Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na samu matar aure, ko kunason cemin kun manta da Zaytoon ne?" Idanu Hayatuddeen yaɗan zaro cikin mamaki yace.
"Wai kana nufi Zaytoon beauty kakeso, ƴar fada ce fa".
Dariya sosai Zakariyya yayi tare da cewa.
"Am so what dan ita ƴar sarki ce, nidai inasonta kuma itama tana sona kuma wallahi Insha Allah Saina aureta, nasan Baba Malam zai shigemini gaba, kuma kasan age mate ɗin Zarah'n ka ne, dan itama yanzu take shekaranta na kusa dana ƙarshe a secondary school, ni dai kam zama corper yayimin amfani a rayuwata dan yacillani zuwa school me daraja, har na gano gwanata." Dariya sukayi dukansu, Zaleeha dake jinsu itama dariya tayi, dan tajima da sanin labarin Zaytoon awajen Zakariyya, kasancewar baya ɓoye mata komai nasa, kafun yayi komai saiya faɗa mata.
Hira sukayi sosai. Haka dai yamma nayi suka watse, Inda ya rage saura Zakariyya shi kaɗai, dan shine zai raka Hayatuddeen ɗin wajen Zarah.
Da Misalin ƙarfe huɗu na yamma kuwa suka nufi gidan su Zarah'n, bayan kowannensu yasha kwalliya cikin tsadaddiyar shadda me kyau.
Koda suka isa gidan su Zarah'n, har cikin falon Babanta akayi musu iso, saida aka kawo musu kayan taɓawa kafun Zarah'n ta samu isowa, tayi kyau sosai abunta cikin shigar riga da zani na atamfar dake jikinta, inda ta yane jikinta da mayafi me kyau, masha Allah tayi kyau sosai, haka Hayatuddeen ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta.
Aladabce ta gaishesu, Zakariyya ya amsa mata fuska asake, idanu ya kashewa Hayatuddeen alaman zaɓin nasa yayi sosai, sannan ya tashi ya basu waje dansuyi zancen su cikin salama. Ganin Zakariyya ya fita ne yasa Hayatuddeen ci gaba da kallon Zarah'n yana sakin murmushi. Jin shirune yasa Zarah taɗan ɗago kai ta saci kallonsa, ganin ita yake kallo yasa ta kawar da kanta gefe tana murmushi. Shiɗin ma murmushin yayi, cikin salon jan hankalinta yace.
"Sannunki da zuwa Amaryata".
ɗago kai tayi taɗan kallesa da mamaki, dan bata tsammaci tun daga yanzu zai ƙirata da sunan amarya ba.
Ganin ta kalleshi ne yasa cikin ƙwarin guiwa yace. "Yess ke amaryata ce, ko kina musu da hakanne ƴan mata, sarauniyar murguɗa baki".
Dariya ne yazo mata amma saitayi murmushi, cikin ranta wani irin daɗi takeji, dan tabbas ta kamu da soyayyan Hayatuddeen ɗin, dan bakaɗan ba yake burgeta, musamman idan yana juya idanunsa like Hamma Saif, abun yana mata kyau sosai. Ganin yanda take ta rurrufe fuskane yasa Hayatuddeen soma yi mata hira, wani lokaci tayi murmushi wani lokacin kuma maganan nata baya wuce.
"Eh ko a'a". ahaka dai sukayi hiran ƙarfe 5 dai-dai ya mata sallama ya tafi, koda yazo tafiya ledan da Ummi ta basa wanda yake cike da kayan shafa ya bata, ƙin amsa tayi kwata kwata, hakanne yasa ya ajiye mata anan cikin falon ya tafi.
Ko acikin mota hiran Zarah'n sukayi shida Zakariyya, ahaka har suka isa gida Hayatuddeen yanata zumuɗi kamar ance masa gibene auren...!






By
*GARKUWAR FULANI*
Littafina na kuɗine biya ɗarinki uku kacal ki karanta ba tare da haƙƙin kowa a kankiba turo katin mtn na ɗari uku ta wannan layin 09097853276.

