Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kama ku to Allah
ya raba lafiya, Ubangiji ta sa masu amfani ne ya
bamu masu albarka, don Hafsat tana can da nata
tsohon cikin.
Kai mutumin lallai kayu aiki, to Allah ya inganta
mana, Ubangiji ya raba su lafiya da shi. Bayan sun nutsu sun huta suka bude tsarabobi suka rinka bin
'yan uwa da dangi suna rabo kowa aka bashi
tsaraba sai ya jinjina kudin da aka kashe masa.
Jikaken abu mai muhimmanci da tsaraba da mutum
sai yaga kamar shi suka yiwa tafiyar. Anty Maryam
ma da Uncle har gida suka zo yi wa su jawahir barka da kuma yi musu sannu da zuwa.
Da yake hutun su suka dakko zasu dade a nan a
gidan Ankul din suke zaune wanda ya zauna farkon
aurensa kafin aiki ya maida shi Abuja.
Jawahir ta
sha murna da ganin Antyna Maryam ta rungume ta suna ta dariya cikin jin dadi da walwala kamar sa
hadiye junansu.
Anty ki ce kin kusa haihuwa don naga cikin naki ya
yi tsini da yawa."
Ta ce "Haka Ankul dinki yake cewa wannan cikin
ya fiye girma da yawa wai yana takura shi don na fiye langwai.
Jawahir tasa dariya ai gaskiya Anty sai yanzu na
gano sirrin da ya sa Ankul ya ke manne miki ko, na
ce ku ke manne wa juna, ashe haka rayuwar aure
take?
Hakika jawahir rayuwar aure aba ce mai dadi da nishadantarwa kwanciyar hankali da samun
nutsuwa. Amma fa duk wa 'yannan abubuwan
basa samuwa sai ka yi da ce da abokin rayuwa
nagari."
Haidar ya yi sallama ya shigo tare da cewa da
Maryam "Antynmu ai kin yi nauyi da yawa, da kin hakura da zuwan da sai muzo har gida mu gaishe
ku."
Ta yi dariya tare da cewar ai bazan iya jure rashin
ganin diyata ba, yanda ake yi min zuzutun kara
kyan da tayi amma da nazo ai na gani idona ya
gane min kyakkyawar kulawar da ka yi ma 'yata. Ya yi murmushi ya kalli jawahir ya ce, "Bebina zamu
fita da Ankul xuwa dare zamu dawo." Ta
marairaice fuska kamar mai shirin kuka ya dafa ta
"Haba bebina mene ne kuma bana so ki bata ranki,
ba ga Antynki nan zata taya ki hira ba, sai mun
dawo zai dauke ta su ta fi. Ta yi murmushi yayin da ta juyo ta kalli Anty maryam. Ta ga ita ba ta saurari
su ma, hankalinta yana kan littafi tana karantawa.
Haidar ya riko ta suka yo falon tsakiya ya zauna a
kujera ya dorata kan cinyarsa "Meye damuwarki
babyna?
Ta yi rau rau da ido har sunkawo kwalla ta ce "Ni ba komai va ne ina tsoron kada Ankul ya sake
cewa ka dawo da Kausar ne, ba zan jure ganin
kana yi mata magana ba bare har ka shiga dakinta
ka kwana mun zama mu biyu da matsayi daya a
wajenka ta saki kuka.
Haidar ya rungume ta yana rarrashinta. "Kar ki damu Bebyna, daman can kaddara da
sha'awar kare kaina daga zina ita ta sani auren
Kausar, ki sa a ranki tsakanina dake mutu ka raba ne
takalmin kaza aurenmu auren zobe ne ba saki
ba yaji ba kishiya har avada.
Kuma na ji wai SULAIMAN BOMBOY za ta aura. Ta ce, "waye kuma SULAIMAN BOMBOY?" Ya ce wani yaro
ne dan karami amma ya nace wai shi a lallai sai ita.
Ta ce, "Um. Ta dako kai da sauri "Allah yayana?
