Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ka yi hakuri Kayyid zan siyo maka jirgin sama me tashi. Ya makale kafada alamar bai yarda ba. Ta ce, "To je ka dakin Yaya ka ce ya zo mu tafi. Ya ce, "To Ya hau san a guje. Ita ma saurin ta yi ta fice ta shiga motar Haidar ta tashe ta ta tafi ba ta taba tuka mota da kanta ba sai yau, amma ta iya don duk sanda za su fita da direba sai ya koya mata. Haidar yana jin tashin mota ya turo Sayyid daga jikinsa ya mike zumbur sai sannan ya tuna ya bar mukullin motarsa a falon kasa. Ya gangaro falon kasan da sauri yana salati, "Inna lillahi wa inna ilaihir raji un. Hankalinsa ya yi mugun tashi. "Na shiga uku. Kadda yarinyar nan ta yi wani wajen yanzu idan wani abu ya samu yarinyar nan yaya zan yi da rayuwata? Ga Sayyid ya ishe shi da ihun kuka yana kiran "Aunty Dole Haidar ya dauki wani mukullin motar ya saba Sayyid a kafada suka fita. Ya shiga mota a hankali yake tuki yana kallon hanya ko zai hango motarsa da jawahir a ciki. Jawahir kuwa cikin nutsuwa da tsoron ta gudanar da tukinta har ta zo kofar gidan Inna tayi hon megadi ya bude mata ta shiga ta yi parking ta sa shi ya jidi kayanta da yake but ya shigar mata da su cikin falon Inna. Inna ta ce, Lafiya na ganki da kaya? Ta ce, "To lafiyar kenan. Inna ta ce, "Me yake faruwa ne na gan ki da kaya kuma kin rame a kan san da kuka zo, ko ba ki da lafiya ne? Ta ce, "To ba dole na rame ba an aurawa wanda ba ya so na ni yana ta gasa ni ga shi nan ai yau ya koro ni gidanmu ko.?" Inna ta dafe kirji ta ce, "Shi da kansa ya ce ki taho gidan? "Shi ne mana Inna kullum sai dai ya kira ni da tatsitsiya ko kwaila, ya mai da ni 'yar aiki na girka masa ya ci ya koshi wallahi sai kwanan nan ya fara yi min magana amma da ko meye sai dai ya rubuto min a takarda sai ni ma na ba shi amsa a rubuce sai ka ce kurame. Inna ta saka salati, "Au ni ina ta murna na zata ciki ne da ke ashe ba wani bayani. Ta ce, "Uhm inna ke nan, to ko matsayin kyakkyawan kallo ba na samu a wajensa duk na yi hakuri na jure to wai yanzu aure zai yi. Inna ta ce, "Aure, lallai ma yaron nan ban ni da shi boye ki zan yi, zan gyara ki na kula da ke har sai kin zama cikalkiyar mace zai raina kansa ne da ni yake zancen. Duk waigen da Haidar yake yi bai hango jawahir ba har ya iso gidansu. Aunty ya samu a falo tana kallon labarun kasa ya sauke Sayyid ya tafi da gudu ya fada jikin Aunty yana kuka. Aunty ta rungume shi tana cewa, "Haba Auta me aka yi maka kake kuka.? "Bayan Auntyn gidan Yaya ce ta gudu ta bar ni. "To yi hakuri tun da an kawo ka wajena ka ji." Ya daga kai Ta kalli Haidar, "Ina jawahir din take?" Ya ce, "Wallahi ban san inda ta tafi ba, kawai na ji karar mota, ashe ita ta fice ta yi tafiyarta. Aunty ta dafe kirji, "Ita kadai ta ja motar ta fita? Wato ka yi mata maganar auren naka ko? To wallahi tashi ka fita duk inda take sai ka je ka nemo ta. Abbansa ya shigo, "Lafiya na gan ku haka? Aunty ta ce, "To ba dole ka ganmu haka ba, ya salwantar min da 'ya. "Wa ce 'ya?" Jawahir mana, wai be san inda take