukatarta. Abban ya dafe kai tare da
fadin, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yanzu shi
kenan
dana ya nakasa? Likita me ya jawo masa buguwar.? Likitan ya ce, "Kada ka damu Alhaji za mu yi bakin
kokarinmu na ganin ya samu lafiya ya dawo
normal.
Abba ya yi masa godiya ya koma dakin da Haidar
ya ke ya
zuba masa ido yana bacci. Jawahir kuwa tun bayan tafiyarsu Haidar asibiti ta
kasa samun sukuni sai kuka take yi tana tunanin a
wane hali Haidar yake yanzu, ta kasa samun
sukunin zuciyarta. Kawarta Bilki ta yi sallama ta
shigo, "A'a lafiya jawahir na ganki haka?
Jawahir ta ce, "Kyale ni Bilki na bi ta dokin zuciya na aikata abin da zai dame ni. "Me yake faruwa ne?"
Jawahir ta kwashe komai ta gaya mata. Bilki ta ce,
"Wallahi ba ki kyauta ba, don yanzu Haidar son ki
yake yi sosai da kin sani ba ki yi masa wannan
dibar albarkar ba, don ba mutunci ba ne mace ta
kai hannu kan mijinta da niyyar duka. Tace, "Uhm kyale ni Bilki zafin marin ne ya gigita ni
ban san lokacin da na kwada masa ba, karar da ya
yi ce ma ta dawo da ni hayyacina."
Bilkisu ta ce, "Yanzu ba surutu za ki tsaya ba tashi
mu je asibitin ki ga yanda jikin nasa yake. Ta ce,
"Kai anya kuwa na je?" Ta ce, "Kwarai ma kuwa, ai tashi kawai mu tafi.
"To ai ban san asibitin da ta tafi kai shi ba.
"To bari na gano idan direban ya dawo sai mu
tambaye shi wanne asibitin ne, ta yi waje. A can
asibiti kuwa Abba ya koma gida Kausar tana
waje, Haidar ya farka Faruk ya gani a gefen gadonsa a zaune, Faruk ya ce masa, "Sunnu ya
kake jin jikin naka? Ya ce, "To da sauki zan ce,
"Haidar ya yi tsu can ya ce Faruk ina jawahir?"
Cikin mamaki Faruk din ya ce, "Me za ka yi mata?
Haidar ya ce, "So nake na san halin da take ciki."
"Me ya same ta?" In ji Faruk, Haidar ya kwashe yanda abin ya faru ya gaya masa, Faruk ya ce, haba
Haidar me ya sa za ka mare ta? Ai kai ma ba ka yi
dai-dai ba. Wallahi yanxu jawahir tana tsananin son
ka tun da take yi maka duk abin da kake so, kuma
take tsananin gudun bacin ranka, ga shi har ta
kasa jure kishinta ta nuna karara. Haidar ka rage zafin zuciya in ba haka ba wata ran zai kai ka ya
baro ka.
Haidar ya ce, "Ai yanxu ya ma kai ni ya baro din, ni
dai don Allah so nake yi ka je gidan ka gano min
halin da take ciki inda hali ma don Allah ka rarrashe
ta ku taho tare."
.
SALON SO
♡♡♡♡27 ♡♡♡♡
.
Faruk ya ce, "Ba ruwana babu inda za ni bare ta
zo ka ci mata mutunci ta zo ta rinka ganin h rashin
kirkina.
Haidar ya ce, "To ni ka kai ni wajen ta na ganta,
Faruk ya yi murmushi, Haidar ko dai ka so ma
son ta ne?"
Haidar ya rintse ido ya ce, "Wallahi ban san
lokacin da son yarinyar nan ya yi min dirar mikiya
ba, ya shige ni.
Inna kwanta da daddare Allah Allah nake gari ya
waye don na ga kyakkyawar fuskar matata kuma
kanwata, wallahi ni kadai na san yanda tsananin
son jawahir yake raina, kai abin da na yi wa
Kausar a gananta ma na yi ne don na auna na ga
tana so na kuwa ko ni kadai nake shirme na.
Faruk ya ce, Ka ga irin abin da na so ka gane
tuntuni ka ki, to yanzu kuwa in ta ji halin da kake
ciki sai ta ce don ka ga ba za iya kwanciya da ita
ba ne, shi yasa ka nemi shiri da ita.
Haidar ya ce, "Ai likita ya ce zan warke fa". Ko da
yake yanzu ne lokacin tantance wanda take
sonka don Allah da wadda a kayi auren sha awa.
"Haidar ya ce, Ni dai don Allah ka je ka taho min
da sahibata ko don na ga halin da take ciki.
Faruk ya ce, "Zan je ai yanxu
Kausar ta turo kofar ta shiga fuskarta a murtuke
babu alamar fara'a, ta je gefe daya ta zauna ba
tare da ta kula wani a cikinsu ba. Faruk ya mike
Haidar bari na je in dawo ko? Duk yanda muka yi
zan zo ka ji.