Koda suka ƙarasa gida kuwa, nan cikin falo suka zauna, tare da soma fara bawa Ummi labarin irin karramawan da akayi musu agidan su Zarah'n, sosai Ummi taji daɗi dan taji ajikinta cewa tayi sa'an surukai na kwarai, saidai fatan Allah ya nuna mana lokacin biki.
Haka dai suka ɗan taɓa hiransu a falon Ummin, kafun daga bisani Zakariyya ya tashi ya tafi, inda Hayatuddeen ya rakasa har waje, saida ya shiga motarsa sannan ya dawo gida.

Tofa haka rayuwa ta kasance, tun daga wannan ranan sai ya zamana duk ƙarshen sati Hayatuddeen yakanje zance gidan su Zarah, Masha Allah kuma dan yasamu karɓuwa sosai awajenta, haka ma iyayenta, tun bata sakewa dashi har ya zamana ayanzu sun zama tamkar wasu abokai saboda shaƙuwa.

Bayan wata ɗaya da bashi zarah ne ya soma service ɗinsa.
Sannu ahankali kuma yake tafiyar da service ɗin nasa yanda ya kamata, dan dukansu acikin Gombe suke service ɗinsu, Khamis da Imran ne kawai aka turasu kudu, amma suma suna ɗan leƙowa gida time to time.
Haka dai rayuwa ta miƙa, kwanaki da watanni na wucewa, yayinda abubuwa da yawa na faruwa, rayuwa tayiwa kowa daɗi.

***
BAYAN SHEKARU UKU. Alhamdulillahi rayuwa ta cigaba da tafiyawa familyn cikin kwanciyar hankali da salama, abubuwan daɗi suna ta faruwa.
Ta ɓangaren Saifuddeen rayuwa ta miƙa masa sosai, budi da alkhairi suna ta shigo masa, ya sake haɓaka yazama babban me arziki da rufin asirin Allah ya tabbata NAKASA BA KASAWA BACE.

Inda acikin shekarun da suka wuce ɗinne, Zaleeha ta koma taci gaba da aikinta.
Ta kuma sake samun ciki ta haifi ɗanta na Miji, wanda yaci sunan Aleeyu, inda akayiwa Baffa Ali takwara, ana kiranshi Haydar.
Ranar da Haydar ya cika shekara biyu ta kuma haifi ƙanwarsa, Wacce Saifudddeen ya yasa mata suna Aysha, ana kiranta Aish itama yanzu shekaranta ɗaya cib.
Yanzu yaran Zaleeha biyar Khareem Khasim Khausar Haydar autan Aish.
Bayan Zaleehan ta haihu kusan da shekara ɗaya ne Ameena ma ta haifo ƴarta mace me kama da ita sak,
Yayinda yanzu yaran Ameena uku Adeel Abbi Rahma.
farincikin da familyn sukayi nasamun ƙaruwa ba ɗan kaɗan bane.
Ɓangaren su Khareem da Ƙaseem Da Khausar Haydar kuwa sun ƙara girma sosai, yayinda asalin kyawunsu ke ƙara bayyana, zuwa yanzu dukansu babu wanda ba a sakashi a makaranta ba, Khausar kuwa kullum ƙara girma take, ga wani irin fitinannen kyaun da take tasowa dashi, kowa ya ganta saidai kaji yana cewa.
"Masha Allah." dan yarinyace me shiga rai, gata da yawan fara'a. Adeel ma ya sake girma abunsa, still kuma har yanzu komai nasa Amminsa ne, Zaleeha ta zama kamar itace ta haifesa, dan komai nasa yana wajenta, akoda yaushe kuma ko unguwa zataje matuƙar basu da school to yana naniƙe da ita.
Abbi ma da Rahma suma yawanci sashin Zaleeha suke,
ba abun dake ƙara sanya su jin daɗi kaman yanda kan ƴaƴan nasu suke ahaɗe, basa taɓa kyarar juna, kowani yaro yana son ɗan uwansa. Akuma cikin shekarun da suka wuce ɗinne akayi bikin Zakariyya da amaryarsa ƴar Sarki wato Zaytoon, wanda suke ƙira da Beauty, saboda kyawunta, Zaytoon yarinyace me hankali da nutsuwa, ga kuma iya girmama nagaba da ita.