Ya ce, "Sosai ma kuwa ta yi saurin kankame shi
tana sumbatarsa, cikin murna ya dako ta yana
dariya muje kada Ankul ya gaji da jira. Suka fito babban falo jawahir ta ce "Ankul ka bar
min Anty ta kwanar min anan." Ankul ya girgiza kai
ya ce, jawahir kenan har yanzu
dai kina tare da kuruciya, to idan haihuwa tazo
kuma cikin dare ku yi yaya da ita, ku da kuke duk
farin shiga? Gaba daya suka sa dariya suka fice ita kuma ta
koma gun Anty maryam suka bude shafin hira. "Kin
gane ne Anty ni fa yanzu abun da nake tsoro
kada Haidar ya dawo da kausar don ban san yanda
zan yi ba, a da ban damu da aurenta sosai ba don
sannan ban damu da Yayan ba, amma anya yanzu yanda nake son Yaya Haidar muka shaku da shi
yake sona yana ririta ni yana tarairayata kamar kwai,
zan juri ganinshi da wata matar, wai! Naga
mace a rungume a kirjin Haidar, subhanallahi Allah
ma ya kiyaye, Anty ai wuka zan soka mata ta mutu
nan take. Maryam ta tuntsire da dariya ta ce "Allah ya kiyaye
jawahir," Anty maryam ta ce "Ai na gaya miki wasu
matan su suke jawowa kansu ake yo musu kishiya,
na farko akwai matan da girman kai da ji da kai
tsabagen muskilanci ya yi musu yawa, to yawanci
masu irin wannan halin sai ki ga har mazajensu na aure su ke yiwa ko suna mantawa a karkashin
mazajen su suke? Dole mazan su ne gaba da su, dole
ne duk matsayinki da jin kanki, ki sauke su ki
yiwa mijinki biyayya ko dan ki samu tsira ma ranar
gobe kiyama, domin aljannar mace ta na tafin kafar
mijinta sai ya daga zaki shiga. Abu na biyu kuma shine, kazanta, sai ki ga mace awaje dagwas
dagwas da ita amma da zarar ta yi aure ta haihu sai
kiga ta zama kazama. Ba za ta tsaya ta tsabtace
kanta ba bare abincinsu ko abin shansu.
Wasu matan za ki ga kudin da aka ba su na cefane
a ciki zasu raga su boye baza su yo cefanan na duka ba bare su sarrafa girkin yanda zai yi dadi. Sai
mace tai abinci garau garau ba wadataccan kayan
miya bare mai kiji abinci kadas babu dadi abinci
babu kyau a fuska.
Bayan ta gama girkin ba ta san tai wanka ba ta
gyara jikinta, a'a sai ki ganta daga ita sai daurin kirji tana ta fama da kaurin wuta. Da kin doshi dakinta sai
zarnin fitsarin da warin dauda. Kin kai wa namiji
abinci ya yi cokali biyu ko uku ya ji ya kasa ci ya
ture saboda rashin dadi.
Baruwanki da kwantar da murya bare ki bincike
shi me ya hana shi cin abincin, a'a ke babu ruwanki sai ki ja kwanon gabanki ki kama ci ko ki kirawo
yaranki ki ce kuzo ku dau abinci babanku ya rage,
babu ruwanki da damuwarsa.
Idan dare ya yi kina kwance cikin yaranki kin saki
baki kina munshari kin bude nono kin saka wa
yaron da kike goyo a baki kin riga kin sabar masa, sai da nono a bakinsa zai yi bacci, da maigidanki ya
zo ya taba ki don ki taso yana da bukatarki ki kama
miya kina faman zumburar baki ke an takura miki
kin gaji, daren ma ba za'a barki ki huta ba, saboda
Allah mijin nan naki waliye ne da ba zai bukataci
mace ba in har Allah ya kare shi daga sharrin zina? Ai kuwa dole ya yi kokarin karo aure ko dan ya
samu me debe masa sha'awa.
Jawahir ta ce, "Yanzu Anty kina ganin wa'yannan
dalilai zasu taimaka wajen yo wa mace kishiya?
Anty maryam ta ce "Kwarai kuwa ai wadannan su
ne kan gaba, idan mace ta zamo bata daraja mijinta bata ganin mutuncin iyayensa tana wulakanta masa
'yan uwa da abokanan arzikinsa to yana kara
aure gudun kada ta rusa masa zumunci da 'yan
uwansa.
