Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saraki kausar ce. Yac, "Wa cece kuma me wannan sunan.? "Ranka ya dade Saraki Kausar dinka da kuka yi karatu America tare ka gudo ka bar ta. "Oh. Kausar kenan kin cika na ci, yanzu sai da kika lalubo ni." "To ya zan yi Haidar wallahi tun ranar da ka taho ban kuma nutsuwa a zuciyata ba sai yau da na ji muryarka. Haidar ciwon son ka ya zamo gyambo a cikin zuciyata. Haidar ni musulma ce ka tallafi rayuwata Haidar ka zo gare ni ka aure ni. "Haba Haidar ka san darajar 'ya mace da kimarta amma duk na watsar na tunkare ka na ba da kai na ke rokonka da ka aure ni. Haidar wace irin zuciya ce da kai? Ka tuna fa kana da kanne mata kuma nan gaba in Allah ya ba ka haihuwa kila ka samu 'ya 'ya mata, to ya za ka ji yayin da 'yarka ko kanwarka ta fada irin wannan halin da na fa da akan kan wani? Ka san kaddarar ubangiji babu inda ba ta fadawa mutum." Haidar ya ce, Ki yi hakuri ba burina na yi miki wulakanci ba, ai duk inda masoyinka yake ya fi makiyinka sau dubu, to amma kin ga yau shekara daya ke nan iyayena sun hada ni aure da wata 'yar karamar kanwata, wadda har a yanzu da nan gaba rainonta nake yi." Kausar ta ce, Haidar don Allah don Annabi ka amincewa bukatata wallahi ni ba ruwana da wata matarka don ba a kanta zan zauna ba. Ya ce, "To shi kenan Kausar ki ba ni lokaci zan yi shawara. Ta ce, "Haba Haidar. Ya ce, "Uhm no kada ki damu ba matsala insha Allahu komai zai zo da sauki. Suka yi sallama kowa ya dire wayar. Haidar ya fada tunani ko na amince da bukatar Kausar na aure ta, ko ni ma na ji yanda auren yake? To ya zan yi da Aunty da Abba? ko da yake in sha Allahu ba za su zamo matsala ba. Haba dai ya kwanta yana sake- saken abinyi. Washegari yana office wajen azahar jawahir ta yi baki kawayenta ne suka zo. An sha hira kuwa inda jawahir take cewa, "Bilki ai kun yi min rashin mutunci wai duk yanda muke da ku aure shekara daya amma kuka kasa leko ni." "To ai kin san abun ne sannan ba kwa shiri da shi mu zo wani abun ya faru sai ya zamo matsala, some kin ga yanzu ai komai normal don yanda kike wannan kyallin goshin na san an samu rabo ma ( Hahaha kunji gulma. Hmmm Ni dai Bomboy ba ruwa na idan Haidar yaji ku). Ta yi dariya, "Uhm kwa ji da shakiyancinku ku zo mu ci abinci." Wajen karfe hudu suka gama shirinsu suka fito za su tafi ta yo musu rakiya har bakin get, megadi yana dan dakinsa yana lazimi, Hira suke yi suna tafawa tare da shewa da dariya. Sai ga motar Haidar ya. [8:35PM, 12/6/2016] : shigo ya danna hon megadi ya taso da sauri ya bude masa get. Haidar ya hango jawahir ba mayafi a jikinta ta yi kwalliya tana ta faman dariya duk sai ya ji kishi da bakin ciki ya dame shi. Yaya za ayi ma ta fito nan a haka? Ga megadi da 'yan aikin gida suna nan du su gano ta. Lallai ma yarinyar nan. Ya yi parking ya fito gunsu ya nufa kawayenta suka gaishe shi ya kalli jawahir ke me ya fito dake nan? Wa ya ba ki izinin zuwa kofar gida.? Kanta a kasa ta ce, "Kawayena ne suka zo shi ne na rako su. Rakiya ba ta isa ba iya kofar cikin gida har sai kin fito bakin get.? Ya shige ciki ya bar ta a