Zuwa yanzu Zakariyya da Hayatuddeen harma dasu Khamis sun tsaya akan ƙafafunsu, dan kuwa Zakariyya baiyi aure bama saida ya tabbatar da ya zama cikakken lowyer ya kama office ɗinsa na nusamman, inda koda ya tashi Aure wanda tare akayi dana Ya Habu Yaya Ahmad ne ya saya musu wasu haɗaɗɗen gida anan cikin G.R.A ɗin, basu kuma da wani nisa da gidan Baba Malam, gidajene me kyaun gaske.

Hayatudeen ma dai buri ya cika dan yanzu haka yana aiki a babban branch ɗin U.B.A Bank, wanda duk wata yake ɗiban 300k amatsayin Salary'nsa, Alhamdulillahi dan yanajin daɗin rayuwarsa, dan ba a iya aikin bankin ya tsaya ba, Hamma Saif ya ware masa dukiyarsa wanda yake na gadonsa ne, bai karɓa ba saidai yace aci gaba da juya musu kaman yanda akeyi adacan baya.
Soyayya kuwa shida Zarah sai abun da yayi gaba yayinda ita kuwa har ta fara karatu a F,C,E Zaytoon kuma na G.S.U.

Sosai Hayatuddeen ke rawan ƙafa wa bikin dan kuwa yanzu har ansaka ranan biki, ankai lefe anyi komai, ko awajen lefe baƙaramin bajinta yayi ba, dan setin akwatuna 16 yayi mata, kowanne shaƙe da kaya masu kyau da tsada, abun saidai ace masha Allah.

Khamis ma ya zama doctor yana aiki awani babban privet hospitall wanda yake mallakin Babansa ne, sai su Imran, Sulaiman, Isma'il, suma kowannensu ya kama aikinsa haiƙan, masu aikin gwamnati nayi haka ma waƴanda suka faɗa kasuwa sunayi, Abun dai saidai ace masha Allah kuma duk sunyi aure Hayatuddeen ne kaɗai ya rage.

Yau ya rage bikin Hayatuddeen saura sati ɗaya rak, inda gaba ɗaya familyɗin suke ta hidima da kuma shirye shiryen biki, sunyi anko yafi kala shida, kowa ji yake da auren na Hayatuddeen, Saifuddeen da kansa ya biyawa Hayatuddeen ɗin sadaki naira 200k, inda kuma yasa aka sake gyaran gidan nasu, tuni dama shi ya rushe ɓangarensa ya maidashi gidan sama inda tura karshine a sama,
Adeel da Khareem Khasim Haydar da Abbi kuwa ya bar musu sashinsa na da ɗin dan yace yafi son duk motsin yaransa a kunnensa, yaran matan kuwa ko wacce tana tare da uwarta duk dama duk sunfi zama a sashin Ummee.

Kasancewar asama nan cikin sashin Ummi inda su Raleeya suka tashi, nan Hayatuddeen zai zauna da Zahrah'n sa, hakan yasa aka sake ƙawata wajen, aka sabunta komai na wajen ya zama sabo dal, ranan da akazo akayiwa Zarah'n jere kuwa ba ƙaramin kyau sashin ya ƙara ba, dan sosai iyayenta suka kashe mata kuɗi wajen saya mata tsadaddun furnitures da kuma kayan kitchine, kowa yaga jeren kuwa sai ya yaba.

Yau take laraba inda za a gudanar da haɗaɗɗiyan Kamu, da yamma kuwa da misalin ƙarfe huɗu su Zaleeha suka tafi wajen Kamu, bayan sun tsantsara adonsu me kyau da burgewa, Zaleeha sai sake murjewa take tana zama wata haɗaɗɗiyar mace da ita, sam yanayin girma ko wani manyanta bai bayyana ajikinta ba, haka zalika ko mace ce ƴar uwarta ta kalleta saita kuma dan tasan Zaleeha macece iya mace, kyau, diri, sura, duk ta haɗa, hakanne yasa ko da yaushe Saifuddeen yake mutowa akanta, domin har yanzu bata sanja ba, tana nan a Zaleehanta nada, me kyawun jiki dana fuska, uwa uba zaƙi kamar zuma.