Jawahir ta ce, "To ai Anti in kika yi la'akari da wasu
mazan kwata kwata ba su san darajar mace ba, sun dauki mace baiwarsu abar korewa sha'awarsu, don
wani namijin zaki ga namiji yana wasa da
dariya a waje ki ga yana tayiwa 'yan mata fara'a
yana jansu da wasa, amma da zarar ya shiga
gidansa sai ki ga ya koma kamar mala'ikan
mutuwa ya murtuke fuska babu alamar fara'a bare wasa, da ya ci karo da kwano ko wani abu nata
akan hanya zai bal da shi, kuma yana da rufin
asirinsa amma sai ya ba wa iyalansa dan kalilan din
kudin da ba za su wadaci girkin gidansa ba, ba
ruwansa bai damu da matsalar da suke ciki ba, bai
ja su a jikinsa ba, bare su saki jiki da shi har su dinga bayyana masa damuwarsu. Anty duk irin
wannan ai rashin adalci ne da sanin
darajar mace ko?
Anty maryam ta ce "Haka ne jawahir amma ni a
ganina idan Allah ya hada ka zama da irin
wa'yannan mazan to sai ka iya zama da su. Na farko mace ta dasa wa zuciyarta hakuri, ta zamo
mai juriya da tawakkali, na biyu ta kasance me
yawan ibada tai ta addu'a tana kai kukanta ga
Allah, na uku ta samu sana'a komai kankantarta
kada ta raina ta ta rike ta hannu biyu.
Na hudu ta zamo mai kyautata masa da yi masa biyayya ko dan ta samu tsira ranar lahira. Na biyar ta
kasance me tsafta da kwalliya da kasancewa
cikin kamshi. Na shida ta kasance cikin koyon iya
kissa da kwantar da kanta tana kaskantar da kanta
ko yaushe tana nuna masa shi ne sama da ita, na
bakwai ta kasance doluwa marar wayo ta zamo me kau da kai da duk wani abu da zai mata, na takwas
ta zamo mace me iya kula da rayuwarta wato tana
cin abubuwan da za su kara mata ni'ima a jikinta.
Na tara mace ta iya kwanciyar aure ta gano wace
irin kwanciyar aure mijinta ya fi bukata, me da me
da me mijinta ya fi sha'awa a jikin mace, sai ta rinka gyara nata yanda zai rinka daukar hankalinsa yana
bashi sha'awa ba tare da na mace daban ya burge
shi ba.
.
SALON SO
PART 38
.
. Abubuwan da mace zata ci su kara mata ni'ima ba lallai sai ta fitar da kudinta
ta sai masu tsada ba, a'a daidai ruwa daidai tsaki, kada ki ce to ke ma ina kika
ga kudin bayan ba baki yake yi ba, ke ba wani abu da za ki siya don gyara
kanki.
To gaskiya wannan rashin wayo ne ai kan ki zaki gyara duk sanda namiji ya
kusance ki ya ji ki zam zam da ke, tsindum da ke dole ne ya rinka tattalinki ya
na baki kyakkyawan kulawa saboda yana son biyan bukatarsa. Amma ke baki
gyara kanki va, kin zauna gundin murhu duk wuta ta kone miki dan ruwan da
yake jikinki, mijinki ya zo ya ji kamas, saboda Allah me kike ganin zai faru?
Dole darajarki ta ragu idonsa, amma idan kika dage da shan su lemo, kankana,
rake, aya gwanda, ayaba, dabino, cukui, inibi, zogale, zaitun, tumatur, kwakwa,
zuma, nono, madara, gurji, dafaffiyar gyada, da sauransu duk irin wannan ba
karamin taimaka mana suke ba na kara mana ni'imar jikinmu.
Ko nera koma ki ka bayar a siyo miki dan kifi ki yi romonsa da kayan kanshi da
alvasa da tumatur kika watsa wake a ciki ya dahu luguf da dan alaiyahu ki yi
shi romo romo shi ma yana taimakawa, ki sami danyar gyada gwangwani daya,
aya gwangwani daya, waken suya gwangwani daya, alkama gwangwani daya, ki
hada ki jika a markado miki ki ta ce shi kamar gasara ki rinka damawa kina sa
madarar ruwa kina sha za ki ga yanda zai taimaka miki ya sakar miki da ni'ima
a jikinki.
