Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi me ya dame ni?" Ta dauko yogougt ta zauna tana yagar kazar tana korawa da nonon har ta koshi. Wajen sha biyu da rabi direba ya kawo Inna da kannanta Auwal da sani da su Hassana da Usaina kannan Haidar. Jawahir ta cukuikuye inna tana tsallen murna. Inna ta dube ta tana dariya ta ce, "Ke cika ni kada ki karasa ni, ni ina can zuciyata ta kasa sukuni sabo da tunanin yaya kwana ke kuma kina kokarin karasa ni. jawahir ta yi dariya, "Amma dai inna a nan za ku kwana ko?" Inna ta tabe fuska ta ce, "Ke ba na son hauka yanzun nan ma za mu juya. Hassana ta ce, "Allah Aunty ni dai gidanki ya ba ni sha awa zan kwana. Usaina ta ce, "Lallai kina so Yaya haidar ya yi tamaula dake kenan.? Jawahir ta ce, ba wani abu da zai yi mata kin ji Usainar nan wai don kar ta kwana, ba abin zai yi miki Hassana." Inna ta ce, "Babu wanda zan bari, kafata kafarsu. Auwal ya ce, "Su Aunty jawahir 'yan gayu. "Gaba daya sukai yi dariya. Sani dauko muku ragowar break din Yaya ku ci. Ta tashi ta shiga kicin ta kwaso musu yogouht da lemummuka da ruwan sanyi ta zube musu. Da ragowar gasassun kajin amarcinta. Inna ta gyara zama da jikokinta suka ci suka koshi. Inna ta kara yi mata fada da nasiha. Karfe hudu suka tafi. Jawahir ta mike ta yi sallah bayan ta idar ta shiga kicin ta dauki kaza daya ta yayyanka ta yanka albasa ta sa gishiri da citta da magi ta dora kan wuta. Ta debi kayanmiya yanda zai wadace ta ta markada ta dora ruwan kuskus. Ta gama hada soyayyiyar miyarta ta dafa kuskus dinta da ya sha karas da koren wake ya yi wara wara da shi gwanin kyau. Ta gasa kifi irin manyan nan ta yi farfesun kayan ciki, ta markade kwa kwa a ciki blinder ta tace ta sa madara, filebo, sukari ta hada lemo me dan karen dadi. Ta samu wasu kayatattun fulas ba irin na safe ba ta kuma jere komai a kai. Ta hau saman dakin nasa, ga mamakinta sai ta gan shi a bude ta gyara masa gadon da ya kwanta ta kade komai ta share masa dakin. Ta wanke bandaki ta goge ta kunna turarukan wuta ta fesa Air freeshner a kowacce kusurwa, ta sakar masa A.C Nan da nan sanyin dadi ya soma tashi. Ta rufo masa dakin ta sauko ta gyara falon kasa da nata dakin ko ina ta feshe shi da Air freshner da turaren wuta dan maiduguri ta saki labulayen ta kunna A.C ta rufe kofar falon ta shige dakinta ta rufe ta fada toilet don yin wanka Sai karfe biyar da rabi Haidar ya dawo gidan a gajiye ga yunwa da take azalzalassa don tun break din da ya yi bai sake cinn wani abun ba. Don shi Allah ya yi shi mutum ne mai kyankyami ba ko ina yake iya cin abinci ba. Megadi ya wangame masa get din ya shigo ya rissina ya yi masa barka da zuwa. Ya murda kofar falon ya shiga tare da yin sallama shiru kamar ba kowa a gidan. Daddadan kamshi ya bugi hancinsa, ko ina tsaf a share a goge ya ji gyara, ya yi sha awar yanda take da tsafta take kula da komai. Ya haye samansa yana tura kofar dakin, nan ma sanyin da kamshin dadi suka yi masa sallama. Ya sheka ya limshe ido ya yi godiya ga Allah, shi kansa falon saman nasa ta canja masa tsarin gyara wanda kuma hakan ya fi kyau yana shiga cikin dakin nasa sai kansa ya kwance, wani hadadden zanin gado ta shimfida masa , ai yanda ta dame gadon ya burge shi ya cire kayansa ya fada toitel ya fara wanka.Ya gama shirinsa ya