Gurin kamu fa yayi guri, an kawata ko ina dake wajen da haɗaɗɗen decoration, pink nd sky, wato kalan kayan ango da Amarya kenan, wanda suka sha kyau har suka gaji, kallo ɗaya zaka musu kaga zallan dacewarsu da juna, tabbas hayatuddeen yayi dacen mace, dan kowa yasan Zarah yarinyace me hankali, da kuma sanyin rai, baruwanta da wasu ƴan ƙananun fitina.
Kamu yayi yanda akeso, inda su Zaleeha sukayi musu ɓarin kuɗi wajen liƙi, Raleeya ma ta taka rawar gani sosai, duk da cewa itama yanzu tana da ciki, wanda dukansa bai wuce 5 month ba, Ahmad kuwa ji yake da cikin sosai, shiyasa ma duk inda zataje yan liƙe da ita, wai bayason wani abu ya sameta.
Adda Rahama ma tazo wajen kamu'n, inda ta nunawa ɗan autan nasu gata sosai, haka dai aka watse a kamu zuciyar kowa cike da farinciki.

Washegari Alhamis kuwa mothers day akayi, wanda Zaleeha ne da kanta ta shiryawa su Ummi, da kuma mahaifiyar Zahrah da sauran dangi, abun kuwa ya ƙawatar sosai, anci ansha sannan angaggaisa da juna, abun dai yayi matuƙa, har akatashi zuciyar iyayen amarya da ango fari tas.
Ranan Jumma'ane da yamma aka gudanar da haɗaɗiyar Walima, wanda acikin familyn su Saifuddeen babu wanda bai samu halasta ba, abun saidai ace masha Allah, yanayin yanda Zaleeha tayi kyau awajen Waliman ne yasa duk inda ta gilma, matan dabasu santa ba suke binta da ido.
Raihana wanda tun ana biki saura sati ɗaya tazo, zuwa yanzu babu wani rashin fahimta atsakaninta da Zaleeha'n, hasalima shiri suke sosai da sosai.
Hannun Zaleehan ta riƙo cikin salon tsokana tace. "Matarnan kizo ki faɗamin wai miye sirrin ne, naga duk inda kikayi idanun matane ke rakaki, wato da wanka da kwalliya kike saye mana zuciyar Hamman mu ko?".
Dariya Zaleeha tayi, tare da cewa.
"Ke zan tambaya miye sirrin ai, gashi sai haihuwa kike amma kinƙi tsufa, then har yanzu banji Saminu yana maganan ƙara aure ba." Dariya suka sa dukansu, Raihana ne takai mata dukan wasa, cikin dariya tace.
"Wallahi dagani ba ƙari."
Haka dai aka tashi a walima bayan anyi wa'azi mai ratsa zuciya, koda suka koma gida yau Ameena itace da Saifuddeen, duk da yasan cewar agajiye take kuwa bai ɗaga mata ƙafa ba, saida suka morewa daren na yau kafun sukayi bacci.

Washegari asabar.
Damisalin ƙarfe sha ɗaya dai-dai dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren Hayatuddeen da kuma Zarah, wanda yasamu halartan manyan mutane da dama, dan har abokan aikin Saifuddeen saida suka halarci ga auren.
Hayatuddeen yasha kyau abunsa cikin farar getzner, gefensa kuwa amininsa kuma ɗan uwansa ne wato Zakariyya shiɗin ma dai yasha kyau abunsa, gasu Imran, Khamis, Isma'il, Sulaiman, duk suma sunsha adonsu, kowannensu yana cike da farincikin auren abokin nasu.

Koda yamma tayi ƙarfe huɗu akaje aka ɗaukowa Hayatuddeen matarsa, wanda Saifuddeen da kansa yaje ɗaukowa autan Ummenshi matarsa, acikin motarsa kuwa akasaka Zarah'n. Direct gidan Ummi aka kawota, inda Ummi da kuma su aunty Mina Goggo Dada, Aunty Kubra, Umman Ishaq, sukayiwa amarya da ƴan uwanta tarba me kyau.

Karfe 8 na dare dai-dai jama'ar gidan suka fara shirin zuwa wajen diner, wanda za'a gudanar a Medugu Hall, musamman aka ɗauko me meckup ta shirya amarya, inda ango ma yasha kyau cikin tsadaddiyar shaddansa wanda take shige da kalan kayan da amaryarsa ta sanya.