Kinga abu mafi sauki idan kika sami ayarki kika jikata ta juku ki ka kai markade
kizo ki tace kayarki ki kara sikari ki rinka sha zata kara miki ni'ima sosai.
To kinga iri iren abubuwan nan idan mace tana yi zata taimaka wa kanta don
kare wulakancin namiji. To idan kuma ta iya gamsar dashi ta san sirrika na iya
kwanciya da da namiji to zata mallake shi a hannunta har a rinka zargin ta
asirce shi ne.
Jawahir ta ce, "To Anty me zai hana murubutanmu ba za su rinka wayar wa da
mutananenmu kai ba, ko dan sanin irin wannan sirrikan kwanciya don su ma su
mallaki mazajensu a hannu a daina yawan mutuwar aure? Maza su daina fita
bariki neman matan banza su rinka tsayawa iya matansu na sunna kawai?
"To ai jawahir matsalar da ake samu kin gane ne, marubutanmu suna iya bakin
kokarinsu na ganin cewar sun ganar da yawancin mutane yanda rayuwar jin
dadi ta aure take, to amma kash! Wani abu da ake kuka dashi wai sai ace suna
bata tarbiyar yara, wai yara kanana suna diban lattattafai suna karantawa, suna
ganin abin da bai kamata ba, wanda gaskiya ni kuma ina ganin ba haka ba ne,
domin idan kinga yarinya ta lalace to dama can lalatacciyarce iyaye suna ina
'ya 'yansu suke fita su shiga gidan amare su rufe kansu suna ganin kaset din
blue film ko America, ko ibo, ko fim din Turawa da yake bayyanar da tsiraici
karara da yanda ake nuna soyayya ta kazamar hanya. Wasu ma tare da samari
suke gani to meye ma ba zai faru ba wajan wannan kallon wa'yansu yaran
kuma da ake batawa ba su da wayewar kan ma da za su yi karatun littafin ake
jansu ayi musu fade, shi kenan hanyar lalacewarsu ta samu.
Wasu yaran kuma rashin kulawa ta iyaye da rashin sa ido akan harkokin su ne
yake jawo hakan, wasu tsabagen kwadayi ne da rashin kamun kai da zubar da
tsantsar da darajarsu ta 'ya 'ya matar ne take jawowa.
Gaskiya bazan taba yarda ace wai karatun littafi yana sa 'yan mata suna
lalacewa ba, saboda duk wata mace da ta san darajar kanta to in har ta
karanta littafi ina ganin zata yi kokarin kare mutuncin kan ta ta yi kokarin kai
budurcinta gidan mijinta, saboda ta karanta littafi taga yanda daren farko ya
kasance ga yarinyar littafin, mijinta ya same ta a cikakkiyar mace ta ga irin
tarairaya da
Kulawar da yake bata taga yanda yake sa
mata albarka har da wata dunkuleliyar kyauta da ya yi mata, to ni a ganina
kowace budurwa zata yi sha'awar hakan har ta yi kokarin kai budurcinta gidan
mijinta
Abu na biyu 'yan matanmu za su iya koyon kissa da shagwaba da kalolin girke
girke da yanda ake tarairayar namiji, zasu san abubuwan da suke kara wa mace
ni'ima wanda za su fara tsuma kansu tun kafin su shiga gidan auren, domin
idan ba'a littafin ba babu in da za su sami hakan saboda al'adar Bahaushe da
kunya babu uwar da zata iya zaunar da 'yarta ta koya mata wa'yannan
abubuwan don zata yi mata aure, za dai ayi wa 'ya fada ki bi mijinki ki yi masa
biyayya, to kin je kina ta biyayya yana wulakantaki ke baki san dalili ba to duk
wa'yannan abubuwa ne da bakya yi, amma aure ya samu tattali kissa biyan
bukata, shagwaba, ladabi da biyayya, iya girki, iya kwanciya, amfani da turaruka
masu kamshi da na tsugunno, ta cikin ikon Allah za'a samu zaman lafiya da
fahimtar juna a cikin aure.
Shi turaren tsugunno ana amfani da shi ne wajen turare gabanka ka tsugunna
akai hayakin yana shiga ciki to yana kara hade mace ne ya matse ta kamar
amarya.