nan. Kawayenta suka ce, "Lallai Haidar yanzu har wani kishinki yake? "To Allah ya sa dai mu jawo miki wata matsalar ba.?" Ta ce, "Haba dai ba komai ai yana da saukin kai shi ke nan kuma fadan ya wuce. "To mu dai mun tafi sai wata rana." Suka fita ta juyo ta shigo cikin gidan. Yana zaune a falo ta tafi za ta shige daki ya ce, "Ke zo nan. Ta dawo ta durkusa nesa da shi. "Daman in ba na nan bain da kike yi ke nan ko? Kalle ki yanda kika fita ga megadi da yaran gida duk suna ganin ki ko kin manta cewar ke matar aure ce? To bari ki ji duk da an aura min ke ba tare da ina son ki ba, to hakan ba zai hana ni yin kishinki ba, kuma dole ne na sa miki ido don ganin yanda kike tafiyar da rayuwarki, kada na kara ganin wata kawa ta zo miki kin ba ta fuska bare su zo su bata miki tarbiya ko su rinka zuwa tsegumi su samu damar bugun cikinki kina gaya musu sirrinki ko? Ita dai ba ta ce koami ba ya karaci fadansa ta tashi ta yi shigewarta daki. Tana barin wajen wayar Kausar ta shigo, "Hello Kausar kina lafiya.? "Lafiya lau Haidar shiru banji ka ba. Ya ce, "Kai kausar kin fiya gaggawa, amma ki ba ni adres din gidanku insha Allahu jibi zan zo, ta saki wani ihun murna yayin da take gaya masa adres din gidansu dake Abuja. Suka yi sallama ya ajiye wayar. Washegari yana zaune a office ya kifa kansa da tebir tunanin yanda zai bulluwa da iyayensa maganar Kausar yake yi. Abokinsa ne ya shigo ya sa me shi a haka. Duk sallamar da yayi bai ji shi ba bare ya amsa masa. Faruk ya kwankwasa masa tebir din gabansa. Haidar ya yi firgigit ya dago kansa ya kalli Faruk din ya saki ajiyar zuciya. Ya ce, "Yaushe ka shigo ban ji shigowarka ba.? Faruk ya ce, "Yaushe dama za ka ji ka tafi cikin wannan zurfaffan tunani haka, wai don Allah me yake damunka ne? jiya da yau duk wani sukoko nake ganin ka. Ya ce, "Ga ni nan dai abubuwan ne suka tarar min "Ba dai matsalar jawahir ba, ca nake mun gama wannan maganar da kai. Haidar ya ce, "Ai ni ba zan taba iya abun da ka ce na yi ba. Ciknin zaro ido ya ce, "Ba dai kana nufin har yanzu babu abun da ya hada ku ba?. Aure shekara daya. "To kai me kake tunanin zai faru? kanwata ce fa. yarinya ce, ko hannunta na kama ai raina ni za ta yi." Faruk ya ce, "Amma wallahi kana daukan alhakinku. Gaskiya ba ka kyauta ba, yaya za ka rinka wahalar da yarinya, kana zaton dutse ce ita ko waliya ce da ba za ta ji sha awa ba? Haidar ya ce, "Ko dai take wahalar da ni tana gasa ni, ka ga dai ni nake gaba da ita ya kamata ta fara neman sulhu da ni, to amma yarinyar nan gaisuwa ce kawai da safe take hada mu. Ga yarinyar ta iya tsara kwalliya komai ta sa sai yayi mata kyau ya yi das a jikinta kamar Aljana. Duk dare yanzu bacci gagarata yake yi, na dinga murkususu ke nan ina juyi sai ka ce dole, ai ba waliyyi ne ni ba, don haka na yanke shawarar aure zan kara a kwanan nan. Faruk ya dafe kirji ya ce, "Aure Haidar! kai kuwa me yayi maka zafi? Ba gwanda ka nemi sulhu da matarka ku dai daita ba. : (Hmmm barshi da kanshi zai sauke wannan jiji-da- kan. Mu dai yan kallo ne kuma yan rahoto. Da fatan dai idan anzo kamen dan leken asiri ba zaku nuna ni ba).
.