ba. Abba ya yi saurin zama don jin faduwar gaba da ya yi, ya kalli dan nasa, "Haidar me ya hada ku har ta fita?" Haidar ya ce, "Ni kaina ban san abun da na yi mata ba, ta ji dai ina waya ta kwace wayar ta tarwatsa ta sai na mike na hau sama, to ban ankara ba na ji tashin motata. Aunty ta ce, "Uhm ka ji ba, in ban da rainin hankali yaushe zai je gabanta yana waya da budurwa suna hirar aure. Ni na san wannan rawar kan da kake yi sai ka jawo mana tashin hankali, ka ga in ka ga ba hali ka sakar min 'ya mu ba neman kai muke yi da ita ba. Abba ya ce, "Duk haka ba ta taso ba, ku kwantar da hankalinku da safe zan je gidan na su sai na ji dalilin tahowar tata. Yanzu tashi ka tafi gida. Aunty ta ce, "Ba fa tabbas din gidan ta tafi dole ne a yi binkicen ta tun daga yau." Ta dauko mayafinta ni bari na je gidan na su yanzu. Ta shiga mota direba ya ja ta suka nufi gidansu jawahir. Tana shiga gidan ta tarar da mommy da Nasir da su Auwal da Sani. Aunty ta zauna duka suka gaishe ta cikin fara'a ta amsa tana wasa da dariya ta su. Suka gaisa da momy da tsokana irin wasan nan na kannan miji. Ta ce, "Yaya kuwa yana nan? Momy ta ce, "Eh yana sama. Auwal je ka gaya masa Aunty ta zo, "Ya hau da saurinsa ya sauko ya ce, "Ki hau saman Ta hau. Bayan 'Yan gaishe gaishe da suka yi sai ta gyara zama ta ce, Yaya ina Jawahir din?" Cikin mamaki ya ce, "Au ta zo ne? "Uhm wai rigima suka yi da mijin nata ta taho. Ya ce, "Ikon Allah ai ni ban ma sani ba bari na tambaye ta Ya dau waya ya kirawo momy ta yi sallama ta shigo ta nemi waje ta zauna. Ya kalle ta ya ce, "Ina jawahir take? Momy ta ce, "Tun da aka yi auren ta ba ta zo gidan nan ba. Wani abu ne? "Wai sun yi rigima da mijin ta taho. Momy ta ce, "Oh ni 'yasu, yara ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba, yanzu duk fadan nan da aka yi wa jawahir sai da ta sabawa nijinta. Aunty ta ce, "A'a ai ba laifinta ba ne, da ai lafiya suke zaune auren nan da ya rakitowa kansa duk shi ya hargitsa musu zaman." Momy ta ce kin ji irin shashancin ko, ai komai na Allah ne, namiji da aka halicce shi don mata hudu ka hana shi kara daya. Aunty ta ce, A'a ba ta fa da laifi ko ke da kika girma da Yaya ai ce zai kara aure da sai kin hana mu sakewa bare ita da ga yin aure shekara daya a ce namiji zai maka kishiya, ai dole a ji kanku. Dady ya ce, Ai kun san ma ba za ta zo nan ba tun da ta san ba goyon baya za ta samu ba. Tana gidan Inna, tun da ta je hannun Inna kuwa kwato ta sai wani ikon Allah. Aunty ta ce, "Ai maganinsa kenan wallahi gwanda ta hora shi tukunna. Momy ta ce, "A'a ni dai ba na son son kai don dai kin ga 'yarki ce kawai kuke son ga sa masa gyada a hannu. Dady ya ce, Ba me wahalar min da da, duk zan tara su na san meye matsalarsu. Hankalin Haidar ya kara mummunan tashi yayin da ta bayyana cewa jawahir ba ta gidansu. Goma na dare Haidar ya isa gidan Inna a gigice yana neman jawahir din. Inna ta fututtuke ta ce ita yaushe rabon da ta ga jawahir ma? Wallahi ya je duk inda jikarta ta take ya nemo mata ita in ba haka ba kuwa ya gamu da fushinta. Haidar kamar zai yi kuka magiya yake yi wa Inna idan ita ta boye jawahir ta fito da ita don ya ga motarsa a gare jin gidanta wadda da ita jawahir din ta fito. Inna ta ce, To sai dai in zuwa ta yi ta ajiye motar ba ta shigo ba ta fice, "Ta ce, "Na gaya maka wannan kame-kamen ba zai yi maka ba, ka je ka nemo min jikata. Sha daya na dare ya bar gidan Inna ya isa gidansa. Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida, amma haka ya kwana yana juyi da tunanin inda za a ga jawahir. Ga yunwa ta gallabe shi ga ba abinci, shi kuwa ko ruwan shayi be iya dafawa ba, bare ya dafa ya sha. Haka ya yi ta juyinsa har aka yi, sallar asuba. Daga masallacin gidansu ya taho a motarsa. Abba ya yi mamakin ganinsa inda yake tambayarsa, "Lafiya haka da asuba.? "To Abba ina zan iya samun sukuni ba a fa ganta ba. "Ba ka ce ka ga motar gidan Inna ba.?" "Ai Inna ta ce ita ba ta shigo mata ba ajiye motar ta yi ta san tana waje. Allah ya kyauta, Abba ya lallaba shi ya yi wanka suka yi break tare. Abban ya dauko shi suka yo gidan Inna wai ko za su ga jawahir din. Amma Inna tana jin tsayuwar mota ta tura ta wani dan daki ta yi zamanta a falo. Abba da Haidar suka shigo duk yanda suka yi don su bigi cikin Inna su ji ko jawahir tana gidan Inna ta fututtuke ta ce ba ta zo mata ba. Dole suka hakura suka yi mata sallama suka fita. A mota kawai Haidar sai ya sawa Abbansa kuka, "Don Allah Abba ka tainaka min a ga jawahir, yanzu in ban gan ta ba ai na shiga uku ya zan yi da rayuwata? Ya dafa kansa ya ce, Ka yi hakuri Haidar za a ganta ne insha Allahu. Bayan fitarsu Inna ta yiwa danta Aminu da yake Abuja waya ta gaya masa komai ta ce tana so ta turo masa jawahir nan kada ya sake ya ce tana gunsa. Aminu ya amsa da to! Ya ce da kansa zai zo tararta filin jirgi. Jawahir ta gama shirinta a boye direban Inna ya kai ta filin jirgi ta hau zuwa Abuja sai da ya ga tashinsu sannan ya dawo ya shaidawa Inna. Can kuwa Uncle dinta yana Airport yana zaman jiranta. Yana hango ta ya taro ta da murna suka rankaya zuwa gidansa matarsa Maryam ta yi farin ciki da ganin jawahir, don Maryam mace ce mai faran-faran da son jama'a ga ta wayayyiya. Irin gogaggun matan nan ne wadanda suka san makamar kama da namiji. Ba bata lokaci Uncle ya karbi takardun makarantar jawahir ya samar mata University of Abuja. Ba bata lokaci jawahir ta zamo daliba a jami'ar. Jawahir an shiga cikin wayayyun 'yan matan jami'a ta goge ta kile, ta kara kyau da girma babu yanda za a yi wanda bai yi mata cikakken sani ba, ya gane ta, don yanda Maryam ta ke gyara ta kamar 'yar cikinta don wani magunguna da tsumi na mata da take dibga mata tana sha. Sai maganin ciko da nono da tsaitsayar da su don har ya zube, shi take ba ta tana sha. Kasancewar hankalinta a kwance yake ta yi 'yar kiba ta murje jikinta mulmul kamar na jariri, sabon haihuwa. Kirjinta ya cika fam yana tsaitsaye ba shi da alamar rankwafawa, duk wanda ya kalle ta sai ya juya ya kara kallonta saboda tsabagen haduwa da wani shirtaccen kyau da ya kara bayayyanar mata.