Jawahir ta kawo gauron numfashi ta ce, "Anty na fahimce ki Allah ka ganar da
yawancin al'umma ko a sami zaman lafiya a tsakanin ma'auratnmu"
"To amin Jawahir."
Ba jumawa Haidar da Ankul suka dawo suka ci abinci. Ankul ya ce da Anty
maryam ta tashi su tafi gida akwati guda jawahir ta yo wa Anty na tsaraba ta
dakko ta kawo mata suka rinka godiya tare da sa albarka.
Sai da Haidar da jawahir suka yi sati biyu a gidansu suna hutawa basu da aikin
yi sai wasanni da junansu su ci cima me kyau su sha me kyau suke ta sutura
me tsada su bada kamshi su manne da junansu suna faranta ran juna.
Yau sun cika sati biyu da dawowa don haka yau Haidar ya fara fita xuwa office,
jawahir duk ta damu kamar wanda zai je ya yi kwanaki a can sai da ya
lallabeta har da yi mata wayo sannan ya fice. Da yake ya dade rabonsa da
office din dole ya samu ayyuka kaca kaca sun yi masa yawa shi yasa bai samu
sukuni ba, sai na fadawa aiki kawai.
Haidar yana tafiya kuwa jawahir ta dauki mota ta tafi wani hadadden gidan
gyaran jiki tsadadde na 'ya'yan wane da 'ya'yan wance, aka yi mata gyaran
gashi aka gyara mata farce aka wanke kafar aka rangada mata kunshin fulawa.
Jikinta ya sha dulka da halawa, jikinta da fuskarta sai wani santsi da taushi
yake yi kamar auduga yana fitar da wani sihirtacce na kyau.
Tana komawa gida kicin ta shiga ta feraye doya ta dora a wuta ta debo
manyan busashen tarwada ta farke cikinta ta kan kare ta kwara masa ruwan
zafi.
Ta hade markade iya ta yi mata abu landa doyar ta dahu ta tsame ta mika wa
iya ta daka mata sakwara, ta hade miyar busashen kifin nan da ta ji onga, kori,
reko, mai da sauren kayan da su ke sa girki armashi, sannan ta cuko zallar
tsokar nama a firinji ta tafasa shi da albasa gishiri da dan magi.
Bayan ya tafasa ta kwankwatsa attaruhu albasa ta dakko tafasashen naman
nan ta hada a turmi ta daka.
Ta ciro shi ta rinka dunkulawa ta fasa kwai ta zuba gishiri onga reko ta dora
manta a wuta ya dau zafi ta rinka daukan dunkulan naman nan tana tsoma sha
a rwan kwan tana sa wa a manta na soyawa, ta gama wannan ta zo ta yanka
salak ta yi masa wanki sosai ta zuba a filet, ta yanyanka tumatur da albasa ta
gewayesu a saman salak da albasar ta kawo dafaffiyar hantarta da ta yi mata
kananan yanka ta zuba a kai.
Bayan ta yada salak, cream ta zuba heinze beans a tsakiya duk wanda ya kalli
hadin salak din dole yawunka ya tsinke, ta debo kayatattun fulas dinta ta zuba
komai taje ta jere su a santara tebir.
Ta debo fararen gobarta manya ta markada ta tace dusar ta markada kankana
da gwanda da ayaba a duk ta tace dusar ta hada akan ruwan gwaibar, ta
daddara rake ta matse ruwan ta hada akai, ta zuba ruwan kwakwa da ruwan
markadaddiyar aya ta zuba madarar ruwa gwangwani biyu ta kawo zumarta me
kyau ta zuba a ciki ta juya ta saka a firinji.
.
SALON SO
.
PART 39 .
.
.
"Subhanallahi! Lallai jawahir kin hada kyakkywan
lemo mai saurin saukar da ni'ima a jikin ta bar wa
iya rama ita kuma ta kara gyara falon da dakin megida ko ina ta turare shi da daddadan turaren
wuta na kamshi kowacce kusurwa ta feshe ta da
Air freeshner.