((((((((((SALON SO)))))))
(((((PART 16 TO 18)))))
Haba Faruk yaya za a yi na kwantarwa da wannan karamar yarinyar kai. shi kenan na ba da kaina girma kuma ya fadi, ni dai kawai aure zan yi na rabu da ita ta karaci tsiyarta ita kadai. Faruk ya daure fuska alamar ba wasa ya ce, "To kai duk abun da ake gaya maka ba za ka ji ba ko, to shi kenan ka je ka aika ta abun daka ga dama, in kuma abu ya kwabe maka kada ka sake ka nemeni tun da ban isa na ba ka shawara ka dauka ba, "Faruk ya juya ya fice tare da bugo kofar. Haidar ya yi ajiyar zuciya tare da tallefe kansa da hannu biyu, "Gaskiya ba na jin zan iya fasa auren nan, ni kawai zan yi auren nan ne don debewa kaina kewa da sha awa saboda kullum ni na san yanda nake kwana ina cutuwa. To me yayi zafi ni dai ba zan kai kaina ga halaka ba bare na nemi matan banza Allah ya kiyaye mu da aikata zina gwara kawai na yi auren, "Haka dai ranar ya wuni babu wata walwala. Alhaji Sa'adu mashi, babban ma'aikacin gwamnati ne wanda aiki yake yawo da shi ko ina a Nigeria. A haka ne ya zo Kano inda ya yi gida ya tare da iyalansa. Da yake makotaka suke da gidansu Haidar to sai shakuwa da aminci suka shiga tsakaninsu. Kasancewar Alhaji Sa'adu ba shi da wani dan uwa a garin kano to da ya samu Abbansu Haidar sai ya rike shi ya zama dan uwanshi na kut da kut. Faruk da Haidar sa'o'in juna ne tare suka ta so iyayensu suka sa su primary tare, secondary ma tare Faruk da Haidar sun shaku da junansu. Abun ya wuce abotaka ya koma 'yan uwantaka. Bayan gama secondary dinsu ne aiki ya kuma mayar da Alhaji sa'adu gida wato katsina ya tatara iyalinsa suka koma can gida. Hakan kuwa bai yi wa su Haidar dadi ba sai dai don basu da yanda za su yi ne, to daga nan ne Haidar da yaya Abba suka tafi America karatu. Bayan dawowarsu ne da za a bikin bude masa kamfaninsa da mahaifinsa ya bude masa to sai ya tafi garin mashi ya lalubo Faruk. Bayan bude kamfanin nasa ne dai suka ci gaba da zumuncinsu. To faruk din yayi aure yana zaune kusa da iyayensa Yau Haidar bai samu zuwa office ba don Abuja yake shirin tafiya, don haka tun tara na safe ya kammala duk shirye shiryensa ya nufi hanyar Abuja. A hanya ya lodar musu tsaraba. Bai samu matsala dangane da kwantaccen da ta yi masa, tun da ya san unguwar da suke zaune fitacciyar unguwa ce ta manyan kasa masu fada a ji ne. Kausar kuwa a na can an gama duk wani shirye shirye na taryar gwarzon masoyi. An gyara falo an kayatar dashi, ana jiran masoyi. Kausar ta yi wanka ta sha kwalliya da dandatsetsen less. wanda za mu iya cewa kwalliyarta ce, ta fito mata da kyau. Don kun san ba a mummunar mace sai marar gyara. don duk munin mace kwalliya sai an ga kyata. Don naka gyara da kwalliya shine mace. Kausar baka ce amma a yanzu da yake durfafi yin shafe shafe da mayuka 'yan kanti za mu iya cewa ta koma fara. Doguwa ce, tana da kiba da fati. ba ta da wani girman nono, kanana ne wanda har sun riga sun zube, amma wayayyiya ce ba ta shiga abin da be shafe ta ba akwai hutu da jin dadi rayuwar duniya. Haidar ya iso lafiya. "Ya kuke murna da rawar jiki a wajen Kausar. Tuni ta sa a ka shigar da Haidar dakin da aka wuni ana gyarashi don zuwasa. Tuni aka gama cika gabasa da kololin abubuwan ci da na sha. Can Kausar ta shigo cikin washe baki tana fara'a don bakin yaki rufuwa ta ta ho ta saurin ta ta zauna kusa da shi a guje ta rirrike hannuwansa, "Oh ni 