(((((((SALON SO)))))))
(((PART 19 TO 20))))
HAIDAR ya kasa samun nutsuwa dole ya nufi gidan abokinsa Faruk don yanke shawarar da za ta fisheshisu. Yana zaune a falo Faruk ya hada kai da guiwa yana ta tunani tare da karanta wasikar jaki. Faruk ya shigo falon tare da yin sallama. Bai jira an amsa sallamar ba don ya san ba zai samu ba ya karaso ya dafa kafadar Haidar ya ce, Me yake faruwa ne da kai aminina? Wace matsala ce kuma take kokarin danno maka kai ne? Kai da za ka yi auren ke ce raini. Ya ce, "Kyale ni Faruk abin duniya duk ya dame ni, ko ka san jawahir ta gudu ban san inda ta nufa ba. Faruk ya dafe kirji ta gudu fa ka ce? Me ya hada ku, ko na ce me ka yi mata? "Uhm kai dai a yi sha'ani, wai daga na yi maganar aure zan yi sai yarinya ta gudu. Faruk ya ce, "Ai madallah ka ga irin abin da nake jiye maka ko, to ai ga irin ta nan yanxu sai ka je ka bunciko ta a duk inda take. Haidar ya ce, "Wallahi ni dai ina zaton tana gidan Inna don mota ta da ta dauko ta taho da ita, na ganta a gidan Innan. Sai dai amma Innan ta kafe ta ce jawahir din ba ta gidanta. Faruk ya ce, Ka ga taso mu kaje kawai mu shammace ta ba tare da munyi sallama ba mu shiga kawai in tana ciki za mu gan ta. Suka mike suka yi gidan Inna Haka suka danna kai falon Inna babu sallam abun mamaki ba jawahir sai Inna da ta yi zumbur za ta tashi ta ce ni har kun tsorata ni lafiya kuka shigo min haka babu sallama? Faruk ya durkusa yana gaishe ta Haidar kuwa zubewa ya yi a kasa yana yi wa Inna magiya inna don Allah don Annabi Inna ki taimaka ki fito min da jawahir. Inna ta ce, Haidar me kake fada ne? Ni na san inda jawahir take ne? Faruk ya ce, "To ai ni abin da ya fi ba ni mamaki ya a ka yi motar ta zo nan gidan, "Inna ta ce, "Ni dai ina zaune aka aiko min da mukullin motar na ajiye na zata ma ko tare suke da Haidar din motar ta lalace musu suka ajiye ta, su je su dawo. Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta ce ga mukullin motarka nan kada ku sake zuwar min idan ba jikata kuka gano min ba. Haidar cikin marairaita kamar zai yi kuka ya ce, "To yanzu Inna ya za a yi da neman jawahir din.? Cikin fada ta ce, To ya za a yi kuwa? Da ka rike ta hannu bibbiyu ai da haka ba ta faru ba ko? Yanxu da ka yi sakaci da ita ta bata ai ko wa sai ya huta. A dauki yarinyar nan cikin girma da mutunci 'yar uwarka ta jini a baka amma ka rinka wulakanta ta. Ya yi saurin cewa, "Wallahi Inna ba wulakantata nake ba wai don kawai na ce, zan kara aure shi ne ta yi tafiyarta. Inna ta ce, "Uhm ai ka ga yanzu ta bar maka filin gidanka ka fi sakewa kai da Amaryar taka sai ka je kai ta yo auren. Faruk ya ce, "Inna hakuri za a yi in dai an san inda take din a fada mana. Ta ce, "To ban sani ba ku tashi ku ba ni waje. **** ****** ****** Maganar jawahir kuwa tana gidan Ankul dinta ta dage da karatu don makaranta biyu zan ce take yi. Tana zuwa jami'a yayin da kuma Ankul dinta ya daukar mata lakcara guda yake dada tunasar da ita da nusar da ita halayyar dan Adam, yanda ake iya zama da su sannan yana koya mata dabaru na iya kasuwanci da yanda za ka sarrafa kudi duk kankantarsu don juya su. Ta bangaren jawahir kam ma iya cewa Alhamdullihi, don komai a ka gaya mata ya zauna a kwalkwalwarta kenan da yake yarinya ce me kaifin basira da kokari. Jawahir ta gama nazarin abun da aka yi musu lakca a yau ta mike a gajiye ta shiga toilet ta yi wanka ta gama shirinta ta fito falo ta samu Auntynta a zaune. Maryam ta kalle ta tayi murmushi, "Tubar kallah 'yar gidan Ankul ba dai kyau ba, zo ki zauna na