Hamma Saif ma wata blue din getzner me tsada ya sanya, wanda tayi masa kyau sosai, hakanne yasa Zaleeha da Ameena ma sanya blue lace me kyau da tsadar gaske, wanda yake shine ankon diner'n.
Adda Rahama, Raihana, Raleeya, suma duk blue lace suka saka wanda yayi musu kyau sosai.
Haka ma abokan Hayatuddeen dukansu anko sukayi na farar shadda, da blue ɗin aiki.
Zakariyya ma farar shadda yasaka, inda Zaytoon ɗin tasa blue ɗin lace, tayi kyau itama sosai, dan kuwa tana da shigan ƙaramin ciki ajikinta.

Koda suka ƙarasa wajen diner'n, basu wani ɓata lokaci ba MC ya soma gabatar da tsare tsaren diner'n, inda yake ƙiran ƴan uwa suna nunawa ango Hayatuddeen da amaryarsa gata.

Lokacin da aka buƙaci Hamma Saif daya fito da matansa zuwa kan high table, baƙaramin ɓarin kuɗi sukayiwa Hayatuddeen da Zarah'n ba, kuɗi suka zuba musu sosai, Hamma Saif kuwa har da dala yayiwa Hayatuddeen liƙi.
Su Adda Rahama ma sun taka rawar gani sosai awajen diner, Ahmad Ishaq, Salisu, Warisu, Saminu, Mudassir, Jabeer, Hisham ma ba abarsu abaya ba dasu da matansu ma sunyiwa autan Umme ɓarin naira.

Ƙarfe 10 dai-dai aka tashi awajen diner'n, kowa ya nufi gida, dan daga ranan bikin ya ƙare.
Koda suka dawo gida Hamma Saif kama matansa yayi suka wuce side ɗinsu.
Hayatuddeen kuwa su Zakariyya ne suka rakashi wajen amaryarsa, saida suka sayi baki kafun sukayi musu sallama, Har compound ɗin gidan Hayatuddeen ya rakosu, sam bakinsa yaƙi rufuwa, su Zakariyya sai tsiya suke masa.
Koda ya dawo ɗakin akan gado ya samu Zarah'n ta naɗe jikinta acikin mayafi, akusa da ita ya zauna tare da kamo hannunta, ya murza ƴan yatsunta, ɗayan hannunsa yasa yaɗan ɗage mayafin dake kanta, ɗago fuskarta tayi, hakan yasa suka sakarwa junansu murmushi. Hannayensa ya buɗe alaman ta shiga jikinsa, akunyace taɗan matso kusa dashi, jawota yayi ya rungumeta atare suka sauƙe ajiyar zuciya, farinciki sukeji acikin zuciyarsu sosai da sosai cikin shauƙi Hayatuddeen ya jawo hannunta, al'wala sukaje sukayi sannan suka fito sukayi nafila kamar yadda addininmu ya koyar damu, kazar ci kici inci ya bata ta ɗanci,
kana tasha badarar daya bata daga nan ya jawota suka hau bisa gado.

Acan ɓangaren Saifudeen kuwa, acikin babban falonsa suka zauna shida matansa, kansa ya ɗaura akan cinyar Zaleeeha, yayinda ya kamo hannun Ameena dake zaune akan sofa.
Cikin ɗan gajiya Ameena ta miƙe tare da cewa.
"Saida safe".
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Sai da safe a ina ɗin kece da shida".
Cikin zaro ido Ameena tace.
"Wayyo Allah na rufa min asiri kin manta na fita yau ke zaki shiga rabani da wannan zala memmen mijin naki Ƴaƴan ko shekara ɗaya bata cikaba, gwara ke ko yanzu kika yaye Aish ta kai yaye".
A hankali ya miƙe zaune ya zuba musu idanu tare da tura baki fuska a shogoɓe yace.
"Har haka na zama marar gata guduna kukeyi, ba matsala ta uku data huɗu na bisa hanya".
Ita dai Ameena murmushi tayi ta saɓa Rahma a kafaɗa ta fita.
Shi kuwa Hamma Saif harara ya watsawa Zaleeha ya miƙe ya nufi bedroom ɗinshi alamun yayi fushi, ita kuwa Zaleeha sauƙa tayi ta nufi ɗakinta.
Nono ta bawa Aish tasha da kyau kana ta mata wonka ta mata shirin bacci ta kaita ɗakin Inna Shatu wacce yanzu a gidan take gaba ɗaya ta dawo nan sashin Zaleeha ita ke kwana da ƴan dugui-dugui ensu.