'yar nan! Allah na gode maka da ka sake hada ni da abun sona, burin zuciyata wato Haidar, ubangiji yanda ka hada mu a nan yanzu ubangiji Allah ka hada mu a gidansa a dakinsa, a matsayin matar aurensa,. Ta shafa. Haidar ya ce, "Irin wannan doguwar addu'a haka to kada ki yi wacce za ki rike ni a gidanku na kasa komawa gida. Ta kyalkyale da dariya ta rinka zuba masa girke girgen da aka yi masa kamar ta ba shi a baki haka ta rinka yi masa. Suna dade suna hira duk wani dan gidasu sai da ya zo suka gaisa. Haka ya shiga ciki ya gaida Babarta da kishiyar babarta. Ta hau da shi falon sama har wajen babanta sai da ya ce, Baban nata yayi murna da ganin shi don ya yaba da hankain haidar a kan zai turo iyayensa don a yi maganar aurensu da Kausar. Babanta ya yi ta sa masa albarka inda Haidar din yake ta malala masa godiya. Haidar sun sauko daga saman sun dawo wajen hirarsu Kausar sai munrna take kamar ta goya shi. Ya sa yaron gidansu ya kawo musu tsaraba a but din motarsa ya yi wa kausar sallama don yana so ya tafi gida kada dare ya yi masa a hanya. Da kyar ta kyale shi ya tafi don gani take yi kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Haidar daga Abuja duk dumbin gajiyar da ya kwaso bai wuce gidansa don hutawa ba sai ya zarce gidansu, yanda ya shiga a hargitsensa Abba da Aunty suka san ba lafiya ba. Bayan sun gaisa ne ya koma gefe daya ya yi zugum da shi yana tunanin ta ina zai fara ne. Abba ya shi, "Haidar lafiya? Me yake faruwa ne? "Wallahi Abba abun da yake damuna ne na rasa ta inda zan bullo masa bare na gaya muku "Ba komai gaya mana ko meye, kana da wadanda za ka gayawa ne wandada suka fi mu? Ai ka ga babu ko? Gaya mana menene damuwarka?" "Wato Abba tun muna America akwai yarinyar da muka yi alkawarin aure da ita, to bayan mun gama na taho gida Abba kuka tayar min da maganar auren jawahir. Abba don kada na bata muku rai ne shi yasa ban yi muku maganar kausar din ba. Ita dai na gaya mata, na ba ta hakuri, to ta tashi hankalinta sosai, to shi ne na kwantar mata da hankalinta da cewar zan aure ta bayan shekara daya. da kyar Babanta ya amince mata shi ne yanxu kuma uban nata ya takura mata da maganar auren, nake so don Allah Abba ku bar ni na aure ta. Aunty kuwa ta mike tsaye cikin fada take nuna shi da yatsa, "Kai ka kiyaye ni, wallahi ka shiga hankalinka. A aura maka 'yar uwar tawa auren naku shekara daya ka ce za ka yi mata kishiya, to ba ka isa ba ka yi kadan jawahir ta fi karfin ka wulakanta ta." Abba ya daga mata hannu ya ce, "Aisha ya isa haka. Haidar tashi ka je gida tukunna sai mun yi shawara za ka ji komai. Ya mike, "To Abba na gode ku tashi lafiya. Aunty sai da safe ya wuce sukuku kamar wanda kwai ya fashewa a ciki Abbansa ya ce, ba a yin haka Aisha ki duba ki gani yaron nan ya yi mana biyayya lokacin da muka tursasa shi auren jawahir yanzu bai kamata ya zo da tasa bukatar mu ki biya masa ita ba, kin san 'ya 'ya amana ne a hannunmu duk da cewar mu muka haife su to idan muka zalince su Allah fa ba zai kyale mu ba sai ya tambaye mu, to kin ga dai bai kamata da farko mun bi son rainmu mun yi masa aure ya hakura sun zauna sannan yanzu ya kawo bukatarsa mu bi son zuciya mu hana shi, aikin ga ba mu dai dai ba bare lamarin aure da ba ayi masa katsalandan. Abun duniya duk ya dagulewa haidar duk dai da ya ga alamun nasara a wajen Abbansa, to Aunty fa Ai ita za ta zamo babbar