dora miki inda muka tsaya don so nake yi ki mallake Haidar tsab yanda ya raina ki yake kiranki da tatsitsiya ko kwaila to yanzu ki zame masa dan hakin da ka raina. Yanzu abin da zan fara miki da shi shine zan koya miki kissoshi kala-kala don haka dauko littafi da biro ki rubuta komai don gudun mantawa. (Saboda haka idan kuna so nima na fada muku to kowa ya/ ta dauko biron shi/ta domin nima saida na rubuta sannan na iya kawo muku badon haka ba........hmmm. Gani nan ina zagayawa fa. Hhhhh su o'o akwai akwai tsoro ji harda rawar jiki kar na ganta ba paper). Jawahir ta mike ta dawo da littafi da biro, "To yanzu za mu fara da kissar tsafta don ita ce kan gaba a kan komai. Ki kasance mai tsaftar gidanki ko da yaushe cikinsa da wajensa. Kicin dinki ya zamo a gyare a share, a goge ki turara masa turarukan wuta me dadin kamshi. Toilet dinki ya zamo kullum cikin gyara idan kika wanke kika goge komau kika cire yana ki masa nasa turaren wutar na musamman ya kasance cikin kamshi wanda mutum ya yi bahaya wannan kamshin zai kashe masa jin warin bahayan nasa, idan ba ki da lokacin yin wanki da kanki to a ajiye almajiri idan sun kai kala biyu zuwa uku ki ba shi ya wanke ya goge miki, idan kin tashi sai ki turare kayan naki da turaren kaya sannan ki jera a kwaba. Sai kuma kwabar ki sa mata turaren kaya don gudun warin ruma da dai sauransu. Ki kasance mai kwasar shimin mijinki, gajeren wandonsa, hankijinsa da dai wani karamin abu da yake amfani da shi ki wanke, ki goge su ki turare su da turaren kaya ki adana masa su. Idan kin shiga wanka ki rinka amfani da daddadan sabulu me kyau da dadin kamshi. Ki rinka cuda hammatarki, kasan nonuwanki, matse-matsin cinyarki, ki rinka wanke gabanki sosai da sabulu me kamshi, duk wani lungu da sako na jikinki ki wanke shi ki gyare shi fes in da ko ina mai gida ya sa kansa zai ji kamshi. Ki kasance ko yaushe cikin gamsasshiyar kwalliya, ki daure da asuba idan kun yi sallah me gidanki zai ja ki ku koma gado ku kwanta, to ki yi kokarin hana kanki bacci. Har sai shi ya yi sai ki janye jikinki a hankali ki tashi ki nufi kicin don hada muku karin kumallo. Kada ki yi masa break kala daya saboda saurin ginsa ki yi masa kalolin break kowanne ki zuba a fulas gudun kada ya huce. Daga nan ki jere su a tebir ki gyara wajan ki da turare ko ina da daddadan kamshi me sanyaya zuciya, sai ki je ki yi wanka ki bata lokaci wajen yin kwalliya wannan fa kwalliyar safe ce ta barka da tashi me gida. Za ki saka les ko atamfa ko shadda ko boyal duk dai wanda ya samu, za ki feshe jikinki da kalolin turaruka masu kyau da dadin kamshi wanda har za a kasa tantance wane irin kamshi kike yi, to sai ki nufi dakin maigida. Ba a tashin miji da hayaniya ko surutu ko ki yi ta jijjiga shi kina kiran wane! ka tashi lokaci ya yi, in kika yi irin haka za ki bata ran maigidanki. Abin da kawai za ki yi shine da kin shiga dakin mijinki kin ga yana bacci ga lokacin tafiya Office ko kasuwa ya kusa, to sai ki zauna a gefen gadon ki sa hannuwanki kina shafar fuskarsa kisa bakinki kina hura kunnunsa a hankali kina shafa fuskarsa tare da dan jan karan hancinsa. Ko ki fara shafar kasan mararsa kadan-kadan. To za ki ga ya tashi a nitse ba tare da magagi ko tsaki ba, da ya mike ya shiga toilet ko kafin ya fito sai ki yi saurin gyara gadon ki debo masa kayan da zai sa hade da best da gajeran wando da dan hankici duk kuma ki feshe su da turaruka masu dadin kamshi ki debomasa takalmansa ki goge su fes, da ya fito daga toilet ki yi gaggawar daukan tawul ki