Ya ce, "Don Allah ka je fa yanzu kada ka ki zuwa
ka ji. Faruk ya ce Insha Allahu kuwa yanzu zan
je.
Faruk ya fita ya bar su Haidar ya juya ya kalli
Kausar ya ce, "Me ya same ki ne na ga kamar
ranki a ba ce? Ko cikinne yake ciwo?"
Ta zumbura baki, "Kai yanzu har ka manta da
barnar da Jawahir ta yi maka a jikinka har kake
cewa a je a taho da ita? To wallahi ni ba zan
yarda ba don ta ga ita ba ta da amfani a wajenka
shine za ta nakasta min kai, wato ka zamo marar
amfani, to wallahi ba zan yarda ba don ita ma sai
na nakasta ta, sai dai duk abin da za a yi a yi."
Haidar ya daka mata tsawa ya ce, "Ke ki shiga
hankalinki kina ganin duk da son da nake wa
jawahir da ta yi miki abu sai da na yi mata marin
da ta gigice, to wallahi ki shiga hankalinki idan
kika sake kika taba min mata wallahi sai kin yi
mugun raina kanki, don sai kin yi mamakin abin
da zan yi miki." Ta mike ta yi waje tana kunkuni
ta zari mota ta nufi gidan Yakumbon Haidar wato
kakarsa ta wajen uba, ta je ta zayyane mata
maganganun karya da gaskiya ta gaya mata,
Yakumbo ta hau sababi ka ji mu da tsinanniyar
yarinya don ba ta son sa shine take neman
hanyar kashe shi, to wallahi bi ba yarda zan yi
ba, tashi ki koma asibitin gani nan zuwa yanzun
nan, "Kausar ta koma asibiti ta tarar su Anti da
Momy da su Yaya Abba sun cika asibitin taf, ana
ta jajen abin da ya faru.
Shi kuwa Faruk da ya je gidan Haidar yayi
sallama falon, su jawahir suna daga kicin suka
amsa sallamar suka fito falon, Faruk ya nemi
waje ya zauna jawahir da Bilkisu suka gaishe shi,
faruk ya ce, Haidar ne ya turo ni na zo na ga
halin da kike ciki in kuma da hali ki zo mu je yana
son ganinki. "Jawahir ta sunkuyar da kai ta ce,
"Gaskiya Yaya Faruk ba zan je inda yaya yake ba,
don in na je ban san irin wulakancin da zai yi min
ba, ka ga kuwa da na je ya bata min rai ai gwara
ban je ba.
Faruk ya ce, "Wallahi Haidar yana wani hali na
mutuwar sonki kin san miskilancinsa ya rasa ta
hanyar da zai bi ya nuna miki Kaunar da yake
miki don yanzu da kin ga irin magiyar da lallamin
da ya rinka yi min sai na zo gare ki dakin
tausaya masa.
Kafin ta yi magana Bilki ta ce, "Faruk bari mu
karasa girkin da za mu kai masa sai mu fito mu
je." Faruk ya ce, to shi kenan bari na je na dawo.
Bilki ta zuzzuba komai a fulas ita kuma jawahir
ta je ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin atamfa
ja! Super Holland dinkin filet ne ya kama jikinta
sai zani da dankwali da ta daura, farar hoda
kawai ta shafa a fuskarta sai dan man leben da
ta shafa ta dauko jan mayafi da jan takalmi ta
saka, kunnanta fashon din yari ne me jan dutse a
tsakiya. Bilkisu ta tafa mata "Amma
yarinyar nan kin yi kyau, kwalliyar taki ta burge ni
sai dai kash kin manta a shafa hadin turarukanki.
Jawahir ta yamutsa fuska, "Kin san fa inda za mu
je za ki ce na shafa hadin turare. Bilki ta ce, to
meye ba wajen mijinki za ki ba, ai gwanda ki
shafa turarukan da kamshinsu zai gigitar da shi
kuma ga karin lada a wajen Ubangiji, don duk
sanda mace ta yi abun da zai farantawa mijinta
har ya ji dadi a ransa to Ubangiji zai ba ta ladan
da ba ta san adadin yawansa ba.
Jawahir ta ce, Haka ne bari na shafa don na
fuskace shi yana son kamshi.
Sun jejjera fulas-fulas din a dan kwando me kyau
ta lullube shi da farin yanki me adon bakin les da
fulawoyi a jiki. Faruk ya dawo suka dunguma a
motarsa zuwa asibiti.
A lokacin ba kowa duk sun tafi sai kausar kawai
da take zaune kan kujera tana karanta jarida, ba
ta daga kai ba balle ta kalli wani a cikinsu. Faruk
ya ce, "To ga ta nan na cika alkawari ko, ga ta
na kawo maka
Haidar ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa na gode
Bilkisu ce ta fara gaishe shi tare da yi masa ya
jiki. Cikin fara'a ya ce, "Ai jiki Alhamdullahi."
Jawahir ta durkusa cikin dari-dari da rawar
murya Kamar
mai shirin kuka ta ce, "Yaya ina wuni? Ya jikin?