Ko ina ta sa ka AC sai sanyin dadi ne yake fita ta
gyara toilet ma shima ta turare shi da daddadan
kamshi, ta rufe sashinsa ta fito ta sakko ta shiga nata sashen ta sake gyarawa ta saki kamshi ta fada
toilet don yin wanka, ta dade tana murzar jikinta da
daddadan sabulu ga ruwan wankan nata ya sha
turaren wanka sai turarin kamshi ne yake tashi
Uku da rabi ta fito daga wanka ta dauro alwala ta
zo gaban mudubi ta fara tsara kwalliya shafa nan goge nan ko ina ya yi das, ta fara gabatar da sallar
la'asar, ta tsara kwalliya da wani pink din les mara
nauyi sai dai anyi masa shafi a ciki, duk da rigar fitet
ce ta dan fara kamata ko don cikin jikinta de da ya
fara bayyana, duk wata gaba ta jikinta ta mulke ta
da turaren kamshi, ta fesa na fesawa ta daura dan kwalin les din ya lafe kan gyaran gashin da ta yi.
Gaskiya ta yi kyau wannan da gasar sarauniyar
kyau zata je babu abin da zai hanata lashe gasar. Ta
dakko turare tana sake fesawa, daidai lokacin da
Haidar ya shigo da kyar yake daga kafa don
tsananin gajiya da yunwa tun break dan safe. Ya zube a kujerar falo yana mai nishi, "Bebina."
"My love." Jawahir ta fito daga cikin daki ta zagayo
gabansa idonsa yana limshe kamshin turarenta da
ya ji ne ya sa shi bude ido.
Subhanallahi, duk kyan jawahir sai yaga yau tafi
kullum kyau kamar wata fure aka dasa don kyau tuni gajiyar da ya kwaso ta ware, ya jawo ta
cinyarsa yana yi mata wani fitinannen kallo mai
tada sha'awa da raunannar zuciyar mai bege.
Ta sa hannunta ta rufe masa idon ya ciji hannun
nata ta yi saurin janyewa ta langabe kai cikin
shagwaba tana 'yar kara tare da yarfe hannun nata.
Shikuwa Haidar tuni ya samu damar zira harshensa
a kyakkyawan bakinta, ya dade yana sumbarta ta
cikin shaukin so da igiyar bege da kyar ta zare
jikinta sakamakon wani nishi da ta ji yana yi gudun
ka da ta jawowa kanta jan gwam ta yi saurin haye wa samanta ta fada toilet dinsa ta hada masa ruwan
wanka, tana fitowa daga toilet din taga ya shigo
idon sa duk ya yi ja saboda fitina, ya sake jawo ta
ya mannata a jikinsa ya sake rungume ta ta
langabe cikin shagwaba take cewa, "My love ka je
ka y wankan kai muke jira fa Bebinka be ci abinci ba. Ya yi saurin cika ta ya dago kai yana shafa cikin
"Haba don Allah me yasa za ki bar min beby da
yunwa kina so ya galabaita ne, taho muje na fara
baki abincin tukuna, in kin koshi nayi wankan. Ta
make kafada ta ce um um ni dai ka shirya muje mu
ci tare. Ya jata ya zaunar da ita a gefen gado, to zauna nan yanzun nan zan fito ba zan dade ba.
Ya shige toilet din da sauri ita kuma ta tashi ta
dakko masa kayan da zai saka farar shirt ce da
bakin wando, ta feshe su da turare bai jima ba ya
fito daure da tawul sai wani akansa, ta yi saurin
tashi ta ciri tawul din kan nasa ta fara goge masa jikinsa, ta jashi gaban madubi ta shafe masa jikinsa,
da lafiyayyan cream me taushi da dadin kamshi, har
da shafa masa farar, hoda ta feshe shi da turare ta
ware masa kyansa ya karba ya saka.
"Au my love na manta ban sa maka man lebe ba"
ya sunkuyo da kansa ta shafa masa. "Inye! Nawan ba, ka kara kyau. Ya yi murmushi
tare da manna mata kiss a lebe ya riko ta suka taho
falo.kasa
suka sauko da kayan abincin ya hau kan kafet aka
baje don jawahir tafi sakewa.