sa kananan kaya. Sun karbe shi kuwa sun yi masa kyau. [07069210827: Ya feshe jikinsa da turaruka ya sauko kasa ya hau tebir ya bude komai, kamshin girkin ya buge shi sha awa da jin dadi suka bige shi. Ya zauna ya rinka dibar garar girki, yana ci komai na kan tebir din sai da ya ci da ya wa ya ci ya koshi ya yi hamdala ga ubangiji. Ya rinka tsiyayar lemon kwa kwar nan yana sha, don Allah daman hausawanmu sun iya hadadden lemo haka, amma muke bugewa kullum yawon siyen juice. Ya cika kofin tangaran da shi ya tashi ya koma kan kushin can gefe daya ya dauki jarida yana karantawa yana kurbar lemon kwakwar. Ita kuwa jawahir tana daki ba ta ma san ya dawo ba ta gama shirya kwalliyarta cikin riga da siket na atamfa kwali wax, rigar fitet ce 'yar firit,siket din ya yi tsantsan a jikinta. Ta dora daurin dan kwali wuyanta da kunnanta wani rantsattse fashion ne mai kyau. Ta feshe ilahirin jikinta da daddadan turaruka masu kamshi. Ta bude kofar dakinta ta fito kamshin da ya ji ne ya sa shi dago kai ya kalle ta, a ransa ya fada, "Yarinyar tana da kyau sai ka ce Aljana, ga shi ta iya gyran jikinta. Yanda siket din ya matse ta dole ta rinka takawa sannu a hankali gudun kada ta harde. Ta shiga kicin ta debo abinci a filet dan kadan sai ka ce wadda za tabawa dan yaye sai robar nono yogougt dake daya hannun nata. Ta zo ta nutse a cikin kujera ta dauki remote ta kunna T V. tashar CNN ta kunno, sannan ta fara cin abincin, yanda take diban abincin kamar ba ta son ci a yangance. Duk abin da take yi idon Haidar yana kanta, ita kuwa ba ta san ma ya dawo ba bare ta san yana falon. A zuciyarsa ya ce, "Yaushe dama za ta girma tana cin wannan dan mitsitsin abincin kamar na 'yar yaye. Can wayarta ta yi kara ta dauka, tana dubawa da murnarta ta dora a kunnanta, "Hello Dadyna. sai ta kunna (Handsfree) Daddy ya ce, "Jawahir yaya kike? Ya megidan naki? "Wallahi lafiya lau Dady muna zaune kalau. "Kina son masu aiki ne a kawo miki? Cikin shagwaba ta ce, "Lah Dady mai aiki, ni wallahi ba na son kowa su zo su yi batawa mutane waje. don iya girkinmu mu biyu da gyaran dakunanmu Dady ai duk zan iya. "To jawahir wanke-wanke fa, ga sharar harbar gidanku.? Dady ka san ba na son kazanta da gama girki nake wanke kayan na goge su na mayar inda suke. Harabar gidan kuma dakin saukar baki yana da yaro da yake gyara masa me bawa fulawowiyin gidan ruwa. "To jawahir wa zai rinka ba su abinci ko har da su za ki yi rinka yin girkin? Ta kara shagwabewa, "Uhm Dady wallahi ba zan yi musu girki ba, abincina daga ni sai Yaya kawai. "To shi ke nan jawahir za a samu haidar din na yi mishi magana na ji yanda za a rinka yi da su wajen ba su abinci." Cikin shagwaba ta ce, "Don Allah Dady kada ka yi masa magana ya zo ya ce sai na rinka girkin da su ka ga wahala zan sha. "To jawahir ai a karkashinku suke, dole ku rinka kula da hakkinsu ko to kwace kuma za ku bar su da yunwa. Cikin shagwaba ta ce, "Haba Dad. to Dady na yarda a kawo tsohuwa amma ba za ta rinka shigo min sashena ba, sai dai ta tsaya can bangaren masu aiki ta rinka da fa musu abincin, ai ya yi ko Daddy.?" "Yauwa ko ke fa jawahir gobe za a kawo ta, Ki kara hakuri jawahir ki dinga biyayya ga mijinki. Allah ya yi muku albarka . To Dad na gode, "good day Dad." Tayi ajiye wayar ta mike ta dau filet din ta