Ya ce, "Lafiya lau jawahir ya naki jikin.?
Ya sa hannu ya dago ta daga tsugunnun ya shafi
kuncinta, ya ce, "Wai haka kuncinki ya tashi
hannuna ya fito radau na marin da na yi miki,
sorry Babyna ki gafarce ni, "Kafin tayi magana
aka turo kofar aka shigo tare da sallama,
Yakwalkwal ce ta shigo rike da hannun Sayyid.
Sayyid ya fincike da gudu ya nufi jawahir yana
cewa, "Anti na anti na, shine rannan kika gudu
unguwa kika bar ni ina ta kiran ki ba ki zo kin tafi
da ni ba. "Jawahir ta dauke shi ai yau da kai zan
tafi kai ta kwana a can ko? Jawahir ba ta ankara
ba ta ji saukar mari a kuncinta, Yagwalgwal ce ta
kuma hau fada, "Annamimiya me kuma ya kawo
ki wajen jikana kin so ki kashe shi, Allah bai baki
nasara ba shi ne kika biyo shi nan ki karasa shi
ko?
Haidar kuwa tuni ya diro daga gadon jinyar ya
tare jawahir yana cewa, "Haba Yagwalgwal ya za
ki doke ta ita ma fa ba lafiya ce da ita ba, me ta
yi miki?"
Yagwalgwal ta ce, "Ubanka ta yi min, shege
sallamamme so kake yanda uwarka ta mallake
Alhaji kai ma jikan mallake ka za ayi,
"Yagwalgwal ta ci gaba da nuna jawahir da dan
yatsa tana yi mata sababi, daga yau na gaya miki
ba ke ba Haidar in ke mayya ce ki ci kanki da
kanki, haka kawai hankalinsa ya kwanta yana
zaune da matarsa lafiya za ki zo ki bata musu
zama.
Jawahir ta mike jikinta ba kwari za ta fita Haidar
ya yi saurin riko hannunta yana cewa, "Haba
Yagwalgwal ya za ki zo ki korar min matata ki ce
sai ta tafi? Ai ba ita ta kawo kanta ba ni na sa a
je a dauko ta in ta tafi waye zai yi jiyya ta?
Kawai mutum da matarsa a nemi raba su. Kan ya
rufe baki bakinsa Yagwalgwal ta ba shi nasa
marin ya dafe kunci ita kuma ta ci gaba da
sababi tana nuna shi da dan yatsa, "Ka shiga
hankalinka ka san da wacce kake magana, idan
ba ka san ciwon kanka ba ai ni na san ciwonka,
yarinya ta nakasa ka ka zamo marar amfani
amma ba za ka guje ta ba, wata rana ma ranka
za ta raba ka da shi.
Jawahir ta fincike hannunta ta yi waje cikin sauri
Haidar ya yunkura zai bi ta Yagwalgwal ta rike
shi, Bilkisu ta bi bayan jawahir yayin da Faruk ya
rufa musu baya. Da kyar da ban hakuri ya shawo
kan jawahir ta shiga motarsa don ya mayar da su
gida. Faruk ya ce, "Don Allah don Annabi jawahir
ki yi hakuri da abin da tsuhowar nan ta yi miki.
Jawahir ta yi saurin katse shi, "Haba yaya Faruk
ka fi kowa sanin ta yanda a ka yi aurenmu da
yaya, ba son sa nake yi ba na aure shi don
biyayyar iyayena na zo nake zaman hakuri da shi,
ya tashi ya dankaro min kishiya ni duk hakurin da
na yi a kansa ba a gani ba kenan.
Fashe da kuka Faruk ya ci gaba da rarrashinta ki
yi hakuri jawahir ki tuna aure kike, aure kuwa
bautar Ubangiji ne kada bacin ran wasu ya sa ki
sabawa megidanki kin ji?"
Yanda na san ki da hakuri da ladabi da biyayya ki
ci gaba da yi komai me wucewa ne wata rana sai
labari kin ji?".
Ta daga kai ya ce, "Yauwa ko ke fa gobe ku
shirya da wuri sai na zo na kai ku ta ce to. Ya
sauke su a gidan shi kuma ya koma asibitin shi
kuwa Haidar tun bayan fitarsu jawahir da
Yagwalgwal ta rike shi don kar ya bi su gado ya
koma ya kwanta ya yi rigingine ya rufe idonsa.
Maganar duniya babu wadda ba a yi masa ba
amma ya yi musu shiru ko motsi bai yi ba dole
suka gaji suka hakura suka bar masa dakin.
Faruk ya shigo ya dinga lallaminsa yana ba shi
baki tare da va shi hakuri sannan ya tashi ya
jawo kwandon da jawahir ta jero masa kayan
abinci.
Dakakkiyar sakwara ce lukui da miyar agushi mai
wadataccen nama, sai jalof din taliya da lemon
kwakwa. Haidar ya ce, "Ka ga yarinyar nan da
zan bata mata rai ba za ta ki yin abinci ba don
gudun kada ta bar ni da yunwa."

Please Login or Register in order to submit comment