Bayan ta kaitane tayi musu saida safe,
sannan ta dawo ɗakinta tayi wonka mai rai da lfy sannan ta ƙenƙesa ado da kwaliya cikin wata azabebbiyar rigar bacci mai fitinenne ƙamshi,
kana a hankali ta nufi ɗakin Hamma Saif ɗin.

A can sashin Ummee kuwa konce take bisa gadonta kausar ƴar shekaru huɗu an shiga na biyar ne,
ke gefenta suna ƴar hirarsu ta kaka da jiki, jikarma mafi soyuwa.

Shigowan Saifudddeen ne yasa Khausar miƙewa da gudu ta faɗa jikin Hamma Saif ɗin cikin muryarta irin ta mahaifiyarta sak tace.
"Oyoyo Baby".
Da yake yana yawan kiranta Baby shiyasa itama wasu lokutan takance mishi Baby,
shafa kanta yayi tare da cewa.
"Ummee da Ummee na bakuyi bacci ba".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Nasan zakazo kayi mana saida safe, kuma ban gankaba ai dole bazanyi bacci ga surutun Khausar, wai tana cemin in anyi Hutu zataje Abuja kuma wai fa dole tare dani zataje".
Dariya yayi cikin jin daɗi shaƙuwar Ummi da Khausar yace.
"Shike nan sai kuje tare, dan wlh Allah ko Ummi Khausar tafi sonki a kan Amminsu ma".
Dariya sukayi baki ɗaya ita kuma sai tsallenta take tayi,
suna cikin haka Zaleeha ta shigo,
bayan ta gaida Ummi ne ta ɗan kalli Khausar tare da haɗe fuska tace.
"Ke Khausar har yanzu bakiyi bacciba wato sai gobe ayita rigima dake kafin ki tafi school kiyitawa mutane kukan bacci bai isheki bako, maza wuce kije kiyi al'wala kizo ki kwanta".
Cikin sanyi tace.
"Ammi nayi al'walan".
hararan Zaleeha Saifudddeen yayi alamun meyasa zatayi mata tsawa,
cikin lallami ya shafa kan Khausar tare da cewa.
"Baby jeki konta ko".
Kai ta gyaɗa kana ta hau gado ta konta jikin Ummi,
ganin haka Hamma Saif yayiwa Umminshi saida safe kamar yadda ya saba kana ya fita ya tafi sashinsun.
hira kaɗan Zaleeha tayi da Ummi kana tabi bayanshi.

A sashin Hayatuddeen kuwa ai rawan kanshi bazai barshi ya ɗagawa Zahra ƙafaba.

A hankali take mgna cikin tsoronshi tace.
"Honey zafi nakeji".
kanshi ya cusa tsakanin wuyanta da kafaɗanta,
cikin rawan murya yace.
"My dear kiyi haƙuri, zanyi a hankali".
hannunta ta ɗan yayyarfa tare da ɗan saƙin ƙara jin yana ratsata.

A sashin Hamma Saif kuwa yana koma sade ɗinsu a falo ya zauna bisa 3 str kana ya ɗaura system ɗinshi kan cinyarshi yana aiki.