shiga kicin. Haidar ya mike ya haura samansa ya yi dai dai a gadonsa yana tunanin hirar jawahir da Daddynta. A ransa yake cewa, "Ko dai don muna 'yan uwa ne halayyarmu da ra'ayinmu suke neman zama daya? Gaskiya ta burgeni da za ta rinka yi min komai da kanta, don ni na tsani gidan da me aiki take yi wa matar gidan da mijinta girki, amma jawahir tana da dadin murya ga dadin saurare, ban so suka gama hirar ta su ba. To haka da i zaman ya ci gaba tsakanin miskilan guda biyu. kowanne yana ji da girman kai da miskilanci babu wanda zai wa dan uwansa magana idan har sun hadu da safe za ta ce masa ina kwana. Yayin da shi kuma yake daukan lokaci kafin ya amsa da lafiya lau. To sai ta yi shigewarta daki ba ta fitowa har sai ya tafi. sannan ta zo ta gyara musu dakunansu ta turare da turaren wuta ta feshe ko ina da Air freshner ta zauna ta shirya musu hadadden girki me gamsarwa. Ta hada masa lemo da kanta kullum da sabon samfir din girki da lemon da take yi masa. Ba ta taba barin waje da datti ko kura ko ina fes a gyare dai dai da wanke kwanikanta ita take yin abinta. Ta gyara kicin dinta fes kamar ba a yi komai a ciki ba. Tukwane ne kawai da kaskon suya saboda maiko take bawa Dela me aikinta ta wanke mata Tun da akawo Dela take zaune a bangaren masu aiki za ta yi girkinsu su uku da maigadi da ita sai yaron gidan da ta yi gama za ta wanke komai ta share ta goge da yake ita ma me tsafta ce shi ya sa suke shiri da jawahir din. Haidar kuwa yana jin dadin yanda jawahir take da tsafta komai take kulawa da shi yanda ya kamata, don haka duk san da ya taso daga office burinsa ya yi sauri ya dawo gida don ya narki special din girki da jawahir za ta yi masa. Ya zauna a kayataccen falonsu yana shakar daddadan kamshin falon. Idan ya tashi daga office yana biyawa ta gidansu a gurguje yake yin komai don yana sauri ya koma gida. Idan Aunty ta ce masa ga abinci ya kan ce um Aunty sai na je gida zan ci. Duk da ba magana suke yi wa junansu ba, to amma hakan bai hana su kyautatawa junansu ba Ana yawan kawo mata kannanta Auwal da Sani da kannan Haidar Hassana da Usaina idan yamma ta yi direba ya mayar da su gida Yaya Abba ma da yaya Nasir suna yawan zuwar mata. Inna ma ta na kan zo amma ba sosai ba iyayensu ne dai har yau ba su zo ba. HAIDAR ya samu kwanciyar hankali don ba a bin da ya ke damunsa don haka jikinsa ya kara murjewa kyansa ya kara daduwa kowa ya kalli fatarsa ya san ta goge da jin dadin duniya ita kuwa jawahir da yake abincin be da meta ba to yanda take haka take babu wata 'yar kiba da ta yi. Shekara daya ke nan da yin auren har yau jawahir ba ta taba lekawa kofar gida ba. Yau asabar da jawahir ta kammala da hada break dinta ta diba ta ci ta gama gyara wajen ta sa turaren wuta ta feshe da gidan ta shige toilet ta yi wanka. Yau shigar turawa tayi 'yar bingilar shimi ta saka iya cibiya me siririn hannu sai dogon wando da ya dame mata cinyoyi da kafar wandon an bude shi ta hade gashinta a tsakiyar kai ta sa tafkeken ribon ta daure shi. Cikinta a dame kamar ba ta zuba masa abinci ba, fuskar nan tata sai fitar da sheki da wa ni asirtaccen kyau ta ke yi, ta gama feshe jikinta da tuararuka ta fito falon inda Haidar ya ke break ta durkusa ta ce, "Ina kwana?" bai juyo ya kalleta ba ya ce, "Lafiya lau. Ta mike ta isa bakinTV