rinka tsane masa ruwan jikinsa sannan ki debo mayukan da yake amfani dasu ki rinka shafa masa a hankali kina yi kina ba shi labari na ban dariya a hirar nishadi. Ki taimaka masa wajen sa kayan nasa, ki sa karamin kum ki taje masa sumar kansa, ki dada dauko turaruka ki kuma feshe shi da su, ki sa masa gilas idan yana da ra'ayi. Ki riko hannunsa ku taho zuwa kan tebir kuna tafe a hankali kina yi masa rausaya tare da yawan shigewa jikinsa har ku iso tebir din. Ki rinka zuba masa komai kina turo masa gabansa kada ki damu da sai kin ci a lokacin, ki rinka hada masa abinci me yawa a gabansa ki rinka tura masa kina yi masa shagwabar bai ci da yawa ba, ko ki ce ke ba ki yarda ba sai ya cinye da sauran abubuwan da za su ja hankalinsa ya saki jikinsa sosai ya ci abinci ya koshi. Idan ya mike don ya tafi office ki roko masa jakarsa kina yi masa 'yar shagwabar Honey da ka tashi daga office ka yo gida kada ka tsaya wani wajen ka ji. Honey idan ka isa office ka tsaida hankalinka ka yi aikinka a nitse kada ka yi tunanin komai bare ya sa min kai a damuwa. Za ki ga ya rungumoki tare da shi miki albarka duk kuma inda yake hankalinsa yana kanki Allah Allah zai yi ya dawo gida don ya tarar da ke. To da ya tafi office ke kuma a wannan lokacin za ki samu ki yi baccinki kafin lokacin girkin rana ki kula me mijinki ya fi so, me ya fi sha awar ci don ki kiyaye wajen girka masa su, shinkafa da miya, ko tuwon shinkafa da miyar taushe, ko danyar kubewa, ko miyar agushi, ko miyar wake da ganye, ko tuwon dawa, ko na masara, tuwon semovita ko ki daka masa sakwara, ko ki dafa kuskus ko taliya, zaki hada masa da soyayyen naman kaji ko gasasshen naman kasuwa ko farfesun kayan ciki, ko farfesun kan rago ko na jelar sa ko farfesun naman karamar dabba, ( A nan ana magana ne idan mijinki mai hali ne, idan kuwa ba mai hali ba ne sai ki yi masa abin da kika tabbatar yana jin dadinsa dai-dai rufin asiri) To idan kika duba abin da ya fi so a cikin yi masa kika gama komai kafin ya dawo, ki dada gyara gidanki ki turare shi da nau'in kamshi kala kala, ki shiga aiki sake fesa wanka sai ki yi kwalliya ki hade da siket ko riga da wando ko doguwar riga ko dinkakken shadda, ko atamfa, boyal, yadi, material, da dai sauransu, to ya kasance karamin dinki ne dai-dai jikinki ki saka wanda da zarar maigida ya dawo za ki tafi cikin salon murna ki ringume shi kina me yi masa barka da zuwa. Ki fara raka shi dakinsa ki cire masa kayan jikinsa ki hada masa ruwan wanka da turaren wanka a ciki da ya shige tolet sai ki kwashe kayan da ya cire ki rataye masa a anga. Ki fito masa da kanana na shan iska. Da ya gama shirnsa ya fito sai ki zo a nitse cikin dabara ki rinka loda masa abinci yana ci kina fara loda masa wani yanda zai ci ba tare da ya gane ya ci da yawa ba. Kina zuba masa sanyayyen abin sha yana ci yana sha, har sai ya koshi ya yi kat sai ki jawo shi ku baje kan kafet ko kujera kuna wasanni da hirarraki masu dadi ko kallo ku, ki rinka karanta masa labarai masu dadi, amma ki kasance ko yaushe kina manne a jikinsa ki rinka yi masa shagwaba kina mai da kanki karamar yarinya a gabansa kina zama doluwa marar wayo ki rinka sa yin dan sokoncin zai rinka sa mijinki dariya, to yawaita masa irin wannan abubuwan shi zai kara muku shakuwa da fahimtar junanku, za ku kasance cikin bege da son junaku ko da yaushe. Idan kin tabbatar kin wa mijinki lodi da abincin rana to yunwa ba za ta gallabe shi da dare ba, don ba a so da daddare a ci abu

Please Login or Register in order to submit comment