Jin sallamar Zaleeha ne yasashi ɗan nago kanshi ido ya lumshe da sauri lokacin data cire ƙaton hijabin daya suturce tsiraitacciyar rigar baccin dake jikinta,
fuska ya haɗe tare da tura baki ya kauda kanshi waishi a dole fushi yakeyi,
murmushi tayi kana a hankali ta tako ta iso gabansa,
hannu tasa ta ɗauke system ɗinshi ta ajiyeshi kan Stull dake gefensu,
bisa cinyarshin ta zauna suna fuskantar juna da kyau, cikin tura baki yace.
"Me hakan?".
hannu tasa ta kunce igiyoyin dake sarfe gaban rigartan cikin shauƙi tace.
"Jarabace hakan, ko nayi laifin matsowa kusa da mijina ne?".
Kanshi ya kawar tare da cewa.
"Zaki karya min cinyafa".
hannunshin ta kamo ta ɗaura kan ƙirjinta tare da cewa.
"Ƙugunka nake son ka karya".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ashe bani kaɗai bane jarabebbe".
hannunta tasa tana zuge zip ɗin boxes shi, cikin murmushi tace.
"Ba doleba inyi jarabar wannan abun daɗin da kake bani".
murmushi yayi mai kama da dariya, yace.
"Yau aikin nakine to in kina son in huce".
da sauri tasa hannu ta kamo nashi ta mannashi kan mararta tare da cewa.
"Dama fushi kakeyi dani ne?".
Kanshi ya jujjuya mata kamar ƙaramin yaro ko gaula hannunshi ya ƙara manna da mararta jin yadda taketa tsiyaya cikin sakartacciyar murya a hankali yace.
"Aaa a, bana fushi dake mai lamɓun daɗeeeeee".
ido ta ɗan zaro jiyo sautin muryar Zahran Hayatuddeen can ƙasa tana kuka.

Su kuwa duk da yadda Hayatuddeen ke binta a hankali yayin amsar budurcin saida tayi kukan zafin da ba'a rasaba,
cikin muryar kuka autan Ummen daya jishi a duniyar da bai taɓa shigaba yake cewa.
"Wayyo daɗi daɗi daɗi wayyo Ummina yau kam autanki ya girma".
ya ƙarishe mgnar da ɗan karfi, kasan cewar a sama suke kuma suma su Hamma Saif a sama suke kuma basuyi bacciba hakanne yasa sukaji duk surutan Autan Ummi.

Ita kuwa Ummi da Khausar tuni sunyi baccinsu.

Dariya Hamma Saif yayi tare da cewa.
"Wayyo My happiness nima bani kayan daɗi, kinji autan Umme can yaji kayan daɗi".
hannu Zaleeha tasa tana zare kayan jikinshi kana shima yana cire mata fingilar rigar jikinta,
cikin wata sassanyan murya Zaleeha tace.
"Zan baka kayan daɗinki Hamma Saif ɗina,Zaujil al'muazzam, in sha Allah ni takace har gaban Abadan, na godewa Allah da nayi halin ƳAR FULANI, domin da nayi sakaci da addu'a nabi zugar muguwar ƙawa da MI,WASMITI, NAYI NADAWA a tsawo rayuwata da ban dawo gidanka ba ƙarƙashin inuwar aure, da nayi babban asarar kamilin mijin tabbas na yardae NAMIJI BAYA KAƊAN dan da nabi shawarar ɗan ƙaramin ƙanina Zakariyya da ban guduba, da a hankali zan gane kaine nake nema mutumin da ya zame min jigon A TAUSAYAWA JUNA, ya zame min BANDIRAWO, a lokacin da na rasa mai taimako a a hannun mugu Dalla, koda yake na gane cewa RUBUTACCEN AL'AMARI shiyasa na gudu dan rabon Ummu Adeel da yaranta, guduwata yasa naiwa kaina kishiya, saida sanadin RIGAR KOWA mutuwa data ɗauke min Adda Maryam ta zama sanadin dawowata gidan mijina cikin HUKUMCIN ALLAH gashi ka zama uban ƴaƴana, kuma, tabbas na shaida zan kuma gayawa duniya wallahi tallahi NAKASA BA KASAWA BACE, dan wani nasasshenma yafi lafiyayyan na miji iya sarrafa mace,
Ni dai ka zame min babban GARKUWA a rayuwar duniya da ƙiyama in sha Allah". Tana gama ya miƙe tsam ruggumeda ita bedroom suka shiga suna shiga ya kontar da ita bisa gado da sauri ya dawo bakin ƙofa cikin sanyi yace.
"Bari in rufe mana ƙofa kada AYSHA ALIYU GARKUWA ta shigo ta samu abin rubutawa fans ɗinta masu son ganin gindin biro, to mu dai a rabu damu, masoyan AYSHA ALIYU GARKUWA ku bita a sabon littafinta da zatayi muku mai suna *GARKUWA*".
Daga nan ya rufe ƙofar ta yadda ban samu damar gani ko jin komaiba.

ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!


Na godewa Allah daya bani damar gama littafin nan lfy kamar

Please Login or Register in order to submit comment