ta dauki takarda da biro ta koma ckin kujera zaman mutu daya ta kwanta tana rubutu. Tun da ta mike Haidar yake bin ta da kallo sai hadiyar yawu kawai yake yi ta yi mugun ba shi sha awa, hankalinsa ya tashi sosai. Ta gama rubutu a takardar ta ninke ta taso cikin nutsuwa ta zo gaban Haidar ta ajiye masa a kan tebir dinta ta juya ta koma daki, shi kuma ya bi ta da kallo. Sai da tashige daki sannan ya ware takardar ya fara karantawa . Yaya Don Allah yaya ina so zan je gidanmu da gidan inna da wajen Aunty. Ina so na taho da sayyid Autan Aunty idan ka yarda. Jawahir Yana gama karantawa ya ajiye ya ci gaba da yin break dinsa sai da ya gama sannan ya mike ya dauko takarda da biro shima ya rubuta mata kamar haka. "In kin shirya ki jira ni na kai ki da kaina, Sayyid kuma in kin ga ba zai takura miki ba kya iya daukoshi Haidar Jawahir duk ta matsu da ta ga amsar da zai ba ta. don ita dai tana so yau ta je gidajen nan ko dan dadewar da ta yi rabonta da fita . Ita jin kanta da miskilancinta ya hana ta ta fito bare ta ga amsar da ya rubuta mata , shi kuma girman kansa da isarsa ba za su bar shi ya kai mata ba. Sai da ya gama kallon sa da hutawarsa sannan ya koma sama. Sai da ta ji tafiyarsa ta fito ta dauki takardar ta karanta, aikuwa sai ta hau tsalle tana murna kamar yarinya. Nan da nan ta shiga shiri a kakale nan a kakale can ko ina ta yi fes kamar wacce aka karawa kyau. Wani dandasheshen less ta saka me dan banzan kyau da shegiyar tsada. Ta yi kyau kamar ka sace ta ka gudu don haduwar da ta yi. Ta kalminta da mayafinta da jakarta duk ruwan less din ne. Takalmin me tsinin dunduniya. ta hakimce a falon tana jiran futowarsa megidan Ba ta jima ba sosai ya fito cikin shiga ta wani danyen boyal baki sai sheki yake yi, hular kansa baka mai gashi, takalminsa baki sai agogon hannunsa na Daimond. Duk sun yi kyau kamar wadanda za su zaben sarauniyar kyau. Ya yi waje ba tare da ya kalle ta ba, ta mike ta rurrufe ko ina ta fito tana takawa sannu a hankali yana kallon ta ta mudubin motar, duk sha awarta ta motsa shi, amma saboda iya jan ajinsa ba zai taba nuna mata ba, ko ya bari ta gane ba. Ta kama murfin mota ta bude ta shiga baya ta zauna, be kalle ta ba kuma be yi mata magana ba be kuma ja motar ba. Ya yagi takarda ya yi rubutu ya cilla mata baya ta dauka ta duba, "Ba ki kai matsayin da zan zama direbanki ba, "Tana gama karantawa ta bude ta fito ta dawo gaban motar ta rufe. Ya kuwa figi motar a guje kamar me shirin tashi sama. Babu wanda ya yi wa kowa magana haka suke tafe sai da suka zo wani super market ya fita ya yo musu tsaraba suka ci gaba da tafiya. Gidansu ya fara kai ta, yana tsayawa ya mika mata takarda ta duba ta karanta a wa daya na baki ki yi ki fito mu tafi. Ba ta ce komai ba ta bude ta fita ta yi sallama falon ta shiga. Aunty tana ganinta ta mike ta taro ta da murna tana jawahir 'yata barka da zuwa 'yata ta kaina." Ta rungumeta ta a jikinta, "Zo mu hau sama Alhaji ya ganki tukunna, "Suka hau ta durkusa har kasa ta gaida Abba cikin fara'a da murna yake amsawa, "Jawahir ke ce haka? lallai yau zan huta da mitar Auntynki." Aunty ta ce, "Wa ya kawo ki ne? ko kun dauki direba ne? Cikin jin kunya ta ce, "Ai yaya ne ya kawo ni. Tana rufe baki ya yi sallama ya shigo kai tsaye ya wuce gaban Abbansu ya zauna