matsala. Yana zaune a falon kasa jawahir ita ma tana waje daya zaune kan kujera tana yi wa Sayyid karatun Alkur'ani yana biyawa. Wayar Haidar ta fara ruri ya daga, "Hello Kausar ina gajiya. Ba gajiya sweety, yaya ka dawo gida? "Lafiya lau kausar ai na sha wahalar tafiya dag kano zuwa Abuja a mota kuma a dawo a ranar, ai akwai wahala. Ko da yake ba komai tun da Hausawa sun ce garin masoyi ba ya nisa, duk ranar da Allah ya mallaka min ke na fanshe wahalata...... Wani katutun bakin ciki ne ya tsayawa jawahir a zuciya, rainin hankali wato a gabana ma yake yi wa mace waya? wallahi bai isa ya yi min wulakanci ba, ina zaman dole a gidansa 'yar sakin fuska ba yayi min bare mu yi hira amma shi ne yake kyalkyala dariya da budurwarsa, kawai sai ta mike a fusace ya riga ya shagala da yin magana a wayar ta fizge wayar daga hannunsa ta doka ta da kasa. Wayar ta tarwatse sai ta ya daki a guje ta rufe kofa duk da haka sai ta fada gado ta sa kuka. (To in banda abun jawahir kukan me kike) Bari dai mu ci gaba labari mu ji me yake faruwa a zukatan guda biyun. Haidar ya bi wayarsa da take tarwatse kan kafet da kallo, "To me jawahir take nufi da za ta fizge masa waya? Kishi take yi ko kuma dai ta fara raina shi ne? Lallai zai yi wa tufkar hanci kada nan gaba abin ya shafi aurensa. Da safe ya gama shirinsa ya sauko ya nufi tebir don yin break ya ga wayam babu break bare alamarsa. Ya kwallawa sayyid kira ya fito da gudunsa, "Ina Antinka?" "Tana daki." "To je ka ka kirawo min ita." Ya kirawo ta ta fito yayin da ta durkusa, "Ga ni." Ke me ya hana ki yin break? Kina nufin haka zan tafi office da yunwa.? Kanta yana sunkuye a kasa ta ce, "Ai ca nake za ka biya ta wajen masoyiyar taka ka ci a can. Ke ba na son shirme kin ji ko, tashi ki je ki hada mana break. Bakin ciki ya ishe ta ba abin ta ce ba za ta yi ba ta sabawa ubangijinta. kawai sai ta mike tana kuka ta nufi kicin din. Sai tausayinta ya kama shi yarinyar tana burge shi ko don biyayyarta. Ta gama soya dankali da kwai ta dafa ruwan shayi sai dammaman kunun gyada da ta yi masa kofi daya kamar yanda yake sha lokaci lokaci. Za ta wuce daki ya yi kirata, "Ke zo nan. Ta dawo ta durkusa. Ya ce, "Ta so ki yi break. Ta girgiza kai na koshi. Ya daka mata tsawa. "Ta so mana jinkinta na rawa ta mike ya hada mata ruwan tea me kauri ya mika mata. Ya tura mata dankali da kwai da biredi gaba ya ce, "Ki ci da yawa ko yanzun nan ranki ya baci. Haka ta rinka ci ana hawaye yana kallonta sayyid kuwa ya tafi wajen Dela za ta yi masa wanka. Haidar ya gama break dinsa ya mike ya nufi office jawahir ta kifa kanta a kan tebir din ta ci kukanta ta koshi ta gama ta shafe hawayenta ta koma daki. Sayyid ya shigo an yi masa wanka ta shirya shi ya rinka jijjiga ta dole ta fito ta hada masa break ta koma daki. Zuciyarta tukuku take yi mata sam ta kasa samun sukuni a zuciyarta tun daga wayar nan da ta ji haidar ya yi, "Wato ma ina ruwanta ne da wayarsa.? To me yake neman faruwa da ita ne? ke wallahi na gaji da zaman banza a gidansa ya zo mu yi duk wace za a yi, na cire tsoronsa da shayin komai don ni mutum ce ba dabba ba yanda yake da a gidansu haka nima nake a gidanmu. Yau ma dai haidar daga office da ya tashi gidansu ya kuma waccewa a kan maganarsa ta jiya. Abbansa ya ce, Ka kara hakuri Haidar a bi komai a hankai ba a son gaggawa don gaggawa tana daga shaidan. Aunty ta ce, Alhaji