Ta je firji ta tsiyayo hadadden lemon ta a je ya dau sanyi kuwa, ta zo ta ajiye ta dauki babban filet ta
bude fulas din ta sako musu sakwarar ta bude
miyar yayin da kamshinta ya bugi hancin Haidar ya
limshe ido yunwarsa ta dawo sabuwa, ta bude
daya filas din shima ta zubo musu hadin curaram
naman da ta soya da kwai, ta bude farantin hadin salak ta kalli Haidar ta ce, "My love bismillah.
Ya kalle ta yana murmushi sannu bebyna na gode
miki Allah ya saka miki da alheri Ubangiji ya yi miki
albarka, burinki kullum ki faranta min ki yi min abin
da zai sani farin ciki.
"To my love in ban yi maka ba wa zan yi wa, ina alfahari, ina matukar farin ciki da baiwar da Allah ya
yi min ta haduwa da gwarzon masoyi
Suka fara cin abinci dole jawahir ta rinka kyalkyala
dariya saboda yanda Haidar ya ta karkare yana ta
ziri tare da suba santi.
Komai sai da suka ci su ka koshi suka yi kat da su. Jawahir ta rinka tsiyaya wa Haidar hadin lemon
yana sha yana zuba santi shi dai ba don ya ji cikinsa
yana barazanar fashewa ba da ba zai bar sha haka
ba.
Jawahir ta kwashe kayan ta mayar kicin Haidar ya
jingina da kujera ya mimmike kafa ya dauki romote din tibi yana danne dannan tashoshi.
Jawahir ta dawo ta zauna ya juyo ya kalle ta cike da
kulawa yana murmushi ya ce, "Ya aka yi ne
bebyna? Ta jawo jikinta ta kwanta a cinyarsa cike
da sangarta, ya sa hannunsa kasan mararta yana
shafawa ya cire dankwalinta yana yaba kyan gashinta ya koma shafa kumatunta yana yaba
santsin fatarta da taushin jikinta kamar auduga.
Ya dora hannunsa kan kirjinta yana shafawa tare
da limshe ido jawahir ta ture hannunsa tare da
cewar "Meye haka kake yi a jikin ta tsitsiyar
kwaila.?" Ya yi saurin rufe mata baki da nasa ya dinga sumbatarta yana ruda mata jiki da wasanni
har sai da ya tabbatar ta manta da maganar
tukunna ya cikata.
Ikon Allah kenan duk yanda jawahir ta tsani
halayyar Haidar ba sa shiri da juna ba sa son
junansu, yau ga shi sun fi kowa kaunar junansu. Halayyar Haidar da jawahir ta tsana ta muskilanci da
kasaita da jan aji tare da rashin hayaniya ko
kwarniya yau tafi kowa murna da alfahari da
muskilancin Haidar da daukan kansa hade da
isarsa da kasaitarsa.
Tun da babu wata budurwa da ta isheshi kallo bare a kai gabatun magana har ya furta mata so, bata isa
ba kowacce.
So, kauna, aminci, yarda, shakuwa, duk ya tara su
ga tauraruwarsa jawahir. Bangaren Haidar kuwa
kullum sai ya yi wa iyayensa addu'a da fatan
gamawarsu da duniya lafiya saboda yanda suka hada shi aure da jawahir yanda da ya tsani
halayyarta ta miskilanci yau ga iyayi shagwaba.
Yanzu ga shi sun zamo abin alfaharinsa don suna
dada hura wutar kaunar jawahir a zuciyarsa.
Hakika ya yi sa'a da ace da samun kammalalliyar
mace ga kyau ga tsafta ga addini, ga usuli me kyau. Allah ya yi mata baiwa kala-kala na iya furta kalami
wanda lokaci daya zata siye zuciyar mai sauraronta.
Abu na biyu ta iya sahirtaccen kallo wanda zai jawo
afkawar mutum kogin begenta. Abu na uku ta iya
kissa da mutum ya so ta ko da baya ksunarta. Abu
na hudu yarinya ce me nutsuwa ga ta da ladabi da biyayya ga hakuri da tawakkali duk ta tara su.
Abu na biyar ta iya nau'ika na girki da abubuwan
sha ga ta da zakin hannu don duk wanda ya ci
girkin ta yai ta zuba santi da ya bawa kenan.
Abu na shida ta iya kwalliya gwanace wajen amfani
da hadaddun turaruka masu dadin kamshi, da san sutturar da ta dace ta saka

Please Login or Register in order to submit comment