ya gaishe su. Abba ya dafa kan Haidar ya ce, "Yau na ga jawahir na gode muku da yanda kuka rike kanku ba ku mu kunya ba. Haidar ya ce, Yanzu ma cewa ta yi na kawo ta za ta dauki Sayyid ga shi ban gan shi ba. Aunty ta ce, jawahir ta Sayyid ai yanzu ba irin da ba ce da kike zuwa ki dauke shi ya yi kwana da kwanaki a gidanku yanzu ai sai ya takuraki. Cikin jin kunya ta ce, "Lah Aunty wallahi ba komai ai ba zai takura ni ba. To shikenan gobe za a kawo miki shi ya yi kwana biyu kawai. Ta ce, to Aunty na gode. Aunty da kanta ta kawo musu abubuwan ci da sha suka sauko kasa da Aunty. Duk yanda Aunty ta yi don ta ji ko da wani abu a tsakaninsu amma jawahir ta ce kalau suke. Haidar ya shigo ya yi wa Aunty sallama ya fita jawahir ta kalli agogon hannunta ta ga awa dayan da ya ba ta saura minti uku ta mike ta ce Aunty zamu tafi. "Haba jawahir tun yanzu? Ta ce, Ai za mu bi ta gidanmu da gidan inna. "To jawahir na gode Allah ya yi muku albarka. Manya ledoji biyu Aunty ta ciko mata da kayayyaki. Abba kuma ya ba ta dubu ishirin. Daman Haidar ya sa maigadi ya shigo musu da tsarabarsu. Ta bude motar ta shiga awa dayan ta cika dai-dai shi ma ya shigo suka tafi. Gidan Inna ya kai ta shi ma sai da ya ba ta takarda ta karanta kar ki wuce awa daya. Ta shiga gidan inna murnarta da tsallenta ta cukuikuye inna. Inna ma murna take yi ta zaunar da ita "Daga ina haka? ke me Haidar din yake baki kika sake zama baturiya haka sai dai rashin kiba amma kin kara kyau ko dai ciki ne dake? Daidai shigowar Haidar a zuciyarsa ya ce, "Ciki yaya za ayi ayi ciki yanzu ai ta yi kankanta. Ya yi sallama falon ya shiga inna ta tare shi da murna duk bakinta yaki rufuwa ganin jikokinta shar dasu babu wata alamar damuwa a tare da su. Inna jikinta sai rawa yake yi ta rasa inda za ta sa kanta don murna, ta kawo musu wancan ta kawo musu wannan tana ta hira. "Dan ka'ida bature ya duba agogo saura minti biyu awa daya ta cika Haidar ya yi wa Inna salllam ta rinka yi masa godiyar wannan uwar tsarabar da suka kawo mata. Ya fita ya koma mota yana jiranta. Sai hira kuma ta dawo sabuwa tsakanin inna da jawahir har ta manta da dan ka'ida lokacin da ya ba ta, to tana ta shan labarai da abubuwan ban dariya daga inna. Ba ta yi aune ba ta ga kara minti arba'in da biye a kan awa dayan da ya ba ta zumbur ta yi ta mike inna za mu tafi sai kin zo. Inna ta ce, Au ba sai magariba za ku tafi ba? "Ta ce, "Uhm yana mota yana jira na. "To shi ke nan na gode ku gaida gida. Allah ya yi muku albarka. A cikin mota ta same shi ya kwantar da kujera ya na shan A.C da sautin rediyo ya lumshe ido kamar mai bacci. Ta bude mota ta shiga ta zauna. Ta fi minti goma ba shi da niyyar ta shi bare ya tuka motar su tafi. Ta gaji da jira ta ce, "Yaya na fito. Ya bude ido daya ya ce, Awa nawa na baki.? Ta ce, "Awa daya." "Sai yanxu awa dayan ta cika.? "A'a Inna ce ta tsayar da ni da hira." "To kin cinye lokacin da za ki yi a gidanku, yanzu gida za mu tafi sai wani lokacin kuma." Gabanta ya fadi, duk da dokin da take yi na zuwa gidansu ga shi ta fito din amma ba damar zuwa gidan nasu. Ita girman kanta ba zai bar ta ta ba shi hakuri ba bare ya hakura yakai ta. Kawai sai ta ji hawaye yana zubo mata. Haidar na kula da ita amma sai ya dauke kansa ya ci gaba da tukinsa kamar be san tana yi