ka rabu da yaron nan, nema yake ya tozarta mu ya bata mana zumunci to wallahi ba ka isa ka shiga tsakanina da dan uwana ba. Abba ya ce, "Haidar tashi ka je gida zan je na nemi Daddyn jawahir din na yi masa bayanin komai, na san shi mutum ne me fahimta ba zai kawo komai ba to daga nan sai mun shirya ranar da za mu je Abujan wajen iyayen yarinyar. Haidar ya rissina, "To Abba na gode Allah ya saka da alheri, ubangiji ya kara girma. Ba komai haidar kai dai ka rike amana kuma ka sawa zuciyarka adalci ya yi musu sallama ya tafi. Yau a falo ya samu jawahir tana kallon wasan Hausa. Be kalli inda take ba ya haye samansa. Ita kuwa daman a cike take ta shi jira take yi ya dawo su yi wace za su yi don ta gaji da zaman gadin gidansa. Sai da ta bari ya kammala dun wani abu dayake yi ya dawo falon kasan ya zauna yana duba jarida sannan ta fara magana ba tare da ta kalle shi ba. "Yaya yau dai magana nake son mu yi da kai. Ba tare da ya dago kai ba ko ya bar karatun jaridar ya ce, Uhm ina sauraronki. Ta ce, "Wai menene matsayina a gidan nan ne? "Bai dago kai ya kalle ta ba ya ce, "Matsayinki kike son sani? Ta ce, "Kwarai kuwa." "Ya ce, "In dai ba mantawa kika yu ba matsayinki yana na kanwata da kuma wai matata ta aure, don wai zance. Ta ce, "To in haka ne me zai hana ka sake ni ko ma huta daga ni har kai da wannan daurin da bai bayin da aka yi mana. Ya ce, mata, "Ai dama ba ni na gayyato ki ba in wanda ya kawo ki ya gaji da zaman naki za ki ga ya zo ya dauke ki. Zumbur ta mike tsaye ta rike kugu ta nuna shi da dan yatsa, "Kai bari ka ji, ni ba irin ballagazayen matan nan ne da ka saba wulakantawa ba, ni na fi karfin wulakancinka, ina bin ka ne gudun kada na sabawa ubangijina da kuma gudun wargajewar zumuncin iyayenmu da nake yi wa biyayya, to yanzu na gaji da zama da kai don ka san ba na son ka a ka ba ni kai, na yi hakurin zaman shekara a gidanka, to yau hakurina ya kare ba zan sake kwana a gidanka ba dole ne ka sake ni. Tana rike da kugu tana yamutsa fuska tare da girgiza jikinta na jin bala'i. Ya kalle ta daga sama har kasa, dariya ce ta kwace masa ya dai daure ya gintse dariyar ya ce, "Ni nan da kika ganni ba zan taba sakinki ba, in kin ga dama ki zauna in baki ga dama ba ki je duk inda za ki amma maganar rabuwa babu don ni ba wawa ba ne. Idan ba ki sani ba ma ki sani aure zan yi kwana nan. Ta dafe kirji, "Aure! Aure fa ka ce? Da gaske kake yi? Wallahi ba zan zauna a gidanka ba bare matar ta zo ita ma ta raina ni, ban da kaddara ma me zai sa na aure ka? Ni me santalelen saurayi da yanzu ina gidansa. Ya mike kuwa cikin sauri zai kai mata mari ta yi saurin kaucewa ya ce, "Ki yi a hankali duk san da kika sake fadar wani namiji a gabana da sunan yana sonki sai kin raina kanki. "Ya yi hayewarsa sama ya bar ta tana kuka. Haka kawai be yi min abun da na nema ba sannan ya ce aure zai yi, wallahi ba zan zauna ba tafiyata zan yi, duk abin da ma zai faru ya faru. "Da sauri ta fada dakinta ta kama hada kayanta tana zuvawa cikin akwati ta turo akwatin da kyar ta kirawo Dela ta ce ta bawa yaron gida ya sawa Haidar a but din motarsa. Cikin rawar jiki ta karbi aiken uban dakinta duk abin da ta san za ta bukata ta sa an kai but. Ta fito da shirinta za ta fita lokacin Sayyid ya tashi daga bacci ya ce, "Aunty ina zaki? Ni ma zan biki. "Ta shafa kansa,

Please Login or Register in order to submit comment