ba. Tana kukanta har da shassheka amma sai ya karo rediyon ma don kada yaji kukan. Ba wanda ya sake cewa da kowa komai har suka je gida Yana tsayar da motar ta bude ta fito tana goge ido ta bubbude ta shiga dakinta ta fada gado ta yi rub da ciki ta ci kukanta ta koshi. Ta shiga ban daki tayi alwalla ta yi sallar la'asar zuciyarta tana ta zuga ta da kada ta yi masa girki don ya dan dani bacin ran da ta ji, to kuma sai ta yi wani tunani ai ita ta fara bata masa kuma girman kai ya hana ta neman afuwarsa to idan ba ta yi masa girki ba ai ta dada shiga hakkinsa kuma ita ba iya cewa za ta yi ya yi hakuri ba, kuma zai yi bacin ran da ya fi nata, ita kuma ba burinta ke nan ba. Duk da irin zaman da suke yi na rashin yiwa juna magana to amma ba ta so ko kadan ta ga ta bata masa rai. shi yasa kullum take yin abin da ta san zai ji dadi. Ta mike ta fito falo takarda ta gani a ninke, "Na fita unguwa sai magariba zan dawo," Ta yaga takardar ta fada kicin ta dora girki . Yau tuwon samovita ta yi miyar danyan kubewa da ta burge kaza a ciki. Sai ta gasa masa dan shila ta soya masa kifi ta hada masa lemon abarba ta jere komai a tebir. Yau Dela ta bawa wanke wanken don zuciyarta a bace take. Kafin ya dawo ta gama abin da take yi ta gyara wajen ta shige dakinta ta kulle kofa. Sai da ya yi sallar magariba sannan ya shig, ga mamakinsa sai ya ga tayi abinci a zatonsa yanda ya bata mata ba za ta yi girkin ba, har yana shirin fita Hotel ya siyo musu. Duk kuma sai ya ji tausayinta ya dame shi a ransa sai ya yi da yasanin bai ki kai ta gidan nasu ba. Ya zauna ya ci abincinsa ya koshi yau har da senti ya mike ya je ya sake alwalla ya yi sallar isha'i. Haka ya yi zaman falon har goma na dare amma bai ga fitowar ta ba, abun ya dame shi dan be ji dadin yanda ta takura kanta ba. Haka tai ya hakura ya je ya kwanta zuciyarsa ta na ta tunane tunane. "Washegari da safe da ta gama komai da ya shafe ta ta daddasa kwalliyarta yadda ta saba ta fito yana tebir yana break ta durkusa ta ce, "Ina kwana.?" Ya amsa, "Lafiya lau jawahir kin kwana kalau.?" "Lafiya kalu." Ta ce ta mike tana koma daki tana mamakin canjin yau da ta samu na sakin fuskar Haidar. Har ya fadi sunanta ba tare da ya ce mata kwaila ko tatsitsiya ba. ******* ******** ****** ******** Haidar bai dade ta fita ba direba ya kawo Sayyid, jawahir ta yi murna da farin cikin ganin sayyid don ta samu abokin debe kewa. Sai magariba Haidar ya dawo sayyid yana jin karar motarsa ya fito a guje ya tarye shi, Haidar ya dauke shi ya rungume shi, "Auta wa ya kawo ka? ina ka baro Auntyn taka? "Tana gida Abba ya ce kada na dade kwana biyu zan yi." Haidar duk ya gama wani abu da zai yi na game da cin abinci, wanka ya sa kananan kaya na shan iska ya haye saman gado yana shan surutun Sayyid da yake ba shi dariya. Wayarsa ta fara ruri alamar ana kiransa. Haidar ya duba ya ga bai san lambarba ya share ya ki dauka, ta katse dan kanta, can aka sake bugowa be dauka ba ta kuma katsewa. Sai da aka yi sau biyar a na shi dan Haidar ya gaji ya dauka, "HELLO. Ya amsa a kasan makogaronsa. Cikin doki Kausar ta amsa, "Ranka ya dade saraki har yazu mulkin yana nan ne ba a sauke ba?" Ya ce, "Wake magana ne? ko sai na ajiye kan wayar ne.? Ta ce, "A'A ayi hakuri

Please Login or Register in order to submit comment